Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 33

Sponsored Links

βšœοΈπŸ”±πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ”±βšœοΈ
*BOOK 2*

*PAGE 33*

To mu shiga daga ciki mana nasan bakasan ansa ranar aure na ba wannan satin mai kamawa zanyi aure kaga ba dad’i mutane su ganni tsaye da kai a nan dan haka bismillah mu shiga daga ciki ina ganin hakan zaifi ”

Cikin suka wuce suka nemi waje a farfajiyar gidan suka zauna,

“Bari in shiga ciki in kawo maka ruwa,”

“Ba bukata ki barshi kawai nagode”

“Ok tunda kace haka yanzun me kake son ji daga gareni?”
Ta tambaya tana binshi da kallo, tunda har ya wanko kafafun shi yazo har nan tasan gaskiyar yake son ji daga bakin ta dan haka babu amfani ta boye mishi.

“Ina son insan komai, idan nace komai Meelat ina nufin komai karki boyemin akan Meenal ,”

Gyara zama tayi da kyau kafin ta fara da cewa,

“Kamar yanda ka sani a shekarun baya da suka wuce kaida Meenal duka mun shaida kuna son junan ku, nasan kayi bakin k’okarin ka wajen ganin ka shawo kanta akan ta baka daman gabatar da kanka a gaban iyayen ta amma hakan bai faru ba har zuwa sanda komai ya faru,
tasha fad’ama na yanda kukayi da ita akan hakan,nasan a lokacin zakayi zaton ko bata sonka ne shi yasa amma kuma ita a gefen ta ba hakan bane, tak’i yarda ka gabatar da kanka din ne saboda tasan da zarar ka kai maganar ka gidan su to zancen aure za’ayi saboda kaima kasan yaran gidan su ba’a barin sukai har matakin da ita takai a lokacin ba tareda an aurar dasu ba,
WallahiΒ³ Meenal bataci amanar kaba ta kuma soka da dukkan zuciyar ta a wancan lokacin,
In baka sani ba bari in fad’a maka idan kuma ka sani hakan zai zama maimaici ne a gareka, ita kanta bata san cewa itama tana cikin wadanda za’a d’aurama aure a wannan lokacin ba har sai ana gobe daurin auren nata, tayi kuka tayi kuka babu kalar borin da batayi ba akan bata son auren amma kuma bata isa ta canza abinda Allah ya riga ya kaddara zai faru a lokacin ba sai dai kuma duk halin da take ciki bata manta da kaiba, ina da labarin kiran da Aunty Hassana tayi maka domin a wajen Meenal ta amshi number dinka,
Kayi hakuri a lokacin nida Maryam mun kasa zuwa asibitin da aka kwantar da kai duba Kane saboda bamu sanda wani idon zamu kalle ka ba, munyi zaton cewa zuwan namu zai iya zama k’arin tsanani a gareka…. ”

Katseta yayi saboda shi ba wancan labarin daya riga ya sani yake son jiba, ah ah halin da Meenal take ciki a yanzun shine damuwar shi,

“Yanzun Meenal tana ina?”

“Tana Tudun wada gidan Hajiya, auren ta da Sarki ya mutu a watannin baya hakan ne yasa ta koma can da zama”

“Me yasa bayan auren ya mutu daga ita har ku babu wanda yayi tunanin nema na?”

“Saboda a iya sanin mu baka k’asar, kuma ko kana k’asar ma ai hakan bai dace ba tunda nidai nasan kayi aure, yanzun da allah yasa kayi katarin ganin ta ba gashi ka biyo sahu ba ”

“Eh bana k’asar kuma nayi auren kamar yanda kikaji, sai dai kuma nima mun rabu da matar”

“Ayya to Allah yayi zab’i da mafi alkhairi”
Cewar Meelat,

“Ameen!
Meelat meke tsakanin AK da Meenal domin a yanda na gansu yau jikina yana bani cewa akwai wani abu a tsakanin su kuma ita waccan yarinyar dana ganni tareda Maryam tace min wai shine mijin da Meenal din zata aura shi yasa Nazo nan dan ina son inji gaskiyar komai daga bakin ki dan nasan bazakiyi min karya ba”

Ajiyar zuciya ta sauke tana kauda kanta gefe dan yanda ya tsareta da ido tasan gaskiyar maganar yake son sani,

Kai Sultana dai bata ji
sam wallahi,inba shegen surutun taba meye ya kaita wani ce mishi AK ne mijin da Meenal din zata aura bayan sun shaida mata komai dake tsakanin Bash din da Meenal, ai da tayi shiru da bakin ta ba lallai yasan cewa auren ya mutu ba,

saida tayi gyaran murya kafin ta amsa mishi da cewa,

“Itafa yarinyar nan daka gani shegen iyayine da ita, ko kuma dai kayi wani abunda ka b’ata mata rai shi yasa ta fad’a maka hakan, nidai nasan akwai kyakyawar alaqa a tsakanin su kamar yanda kaima kasan shi din d’an uwanta ne bayan hakan kuma ban san wani abun ba zaifi dacewa ka tun kare Meenal d’in kuyi magana kai tsaye ta yanda zakaji komai a bakinta”

Sun danyi hira kad’an kafin ta rakoshi k’ofar gida sukayi Sallama shi ya shiga motar shi ya tafi ita kuma ta dawo gida,

Tana shiga gidan Maryam ta fara kira ta fad’a mata cewa suzo ita da Sultana su sameta tana jiran su, a wannan ranar kuma Sultana bata dawo gidan Hajiya ba a Unguwar malamai tayi zaman ta saboda su sunyi zaton cewa tunda Bash yasan inda Meenal take zaije can ya neme ta.

*washe gari*

Hajiya, AK da Meenal ne zaune akan dinning suna karin kumallon safe,

Wato dai Hajiya bata k’ara tabbatar da cewa soyayya yana sa mutum ya zama wani abun daban ba sai yanzun da so ya damk’e mata wuyan D’an mai k’arfi, gayen nan fa gaba d’aya ya fitsare kafafuwan shi yayi fatali da wani abu da akeji in ana gaban sirikai mai suna kunya,
Dan dai Hajiya ko tana waje ko bata babu abinda ya dame shi zai aiwatar da abunda yayi niyya ne kawai abinshi,

Domin dai tunda ya dawo masallaci yana komawa d’akin shi kayan shi ya tattaro shida su (Kabir wani yaron shine dake mishi aikaceΒ² idan yana gari) ya dawo dasu sashen Hajiya a cikin d’aya daga cikin d’akunan kasa ya zuba kayan, duk wani abu na bukata nashi sai da yasa su kabir din suka kwaso mishi,
Tunda farar safiya masu aiki sukazo suka fara aikin yima gidan kwas kwarima, inda duk yake da buk’atar gyara an gyara sauran kuma ko ina aka bishi da sabon fenti gyara sosai akema gidan wanda badan komai ake yin shiba sai dan shirin bikin Musty,

Hajiya tayi mamakin ganin AK ya kawo kayan shi sashen ta dan haka gaza yin shiru tayi saida ta magantu,

“Kai wai nace wannan kayan naka da naga ka kwaso ka kawo nan badai kana nufin k’aura kayi daga can sashen ka ka dawo nan bako?”

“Kema dai Hajiya kin san bana son kamshin sabon fenti kawai zan zauna anan ne na yan kwanaki kafin ranar bikin zan koma sashe na”

“Ah ah Abdul wannan batu dai duk wanda yaji yasan gulma ne dajin baki, tsakani da Allah tun tuni kasan zakasa ayi aikin fentin gidan nan baka sa anyi tun kafin ka dawo ba sai yanzun daka dawo ne zaka wani tattaro min kayan ka kayo sashena wato dai shi kenan ni bani da sirri, duk wanda ya kwaso gyayyar shi wajena zai sauka,
To ta ina ma zan yarda niko inyi rayuwa hankali kwance da kai sankacecen k’ato a sashe guda bayan nasan ina da budurwar daka ce kana so a cikin sashen,”

“Hajiya ban gane ba wani irin magana kenan kikeyi? Kenan dan Meenal tana zama anan tare dake shi kenan ni kuma bazan dawo in zauna anan d’inba,
To miye laifin zaman nawa tunda dai ni ba dodo bane balle kice zanbi dare in cinye miki ita”
Ya fad’a rai bace tsohuwar nan fa ya lura da cewa magana kawai take nema dashi,

“Ah ah fa koma me zakace sai dai kace wallahi, amma ni bazaku mai dani sakarya ba bayan kasan yanda allah ya daura min saurin yin bacci,
So kake ni ina can saman gado ina baccin asara kai kuma kaida ita kuna zaune falo kuna hira, kai din nan dai mai ido a tsaitsaye Allah kadai yasan abunda zaka iya aikatawa a bayan idona,
Dan haka maganin kar ayi tofa kada a soma shi yafi”

“Kenan dai Hajiya kina nufin so kikeyi kice baki yarda dani ba wato ga d’an iska ya dawo sasanki koh?”

Saurin tarar numfashin shi tayi da cewa,

“Ah wallahi karkayi min k’age kasa min magana a baki kasani fad’in abinda ba shine a cikin zuciyata ba, nidai gaskiya nike fada maka dan kar kayi zaton wai ko rashin yarda ne yasa bazanyi shedar kaba,
Ah ah kulawa dai nike nunawa dan yanda naga kana nan nan da ita tofa ana iya samun matsala badai fata nikeyi ba Allah ma dai ya kiyaye dan ni ban haifi dan iska ko yar iskaba insha Allah kuma zuriata bazaku lalace ba,
Duk ma abar maganar badai kace zaman kwanaki kawai zakayi ka koma naka sashen ba, to ga sharud’a,
Na farko babu doguwar hirar da za’a raba dare ba’aje an kwanta ba, na biyu kuma baka ba haura sama ko magana kake so kayi dani sai dai ka jira idan na sauko ko kuma ka kirani a waya na uku kuma kowa ya zauna a inda yake atoh dan mu a zamanin mu ko hannun ki kika sake kikabar namiji ya rike sai dai ki wayi gari kiganki da ciki riki riki,”

Wai dan Allah jama’a mai Hajiya ta d’auki shi, bawan Allah dashi har shine za’a kafama wasu sharud’a dan kawai zaiyi zama na kwana biyu a sashen daba nashi ba,
To yasin Hajiya bata san shi bane yanzun ne zai gwada mata cewa da gaske fa auren yake so, ko dai ta tashi tsaye ta tura a nemo mishi auren jikarta ko kuma shi yayi gaban kanshi.

Hakan ne kuma yasa a wannan safen zaman da sukayi na karin ya tsiri nuna kulawar shi akan Meenal din da gangan a gaban Hajiyar,
Tea Meenal din ta had’a da niyyar karyawa dashi kamar koda yaushe domin so takeyi ta gama da wuri ta wuce unguwar malamai dan rashin Sultana a gidan yasa tanajin gidan ba dad’i dan in Sultana tana waje ta iya d’aukema wanda take dashi kewa saboda barkwancin ta,
Sai gashi ita data had’a tea ma kanta sunyi raba dai dai din shi da Ak domin idan ta d’aura ta kurb’a tana ajiyewa shima zai d’auki cup din ya daidaita dai dai bakin ta yasha, da suka shanye tea d’in kuma kunun gyad’ar da Hajiya ta zuba mishi shi ya koma yana bata a baki har ma in kunun da d’an dangwali gefen bakinta saboda tsabar iya hege yatsar shi yake kaiwa wajen ya goge kunun dashi sai ya lashe da hakorin shi,
Duk wannan iskancin da yakeyi Hajiya kin kulashi tayi dan tasan wani abun ma yanayi ne saboda d’azun tayi magana to bazata biye mishi ya nemi maida ita sakara’u ba,
shiko kunyar ta bayaji wai a gaban idon ta AK ya zauna yana cida Meenal abinci baki,
Ita dai ido da baki kawai ta sake tana binsu da kallon ikon Allah saboda yanda shi uban gayyar ya nuna kamar ya manta da zaman ta a wajen,
Abincin ya d’ibo a cikin spoon ya k’ara nufo bakin Meenal dashi,

“Haaa nace Allah kuwa ina fad’a miki idan baki tsaya kinci abincin nan ba babu inda zakije yau a gidan nan”

“To Yaya ai na fad’a maka na koshi, nifa tea kawai nike sha da safe amma Kali ka gani fa tun dazun kake duramin cous cous din nan bayan nasha tea nasha kunun gyad’a Allah idan ka matsamun amai zai sani”
Ta karasa fada a marairaice dan Wallahi shi dai ke aikatawa amma ita kunyar ke kamawa,

“Kalli ki ganifa saura kad’an ya rage daure kawai ki cinye sai kije ki kwanta abinki dan yau babu zuwa yawo ni dake a gidan nan zamu wuni muna d’ebema Hajiya kewa, Hajiya mai zaki dafa mana anjima ”
Banza dashi Hajiya tayi kamar bataji mai yake cewa ba,

“Hajiya nidai dan allah kice mishi ya kyaleni haka wallahi na koshi”

“To dan ubanka tace ta koshi ai sai ka gyaleta haka ko ana dole ne? Gaba d’aya kabi ka matsama yarinyar mutane saboda tsabar rashin kunya ma a gabana ka ajiyeta kana bata abinci a baki, wai yaushe ka zama haka bani da labari Abdul?
Ke kuma dayar munafukan inace tun d’azun baki yake kina karb’a kamar bakisan da zamana a wajen ba sai yanzun ne zaki sakoni a shirmen ku, kai kuma Allah ina fada maka idan baka dena wannan b’are b’aren jikin ba tofa tattara ta zanyi ta koma gidan ubanta dan bazaku dunga abubuwan ku a gabana ba idan ku baku san kunya ba to ni ku barni da jin kunya”

Haka dai suka gama karin safen Hajiya nata faman mita,

A wannan ranar kasa wa AK yayi ya tsare ya hana Meenal zuwa ko ina kamar yanda yace, dan tunda ya tattaro ya tare a sashen Hajiyan idan kunga ya fita to masallaci zaije yana dawowa kuma zai koma dan harta baccin da yace Meenal tayi bai barta tayi ba dashi suka shiga kitchen da rana Larai nata mishi tsiyar cewa kar ya bada maza fa in dan in yace haka zaiyi to kafin aure zai zama mijin tace,
tun Meenal na nokewa dan dole ta gaji ta sake jiki saboda yanda yake nuna damuwa da kulawar shi mad’aukaki akanta, motsi kad’an zatayi ya fara tambayar ta miya faru?
Haka ya dunga riritata irin riritawar da bata tab’a tunanin samun kwatan kwacin shi a tareda shiba,
duk da hakan ya matuk’ar faranta ran Hajiya amma sai bata nuna ba sai ma kushe su data dungayi akan in basu kama kansu ba dukan su zata kora subar mata gidan da dare yayi shida kanshi ya fita bayan ya tambaye su abinda suke son ci yaje ya siyo ya dawo suka zauna su ukun suka ci karfen 10 na dare Hajiya ta raka Meenal har d’aki saida ta tabbatar da cewa Meenal din ta rufe k’ofar ta da key kafin itama ta shige nata d’akin.

washe gari ma bai fita ba yana manne da Meenal d’in har su Meelat Maryam Sultana da kuma Maimoon suka iso gidan domin koda Moon ta iso can gidan su Meelat ta sauka abunta acewar ta ko zata koma gidan Hajiya sai sun gama biki.

“Hajiya nayi ma su kabir magana gobe zasu gyara sashen saukar bak’in gidan nan dan anan gidan nike son mu sauke bak’in mu tunda muna da isasshen masauki basai mun kaisu Hotel ba dan haka ki shiga ki duba abubuwan da ake buk’ata wanda babu a sashen sai a siyo a saka,
Abincin da za’aci kuma har a gama taron bikin kowa ya watse munyi magana da Hajiya Yar ba’u itace zata dunga girkawa,”

“To kayi kyan kai kam dan dama nima naso inyi maka magana Allah yasa dai agama taron lafiya, kunyi magana da iyayen ka sun fada maka ranar da zasu iso kuwa?”

“Ba muyi magana dasu ba” ya bata amsa,

Tunda Meenal taji kukan motar ta tasan Sultana ce ta dawo gidan, dan ta fada musu cewa AK ya hanata fita ko ina gashi kuma gobe ne zasu gabatar da event din su wanda suka shirya gabatar dashi a makaranta dan haka tasan dole dama zasu biyo ta,
Sai dai ga mamakin ta koda suka shigo sai taga harda Moon a cikin tawagar nasu,
da gudu Sultana da Moon suka kwaso ita Sultanan Hajiya ta nufa tana fad’in tayi kewarta ita ko Moon wajen Meenal ta nufa Ak yana ganin hakan yayi saurin shiga tsakanin su ya maida Meenal din bayan shi yana d’aure fuska,

“Ke miye haka kukeyi daga shigowar ki zaki kwaso gudu kice wani zaki rungume ta? Bakiga kin fita girman jiki bane ko salon dukan ku ku fad’i kujama mutane aiki?”
Ak manya shifa ba komai yasa ya shiga tsakanin nasu ba sai kishi, tayama zai yarda yana zaune yana kallo ita moon din kawai ta wani kwaso gudu tace zata rungume mishi mata, ah ah fa sam ba wannan maganar kuma itama Meenal zaija mata layi ne da yanda yaga sunayi,
Karma Sultana taji labari dan ya lura da yarinyar nan shegen son jiki gareta ko zama zatayi saita jingina ko ta kwanta a jikin Meenal din duk ta sakar mata nauyin ta shifa bazai yarda da hakan ba, abu indai nashi ne yafi so yaci gaba da zama a matsayin nashin kawai.

“Kai Yaya dan Allah mun dade fa bamuga juna ba ai kaima kasan dole in so rungumar ta kodan inji dumin jikin bloody na a nawa jikin,”

“Aiko bazaki jishi ba, dallah can nemi wajen zama ki zauna ku kun girma amma har yanzun kun kasa dena behaving irin na yara,”

Tura baki tayi ta mik’a hannun ta ta kamo na Meenal wacce take mik’o mata,

“Ke yar nan ke kuma daga ina kika fad’o nike ganin ki daga sama babu labari?”
Hajiya ta tambaya tana bin Moon din da kallon mamaki,

“Daga Lagos mana zuwa Zaria, kuma dan zanzo ai bai zama dole sai na kira na fad’a miki ba, kuma ni biki nazo shi yasa ma ban sauka anan ba na sauka acan”

“Ikon allah ita uwar taki itace duk ta kitsa miki hakan kafin ki baro garin naku? Wato har ankai matakin da zaki shigo garin nan amma ki kasa sauka a gidan nan sai dai ki sauka acan wani gidan da baki had’a uwar komai dasu ba koh to ko kinki ko kinso nidai nice dolen ki dan ubanki, babu dangin iya balle na baba kinje gidan mutane kin tare to uwar me kikazo yimin anan d’in tunda nidai ai ban tura miki katin gayyata ba, yara iyayen ku sun barku a gaban su sunki su aurar daku nidai wallahi in ma bakin jini ke gareki ba a wajena kika d’auko ba sai dai can gefen uwar ki, kuma insha Allah su iyayen naki zasu iso su sameni basu barin garin nan sai sun tsaida zancen auren ki da koma waye inba haka ni dasu ne”

“To wai Hajiya ni ce miki nayi na shirya auren a yanzun ne?”

“Aikin banza dama waye zai tsaya biye miki? Wacece ke da kike zaton cewa dole sai abinda kike so za’a miki aure dai ko baki tashi ba ni na tashi aurar dake,
inba ma rashin zuciya da rashin sanin ciwon kaiba ku kenan kullum kuna siyan ankon biki kuna zuwa bikin kawaye amma ko kishin ace kuyi auren kuma bakwayi,
To gata nan dai ita naki yar uwar daga mutuwar auren ta harta samu wani mijin ke koh kina nan kullum sai k’ara girman jiki da yawan shekaru kikeyi amma shiru babu mashin shine kiji da kyau to bana na shirya tsaf babu yaro ko yarinyar da zan k’ara bari su shekara a gaban iyayen su indai sun isa aure kuma suna da halin yi sai sunyi, duk ku gama tsalle tsallen ku nice maganin ku.

*UMMIEE CE*✍🏼

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button