Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 40

Sponsored Links

โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ
*BOOK 2*

*PAGE 40*

No editing ๐Ÿ˜’

A wannan daren su Moon sun dad’e basuyi bacci ba domin Sarki yana barin gidan ya kira wayarta yana mata tsiyar cewa “ashe har haka yayi nisa a cikin zuciyar ta bai sani ba tunda gashi harta kasa rik’ewa ko kunya batajiba taje tana kukan tana son shi a gaban Hajiya, ai shi bai san cewa shi d’in d’an baiwa bane sai yau dan haka ta bar kuka tunda dai ta nuna tana so to jira kad’an kawai zatayi kafin ya canza mata suna daga Maimoon Usman Abdul Khareem,
Zuwa Maimoon Usman Sufyaan,
Tun yana hanya suke magana da ita bai yanke wayar ba har saida yakai gidan shi kafin ya mata sallama kuma sai da yasa ta had’ashi da Meenal,

“Kanwata nace wato da yike kin samu wani Yayan makwafina shi yasa ko tunawa dani ma bakyayi yanzun koh?”

“Ah ah wallahi Ya Sarki ba haka bane, kaga ga hidimar karatu da kuma shirye shiryen bikin besty Meelat da muke tayi shi ya d’auke min hankali yasa ban kira kaba amma kayi hakuri na manta kuma ban tayaka murnar sabon gidaba Allah yasa alkhairi ina kuma tayaka murnar samun soyayyar yar uwata allah dai ya nuna mana ranar ”

“Ameen ya rabbi nagode da addu’a ai nasan dama bai wuce kice inyi hakurin ba bayan kin ware ni a gefe kuna biki babu sanarwa balle insa rai da goron gayyata, bana ma ko kud’in ankon ba’a nema a hannu naba nace too abun har yakai haka? anya ba’a canza min matsayi ba kuwa uwar malam?”
Dariya tayi kafin tace

“ah ah wallahi ba haka bane yayan mu karkayi fushi ai ba’a gama bikin ba bama a fara ba tunda gaka ka iso aini kuma nasan daga daren yau na tashi daga Meenal na koma Hajiya Ameena mai uwa a gindin murhu ai bayacin tuwon shi gaya allah dai ya k’ara arziki Ya maimartaba angon Maimunatu”

“Wannan irin kod’awa da kikamin Meenal ai dole a baki kyauta yanzun fad’amin cash kike so ko kuma transfer dan gudun mawar da kika bayar yau dama kin cancanci tukuici mai tsokama kuwa, dan haka ko nawa kike buk’ata ki nemi Salman gobe ya baki kamar yanda aka saba… ”
“Wai Salman Yayan mu? Ah ah nidai karka had’ani da Salman fad’a mukeyi dashi gobe dai idan na shigo unguwar zan aiko ko kuma in amsa sakon ta hannun mutuniyar ka” sallama sukayi ta maida ma moon wayar,
ikon Allah wato dai kusancin da basu samu a baya tsakanin shida itaba shine yake son wanzuwa a yanzun a sanda take gidan shifa ita zata iya rantsuwa da Allah cewa basu tab’a zaman hira a tsakanin suba koda ya kirata a waya kawai zai tambayeta lafiyar tane sannan kuma yaji ko akwai wani abunda take buk’ata, itama kuma bata neman shi sai in tana da wani buk’ata na kud’i ko kuma idan fita zuwa wani wajen ya kama zata kira ta nemi izini amma kun gani tun bayan rabuwar su komai ya canza yanda yake mata wallahi kamar dai ba Yayan su Sufyaan mai karnukan nan data sani a shekarun baya ba wanda ko muryar shi kaji dole ka kama kanka,
haka Sultana tasa Meenal a gaba da tarin tambayoyi dan itafa tayi mamaki bata tab’a zaton cewa haka zataga Sarki ba dan haka ta gaza hakuri sai da ta tanka,

“Wai dama wannan shine Ya Sarkin?”
Saboda ita dai ba sanin shi tayi ba kuma a yanda take jin su Maryam na bada labarin shi tayi zaton cewa zatagan shi wani dattijo ne irin kamar dai wanda yake nemar shekaru 40 da wasu hayaniya a sama haka,
amma sab’anin hakan sai ta ganshi wani wankakken d’an gayu dashi wanda kai a kallo d’aya ma wallahi bazaka ce yana da yara har 4 har sun fara zama yan mata ba sai dai kace saurayi ne irin wanda baiyi aure da wuri ba d’in nan dan sam jikin shi bai nuna adadin shekarun shiba,
Koda tayi tambayar Meenal shareta tayi dan haka taci gaba da cewa

“Ke Meenal wai wani irin zama ne kukayi kukoh harna tsayin shekaru har 6 amma aka kasa samun cigaba?
Daga ke harshi kukayi ma kanku bak’in ciki wato yanda yasa miki na mujiya kema haka kika sa mishi saboda tsabar rashin sanin ciwon kai, Ni wallahi in fad’a miki gaskiya babu ta yanda za’ayi in rayu da irin wannan mijin irin rayuwar da kukayi gida d’aya kuma kuna ganin juna ace in sa mishi ido inyi ta kallo ban kai mishi cafka ba yo dan Allah kwace goruba a hannun kuturu har wani abunda za’a tsaya ana ba kai wahala ne, na rantse da Allah shida kanshi ma zai kawo kan shi har inda nike koda dad’in rai ko babu batareda ya tsaya shawara da kowa ba,
koda yike bari dai inyi shiru tunda mai afkuwa ta riga ta afku harta wuce inaga dai Allah yasan abunda ya shirya shi yasa ban bayyana a zaria ba a wancan lokacin su kuma wadanda ke tare dake suka kasa baki mafitar daya dace,
ke kuma Moon bari kiji in fad’a miki wallahi idan har kika sake kikace kema irin wutar da yar uwarki tayi a baya zakiyi to ki sani koni nan sai na miki Allah ya isa idan ita rashin rabone ya rabasu to ke ki d’auka cewa dama can kece mai rabon ba ita ba, zan kuma baki shawara daga yau daga ita harshi karki k’ara musu kallo a matsayin wadanda suka tab’a rayuwa karkashin inuwar aure ki d’auka cewa ita d’in dai kawai k’anwa take a gareshi kamar yanda nidake dama kowa ya shaida hakan,
Sarki dai yana sonki kema kuma kina son shi dan haka nemo zanin goyo kiyi d’amara ki goye abinki tsaf wallahi, karki sake koda wasa kice zaki dunga tunawa cewa yana da wata matar bayan ke a duk sanda kuka kasance tare, nuna mishi cewa shi shikadan shi shi kika sani shi kika waya kike kuma gani a gaban ki da bayanki dan shi din dai shine duniyar ki ,
Ki nuna mishi kauna ta hanyar nuna kulawar ki akan dukan abunda ya nuna miki yana da mahimmanci a wajen shi, ki tayashi son iyayen shi, yan uwan shi da yaran da ya haifa, bance ki nuna soyayyar ki ga matar shiba dan ba dolen ki bace ita, sai dai kiyi kokari ki dunga danne kishin ta a gaban shi karki yarda in kina hira dashi kice zaki dunga sakota a cikin hirar ku haka kuma shima karki yarda ya dunga kawo miki hirar ta kowacce ta tsaya matsayin ta ki kuma dunga kiyayewa karki yarda kice zaki shiga hakkin ta wato misali kiran waya a sanda kika san yana gida,
In fad’a miki gaskiya wannan had’i naku yamin dad’i dan tsakanina da Allah dama tunanin wacce zata shige cikin gidan nan tayi luff a matsayin matar gidan madadin Meenal kullum shike cimin tuwo a kwarya ke gidan nan fa Yasin duk wacce ta shige shi matsayin mata to ta kwantar da kai tayi luf taci arzikin ta hankali kwance abinta kinga ni dama ban tab’a shiga ba kullum dai idan nazo wuce shi sai na yaba a cikin zuciyata yanzun kuma ga dama ta samu kina shigewa gidan nan ai mu shar abunmu wallahi ,
bari in baki wata shawara ban sani ba ko zaki d’auka kinga zama gida d’aya keda kishiya na rantse miki da Allah sai kin kai zuciyar ki kololuwar nesa dan yau da gobe duk yanda zata takale ki ku raba hali sai tayi ke wani abun ma da gayya zatayi dan dai kawai taga ta b’ata miki rai balle kuma kishiya irin matar shi da naji labarin nata kishin yake a sarari dan haka nidai a nawa hangen gara ki lallab’o shi ya ajiye ki a wannan gidan nashi na garin nan ita kuma taci gaba da zama a Kaduna,
Falalane mai girma raba gari da kishiya domin idan dai tana inda take kema kina naki wajen wata rana ma mantawa zaki dungayi cewa bake kad’ai bane domin idan yana wajen ta gani zakiyi kamar tafiya yayi ya dawo gareki, tana da masaukin ta anan cikin gidan iyayen shi dan haka baki da fargaba cewa idan tazo zata sauka a gidan ki, zuwa Kaduna ki tare ba dole bane a gareki in kinso dai kina iya zuwa can din lokaci bayan lokaci amma dai ya zamana cewa nan dai kece mai iko dashi, wallahi nayi miki murna kwarai kekam Allah dai ya sanya alkhairi yasa ace gara da akayi barkan ki da shigowa cikin ahalin mu duk da dai naji babu dad’i kad’an a sanda naji Hajiya tace da taso ne ta badaki ga d’an uwana ya Sheikh amma ba komai na hakura dan bazan miki bakin ciki ba”.
Hira sosai suka sha a wannan dare kafi bacci ya nuna musu fin k’arfi wajen yi gaba da kowacce a cikin su, yau dai rana na farko da Moon ta samu damar yin bacci cikin salama sab’anin sauran ranakun da suka wuce wad’anda ta dunga lissafin yanda abubuwa zasu kasance sai gashi Allah da ikon shi komai ya tafi a saukake ba tareda an samu rarrabuwar kawuna ba.

*WASHE GARI*

Gidan Hajiya mak’il ya cika da bak’i na nesa dana kusa kowa ya hallara sai faman hadaยฒ kawai akeyi, cikar gidan kuma ya k’aru ne kasancewar ba iya ahalin gidan ne kad’ai suka samu damar isowa a wannan rana ba harda abokanan su Musty kamar yanda AK yace anan zasu sauka anan d’in suka sauka,abokan sune wasu tun na yarinta wasu kuma anyi makaranta tare sai dai kuma kai mai kallo da zarar ka gansu ko baka tambaya ba kasan babu sakarai a cikin su domin duk kan su kowa yana da abun hannun shi duk wanda ka kalla dole sai kaji kamar karka dena kallon shi dan sun san hannun su gashi ko wannen su sunsha wanka sun gaji kamshin ko har baka tantance na wani ga kuma giyar kud’i dake d’ibar su sai suka zama abun sha’awa a wajen sauran matasa sai dai sunji babi dad’i bayan isowar su da suka samu labarin cewa babu wani shagalin da aka shirya na cashewa a bikin na abokin su domin fa sunzo da niyyar su warwasa biki dai na rana d’aya dan haka suka tada balli cewa basu yarda ba ko ba’ayi komai ba su zasu shirya ma amarya da ango dinner,
da kyar suka samu Mai Jama’a yasa baki aka tsaida batun dinner d’in dan shi da Musty cewa yayi baya buk’atar bidi’a su bisu da addu’a kawai.

A gefen su Meenal ko suma dai tun wayewar gari suka fice daga gidan domin agenda dinsu na yau shine kunshi da gyaran gashi da yamma kuma zasu gabatar da bridal shower wanda iyasu mata ne zasu halarta gobe kuma shine zasu gabatar da kwarya kwaryar walimar da suka shirya wanda maza da matan dukan su zasu halarta, kud’i masu nauyi AK ya sauke ma sultana kafin fitar su a matsayin kudin kunshi dana gyaran kai nasu dana amaryar su, su kuma sauran abokan sosai suka nuna nasu bajintar wajen saukema k’awayen na amarya komai zasu buk’ata dan haka suma kawayen babu tausayi haka suka dunga lissafo musu abubuwan da suke buk’ata harda wad’anda basu zama dole ba, Safiyya matar Yusuf wase itama a ranar ta iso dan haka itama gidan Hajiya ta ajiye su Affan ta shige cikin su Moon aka cigaba da gudanar da abubuwa da ita, kuma shima Sarki kamar yanda yayi alkawari ya sauke ma Meenal d’in Alert mai nauyi a cikin wayarta wanda har saida Sultana ta dunga mamaki wai sudai mazan zaria idan zasuyi kyauta a dunkule sukeyin shi kamar basu san zafin nema ba, ita ma dai Allah ya had’ata da wanda zata shak’o wuyar shi tayi ta goge mishi hadda.

****

A jiya kasancewar koda Sarki ya isa unguwar na malamai dare ya riga yayi sai kawai ya wuce gidan shi ya nemi wajen bacci,
Bayan gari ya waye kuma yana dawowa daga sallan asuba yayi wanka ya shirya ya wuce gidan su, kowa yayi mamakin irin sammakon daya bugo daga Kaduna dan haka sai uwar gida ta fara tambayar shi da cewa “lafiya kuwa wannan irin tafiya na sassafe”
Kai ya maida k’asa cike da rashin gaskiya yana non nokewa ya amsa mata da cewa, “lafiya lau”
“Ko wani abu ya farune?” Ta k’ara tambaya,

“Ah ah babu abunda ya faru, da yike nayi shigowar dare ne a jiyan shi yasa ban shigo nan din ba,” sai da ya k’ara duk’ar dakai kafin yace,

“Ina son zan k’ara aure!”
Shiru yayi yana jiran jin amsar da zata bashi,
Ita ko sai tayi shiru abinta kamar ma bataji mai yace d’in ba,
D’aurawa yayi da cewa,

“Na tura can gidan su yarinyar wajen iyayen ta a Lagos sai dai kuma a lokacin shi mahaifin ta bayan sunyi magana da wanda na tura yace a dakace su saboda waliyin dazai bada auren ta baya k’asar idan ya dawo sai su koma ayi magana, to jiya dana iso naje na gaisheda kakarta ita kuma ta shaida min cewa indai na shirya to suma a shirye suke dan basa son abin ya d’auki lokaci, tana dai nufin idan za’aje a tafi da komai na neman aure kawai dan a cewarta bata son a wuce nan da wata d’aya yau iyayen yarinyar zasu shigo gari shi yasa nace bari in zo in muku bayani”

“To ubana mai kake nema a gunmu kuma tunda ka riga ka shirya harka riga ka tura magabatan ka mu nan bamu da labari daka kawo min zancen yanzun mi kake so ni kuma ince ne? Ai ni kuma bani data cewa sai dai in muku fatan Alkhairi tunda kai dai ka zama d’an kanka har kayi girman da zaka tura wasu can daban nema maka aure bayan mu iyayen ka muna raye to ai ba laifi idan ansa ranar sai a shaida mana mu sanar da yan uwa,dama ka dad’e kana neman auren ne abunka mu bamu da labari, kai yanzun inba rashin ta ido irin naka ba yaushe ka rabu da ita wancan shine yanzun da matar ka ke fama da jikinta yau lafiya gobe ciwo shine zaka tattago wani sabon aure, koda yike ai in bakayi ba baka gaji iyayen ka ba”

“Kiyi Hakuri Hajiya ita yarinyar dama nidai na dade ina ra’ayin ta ban samu damar gabatar da kaina bane sai yanzun”

“Ai Allah ๐Ÿค” to sannu aikuwa na maka murna to wasu iyayen ka tura can gidan su tunda su dai iyayen ka na nan banji suna labarin ba?”

Duk’ar da kai yayi kafin yace “Brigadier ne ya nemo min auren ta”

“Brigadier dai uban matar ka?” Ta tambaya tana mai jinjina abun,
“Kai amma dai kam kam sam baka da kawaici baka da ta ido, yanzun ka rasa wanda zaka aika nema maka aure sai uban matar da kake aure Sarki wannan wani irin rayuwa ce, wai ma tukun na ita yarinyar da kake neman wacece ita?”

“sunan ta Maimuna iyayen ta dukan su yan nan ne amma mazauna Lagos ne”

“Su waye iyayen nata anan d’in nike son sani?”

Allah ne ya taimake shi wayar shi tayi k’ara a daidai lokacin da take jiran amsa daga gareshi dan haka sai yayi amfani da wannan damar ya sulale ya fice daga gidan,
Gidan Malam ya wuce suka had’e da ya Sheikh a sashen Malam din sukayi ta hira.

Da dare Hajiya ta tara su Baba Usman a falon ta maganar zuwa neman auren AK da take son suje a gobe ta fara gabatar musu,
Dukan su daga iyaye mazan har matan kowa ya nuna farin ciki da jin dadin shi na had’in auren a bayyane, bayan an gama tattauna akan auren su AK maganar Moon shima Abba Ahmad ya sako hajiya bata katse mishi hanzari ba har sai da yakai karshen zancen shi da cewa maneman auren Moon d’in zasu iso gidan a gobe dan ya kirasu cewa ya iso k’asar dan haka gara suzo a tsaida komai daya kamata,
“Suwa ke neman aure Maimunan?”
Hajiya ta tambaya,

Gyara zama yayi dan yasan anzo inda yake tsoro azo din,

“Hajiya dama munk’i shaida miki ne mukace sai munzo sai a gabatar da komai a gaban ki,
Wannan yaron d’an gidan Malam Sulaiman na unguwar malamai d’an yayan su Mukhtar mijin Jiddan ki shine yaje har can Lagos da zancen yana neman auren Maimunatun Brigadier uban matar shi ne kuma yaje mishi neman auran shida abokan shi mutum biyu cikin su harda tsohon abokina,
To dai tun lokacin nace musu su d’an dakata har in iso k’asar saboda in gabatar miki da zancen kafin isowar su”

“Masha Allah sai dai kuma ban gane dogon kwatancen naka ba naji kace d’an yayan Mukhtar, wai mijin Jidda na kake magana ko wani daban?”

“Eh shi dai Hajiya”

“Ikon Allah to waye yayan nashi ni ban gane shiba”

Shiru yayi yana kallon gefen da Baba Usman yake zaune wanda ya fuske abinshi kamar bai san akan me suke magana ba,
“Hajiya shifa yaron shine mijin da Allah yasa ya auri Meenal a shekarun baya”

“Ohh wai kana so kace min Sufyaan dai Sarki wanda aka aura ma Meenal ya saki shine ya dawo neman auren Moon yar uwarta kuma?”

Cacaca falon ya haura da surutan mata har baka gane abunda suke cewa, dan a karkace zancen ya shiga kunnuwan su,
Gyara zama Hajiya tati dan taba kowa damar tofa albarkacin bakin shi, Abba Ahmad shi dai da yaga surutan yak’i karewa shi ya tsawata musu da cewa,

“Dan Allah kuyi ma mutane shiru ku barmu mu tattauna abunda ya taramu anan”
Shirun sukayi suka koma jimami k’asaยฒ inba rainin wayau ba taya ma ya auri Meenal yanzun kuma ya dawo yace Moon yake so ai wannan sam ba maganar da hankali zai d’auka bane,
Sufa matan sun natsu ne dan sun san cewa babu ma ta yanda za’ayi Hajiya ta goyi bayan al’amarin amma wai sai suka jiyo muryar Hajiya tana cewa,

“Aiko dai indai Sarki ne Maimunatu kam ta more miji dan Wallahi samun miji irin shi dai yanzun sai an tona, dan haka suna isowa babu b’ata lokaci su gabatar da komai kawai ayi batun sa rana dan haka sai ka kirasu ka sheda musu suzo da shirin su”
Duka jama’ar falon da kallo irin na mad’aukakin mamaki suka dunga binta,
Anya wannan Hajiyar da suka sani ne kuwa?
Umma ce ta gaza shiru tayi magana cewa,

“Hajiya tsohon mijin Aminatu fa ake magana taya kuma za’ace Maimoon ta aure shi, in auren za’a mata ai gara a bata dama ta fad’i wanda take so sai a aura mata in ma babu ga d’an yar uwata nan Lukman tun bata kai haka ba yake kwakwa a kanta”

Sai da Hajiya ta k’are mata kallo tsaf kafin tace,
“Shi auren Sarki da Moon d’in akwai ta inda Allah ya haramta shi a musulunce ne?”

Shiru falon yayi wannan Karon ma Umman ce dai ta amsa da cewa,
“Amma Hajiya kusancin yayi yawa kuma Ana barin halak kodan kunya”

“To nidai na riga na gama magana Moon dai Sarki ta zab’a a matsayin miji in baki sani ba ni na fad’a miki yanzun dan haka shi zata aura, shi dan yar uwarki tace bata son shi dan haka babu mai mata dole, ku kuma jini da kyau maganar nan ta tsaya iya nan bana son in dunga jin wasu k’ananun magana suna tasowa a bayan fage, dama can Allah yayi cewa Moon ce matar shi tun farko wanda kuma duk yace zaiyi jayayya da hukuncin Allah to ya shirya shida Ubangijin shi, ba kuma Moon ba duk wata yar data isa aure ina bukatar ganin magabatan wad’anda ke neman su kafin kubar garin nan”.
Tana gama kora musu nata jawaban ta haye sama abinta ta barsu suna k’ara cakalkala zancen,
A daren Abba Ahmad ya kira Brigadier sukayi magana shi kuma ya tabbatar mishi da cewa insha Allah zasuyi k’okarin isowa Zaria a gobe, wannan kenan,

A daren Meenal Sultana da Safiyya matar Yusuf suka dawo gidan na Hajiya dan AK ya shaida ma Meenal cewa karsu sake suce zasu kwana a unguwar malamai su dawo gida su kwana,

Bayan dawowar su har sunyi wanka sun kwanta suna hira tsakanin su ya kira wayarta akan ta fito ta same shi yana jiran ta, tana tura baki tana komai haka nan tasa hijab ta fita badan taso ba dan Wallahi yau ba karamin gajiya tayi ba,
Bashi a falo dan haka sai ta bude kofar falon ta fito dan har yanzun akwai hayaniyar a gidan tasan kila yana farfajiyar gidan,
Koda ta fito bata lura dashi ba sai ji tayi kawai ya jata zuwa bayan wata k’aramar bishiya dake kofar falon,

“Waiyo Allah na wanene kai miye haka” take fad’a tana son kwacewa,
Juyo da ita yayi yana dariya,
“Kedai matsoraciya ce wallahi, yanzun nan ke fisabilillahi da ban kira ki ba haka zaki kwanta kuma har ki iya yin bacci abinki bayan kin san yau uni nayi da yunwar son ganin fuskar ki, da ace Sultana bata d’auki hoton kwalliyar ki ta turamin bafa da shike nan kin sha dani,ai dai kema kin san hakan bai dace ba nina fa” fa d’a yana lankwashe kanshi a gefen kafad’ar shi,
“To kaima ba kana cikin naka abokan ba! Shi yasa ai ban kira ka ba saboda kar in dame ka”

“Waye yace miki zaki dameni ne?”

“Ba kowa”
“To fad’amin kinyi kewa na yau”
Murmushi tayi tana d’an rausayar da kai gefe,
“Allah nidai gani nikeyi sam kamar baki wani damu dani ba”

“Na damu dakai mana”

“Tsaya kiga hotunan da Sultana ta tura min” ya fad’a yana nuna mata hotunan a cikin wayar shi,
“Kinyi kyau amma dai gaskiya ni bana son kina goga wannan abun a bakin ki in zaki fita koda ko inda zaki shiga babu mata”
“Me?” Ta tambaya tana d’ago kanta ta kalle shi,
Shi kuma sai yakai yatsar shi dai dai bakinta a jikin hoton, “wannan jan abun da kika goga a bakin ki nike magana”
“Wai jambaki? Baiyi min kyau bane? To amma ai yau kowa yace nayi kyau”
Ta fad’a a shagwabe,
“Eh ai nima saboda kyan da kikayi yayi yawa shi yasa nayi magana dan bana son inga kin shiga waje idanu sunyi miki yawa inba haka ba kuma lallai zaki fara yawo da facemask”
Dariya ma ya bata dan haka ta dara
“Waima facemask ana zaune kalau kaima ai kana da kyau me yasa baka sawa idan zaka fita?”
“Ina sawa mana kece dai baki gani ba”

“To nidai zanje in kwanta kaga dare yayi”

“Ke yanzun nan fa kika fito” ya fad’a yana riko hannun ta,
“To ai na gaji da yawa ne yau”

“Ok tunda kin gaji saiki zauna a gida gobe basai kinje ko ina ba”
“Tab lallai ma bikin Meelat nefa”

“Eh bikin nata fa so kike insa miki ido kiyi ta ba kanki wahala shike nan bazaki huta ba, kinga nima duk yau haka nike ta jina kamar banda lafiya kuma nan d’ina sai k’aikayi yakeyi”
Ya fad’i hakan a yayin da yakai hannun ta d’aya gefen fuskar shi dai dai wajen dimple din shi,

“Me yake damun ka to? In sosa maka?” Ta tambaya ta kallon shi da tausayi a fuskar ta,

“Ai ba sosawa akeyi ba”

“Me akeyi?”

Jawota yayi zuwa gaban shi kafin ta ankara taji Sautin muah a gefen nata fuskar,

Kwacewa tayi tana kai mishi duka, “Allah nidai ban yarda ba ai nace maka bana son haka amma baka ji,”

“Ok ok sorry to zoki rama to shi kenan”
Daga bayan su sukaji tafi na tashi RAF RAF RAF,

“Kai amma AK kaf shekarar nan banga mara kirki kamar ka ba,
Yanzun nan dama ashe tsabar munafunci har budurwa gareka shine mu bamu da labari, wacece ita? To yau dai Allah ya tona maka asiri anyi walkiya mun ganka,
Wallahi Musty baka kyauta min ba daka kasa kirana tun tuni ka bani labari ni kuma in tattaro kayana in dawo nan in tare ayi komai a gaba na”

“Kai dallah ai da ace a lokacin na fad’a muku karyatani zakuyi amma yanzun da Allah yasa kaji kuma ka gani kaga kaima sai kaba wasu labari, yanzun dai muje ciki dan Allah ka wani zo duk ka tsorata min Ya”cewar Musty,

“Kan uba wallahi ban wucewa sai naga ko wacece” wayar Shi ya ciro ya fara musu hotuna duk da cewa wajen babu haske sosai,
Shi kuma AK ganin haka sai yaja Meenal din ya maidata bayan Shi ya boye,

“Faisal zanci uban ka in baka dena d’aukar mu hoto ba,
Matar tawace kake son d’auka ka watsa kowa yagani?”
Yan hannun Meenal din yayi sai da suka kai bakin kofar falon ya bud’e ya tura ta,
“Wuce ciki sai da safe”
Shi kuma Faisal cewa yayi “haba AK wannan ai wulakanci ne bazaka bar yarinya ta gaisheni ba haka akeyi duk kabi ka wani boyeta to yanzun ya za’ayi idan na ganta gobe in ganeta? Kai dai d’an iskane wallahi kuma wallahi kowa sai yaji zancen nan haba ashe Shi yasa ka barmu a waje ka shigo ciki wato kazo duba lafiyar fulawar ka”.

Juyawa yayi da gudu zuwa inda sauran abokan su suke yana basu labari su kuma kamar masu jira haka suka taso AK gaba akan cewa lallai fa ya kira musu ita ta fito ta gaishe su su ganta, Shi kuma yace musu uban kuturu yayi kad’an,
Ya dai sha sharri ba kad’an ba kowa da abunda yake cewa wasu na fad’in wai Allah yayi ya samu aljanar data aureshi ta rabu dashi da kyar wasu kuma na cewa, wai hala dai bashi ita akayi dan sun san da wuya ace shine ya ganta yace yana so,
Sanda Yusuf ya zauna ya fara basu labarin badakalar da aka sha kafin ya furta mata yana son ta koh kasa zama a cikin su Ak yayi dan haka suka hauro kamar zasu cinye namar Shi d’anye.

 

*Ummiee ce*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button