Sponsored Links
Hausa NovelsUncle Datti Hausa Novel

Uncle Datti 43-44

Sponsored Links

4️⃣3️⃣—4️⃣4️⃣

Kuka ta fashe da shi tana pleading d’in shi ya barta, ganin yanda take kukan ne sai ya dawo cikin hayyacin shi yayi saurin sakin ta ya mirgina gefe yayin da hawaye ke bin fuskar shi” anya iyayen su sun san irin matsalar da yake fuskanta game da sha’awar baby?
Sun san yanda yake azaftuwa da son ta da kuma mararin samun d’umin jikin ta?
“Ina ma ace za su taisawa halin da yake ciki su amince da auren shi da baby wanda ta zame mishi jigo a rayuwan shi.
B’angaren Fu’ad yana nan a b’angaren Ummi har ya gama wanke mata plate ya dawo ya zauna suna hira.
Shiru shiru ya zauna yana jiran ya ga dawowan ta amma bata dawo ba, tun yana fahimtar abunda Ummin take fad’a yana maida mata da martani har ya koma yana amsa mata da “uuhhmm, a’a, jefi-jefi yana kallon wrists watch d’in da ke mak’ale a hannun shi yana jan tsaki…..har sai da Ummi ta lura da hakan ta hau tambayar shi lafiya yake jan tsaki shi kad’ai, cuz tayi mamaki sosai.
” Tsaki mai k’arfi ya ja tare da jan gwaron numfashi ya gyara zama, ya d’au remote ya rage k’arar TV d’in ya yana kallon ta kamar zai fashe da kuka”wai Ummi wani irin aika ne kika yi ma Nana har yanzu bata dawo ba ki duba tun safe ta fita and know yanzu kusan karfe shabiyu fa na rana har yanzu bata dawo ba like an aike ta wani gari, ni fa gaskiya bana son son hakan, idan ma aika ne sai a bani idan kuma bana nan ajira idan na dawo sai a aike ni”.
Shiru tayi tana kallon yanda ya rufe ido saboda tsabar kishi yake ta masifa ya manta da cewa ita d’in surukar shi ce to be, halin yaran zamani sai su.
Fuskar ta na bayyana tsantsar mamaki tace” Nanar ce tace maka na aike ta?
“Eeehhhh ko kin manta da aikan da kika yi a gidan k’awar ki?
” Ba dai ni ba ban aiki ta ba sai dai ko Umman ku zaka tambaya ko ta aike ta”.
Shiru rayi ranshi babu dad’i” wato ta raina shi ya tambaye ta shine zata mishi k’arya, sakar zuci ya kama yi shi kad’ai saurin yayi saurin kawar da zancen baya son ya kawo abunda zai fara zargin ta……..,
Mik’ewa ta ga yayi ta bishi da kallo da mamakin a fuskan ta” a’a ba dai ka gaji da hirar ba ina kuma za ka?
“Yayi ajiyar zuciya so yake ya controlling zuciyar shi” d’akin zan tafi na gaji ne my Ummi, yana gama fad’a cikin sauri ya sa kai ya fita, ta bi bayan shi da kallo tana girgiza kai.
Ba shi ya zame ko ina ba d’akin Umma ya nufa ya tarar da ita a parlour ya tarar Mardiya ta blending fruits ta had’a mata da mada ta kawo mata tana sha.
Ganin da tayi mishi ta so ta fahimci wani abu sai ta batsar, zama yayi a gefen ta ba tare da ya tanka mata ba itama bata bi ta kan shi ba har sai da ya gaji ya kalli Mardiya da ta zauna gefen Umma yace” keeeeee me yasa baku fita tare da Nana ba kika barta ita d’aya ta tafi?
“Dai-dai ta d’au cukali ta d’ebo fruits d’in ta kai baki tana tattaunawa yayi tambayar, a hankali take taunawa sai ya kulu” ba da ke nake ba kin yi shiru kina jin mutane? Cikin had’e rai yayi maganar”.
“Wai kai me yake damun ka ne yau? baka ga tana taunar abu bane so kake ta kware?
” Amma ai sai ta amsa min ba ta yi shiru tana jina ba”.
“Da abunda ke ba kin ta zata bud’i baki tayi maganar? Kaiiii Fu’ad fita ka bani waje na lura yau da bori ka tashi………, banda zancen wofi tare suke fita ne?
” Ganin yanda Umma ta d’au zafi sai ya yayyafa ma kan shi ruwan sanyi ya sa kai ya fita yana magana ciki-ciki” yarinyar nan ina ta tafi ne zata dawo ta same ni sai ta had’u da fushi na.
Garden ya nufa ya zauna daga wajen yana kallon bakin gate d’in ko zai ga gilmewan ta ta shigo ciki har kusan k’arfe biyu bai ji d’uriyar ta ba su Ummi kam basu lura da cewa bata ciki ba cuz always a d’aki take yini tun dawowan ta gida, haka ma tsohuwa da Nanar take zama a b’angaren ta a tunin ta ko tana d’akin ne.
Zumburr ya mik’e ya nufi site d’in tsohuwa nan ya had’u da Aina ta shawo kwana shi kuma zai fita ta matsa gefe ta bashi waje…….a’a yi a hankali karka buge ni man Fu’ad, lafiya na ganka a hakan duk ka rud’e.
“Mtssew wallahi Aunty Nana ce ta fita tace min Ummin ta aike ta, to bayan fitan ta nayi ta jiran ta bata dawo ba shine na zo na duba ko tana d’aki.
“Shine duk ka wani d’aga hankalin ka? Muje to ko zamu same ta sai dai matsala na da ita d’aya bana son jin kukan nan nata wallahi.
” To ya zata yi ai dole ne a hankali zata adopting system d’in rabuwa da d’an ta.
A tare suka shige d’akin suka duba basu same ta ba, Aina har bandaki ta duba nan ma bata nan suka fito k’ofar gidan, nan ne hankalin Fu’ad ya fara tashi gashi yanzu yamma yayi.
“Ina zuwa aunty….., car key d’in shi ya d’auko ya fito ya nufi parking space suka shige mota yace ma Ainar itama ta shigo su tafi zo za su same ta a hanya.
Bata yi musu ba ta shige ya tada motar da mugun gudu ya bar gidan.
Tuk’i yake a hanya bai ma san inda za shi ba daga k’arshe ya fita bayan gari inda ya saba tafiya ya refreshing brain d’in shi ya fita ya bar Aina da mamaki ya cika ta tayi shiru tana kallon abunda zai biyo baya.
Sassarfa yake a gurin he was totally confused ya rasa ta ina zai bi gan ta, wawan naushi ya kai ma iska kana ya cije libs d’in shi da k’arfi har sai da yaji zafi ya runtse ido da k’arfi…….., ba iya zafin cizon ne kadai ba rashin sanin inda Nana take shi yafi komai d’aga mishi hankali a wannan lokacin.
Tunani ya cunkushe mishi sosai har ta kama ya sara samun kwakwaran solution guda d’aya…….,runtse ido yayi ba tare da ya bud’e ba abunda ya fad’o mishi a rai shine yanayin yanda ta rud’e a lokacin da yake tambayar ta………, da kuma amsa mishi da tayi cikin sauri ba tare da ta tsaya ba……., that means tana tare da Datti kenan?ina ta samo shi har ta yarda ta bi shi?
Gidan shi mana idan ba gurin ba ina zata je?, tambayar da yayi ma kan shi kenan tare da samo amsa ma kan shi……..rasss gaban shi ya fad’i yayi saurin shigewa mota Aina dai bata ce mishi komai ba har yanzu shima haka ya ja motar a 360 ba su suka tsaya a ko ina ba sai gidan Datti.
B’angaren Nana tana ganin ya sake ta tayi saurin saukowa daga gadon a tsorace ta d’auko kayan ta ta maida jikin ta, rigar garin kokawa da shi har ya d’an yage ta gaba, da gudu ta fito shima ya mik’e da boxer ya bi bayan ta yana kokarin tsayar da ita ina sai parlour ya ci sa’ar kamo ta ra rungume ta yana maida ajiyar zuciya kamar wanda za’a kwace mishi ita……..tana fitowa tayi kicibissss da Fu’ad wanda shigowan shi kenan nan ya ga yanda Dattin ya rungume shi Aina kam tsayawa tayi a waje tana jira domin bata k’aunar shigan gidan.
Wani irin tarsashin k’una zuciyar yayi mishi, ji yake kamar an caka mishi mashi a kahon zuciyan shi yayi saurin dafewa ya ba su baya da sauri”, ba zai iya jurar kallon su a hakan ba….scene din will make him go crazy cuz abunda ya gani ya tempering d’in shi sosai har yayi dana sani da bai zo ba balle ya tarar da abunda zai d’aga mishi hankali.
Nana dai tunda ta had’a ido da Fu’ad taji jikin ta ya d’auki rawa kirjin ta kuwa ya hau luguden bugu da k’arfi……,
Datti kamm ko ajikin shi illa ma dad’i da yaji a ranshi, da ace ya san da zuwan Fu’ad da a parlour zai danna Nanar ya hau kanta yayi ridding d’in ta suna ihun dad’i kamar yanda suka saba yayi ta latsar ta tana latsar shi wata k’ila idan ya gan su a hakan zai ce ya janye ya fasa auren.
Sai shige mata yayi ya rik’o waist d’in ta da hannun shi, bakin shi ya kai saman wuyan ta yana shinshinar ta yana magana da wani irin murya” yanzu ka gane cewa tsakanina da kai akwai ban-banci……., idan ka aure Nana saura na ne sai da na ci na rage maka ka kwasa…….., sai da taji dad’ina nima naji nata……, muka shayar da juna zuman da babu wanda zamu d’and’ana ma juna irin ta…………, duk yana fad’a ne ba tare da ya daina shinshinar ta ba lokaci guda yana gyara mata zaman suman ta da ya barbazu a saman kafad’an ta………haushin shi taji sosai kalaman ta ture shi da sauri tazo gaban ya watso mata birkitaccen mugun kallo kana ya juyo yana kallon Datti.
Duk yanda ya so ya danne kishi shi karya bayyana shi a fili amma sai ya kasa, Datti ya kai shi iya wuya…..ya kai limit d’in da ba ya jin zai iya danne abun da ke bugun shi a zuci.”
“Ai shi bunsuru duk inda yake sai ya nuna halin bunsurancin shi……, kuma sai babba ya ja girman shi kafin a bashi girma…….., ni nafi k’arfin na sayar da akuya nazo ina cin dangan k’ara.
Yana maganar tazo mishi kamar dirar mashi…., a basata yaji maganar bai tsammaci zai samu amsa daga gare shi ba”.
” Murmushin takaici ya sake” Fu’ad kenan babu abunda ka sani game da rayuwar duniya kwakwalwar ka tayi kad’an ta fahimtar da kai hatsarin da ke tattare da auren Nana.
“Idan ka aure ta gangar jikin ta kadai zaka aura zuciyar ta na tare da ni……..,ina so ka rubuta ka ajiye sai ana son ka kafin a mallaka maka zuciya da gangar jikin ka…….ko a hakan na barka ya kamata ka fahimci inda magana na ya dosa…….ga misali nan ka gani a gaban ka ba tilasta ta nayi ba ta kawo min kanta…..muka dirji juna”, uhhmm ina taya ka bak’in cikin auren fanko, shuk’ar wani wanda ya raya ta da ruwan jikin shi shi yake ban ruwa mata”.
Kunnuwan ta tayi saurin toshewa da tafukan hannun ta zuciyan ta na bugawa da k’arfi.
Idan ta fahimce shi yana nufin kawo mishi kanta kenan tayi? Lallai yayi mata gadarzaren da warware shi zai yi wuya, da na sani iya da na sani tayi shi fiye da a k’irga na zuwan ta gidan.
“Fu’ad na nan daskare a guri d’aya ya kasa ko da kyaklyawan motsi, bakin shi yayi mishi nauyi ya kuma rasa k’almar da zai yi amfani da shi don ya rama abunda aka fad’a mishi kasa cewa komai yayi da sauri ya fita daga parlourn zuciyan shi nayi mishi tafarfasa, Nana ta bi bayan shi da sauri Datti ya shafa suman kanshi yana murmushin mugun ta yayin da a heart d’in shi yake cewa” kiyi hakuri baby duk son na mallake ki ne ya jawo haka, ya biyo ta wani hanya ne ya nad’a min tarko kuma tarkon ta kama da ni, nima dole na biyo mishi ta wata hanyar ni da shi zan ga wani jarumin ne zai yi nasarar auren ki”.
B’angaren Fu’ad kuwa a waje ya tarar da Aina ta rik’e k’ugu tana jiran shi cuz ta kasa jure tsayuwa……., fuuuu ya zo zai wuce ta tayi saurin shan gaban shi tace” baka ganni bane kake k’orarin wuce ni?
Yayi yayi ya rik’e kukan a ranshi amma ya kasa sai ya fashe da mahaukacin kuka kamar k’aramin yaro” auren Nana zai yi ya aure ganganar jikin ta kamar yanda Datti ya fad’a? ko kuma hak’ura zai yi da ita da ita ya fasa auren ta?
Idan yace zai fasa auren ta kenan Datti yaci bulus a kan shi? Idan kuma yace zai aure ta bai san wani irin zama zai yi da ita ba bayan ya kamata red handed da shi sun gama aikata zina”.
Da ya d’auka cewa tilasta ta yake yi kafin ya samu biyan bukatan shi shi yasa tausayin ta ya shige shi har ya fara son ta yake jin zai iya zaman aure da ita, sai yanzu ya fahimci cewa itama jin dad’in abun take yi munafurtar shi take yi kamar bata so ashe itama jikin shi take so! tunda har ta iya kawo kanta gare shi.
Shiru gurin ya d’auka banda sautin kukan shi babu abunda ke tashi a wajen, sai kan Aina ya mugun d’aurewa tace” fad’a min mana baka samu Nanar bane?
Kai ya girgiza mata hawaye na ta zarya a saman fuskar shi” aunty aina nayi mugun gamo…idanuwa na sun gane min abunda har abada ba zan so na sake gani ba………tambayar shi ta kuma yi tana cewa”me idanuwan naka suka gane mak…….cakkk maganar ta mak’ale a mak’ogoron ta ta kasa kasa fitowa……..ba komai ne ya saka ta hakan ba illa ganin Nana da tayi ta mak’ure a guri d’aya tana kuka ga suturar jikin ta a yage”
“Whatttt”, ta fad’a a mugun mamakin ce ta tsorata matuka da ganin ta, sai yanzu ta fahimci inda maganar Fu’ad ya dosa wato kama Nana yayi kenan suna aikata zina.
Inalillahi wa’inna ilaihiraji’un me zata yi banda hawaye.
” Ashe ba za ki nutsu ki san mutumcin kanki ba, sai ki bari namiji na gara ki yanda ya ke so……..,wace irin rayuwar akuyanci ne kika zabar ma kanki?
“Ga wanda ya taimaka miki zai aure ki kin zo kina bibiyan wanda ya b’ata miki rayuwa?
Nana na kallon ta tana mamakin yanda itama Ainar tayi mata mummunar fahimta, ta bud’e baki zata yi magana Aunty Aina tayi saurin d’aga mata hannu ta hanyar dakatar da ita………….tace yi min shiru kar ki fara tunanin maganganun ki za su yi tasiri a zuciya na……., tsakanin ki da Datti na rasa gane wa ke son jikin wani”.
Kuka ne mai tsananin k’arfin gaske ya kwace ma Nana tace” don Allah Aunty ki fahimce ni ban aikata abunda kuke zato ba wallahi Sadeeq naje gani shine fa……..
“Kar ki raina wa mutane wayo wannnan rigar da aka yaga ta Sadeeq din ya yago?
Ajiyar zuciya ta sauk’e cikin kuka tana jin zafi a ranta bata da kalmar da zata yi amfani da shi ta wanke kanta.
” Aunty ba zan iya ci gaba da tsayuwan nan ba zuciya ta zata iya faso k’irjina ta fito………, yana fad’a ya sa kai ya bar wajen Aina da Nana suka bi bayan shi da sauri.
A mota suka tarar da shi Aina ta zagaya ta d’ayan gefen ta shiga, ganin haka Nana ta kai hannu ta bud’e gidan baya zata shiga, Aina tace ai sai dai ki tafi da k’afar ki ko kuma ki koma wajen wanda kika zo gurin shi ya samar miki abun hawa amma mu kam baza ki bi mu”.
“Fu’ad d’aga mota mu tafi kar haushi ya sa na kai mata bugu dan a yanda nake jina din nan zan iya b’arar mata da hak’ora.
Bayan sun iso gida Aina tayi wuffff ta shige gida ko ta barsu yayin da Nana da Fu’ad ke cikin mota ta k’i saukowa shi kuma yana jiran ta fito.
Gajiya yayi da jiran ta ya juyo yana masifa” ba za ki fita ki bar min mota ba ko sai nace miki ki fita”.
Marairace murya tayi tana sharar kwalla” don Allah ya Fu’ad kayi hakuri ka saurare ni kaji mai zan fad’a Allah ba abunda ka d’auka bane….., kaima ka san ba zan yarda na kuma tafka kuskuren da nayi a baya ba”.
Iska ya fuzar tare da bugun steering d’in motar kafin ya juyo ya tsare ta da firgitattun idanuwan shi suka kad’a zuwa launin ja” me zaki fad’a na gamsu da shi bayan abunda idanuwana suka gane min?
Upon all the fightings and sacrifices did you end up betraying me, nayi trusting d’in ki amma kin yi breaking truest d’ina ta yaya kike so na k’ara yarda da ke? Idan muka yi aure wani irin tarbiya zaki ba ma yara na?
I’m trying to make you a woman that every man will be proud to have you but ki failing d’ina Nana,
Kin tozarta ni a gaban Datti kinanta da me yace? Cewa fa yayi ke sauran shi ne, kin san yanda k’almar nan take da zafi? Yanda kika zan zafin fitan rai haka nake jin ta a raina”.
“Kukan ta ne ya dad’a tsananta, she don’t have a single wads to prove her self. Tsabar kukan da take yi sai da taji azabebben ciwon kai ya kama ta.
Hanky ya mik’a mata yace ta karb’a ta share hawayen ta kuma ta tabbatar ta daina kuka kafin ta shiga gida, idan su Ummi suka tambaye ta tace tare suke da shi.
Kai ta gyad’a mishi ta kana ta k’arb’a ta share tana gamawa ta fita daga motan ta shige gida.
Yana nan a zauna a cikin mota he cried bitterly kamar ran shi ake zarewa a lokacin shima, tsabar kuka har majina yake had’awa da kyar ya iya fitowa yayi ma motar key ya nufi d’akin shi ya danna lock ya kwanta a take jikin shi ya d’auki zafi rad’au.
B’angaren Nana kuwa cikin sa’a har ta shigo room d’in ta bata had’u da kowa a hanya ba.
Rigar jikin ta ta cire ta shiga ban d’aki tayi ta tsarkake jikin ta” cuz ta zubar da sperm a sanda yake romancing d’in ta, bayan ta gama ne ta d’aura alwala ta fara gabatar da sallolin da ake binta, tayi addu’a ta shafa kana ta koma ta kwanta.
Duk jikin ta nayi mata tsami nonowan ta ma haka balle uwa uba HQ d’in ta da ya sha hannun Datti a time d’in da yake fingering d’in ta.
Hawaye taji ya sauko mata da sa hannu ta goge” ita dai bata zo duniya a sa’a ba, rabuwan ta da farin ciki tun kafin Datti ya k’eta mata haddi, yanzu rayuwar ta kullum cikin bak’in ciki yake.
Haka ta zauna a d’akin ko fitowa bata yi ba har kusan karfe goma da rabi na dare tsohuwa da ta damu sosai yau tun zafe bata ji d’uriyar ta ba ta tambaye Aina ko Nanar na d’aki.
Tambayar ya matuk’ar kular da ita ace tun safe kake kwana site d’aya da mutum baka gan shi ba sai yanzu kake tambayar inda yake?, “oho ban sani ba baki san inda d’akin ta yake bane da zaki tambaye ni?
” Tab’e baki tayi tace” au maida wukar na ga ai yar uwar ki ce shi yasa na tambaya zaki fini sanin lafiyar ta”.
“Tsaki Aina tayi bata sake bin ta kanta ba ganin haka tsohuwa ta ja baki tayi shiru jefi-jefi tana satar kallon k’ofan d’akin Nana, abun duniya duk ya ishe ta.
Uban tagumi ta had’a bata daddara ba tace” ke ko y’an nan ko zaki duba mana ita? Allah tsoro ya fara kama ni kin san raba ta da akayi da shegen d’an ta nan fa kar ta kuma guduwa bamu san ba……..Shiru tayi a sakamakon muguwar hararar da Ainar ta aika mata da shi……..ta natsu tsitttttttt abun ta.
Kallon k’ofan d’akin Nanan tayi tana so ta shiga amma tana kunyar ta, musamman da ta tuna yanda take mata ba’a a kan haife shegen da tayi……da ta gano cewa ashe uban shegen na nan a gidan su sai jikin ta yayi sanyi tun daga ranar take kunyar Nanar.
Kamar baza ta tafi ba sai ta mik’e ta nufi d’akin ta tsaya a bakin k’ofa kamar ta shiga ne kamar kar ta shiga, kusan minti biyar ta d’auka a tsaye a wajen Aina na kallon ta sai ta manta da abunda ke damun ta taji dariya na neman subuce mata musamman yanda ta ga tana rarraba ido kamar an tare burgu a rami, da kyar ta da ke tayi kamar bata gan ta ba.
Tsohuwa kam ana nan an dab’e duk abun kunya ya gama kama ta, k’arfin hali tayi ta shiga ta wulla ido………, daga kwance ta hango ta ta lumshe ido kamar mai jin barci amma a zahirin gaske ba barcin take yi ba, tsabar tunani ne yayi mata katutu a zuciyan ta.
Zama tayi a gefen gadon ta tab’o ta da hannu Nana tayi saurin bud’e ido tana kallon ta. Fuskar ta ne ya bayyana tsantsar mamakin ganin ta a d’akin.
“Murya irin ta borin kunya tace” lafiya yau ko d’uriyar ki banji ba a parlour, wallahi duk na damu, yanda ta kare maganar cikin k’arya murya ta yi shi.
“Nana dai ta cika da mamaki sosai, yaushe tsohuwa ta fara damuwa da ita har bata gan ta ba take neman ta, sai ta batsar tace” babu komai kaina ne ke ciwo”.
“Ayya ai kya yi magana likitan gida ya duba ki zama da ciwo ai ba dad’i musamman yanzu da dare yayi ciwon dare ai yafi tsanani”.
” A’a ba sai an kira shi ba na sha magani ma har kan ya daina min ciwo yanzu ma barci na fara shine kika tarar da ni a haka”.
“Ashaa ai ban sani ba da ban tashe ki ba, yanzu sai ki koma ki kwanta Allah ya bada lafiya”.
Ameen ta amsa tsohuwa ta fita ta bar d’akin, a parlour ta tarar da Aina ta ja tsaki tace” to y’ar bak’in ciki da kin d’auka jika ta ta gudu ne? Mtswwe ta kuma jan tsaki tayi shigewan ta d’aki, da ta tuna da d’an bunsurun jikan ta ta shige d’aki tana kuka wi-wi da ido” Alhaji daga d’akin shi ya fito ya tarar tana kuka hankalin shi ya matuk’ar tashi sosai yake tambayar lafiya, sai ta rushe da uban kuka tace” wallahi sai da na d’auki alhakin yarinyar nan na dinga ci mata mutunci ashe munafukin na nan a cikin gidan nan”.
“Hege kawai marar mutunci daga bashi amanar y’a ya lallab’a ya farketa karshe ma ya dura mata ciki ta haife mishi.”
Allah da na san hakan zata faru da tun lokacin da take fad’a mana abunda yake yi mata muna k’aryata ta da na d’auki ice na kwala mishi a wajen na cire abun ko na nakasa ta yanda abun ba zai tashi ba balle ya samu k’arfin fasa gaban ta”.
“Hmmmmm aikin gama ya riga da ya gama sai dai muyi hakuri kawai mu rungumi k’addara”.
” Ni yaron ma yanda ka san na murde shi ya mutu kowa ya huta, yanzu ko kwatance aka tashi yi da gidan nan za’a ce wanda d’an uwan ta yayi mata ciki ta haihu ni kuma ace tsohuwar da jikokin da suka haifi shege”, ta kuma k’ara sautin kukan har da majina da dai ya rasa yanda zai yi da fitinar ta yayi mata sallama ya koma d’aki abun shi ya bar ta nan taci gaba da kukan nata.
Daren daranar Fu’ad ko rintsawa bai yi ba idan ya kulle ido sai hoton abun ya dawo mishi sabo nan da nan sai gaban shi ya fad’i yayi saurin bud’ewa ido yana hawaye.
Aina kam a nata b’angaren tunanin halin da y’ar uwar ta take nema ta jefa kan ta a ciki da kuma Datti da yake cikin halin da yake tsananin bukatan taimako har take jin a ranta kamar ko Nanar tayi aure Datti ba daina bibiyan ta zai yi ba, da wannan tunanin ta yanke hukuncin gobe da safe idan Allah ya kaimu ta sake tuntub’ar Alhaji kan maganar su ta baya, sai dai tana amsar da zata samu a wurin shi.

 

*eedatou*

 

 

*💫SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*

“`{The more we shine bright the more we educate and entighten our readers}“`

https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45
🍇🍇🍇 *UNCLE DATTI*🍇🍇🍇.
“`JIKINA YAKE SO!“`
©
*eedatou✍🏻*
“`Follow and ✅ote me on Wattpad:“` *eedatou*
~Ina so duk wanda ya karanta wan d’auki hakuri labari ne wanda aka tsara tun daga farko har karshen littafin, darasin kawai ake so, da fatan zaku fahimce ni, kuma baza kuce nayi ma wani adalci banyi ma wani ba, ni kaina ba lallai ne sai wanda nake so zan bawa narasa ba,~

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button