Sponsored Links
Duk Karfin Izzata Book 1Hausa Novels

Duk karfin Izzata Book 1 Page 12

Sponsored Links

*Star Lady*

 

 

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

 

*Episode 12*

A zafafe Aryan yace ke kima mutane shiru a nan “idon kowa na palon yadawo kan Aryan ya turnuke fuskar nan tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ” Yusuf da Khalid kuwa sai murnushi suke “Abba ya dube’sa kana yace “ina ruwan ka, kai takewa hirane, chigaba da faɗamin ƴata ya kukayi kasanima ko dashi zaayi bikin ” Aryan zai sake magana idonsa yasauka kan aunty amarya dake wurga masa mugun kallo ganin hakan yasa yamike yabar palan

…..dariya diyana tayi san nan tace “Abba nifa matar sojane soja zan aura irin mugayen sojojin nan masu manya manya bindiga ” Ammi ganin diyana tafara sakin layi yasa tamata magana da harchen fullanchi tache tatashi suje suyi sallar mangariba ” ba musu suka miƙe suka nufi ɗakin su ” Aunty amarya mikewa tayi tafiche sai huchi take ” mai martaba yace dasu Yusuf kutashi mutafi masallachi mikewa sukayi gaba ɗaya matasan suka fiche ” Ammi ta dubi Ummi tace yakamata muma muje muyi sallah Koh, atare suka mike suka fita

Misalin karfe 8 na dare gaba ɗayansu sunhadu a palo dan chin abinchin dare amma banda DON da kuma Aryan basuzoba ” yusuf ne yakalli diyana yace sister jiki dubo yaya Aryan a daki kiche yazo muchi abinchi ” to diyana tace tare da mikewa zata fita ” kamar daga sama sukaji Aunty amarya tana faɗin ke dawo kizauna Umar tashi kaje ka kirashi ” kallo mai martaba yusuf yayi kana yajuya ya kalli Khalid zaiyi magana ke nan Abba yarigasa da chewa “jeki kirasa diyana da sauri ta fita daga palon dan ganin mugun kallon da Aunty amarya ke mata ” farinchikine ya lulluɓe Khalid da Yusuf sai murnushi suke

Da sallama tashiga palon babu kowa kai tsaye tawuche betroom batayi sallama tashige kwanche yake a kan gado idansa a lunshe har bakin gadon taje ta duƙa a nitse tace yaya Aryan shiru bai amsaba dataji shiru sai tamike ta zauna a gefen gadon tasa hannu tana bubbuga hannunsa tana kiran su nansa, shiru shiru bai amsaba baikumayi motsiba ganin hakan yasa, tasa hannunta tana kokarin buɗe idon’sa dakarfi ” a zafafe ya damki hannun nata batare daya buɗe idon ba ” aruɗe take kokarin kwache hannunta dan tagudu ” slowly ya ware manya manya ash eyes ɗin nan nasa akan face ɗinta ” sanye take chikin jallabiya baki still dai kanta ba ɗan kwali ” a tsorace tasoma magana dan allah kayi hakuri allah bazan sakeba ” kara daure fuska yayi sosai yafara Magana, meyakawoki ɗakin nan ” Abba ne yace nakiraka tabashi amsa ” jinjina kai yayi tare da mikewa zaune ya saki hannun nata, aiko kamar jira take yasaketa ta yunkura aguje zata sauƙa gadon ” a zafafe Aryan ya damkoh gashin kanta ya jawota baya har saida tafaɗa kan chinyarsa ” kware baki tayi zatayi ihu yasa hannu da sauri ya rufe mata baki yana kallanta ” girgiza masa kai tafarayi tana hawaye ” calmly yafara magana wani uncle nakune yace yana sonki kuma dayace yanason naki mekikache masa yayi maganar tare da zame hannunsa daga bakinta dakuma rikon dayayiwa gashin kanta ” chikin shesshekar kuka tace uncle Omar kuma ni bani yafaɗawaba Zahra ya faɗawa kuma ninache’wa Zahra tafaɗa masa soja nakeso soja zan aura ” kara waro ido waje Aryan yayi yana kallanta yadda take magana a nitse yama rasa me zaiche mata ” bayan tagama magana’ne ” yace to tashimin a kafa” da sauri tamike tana kokarin sauka daga gadan ” ai banchi ki sauka bakoh chewa nayi kitashimin a kafa kawai juyo nan ki kalleni kuma ki saurari abunda zan faɗamiki chewar Aryan ” a hankali ta gyara zamanta a kan gadon san nan tajuyo tana fuskantarshi ” Aryan yace sau’nawa yanzu inamiki magana a kan ɗan kwali eh, ” shiru tayi kana ta sunkuyar da kai ” meyasa bakyajin maganata meyasa kikesan ɓatamin raine eh ” ɗago kai tayi ta ɗan kallesa taga ita yake kallo a hankali tace kayi hakuri zan rinka sawa ” jinjina kai yayi yana faɗin to meyasama bakisan ɗan kwali ne ” turo dan bakin nan nata tayi tana faɗin Allah yaya Aryan zafi nakeji idan nasa ɗan kwali gashinne yayi yawa shiyasafa nache ra nan ka askemin kaki ” shiru yaɗanyi kafin nan yace Aunty amarya na falone ” eh tana nan tabashi amsa ” ok to tashi kije inazuwa chewar Aryan ” da sauri tamike dan daman kamar a kan ƙaya take har takai bakin kofa kome tatuna saikuma tajuyo ta fashe da kuka” da mamaki Aryan ke kallonta” kuka take sosai gashi tana tsaye taki tafiya ” alama yamata da hannu a kan tazo ” ba musu tazo kusa da gadan ta duka tana kuka ” meyafaru kuma meyasaki kuka Aryan ya tambayeta ” chikin kuka tace innar yaya bello tafaɗamin idan nabari namiji yataba jikina to zansamu chiki shine kuma gashi kai kataba jikina ” Aryan baima san sanda dariya ta kubche masaba ” ganin yana mata dariya yasa tasake kara sautin kukan nata ” shiru yayi yana kallan yadda take rera kuka tsakaninta da allah yama rasa me zai chemata kusan 10 tukun nan idea tazo masa, ya sa hannu ya ɗago habarta kasa kasa yace kidena kuka ni ai yayankine ko nataɓaki bazaki samu chikiba amma idan kikayiwa wani namiji magana ko kikabari yataba hannuki tabbas zaki samu chiki ” da sauri tace to yanzu yaya Aryan bazan samu chikiba ” eh bazaki samuba ai nafaɗamiki ni yayankine babu abunda zaki samu dan natabaki ” mikewa tayi tana dariya kamar ba mai kuka yanzun nanba ” zuba mata ido yayi yana kallanta chan kuma yace sannu mai kuka da dariya lokachi guda ” hannutasa ta rufe fuska tajuya tanufi hanyar fita ” binta yayi da kallo har tafiche wani nauyayyar ajiyar zuchiya ya sauke san nan
yamike yanufi toilet danyin wanka
A gurguje yayi wanka yafito yasa farar jallabiya yafito yanufi palan mai martaba ” da sallam yashiga lokachin kuwa duk matasan sungama chin abinchinsu kowa ya watse sauran Ammi da Ummi sai mai martaba
Zama yayi tare da gaidasu ” Ummi takira masu aiki sukazo suka zuba masa white rice an beans da steew yaji kaji sai wani ferfesu a ɗayan plate ɗin suka tura masa gabansa ” a nitse yafara chin abinchin ” mikewa Ammi tayi tanawa Ummi da mai martaba sai dasafe ” Ammi pls kifaɗawa yarinyar nan takawomin coffee dawuri dan inajin barchi chewar Aryan “to kawai Ammi tace san nan tafice

A bangarensu diyana kuwa zaune suke a ɗaki zahra da hiyana sunna karatun boko amrat na karatun qur’ani lamrat na buga game a wayar Zahra Aunty diyana kuwa tana zaune gaban mirriow, wai taga wani kwalli a wayar zahra zatayi irinsa sai faman pente pente takewa fuskarta ” ba ƙarya tayi kyau sosai dan diyana daman akoi san kwalliya shiyasa ta dage takoyi kwalliya sosai awajen Zahra
Bayan tagama kwalliyar ne, tamike tanufi wajen kayansawarsu wani wandon jeans blue ta daukoh da t-shirt pink tanufi toilet jim kaɗan saigata ta fito wow bakaramin kyau tayiba ga wandon ya ɗan kamata shape nata yafito sosai yaukam tatara gashin kanta ta ɗaure a tsakiyar, high heel blue ta daukoh kalan wandon tasa a kafarta diyana akoi san high heel sosai ” hiyana che ta ɗago tana kallanta kana tace diyana kwalliya da daddaren nan inazakije, gaba ɗaya su zahra ma suka ɗago suna kallanta ” babu inda zanje kawai dai yau naji inasanyin kwalliyar darene ” wow my diyana kinyi kyau sosai chewar Zahra ” Allah aunty zahra to pls ki ɗaukeni hoto mai kyau a wayarki kinji ” to zahra tace. San nan ta karɓi wayar daga hannun lamrat tafara yiwa diyana hotona ” da sallama Ammi tashigo ɗakin tasamesu sai hoto Zahra ke ɗaukan diyana girgiza kai kawai Ammi tayi kana ” tace ke diyana kije kikaiwa yayanku Aryan coffee yanzun nan ” to kawai diyana tace Ammi kuma tayi waje tanufi betroom ɗinta ” ya isa hotan haka Aunty zahra bari naje nakaiwa yaya Aryan coffee karna ɓata lokachi ya bugeni idanna dawo saiki kara ɗaukana wasu ” to kawai zahra tache ” juyawa diyana tayi tanufi hanyar fita hartakai bakin kofar fita saikuma ta juyo ta dawo ta daukoh dan karamin gyale pink tasa a kanta tafiche tanufi kichin ” a gurguje ta haɗa coffee ɗin ta ɗaukoh tanufo bangaren Aryan

Da sallama tashiga palon babu kowa kai tsaye betroom ɗin tanufa basallama tashiga babu kowa a chiki dan haka tanufi kan table ɗin ta ajiye coffee ɗin har zata juya tafita saikuma idanta ya sauka kan hotunan Aryan dake kan drowar gefen gado ansasu chikin freme kanana,
zagayowa tayi tawajen ta zauna a bakin gadon tasa hannu ta ɗaukoh hotu nan dukka ukun ɗaya shida don ne sunsa kakin sojoji ɗayan kuma shi kaɗai ne sanye da jeans baki da white t-shirt ɗayan kuma shida don da yusuf ne dukkansu da wandon sojoji ajikinsu da green t-shirt, shiru tayi tana kallansu chankuma tace kai ashe da gaskenefa hiyana nakama da wan nan mugun tayi maganar tana nuna don kai kuma yaya Aryan inshaa allah soja zan aura wanda zaimin maganinka da kai da bindigar taka, allah sarki yaya yusuf wlh a gidan nan shida yaya Khalid ne kawai mutanen kirki hakadai diyana tayita surutun ta ita kaɗai har ya isheta san na ta ajiye hoto nan tamike tajuyo zata nufi waje idanta ya sauka chikin nashi tsaye yake abakin kofar shigowa betroom ɗin ya harɗe hannu a kirji ya zuba mata ash eyes nashi kallanta kawai yake yakasa ɗauke kai
Murya na rawa tace ina wuni yaya Aryan ” ajiyar zuchiya Aryan ya sauke san nan yakarisa shigowa ɗakin yazauna a bakin gado ” diyana naganin ya matsa a hanya yazo ya zauna a bakin gado ta watsa a guje zatayi waje saidai tamanta high heel tasa bazata iya gudu sosaiba,
taku biyu Aryan yayi ya damki kugunta ta baya tsabar tsoro da razana yasa nunfashinta ɗaukewa ɗif ” jin jikinta ya sakine yasa ya riketa da kyau kana ya juyo da ita yana kallan fuskarta da alamar ta sume fa ɗaukan ta yayi ya kaita kan faffaɗar gadansa ya kwantar da ita, zubamata ido yayi sosai yana kallanta from head to toe wow ya furta a filli kana yace masha allah koba komai yaudai ansa ɗan kwalin nan shafa gefen fuskarsa yayi tare da sauke ajiyar zuchiya yajuya yanufi inda ta ajiye masa coffee ɗin
Daukan cup ɗin yayi yabar plate ɗin yanufi saman sofa ya zauna yafara sha a nitse sai dayaga sha san nan yamike yanufi freig ruwan faro ya ɗaukoh yadawo kan gadan zama yayi a gefen gadan san nan yabuɗe robar ruwan ya tarfa a hannunsa ya shafa mata a fuska dogon numfashi taja tareda sauke nauyayyar ajiyar zuchiya a hankali tafara buɗe idanta karaf ta saukesu a chikin nashi dankuwa shima kallanta yake ” da sauri ta rufe idan ta tana faɗin dan allah yaya Aryan karka bugeni natuba bazan sake taba maka komai na ɗakin kaba ” wai ma menamikine dakike chemin mugu akoda yaushe chewar Aryan ” batare data buɗe idoba tace natuba bazan sake chewaba ” to idan kikasakefa ” da sauri tace kamin duk abun da kakeso ” kintabbatar inkinsake namiki kome nakeso chewar Aryan ” eh nayarda kamin kome kakeso amma dai yanzu kayi hakuri wlh barchi nakeji ” Aryan ya jinjina kai yana faɗin to buɗe idon ki, ki kalleni ” slowly tabuɗe idon still dai ita yake kallo ganin bazata iya haɗa ido dashi bane yasa ta juya idonta tana kallansama ” murmushi kaɗan Aryan yayi a’zuchiyarsa kuwa yana faɗin a shedai tanajin kunya ” jin yayi shirune yasa tace yaya Aryan intafi ɗaki ” kinasan tafiyane chewar Aryan ” da sauri tace eh ” ok to tashi kije dasafe zamiyi maganar danake san muyin ” da sauri tamike har takai bakin kofa sai taji Aryan yace ke, da sauri ta juyo tana kallansa ” a hankali yafurta kinyi kyau sosai dakikasa ɗan kwali ” murmushi tayi san nan tace to yaya Aryan tunda nayi kyau pls kamin hoto idan kamin ni kaɗai sai kuma kamana mubiyu ” ok to zokitsaya namiki ” da sauri ta dawo chikin ɗakin wayarsa ya ɗaukoh yafara daukanta hoto duk san hotonta sai da, da kanta tace to ya isa yaya Aryan saura nida kai kama ko guda ɗayane tare ” Aryan yace ok to zoki zauna yayi maganar yana nuna mata gefensa ” zama tazo tayi a gefensa ” ɗan karkatowa kaɗan yayi yarage tsawonsa ya haɗe kansu ya saita wayar yafa ɗaukansu hoto sai daya musu kala 10 tukun nan yace to jeki kwanta ” to tache masa san nan tamike tafiche daga ɗakin ” ajiyar zuchiya mai nauyi ya sauke san nan a fili yace Aryan waishin meyake damunkane shiru yayi yana tunani dayaga tunanin nan bawata mafita dazata bashi sai ya karisa hawa gadon kawai ya kwanta ya ɗauki remote ya rage gudun AC yayi shiru kamar mai tunani yana fuskantar sama har barchi ɓarawo ya ɗaukesa

Diyana kuwa tana fita tayi bangarensu basallama kawai tafaɗa ɗakinsu zaune tasamu zahra a kan gado zahra naganinta tamike tana ” faɗin diyana lfy kika Jima allah dai yasa yaya Aryan bai bugekiba”guntun tsaki diyana taja san nan tace eh bai bugeniba” Alhadulillah zahra tace san nan takoma ta kwanta ” itama diyana kayan jikinta tachire tasa na barchi ta haugado tana faɗin hmmmm wato hiyana kam barchinta ma tayi koh ” to me zata zauna tamiki barchita zatayimana chewar zahra ” diyana bata sake magana ba saima juyawa datayi tana fuskantar yamma har barchi ya ɗauketa

Misalin karfe 4 na asuba gaba ɗaya family sun haɗu suna sahur ban da don ” Aryan ya dubi diyana yace ke jeki kawomin coffee ” diyana na kokarin mikewa ” aunty amarya ta dakamata tsawa ke yizamanki bazata kawoba kuma daga yau nahana maganar coffee idan kannenka maza bazasu kawoma ba to kahakura da sha ” shiru palon yayi babu wanda ya tanka diyana kuwa tsayuwa tayi tarasa maganar wazata bi, idan taje takawo coffee aunty amarya zata hukuntata, idankuma bata kawoba yaya Aryan zai hukuntata kawai sai tafasa ihu ” gabaɗaya jamaa’ar palon suka ɗago suna kallonta ” a nitse Aryan yace kukan ya isa zokiyi zamanki kyale coffee ɗin ” ai tunbai gama maganaba ta zauna abunta takuma yi shiru ” dogon tsaki fahad yaja san nan yace darabon wlh nizan babballa yarinyar nan yanzu dan iskanchi me aka…. bai karisa baganarba sakamakon mugun kallon da Aryan ya wurgamasa ” aunty amarya kuwa mike tayi tana faɗin kai idan kagama kazo ɗaki inada magana da kai tayi maganar tana nuna Aryan san nan ta fice ” dogon tsaki aiman yaja san nan shima yamike yana faɗin dole nabar kasar nan gobe yayi waje ” mai marbata kam ido kawai yake binsu dashi ” Ummi tace ba akaiwa prince a’binchinsaba’fa ” Ammi tace to su tashi sukai masa mana ” fahad yamike yana faɗin barinaje na kaimasa san nan yayi waje

Mikewa aryan yayi zaiyi waje ” Mai martaba yace inazaka ” alwala zanje nayi Aryan yabashi amsa ” ok idan mundawo masallahchin kasameni a ɗaki chewar mai marbata ” ok kawai Aryan ya amsa dashi san nan yayi waje ” mai martaba ma mikewa yayi yana faɗin to yakamata kuje kuyi alwala dan sauran 20 mnt afara kiran Sallah yana gama faɗin haka yanufi ɗakinsa ” mikewa sukayi da ɗai ɗai sukabar palon

Misalin karfe 9 zaune take a chikin class nasu uncle nasu yashigo yana tambayat wacece fateema abubakar saraki ” da sauri zahra tace nine” oh to kifito zakuje duba uncle nakune bai da lfy kowani class zamu ɗauki mutun ɗaya ” to kawai zahra tace san nan ta ɗauki jakarta tafito sukayi waje da uncle nasu yan mata 7 tasamu tsaye a wajen tare suka jera har wajen motar makarantar suka shiga da gudu motar tabar makarantar ” suna tafiyane Zahra ke tambayar yanmatan wani uncle ne bai da lfy
Sukache mata wlh suma basu saniba ” shiru zahra tayi batasake maganaba har suka isa gidan uncle ɗin driver na parking suka fito uncle Aminu yamusu jagora zuwa chikin gida ga mamakinta saitaga uncle Omar nefa nan tafa tunanin wai ba jiya suka rabu lfy’ba kodai accident yayine ga kafarsa duk bandeji gashi har goshinsa, tayi nisa chikin tunanin sai taji muryan uncle Omar yana faɗin fateema har dake a kazo ” eh uncle inawuni yajiki zahra tabashi amsa ” lfy fateema jiki da sauki ” to allah yakara sauki chewar Zahra gaba ɗaya suka amsa da amin san nan suka mike suka masa sallama yana musu godiya har suka fice sukaje sukashiga motar makarantar ta maidasu

Misalin karfe 5 na yamma zahra hiyana diyana amrat lamat suna zaune a palon Ammi suna kallo ” hiyana tace lamrat kije kikawomin fura da nono a palon mai martaba dan na freig ɗin Ammi yakare ” hararar wasa Zahra tawa hiyana tana faɗin yanzu sai’kisha furar a gabanmu bazakiji kunyaba idan wani yashigo yaga baki a’zumifa ” murmushi kaɗan hiyana tayi amma saida ɗimple nata ya lotsa tace aa aunty zahra bafa a nan zansha ba ɗaki zantafi mana ” Zahra zatayi magana ” diyana tarigata dachewa to ina ruwan wani dake inbaki azumin ma ina ruwansu nifa wlh inniche koh har tsakar gida zanje inachin chingom ” baki buɗe Zahra da hiyana ke kallon diyana itakam ko ajikinta dan batamasan abun datake faɗinba kawai duk maganar dayazo bakinta take faɗi ” lamrat kuwa mikewa tayi tafita tanufi palon mai martaba ” daukoh fura biyu tayi da nono roba 1 san nan ta ɗauki kwarya yajuye nonon a chiki tajefa furar a chiki kwaryan san nan tasa ludayi ta dauka tafito tanufi part din Ammi ” daga nesa yusuf ke kallanta tana tafiya a nitse chikin kwanchiyar hankala sai murnushi yake ” tazo dai dai zata shiga ɓan garen Ammi tayi karo da haidar nono yazube masa ajiki ” wani wawan mari ya sakar mata a kumatu ” wani ƙara tafasa ta kwasa aguje tai chikin gidan kai tsaye palo Ammi tanufa ” shikuma haidar yanaganin ta tafi yaja doguwar tsaki yajuya zai wuche part nasu kamar daga sama yaji saukar mari shima, a razane ya ɗago kai, ” ido huɗu sukayi da Yusuf fuskar nan tamkar an aikomasa da mutu a kausashe yace metamaka kamareta eh ” murya narawa haidar yace kayi hakuri yaya yusuf wlh raina ne yabachi ” shoot up wai kubaku da tausayine eh yanzu kowani kagani zai mareta bazaka hanashiba to wlh idan kasake gigin taɓa yarin yar nan sai ranka ya ɓachi wuche kabani waje chewar yusuf ” jiki ba kwari haidar yawuche ” yusuf kuwa yabi bayan lamrat

Da sallama yashigo balan kwanche kan kafar hiyana yasameta sai kuka take ” a nitse yace my baby taso kizo ” aiko tanajin muryansa tamike da gudu tanufeshi hannu yabuɗe mata tafaɗa kirjinsa tana kuka kasa kasa ” hannu yasa yaɗago habarta kasa kasa yafara magana ya isa haka kukan kinji goge hawayenki yayi maganar tare da ɗan sakinta kana yazaro hand’kee daga aljihunsa yamiƙa mata ” hannu tasa ta amshi hand Kee ɗin tagoge hawayenta” shikuma yarikoh hannunta suka fiche daga palon ”

Su zahra dai baki bude suke kallan yaya Yusuf har ya fice rike da hiyana ” mikewa Zahra tayi tana faɗin lokachin shirya kayan buɗa baki yayi tayi gaba su hiyanama suka mike sukabi bayanta

yusuf kuwa suna fita shida lamrat sukayi bangaren Ummi ” da sallama suka shiga palon ” Ummi dake zaune kan kujera mai zaman mutun biyu ta amsa da waalaikassalam, shigowa chiki sukayi yana rike da hannunta ” Ummi naganinsu tafara murmushi tana faɗin waya taɓomini lamra’ta Naga alamar tayi kuka ” murmushi yusuf yayi kana yace babu kowa shagwaɓa chekawai ” Ummi tace to taso kizo kusa dani ” da sauri lamrat ta mike takoma kusa da Ummi ” yusuf zaiyi magana sai aka kirasa a waya mikewa yayi yace Ummi inazuwa yayi waje.

 

To a kwana a tashi babu wuya awajen allah yau jirginsu mai martaba yatashi zuwa Umrah gaba ɗaya yan gidan suntafi sauran yammatan Ammi kawai suma dan ba abasu hutun makaranta bane shiyasa dagasu sai masu aiki aka bari a gidan sai security dakuma wasu daga chikin sojojin yaya prince da yaya Aryan da yaya yusuf
“yauma kamar kullun shirinsu sukayi tsab nazuwa school suka fito harabar gidan nantake drivers ɗin su, sukazo da gudu suka buɗe musu motochin suna shiga suma drivers ɗin suka shiga dagudu suka tada motochin suka bar gidan gudu suke da motochin sosai chikin ƙanƙannin lokachi suka isa school ɗin, suna parking su hiyana suka fito suka nufi wajen dasuke zama kafin a shiga class ” drivers kuma suka juya kan motochin suka koma gida ”

misalin karfe 9 na safe bayan antashi break zaune suke sunata hirarsu awajen game na makarantar kamar daga sama sukaji jabir yana faɗin “hiyana taso muje, chikin tsiwa diyana tace wlh yaukam babu inda zataje Exam fa akeyi bata gama rufe bakiba taga jabir yaɗaga hannu a fusache zai..

more comments an share

*💫STAR LADY💫*

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star Lady*

 

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

 

*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button