Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 34

Sponsored Links

βšœοΈπŸ”±πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ”±βšœοΈ
*BOOK 2*

*PAGE 34*

No editing πŸ˜’

*INA MAI BA MASU KARATU HAK’URI AKAN SHIRUN DA SUKAJI KWANA BIYU, HAKAN YA FARU NE SAKAMAKON MATSALAR RASHIN WUTA DA MUKA SAMU,*

*~Ina kuke masoya kuma yan uwana makaranta?,~*

~shin kuna da labarin cewa gwanar ku kuma gwanata *JAMILA MUSA MARUBUCIYAR SHAHARAR REN LITTAFIN NAN MAI TAKEN KWARATA* tak’ara dawo muku da wani zazzafan labari mai cike da sark’ak’iyar hassada makirci munafunci bita da kulli kai harma da tsantsar SOYAYYAR da a dare d’aya ya juye ya koma wutar kiyayyar juna?~

*WUTAR K’IYAYYA* ~ce keci take kuma gudana a cikin rayuwar wani ahalin da suke jini d’aya ma’ana uwa d’aya uba d’aya?~
~idan baku manta ba a baya itace dai wacce ta rubuta muku littafan nan masu d’auke da tsantsar fadakantar wa gami da nishad’in da har yanzun da yawa daga cikin mu nasan bama gajiya da karanta shi,~
~ina magana ne akan littafan ta kad’an daga ciki irin su~ *KWARATA, BOYAYYAR SOYAYYA, ZAWARCI, SO MUGUN WASA Dama wasu wad’anda ban kira sunan suba*
~wadan nan littafan dana lissafo ko banyi k’ari bayani akan suba nasan kun san me suka k’unsa~
~To wannan karan ma dai so nike ku shirya tsaf ban kuma ce kuyi garaje gurin karatu ba, ah ah karatun littafin Hajiyata nutsuwa yake buk’ata, littafin~*WUTAR K’IYAYYA* ~zai zo muku a kyauta ne kedai qawata daure ki loda ma wayar ki data da kuma isashshen caji domin ki samu damar karantu a natse na tabbata zakiji dadin shi domin ko namu ba irin nasu bane~
*karku manta littafin WUTAR K’IYAYYA kyauta ne ga masu buk’ata daga farko suyi magana dani kai tsaye ta wannan number din* 08061358462 *ni kuma zan an taya su cikin group din zaku same shi daga farko kuma batareda kunsha wahalar nema a wani wajen ba*

************Kunga kutashi muje ciki dan Allah,”
Meenal ta fad’a tana tarar numfashin Hajiya saboda jin da tayi Hajiyar tana neman mai da chapter din ya juya kanta shiko dama AK tunda ta fara surutun ya mik’e yabar musu falon dan Wallahi ya sani tsaf Hajiya tana iya kwafsa mishi a gaban yaran nan bai kuma bar falon ba sai da yakai bakin shi dai dai kunnen Meenal ya shaida mata cewa bai fa yarda da wani rungume rungume ba sannan ya fice abinshi jin Hajiya naci gaba da surutun ta na fama,
inba haka ba dan Allah miye kuma nayi masu terere daga zuwan Moon din zata wani fara shelanta mata cewa ita Meenal ta samu miji?
Itafa Hajiya matsalarta kenan duk maganar da yazo bakinta fad’in shi kawai take bata wani lura dako su waye ke wajen salon duk tasa kananun yara su gama raina mutum,

Basar da kashe din da AK ya mata Meenal tayi dan tun bai bar falon ba ta fuske taje ta rungume Moon d’in irin rungumar da akema mutum na gefe tana mai cigaba da cewa,

“Kema dai kamar wata wacce baki san halin Hajiya ba da zaki wani biye mata kina son b’ata ranki daga shigowar ki ko hutawa bakiyi ba ku wuce muje ciki kafin ta huce dan Hajiya kwana nan bata dako wani magana sai na aurar da mutum”

“Eh lallai kam ai dama dole ki goyi bayan yar uwarki ni ki kwaye min nawa bayan!
Kwana nawa ne dududu ita Maimunan zatayi ta tafi tabar ni dake a gidan nan? Batun aure kuma dan uban mutum ko yak’i ko yaso dole yayi shi in mutum baiyi ta arziki ba aiba abun kunya bane in kunji shela a masallaci ana sanarwa dan mu bayau farau a kan muba yima mace auren bazata,
Oh wato ma ga azababbiyar tsohuwa koh shine har kike cewa ku wuce to karko ku sake kuce zaku hau min sama gara duk ku tattara kuzo ku fice min a sashe dan babu wacce na gayyato dama a cikin ku”

Tsam suka mik’e ganin abun na hajiya bamai k’arewa bane suka fice daga sashen zuwa side d’in Hajiya Jummai acan suka baje hajar su ta firar yaushe gamo tunda dai ba laifi an dad’e ba’a had’uba kullum sai dai chat da kuma kiran waya,

Suna cikin hirar nasu ne kuma Meelat ta kawo zancen zuwan da Bash yayi wajen ta da kuma labarin Meenal din daya tambayeta duk saida ta bata Meenal labari sannan kuma Meelat din ta tambayi Meenal ko bash din yazo wajen ta?dan allah ya sani ita dai bata so Bash din ya bayyana ba taso ace ko zai bayyana sai komai ya k’an kama tsakanin AK da Meenal din ba kuma wai dan bata son Bash d’in bane ah ah ita dai tafi son ace AK ne ya samu Meenal din akan duk sauran wadanda suka nuna ra’ayin su akan Meenal d’in.

Sosai jikin Meenal yayi sanyi ba tareda ta iya ba Meelat dasu Maryam din da suka zubo mata ido suna jiran amsa daga gareta ba,
Tayi matuk’ar mamaki dajin cewa har yanzun ashe Bash dinta Bash dai nata a shekarun baya d’an gidan master wai ashe har yanzun bai manta da ita ba tunda gashi har ya iya neman ta a ranar daya ganta,

Allah Sarki rayuwa kenan a baya bata tab’a zaton cewa zasuyi rabuwa ta bazata irin rabuwar da sukayi dashi wanda ko sallama basuyi a yayin rabuwar ba, bayan auren ta kuma tunda ta tabbatar da cewa shi kenan ta rasa shi sai ta rungumi kaddarar ta duk da cewa a lokacin tana da number din wayar shi akai amma bata tab’a gwada kiran shi ko sau d’aya ba saboda bata san me zata ce mishi idan ta kira shi d’in ba,
A wajen Aisha ta samu labarin halin daya samu kanshi a ciki yayin zuwan shi gidan Hajiya kuma bata tab’a tattauna maganar dasu Meelat ba suma kuma tun bayan auren ta babu wanda ya k’ara tada hirar wani daga cikin samarin ta a cikin su, sun tona k’asa sun burne komai saboda basa son hankalin ta ya tashi, daga bayane ma takejin cewa wai baya k’asar lokacin data samu labarin hakan ta bishi da fatan alkhairi saboda Bash mutum ne yana daga cikin mutanen da bazata iya mantawa dasu ba dan ya nuna mata kauna tun zamanin da take cikin k’uruciyar ta ta kuma yarda cewa Allah yayi cewa ba shine Mijinta ba shi yasa tun farko bata bashi damar zuwa gidan suba,
Sai gashi kuma yanzun kwatsam yana son dawowa gareta a dai dai lokacin data amsa soyayyar wanin shi bayan kuma shi ta dad’e da mishi delete all a cikin memory d’in ta,
Yanzun idan ya dawo ya k’ara gabatar da kanshi a karo na biyu ya zatayi?,
da wani fuskar zata tarbeshi alhalin ita tuni ta dad’e da yima nashi soyayyar kabari ta birni a matsayin matacce.

Shiru tayi domin gaba d’aya ta riga ta tayi b’acewar b’at a cikin tunanin halin da take ciki a yanzun yanda abubuwa suke neman jagula mata lissafi duk yanda take kamewa amma abun mamaki kamar wacce akayi shelar mutuwar auren ta domin dai kullum mazaje ne ke kawo mata hari ba’a makaranta ba ba kuma cikin gari ba kamar dai ita kad’aice bazawara a gari,
Ga AK, ga Salman, ga Aliyu, ga kuma Ya Hashim sannan kuma yanzun ga bash ya dawo bata ma sa sauran samarin dake faman biyayyar ta wad’anda bata da alaqa dasu a lissafi ba dan har yanzun wasu ma basu san katamai man gidan suba balle su kawo mata hari,

“Allah Sarki Bash nayi zaton ko ya manta dani tuntuni ai?” Ta furta kalmar a sanyaye,

Tab’e baki Sultana tayi kafin tace,
“Shidai kam alamu sun nuna cewa bai manta dake dinba har yanzun, gashi kuma ke tuni kin dad’e da mantawa dashi ni kam na gode Allah da yasa gayen nan ya dawo a makare, dan haka bari kiji duk ma ranar daya sake ya kawo kanshi wajen ki karki wani tsaya yin mishi muna muna ko munafunci ki fito fili ki fad’a mishi gaskiyar cewa tafiyar sa’ar ki da nashi basu jera hanya ba tunda gashi a wannan karon ma dai yana ji yana gani zai k’ara rasaki, zaifi mishi sauk’i idan ya tafi wani wajen ya k’ara lalube ko zai dace da samun abokiyar tafiya, kai ni ina rokon allah ma ya mantar dashi ke gaba d’aya wallahi Allah yasa kuma k’in tunkarar naki da yayi hakan ba yana nufin cewa zaiyi miki shigar k’arfi bane wannan karon ,
Dan yana iya komawa gefe yace zai tura iyayen shi kai tsaye wajen su Baba Malam kafin ya gabatar da kanshi gareki a karo na biyu, duba da abinda ya faru a shekarun baya sanadiyar rashin gabatar da kanshi da yayi a gaban iyayen ki”
Ta k’arasa fad’a tana watsa hannuwa dan itafa tsakani da Allah duk wani wanda zai fito yanzun yace Meenal yake so to dole nema ta taya AK adawa dashi domin ba karamin dacewa take ganin Meenal tayi na samu AK ba, dan haka bazata yarda wani can yazo yace zaiyi takara da AK ba,

Ba iya Meenal bace kad’ai taji saukar kalmar da Sultana ta fad’a a cikin k’irjin taba har su Moon sai da suka zazzaburo,

“Kina nufin idan saurayi yaga kamar ke idan ya nemeki zaki bashi ciwon kai shine zaisa ya wuce wajen iyayen ki kai tsaye ya gabatar da kanshi a wajen su?”
Moon ta tambayi hakan a k’age da son jin amsar da Sultana zata bata,

“Eh kwarai kuwa kusan hakan ne amma shi ni a nawa tunanin ina ganin kamar tunda ai tun farko yasan dokar gidan su Meenal din shine yake so ya koma yabi tsarin duba da cewa rashin bin tsarin yana daga cikin dalilan da sukayi jagoran cin daya rasata a shekarun baya,
Kuyi nazarin magana ta da kyau zaku fahimta, Meenal kinga dai ban san wani irin so kikama Bash din nan a baya ba, amma koma dai yayane ni zan fad’a miki gaskiya duk wanda zai soki a yanzun bana tunanin zai miki so irin wanda AK yake miki a yanzun kai ni banma ga uban meye ya hanaki kiba bawan Allan nan damar gabatar da kanshi a gidan kuba wai so kike sai an k’ara miki wani auren dolen ne kafin ki dawo cikin hayyacin ki?”

Hummm suka dunga fad’a suna gyad’a kai cike da nazarin kalaman Sultanan dan dukan su sun san cewa gaskiya ta fad’a,

Ita ko Moon a gefen ta ba k’aramin tashin hankali takeji a cikin k’irjin taba, kenan idan ta auna kalaman Sultanan hakan yana nufin cewa shima Sarki yana iya zagayewa yaje ya nemi aurenta ta baya batareda ya nemi jin nata ra’ayin ba?
Duba da cewa tun sanda ya mata magana da farko ta nuna mishi ah ah bai k’ara tada zancen ba kuma ko a fuska bai nuna mata damuwa ba, ita kuma nauyin shi da takeji yasa har yau ta kasa k’ara tada maganar, to idan kuma tayi shiru har yaje ya zagaya ya nemi auren ta ta bayan gida maganar ta fito daga baya da wani idon zata d’aga ta kalli Meenal wani kalan bayani zata mata waiyo Allah ta shiga uku, zufa ta dunga had’awa ta ciki duk da sanyin fanka da ac din daya cika falon na Hajiya Jummai.

Abinda ya faru a Lagos kafin ta taho,

Tsakanin ta da Sarki lafiya lau sukaci gaba da ganin juna babu wani abunda ya canza a tsakanin su domin dai duk da cewa bai k’ara taso mata da maganar zuwa neman auren ta wajen Baba Usman ba hakan bai hana shi cigaba da nuna mata kauna da soyayyar da yake mata ba,
Da farko had’uwar su iya waje biyu suke yin shi kodai a wajen aikin ta ko kuma da yamma a can inda suka saba had’uwa amma sai gashi daga baya kuma har gidan su yake binta,
Ranar farko daya fara zuwa gidan tayi mamaki kwarai dan batayi zaton cewa shi d’in ne da gaske ba domin dai ko a ranar yaje can wajen aikin ta ya sameta sai dai bai dad’e sosai ba ya mata Sallama ya tafi a matsayin cewa sai sun had’u da yamma, da yamman tayi bai samu zuwa can wajen ba dan ya kirata ya sheda mata ta kirasu tayi order din abinda take buk’ata kawai sukai mata gida dan yayi busy bazai samu damar had’uwa da ita ba amma idan ya kammala abinda yakeyi d wuri zai neme ta,
To itama jin hakan da yace sai bata damu kanta da cewa sai taje d’in ba sai tayi zaman ta kawai a gida,
Daren ranar suna zaune a falo suna hira ita dasu Umma da sauran k’annin ta kiran shi ya shigo cikin wayar ta,
Tashi tayi tsam bayan ta d’aga wayar ta koma d’aki saboda bata son tayi wani abunda zaisa Umman tayi zargin cewa har yanzun ashe suna tare ita da Sarkin duba da yanda ta fito k’iriΒ² ta nuna mata rashin amincewar ta akan alaqar tasu dan ita dai tace bata yarda da auren cin amana ba, ta ina ma za’a fara ace wai mijin daya auri Meenal ya saka shine zai auri Moon a yanzun bayan dukan su kowa yasan bayan k’awance harda alaqa ta jini a tsakanin su,

Tunda ta amsa sallamar daya mata bata yarda ta k’ara furta komai ba sai da ta tabbatar da cewa ta maida k’ofar dakin ta ta kulle shi da kyau,

“Barka da dare dafatan ka wuni lafiya”

“Alhamdulillah ya kike?”
Ya tambaya
“Ina lafiya”
“Me kikeyi ne?” Ya k’ara tambaya,

“Ba komai”

“Ok to fito gani a farfajiyar gidan ku”

“Na’am” ta amsa dashi bayan ta ciro wayar daga kunnen ta ta duba Number din domin tantancewa,

“Eh ki fito nace ko insa ayi min iso ne in shigo ciki?” Ya fad’a ko a jikin shi,

“Uhmm uhmm wai nan gidan kake magana”

“Kuna da wani gidan bayan wannan ne anan Lagos dama?”

“Ah ah amma ai baka cemin zaka zo ba, umm bawani nan nasan ma wasa kawai kakeyi min”

Murmushi yayi daga can gefen shi, murmushin da harta cikin wayan sai da ta jiyo shi, kafin ya daura da cewa,
“Yanzun dai koma wasa ne ko gaske duk idan kika fito zaki tabbatar in kuma kika b’ata min lokaci wallahi cikin gidan zan shigo kinji dai na rantse miki dan haka ki fito yanzun” yana gama fad’in hakan ya yanke wayar shi,

Sororo tayi da wayar a kunne,
Cike da mamaki to wai ma meyazo yi a gidan su da daddaren nan salon ya tona mata asiri a wajen Umman su, yanzun in Umman su tasan cewa Sarki na cikin gidan nan yazo hira wajen ta ya zatayi?
Tunawa da rantsuwar da yayi cewa idan ta b’ata lokaci zai shigo cikin gidan ne hakan yasa dole ta fito daga cikin d’akin ko mayafi bata d’auka gudun karma Umman su taga fitan ta, ta k’ofar baya tabi a sace kamar b’arauniya sai da ta fice kafin ta tsaya ta warware dan kwalin rigar dake jikinta ya yafashi tana sauke ajiyar zuciya tun daga nesa ta hango shi zaune akan fararen kujerun dake farfajiyar gidan, gabanta naci gaba da fad’uwa haka dai ta daure taci gaba da taku harta isa inda yake wanda shima hango tahowar nata ne yasa shi mik’ewa dan ya tarota,

“Shine kazo nan bayan kuma baka fad’amin cewa zaka zoba” shine kalmar data fara furtawa tun bata samu zarafin zama ba,

“Bakiyi farin cikin ganina ba kenan? Niko kinga na kasa daurema zuwa gida in kwanta batareda nayi tozali da wad’annan fararen idanuwan naki ba shi yasa na biyo dare na taho kawai dan in ganki,nayi zato zakiyi farin ciki kema amma tunda bakiyi farin ciki ba kiyi hakuri kina iya komawa ciki tunda na ganki”

Juyawa yayi da niyar tafiya tayi saurin shan gaban shi,

“To ni ai bance ka tafi ba kawai dai nayi mamaki ne da kace min gaka tunda naga ko d’azun munyi waya kuma baka cemin zaka zo ba”

“Ai nace miki kawai nazo ne dan in kalli fuskar ki a zahiri kuma na gani hankali ya kwanta kije ciki sai da safe”ya fad’i hakan yana zura hannayen shi a aljihun wandon jikin shi,

Bata samu zarafin cewa komai ba Baba Usman ya bayyana a wajen daga cikin gidan ya fito da alama fita zaiyi, ba karamin tashin hankali ne ya risketa ba sai dai kuma ta danne hakan dan ba lallai bane a zatonta ya gane Sarki, kasa tayi da muryar ta,

“Kagani kaja min ko ga Baba nan ya firo”
Bai kulata ba saima wucewa da yayi ya k’arasa wajen baba Usman din sukayi gaisuwar da bataji me sukace ba dan Sarki bai tsaya ba sai da ya raka Baba Usman din har mota sannan ya koma inda take tsaye,

“To yane yanzun dai bari in wuce kar in shiga lokacin ki da yawa”

“Me kace ma Baba?”
Ta tambaya tana bin shi da kallo a sanyaye,
“Babu” kawai ya bata ansa dashi,

“Babu me? ” ita kuma ta tambaya,

“Bance mishi komai ba, me kike tunanin zance mishi bayan gaisuwa, amma ke idan ya dawo ya tambaye ki cewa me nazoyi wajen ki wani amsar zaki bashi?”
Ya tambaya yana tsareta da ido,
Juyawa tayi sai da tayi taku d’aya biyu ba tareda yayi yunk’urin tsaidata ba kafin taci burki ta juyo ba tareda ta kalli idon shiba tace,
“Sai da safe”
Tana gama fad’in hakan ta juya tayi cikin gidan da sauri gabanta yana tsanan ta fad’uwa dan batasan me zai biyo baya ba kuma,
Sarki bai gusa daga inda ta barshi tsaye ba harta shige cikin gidan, shi dariya ma ta bashi wallahi dan Allah kuga duk yanda tabi ta rud’e shifa gaba d’aya baiga abun tashin hankali a cikin al’amarin nan ba da take ta faman son ta hana ma kanta abinda zuciyar ta keso wanda kuma bawai hakan ya haramta a gareta bane, aiko mai kankat zai mata Allah dai yakai su Zaria lafiya,
Cikin masu gadin su ya kira guda ya bashi sako yace ya mik’a mata cikin gidan,
Ranar kwanan d’ar d’ar tayi domin motsi kad’an idan taji sai taga kamar Baba Usman ne zai aiko ayi mishi kiranta dan yaji ko waye yagan su tare, ko sakon da Sarki ya bayar aka biyota dashi bata bi ta kanshi ba k’annen tane sukayi didima a kanshi,

Tun daga ranar Sarki ya tsiri yi mata zuwan bazata bazai tab’a fad’a mata cewa zaizo ba sai ya shigo cikin gidan sannan zai kirata cewa yana jiran ta, ita kuma ta kasa fitowa ta fad’a mishi cewar ya rufa mata asiri ya dena zuwa gidan, kuma bayan ganin farko da Baba Usman ya musu sau biyu ya k’ara ganin su tare bai kuma yi mata magana ba har sai ana gobe zata wuce Zaria a gaban Umman su ya kirata yake tambayar ta cewa,

“Maimoon wanene wanda naga yana zuwa wajen ki hira a yan kwanakin nan?”

TsuruΒ² tayi uwa an jijjiga bera a cikin buta,

“Hira kuma Baban su ai a dai cikin kwanakin nan bana jin akwai wani saurayin dake zuwa hira wajen ta” cewar Ummah

“Kece dai baki san ana zuwa hira wajen nata ba amma ai gata nan zaune a gaban ki kinji ta musa abinda nace ne? Ke Maimoon dake nake magana”

“Abokin aikina ne”ta tsinci kanta da furtawa dan tasan yau ta shiga uku idan har Ummah tasan Sarki na zuwa hira gidan nan wajen ta,

“Shi abokin aikin naki yake zuwa gidan nan har kike Rita ni ina gidan nan bani da labari” umman su ta fad’a cike da mamaki,

“Kiyi hakuri” Moon tace kanta a k’asa,

Shi kuma Baba Usman d’aurawa yayi da cewa,

“Kin san me yasa na kiraki nan?”

“Ah ah ” ta furta tana girgiza kai,

“Masha Allah to dama kiranki nayi dan in baki hakkin ki a matsayin ki na budurwa, shin akwai tsayayyen saurayin da kika tsayar a cikin samarin kine? Ina nufin wanda kike da burin aure?”

“Baban su kaima dai kamar baka san hali ba, ina ma take kula samarin balle harta tsaida tsayayye nidai dama ai tun tuni nike ta maka magana akan Lukman d’an wajen Hajiya Hasiya ka sani sarai tun tuni yake bibiyarta take mishi wulakanci amma har yanzun yaron nan ya kasa hak’ura ya nemi wata ya aura, ita kuma da kullum take ikirarin cewa bata son shi ta fitar da wani mijin tayi aure tak’i tasa har yan uwana sun fara ganin kamar nice bana son in had’a zuria dasu to nidai tunda abin ya zama haka gara aba shi Lukman din komai koba komai dukan mu mun sheda yana son ta….”

Saurin tarar numfashin ta Moon tayi da cewa,

“Wallahi Umma nidai bana son shi, dan Allah karki matsa kice sena aure shi”

“To Moon in baki auri Lukman ba wa kika tsayar ne bayan kullum nan ko mazan sun biyoki har gidan nan ma ba kulasu kikeyi ba, so kike mu zuba miki ido kici gaba da zama a gaban ki dan kawai muna zaune a kudu? Kina zaton inda a arewa ne har zamu yarda ki kawo uwar haka ba tareda mun aurar dake bane?
Abban su nidai ina goyon bayan ka tunda tace bata son lukman d’in to kai ka duba a gefen ka kawai tunda ruwan ido yasa ta k’asa tsaida tsayayye”

Kuka Moon din ta fashe musu dashi, cikin kukan take cewa “Dan Allah Baba karka min auren dole”

“To Maimoon ya kike so muyi dake? So kike musa miki ido kiyi ta zama babu aure ne?”

“Ah ah ai zan kawo mijin auren idan na samu”

“To kiji ni da kyau, sati d’aya kacal na baki daga yau kije ki zauna kiyi nazari da kyau ki tantance a cikin samarin ki ki fidda gwani, koma waye shi ina so ki gabatar mana dashi idan mun isa Zaria yazo gida ayi magana saboda Abban ku Ahmad zai shigo k’asa ina buk’atar tabbatar da tabbatuwar zancen auren ki kafin sanda zai koma kinji na fad’a miki, tashi ki tafi”

Jiki ba kwari ta mik’e tabar falon cike da tashin hankali,
Dan Allah ita ta ina zata vara fidda miji a cikin sati d’aya kachal, sati d’aya fa kuma tasan kome zatayi bazai canza daga yanda yace sati d’ayan ba,

Bayan fitan ta ne Baba Usman yake ba Umma labarin cewa akwai wad’anda sukazo neman auren Moon din a wajen shi baya son taga kamar ya mata dole ne shi yasa ya bata dama in akwai wanda take so to ta gabatar dashi dan babu fashi indai Allah ya kawo Abba Ahmad lafiya tofa bazai bar k’asa ba sai sun kammala zancen auren da yaran,
Sai dai kuma kids Umma ta tambaye shi waye ke neman auren na Moon bai fad’a mata ko waye ba sai ma k’okarin d’auke hankalin ta da yayi da wani hirar a sanda ya shaida mata cewa yanzun hakan isar su Zaria Hajiya ke jira dan suje su nemar ma AK auren Meenal a wajen iyayen ta maza,
Ita ko sosai tayi farin ciki dajin labarin cew AK ne keson auren Meenal wannan karon,
Taso ta kawo mishi zancen Sarki da yake son Moon sai kuma ta hana kanta,
Bayan Ummah tabar wajen Baba Usman wajen Moon ta wuce dan tana buk’atar magana da ita,

“Maimoon kin daiji abinda Baban ku yace koh? Sanin kanki ne kuma sati d’ayan nan daya diba miki yana ciki babu wani sauran uzurin da zai miki,
Maimoon nidai nayi miki sha’awar ki auri Lukman bama wai dan saboda kasancewar shi yaron yayata ba ah ah sai dan na yaba da tarbiyar shi da kuma soyayyar shi gareki, amma tunda kince bakya son shi bazan miki dole ba sai dai zan baki shawara duk mijin da zaki gabatar a gaban iyayen ki ina son ki fara natsuwa ki tabbar da cewa shin kina son shi har cikin zuciyar ki ko ah ah”
Ta d’an bata shawarwari kafin ta fice tabar mata d’akin,
Ita dai wallah tana cikin tsaka mai wuya domin dai tunda Sarki ya shigo cikin rayuwarta tayi fatali da duk sauran samarin da suke ta mata naci a baya,
Sai yanzun data riga ta gama Koran kowa ne kuma za’ace a cikin sati d’aya ake buk’atar ta fidda mijin aure?

A wannan ranar ma Sarki yazo wajen ta hira sai dai kuma tun zuwan shi ya gane akwai abunda ke damun ta amma juyin duniya yayi da ita akan ta fad’a mishi mike damunta tak’i, hirar ranar dai babu armashi haka suka rabu ya mata Sallama akan sai sun had’u a zaria.

Shi kuma sarki tsakanin shi da Teemah yanzun kam komai zam zam dan bakin kokari Teemah tanayi wajen bashi kulawa abinda baiyi tsammanin cewa zata iya yinsu a shekarun baya ba shi takeyi mishi a yanzun, idan kaga yanda suke rayuwa bazakayi zaton cewa ba haka suka rayu tun farko ba, shi kanshi saboda kwanciyar hankalin daya samu harda wata yar k’iba yayi, batun gyaran gidan su na KD ko tuni Salman yayi tsaye komai ya kammala kayan su wanda teemah ke buk’ata tuni aka tura su zuwa KD duk wani shiri na tashi sun riga sun gamayi, kasuwancin Teemah din kuma ta mik’a shi a hannun Azizah ranar da Moon zata wuce Zaria suma shine ranar da zasu wuce KD,

Ita Moon daga gidan su kanin ta imran ne ya kaita airports a wajen shiga jirgine kuma suka had’e da Sarki da nashi iyalan wato matar shi da kannin ta wad’anda zasu mata rakiya zuwa sabon gida,
Sam Sarki bai shaida mata cewa shima wannan jirgin zaibi ba duk da cewa shine ya biya mata kudin jirgin, kai jama’a wallahi maza dai sun kware a wajen iya munafunci wai ita Moon itace Sarki zai nuna kamar bai Santa ba balle yasan daga inda ta fito a cikin jirgin nan tafa ganshi ya ganta amma sai ya wani d’auke kai sai wani iyayi yakeyi yana wani faman tarairayo tsohuwar matar shi zuwa jikin shi ita kuma sai wani k’ara langwabewa takeyi a jikin shi kamar dai a kanta aka vara d’aukan cikin haihuwa, zama na awan nine amma ji Moon tayi uwa kwana sukayi suna tafiya saboda tsabar kishi gashi kuma duk yanda taso d’auke kanta daga kallon shida matar nashi hakan ya gagara sai dai dasun had’a ido ita kuma take jifan shi da harara,
Wallahi mutumin nan ma ya raina ma kanshi wayau dama yasan yana son matar shi har haka shine kuma zaizo yace yana son ta bai kuma ji kunyar idon taba yake kwantar da matar nashi a jikin shi wato hummm ba komai ai wallahi yayi da ya,
Ba karamin Hamdala tayi ba a sanda jirgin su ya sauka, bayan saukan su dama so tayi ta d’auki drop kawai ya wuce da ita Zaria kai tsaye sai gashi wai dan munafunci suna sauka Sarki ya fad’a kiranta a waya, tana kallon kiran ita kuma tayi mishi banza,
Ganin bata dauki wayar ba shi kuma sai ya tura mata messages yana shaida mata cewa ta jira akwai wanda zaizo ya kaita zaria,
Tsaki tayi bayan ta karanta a bayyane ta furta cewa, Allah ya kyauta tahau motar shi ko jirgin nan inda tasan cewa dashi da matar shi a ciki da bata hauba,

Duk abinda takeyi yana lura da ita hakan nema yasa bayan su Teemah sun shiga mota ita koma ya koma inda take tana shirin shiga motar da zai kaita zaria, mai da k’ofar data bude yayi ya rufe,

“Ba nace miki akwai wanda zaizo ya kaiki ba me yasa bakyajin magana ne, Kwaro kai”
Ya kira sunan kwaron bayan yaja hannun ta,

“Ka d’auko kayanta kasa a mota ka kuma sallami shi wannan mutumin”
Ya k’arasa fad’a yana cigaba da jan hannun ta zuwa motar da kwaro wanda bai dade da isowa wajen ba ya faka a kusa dasu,
“Ok Sir” shi kuma kwaro ya furta sai da ya sallami mai motan da wasu yan kud’ad’e kafin mutumin da kanshi ya maida kayan nata zuwa motar kwaron,

“Ni dai ka sake min hannu ina ruwanka dani ne wai,ina ce jirgi d’aya muka hawo tun daga Lagos zuwa nan amma ka fuske ka nuna kamar baka tab’a ganina ba sai yanzun ne idanuwan ka suka shaida maka ni?”
Ta tambaya cikin fushi tana kwace hannun ta,

“Too haka akayi?” Ya tambaya yana dafe gemu,

“Ah ah ba haka akayi ba kuma ni bazan bi motar kaba tunda ba kai ka kawoni ba kasa ya maida min kayana cikin motar daya cirosu”
Ta fad’a tana dafe kugu bayan ta b’ata fuska ta zunburo baki tana jijjige jijjige,

Shi dai kwaro lallab’awa yayi ya shige gefen direba ya zauna cike da mamaki,
Shifa yarinyar nan kallon idon sani yake mata sai dai kuma ya kasa gano a inda ya Santa amma kam tabbas ya Santa,
To wai ma da Sarki yake ta wani lallab’ata kar dai ace Sarki wani auren zai k’ara,
Kashe kunne yayi yana sauraren hirar su a yayinda Sarki yake cewa,

“Moon please ki adana rikicin ki ba yanzun ba, naji nayi laifi kiyi hakuri kibi kwaro ya tafi dake idan nazo zan amshi hukuncina”

“Moon “kwaro ya maimaita a bayyane, k’ara lekowa yayi, a bayyane ya k’ara cewa,

“Wallahi itace, Moon dai k’awar Meenal, Meenal fa matar da Sarki ya saka tome ya had’ashi da Moon kuma?.

*Ummiee ce*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button