Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 35

Sponsored Links

⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️
*BOOK 2*

*PAGE 35*

Tanaji tana gani haka Sarki ya juya zuwa wajen motar da matar shi take ciki ya shige ciki abinshi bayanda yasata a motar Kwaro ya kulle duk rikicin datakeyi na cewa ita bazata hau motar ba haka yayi kunnen uwar shegu da ita bai k’ara kulata ba tun bayan da yace mata ta adana rikicin ta har su had’u a Zaria ,
Kallo mai cike da madaukakin mamaki tabi bayan shi da shi har zuwa sanda mota biyun da akazo daukar su dashi suka fice daga cikin airports ɗin,
Hummm Namiji dan baban shi,
Bata san ya zata kwatanta abinda taji a cikin zuciyarta a dai dai wannan lokacin ba, abunda tasani kawai shine bataji dadin halin ko in kula ɗin daya nuna mata a cikin jirgin ba, to amma idan tace tayi fushi wani dalili take dashi nayin fushin alhalin iya kalmar I LOVE YOU ne kaɗai ya shiga tsakanin su, bayan shi kuma har yanzun ta kasa bashi damar da zai gabatar da kanshi a gidan su balle ya tantance matsayin shi,
To ma wai me yasa zataji zafi dan ya nuna kulawan shi akan matar shi? zuciyarta ta tambayeta, ance kasowa dan uwanka abinda kake soma kanka ai itama bazataji dad’i ace mijinta ya kula wata budurwa a gaban idonta ba,
Itafa laifin shi kawai take son gani ba kuma komai ya kawo hakan ba sai tsabar kishin shi, batayi zaton zataji kishi irin haka dan kawai ta ganshi tareda matar shiba,
“To amma ai yasan ina son shi dan haka dole yasan zanji kishi”, sai da ta tura baki gaba kafin murya ƙasa² cike da ƙunƙuni ta Kara cewa “kuma wallahi nima sai na rama”

“Na’am kina magana ne?”kwaro dake tuƙi ya tambaya,
“Ni ba dakai nakeyi ba”ta amsa mishi tana kauda kanta gefe, shima sai bai ƙara bi takan taba sukaci gaba da tafiya.

Shiko Sarki a gefen shi dariya ma moon ɗin ta bashi, wai me yasa su mata basa son zaman lafiya ne wai?
Ita yanzun tana fushi dashi cewa bai kulata ba duk da cewa ya ganta, to fisabilillah wani irin neman magana ne wannan? To so tayi shikenan kawai daya ganta d’in sai yabar matar shi da nata ahalin ya dawo gefen ta ya tare bayan kowa yana da mazaunin shi ko me take so yayi?
To idan ma ya kulata me take so yayi matane? Ita da kullum take nuna cewa babu komai a tsakanin su tunda KO zuwan da yakeyi gidan su a sace take fitowa bata son asan cewa yana zuwa wajenta,
Humm gaskiya rikicin mata sai su ita nata ma wasa ne bata san cewa inda ace matar shi tasan abinda yake tsakanin shi da itaba da Allah kad’ai yasan kalar tashin hankalin da zasuyi, shi bai shirya yin fitina dako wacce daga cikin suba in jarumta take son nunawa ta bari tukun har zancen auren su ya tabbata sai ya tabbatar da jarumace ita.

Sak’o ya tura ma Moon d’in kamar haka “Kar kiyi fushi Baby zan kiraki idan Allah yasa kun sauka lafiya, ya kike”

Koda saƙon shi ya isa cikin wayarta sai da ta karanta shi ta ƙara mai maita shi kusan sau uku, to mema yake nufi da cewa kar tayi fushi? To in tace tayi fushi ma ai bata da dalilin yin fushin wacece ita a wajen shi? menene matsayin ta? sune tambayoyin da take buƙatar amsar su daga gareshi, to dan Allah a yanda yake nunawa ne zata wani fito kai tsaye tace mishi iyayenta sun bata sati d’aya ta fidda mijin aure kuma ita shi zuciyarta ta zab’a,
Tunda harta yarda ta kula mai mata ai dama tasan dole zata fuskanci abubuwa fiye ma da wanda yayi mata a yau,
“Nace kiyi hakuri” ya kara tura mata,

Ita kuma sai ta tura mishi amsa kamar haka,
“don’t Baby me, i am not your Baby😒”
Bai ƙara tura mata ko wani saƙo ba tun bayan daya karanta amsar data tura mishi , dan yaga alaman rikici takeji da gaske,

Acan gidan Sarki kuwa yan Zaria ne maƙil waɗanda sukazo domin tarewar tun daga kan iyalan gidan Malam yan gidan su da kuma yan uwan Uwar gida sun kammala gyaran gidan tsaf sai isowar masu gidan kadai sukeyi, dan haka koda suka isa babu ɓata lokaci akaci gaba da gabatar da walima yan Zaria basu bar gidan ba sai yamma sukabar masu gidan suna huta gajiyar tafiyar da sukayi kafin wucewar su kuma saida Malam Sulaiman suka zaunar dasu suka musu nasiha akan hak’uri da kuma zaman lafiya a tsakanin su especially its Teemah da bata da kowa a garin sai Mijinta da yaranta Uku wadanda Uwar gida ta dawo mata dasu hannun ta, to muma dai sai muce Allah ya zaunar dasu lafiya.

Zaman shiru akayi a cikin mota tsakanin Kwaro da Moon babu wanda ya kula Wani har sai da suka isa jaji, fakawa yayi a kofar wani shagon da ake saida snacks a cikin motar ya barta ya shiga cikin shagon, bai jima ba ya dawo ya bud’e gefen shi ya shiga saida zauna kafin ya juya baya ta gefen da take ya mik’a mata ledar hannun shi, “Sarki yace bakici komai ba”
Amsar ledar tayi bayan ta mishi godiya, shidai har yanzun bai dena mamaki ba, bai k’ara tabbatar da cewa lallai Moon din da yake hasashe bane har sai da bayan isar su Zaria ya tambayeta Ina suka nufa ita kuma ta shaida mishi da cewa unguwar malamai zai kaita, a gidan Baba Malam ta sauka wajen Mommy Hauwa saida taci abinci ta huta kafin ta kira Meelat ta tambayeta suna inane? Ita kuma taje ta same su. Wannan shine abinda ya faru, tunda ta sauka kuma taki d’aukar wayar da Sarki yake ta faman jera mata kira da tarin sak’onni,

*****

“Yanzun Meenal idan Bash yazo wajen ki wani irin tarba zaki mishi? ”
Maryam ce ta k’ara jefo tambayar jin dukan su sunyi shiru,
Ajiyar zuciya mai nauyi Meenal din ta sauke,
“Zanyi murna da ganin shi mana, koba komai nasan ya damu dani sai dai ni kuma a yanzun bana jin komai a kanshi, ba kuma wai Ina kinshi bane ah ah Bebs please let’s close this chapter I really don’t want to think about it anymore, ke Moon wai ma uban me ya wani kaiki zuwa ki sauka a unguwar malamai bayan kin san cewa ni ina nan?”

“Saboda bikina tazo shi yasa dole zata zauna kusa dani har a gama komai idan ta kaini gidan mijina saita dawo nan”
Meelat taba Meenal amsa tana hararar ta.
Washe garin ranar ne kuma suka gabatar da event din da suka shirya ma Meelat a school ,

kamar yanda suka shirya surprising dinta takoyi mamaki kwarai ta yanda har suka shirya komai na program din batareda sanin taba, hakan kuma bai hanata nuna dad’in taba sosai domin ba iya friends dinsu na cikin makaranta bane kawai suka samu damar halartar wajen harma da wasu daga cikin tsoffin k’awayen su na primary secondary dama yan uwa na kusa, sun shirya abun ya tsaru sosai kuma Meelart din ta samu tarin kyaututtuka daga abokanan arziki, anci ansha anyi raha haka kuma anyi ma Amarya fatan Allah ya basu zaman lafiya ita da mijinta a gidan auren su, daga school da aka watse taro dukan su unguwar malamai suka wuce, wanda hakan kuma yasa Meenal bata samu damar komawa gidaba dole a nan unguwar malaman suka kwana.

Shiko AK a gefen shi tun rana yake faman jerama wayarta kira sai dai kuma ga mamakin shi wayar zatayi ta karane kawai har zuwa sanda zata gaji ta yanke batareda an d’auki kirar ba,
Yasan cewa dole zatayi busy saboda program d’in dan haka sai ya mata uzuri da zaton ko idan tazo taga tarin missed call dinshi ita ma zata neme shi daga baya,
Sai dai kuma abin haushi haka aka wuni zungur ko sau d’aya bata kira ba shima kuma daya gaji da jiran kiran nata ya k’ara kira bata dauka ba daga karshe ma sai aka dunga fada mishi cewa wayar tana kashe,
Yaji fushi sosai dan ya shak’a domin dai ta fita gidane yau d’in da sassafe ko neman shi batayi ba balle suyi sallama,
Messages din safe daya tura mata ma bata bashi reply ba koba komai ai yaci ace ta kira shi taji ya yake amma batayi hakan ba, shi kuma ya yarda girman ya kirata tak’i d’aukar wayar d’auriya ya aro ya d’aura ma kanshi dan so yake yaga iya gudun ruwan ta in har ba itace ta kira shiba to bazai nemeta ba wannan shine hukuncin ta. (Bari mu koma gefe mu gani zai iya k’in kiran🤷🏻‍♀️)

Ita KO gaba d’aya yau d’in yanda abubuwan suka sha mata kaine yasa dole ta fita daga wani batun d’aukar wayarta ta duba ko ya kirata ba kuma wai dan ta manta da batun shi bane ah ah komai takeyi yana nan mak’ale a cikin zuciyar ta kawai dai bata son ta raba hankalin ta biyu ne dan shi idan ya kira waya bai san yayi magana na minti d’aya ko biyu ya yanke kira ba, ah ah ko bazaice komai ba haka zai ajiye wayar kuma yace dole sai ita ta mishi hira,
yar karamar wayarta ce a tareda ita wayar da shi AK yaketa kira a cikin mota ta barta k’aramar kuma shi bashi da wannan number din,
Bata waiwayi babbar wayar ba sai da dare, koda ta d’auko ta kuma ta dad’e da mutuwa dan haka sai bata damu da kunnawa ba kawai sai ta mak’alata a caji sukaci gaba da hirar yanda taron ya k’ayatar ita dasu Moon.

Duk yanda ranshi ya b’aci na rashin kunna wayar nata haka ya daure da dare yayi kuma kasawa yayi ya tsare yana jiran ta dawo gidan ta fad’amishi dalilin ta na kama ta kashe amma har k’arfe 10 na dare ya wuce basu ba alamar su, gaza hak’uri yayi yana ciccjiwa haka dai ya daure ya kira wayar Sultana, bayan ta amsa kiran ko gaisuwar da take mishi bai amsa ba ya jefo mata tambaya kamar haka,

“Ina Dr take?”
koda bai kira suna ba tasan Meenal yake nufi, dan haka sai ta amsa mishi da cewa “tana falon Baba Malam in kai mata wayar ne?”

“Me takeyi acan d’in ne? Ita Ina takai wayarta Nike ta kira a kashe? ”

“Wayarta ya mutu babu caji bari in kai mata wayar”

“OK kuma idan kin shiga bance ki bata wayar ba, kawai dai ki zauna kusa da itane yanda zanji muryarta”

Amsawa tayi da cewa to kafin ta tashi ta wuce falon Malam d’in,

Ya Sa’eed, Ya Sheikh, Ya Naseer sai Meenal cikon na 4 sune zaune a falon suna hira a tsakanin su Meenal da Ya Sa’eed su nasu hirar suna tattaunawa ne inda yake tambayar ta cewa ya suke ciki tsakanin ta dasu Aliyu, wayarta dake caji a gefenta ta d’auko saida ta kunna wayar kafin ta shiga cikin WhatsApp ta nuna mishi chat d’inta da Ya Hashim inda yake fad’amata cewar yana son ta bashi ranar da zaizo gida ya sameta yana son su tattauna wani magana a tsakanin su, ita kuma ta dai bud’e sak’on ne kawai ta karanta amma bata bashi amsa ba saboda bata riga ta yanke inda zasu had’uba,
Bata son ya sameta a gidan hajiya ne saboda tana tsoron AK,
Eh mana dole tace tana tsoron shi tunda tasan idan yaga Hashim din kai tsaye cewa zaiyi saurayin tane ita bata son ma yaga Hashim din dan tsakani da Allah Hashim dai ya mata tsufa wallahi tasan idan AK ya ganshi ma dariya zai mata, shifa yanzun saboda tsabar samun waje wai har itane zai kafama masu gadin gidan dokar cewa duk wanda yazo gidan su fara tambayan shi wajen wa yazo inhar mutum yace wajen ta yazo to karsu barshi ya shiga su fad’ama kowa waye cewa bata nan, dan Allah jama’a kuji wani k’arfin halifa irin na AK FISABILILLAH haka ake rayuwa gaskiya saurayi a cikin gida baiyi ba wallahi,

“To me yasa baki bashi amsa ba, Meenal Ina jiye miki abinda zaije ya dawo fa,” ya fad’a murya k’asa² kamar yanda suke magana shida ita d’in tun d’azun babu maijin abinda suke tattauna wa,

“Zanyi kokari gobe idan na koma gida ince mishi yazo”
“Ah ah kawo wayarki dai ki tura mishi sak’on yanzun”
Badan taso ba haka tayi typing ta tura ma Hashim din cewa yazo tudun wada gobe ya sameta da rana dan tasan da rana AK bai cika zama gida ba,
“Shi kuma Aliyu fa?” Ya k’ara tambaya, “to ai shi cewa kawai yayi insa rana zaizo mu gaisa,”ta fad’a tana tura baki,
“OK tunda abin ya zama haka shima ki tura mishi sak’on yazo gidan gobe ya sameki”
“To kai Ya’ya idan dukan su sukazo a lokaci d’aya kuma fa?”
“Uhumm Meenal kenan to ke zaki bari suzo duka a lokaci d’ayan ne? Ai kowa lokaci zaki bashi, na tabbatar da cewa dukan su zasu kiraki a goben dan ki basu lokacin da zasu zo su sameki ke kuma saiki basu lokacin daya dace”

Suko Ya Sheikh da Ya Naseer suna hira ne akan walimar da aka gabatar a gidan Sarki domin shi Ya Sheikh shi Malam ya wakilta zuwa walimar a maimakon shi sabida daga Sarki har Ya Sheikh din basu wani san juna sosaiba, yanda Sarki ya nunajin dad’in shi da zuwan su gidan nashi da kuma yanda ya dunga nan nan dasu shine abinda ya burge Sheikh d’in har hakan yasa yanzun ya d’auko hirar suke tattaunawa,
Koda Sultana ta shiga falon bayan gaisuwa gefen da Meenal take itama ta rab’a ta zauna, a kunne ta rad’ama Meenal cewa “ko dai shima Yayan mu ya shiga sahun zawarawane”tana nufin ya Sa’eed ko shima son Meenal din yake,

“Dallah can matsa OK kibani waje yar rainin wayau kawai kuma sai Allah ya saka min”
“Allah ya baki hak’uri”cewar sultana tana gyara rik’on wayar dake hannun ta,
Sun dade a falon suna hira har zuwa sanda Malam ya shigo kafin sultana ta janye Meenal din daga falon suka koma wajen Moon wacce ke falon Mommy Hauwa rik’e da waya tana dakon jiran kira daga Sarki,
Wallahi Sarki yayi mugun bata mamaki wai ita maimoon itace Sarki ya banzatar tun rabuwar su a airport daya tura mata massage lokacin suna hanya har yanzun bai Kara bi takanta ba domin ko message d’in daya saba tura mata unin yau gaba ko sau d’aya bai tura mata message ba kuma bai kirata ba,
Tayi tayi ta danne ta nuna irin bata damuba d’in nan amma wallahi maganar gaskiya ta kasa danne hakan, idan ita kuma ta d’auki waya da niyyar ta kirashi sai taji kai inah, ai in ta kirashi to ta fad’i ba nauyi wallahi, dan shirun da yayi ita ta d’auke shi ne a matsayin cewa wato tunda ya koma sabon gida ya tare cikin iyalinshi shi yasa ya manta da ita to ai ba komai domin a sanda zaiyi lokacin ta itama kuma zata rama ne.

Washe gari Meenal ta koma gida a daren jiya kuma sam koda wayar ta tayi caji bata damu da cewa bari ta kira AK ba tak’i kiran shine saboda tasan yana iya cewa ta koma gida a wannan daren,
Koda ta isa ta tarar da motar shi a cikin gidan ta kuma ji dad’in hakan dan ko babu komai itama tayi kewa, gaza shigewa sashen Hajiya tayi har saida ta juya akalar tafiyar ta zuwa side d’in shi, hannu takai ta bud’e k’ofar amma sai tajita a kulle ta nocking ta farayi wai ko Allah zai sa ya jiyota daga ciki yazo ya bud’e mata, sai dai kuma har ta gaji da dukan k’ofar baizo ya bud’e mata ba, jikinta yayi sanyi sosai harta fara tunanin to kodai yayi fushine tunda tun jiya data fita babu kiran waya ba sak’o, to amma ai koma menene bai kamata yace zaiyi fushi da ita har haka ba koba komai ai yasan dole zatayi busy a jiyan ba gashi yanzun yau ta dawo ba, shine dan wulakanci har ita zata zo tana buga mishi k’ofa amma yak’i zuwa ya bud’e mata dan kawai ya samu tazo ganin shi, aiko yayi da y’a wallahi, juyawa tayi jiki a sanyaye ta wuce sashen Hajiya,

Shiko AK dama sunyi da Sultana cewa idan Meenal ta baro unguwar malamai ta kirashi, dan haka tana wucewa Sultanar ta kira shi ta shaida mishi cewa Dr fa tana hanyar komowa zuwa gida, sai da ya duba agogo ya auna dai dai lokacin isowar ta kafin ya taso daga cikin bedroom din shi ya fito falon ya murzama k’ofar falon key, sannan ya koma ya nemi waje ya zauna wayar shi a gefen shi yana jiran isowar ta.
Kamar yanda ya kiyasta bata wuce adadin lokacin daya d’iba mata ba ta iso gidan yana kuma jin shigowar motar ta ya mik’e zumbur zuwa bakin window ya yaye labulen wajen yaci gaba da tsayuwa yana kallon ta harta fito daga cikin motar, yalwataccen murmushi ne ya kawata fuskar shi a yayinda yaga ta nufo sashen nashi dan haka sai kawai ya saki labulen ya koma kan kujera ya d’aura kafa d’aya kan d’aya kuma duk bugun da takema k’ofar yanajin ta dan daga karshema tasowa yayi ya lab’e a wajen window yana lekota har zuwa sanda ta gaji da dukan k’ofar ta juya, yayi mamaki da yaga ta k’ara dawowa bakin k’ofar kuma yayi zaton ko zataci gaba da nocking ne sai kuma yaga ta fara danne danne a wayarta babu b’ata lokaci kiran ya shiga, tabbas da ace bai sanya wayar shi a silent ba da asirin shi ya tonu a lokacin dan yasan tabbas zata iyajin k’arar wayar nashi, kira uku tayi bai d’auka ba dan haka dole tabar wajen a fusace.

Kamar yanda ya sa’eed yayi hasashe hakan ne ya faru domin da Aliyu da Hashim dukan su sun kirata da safen dan suji lokacin da zasu zo gidan su sameta,
Ta shaida ma Ya Hashim cewa zuwa 12 shi kuma Aliyu zuwa k’arfe 2,

Dan haka 12 dai dai kamar mai auna lokaci domin ko 12 nayi Isah ya sallama falon na Hajiya cewa Meenal d’in tayi bak’o, bata wani damu ba tunda ai ta riga tasan da zuwan shi dan haka sai kawai tacema Isah ya shigo dashi ita kuma ta haura sama wajen Hajiya dake d’aki ta shaida mata cewa ga ya Hashim yazo gidan zasu gaisa,

Hajiya bata wani nuna damuwa ba sai ma cewa da tayi tana mishi barka da zuwa taci gaba da abinda takeyi,

Fitowa Meenal din tayi ta sauko k’asa shiko Hashim tun daga kan benen yake binta da kallo dan shifa dama Allah ya sani batun yauba ya dad’e yana kwad’ayin yarinyar nan abinda ya hana shi motsin k’arfi a shekarun baya yasan ko ya nema Malam bazai bashi ita ba,
Amma yanzun da take matsayin bazawara yasan bazai sha wahala wajen shawo kan dangiba wajen ganin sun goya mishi baya,

Da fara’a ta sauko,

“Barka da zuwa ya Hashim ya aiyuka, kayi hak’uri na barka kana jira koh?”

“Ah haba dai babu damuwa ai dafatan kina lafiya ya likita ya gidan ya karatu kuma?” Alhamdulillah wallahi ba kasha ruwa ba” ta fad’a tana nuna center table d’in gaban shi wanda aka jera kayan motsa baki,
Ruwa kad’ai yakai hannu ya d’auka ya bud’e murfin ya tsiyaya ma daidaici a cikin kofi kafin yakai kofin bakin shi yasha ruwan,

“Alhamdulillah” ya fad’a bayan ya gama shan ruwan sai ya maida kofin ya ajiye,

“Ina fatan dai zuwan nan nawa bazai zama takurawa a gareki ba”ya furta hakan yana mai kureta da idanu,

“Ah haba dai ko d’aya ai saboda nasan bazan takura ba shi yasa nace kazo yau dan yau ne nike da damar zama a gida cikin satin nan ina da bikin Aminiyata”
Gyara zaman Babbar rigar dake jikinshi yayi yana k’ara gyara zama da kyau ya fuskance ta,

“Wato ainihin abinda yasa kikaji na nemi son ganin ki domin mu dai daita Meenal ba komai bane sai dan in shaida miki sirrin dake cikin zuciyata”

Da kallo ta cigaba da binshi tana jin abun wani iri, abun ya mata bambara kwai dan Wallahi shifa Hashim din ba yaro bane amma jibi yanda yazo yasata a gaba ko kunya wai shi a dole yaxo fad’a mata cewa yana sonta,

“Kina jina koh Meenal? Kinga dai ni ba bak’on ki bane kin san ni kin san waye ni kin san iyayena, gidana, matana, yara na dama komai nawa duk kina da masaniya akan su, to abinda nike so in shaida miki shine nidai na ganki kuma kinyi min dan haka ina son ki da aure, kar kiyi zaton ko yanzun ne na fara sonki ah ah tun kafin Malam ya badaki ga wancan wanda ya kasa rik’ekin nike son ki ina tabbatar miki da cewa da ace nasan cewa rik’on sakainar kashi zai miki da tun lokacin na fito mun kara mai rabo ya d’auka a tsakanin mu, amma da yike Allah yace ked’in rabona ce shi yasa ya sako min ke salin alin, dan haka nidai yanzun kin san cewa niba yaro bane dan haka bazan juri zuwa hira ba na dai fara sanar miki ne kafin inkai maganar gaban Baba Malam dan bana son abin ya d’auki lokaci”

Ku nemo ruwa ku an taya ma yar gidan malam dan zantukan bak’onta dai sun sumar da ita🤣.

*Ummiee ce*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button