Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 41

Sponsored Links

โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ
*BOOK 2*

*PAGE 41*

Washe gari kasawa AK yayi ya tsare tun asuba yake jiran saukowar Meenal k’asa, dan haka tana saukowa koh gaisuwa bai tsaya sun yi ba yake ce mata,

“Amma da wuri zaku fita daga gidan nan yau koh?”

“Eh ina kwana!”ta bashi amsa,

“Lafiya lau ya gajiyar ki”

“alhamdulillah”

“Idan zaki fita yau ki d’auki abubuwan da kika san zaki buk’ata dan bana son yawon nan tsakanin nan da can unguwar ki zauna a can d’in kawai idan an gama bikin kya dawo ni kuma in ina son ganin ki zan biyoki can d’in kindai ga yanda gidan nan ya cika da maza ni kuma bazan yarda kiyi ta faman shige da fice a gaban su ba,”

Allah mai iko dafa itace tace mishi zata je can d’in ta tare ta tabbata sai yayi tsalle ya dire kafin ya kafta mata kashedin cewa Shi sam bai yarda da hakan ba, amma gashi yanzun a sauk’ake ya sallama ta ai ita hakan ma gaba ta kaita, dan haka bata tsaya jayayya ba sai kawai ta amsa mishi da cewa
“to”

“Zo muje ki gaishe dasu Abba” ya fad’a yana jan hannun ta suka fice daga falon na Hajiya zuwa sashen su Abba Ahmad,
kai jama’a AK dai sam ya manta da wani abu wai Shi kunya domin dai can yaje gaban iyayen shi wai yana gabatar musu da Meenal din a matsayin sirikar su,
Shi bai san da batun zaman da akayi a gidan jiya ba dan lokacin baya gidan dan haka saiya kama rokon Abba Ahmad din cewa dama su yake jira suje su nemo mishi auren ta.

Da wurin suka wuce kamar yanda ya buk’ata ba tareda tarin abokan shi wadanda sukaci burin son ganin ko wacece Yarinyar da shi d’in wa kwarema ba, wannan rana dai ko ina ya zama busy gidan Hajiya suna ta shirin zuwa d’aurin auren Musty da neman auren AK kuma da zasu gabatar a gidan Malam bayan an gama d’aurin auren ga kuma shirin tarbar bak’in su wad’anda zasu taho neman auren Maimoon da sukeyi,

A gefen Sarki koh koda ya shiga gidan Malam yaso ne dama ya same Shi yayi mishi bayanin
Neman auren da za’aje mishi ayau sannan kuma yaso ace batun neman auren nashi ya fitane ta bakin Malam d’in ta yanda basai anyi ta surutai akan hakan ba sai dai kuma koda ya shiga bai iske Malam ba wai yayi sammakon zuwa kano wajen wani d’aurin auren shida Ya Sa’eed amma Baba Adamu da Baba Auta su suna gida,
Abune da bazai yuwuba wato yace zai kai batun ga Baba Auta duk da cewa yasan bazaik’i zuwa ba amma shi dai yana jin kunya gaskiya, dan haka bayan sun d’an tab’a hira shida Sheikh sai ya wuce sashen na Baba Adamu bayan gaisuwa sun d’an tab’a hira dashi dan gane da aikin Sarkin dama fannin kasuwancin su kafin Sarkin ya gyara zama ya fara korama Baba Adamun abunda ke tafe dashi,

“Baba wato dama aure nike so in k’ara!”

“Ah ah masha Allah kaga jarumi to yanzun fa ya ake ciki?”
Adamun ya tambaya yana taya shi murna

“Eh to da yike ita Yarinyar ita da iyayen ta dukan su a Lagos suke zama, ni kuma ganin idan na kawo maganar nan wajen ku kamar zan baku aiki na tashin da zakuyi kuje har can sai kawai naje ma Baba Brigadier da maganan shine shi kuma ya d’auki abokan shi suka je can gidan su Yarinyar suka samu mahaifin ta domin neman izini,to baban dai tun lokacin ya sheda musu cewa yayan shine waliyin ita Yarinyar kuma shi ba anan Nigeria yake zaune ba, dan haka sai ya had’asu da yayan nashi sukayi magana akan idan ya shigo sai suzo nan agabatar da komai daya dace, to jiya dana shigo gari naje can family house din su munyi magana da kakarta ta kuma shaida min cewa in za’aje atafi da komai na neman aure dan so take asa rana gaba d’aya,”

“Masha Allah kace yar Babbar gida ka nemo mana to ai bashi da komai mu ai hakan ya mana badai kai ka riga ka shirya ba?”

“A shirye nake duk yanda suka yanke yamin,”

“Ina ne family house din nasu?”

“Iyalan gidan Prof Abdul Khareem ne wanda ke tudun wada”

“Prof mahaifin Mommyn ku tanan gidan kake nufi?”

“Eh shi nake nufi”

Jin jina kai Baba Adamu yayi kafin ya kara jefo mishi tambaya cewa,
“Kuma su can d’in sunsan cewa kaine ke neman auren yarsu?”

“Eh sun sani dan dafarko ma ita Yarinyar taki saurarena amma da mukaje can gidan wajen Baban ta shi ya fahimce mu kakar suma kuma ta bada goyon baya”

“Wai kana so kace min Hajiya tasan da cewa kaine ke neman auren jikarta a karo na biyu kuma harta amince?” Baba Adamu ya fad’a cike da mamaki

“Eh ta sani, itama Meenal ta sani dan itace ma tayi min jagora wajen yar uwar nata”

“Ah to masha Allah dama ai amincewar nasu shi mukafi buk’ata, tashi kaje insha Allah za’a gabatar da komai yau basai gobe ba karka damu dasu iyayen ka na nan kuma ni zan musu bayanin komai da kaina,”

Su Brigadier sun iso shida abokan shi su biyu sai, kuma shida kanshi ya zauna da Malam Sulaiman ya mishi bayani akan dalilin su na zuwa garin,
ba k’aramin kunyar abinda Sarki ya aikata Malam Sulaiman yaji ba, ta ina ake haka fisabilillahi ka taso Baban matar ka tundaga wata uwa duniya ya taho har Zaria nema maka aure, shi dai yace babu inda zashi dan haka sai ya wakilta kanin shi Lawal da kuma Baba Adamu suka kwashi juna su biyar zuwa gidan Hajiya,
Sun samu tarba na girma da mutuntawa a wajen su Abba Ahmad babu b’ata lokaci kuma suka gabatar da komai daya dace na neman aure tun daga kan kud’in gaisuwar uwa da uba goro da cingum komai da ake buk’atar shi a wajen sun gabatar dan haka aka tsaida rana nan da wata uku idan Allah ya kaimu da rayuwa,
Sai bayan da komai ya kammala kafin shima Baba Usman ya bijiro ma da Baba Adamu zancen son zuwan da sukayi can wajen su ayau dan su nema ma AK auren Aminatu suma,
Sun d’anyi maganganu dan ya shaida musu cewa Malam baya nan amma tunda har Allah yasa su sunzo nan ai basai sun basu wani wahala ba kuma tunda dai har su yaran sun dai daita a tsakanin su zaiyi ma Malam bayani idan sun tashi zuwa sai suzo suma kamar dai haka da duk wani abun buk’ata na sanya rana shi dai ya basu Meenal duk da cewa dama Meenal din tasu ce.

To an dai watse taro cike da tarin farin ciki na murnar arzikin da ake shirin kullawa, tare dukan su suka wuce wajen d’aurin auren ana gama wa kuma su brigadier suka juya basu kwana ba duk da cewa Sarki yayi musu tayin kwanan,

A gurguje…..

Gefen Amarya da k’awayen ta lafiya lau sukaci gaba da gudanar da shagulgulan bikin su an d’aura auren Jamila da Angonta Mustapha da rana bayan an sauko daga masallacin juma’a da yamma aka gudanar da kayatacciyar walima wanda ango da amarya suka halarta tareda abokan su,
anayin sallan magrib kuma angwaye suka kawo mota suka kwashi Amarya da kawayen ta zuwa GRA gidan amarya anayin sallan ishsha’i kuma suka k’ara kwasan su bayan an k’ara shirya amaryar zuwa wajen dinner, sai da aka kwashe yan uwa kaf kafin Amarya da kawayen ta suka fita daga k’arshe gaskiyar yan magana da suke cewa ko wacce mace ranar auren ta ana k’ara mata kyau domin dai wani irin kyau mai d’aukar hankali Meelat ta tsatso a wannan ranar, a cikin wad’anda suka zo d’aukar amarya har da AK sai dai shi ya shaida musu cewa ba d’aukar Amaryar Musty yazo ba ah ah shi yaxo d’aukar nashi amaryar ne tunda har ubanta yace ya bashi ta riga ta zama nashi kuma yanda kuraye sukayi yawa a wajen gara ya kula da kayan shi,

Sultana da Maryam ne suka rik’o Meelat tareda wata yar uwar su Meelat din suka fito da ita Musty dake cikin motar da zasu saka amaryar da kanshi ya fito ya tari abinshi ya janye ta zuwa cikin motar, AK dake cikin nashi motar ne shima ya fito a sanda ya hango Faisal na k’okarin sa Sultana da Meenal su shiga cikin motar shi,
Gaban Meenal din yasha fuska a d’aure yake cewa “ina kike shirin zuwa da wannan kwalliyar na fuskar ki”

“Me kwalliya na yayi yanzun kuma?”

“Amma ai nace miki bana son kina goga wannan abun a bakin ki a sanda zaki shiga cikin mutane koh?”
Hankacin shi ya ciro daga cikin aljihun rigar shi,
“Nidai dan Allah karka goge min ina son abuna a haka” ta fad’a tana tura baki,
“Aminatu” wata daga cikin kawayen su dake tareda Maryam a wajen motar Sadeeq ta kirata, dan haka saita juya da sauri tabar wajen tana mishi gwalo, shi kuma sai ya k’arasa wajen Faisal suna magana,
K’awar nata ce ke tambayan ta bayan ta k’arasa inda suke,
“Friend amma dai wannan yayan ki ne koh?” Ta tambaya tana nuna mata AK,

“Eh Yayana ne” meenal ta bata amsa,
“Yana da mata?” Ta k’ara tambaya,
“Ah ah”

“Oh saurayi ne kenan bashi da mata?”ta k’ara tambaya tana gyad’a kai,

“Eh saurayine” meenal ta k’ara amsa mata,

“To dan Allah friend kid’an gabatar dani a gunshi mana wallahi nidai ina son shi yamin shine dai dai kalar mijin da nike son aure” ta k’asa fad’a tana karye wuya alamun rok’o,
Fuuuu Meenal ta wuce tabar wajen a fusace zuwa wajen da motar AK yake tana isa ta bud’e bayan motar ta shiga ta kullo k’ofar motar da k’arfi a fusace,

Sultana ce ta k’arasa inda Yarinyar take tana dariya ta dafa kafadarta take cewa,
“Ke baki san shine mijin da zata aura ba shine zaki wani kirata kice kina son mijinta, gaskiya dai baki kyauta ba”tana gama fad’ar hakan ta wuce abinta ta shige motar Faisal,
Shiko AK ganin da yayi ta wuce su a fusace da kuma yanda ta bud’e bayan motar ta shiga hakan ne yasa ya juya zuwa wajen motar shima ya bud’e bayan ya shiga ya sameta tana ta faman cika tana batsewa,

“Ya akayi ne? Meya sameki?”

Sai da ta watsa mishi harara mai lafiya tana turo baki tace “duk ba kai bane,”

“Ni kuma mai nayi?”

“Eh ai haka zakace da ace baka fito daga cikin motar ka shiga cikin yan mata ba ai da bazata ganka ba balle harta wani cemin wai tana sonka” ta fad’a tana kauda kai gefe,

Murmushi yayi ita kuma Sautin murmushin nashi ne yasa ta juyo taci gaba da masifa,
Shidai bai kulata ba hartayi ta gaji ashe wai shirun da yayi mata kuma yayi laifi dan haka sai kawai ta kama murfin kofar da niyyar bud’ewa ta fice,
Fincikota yayi ta fad’o cikin jikin shi kuma yasa hannu ya kulleta gam a jikin nashi,

“Yi hakuri to naji nayi laifi in ma kince karmuje can d’in ai sai muyi zaman mu basai munje ba”

“Tab duk wannan kwalliyar da nayi ne zan wani zauna a mota bikin Meelat dina akeyi fa”

“Oh dama kwalliyar badan ni akayi ba kenan anyi ne dan wasu su gani, ai kin tunanin ma d’azun nace a goge jan bakin nan kika k’i”
Mutsu mutsu ta fara a jikin nashi tana son kwacewa,

“Nidai kabar min kwalliya ta kuma kana ganin duk sun wuce fa”
Sakin ta yayi da sauri ya fice daga motar ya zagaya gefen direba ya zauna bayan ya gyara rigar shi data fara yamutse wa sakamakon mutstsukan data sha a wajen Meenal,
“Anan zaki zauna ko zaki dawo nan ne?” Ya tambaya batareda ya waigoba ya kunna motar, tsallakowa ita kuma tayi batareda ta fita ba ta dawo gaban motar,
Tissue ta yago bayan ta zauna ta goge jan bakin dake bakinta sai da ya fita tass kafin ta maye gurbin shi da lips glows ta d’an k’ara goga hoda kad’an ta kuma gyara zaman d’aurin kanta, da gefen ido yake kallon ta harta gama basu yi tafiya mai nisa ba suka isa inda ake gabatar da Dinner d’in koda suka isa amarya da ango sun shige babu wasu mutane sosai a waje,
Bude kofar shi yayi yafita kafin ya zagaya ya bud’e mata nata side din ya mik’a mata hannun shi ta kama ya fito da ita, gefe ya maidata ta jingina da jikin motar shi kuma yasa kanshi cikin motar wani chain ya ciro a cikin dashboard ya fito dashi a hannun shi sai da ya maida kofar motar ya rufe kafin ya riko hannun ta na hagu ya mak’ala mata chain din da aka k’awata shi da wasu irin duwatsu masu gyalgyali, d’ayan chain din dake tare dana hannun ta makala a nashi hannun shima sai kuma ya cire wani d’an karfe k’arami dake matsayin mabud’in chain din ya saka a cikin aljihun shi,
“Menene wannan d’in?”
Ta tambaya,

“Idon ma tambayi kin d’auka zan barki hannu sake ne in mun shiga kiyi ta yawo idon kowa a kanki?”

“Wai shi yasa kasamin ankwa a hannu? Kai dan Allah yaya to haka zamu shiga ciki mutane suna kallon mu kuma fa harda yan gidan mu a ciki”

“Eh haka na yanke kinga idan muka shiga a hakan duk wanda yagan ki yasan cewa matata ce a tareda ni”
Kamar ta bude baki tayi ta kurma ihu haka taji sai dai kuma idan tayi mishi kuka ai ta bada kanta dan haka kawai ta bud’e yar k’aramar Purse din dake rik’e a hannun ta ta ciro face mask guda biyu, ta mik’a mishi guda d’aya itama tasa d’aya,
“Me kikeyi da facemask a cikin purse kuma?”
“Shi nasa d’azun da zamuje wajen walima dan ni bani da niqab,”

“Kuma sai kikafi yin kyau ma a hakan”

Sun gudanar da Dinner lafiya har zuwa kusan 12 dare kafin taron ya tashi masu komawa gidan Amarya aka wuce dasu tare da amaryar sauran jama’a kuma suka koma unguwar malamai, andai yi biki lafiya an kuma watse yan nesa dana kusa kowa ya koma inda ya fito,

*Muje a gurguje*

Bayan kwana biyu su Baba Usman suna ta jiran kira daga Baba Adamu dan suji yaushe ne zasu je tunda dai Malam ya dawo,
Shi kuma a gefen Baba Adamu abubuwan ne suka d’an sha mishi kai dalilin hakan ko zama bai samu sunyi da Malam ba balle kuma ya shaida mishi yanda sukayi a yayin zuwan su tudun wada neman auren Moon dan ko labarin neman auren ma a bakin Baba Lawal jama’ar gidan sukaji haka ko suka dunga kucin cina zancen da cewa ba’a kyauta ma Aminatu ba taya Sarki kuma zai koma yace yar uwarta yake nema da aure kuma,
Sun daiyi maganganu wanda hatta da uwar gida bata so hakan ba sai dai kuma tunda an riga an gabatar da komai har an tsaida ranar biki sai kawai ta bisu da addu’a allah yasa ita Moon d’in ta zama cikon farin cikin da Sarki ya rasa tsayin shekaru,

A gefen Salman ko ya riga ya gama yanke hukuncin tun karar Malam tunda gashi daga uwa har uban shi babu wanda ya d’auki maganar shi nason auren Meenal da mahimmanci balle wanin su ya shige mishi gaba amma gashi shi ai Sarki yaga yar uwar Meenal din yana so har an bashi,
Gafen Aliyu daya Hashim suma duk sun shirya tsaf dan zuwa gabatar da kai a gaban Malam domin suma sun bincika anan gida sun gane cewa har yanzun ba’a fara zancen auren Aminatu a cikin gidan ba dan haka kowa ya yanke hukuncin gabatar da kanshi kawai wata kila shine mai rabo,

A gefen Sheikh Naseer da Meenal kam Alhamdulillah yanzun abubuwa sun d’anyi sauk’i ba kamar kwanan baya dako zaman inuwa d’aya bata son yi dashi ba,
Tun dawowar ta gidan lokacin bikin Meelat bata yarda ta koma gidan Hajiya ba har yanzun dan yanzun ya zama gidan sirikan ta, kullum safe da yamma da ita ake karatu a falon Baba Malam kuma Sheikh ne Malamin, sosai malam yasa ido yake lura da yanayin kusancin dake tsakanin ta da sheikh d’in yanda suke mu’amala ya matuk’ar kwantar mishi da hankali dan haka yanzun ne dai dai lokacin daya dace ya agabatar da nashi tsarin a kansu,
Dan haka ba tareda ya nemi shawara da kowa ba kawai wata rana bayan sun kammala karatun su da maza keyi da dare kamar kullum idan an idar da karatun wanda Sheikh ke gabatar wa shi kuma Malam sai ya rufe da addu’a,
To yauma dai bayan sun kammala karatun anyi addu’a har mazan sun fara shirin fita malam ya dakatar dasu, dan haka duk suka dawo cikin masallacin suka zazzauna suna jiran jin me zai gabatar musu,

Gyarar murya yayi kamar yanda ya saba aduk sanda zaiyi magana kafin ya daura a yayinda ya maida kallon shi kan Sheikh yake cewa,

“Nasan zakuyi mamakin yanda na dakatar daku daga tafiya kuyi hakuri wani d’an sanarwa nike son yi”

Ba komai Malam duk sukace suna cigaba da sauraren shi,
Shi kuma yaci gaba da cewa,
“Alhamdulillah nasan dukan ku nan dai kun wayi wannan bawan Allahn da a yanzun shine mai gabatar mana da karatun tukan da mukeyi, to masha Allah ga wadanda basu san ko waye shi d’in ba shi d’in dai yarona ne domin ko d’an da kanwata ta haifane a can k’asar larabawa ya gabatar da karatun tukan shi, dan haka nike son yau a yau a gaban dukan ku ku shaida ni Malam Al mustapha na bashi auren d’aya daga cikin yayana mata dan bazan yarda yaci gaba da zama a matsayin gwauro ko kuma yabar garin nan batareda mata ba”

Kabbara gaba d’aya masallacin ya d’auka jama’a na fatan alkhairi da cewa kwarai hakan ne ya dace dama bai kamata abar Babban mutum babu mata ba, wani dattijo ne shima ya mik’e yake k’ara sanarwa cema shima yana da yan mata a gidan shi yana kuma rokon alfarma ko sheikh zaizo gidan shi ya duba cikin yaran shi shima, tunda koba komai ai Babban mutum kamar Sheikh mace d’aya bazata wadace shiba,
Duk fa yanda sheikh yaso ya zame sun hana shi damar hakan dan wani ma daya tashi cewa yayi shi kuma ya bashi gidan da zai zauna da matan anan cikin garin Zaria, kai kyaututtuka dai kala da kala Sheikh yasha shi a wannan rana data zame mishi tsaka mai wuya dan shi dai bai san ko wacce yar malam yake nufi ba tunda bai kira suna ba,
Wai shi da yake batun tattarawa ya koma Abuja shine ake batun yi mishi tarko a Zaria shi ina shi ina auren mata har biyu fisabilillahi.
Haka aka watse karatun ranar kowa na farin ciki shi kuma aka barshi cikin jimami, a wannan daren kaf unguwar ya d’auka cewa ai Malam yaba Sheikh mata kowa idan ya tambaya cewa wacece a cikin yaran gidan aka ba sheikh din sai kowa yace bai sani ba,
Kafin gari ya waye labari ya isa kunnen Salman Aliyu harda Hashim,
Dan haka gari na wayewa Salman ne ya fara isa falon Malam ya gabatar da kanshi matsayin mai neman auren Aminatu,
Shigar shi d’akin da gabatar da kanshi babu jimawa sai ga Hashim koda ya shiga ya samu Salman kuma hakan bai hanashi gabatar da kanshi ba shima a gaban Malam matsayin mai neman auren Aminatu shima,
Babu wanda Malam yaba amsa a cikin su har Aliyu shima ya iso shima dai yanda suka gabatar da kansu hakan shima yayi,

Sai da gama jin ta bakin su dukan su kafin yace musu duk suyi hakuri su koma zai nemi ganin Aminatun zai neme su daga baya,

Ana cikin wannan al ajabi ahalin gidan master suma suka iso gidan da rana tsaka,
Bash ne da iyayen shi hudu maza,
Sun gabatar da kansu a matsayin masu neman auren Aminatu suma sun kuma k’ara daba Malam din labarin abinda ya faru a baya wato lokacin da shi Bash ya rasata da irin jinyar da yayi ta sanadin rashin ta,
Sannan suka shaida mishi cewa su dai a shirye suke suna fatan kuma wannan karan za’aba d’an su.

*Ummiee ce*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button