Sponsored Links
Duk Karfin Izzata Book 1Hausa NovelsHausa Novels and Love Stories

Duk karfin Izzata Book 1 Paga 2

Sponsored Links

Episode 2*

Khalid rike da hannu zahra suka fito daga part ɗin,Ammi suka nufi part ɗin Ummi suna tafiya suna hira kamar wasu friend, a dai dai kofar da zata sada su da part ɗin Ummi, su kayi karo da yusuf fiskar nan a daure kamar bai ma san menene dariyaba, nan take jikin zahra ya hau kerma, murya na rawa tache “inawuni yaya yusuf,bai bai amsa ba ya ra ɓa ta gefen su zai wuche, da sauri Khalid ya damki dam tsen hannun sa, juyowa Yusuf yayi yana kallan chikin idon Khalid ɗin “me kuma kake kallo na eh idan bazaka amsa gai suwar Zahra ba ni ba yayan ka bane dazaka raɓa gefe’na ka wuche ” a kule Yusuf yace sorry ykk “ban sani ba Khalid ya faɗa yana sakin hannun Yusuf ɗin,aiko kamar jira yake Khalid yasake sa da sauri ya wuche ya barsu tsaye, dawo da kallan sa Khalid yayi kan Zahra dake tsaye kamar zatayi fitsari a wando saboda tsoro”menene Auta,chikin rawar murya Zahra tace,”yaya Khalid shiyasa fa nache maka kai da Aunty farida da Aunty mardiya ne kawai kuke sona sai Aunty salma, kana ganin yaya Yusuf ko gaisuwa ta bai amsa ba bare ma ya tambayeni ko ina lfy,ta karisa maganar kamar zatayi kuka, kakalo murmushin dole Khalid yayi dan ko shi kansa Yusuf ya ɓata masa Rae “karki damu Auta muje mutafi hai ki rabu dasu tun da ni ina son ki kinji yayi maganar yana shafa kanta “to shike nan yaya Khalid muje, chiki suka nufa a kofar balon Ummi sukayi sallama kafin su shiga komai na chikin palon Ummi irin na Ammi ne har colour komai iri ɗaya

Wata kyakkyawar mata che zaune saman sofa mai zaman mutun 2 a gaban ta kuwa sofa table ne dake ɗauke da kwan dan fruit mai kyan gaske a hankali take gatsar Apple ɗin take hannun ta fara che itama tas kaman nin ta ɗaya da yusuf a kallan zata kai 36 years, da gudu Zahra ta tafi ta faɗa jikin ta tana faɗin Aunty “farida na dawo “kai Auta zaki balla ni ai, dari Zahra tayi tana faɗin to Aunty na tashi, karisa shigowa chikin palon Khalid yayi ya zauna saman sofa mai ma zaunin mutun 3 yana faɗin “Aunty babba barka da hutawa,murmushi Aunty farida tayi kafin tace ai kune manya yanzu na bar muku girman, da sauri Zahra ta miƙe zaune tana faɗin “Aunty farida harda ni, ki kabawa girman “eh Auta har dake mana,tsalle Zahra tayi, tana faɗin nima na zama babba yan zukam, murmushi kawai Khalid da Aunty farida keyi suna kallan irin farin chikin da kanwar tasu ke chiki

Wayar Aunty farida dake zaune kusa da Zahra yafara kara alamar shigowar kira,da sauri Zahra ta ɗau wayar tana faɗin ni zanyi picking call ɗin ni zanyi picking call ɗin,” to Auta yimana chewar Aunty farida tayi maganar tana kokarin ajiye Apple dake hannun ta a chikin kwandan fruit ɗin, takawo wayar Zahra tayi dai dai sai tin fuskar ta zatayi picking call ɗin, a sukwane tamiƙawa Aunty farida wayar ta hannun ta har kema yake, ansar wayar Aunty farida tayi tana kallan Zahra da mamaKi, dariya Khalid yayi kafin yace Auta lfy irin wan nan riki chewa haka DON ko Aryan ne suka kira wayar ko, Zahra dai shiru tayi bata che komai ba, zai faman zazzare ido take
Picking call ɗin Aunty farida tayi takara wayar a kunen’ta “hello Aryan ykk, daga ɗayan ɓangaren Aryan yace lfy lau Aunty babba ykk “ina lfy y prince, bai bata amsa ba sai dai yace “kinyi magana da Abba ne “aa bamuyi ba lfy dai koh ta tambaya a ɗan ruɗe “eh to lfy kedai in kinyi waya dashi sai muyi magana ” aa Aryan wlh ban yar daba za kasa nashiga tunani pls kafa ɗa min da wata matsala ne “aa Aunty farida babu komai ke dai ki kula mana da kanki kinji, bai jira amsar taba ya katse kiran, dagowa Aunty farida tayi tana kallan Zahra”Auta lfy kika nitsu haka “turo baki Zahra tayi tace ba komai, Khalid kuwa sai dariya yake musu dan yasan dalilin nisuwar Zahra, dawo da kallanta Aunty farida tayi tana faɗin lfy, bro kake kallan mu haka,” lfy lau kawai ina mamakin irin son damuke miki ne, duk zafin ran DON da Aryan in zasuyi magana dake sas sauta murya suke, idan ran DON ya ɓachi gaba ɗaya gd kai bama gd kawai ba gaba ɗaya family mu ba mai iya tin karar sa sai ke komai ɓachin ran da yake chiki inya ganki sai ya sas’sauta zuchiyar sa kike ɗai kike sashi ya chan za magana inyayi abun yana bani mamaki, murmushi Aunty farida tayi kafin tace kasan meyasa gaba ɗayan ku kuke kau nata “aa ban sani ba “saboda nima ina matikar kaunar ne, duk da ba iyayen mu ɗaya ba narike ku da zuchiya ɗaya “da sauri Zahra tace Aunty farida daman ba Abba bane ya haifi su yaya Khalid “eh Auta ba Abba bane marigayi bappa usman ne baban su yaya Khalid yaya Ahmad dakuma Aunty Salma, “kai Aunty farida to ya akayi haka ni ban san bappa usman ɗin bama chewar Zahra tafaɗa da mamaki a fuskar’ta “kai Auta kiche dai tarihi kike son sani to matso nabaki tarihin a gurguje dan zanje wajen Abba,kara matso kusa da Aunty farida Zahra tayi ta kasa kunne, Aunty farida ta gyara zama tafara magana kamar haka

*Abba su uku ne awajen baban su sarki khalid awan chan lokachin, Abba shine babba sai bappa usman sai bappa Aliyu ne ƙarami kakan mu shi ya haɗa auren Abba da Ummi na alokachin, baban Ummi shine sarkin katsina ansha biki sosai, bayan auren ummi na da Abba da shekara ɗaya Allah ya albarka che da samun Aihuwa ɗiya mace kuma bakowa bace face ni, ina da shakata biyu a duniya Ummi na ta haifi Mardiya, an haifi Mardiya da wata uku Abba yace zai kara Aure da farko Ummi na taki yar da amma daga baya sai ta aminche Abba ya auro yar sarkin gombe kuma itace Aunty amarya, bayan auren su da wata 10 Aunty Maryam ta haifi ɗiya mace Abba yasa mata suna maryam,alokachin ne kuma bappa usman yayi Aure ya Auri umma’n su Khalid itama data zo ya mace ta haifa, Abba ya shiga tunani da damuwa dan yana son ɗa namiji gashi shiru shiru daga Ummi har Aunty amarya ba wan da yasake Aihuwa, wani taro dasu Abba sukaje da kakan mu garin yola a chan yaga Ammi ya dage sai ita Ammi ba fulatanan ruga che iyayen ta sunki bawa Abba auren ta amma Abba yana che haka suka hakura suka bashi Auren Ammi a kasha biki auren Ammi da wata uku tasamu chiki a tare suka samu chiki da Umma’n su Khalid chikin Ammi na da wata 3 Aunty Amarya ma tasamu chiki chikin Aunty Amarya na da wata 4 Ummi na ma tana mu chiki kamar abun haɗin baki rana ɗaya Ammi da Umma’n Khalid su aihu Ammi ta haifi ɗa namiji Umma’n su Khalid ta haifi yan biyu namiji da mace, bappa Usman yayiwa kakan mu takwara yawa ɗan sa na mijin suna Khalid,macen kuma salma, Abba kuma ya sawa prince Safras musha murna sosai a satin da a ka haifi khalid da prince a satin kakan mu mace ta rasu musha kuka da bakin chiki sosai, kakan mu tana da wata uku da rasuwa Aunty Amarya ta haifi yan biyu Abba yasa musu suna Aryan da Aiman, Aryan suna da wata uku Ummi na ta haifi yusuf daga nanne basu sake hai huwaba, Khalid da salma na da shakara biyu Umma’n su ta haifi Ahmad, shiyasa kikaga da yaya prince yaya khalid yaya Aryan yaya Aiman yaya Yusuf dakuma yaya Ahmad sun taso kamar wasu ta gwaye dan dukkan su banda Ahmad ba wan da yabawa ɗan uwan da full 1 year, shiru shiru su Safras na da shakara uku Ammi ta haifi Fahad, Fahad na da shekara uku Ammi da Aunty Amarya suha aihu a tare kuma dukka ƴaƴa maza suka haifa, Abba yasa musu suna Umar da Haidar Umar na koyan zama kakan mu da bappa Usman sukayi haɗari a kan hanyar su na dawowa daga wani taro dasuka je maiduguri munji mutuwar bappa usman wan da har gobe ma inajin mutuwar bazan taba daina jin mutuwar bappa usman ba har nakoma ga Allah, tun lokachin da aka sanar da Umma bappa Usman ya rasu ta faɗi bata sake lfy ba har itama takoma ga Allah, Ammi ta ɗauki su Khalid ta haɗa su dasu prince tariƙe, Abba ne ya karɓi sarauta bayan mutuwar kakan mu sarki Khalid Abba ya karɓi sarauta wajen da shekara 5 Ammi ta haife ki tun daga kanki ba wanda yasake Aihuwa har yanzu to kinji ta kai chan chen tarihi idan idan kina san jin komai kine kisamu Ummi taba ki lbr Aunty farida ta karisa maganar tana sauke ajiyar zuchiya*

Ji su kayi daga bayan su ana faɗin ae basai tazo waje naba wan nan lbr dakika batama ya isa, murmushi sukayi gaba ɗayan su Khalid yace “ina wuni ummi “lfy lau baba saukar yau she Ummi tayi maganar tana kokarin zama saman sofa mai zaman mutun 1 “ɗazun mu kazo Ummi “to ina sauran ko kai ka ɗai kazo “Aunty farida tace aa Yusuf ya shigo kina bar chi ai daman shida yusuf ɗin da Aiman da Ahmad ne sukazo ƴa’ƴan basu zo ba,Aunty farida ta karisa maganar tana dariya, murmushi nasu irin na manya Ummi tayi tana faɗin ” kawai Ummi tayi batare datayi magana ba “Aunty tashi kije ki kiramin Haidar da Umar kinji chewar Aunty farida, miƙewa Zahra tayi jiki ba kwari ta fice daga palo, fita tayi daga ɓangaren Ummi gaba ɗaya, ta ɗan yi tafiya kafun tashiga ɓangaren su Haidar, da sallama a bakin ta ta shiga palon, babu kowa, shiru ta tsaya tana waswasin taje betroom na su ne, kokuma tajuya taje tachewa Aunty farida bata gansuba kamar daga sama taji anche “what are you doing here ɗago ido,tayi tana kallan sa yana sanye chikin 3cuter wando ruwan kasa da farar riga mara nauyi, saurayi ne dan shekarun sa zasu fi 25 ba kyakkyawar gaske ne kaman nin sa ɗaya da DON ban ban chin sa da DON shi idan sa fari ne DON kuma light green, murya na rawa Zahra tafara magana “Aunty farida che tache nakira mata yaya Haidar da Yaya Umar “daman Aunty farida ta zone ya tambaya yana chiro waya daga aljihun sa “eh tazo tana part ɗin Ummi, shiru yayi bai sake chewa komai ba, itama Zahra shiru ta tsaya almost 10 mnt a hankali ta ɗago kai dan taga wai ya tafine ko yana nan, yana tsaye a jikin stair case ɗin yana latsa wayar sa chikin tsoro da fargaban amsan da zai bata tace “yaya Fahad ina su yaya Haidar ɗin, shiri yayi bai tanka ba kamar ma bai san akoi mutun awajen ba ko sai latsa wayar sa yake, chikin tsoro Zahra ta sake mai mai ta tambayar “tayi yaya Fahad ina su yaya Haidar, wani dogon tsaki Fahad yaja chikin tsawa yake faɗin “wai kin bani ajiyar sune abeg get out, tun bai kai karshen maganar ba Zahra ta fita da gudu dan daman kamar a kan kaya take

Da gudu tashiga palon Ummi kan chin yar Aunty farida ta faɗa tana Kuka “subhanallah Auta meyafaru wa ya taɓaki chewar Aunty farida Zahra dai kukan ta take batayi magana ba “ai kema Aunty farida kinsan halin su banso kika aiki Zahra wajen suba, yanzu kilama ta haɗu da Yusuf ne a hanya ya daka mata tsawa, chewar Khalid Aunty farida tasa hannu tana shafa kan Zahra tana faɗin “sorry my lovely Auta kyalesu duk abun da suke miki kitara saiki rama akan ƴa’ƴansu in sunyi aure sun aihu kinji koh share hawayen ki,
dariya khalid yayi sosai san nan yace wai wa yaga yara, tab waƴan’nan akoi zan chen aure ma a’lamarin sune, ai wlh ko zan chen mace ban taɓaji sun yiba, mutane kamar dutse basu da shauki ƴanzu haka maganar danake miki friend mu hisham zai yi aure bakin san Hisham ba Aunty farida ta gyaɗa kai alamar eh “to Hisham dan yayi Aure Aryan da DON suka raba gari dashi “what? Kana nufin saboda Hisham yayi aure ne DON da Aryan zasu raba gari dashi, abotar kufa tun yarinta kai ina hakan ba zai yuba ” to gashima yayuwu kuwa dan ba yadda bamuyi dasu ba akan suzo bikin sunki zuwa,shima Aiman damuka samu muka lallaɓashi yazo yaki halaktar daurin auren, shi kuma Yusuf ɗaurin aure kawai yaje yaki zuwa wajen walimar ” tab to wlh basu isaba dolene su zauna tare da Hisham kilama sanadiyar zaman nasu suma sufara sha’awar auren yanzufa kusan 30 years kuke dashi kun zauna ba abunda kuka iya daga mai rike bin diga sai mai rike sirin jin Allura sai mai fama da laptop wai da sunan zane, Khalid ya dukar da kai kasa dan anzo kansa shima dan shine mai fama da laptop, aunty farida tachi gaba da chewa “sai mai fama da rigar lauyoyi gamasu tasowa nan yanzu duk kun lalata musu tunani dan suma ba mai wani maganar aure chikin su, duk kun chika mana gida, to mun gaji da ganin ku ƴaƴa muke san gani, su Ammi suna bukatar jikoki gashi ni tunda nayi aure ɗa 1 Allah yabani karamin Safras har yanzu shiru kakeji ban samu kariba to gwaranima, mardiya ko ɗayan bata samuba dan haka muna bukatar ƴaƴa agidan nan, yanzu haka Fahad shekarun sa inban mantaba zasukai 25 ga Haidar da Umar suma sun kai 23 ga Zahra Auta an zama yan mata yanzu haka Zahra nada 16 years to mekuke bukata dayawuche aure Allah ya hore muku komai,to yazama dole kuyi aure yan zu kam takarisa maganar da alamar ɓachin rai a face ɗinta, Ummi dai ido ta zuba musu tana kallon su dan ita ba mai yawan magana ba che ” laaa ni Aunty farida kin tunamin ma inasan muyi wata magana, chewar khalid ɗin “ok to inzo muje waje ke nan, Khalid ya ɗan sachi kallan inda Zahra da Ummi suke san nan yace eh to muje palan Abba zai fi tunda nasan yanzu baya nan yana fada “to muje amma kafin nan bari nayi waya da yan uwan kan nan dan inasan gabaɗayan mu muhadu a palan Abba bayan sallar issha “to kawai Khalid yace tare da mikewa yanufi hanyar fita “Ummi tache adawo lfy Baba tunda abun sirri ne “murmushi yayi yana shafa kansa batare da yache komai ba yafiche daga palon

To

(Garin yola ✈️🛬

 

kyakkyawar yarinya che fara tas ga dogon hanchi har baka doguwa che amma ba sosai ba bata da kiba duk da tana sanye chikin hijabi, hakan bai hana gashin dake kwanche a gaban goshin ta fito waba dark black ne gashin very smooth gata da manya manyan blue eyes, laɓɓan’ta ɗan karami pink colour bazata wuche 14 years ba sanye take chiki wata ko ɗadɗiyar atamfa ta koɗe tayi fari ga wata je mam miyar hijabi baki ne amma saboda koɗewa sai da ya dawo ash colour tsaye take tana riƙe da bokiti irin na penti almost 5mnt tana tsaye chikin fushi tafara magana da harchen fullanchi “hiyana idan bazaki fitoba wlh tafiyata zanyi na barki, tayi maganar tana kallan kofar wani gida
Gida ne ɗan ma dai dai chi kofar gidan ansa masa buhu an rufe a matsayin labule,irin gidan fulanin nanne masu kiwon shanu ke waye gidan yake da zana, daga chikin gidan hiyana ta da wata murya mai daɗin gaske tana faɗin adin kai diyana ina zuwa ina dubawa amrat hijabi ne “to wai waya chemaki amrat zata bi mu ne, zamuɗebo har da rabonta dan haka ta zauna a gida taƙarisa maganar tana yamutsa fuska ” yaye labulen buhun hiyana tai tafito, subhanallah sarki ya tabbata ga ubangiji da yayi wan nan halittar hiyana tafi diyana kyau sosai ta ɗan fita fita tsawo, kuma da alama zata ɗan fita shekaru dan hiyana zata kai 16 years farache sosai tafi diyana haske idon tama yafi na diyana girma da shiga colour idon ta yayi blue sosai kyakkyawa che ajin farko, rike take da hannun wata yarinya wadda bazata wuche 11 years ba yarinyar tana kama da diyana sosai sai dai ita idon ta baki ne manya manya, karaso’wa wajen da diyana ke tsaye su kayi hiyana na faɗin kiyi hakuri diyana kinji “haba hiyana ke che babba amma keche ke ja’mana duka kullun “to shike nan diyana kiyi hakuri zan gyara kinji muje to “aa bazamu tafi da amrat bafa ki mai data gida “diyana kibari mutafi da ita mana babu kowa fa a gidan bappa kuma yayi barchi kin sani bansan mu barta a gd ita kaɗai “nikuma Allah hiyana bansan amrat tabi’mu rafin nan akoi wahala Allah “to yanzu kam tun da mun fito muje kawai mu daina ɓata lokachi, juyawa diyana tana tura ɗan karamin bakin tan nan suka jera su kasa amrat a tsakiya

Wani dan siririn hanya suka nufa mai chike da dogayen chi yayi tsakiyar chi yayin suka kutsa tafiya sukayi mai nisan sosai kafin su isa wani rafi mai girma gefe gefen rafin chike yake da gona’ki da shuke shuke, ruwa suka ɗiba a buket ɗin dasuka riƙe hiyana ta ɗora’wa diyana nata buket ɗin chike da ruwa san nan da kyar itama ta ɗora nata ta kamo hannun amrat suka fito daga rafin suka kama hanyar gd, tafiya suke ba wan da yace da ɗan uwan sa ko kala, a dai dai wata katuwar bishiyar mangoro wani saurayin da bazai wuchi 24 years wani ɗan dotti dashi pusu pusu kamar an kwato shi daga bakin Kura ba yasha gaban hiyana birki suka ja suka tsaya suna kallan sa, ɗaure fuska diyana tayi tana faɗin “buba me haka dan Allah kabamu hanya mu wuche, wani kallan uku 10 buba ya watsawa diyana kafin yace “ke ba take nake ba tukun nan kibari nagama da hiyana zan dawo kanki “chikin sanyin murya hiyana tafara Magana buba kayi hakuri kaji kabar mu,mutafi wlh ruwan nan akoi nauyi kabari in muka dawo ɗiban na biyu sai mu tsaya muji me zakache “ke ni sa’ankine dazaki che na jira ku to baku isa ba yanzu nake san yin maganata idan ruwan yamuku nauyi,sai ku sauke kasa ku ajiye idan nagama maganan da zanyi sai ku ɗauki ruwan kutafi, diyana sarkin rashin hakuri a kule ta juye’wa buba ruwan dake kanta ajikin sa tun daga kansa har kafa yamike shar’kaf ta watsa a guje tanufi hanyar gida, dafe kai hiyana tayi tana faɗin “kayi hakuri buba..bata kai karshen maganar ba buba ya buge ruwan dake kanta ya faɗi kasa ya zube ɗaukar boket ɗin buba yayi yafara bugawa da katsa yana kokarin fasawa, hiyana kuwa ganin hankalin buba ya koma kan yana san fasa musu boket ne yasa ta kama hannun Amrat suka kwasa aguje sukayi hanyar gd, sai buba ya gama fashe musu bo’kitan gaba ɗaya san nan yabi bayan su a guje

Da gudu diyana ta faɗa gd wani ɗakin buk’ka tashiga,sai haki take tana numfashi da kyar, wani bawan Allah dake zaune chikin ɗakin, a kan gadon chiyawa, daka gan shi kaga ka mannin hiyana duk da tsufa da wahala dake tattare dashi ba zai hana ka gane kyan sa ba “diyana lfy kika shigo kina haki haka meyasaki gudu wani kika tso kana ko “bappa wlh buba ne shine zai bugeni na gudu kuma ba abun dana masa, bappa zaiyi magana sai ga hiyana tashigo rike da amrat dukkan su sai haki suke suna numfashi sama saman “hiyana har dake yau kuma bappa ya tambaya yana kallan hiyana, chikin sar’kewar murya hiyana tace “aa bappa laifin diyana che ta shafe ni, “ya Allah ya kawo muku mafita ƴa’ƴana, har suna haɗa baki wajen chewa ameen bappa, basu gama rufe baki ba aka ba paɗo ɗakin babu ko sallama wata mata che baka mai ƙaton hanchi, damkoh wuyar hiyana ta jata zuwa tsakar gd ta hau bugu matar nan tsaka nin ta da Allah take bugun hiyana, ta ko ina ihu hiyana keyi tana faɗin “dan Allah inna kiyi hakuri, “au kinsan da hakuri ke nan koh har buba zaku jiƙa da ruwa kuma ku zage’shi koh to wlh yau sai kun yabawa aya zakin ta, komawa ɗakin tayi ta damkoh diyana da gudu Amrat tayi bayan bappa ta buye, inna kuwa jan diyana tayi har tsakar gd ta ɗaukoh wani itache ta hau bugun hiyana da diyana dashi bugun su take sosai duk inda ta samu take sauke musu itachen, tun kukan su na iya fita har sautin kukan ya daina fita,duka sosai inna tamusu sai da ta faffashe musu jiki, san nan ta kyalesu takoma gefe kan wani dutse ta zauna tana mai da numfashi, su kuma suka dun kule waje ɗaya suna kuka, sai da inna ta gama hutawa san nan ta ɗago ta dube su tafara magana, “ke hiyana ko kina so ko baki so buba zaki aura dan kin samu ma zai rufa miki asiri, kuma kutashi tun da kun fusata buba ya fasa buket ɗin ɗiban ruwan to da kofi zaku koma ɗiban, wlh kutashi ku ɗauki kofi kutafi kufara ɗiba min ruwa yanzun nan, ku chika komai na gd san nan ku chika durum na dabbobin nan,kutashi tun ban zo na karai’raya kuba ta karisa maganar chikin tsawa, da kyar suka miƙe har suna tangal tangal suka sufi wani ɗan ki chin suka ɗaukoh kofi kowache ta ɗauki cup 1 suka fito suna kuka suka nufi waje

Bappa na zaune chikin ɗaki yana hawaye Amrat ta fito daga buyan datayi a bayan sa tafara goge masa hawayen tana faɗin bappa ka daina kuka kaji, rungume ta bappa yayi yachigaba ga kwalla

Su hiyana kuwa han yan rafin suka nufa suna rike da kofin suna kuka, “chikin kuka hiyana tace yanzu diyana bakin ga irin abun danake faɗamiki ba, kullun ina faɗamiki komai buba zai mana muyi hakuri dan in mu kache zamu biye masa wlh mu zamu sha wahala komai kan mu zai dawo amma ke bakiji,bansan wani irin kai ne dake ba “share kwallan fiskar ta diyana tayi tana faɗin yanzu hiyana haka zamu chigaba da rayuwa ni gaskiya bazan iya jure wa ba, yazamuyi mu ɗebo ruwa da kofi kuma a che mu chika abuba dake gida da ruwa har dana dabbobi nidai bazan iyaba “to duk bake kika jaba da zaki che bazaki iyaba kin nafa sane da kyar bappa yasamu yaje chikin birni ya sawo mana buket ɗin nan, yanzu gashi kinsa buba ya fasa bappa kuma ba takawa yake ba yanzu bare ya sawo mana wani ai dole ma mu ɗebo ruwa da kofin tun da dai kin san inna in tayi magana ba wan da ya isa yasa ta chanza, shiru diyana tayi bata sake chewa komai ba harsuka kai bakin rafin suka ɗebo ruwa a kofin suka juyo suka kama hanyar gd
*DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button