Sponsored Links
Duk Karfin Izzata Book 1Hausa NovelsHausa Novels and Love Stories

Duk karfin Izzata Book 1 Paga 1

Sponsored Links

Episode 1*

💖الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر💖

 

London United Kingdom

Wasu haɗaɗun samari ne zaune awani katafaren palo mai girman gaske,Mai ɗauke da manya manya sofa set 2,launin Brown da ratsin milk, gawasu triple staircase ɗaya ta bangaren hagu ɗaya bangaren dama ɗayan kuma a tsakiya daga gefe kuma wani haɗaɗen table ɗin chin abin chine, ga wata makekiyar Tv a gefe guda,palon yaji komai da ake buƙata dan in nache zan tsaya zayyana muku ha’ɗuwar palon nan tofa sae mukare littafin nan a palo kawae, kae dakaga wajen kasan baƙara min dukiya aka narka awajen ba,”zaune suke,shiru ba mai magana ” kowa da abin dayake fuskar nan tasu kuwa tamkar an aiko musu da sakon mutuwa ” gasu kyawawa sosai kamar larabawa

Farare ne sosai dukkan su kamannin su ɗaya kallo ɗaya zaka musu kagane yan uwan juna ne amma biyu dake zaune a saman sofa mai zaman mutun 2 nan,sunfi kama da juna sosai dan kuwa kamar an tsaga kara, haka suke suna da dogon hanchi sosai, ga manya manyan ido sai dai abun mamakin kowa dakalar idansa biyu daga chikinsu dake zaune saman sofa guda kwayar idansu ash colour ne biyun dake gefe kuma idan nasu light green ne shikuma ɗayan idan sa baki ne, ga idon nasu manya manya ” ga ɗan karamin red lips, ga lallausan bakin saje kwanche a guskar su, sai dai uku daga chikin su gemun su bai da tsawo sosai san nan kuma suna da gashin kai mai tsawo har baya kamar mace.

“wani haɗaɗen saurayi ne ya sauko daga staircase ɗin tsakiya yana faɗin haba DON yabaku’shiryaba Aryan Aiman yusuf Ahmad me kuke jira

(nikoh nache daman wayannan turawan sunajin hausane)

ɗago ido DON yayi “wadda shi idansa ya kasanche light green ne,yana faɗin “shirin zuwa in kuma Khalid,Akule khalid yace “shirin zuwa Nageria mana ko kun manta gobe za’a ɗaura auren hisham,mike DON yayi yana faɗin “bazanje ba nikam san nan yanufi saman stair ɗin ban garen hagu,da sauri khalid yajuya daniyar yasha gabansa,Yusuf yamike yarike sa, a’fusache khalid Yajuyo yana faɗin “yusuf kasakeni ” Yusuf ya ɗago ido shima dai idan nasa light green gasu manya manya masu kyan gaske yache “aa khalid bazan sakekaba kafasan kokabishi ba chanza magana zaiba saidaima kubata,yakamata ache idan dasabo kasaba ɗan kasan, yaya prince fa idan yayi magana to yayine baya chan zawa, shiyasa muka chanza masa suna daga prince Safras muka maidashi DON, dan in yayi maganafa it’s done angama baya chanza wa “pls yusuf ka kyaleni wlh yau kam dole DON, ya chanza magana haba dan allah ai kobazaije bikin kowaba dole yaje na hisham, saboda tare muka taso gaba ɗayan mu, dukkan mu abu ɗaya’ne chewar khalid “ɗaya daga chikin matasan dake zaune saman sofan ne yamike yache “to ni ma dai ba zuwa zanyi ba, yana gama fadin haka yajuya yanufi stair ɗin ban garen hagu “a fusache yusuf yajuyo yana binsa da kallo yace what wae Aryan meyake damun kune “ɗaya daga chikin su’ma yasake mikewa yana faɗin to dai kunsan tsakanina da Aryan, babu ban ban chi, idan yayi abu, nima zanyi idankuma bai yi’ba nima bazan yiba, dan tare aka haife mu kuma tare muke komai, yana kaiwa nan ya juya shima yanufi stair ɗin bangaren dama ” kwashe wa da dariya Ahmad yayi, yana fadin amma Aryan da Aiman yan iska’ne wlh anafaman kashe wutar da DON yake kokari kunna’wa su kuma zasu kunna nasu. “akule yusuf yache kaikuma Ahmad menene hakan to ae wan nan ba abun dariya bane,ae ko zakuyi’wa, kowa irin wan nan rashin mutunchin tofa banda hisham, kar’kamanta fa tare muka taso, tare mukeyi duk wani abun daza muyi komai namu iri’ɗaya duk da iyayen mu ba ɗaya ba, katashi muje mushawo kan DON tukunnan muje musamu yaya Aryan, dan shine matsalar idan yache zaije tofa Aiman mai sau’kine, dan shi duk abun da Aryan ya aika’ta shima ae’katawa zai yi ” kama hanyar tafiya khalid yayi yana faɗin wlh yau DON ya batamin rai haba dan allah ” da sauri Ahmad ya rufe’masa baki da hannun sa yache ya isa yanzu dai muje mushawo kansu dan sulhu muke nema dasu ba faɗa ba “faɗa masa dai chewar yusuf ” haurawa saman stair sukayi wani katafaren hadadde palo suka shiga ” palan ya tsaru iya tsaruwa komai na chikinsa farine tas harta labulayen suma farare ne tas ga manya manya sofa set ɗaya gawani makekiyar plasma TV dake gefe,babu kowa a palon sae karan AC dake tayi, kai tsaye suka nufi chikin betroom ɗin,”subhanallah tsarki ya tabbata ga ubangiji jama’a ninaga aljannar duniya,manya manya sofa set ne,set 1 ga wani ɗan karamin table a tsakiya,gefe guda kuwa wani katafaren gado wadda ko mutun 10 zasu iya kwan chiya a kae, daga ɓan garen hagu kuwa kofar dressing room ne,sae kofar toilet kusa da dressing room ɗin, betroom ɗin ya tsaru’ne sosai idan nache zan tsaya zayya no muku tsaru war batroom ɗin nan to zamu kwana mu wuni bamu gama ba”kwanche DON yake akan katafaren gadon’sa dake shin fiɗe da white bet shit,kwan che yake ya miƙe kafar’sa har tawuche gadon tsawo,ya chire rigar sa faffaɗar kirjin nan nasa abuɗe ga wani gashi dark black mai tsantsi kwan che a kan faffadar kirjin nasa, damtsen hannun nan nashi kuwa tamkar zasu fashe,saboda karfi, kamar wani sa’daukin yaƙi,”yana’jin shigon war su Khalid amma ko kallan inda suke baiyi ba
yusuf ya wuche wajen courting ɗin yasa hannu ya yaye,wata kofar glass ne ya bayyana awajen daga chikin daki kana kallan me a wajen,wajen shaƙa’tawane mai dauke da runfa da kugeru awajen da wata table a tsaki yar kugerun, agefen kuwa wani dan karamin pool ne mai kama da baf ɗin wanka, yana ɗauke ta sky blue ruwa

“DON pls katashi muna’san magana, da kai ne chewar Yusuf” shiru DON yayi kamar baiji su ba “hayewa gadon Khalid yayi,yana faɗin pls prince katashi mana, ko kallan inda suke DON bai yi’ba bare su sa ran zai amsa musu, “haba big bro dan allah to imma bazaka tashi ba,pls kaba mu amsa dan awan nan karan ba shiru muke san kayiba, kanaji koh chewar yusuf ” DON dae bai tanka su ba “a fusace Ahmad yace look DON dan Allah kar ka che bazakaje bikin hisham ba wlh idan kayi haka baka kyauta ba,kasani hisham fa jinin mune ” dogon tsaki DON yaja atakai che yace in kungama zanchen naku saiku fita kubar’min ɗaki, dan kuna damuna wlh ” afusa’che Khalid yafara magana wlh bazamufita mu zakawa iskan’chi to barikaji dole kaje bikin hisham, in bahakaba sai dai kazaba ko,mu kokuma ka kasanche kai kadai “a’takaiche DON yace ae daman ni ka ɗae nafijin daɗin rayuwa “haka kache koh, baisake che musu ko uppan ba haka sukayita surutun su har suka gaji sukamike suka fita suna fita ” DON ya daukoh wata remot ya saita’ta saitin kofar dakin ya danna remot din jikake lok lok kofar tana kulle kanta,ajiye remot ɗin yayi yajuya yana fiskantar wajen shaka tawan,

Su yusuf kuwa suna fita dakin, DON ɗakin, Aryan suka nufa wani ɗan corridor suka bi ɗan tafiya kaɗan sukayi suka shiga palo Aryan, komai na palan iri ɗaya ne dana DON sai dai na Aryan ash colour ne babu kowa a palo kai tsaye betroom ɗin sa suka nufa,da sallama a bakinsu suka shiga, Aryan yana zaune yana aiki a laptop shikuma Aiman na kwanche yana latsa waya ” chikin ladabi da neman sulhu yusuf yafara magana wai me hakane bro,baikamata muyiwa hisham haka’ba,pls kar kuche baza kuje ba ” daga Aryan har Aiman ɗin ba wan da ya tanka yusuf ” akule yusuf yakuma chewa pls wai meyasa ku keyin hakane dan Allah ” yusuf idan fa yaya Aryan ya yarda zaije nima wlh zan je, amma in bazai jeba takin takalmi babu inda zanje nima chewar Aiman ” juyo Yusuf yayi yana kallan Aryan da ko kallan in da suke su bai’yiba bro dan allah kar kache bazakaje ba’ dan wlh ko bazakaje bikin kowa ba ya’zama dole kaje na hisham dan kuwa hisham yazama tam kar jinin mu ya’zama tamkar ɗan uwan mu,a’fusache Aryan yajuyo’ yana faɗin “kasan dai bani da yayan daya wuche DON koh to ko bikin shi ake bazan jeba ” a’fusache khalid yache wai meyasa bakuda hali mai kyau ne dan allah, daurin aurefa kawai zakuje,”shiri Aryan yayi bai sake tan kasu ba yachi gaba da aikin sa ” yusuf kuwa kallan Aiman yayi yace bro zo muje waje muyi magana

palon suka fita, yusuf yayita lallaɓa Aiman har ya yarda zai bisu “kowa ya nufi ɗakin sa dan shirin tafiyar,

shir’yawa sosai sukayi suka fito suka haɗu a babban palo,”to bari na tambayo mana Aryan sae muyi using jet nashi koh chewar yusuf ya karisa maganar yana hayewa stair ɗin yanufi dakin Aryan, a kwanche ya same sa yana latsa waya, harara Yusuf ya wunga masa kafin yache zamuyi anfani da jet naka “batare da ya kalle’sa ba yache adawo lfy ” juyawa yusuf yayi yafito, yasa mu su Khalid a palo suka jera zuwa waje motochi 4 suka ɗauke su zuwa Airport, Khalid Yusuf, suka shiga mota ɗaya Aiman Ahmad suma motar su ɗaya, saura moto chi 2 kuma sojoji yaran Yusuf ne a chiki, a jere motochin suka chera da matsakai chin gudu suka miƙi hanyar fita daga gd, da sauri security dake bakin gate suka wan gale katafaren gate ɗin, a hankali suƙa danna han chin moto chin waje,suna fita su ka karawa motochin gudu, sosai suke sharara gudu chikin kan kanin lokachi suka isa Airport, suna isa suka tarar an gama shirya komai su ka ɗai ake jira su tashi, basu wani ɓata lokachi ba suka fito daga motochin,suka nufi jet ɗin Aryan suka shiga suka zauna ba wan da yache da ɗan uwan sa kala kamar an musu zuwa dole karfe 7 na safe jirgin nasu ya ɗaga suka lula a sararin, sama’niya sai babban birnin tarayya Abuja Nigeria

Jirgin su na sauka a Airport na Babban burnin ta’rayya, dan kara dan karan motochi masu numfashi ne sukazo ɗau kan su, wan ɗa a’kallah yawan motochin zasu kai 8 ga kuma motochin 5 na sojoji abaya ” wasu jib ga jib gan sojoji guda 4 ne suka diro kasa daga samar motar su fiskar sun nan babu annuri ko kaɗan riƙe suke da manya manya Gun a hannun su, su na takawa irin takun jaruman maza,suka nufi su Yusuf, da sauri biyu suka tare bayan su biyu kuma suka tare gaba, Yusuf kuwa sae taku yake kamar wani sa dauki,har suka karisa wajen motochin,da sauri sojojin dasu gaban su suka fara buɗe musu kofar motochin, Khalid da Yusuf suka shiga mota ɗaya Aiman da Ahmad kuma suka shiga mota ɗaya,hannu sojojin suka ɗaga suka sara wa Yusuf san nan suka rufe kofar motochin,da gudu suka juya suka nufi nasu motar, sauri sauri suka motochin key, da matsakai chin gudu suka bar Airport ɗin,suka miki shin fi ɗadɗiyar titi gudu suke shararawa sosai har suka kusa chikin anguwar wuse 2 bakin wani katafaren gida na alfarman kae kaga ganin gidan kasan ya tsaru,suna karisawa bakin gate ɗin suka rage gudun motochin nasu, wani soja dake zaune kan plastic chair ne ya taso da sauri ya wan gale musu katafaren gate ɗin, kusa motochin chikin gida sukayi kai tsaye parking space suka nufa suna kashe motochin sojojin suka fito da sauri suka buɗewa su Yusuf kofar motar, a nitse suka fito,jingina da jikin motar Yusuf yayi yana bin gidan da kallo,gidan part 4

wani saurayi ne yafito daga ɗaya daga chikin part na gidan ya nufo su Yusuf yana ɗan murnushi, da sauri ya karisa wajen yayi hugging na Yusuf yana faɗin Wellcome,my brother’s bai jira amsar Yusuf ba yasake sa yabi su Khalid ma ɗaya bayan ɗaya yana hugging nasu, bayan yagama hugging nasu ne ya dawo da kallan sa kan Yusuf yana faɗin,”Yusuf DON da Aryan basu zo bakoh “sorry hisham Yusuf ya faɗa yana ɗan sosa kai, murmushi hisham ya ɗanyi yana faɗin bismillah muje chiki,gaba yayi suka bishi a baya,part nashi suka nufa,a haɗaɗ’ɗiyar palon sa suka zaune, shiru sukayi ba mai magana dan duk kansu ba masu yawan surutu bane almost 15 mnt Yusuf ya katse musu shirun da chewa, ” Hisham ana gama daurin aure nanfa, zamu wuche kano,da sauri Hisham ya ɗago yana faɗin “haba yusuf sai kace ko rin ku ake dan Allah kun fa San ni bani da wani friends Sai ku taya kuke san naje wajen dinner ba friends, “aa Hisham tun dana che maka ana ɗaura aure zamu wuche tofa sai mun tafi,dan kuwa mu iya ɗau rin aure kawai mu kazo “nasani Yusuf amma pls ku bari sae gobe ku wuche,mikewa Aiman yayi yana faɗin “yau zamu tafi ba sae gobe ba kuma karfe 4 dai dai zamu bar garin man ko an daura auren ko ba a daura ba yana gama faɗin hakan yanufi waje, girgiza kae kawai Khalid yake, shiru Hisham yayi dan kuwa yasan ko me zai che musu bazasu tsaya ba tunda su kache yau zasu wuche tofa ba abun da zai hana su tafiya,dan duk chikin su ba mai magana ya sauya in sun yi magana sun yi ne ba chan’ji,shiri suka zauna palon ba wan da yasake chewa ko uppan

Aiman kuwa yana fitowa waje kai tsaye inda sukayi parkin na motochin su yanufa, da gudu ɗaya daga chikin sojojin dasuka zo dasu ya nufo shi buɗe masa mota yayi,Aiman yashiga ya zauna,ya zuro kafar sa waje ya chiro wayar sa yana latsawa, gefe sojan yakoma ya tsaya yana jiran permission su tafi almost 20 mnt yana zaune yana latsa wayar sa, ɗago kai yayi zai yiwa sojan magana sai wayar sa tafara ringing,bin screen ɗin wayar yayi da kallon ganin sunan Aunty Mardiya che ya sashi jan dogon tsaki,har wayar ta katse bai ɗaga ba kira na 2 yasake shigowa, tsaki yakuma ja kafin yayi picking call ɗin ya kara wayar a kunne yana faɗin hello, daga ɗayan ɓangaren “Aunty mardiya tace hello Aiman ykk ” daure fuska yayi kamar yana gaban ta yace lfy ykk ” ina lfy wai da gaskene kun shigo naija “eh mun shigo sai akayi yaya “to dan Allah za kuzo gida na,tsaki yaja kafin yace “wai meyasa kekam Aunty mardiya baki da wata matsala ne arayuwan ki kedai burin ki kawai a zo gidan ki, kin dai san baza mu zoba “dan Allah Aiman ka daina faɗin hakan kaji pls kuzo mana koda 5 mnt mu gai sane kawai,ni kasan da za abar ni nazo na gan ku wlh da zanzo,duk da niche babba ” Aunty mardiya sai anjima kuma baza mu zoba yana gama faɗin haka ya katse kiran, ɗago ido yayi zai yiwa sojan magana idan sa ya sauka kan wata budurwa dake tsaye a kusa da mur fin motar kawar da kan sa yayi kamar bai ganta ba, chikin ran gwaɗa ta karaso gaban sa ta kashe murya tana faɗin “aslm ykk, tam kar bai san da mutun awajen ba, sake matsowa tayi kusa dashi sosai har kamar zata taka masa kafa “tace sunana Zubee,kuma ni babban kawar amarya che nasan kaima kana ɗaya daga chikin friend ɗin ango Ko,shiru Aiman bai ko kalli inda take ba bare tasa ran zai amsa mata, sake kashe murya tayi tana faɗin haba ƙyaƙkyawan saurayi inama magana kana share ni me yayi zafi kodai ban maka bane, “wani tsawa ya mata leave this place, jin hakan yasa sojan ya karaso wajen da gudu ita kuma zubee tsabar tsorata sai da jakar hannun ta ya faɗin jiki na rawa ta duƙa kasa ta ɗauki jakar da gudu tabar wajen,a fusache yabawa sojan umarni daya shiga motar yaka sutafi, da sauri ya shiga ma zaunin driver shi kuma Aiman ya mai da kafar sa chikin motar ya rufe marfin motar da sauri sojan yama motar key yaja suka nufi gate security suka gan gale masa gate ɗin ya danna han chin motar waje gudu yake shararawa sosai”oga ina muka nufa sojan ya tambaya yana kallan face ɗin Aiman ta chikin miro ” hotel Aiman ya bashi amsa a takai che gudu sosai sojan ke shararawa da motar chikin kan kanin lokachi suka isa wani katafaren hotel, horn yayi a bakin gate ɗin mai gadi ya wan gale masu gate ɗin, a hankali ya kusa motar chikin hotel ɗin parking space nasu yanufa yana kashe motar yafito ya buɗewa Aiman kofar, a nitse ya zuro kafar sa waje kafin yafito gaba ɗaya, chiki reception yanufa sojan na biye da shi ɗaki ya kama ya karɓi key yawuche, shiga chikin ɗakin yayi shikuma sojan ya tsaya a bakin kofar ɗakin, a gurguje yanufi toilet yayi wanka yafito ɗaure da towel yanufi waje, sojan na tsaye a bakin kofa Aiman ya fito”Abbas kaje ka ɗauko min trolley na a mota, da sauri Abbas ya wuche ya koma mita within 2 mnt sai ga Abba ya dawo rike da trolley, Aiman na tsaye a bakin kofa,Abba yazo ya miƙa masa trolley ɗin,ansa yayi ya koma chikin ɗakin Abbas kuma ya gyara tsayuwar sa a bakin kofar, jallabiya baka Aiman ya fitar yasa,da sauri sauri ya haye gado ya kwanta ba jimawa barchi yayi awan gaba dashi

Around 1:20 su Hisham sungama shirin zuwa wajen ɗaurin aure Hisham na sanye chikin dakakkiyar shadda fara tas,ya sanya kula baki da takalmi baki, Yusuf kuwa sanye yake chikin wandon jeans baki da t-shirt ash ya gyara gashin kan san nan kamar wani balarabe, Khalid na sanye chikin blue jeans da white t-shirt Ahmad ma na sanye chikin blue jeans da black t-shirt dukkan su sunyi kyau sosai “wae ina Aiman ne Hisham ya tambaya yana kallan Yusuf ” guntun tsaki Yusuf yaja yana faɗin oh bari dai na kirasa awaya muji chiro wayar sa yayi daga aljihu yanufi waje yana kiran layin Aiman ɗin

Hotel

Aiman na chikin barchi yaji wayar sa na ringing wani dogon tsaki yaja, batare daya buɗe ido ba yasa hannu yana lalubar wayar da kyar ya isa ɗauko wayar dan har kiran ta kusa yan kewa da kyar ya iya ware idon sa dan barchin daya masa yawa picking call ɗin yayi yana faɗin wae dan Allah Yusuf me namaka ne da kake ta’kurawa rayuwata “Yusuf yace amma gaskiya Aiman baka kyauta ba dan Allah menene hakan wato ma barchi kaje kake koh to kazo mutafi ɗau’rin auren lokachi yayi chewar Yusuf, a fusache Aiman yace “bazan jeba yana yana kai karshen maganar batare daya jira amsar yusuf ba ya katse kiran yayi wurgi gefe da wayar ya chigaba da barchin sa

Yusuf kuwa Aiman na katse kiran ya juya jiki ba kwari ya koma chikin palon a zuchiyar sa yana faɗin wlh yau Aiman da nine yayan ka da sai nayi maganin ka, wan nan wani irin wulakanchine kan chine sae kace ba tare suka taso da Hisham ba a sanyaye ya shiga chikin palon, Hisham na ganin sa yace”Aiman ɗin yace bazai zo bako,shiru Yusuf yayi dan ban san amsar da zai bawa Hisham ba kunyar haɗa ido da Hisham ɗin yake ji, dafa kafaɗarsa Hisham yazo yayi yana faɗin karka damu yusuf nasan halin ku gaba ɗaya SO duk wani abun daya da suke gudun zuwa aure nawa nasa,ni ban ma taba tunani daman zaku so aure naba,kadai na damuwa ngd sosai da zuwan da kukayi, kasani DON da Aryan Bawai basu sona bane yasa suka ki zuwa jiya da daddare DON ya turomin 1m a matsayin gift haka Aryan ma 1m ya turamin to kaga bawai basa sona bane kawai sudai a nasu ganin dakuma tunanin su duk wan da ya raɓi mace to yaza mai rauni sukuma kasan basa san mauni sunfi san kullun su ji su zam zam,”murnushi kaɗan yusuf yayi zai yi magana Hisham yace “No badai yanzuba, yanzu kam muje lokachi yayi ana jiran mu, jerawa sukayi gaba ɗayan su suka fito harabar gidan,
su yusuf suka shiga motochin da suka zo dasu Hisham kuwa yashiga nashi motar,suka yiwa motochin key, security ya wangale masu gate da gudu suka danna hanchin motochin waje sosai suke gudu dan sunyi latti kai tsaye babban masallachin jummaa suka nufa a harabar masallachi sukayi parking dub bannin jamaa ne suka halak chi ɗaurin auren kama daga minister’s governors members har shugaban kasa muhammadu buhari yazo ɗau rin auren dashi da Shugaban kasa mai jiran gado tinibu, misalin karfe 2 dai dai na rana dubbanni jama’a suka she’da ɗau rin auren Hisham Nasir alkali tare da matar sa ilham Abdussalam, ana gama ɗau rin aure Yusuf ya dawo chikin mota da sauri dan yaji jama’a nata faɗin ina yayan Abubakar saraki ma sunzo bikin, yana zaune chikin mota yana jin jama’a na ta neman family Abubakar saraki,amma yayi kamar bar ji ba, buɗe kofar motar da Yusuf ke chiki ango Hisham yayi yashiga ya zauna yana faɗin “yanzu Yusuf abun da kayi ka kyauta eh ” ɗaure fuska Yusuf yayi yace to me kuma nayi “ka fini sanin me kayi ae ka dubi yan da jama’a ke naman ku kuzo kuyi hoto kowa Burin sa yayi hoto da family Abubakar saraki, amma ka watsa musu kasa a ido koh “kaga Hisham idan kagama dana ka jama’a mutafi dan ni yanzuma zan wuche kano, Hisham zaiyi magana Khalid ya buɗe kofar motar yashigo yana faɗin “Hisham me kuma ka zauna kake a nan baza kaje kutafi walimar bane “yanzu Khalid kuna nufin da gaske baza kuje walimar nawa ba Hisham yayi tambayar yana kallan fuskar Khalid, Khalid zai yi magana Yusuf ya riga shi da chewa “gaskiya ba zamuje ba ae nafaɗama iya ɗau rin aure kawai mukazo dan haka yanzu zamu wuche tun da angama abun daya kawo mu, shiru Hisham yayi yana tunani, ganin yanayin da Hisham ya shi gane yasa Khalid chewa, ” No Hisham dole zamuje walimar taso muje ga jamaa na chan na jiran mu,jiki ba kwari Hisham ya fito daga motar Khalid na rike da hannun sa suka bar Yusuf a chikin motar,

Fito Yusuf yayi ya kira sojojin sa tare da basu umarnin akan su wuche Airport dashi, da sauri suka shiga mota suka wa motochin key suka bar masallachi sae tsaye Airport suka nufa, jirgin kasuwa Yusuf yabi yabar wa su Khalid jet ɗin Aryan a Airport ɗin tare da sojoji 2 ya tafa ya nar biyu su taho dasu Khalid,

Karfe 3:45 jirgin su ba yusuf ya sauka a malam Aminu Kano international Airport,bai sanar da kowa zu’wan nasa ba ba wan dayazo ɗaukan sa motar haya suka hau shida sojojin nasa suka nufi gd, a bakin gani gidan sarki mai motar ha’yan ya ajiye su sauƙa Yusuf yayi ya biya sa kuɗin sa yanufi chikin gd sojojin na biye dashi, ɓangaren sa yanufa natare daya shiga chikin gd ba a bakin ɗan karamin gate na shiga ban garen nasa sojojin suka tsaya shi kuma ya wuche chiki, wanka yayi a gur guje ya zura jallabiya ya kwanta ba jimawa barchi yayi awan gaba dashi

Aban garen su Khalid kuwa ansha walima duk chikin su Khalid ne kaɗai ya halak chi walimar karfe 4 dai dai a ka tashi taron, wajen holl ɗin Khalid yafito da sauri yana kiran layin Yusuf, wayar tayi ta ringing sai da ta kusa katsewa Yusuf ya ɗaga chikin muryan barchi yace,”hello “ina kake ne Yusuf lokachin tayi fa yayi “ina kano mana ” kano kuma Khalid ya tambaya yana riƙe haɓa “wani dogon tsaki Yusuf yaja yana faɗin kaga Khalid dan Allah ka kyale ni wlh bar chi nake kata dani ” to yanzu Yusuf mota kake so mubi zuwa kano ne kokuma me menene dazaka dafi kabar mu “oh my god nima Khalid bada jet na zaba jirgin kasuwa nabi jet ɗin na Airport na bar muku, yana gama faɗin hakan ba tare daya jira amsar Khalid ba ya katse kiran, bin wayar da kallo Khalid yayi yana faɗin ya Allah ka shirya min yaran bappa ba mutane ne sai kache wasu aljanu bazaka taba gane kan suba in sun juya ba mai iya juyo su, layin Aiman yafara kira again har ta katse Aiman bai ɗaga ba, tsaki Khalid yaja yasake kira, wayar nata ringing har ta kusa katsewa Aiman yayi picking, “ina kake Aiman Khalid ya tambaya a fusace, chikin muryan barchi Aiman yace ” wai dan Allah menene naha bazaku bar mutun yayi bar chin sa ba “au barchi ma kake ke nan to wlh sai dai ka kwana a Abuja dan tafiya ta,zanyi, wani dogon tsaki Aiman yaja yana faɗin to a sauka lfy san nan ya katse kiran, Khalid kamar yayi wurgi da wayar dan haushi haka yasake hakura yafara neman layin Ahmad kira ɗaya Ahmad yayi picking ” ina kake chewar Khalid “haba Khalid ni karamin yaro ne da zaka min irin wan nan tambayar, a fusace Khalid yace to wlh idan ba kazo Airport nan da 20 mnt ba tafiya ta zanyi na bar ku ” to yaya Khalid a Allah ya sare hanya yana kai kar shen maganar ya katse kiran, a fusache Khalid ya juya yanufi motar su yana faɗin wlh ku kam idan mutun ya biye muku zaku kashe sa da bakin chiki, chikin mota yashiga driver ya ja motar da gudu suka nufi Airport, abun ma maki ko da yaje Airport ɗin zaune yasamu Aiman da Ahmad chikin jirgin suna jiran sa dan bakin chiki ko sannu bai che musu ba ya shiga jet ɗin shima ya zauna suma ko sannu basu che masa ba har jirgin su ya ɗaga

Karfe 6 na yamma dai dai jirgin su yayi landing a malam Aminu Kano international Airport kano basu wani ɓata lokachi ba suka fito shiri suka tsaya sai yanzu suka tuna basu sanar da zu wan su ba wan daya zo ɗaukan su wuche Aiman yayi ya fita Airport ɗin ya tari motar haya yashiga abunsa, ganin Aiman shiga motar haya ne yasa suma suka fito suka tari motochi biyu na haya suka hau suna nufi gd a bakin gate sukache da mai motan ya tsaya suka sauka,suka Biya shi suka nufi chikin gd,kowa ya nufi ɓangaren sa Khalid kuwa yanufi babban gate ɗin ya shiga chikin gd a dai dai bakin gate ɗin ya haɗu da Umar da haidar sosai suma suke kama da su yusuf ko ba’a faɗa ma ba kasan kannen sune “kai haidar ina yusuf Khalid ya tambaya yana kallan fiskar haidar “haidar yache nima ban sani ba yaya Khalid daman yaya yusuf na gidan nan na,juyo da kallan sa Khalid yayi kan Umar dake tsaye yana mur tuƙe fiska “kai Umar awani ban gare Aunty farida take,kara ɗaure fuska yayi yace “kai yaya Khalid dan Allah ka shiga chiki ka duba mana mu ka daina tambayar, mu tana gama faɗin haka yaja hannun Haidar suka nufi waje, baki buɗe Khalid ke kallan ikon Allah a zuchiyar sa yake faɗin, gaba ɗayan su ƴa’ƴan bappa halin su ɗaya ba yaran ba ba man yan ba, juyawa yayi shige chikin gida,

Wani katafaren Falo na Al’farma Khalid ya doka sallama,haɗuwar falon ya zarce tunanin me tunani yaji komai na furniture,wasu hadaddun Sofa set ne,Launin Milk colour,masu numfashi,a tsakiya kuma akwai Sofa tabls,daga gefen Hagu,Tv stand ne,baka jin sautin komai sai Sanyin A.c dake ratsa sassan jiki, yan matane 3 ke tsaye a tsakiyar palon suna goge goge da alama kuyangu ne,har kasa suka duƙa suka gaida Khalid fuska ba yabo ba fallasa ya amsa yana tambayar su “ina Ammi, “tana chikin ɗaki suka amsa masa, bai jira sun kai karshen maganar ba ya haura stair case ɗin,wani ɗan karamin haɗaɗɗen palo ne a saman mai ɗauke da sofa set 1 ash colour atsakiya kuma a kwai sofa table gefen dama kuwa wani makekiyar Tv awajen,palon ɗauke yake da ko’fofin betroom’s 4 a chikin sa,babu kowa a palo sai sanyin A.c dake tashi bakin kofar betroom ɗin Khalid yanufa sallama yayi ya gyara tsayuwar sa yana jiran a masa izinin shigowa almost 7 mnt kafin a amsa masa sallamar tasa tare da izinin shigowa, tura kofar yayi ya shiga

Wata kyakkyawa mata che sosai, kamannin ta ɗaya da DON,fuskarta ɗauke da murmushi,a zaune take saman tulu irin na gidan sarauta,babbar macace A ƙalla tayi 45 years,irin hajiyoyin nan ne wanda naira ta zauna masu,jikinta na sanye da tsadadden cord lace,wanda akayi mata bubu gown dashi,duka hannayenta da wuyanta,Kayan adone na Zallar zinayi, karisawa chiki Khalid yayi ya zauna a kasa a gaban ta,chikin ladabi da girmama,yace “barka da hutawa Ammi,shafa kansa Ammi tayi yace “baba saukar yau she “yanzu nan muka zo Ammi “to zuwa babu sallama,ina sauran yan uwan naka, “prince da Aryan basu zo ba suna London “ni basu nake tambaya ba ina ruwa na dasu,murmushi Khalid yayi daman da gangan ya kawo wa Ammi zan chen DON “baba ba kache komai ba ko dai kai kaɗai kazo ne “aa Ammi ni da su Yusuf ne amma ae kin san halin su ni ko in da suke ma ban sani ba “to ka sanar da Salma kun zone “aa Ammi kamar yadda bamu sanar ɗa ku ba haka ba wan da muka faɗawa “to yaka mata ku sanar da ita dan kaga kuka ɗai gare ta ku rinka tau saya mata “to shike nan Ammi zanyi yadda kika che amma ina Aunty farida “inajin tana bangaren Ummi,mikewa yayi yana faɗin to Ammi bari na dubo ta, “ok kawai Ammi tace, yana kokarin fita daga ɗakin wata kyakkyawar budurwa tashigo wadda a shekaru bazata wuche 16 ba kyakkyawa che sosai duk kaman nin su ɗaya dasu DON da gudu tatafi ta faɗa kirjin Khalid tana faɗin “oyoyo yaya Khalid, rungume Khalid yayi shima yana faɗin “oyoyo Auta oyoyo, ina kika fito hakan nan sai kam shi kike ” turo baki Zahra tayi tace daga wajen Aunty farida nake “ina take Aunty farida yayi maganar yana raba jikin sa da nata ” tana ɓangaren Ummi “ok to muje ki rakani “aa yaya Khalid ni tun danaga ka nasan ba kai kaɗai kazo ba, nasan su yaya prince ma sun zo ni bazan fita ba ina tsoran su “murmushi Khalid yayi yana faɗin”kai Auta tsoran me kuma ai dani zamuje “Allah yaya Khalid shiyasa nafi son ka dan duk gidan nan kai kaɗai ne mai sona ” aa Auta kowa na gidan nan na son ki “aa yaya Khalid badai kowa ba Aunty Maryam da yaya prince da yaya Aryan da yaya Aiman, “girgiza kai kawai Khalid yayi ya ja hannun ta suka nufi waje yana faɗin,Ammi mun tafi, Ammi dai murmushi kawai take tana binsu da ido..✍️

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button