Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 42

Sponsored Links

โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ
*BOOK 2*

*PAGE 42*

To suma dai daga bash d’in har iyayen nashi bayan malam ya gama sauraren bayanan su hak’uri ya basu akan zai nemi jin ta bakin Meenal din dan haka zai neme su daga baya,
Jin hakan sai su kuma suka rok’e shi akan ko Bash din zai iya fara zuwa wajen Meenal d’in?,
Malam yasan ko yace musu ah ah indai yaran yanzun ne yasan sai shi Bash din ya nemi hanyar da zai samu ganawa da Meenal din dan haka sai kawai yace musu babu damuwa yaba Bash din damar zuwa ya gana da ita,
To sudai sun tafi da hope d’in cewa za’a dace dan haka suka tafi cikin farin ciki.

A cikin gidan Malam d’in ko dama tun cikin dare har zuwa wayewar gari kowa hasashe kawai yakeyi akan wacece Malam zai had’a aure da Sheikh domin dai yanzun haka a cikin gidan Malam kawai yanzun haka suna da yan mata guda d’ai d’ai har 5 wadanda dukan su sun isa aure, duk da a cikin su akwai wad’anda aka fara zancen auren su amma sun sam tsaf Malam yana iya canza ra’ayin shi,
Tun cikin daren har gari ya waye musu kawai akeyi wannan idan yace wacce malam zai ba sheikh sai wani kuma yace ah ah wacce kaza dai sukafi dacewa ita da Sheikh sudai iyayen su mata babu wacce tace ko kanzil su yaran gidan da sirikan gidan ne kawai keta faman yin hasashen su,duk wannan hasashen babu wanda ya kawo zancen had’in Meenal da Sheikh dan a ganin su tunda akwai yan mata a gidan bai zama lallai malam ya kawo ta a lissafi ba,
Sai gashi basu gama hasashen nasu ba suka fara ganin jerin gwanon da akema falon na Malam yau,
Duk abinda ya faru a gaban Farouq da Sa’eed ya faru saboda zuwan Salman yayi dai dai da suma suna cikin falon na Malam kuma har sai da Malam ya sallami su Salman din suma suka bar falon dan haka su biyun su suka shiga da labarin cikin gidan,
Koda suka shiga falon Mommy Hauwa musu kawai akeyi dan tun safe Sultana ta tasa Fauxieyerh a gaba da tsokana akan cewa tasan had’in da malam yayi ita yaba yayan ta, suma kuma sauran yan falon duk sai suka yarda da maganar Sultana duba da cewa kowa yasan cewa akwai shiri sosai a tsakanin Sheikh da Fauxieyerh dan haka sai suka sata a gaba da tsokana cikin masu tsokanarta kuma harda Meenal da Moon ita dai Moon cewa tayi wannan had’i yayi dai dai dan dama mace inba irin Fauxieyerh ba babu wacce zata iya zama da Ya Sheikh ta dadin rai haba shikenan mutum ya maida kanshi ina zaka masallaci ina ka fito islamiya, dan haka sun san Fauxieyerh cema ba kowa ba duk da cewa
A sashen Baba Auta akwai Fauxieyerh da Fatima, sashen Baba Adamu kuma Rayhan, sai can sashen Malam kuma Akwai Aisha da Asma’u, amma duk sauran dai basuga dacewar su da Sheikh ba sai Fauxieyerh,
Suna cikin hirar ne su ya Sa’eed suka shigo ko zama basuyi ba Sa’eed ya fara kiran sunan Meenal,
“Kai yayan mu tun baka zauna ba daga shigowa ka faramin kiran mafarauta gani nan fa ko ka fara makanta ne dan na lura idan Maman twins tana kusa baka gane mutane”
Ta fad’a daga inda take zaune akan kujera Sultana na tsaye ta bayan ta tana mata kitson kalaba a kanta,
Karasawa shi kuma yayi ya zauna bayan ya amsa gaisuwar da yan falon suka mishi ne yake cewa,
“Ke ya kukayi keda su Ya Hashim?”
Sai da ta wulwulga idonta cikin falon tana mishi alamu da idanu,

“Ni ba wannan ne a gabana ba dukan su yan falon dai imu imune babu bare,
Amma Meenal ai ce miki nayi idan baki ra’ayin ko d’aya daga cikin su to ki dakatar dasu daga zuwa kai maganar nan gaban Baba, wato ashe duk shawarar dana baki babu wacce kika d’auka to tunda haka kika zab’arma kanki yanzun ai sai ki shirya dan dukan su gasu can sunzo sun gabatar ma da Baba kansu a matsayin masu son auren ki ciki harda wancan mara kunyar Salman”
Natsuwa sauran yan cikin falon sukayi suna sauraron shi kamar su yake ba labarin ba Meenal ba, yana kai k’arshe suka had’a baki masu cewa “what” da zare ido nayi masu cewa “me” da zare ido suma sunayi ita dai Meenal kusan sumar zaune tayi,

“Shi Salman din ne yanzun haka yaje ma Baba da batun cewa ita Meenal din yake son aure?”
Aunty Murja wacce harda ita ake zaune a falon ta tambaya,

“Kwarai kuwa Anty bayan shima harda Aliyun Yola da kuma Ya Hashim, dukan su haka suka jera sahu a gaban Baba dukan su wai auren Meenal suke son yi dan sunji jiya yayi sanarwar cewa ya bama Sheikh mata a cikin yaran shi mata,
Gata a zaune Aunty nan na tashi na tafi har gidan Hajiya na sameta na bata shawara saboda su biyun ni suka fara sama akan maganar ta ni kuma na dakatar dasu daga zuwa wajen Baba nace su fara samun ta da maganar tukun, ban ma san cewa wai ashe harda Salman shima son ta yakeyi ba”
Kallon shi ya maida kan Meenal din yana mai cigaba da cewa.
“To ai gashi nan baki dakatar dasu ba sun taho sun aikata abinda na gudar miki kuma shi baba yace musu suje tukun sai yaji ta bakin ki kin san ko cikin ukun nan dole ki d’auki d’aya”

Daga bayan su Mommy Hauwa ta amsa da cewa,
“Babu wanda ya zamar mata dole a cikin su, domin nidai kaf din su banga mijin dazan iya aurama Meenal d’ina ba, in suna ganin dan sun kai maganar gaban Baban ku shine zaisa a tilasta mata ta zab’i d’aya daga cikin su to sunyi tumbur ai na fad’a tun a baya cewa Meenal ta gama yin aure a cikin ahalin nan kuma ta gama d’in kenan, wallahi koda ace akwai wanda take so a cikin su bazata aure shiba balle kuma nasan tunda ba nonon mahaukaciya tasha ba bazata ma fara ba,”
K’arasowa falon tayi fuska d’aure ta nemi kujera ta zauna,
Aunty Murja itama ta amsa da cewa “gaskiya kam kaf din su babu mijin auren Meenal anan yanzun shi Salman baiji kunyar Baban naku ba harya iya zuwa yace mishi yana son yabashi auren ita Meenal din?
Oh wato harya manta da abinda yayan shi yayi koh wato shi rasa kunya, ko koh dan yaga a lokacin babu abinda ya faru, shi kuma wancan Babban banzan Hashim haka ya wanko nashi kafafuwan tsofai tsofai shima ya taho da kanshi ba aike ba, to dai kaf cikin su garama Aliyun shima kuma duka duka yaushe yayi auren dahar yake neman k’ari, ko ko ita Meenal din ita k’adaice mace da duk zasu daka mata wawaso haka,
To wannan yak’in dai naki ne ke Meenal dan haka tun kafin tafiya tayi nisa gara ki shaida ma Baban naku cewa bakiga mijin aure a cikin suba,”

Cacaca haka falon ya k’ara rudewa gaba d’aya aka ture zancen Sheikh da Fauxieyerh da akeyi aka cigaba da caccakar zancen su Hashim barin ma da ita Meenal din ta basu labarin yanda tayi dasu duka ukun tun sanda suka tunkare ta da maganar, Hashim dai yafi kowa shan caccaka sai ko Salman duk da wasu suna ganin cewa shi Salman ai da ace ba Yayan shine ta aura da farko ba tofa da kosu sai su taya shi yak’i, ita kuma Mommy Hauwa dai ta tsaya akan bakanta kan cewa babu Meenal ba k’arayin wani aure a cikin wannan ahalin,
Duk da tasan batun neman auren Meenal da AK takeyi bata kawo zancen ba dan karma suce saboda d’an yayan ta yana son Meenal din ne yasa tace haka,
Magana dai koya akayi ta a gidan yawa sai ta fita, dan haka cikin lokaci k’ank’ani maganar ta bazu a cikin gidan dama mak’ota, Mommy da kanta tace Meenal din su koma can gidan Hajiya dan tasan tunda akayi haka tofa dole Malam zai nemi jin ta bakin Meenal din,
Ita dama Sultana abinda take so kenan dan tun d’azun take faman kiran wayar Hajiya amma abun haushi layin ta a kashe koya akayi Hajiya tabar wayarta ta mutu oho domin ita dai ko 98 percent gareta zatace a sa mata caji tafiso taga wayarta da 100 percent koda yaushe, ta kunsa gulma iya gulma jira kawai takeyi su isa ta fesa mata,
Itafa Sultana da Moon yanda suka damu ita uwar gayyar ko a jikinta wannan karon tunda ta samu goyon bayan Mommy Hauwa tasan bazata yarda a k’ara mata wani auren dole ba koda ko ace bata da tsayayyen saurayi balle kuma ita da take da AK,

Suma da suka d’aga hankali suna dai tausaya mata ne kawai amma ita jikinta yana bata cewa sam Baban ta Malam bazai k’ara maimaita kuskeren baya a karo na biyu ba, badai yace musu duk suje sai yaji ta bakinta bane?
To ita kuma abu mai sauk’i kalmar eh ne ko ah ah fa, ya rabata dasu dukan su,

Abinda kamar wanda dama can an riga an tsara shine domin ganin ahalin Bash sai ya k’ara ba kowa mamaki ace mace d’aya maza hudu sun gabatar da kansu a matsayin masu neman auren ta kuma duka a rana d’aya! Yau dai yan gidan Malam na ganin ikon Allah.

Yaro Malam ya aika sashen Baba Auta dan ya kira mishi Meenal tazo su gana da bash kafin su wuce,
Sai gashi yaron ya dawo mishi da amsar cewa ance Aunty Meenal tana tudun wada gidan Hajiya kaka,
Hakuri Malam yaba su akan cewa Ashe Meenal d’in bata gidan, dan haka dole suka wuce inda shi kuma Bash a ranshi ya yanke hukuncin cewa can gidan Hajiya zai bita tunda dai yanzun ya samu lasisin dazai tun kareta,
Nasan masu karatu zasuce to meya hana bash zuwa gareta tun kwanan baya? Abinda ya faru shine a sanda yabar gidan su Meelat gidan su ya koma,
Yana isa kuma da murnar shi da komai ya isa d’akin hajiyar su wacce ita kuma ganin shi cikin farin cikine yasa ta tambaya ya akayi ne tagan shi yana ta washe baki? ,
Babu b’ata lokaci shi kuma ya zauna ya zayyane mata ganin da yayi ma Meenal harma da bayanan daya samu akan ta na mutuwar auren ta,
Ta tausaya mishi kuma ta tayashi murna daga baya domin ita duk tsayin lokacin nan tayi zaton cewa shi bash din tuni ya dade da cire Meenal din a cikin zuciyar shi,
Amma irin farin cikin data ganshi a ciki yau saita gane cewa soyayyar Meenal din ashe ba mutuwa tayi ba dogon bacci dai tayi yanzun kuma ta taso,
Tana son d’anta dan haka take son farin cikin shi, ita bazataja da hukuncin Allah ba tunda tasan irin wahalan da Bash din yayi a shekarun baya wata kila yanzun dawowarta gareshi ya zama alkhairi a garesu baki d’aya,
Dan haka sai ta tuntube shi cewa to yaushe zaije ya k’ara gabatar da kanshi a wajen Meenal din karo na biyu?
Shi kuma sai yace mata baya son ya k’ara maimaita kuskuren da yayi a baya dan haka bazai tunkari Meenal d’inba har sai an nemo mishi izini a wajen iyayen ta,
An fara maganar cewa za’a tura can gidan Malam neman izini ne kuma a lokacin jikin Master ya motsa dan jinya yakeyi har yanzun ciwon nashi yakan d’an motsa mishi lokaci bayan lokaci,
Motsawar ciwon ne kuma yasa aka ajiye maganar zuwa gidan malam da sunan sai sun dawo daga ganin likita wanda harda Bash d’in suka tattara suka tafi, sunyi zaton tafiyar bazai jasu tsayin kwanaki ba sai dai kuma suna barin k’asa jikin ya k’ara rikece wa basu dai suka dawo k’asar ba sai jiya kuma suna dawowa a jiyan aka wakilta wadanda zasu taho tambaya gidan malam kuma yau suka iso yanzun zasu saurari kira daga malam ne kamar yanda yace musu.

Koda su sultana suka isa tudun wada Hajiya bata gida tana can gidan Dadah Turai, amma Sultana bata huta ba sai da tabi ta har can gidan,
A kofar gidan suka had’u ita Hajiya tana dawowa ita kuma Sultana tana k’ok’arin shiga,

“Ke kuma lafiya wato kin shigo gidan baki sameni ba shine bari ki biyo sahuna, to juya mu koma gani nan nima na fito in ma gulma kika gintso mu koma can muyi ta”

“Hajiya ai tunda kikaga na kasa zama na biyoki kema kin san cewa da walakin wai goro a cikin miya labari ne da d’umi d’umin shi yake tafe dani nayi ta kiran wayar ki tun ina unguwar malamai amma a kashe,”

“Ba dole kiji wayata a kashe ba yar nan, Allah ya had’ani da jikoki masu bak’ar barna, ina zaman zamana fa a cikin sashena d’an nan na wajen Hasana inda kika san an aiko shi haka ya biyo ni ban san uban me yakai wayata hannun shiba sai k’arar fad’uwarta kawai naji taratsatsa ya rotse kayan kwalbar a ties to dai haka na kwashe shi shida wayar bayan na zane mishi jiki tsaf da zabori nakai shi wajen uwar shi kuma na fad’a mata wallahi sabuwar waya fil nike bukata kafin nan da faduwar rana inba haka ba ran uban kowa saiya ba’ci dan nidai bazan d’auki Asara ba tunda bance ta saki d’anta ya biyoni har sashena ya nakashe min wayata yar shafa ba”
Suna tafe suna hira hat suka isa falon Hajiya, sai da Hajiya ta zauna sannan tace to ya akayi kinje kin taso keyata kuma bakice dani komai ba,

“Hajiya Ina aka kwana batun neman auren Meenal ne?” Sultana ta tambaya,

“Ke aini kin tuna min,
Nidai Allah ya had’ani da mashiriritan yara wallahi, kigafa tun ranar da akasa ranar auren Moon dasu Usman sukayi magana da Adamu a falon nan yace musu zai kai maganar gaban Malam idan ya basu lokaci sai suje agabatar da komai to nidai tun ranar banji wani ya k’ara tada maganar ba a cikin su,
Ke tsaya wani abu ya farune da kike tambaya ta?”

“Humm Hajiya ke kina nan kin saki baki to abubuwa suna can suna faruwa a gidan Malam”

“Me kuma ya faru yar nan?”

“Kinga Hajiya jiya da dare Malam yayi sanarwar cewa yaba Yayana Sheikh auren d’aya daga cikin yayan shi,
To wallahi tun daren jiyan muke canki canka, mun kaso gano wacce malam yake son had’asu da Ya Sheikh sai kuma kawai yau da safen nan sai ga jerin gwanon maza har uku sunje sun gabatar da kansu wajen Malam din da sunan wai suna son auren Meenal”

Katseta Hajiya tayi da cewa,
“Mazaje uku kuma daga ina aka samo su?”

“Kinga kanin Sarki Salman shiya fara zuwa dan dama tuntuni yake bibiyar Meenal din ita kuma ta taka mishi burki, todai tun baibar falon Malam ba saiga wani shi kuma wai Ya Hashim sai kuma Ya Aliyu shima”

“Uhumm sai shi kuma malam d’in yace dasu me?”

“Ce musu fa yayi wai suje duk zai neme su idan yaji ta bakin Meenal din, mu bamu san meke faruwa ba muna zaune suya Farouq ne suka shigo da labarin shine ita kuma Mommy Hauwa tace mu dawo nan”

“Ah lallai ma, to ai ba laifi su ai sunje tambaya ne koh?”
“Eh ” Sultana ta amsa,
“Toni kuma auren zan tura a nemo min shi a yau basai gobe ba bari ki gani ai da zafi zafi akan daki k’arfe allah ma yasa akwai sauran lokaci har yanzun tunda yanzun nema ake idar da sallan azahar”

Tana gama fad’in hakan ta fice daga falon,
Ita ko Sultana tsallen murna ta kamayi dan ita dama abinda take so kenan,
Ita dai haka nan kawai taji tana matuk’ar sha’awar ganin AK ya auri Meenal, dan haka sai ta nemi waje ta zauna ta lalubo wayarta ta danna ma number din AK kira,
Yanke kiran nata yayi kamar yanda ya saba sai shi kuma ya kirata daga baya,
Babu b’ata lokaci ta d’auka sukaci gaba da gaisawa,
“Nace ne dama bari in tambaya inji yaushe zaka shigo gari?”
“Wani abu ya faru ne Sultana?”

“Eh to gaskiya dai abubuwa na shirin faruwa zaifi kyau ace dai kana kusa”

“Bani labari maiya faru kuma karki boye min komai”

Gyara zama tayi ta kora mishi labarin abubuwan da suka faru tsakanin jiya da yau bata boye mishi komai ba,
Godiya yayi mata shi kuma akan cewa zai kamo hanya yanzun amma karta shaida ma Meenal din cewa sunyi waya,
Fatan Allah ya kiyaye hanya tayi mishi kafin suka sauka akan layi,

Hajiya ko tana fita sashen Abba Ahmad ta wuce kai tsaye, ta same shi yana cin abincin rana dan haka itama saita nemi waje ta zauna,

“Kai Ahmad nace ya kuke ciki ne akan maganar zuwa neman nan ne wai?”

“Hajiya ai kinsan shi Adamun cewa yayi yanda sukayi da Malam zai tuntub’e mu shi muke jira dai har yanzun”

“Toni na gaji da jira malam dai yana nan a gari dan haka yanzun nike so ku shirya k’afata kafarku muje a nemo auren nan insan a wata matsayar muke,
Haba jama’a wai inace da kune masu naci kullum kuna magana akan cewa yaron nan yak’i fadda matar aure yanzun kuma ya fidda amma magana sai tafiyar hawainiya take,
Ni inda ace tun farko nasan haka zaku b’atamin lokaci wallahi dako kusa bazan tsaya ina jiran isowar kuba tunda dai allah yasa ina da mutanen arzikin da zasu shigemin gaba wajen ganin abun nan ya tabbata dan haka yanzun ka d’aga waya ka kiramin Usman yazo idan ma kud’in da zakuyi hidimar kuke bakin cikin fitarwa a aljihun ku ni allah yasa na nemi kud’i kuma na tara tun baku da wayau,
Dan haka yazo yamin lissafi daga naira 1 zuwa adadin dazai isa a siya abun bukata na zuwa neman aure dan yau gidan nan ba’a bacci sai nasan ina muka kwana”

“Hajiya toki bari in tuntubi shi Adamun muji ta bakin shi tukun!”

“Ba Adamu ba Adumo kaji koh nace ba Adamu ba Adumo to bari kaji wallahi a yau d’in nan zaku ai watar da abinda nasa ku k’afata kuma kafarku dan karma ku dawo kuzo kuna sheqa min k’aryar abinda ba’ayi ba,”
Tana gama fad’in hakan ta fice daga sashen ta wuce sashen baba Usman cigewa tayi a falon ta fara kiran sunan shi,
Tare shida Umma suka fito falon,
“Biyoni muje” ta fad’a tana wucewa gaba dan haka sai ya take mata baya sashen Abba Ahmad suka k’ara komawa abinda ta fad’ama Abban shi ta k’ara maimaitawa a gaban Baba Usman ta kuma sashi ya kira samarin gidan akayi list na komai da ake buk’ata ya basu kud’i sukaje siyowa goro da cingum dama duk abinda ta lissafa akwai shi a kasuwar tudun wada dan haka yan aiken basu jimaba suka dawo da kaya nik’i niki, kafin dawowar su kuma ta shiga can gidan su Dadah ta taso keyar mazan gidan mutum biyu ta kuma sa Sultana ta kira mata Musty a waya tayi magana dashi akan cewa koma ina yake ko me yakeyi ya sake yazo gida ya sameta,

Gangami sosai Hajiya ta had’a bayan ta tabbatar da cewa komai ya kammala yanda take bukata ne kuma tasa suka shiga cikin mota suka bar gidan zuwa Unguwar Malamai.

To gadai Hajiya can tayi gangami, kuyi addu’a Allah yasa karta dawo sai ta amso auren jikokin ta Ameen please ๐Ÿ™.

*Ummiee ce*โœ๐Ÿผ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button