Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 7

Sponsored Links

7
*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*

I’m on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

***
Kukan ta ne yake karuwa Mama na tsaye a kanta, ta ja tsaki tace

“Bana son shirman banza kina ji na? Akan namiji zaki zauna kina rafka wannan kukan kamar uwarki ce ta mutu ko ubanki?”

“Mafita nake so mu samawa kanmu, saboda anga zaki huta shine aka shiga aka fita ake so ayi mana bakin ciki, idan ba haka ba, me ya kawo wadannan zantukan?”

Cikin kuka tace

“Wallahi Mama nasan Iman ce taje ta samu Gaji da maganar tunda dama ita yace yana so ai, shine dan taga wanda yazo wajen nata talaka ne shine zata min bakin ciki, toh wallahi babu wanda ya isa ya hanani auren Bashir, naji na gani kowanne hali ne dashi.”

Shiru Maman tayi tana kallon yar ta ta, idan har ta bari maganar ta sha ruwa akwai matsala, sanin cewa Zeenat din ba wani farin jini bane da ita, dama dai jamaar Iman din ne tun farko take sanin yadda zatayi, dole ta san abinda ya kamata amma duk da haka ba zata nunawa Zeenat din komai ba

” Kina jina? Ki tashi ki tafi dakin ku, ki daina wannan kukan tunda ba ubanki bane ya mutu, zan san yadda zanyi komai ya daidaita.”

Da bayan hannun ta ta goge kukan, ta fice tana rangaji, tana sake kudurewa a ranta babu gudu babu ja da baya a auren ta da Bashir din.

Tana isa daki ta tarar da missed calls din sa, ta bi kiran da sauri tana sake daidai ta kanta.

” Gani a waje.” Yace tana dagawa.

” Mu hadu a bayan layi akwai matsala karka zo gida.”

” Me ya faru?” Yace a kidime.

” Babu komai gani nan zuwa.”

Kashe wayar ta, tasan zai ta tambayar ta menene gwara kawai taje suyi magana su sama wa kansu mafita dan ba zata iya hakura dashi ba.

Ficewa tayi ta kofar kitchen bayan ta gyara fuskar ta, ta bar gidan cikin sauri tana tsoron haduwa da Ya Habib ko wani.
A chan bayan layin ta hange shi jikin motar sa, a tsaye yake yana ta jijjiga jikin sa daga gani baya cikin nutsuwar sa, tana isa ya juyo da sauri.

” Lafiya baby?” Yace yana riko hannun ta. Kuka ta saka da sauri yace

” Na shiga uku, me ya faru?”

” Abba ne yace wai na rabu da kai, wai yayi bin…”

” Shisshsh…” Yace da sauri yana dora hannun sa a saman bakin ta

” Kinsan dai hakan ba gaskiya bane ko? Sharri akayi min ko menene akace domin a hana mu aure, duk wanda ya yi min wannan sharrin na bar shi da Allah kawai.” Yace yana girgiza kansa

” Shikenan yanzu rabuwa zaki dani? Nasan rayuwata shikenan ta kare, idan har zaki iya yarda mahassada su shiga tsakanin mu, bakya so na baby, rayuwata shikenan ni.”

” Ni ban yarda da duk abinda akace ba ai, kawai sharri ne na sani, amma ya zanyi da Abba? Bayan shi din kaifi daya ne akan maganar sa.”

” Dan Allah Zeenat karki yarda a raba mu, wallahi Ina sonki , bansan ya zanyi da rayuwa ta ba idan har baki aure ni ba.”

Hawaye ya fara yi tayi saurin sa hannu ta goge masa

“Zanyi duk yadda zanyi, ba zan bari a raba mu ba…”

” Da gaske? Kinyi alkawari?”

” Nayi maka alkawari.”

” Dan Allah karki saba alkawari dan Allah, ki taimaka wa rayuwa ta, kinji?”

” Karka damu.” Tace tana jin wani karfin zuciya,

” Ba zan taba yarda su yi min abinda bana so ba, Kai nake so kuma duk yadda kake ina son ka a haka.*

“Nagode nagode baby, in sha Allah ba zakiyi dana sanin amincewa dani ba.”

Zatayi magana wayar sa tayi kara

” Sorry.” Yace mata kafin ya daga yana rage volume din wayar sosai

” Malam tun dazu nake jiran ka, ka dawo min da mota zan fita, wai ina ka tsaya ne?”

” Gani nan yanzu in sha Allah.”

Ya kashe kiran ya ce

” Baby bari naje, urgent call daga Baba, zamuyi waya kinji?”

” Tam shikenan.” Tace a sanyaye

” Yawwa ga sakon ki…” Ya bud’e murfin motar ya fiddo da ledoji, hannu tasa ta karba tayi godiya, ta juya ta soma tafiya shi kuma ya shiga motar ya tada ita da sauri ya bar wajen, yasan ba zasu kare kalou ba da ita, amma kuma hakan shine kadai zai kankaro masa mutuncin sa.

***Daki ta koma ta ajiye ledar bayan ta bud’e taga ice cream ne da Pizza, sai charger waya da yake ta lalace ta ta, sai wasu tarkachen alawoyi. Bata taba komai ba sai charger din ta jona wayarta a jiki sannan ta fice zuwa bangaren Gaji dan ta samu Iman a yi wacce za’a yi.
Iman din ce kuwa kadai a falon tana karanta hisnul muslim. Sai ganin mutum tayi a kanta, bata tanka mata ba ta sauke kanta ta cigaba da karatun ta kawai.

“Saboda kina bakin ciki kin samu fakiri talaka shine zaki kai munafurci kice Bashir bashi da hali ko?”

“Wacce irin magana ce wannan Zeenat?”

” Malama karki pretending kaman baki sani ba, idan bake kika fad’a ma Gaji wata magana akan Bashir ba waye ya samu Abba ya fad’a masa Bashir bashi da hali me kyau?”

Tashi tayi zaune tana kallon ta, ta girgiza kanta kawai kafin tace

” Kinsan bani da lokacin batawa akan irin wadannan maganganun, dan haka please bana son maganar.”

” Zaki ce bakya so mana kina min bakin ciki, toh wallahi sai dai ki mutu da bakin ciki amma aure na dashi babu fashi, kije chan kiji da wanda zaki aura, mutum kamar shi ya kawo talauci duniya.”

Tashi kawai tayi ta bar falon zuwa bedroom din Gaji dan ba zata iya irin wannan shirmen na Zeenat ba, sai dai da gaske maganar ta taba ta, har taji ta rasa gaba daya walwala da farin cikin ta, kwanciya kawai tayi ta rufe idon ta tana hasaso rayuwar ta nan gaba!

***Cikin shigar Khaki pants da wata jibgegiyar rigar sanyi da ya saka a saman armless rigar sa ya fito, kansa da yake a kwance yasha gyara ya tsaya yana sake dubawa a katon mudubin da yake ajiye a falon, yasan Takawa zai saurare shi ya kuma bi abinda yake so sai dai baya son ko kad’an karya ko wasa ya shigo a cikin maganar auren sa. Kallon kafar sa yayi, sai ya koma ya sauya takalmin zuwa wani daban sannan ya fice yana tura hannun sa cikin aljihun dogon wandon nasa.
Suna tsaye k’yam suna jiran fitowar sa, kowanne su cikin shigar da take nuna shi din waye, bud’e masa motar akayi da sauri ya fad’a yana makala bakin glass din sa yasan yau zai same shi a wajen hutawar sa, in da ya dace da maganar da zasu tattauna, shiyasa ma yayi shigar sa da yasan Takawan bazai masa surutu ba, dan ya riga ya san shi, ko yace kowa ya san shi da tsanar manyan kaya musamman a lokacin zafi sai yace wai takura masa suke.
Da yake sun san in da zasu, kai tsaye suka wuce dashi Family house din, in da Takawan ke hutawa a duk ranaku irin wannan ba tare da shigowar wani shaani na mulki ba. Iyakar abinda ya shafi kansa da iyalin sa kawai yake tattaunawa a rana cikin saukakakkiyat shiga da ba zaka taba cewa sarki bane duba da ko yaushe yana nannade cikin rawani da manyan kaya.
A kofar wajen motocin nasa suka tsaya, ya balle murfin tare da me bud’e masa ya fito yana kallon ko ina na harabar gidan. Kansa sanye da hular sanyi ya cire glass din idon sa ya shiga takawa zuwa ciki. Gaisuwar da ya tsana ya dinga kokarin kaucewa har ya dangana da inda takawan yake ya hange shi a zaune a cikin wajen yayi matashi da pillow yana kallon yadda yan yaran da suka kasance jikokin sa ke wasa a wajen.
Sarkin dogarai ne ya fara ganin shi,ya washe cikin farin cikin ganin shi yace

“Maraba da Yarima!”

“Sarkin dogarai…”

Muryar sa ta saka takawa d’agowa, ya gyara daga gishingid’ar da yayi, ya fad’ad’a fara’ar fuskar sa da tayi ma Moh iso har gaban kakan nasa. Russunawa yayi cikin girmamawa ya kai gaisuwa, hannu ya mik’a masa ya matso kusa dashi sosai, ya shafi saman kansa

” Sai yau kaga damar leko ni ko Muhammadu?”

” Tuba nake Takawa, ayyukan ne suka yi min yawa.”

” Toh madallah, naji kace kana son gani na, toh gani ya akayi?”

” Dama magana ce akan abinda Bubu yayi maka magana.”

” Auren ka? Jairi toh sai akayi yaya?”

Dariya ya saka sosai

” Toh kunce sai nayi aure yanzu kuma nazo da maganar kuma, sai na fasa auren ma gaba daya.”

” Fasa mana, waya yayi asara? Kaji dan nema.”

Dariya suka saka a tare, kafin Takawa yace

” Toh sai ka fadi a inda yarinyar take ko? Idan yaso sai a nemi iyayenta.”

” A ah ni dai Takawa, ayi min aikin gafara a bari a samu wasu suje su nema min auren ta.”

” Wasu?” Yace yana kallon sa

” Eh a dangi haka ba, ba manya sosai ba, Ina nufin ba cikin manyan masarauta ba, yan chan kasa kasan dai.”

” A wanne dalili?”

” Kawai ni bana so suji tsoro su ga kamar mun fi karfin su.”

Girgiza kai Takawa yayi

” A neman aure babu boye boye Muhammadu, a sak dinka zaka je, kai ne fa jika na farko a gidan nan, sannan a wajen mahaifin ka, wanne irin tunani ne haka ya shiga kanka?”

Sosa kai Moh yayi yana marairaice fuska

“Ni dai dan Allah takawa, a bar wasu suje.”

“Sam sam kaima kasan hakan ba mai yiwuwa bane, dole ne su san kai din daga gidan da ka fito.”

Shiru yayi yana jin kamar ya daure kansa da ya budewa Takawa zuciyar sa, yasan shi sarai da tsayawa akan ra’ayin farko, amma yayi tunani zai fuskance shi duba da irin son da yake masa, dama Musaddik ya gaya masa, babu me yarda da shirmen sa kamar yadda yake jaddada masa a kullum, babu me biye masa ko bashi goyon baya. Tun daga lokacin yasan sarai babu me tsayawa ya saurare shi, balle ya yarda da tsarin sa. Ammin sa ce kadai itama bata ja da maganar Takawa, ballantana Bubu da baya iya aiwatar da komai sai abinda Takawa din yace.

“Kana jina Muhammadu, maganar da kazo da ita bata kamawa bace. A tsari na gidan nan ma zamu iya aika musu suzo nan din domin muna da damar bada diyar tasu, sai dai ba zamuyi haka ba, zamu basu girman su da darajar su in Sha Allah, za kuma musu duk abinda Muhammad yake so amma banda shiririta.”

Ya karashe yana murmushi, murnushin shima yayi kawai ba tare da yace komai ba. Suka cigaba da hira irin wadda suka saba har be san iya adadin awoyin da ya bata ba, sai da suka ci abinci da Takawar sannan ya lallaba ya shiga gidan ya gaida matan gidan ya kare a dakin kakarsa ya tarar da yan matan family din sunzo suna da wani get-together da suka shirya sannan suyi maganar tsari bikin Abidah guda daga cikin jikokin gidan.
A kaidar sa baya sakar musu fuska ko kad’an domin suna da rainin hankali sosai, duk da shi basa yi masa neman ma ya kula su suke amma shi sam baya tsayawa shirmen su, da gaske suka shakkar shiga shirgin sa hakan yasa yana shigowa shashen suka dinga yayewa da d’aya d’aya.
Dan tsiririn tsaki yaja sanda suka gama ficewa ya zauna yana muzurai a dole baya son raini shi. Mutane da yawa na fad’a masa yadda yake abubuwan sa kadai ya tabbatar da shi din jini ne na sarauta amma shi sam be san ma yana yi ba ma.
Ya dan jima a wajen nata kafin ya tafi yana jin zai dan dade kafin ya sake waiwayo su duba da tafiyar dake gaban sa akan aikin sa.

***Yana zaune a gate din gidan yana dakon shigowar Abba Babban, a kan idon sa ya dawo ya tashi da sauri ya tare shi ya bud’e masa kofar mota.

“Sannu da zuwa Abba.”

“Yawwa Ibrahim, kaine yau a gate din kenan.”

” Wallahi kuwa Abba, sannu da dawowa, ya aiki?”

” Alhamdulillah mun gode Allah, ya naka aikin?”

” Alhamdulillah.” Yace yana tuna abinda ya faru dashi.

” Allah ya taimaka ya bada sa’a.”

” Amin Abba.” Yace yana bin sa rik’e da jakar sa a baya.

” Mika jakar ciki bari na fara gano Gaji.”

Yace yana bin hanyar da zata kaishi bangaren Gajin, da sauri Khalil din ya kai masa jakar ya dawo ya zauna yana jiran ya fito. Ya dan jima a wajen Gajin kafin ya fito sai dai ganin Khalil ya saka shi mamaki, abunka da Babba nan da nan ya gane akwai wani abu.

” Ya akayi Khalil? Kana son gani na ne?”

” Eh Abba.” Yace yana sosa kansa

” Haba ko da naji, toh zan turo a kiraka kaji?”

” Toh Abba Nagode.” Girgiza kai Abban yayi ya wuce bangaren sa. Maimakon ya koma gida sai yayi zaman sa anan yana jiran kiran Abban. Yana zaune kuwa yaga fitowar Sadik ya tashi da sauri ya tare shi

“Yawwa wai kazo in ji Abba.”

Rik’e hannun sa yayi suka koma yana jin wani iri a ransa, bakin sa dauke da addu’a ya shiga falon ya tarar Abban ya chanja kaya yana zaune da alama abinci ya gama ci. A chan gefe ya zauna yana jin kunya.

“Yawwa ina jin ka Ibrahim, ya akayi?”

Shiru yayi yana tsara yadda ya kamata ya ce, sai da ya dau sakanni yana hado maganar kafin yace

“Dama Abba akan maganar Fatima ne.”

“Uhum ina jinka. Ya akayi?”

“Dama… Dama so nake dama a bani dama kamar yadda tsarin gidan nan yake.”

Murmushi Abba yayi cikin jin dadi yace

“Masha ALLAH naji dadin wannan abu matuka, Allah ya tabbatar mana da alkhairi kaji? Allah yayi muku albarka.”

” Amin Abba.” Yace a ciki-ciki farin ciki na kamashi,

” Kaje ku daidaita idan Allah yayi mu haka muke so, an riga an zama daya ai in sha Allah babu wata matsala.”

” Nagode Sosai Abba, Allah ya kara girma.”

” Amin.” Yace yana chanja tasha a tv, shiru Khalil din yayi kafin ya mike

” A huta lafiya Abba.”

” Yawwa Ibrahim.”

Yana fita ya daka tsalle a wajen yace

“Yes!!”

Da sauri ya bar wajen yana jin kamar ya same ta ya gama ne, zai nuna wa fakirin saurayin ta cewa dan gida yafi bare.

***Sabon yadi ne me saukin kudi sosai, dinkin ma irin dan 1500 din nan ne, a rayuwar sa be taba hasashen saka ire-iren kayan da yake sakawa a yanzu ba, wani kallo Musaddik yake masa yana jin kamar ya kamashi yayi ta bugu.

“Yanzu Moh irin kayan da zaka saka kenan zaka ganin sirikin ka?”

“Wait and see.” Yace yana kawo wata leda a kusa dashi, ya wurga masa yana cigaba da kallon kansa a mudubi

“Ka chanja mu tafi idan yaso muyi sallar magriba a hanya sai mu karasa.”

“Na saka me?” Musaddik yace da sauri yana bud’e ledar.

“Wait what! Kana nufin ni zan saka wannan kayan.”

“Mu nawa ne a dakin nan?”

“You must be kidding me, haba haba an fad’a ma kowa ma irin ka ne.”

“Allah su zaka saka mu tafi, kayi sauri karka batan lokaci I’m dying to see my love.”

“Aiko sai dai ka tafi kai kadai wannan karyar ba dani ba.”

“Da wa toh? Wa nake dashi bayan kai? Kasan da ace ban samu kanta ba dole kaima ka tattaro ka dawo sabon shagon nan dana zauna mu zauna tare. Allah dai ya taimake ka wallahi.”

” Ai wallahi babu yarinyar da ta isa nayi mata irin wannan son, the whole you, Captain Muhammad Ahmad Santuraki, dan ga sarki jikin sarki sannan kuma babban soja, ko da yake fa dama ance ku sojoji baku iya soyayya ba, musamman idan allurar ku ta motsa.”

Daina abinda yake yayi ya matso kusa dashi

” Idan bansa an saka min kai frog jump ba, kace ba suna na Muhammad ba.”

Dariya maganar ta bawa Musaddik,

” Ni zaka saka frog jump?”

” Sosai, ka cigaba da batan lokaci kaga.”

Tashi Musaddik yayi ya sake daga kayan, kafin ya fara sawa yana cigaba da mita.

” Kanka akeji wallahi.” Moh yace yana cire agogon hannun sa.

” Ka cire watch dinka please, anything da zai sa ta zama suspicious, I don’t care idan kowa na gidan su yasan ni waye, amma ita? Da marikiyarta will be the last da zasu sani, surprise ne me kyau nake son basu dukka, sai dai kowanne da yadda surprise din zai zo masa.”

” Wicked soul.” Musaddik yace yana jefar ta watch dinsa akan mirrow

” What ever!” Yace yana yin gaba yabi bayan sa yana jin dadin kayan jikin sa, babu nauyi shawai shawai amma kuma ba zai yarda Moh din yasan ya ji dadin kayan ba.

A daidai shagon aka daajiye su, yace su je chan in da suka saba jiran sa su jirashi zai kirasu. Duk da basu so ba amma haka suka tafi suka barsu, Musaddik ya dinga jan tsaki suna tafiya a k’asa har suka isa kofar gidan. Wayar sa ya ciro ya kira ta, tayi ta ringing bata daga ba,

” Bata daga ba.”

” Da ka kirata tun kafin muzo ai.”

” Wannan ba matsala bace, bari kaga.”

Ya kwankwasa gate din kafin ya dan tura shi suka shiga, dai-dai lokacin Khalil ya taho zai fita sukayi kichibis, wani kallo ya bisu dashi irin na sama da k’asan nan, kafin ya tuntsure da dariya sosai, hakan yayi bala’in bata ran Musaddik da dama chan baya daukar nonsense.

” Malam lafiya zaka kalle mu kayi dariya?”

” Lafiyar kenan, sai dai kun makara, dan gida ya shiga ya fita ya gama tabbatar da komai akansa, sai abi wani sarkin dan an riga an gama magana kuma su din ba kananan mutane bane da zasu sauya maganar su.”

” Kana nufin?” Musaddik yace a zafafe

” Ina nufin kamar yadda na fada mishi ne a baya, Iman matata ce an riga an gama magana rana kawai ake jira a saka mana.”

Wani kallo Moh yayi masa da ya saka Khalil shan jinin jikin sa, amma sai ya dake ya cigaba da gaggayawa musu magana. Muhammad be ce komai ba har ya gama, ya juya ya fice ya barsu a tsaye kamar mutum mutumi.

” I have no option than to show him my real identify, idan yaso duk abinda ya biyo baya yayi kuka da kansa ba da kowa ba, karfe nawa ne appointment dinsa?”

” Da safe ne, goma kamar.”

” Owk Allah ya kaimu.”

” Amin.” Musaddik ya amsa ransa na sake baci akan abinda Khalil din yayi musu

HALIN GIRMA

Hafsat Rano

WAIWAYE……ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau’in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI…..yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI’AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR…ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .

___________

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button