Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 8

Sponsored Links

08
*zafafa biyar na kudine,tuntubi wadan nan numbers din don samun naki copy din ki karanta cikin aminci*

08184017082
Ko
09134848107

*_follow us @ instagram_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1h9y2qgfg67x5&utm_content=nj79azb

Or facebook
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

___________________________

Dan kwantar da kujarar yayi kana ya miqe sosai Samanta yana jin yadda gajiya take bin jikinsa,don gaba daya wunin yau bai shirya fita ba,ya shirya zama ya huta sosai a gida,saboda satin gaba daya cikin aiki ya yisu,babu dare babu raba,har inda ma a tsarinsa babu schedule na zuwansa sai daya ratso masa a sannan din.

hannayensa saman kansa yayin da idanuwansa suke a rufe,yayi nisa a tunaninsa sosai,busy busy ne dashi irin wanda mutane da yawa ke mamakinsa,sam bai bawa kansa hutu ba.

a qalla ya kusa minti ashirin a zaune a haka,wanda hakanan yaji zaman yayi masa dadi,ko ba komai ya dan samu break na wasu mintuna.

Dan waiwayawa yayi gefansa,a sannan ya hango tahowar professor shi da wasu mutane hudu,saiya miqe ya gyara zamansa,ya kuma kunna motar yana jiran qarasowarsa.

yana jin sanda ya shiga yana sallama da mutanen,suka maida murfin motar suka rufe masa,don haka saiya tashi motar,dai dai sanda professor ya furta
“alhamdulillah”yana sauke ajiyar numfashi.

A nutse yake tuqin har suka fita daga airport din,a hankali professor rashid yace
“lawan….ko ka sake koyon sabon salon tuqi ne?”raba idanu samir yayi hagunsa da damansa,saiya lanqwashe murya yace
“eh alhaji”dan jim professor yayi sannan yace
“to yayi kyau”daga haka bai sake cewa komai ba,zaman shuru yaci gaba da ratsawa a tsakaninsu.

“Daka sani ai baka wahalar da kanka ba samir…..”yaji abban nashi ya fada bayan tsahon wani lokaci,ya ganeshi kenan,qyaleshi yayi kamar bai gane ba,qaramin murmushi ya subuce a kuncinsa,jerarrun fararen haqoransa suka bayyan,har yayi kamar bazaice komai ba sai kuma ya tanka
“yau daya dai abba….ai nima na samu ladan yau din”wayar hannunsa professor ya ajjiye,ya tsurawa gaban motar idanu,kamar anan fuskar samir din take,baisan me yasa a kullum shi da tilon dan nasa komai nasu yasha banban ba,komai nasu ba iri daya bane,abinda yake sam ba cikin tsari da burinsa ba,ya jima da sanin cewa ba haka yakeso ya kasance ba,ba haka tsarinsa yaso ya zama ba,to amma duk ta inda yake tunanin zai gyarota babu wani sauran dama data rage masa,don haka a maimakon yayi magana,saiya buge da hade yatsunsa waje daya,yana maida tunaninsa wani waje daban.

Duk sanda yayi tafiya irin wannan ya dawo iyalansa dama ma’aikatan gidan kan cika da murna,kamar yanzun,da samir ke biye dashi dauke da wata qawatacciyar qaramar jaka mai zubin akwati,yana biye da professor har zuwa cikin qawataccen falon gidan,mai yalwa da kuma burgewa,wanda ya wadata da dukkan wani nau’in kayan alatun rayuwa.

mutum uku ne ke dakonsa zaune cikin falon,biyu daga cikinsun matasan yammata ne,daya tafi daya tsaho da haske,kamar yadda daya tafi daya shekaru da basu wani taka kara sun karya ba,don dukkansu ba zasu gaza shekara sha tara da ashirin ba.

Daga wata kujera kuma mai mazaunin mutum biyu,macace xaune itama wadda ta mallaki shekaru ɗai ɗai har shekara hamsin,saidai idan har kai mai kallo xa’a qyaleka kayi mata ƙiyasin shekaru,to ba shakka zaka ce dauka cewa bata wuce shekara talatin da biyar ba.

Tun a kallon farko xaka bata sunan HAMSHAQIYA saboda ta cancanci sunan,fara ce sol,shekarunta sam basu boye hasken fatarta ba,tana da matsakaicin kyau wanda ya cakuda da tarin ado da qawar da take qawata kanta dashi kullum kwanan duniya,kallon farko zai gaya maka ta saba da ado ya zame mata jiki,salon irin abun nan da hausawa suke cewa WANKA YABI JIKI,tun daba hannayenta zuwa wuyanta kayan ado ne na mata,fuskarta wadace take da murmushi kamar bakinta zai yage,idanunta qur bisa saman fuskar wadan nan halittu guda biyu,wato samir da professor,tana dubansu da wani irin kallo me nauyi da zurfi.

Dukkaninsu suka miqe kowanne fuskarsa na nuna tsantsar farinciki,daya daga cikin matasan yammatan nan wadda da alama batakai shekarun daya ba ita ta tako da sauri zuwa inda professor yake
“Abba…..sannu da dawowa”ta fada da ‘yar siga ta shagwaba,da alama kuma hakan habit dinta ne,tana dora kanta saman kafadarsa,kamar marayan daya samu tallafi,murmushi ya saka yadan dora kansa saman kanta
“barka kadai auta….na sameku lafiya?”
“lafiya qalau abba,saidai munyi missing dinka”murmushin yakuma saki
“gani na dawo ai jauhar,duk wata kewa ta qare ko?”kai ta gyada,sai dayar itama ta matso,tasa hannu kadan tana gyara eye glasses dinta,fuskarta itama murmushinne kwance
“barka da zuwa abba”
“barka kadai lelen abba…..na sameku lafiya?”
“lafiya lau abba ya hanya?”
“alhmdlh,ya karatu?”saida ta saki wani ni’imtacce murmushi,tana jin wani dadi na ratsata,ta daga idanun a hankali ta maida gashi,samir…….wanda har yanzu yake tsaye a bayan abban nasu tamkar wani dogari,hannayensa zube cikin aljihun wandonsa yana kallon dukkan abinda ke faruwa, inside him yana jin tsaiwarsa a wajen cikin abubuwan da suke gundurarsa nan da nan,ya qagu duka a gama wadan nan gaishe gaishen.

dauke idanunta tayi ta maida kan abban,a duniya tana jin dadi tana alfahari abban nasu ya tambayeta karatunta,tana jin wani qwarin gwiwa yana shigarta aduk sanda ya tambayeta wani abu daya danganci karatunta,takanji burinta kwadayinta da qwarim gwiwarta yana daduwa
“alhmdlh abba….komai lafiya”
“ma sha Allah”ya fada yana maida dubansa xuwa gareta,har yanzu bata matsa daga inda take tsaye ba,amma hankalinta idanuwanta da hankalinta dukka yana kansu
“sarautar mata…….yada tsaiwa a nan?”murmushi ta saki
“to ai naga hankalinka duka yana kan yaranka,kaga gwara na barku ku gama tukunna…..barka da dawowa”
“barka kadai…..na sameku lafiya?”
“alhmdlh”ta fada taba jifansa da wani murmushin,saita tako a hankali ta raba ta gefansa,idanunta saman fuskar samir,suna hada idanu ya kauda kansa ya miqa mata jakar professor dake riqe a hannunsa,hannu ta miqa zata amsa tana cewa
“ka kyauta samir”ya fahimci abinda take nufi,saiya saki qaramin murmushi yana juyawa kadan zai fita
“ya da haka son…ka bari daddy ya kintsa muci abincin rana tare mana”ta furta cikin nuna zallar kulawa,kansa ya girgiza yana sosa kan mashi da tsinin key din mota,shida yakeson tsallakewa fadan professor,yayi imanin idan ya zauna suci abin tare zai tono laifin da shi yaketa qoqarin bunnewa ne
“akwai abubuwa da yawa dana bari,zanje na rage wasu,bazan jima yau a waje ba zan dawo gida” sanda yake maganar shima professor ya nufi hanyar da zata sadashi da sassansa da suka qunshi bedrooms manya guda biyu,da.katafaren falo guda daya
“da zaki daina wahalar da kanki wajen tsaidashi,ki barshi ya tafi kawai, saboda haka yakeso,hakan ya tsarawa kansa kamar ko yaushe” sarai samir yasan magana ce mai harshen damo yayi masa,sai data waiwayo ya kalli samir
“ohk….saika dawo,Allah ya tsare” kansa ya gyada sannan ya juya zai fice,itama ta rufawa professor baya.

“ya saraki”kiran da aka masa shine abu na biyu daya shiga kunnensa daga hirar professor da matarshi,sai yaja tunga ya tsaya sannan ya waiwayo a hankali sanda take tasowa a shagwabe ta riskeshi.

Idanuwan najwa tar bisa fuskar jawahir sanda take nufar yayan nasu,saita sanya hannunta ta cire airpiece guda daya cikin biyun dake maqale a kunneta,tana jin wani abu na tokare zuciyarta,ta tsani taga tana magana dashi sam,tana son taji yanzun me zatace da shi ne.

“ya saraki…..please,alqawarinmu fa” ajiyar zuciya yayi hade da lumshe idanu,lokaci guda kuma ya furzar da iska daga bakinsa,baice komai ba saiya cusa hannunsa cikin aljihunsa ya fiddo sabbin ‘yan dari biyar biyar masu dama ya miqa mata,wani dan tsalle ta saki bayan ta amshu kudin
“thank you so much,am proud of you my yaya”murmushi kawai ya bita dashi sannan ya taka ya fice.

kudin na hannunta tana juyasu,fuskarta a wadace da murmushi ta koma kujerar data tashi akai ta zauna,duk abun nan da ake idanun najwa a kanta,tana binta da wani kallo da zai nuna maka zallar tkaici da haushinta daya cika mata zuciya,sam jawahir batasa me take ba tana irga kudinta hankali kwance,ganin cewa da gaske jawahir batasan tana yi ba,lissafin kudinta kawai take,saita miqa hannu ta fusge kudin a tare tana furta
“banza”da qarfi,hakan yaja mata hankalin jawahir din yadda takeso,dubanta take baki bude
“me na miki ya najwa”
“banza”ta sake maimaitawa tana hararta,idanuwanta kamar zasu fado akan jawahir din
“wai me na miki?”
“ke wai.me yasa baki da zuciya,kuma baki da kishin kanki?,na meye zaki tambayesa kudi,momi ba zata baki bane da ba zaki tambayeta ba?”sosai jawahir ta bata fuska tana kallon najwan,ranta a dan bace
“amma shi da momyn ai duk daya ne ko?,kuma ko ita ai taga ina tambayarsa,kuma bata ce komai ba”baki najwa ta tabe
‘bakya ganewa,kuma ba zaki taba ganewa ba…..”
“nidai koma meye bani kudina”ta furta tana miqa mata hannu
“naqi na bayar din”najwa ta fada tana cusa kudin a gefan cinyarta,sai jawahir din ta sake gimtse fuska sosai
“kinga ki bani kudina ya najwa,ko momy tace ki daina shiga harkata ko?”
“idan kina da qarfi ki danne ni ki qwata,sarai dai kinsan babu abinda zanyi da kudin nan…..”.

A hankali ta buda qofa ta dawo ta cikin falon,idauwanta ya sauka a kansu sanda jawahir ke sake maimaita wa najwan ta bata kudinta
“lafiyanku?”momyn ta jefa musu tambayarsu,wanda banda tayi magana babu wanda yaga fitowarta cikinsu
“momy….ya saraki na tambaya kudin ankon yasmin tun rannan,to ya bani shine ya najwa ta karba ta hanani,tana masifar wai don me zan tambaya ya saraki”jawahir tayi caraf ta gaya mata,sai data tabbatar ta aikawa jawahir saqon harara sannan ta maida dubanta ga mony da nufun yin nata bayanin
“momy wai ba…..”wani kallo momyn ta aika mata,sannan ta daga hannunta kawai ba tare da tabi takan qorafin da takeso. sako.mata ba tace
“bata kudinta”fuska ta bata
“momy….”
“nace ki bata kudinta ha’an…?”ta fada da dan zafi zafi yanzun a muryarta,fuskar najwa a cunkuse,ta zaro kudin ta jefawa jawahir,ya fada saman cinyarta,bata damu ba ta dauki kudinta taci gaba da irgawa,momyn ta kalleta
“ajjiye kudin nan kizo kitchen ki hadama daddynku drink”
“to momy”ta amsa mata tana miqewa da kudinta a hannu tabi bayanta,yayin da najwa ta bita da harara,tana jin kamar ta shaqeta,saita gyara glass din fuskarta,ta kuma gyara zaman qaton littafin dake ken cinyarta taci gaba da dubawa,can qasan ranta abubuwa da yawa na mata yawo,inda tana da qarfin iko da sai ta canza abubuwa da dama cikin gidan nasu,abubuwa masu tarin yawa da basuyi rayuwarta yadda takeso ba,basu zauna kuma a gurbi da muhallin da takeson ganinsu ba.

*_9:30 am_*

*_DARMANAWA HOUSING ESTATE_*

*_PROFESSOR RASHID USMAN AZARE RESIDENT_*

Daya ne daga cikin jerin qawatattun gidaje dake gine cikin unguwar,,wanda suka qawatu aka kuma ginasu bisa basira da kuma kyakkyawan tsari.

Gini ne na alfarma mai cike da qayatarwa da ban sha’awa,kamar yadda akasan ire iren gidajen masu sukuni suke da kuma unguwaninsu.

A hankali momy ta daga kanta,fuskarta na fidda wani irin murmushi mai haske tunda ta jiyo sautin muryarsa,tun gabanin ma ya iso inda suke din,yayin da ta tsaida dukkan abinda takeyi,ciki harda cin abincinta,da kuma hira da take da ‘yammatan dake gefanta su uku,najwa jawahir da kuma ramla da take ‘yar ruqo a wajenta.

Dukkaninsu sunsan meye ta baiwa hankalinta haka gaba daya,ba wacce bata saba da ganin tarin kulawa da qauna daga gareta ba zuwa ga samir,wadda ta banbamta da ta kowanne da dake cikin gidan.

Kallo daya professor yayi mata yaci gaba da cin abincinsa a nutse,don shi din ma hakan ba baqon al’amari bane a wajensa,illa dai ya kada kansa sannan ya maida hankalinsa ga farantin gabansa.

Cikin sakanni da basu kai goma ba ya bayyana cikin falon dab dasu,matashin saurayi muhammad samir me laqabin saraki,ma’abocin tsaho,wanda murjewar jikinsa ta hana bayyanuwar tsayin da Allah yayi masa yadda za’a fahimta,ya mallaki kalar fatar da hausawa suke kira da wankan tarwada amma irin wankan tarwadan nan dake da haske,taqi kadan zai dada ka kirayeshi da farar fata,matsakaicin kyau gareshi,saidai abubuwa guda biyu sun taru sun qarawa siffarsa kyau da cikar haiba KWARJINI da yake dashi,da kuma wasu lumsassun idanuwa masu kama da na me jin bacci.

Yana da sanyin murya,irin sanyin da bai hana bayyanar cikar mazantakarsa gami da jarumtarsa ba,sam ba miskili bane,kamar yadda wasu mutane da yawa suke masa kallon haka,abubuwa ne guda biyu suka sanya suke masa wannan kallon,baya shiga sabgar da bata shafeshi ba,bashi da shishshigi sam,hakanan bai fiya magana kan abinda yasan yana da qarancin muhimmanci,koma kwata kwata bashi da muhimmancin,yana da kamewa da wata irin nutsuwa mai jan hankali,yana da zurfin ciki a yawancin lokuta,komai nasa bisa tsari da dacewa yake tafiya,shi yasa wasu ke ganin abune mai wuyar gaske iya zama dashi,abunda basu sani ba shine,zama dashi din wani abune mai dadi ga duk wanda ya soma mu’amala dashi.

Akwai boyayyun halayyensa da ba kowanne ya sanshi dasu ba,ciki kuwa harda makusantansa,yana da tausayi yana da taimako,a wasu abubuwan ba zaka taba tsammanin cewa ya fito daga gidan girma da arziqi irin wannan ba,rayuwa sassauqa da yakan gudanar….saidai,matuqar kazo lokacin da yake kan tsininsa,zaka dauka baida kirki ko kadan.

Muhammad samir,da namiji guda daya tilo da Allah ya mallakawa professor rashid usman azare,wanda tarin banbamce babancen halaye da zabi na rayuwa yaso ya zama babban shinge tsakaninsa da mahaifinsa da samun dukkan wata yarda da qauna tashi.

“welcome son…..na tsammaci yau ba zaka fita ba?,naji shurun yayi yawa,duk da na kira wayarka taqi shiga….saina zabi na barka ba tare dana aika ba,wala’alla kana bacci ne kada a katse maka shi” hajiya jidda wadda auke kira da mommy ta fada,dukkan kulawarta tana tare da samir din,fuskarta na fidda wani kalar murmushi dake nuna farincikin dake tattare da ita na ganin fitowar samir din,kamar yaune lokaci na farko data fara ganinsa,ko kuma wani gari yayi tafiya mai nisan zango ya dawo a yau din.

Washewa fuskarsa tayi da wani murmushi mai aji,ya soma qoqarin jan kujera daya don yiwa kansa mazauni sannan ya amsa mata
“A’ah anna….bani da wani abu da zan aiwatar ne da safen….shi yasa na zabi na huta kafin na fita yau,don jiya ban samu zama yadda naso ba” ya qarashe maganar yana duqawa zuwa qasa gefan mahaifinsa,muryarsa cike da tsantsar ladabi ya furta
“Barka da asuba daddy” kallo daya yayi masa ya maida kansa ga abincinsa yana amsa masa da
“Ka tashi lafiya?”
“Lafiya alhmdlh” sai ya maida dubansa ga mommy wato hajiya jidda
“Barka da asuba mommy”
“Barka kadai yarona….da fatan ka tashi lafiya”
“lafiya qalau alhdmdlh”
“To ma sha Allah” ta amsa masa fuskarta na nuna jin dadin samunsa lafiya da tayi kamar kullum,saita miqe da kanta ta fara bude dukkan wani kwano dake saman teburin sanda qannensa ke gaisheshi daya bayan daya yana amsa musu,kamar yadda ta saba tanayi kullum kwanan duniya matuqar ya halarci wajen cin abinci,zata bude masa dukka ya zaba abinda yakeson ci,don wani lokaci ma abinda ya zaba yana so shi za’a dafa kowa da kowa,koda ba zabinka kenan ba,tun suna yiwa mommy mita da qorafi har ya zame musu jiki.
“Me zakaci a ciki samir?,Allah yasa akwai wanda ya dace da ra’ayinka” mommy ta fada tana murmushi kamar kullum,wanda baka rabata dashi saman fuskarta,sai a sannan alhj mukhtar yayi magana tun fitowar samir din,idanuwansa saman fuskar mommy,wani abu na yawo saman zuciyarsa,wani abu mai nauyin daya wuce a aunashi a mizani
“Ki kalleshi mana da kyau,ba yau ko jiya ko shekaran jiya aka haifeshi ba,amma kullum kina kallonshi ne kamar ranar nan da aka miqo miki shi cikin tsumman goyo,a qa’ida ya isa aure,a kuma qa’idance kamata yayi ace a gaban matarsa yake” kanta ta langabe tana duban professor
“Haba daddy…..kai kake ma samir kallon yayi girma har haka,ni kam a wajena har yanzu kamar yaron goye nake kallonsa…..bugu da qari ma daddy idan ba’a kula da samir ba…wa zamu kula dashi?,karka manta shi kadai Allah ya bamu….”
“Abbaaaa”sautin muryar jawahir tayi kutse cikin maganar mummy,sautin daya fito a narke,kamar me shirin sakin kuka,waiwayawa suka dukka suna kallonta,sai daddyn ya daga hannayensa duka biyun kafin yace
“You see…..su kuma daughters dina ki kaisu ina?” Murmushi ya saki,wani abu na lilo can qasan ranta da zuciyarta
“Dole dukkaninsu subi bayan samir a wajena” a nutse tsaf daddyn ya waiwaya ya dubi samir din sosai kuma kai tsaye,duk da idanun samir din na kai kawo ne tsakanin yan uwansa,fuskarsa tana fitar da wani murmushi me sanyi mai kuma cike da nutsuwa
“Gwara da kika ce a wajenki,ta ina yaronkin zai kama qafar yarana?,yaron naki da ba jin magana yake ba,wanda ya sarayar da alqiblarsa,babu wanda ya gane har yau inda yasa gaba” samir ya gama fahimtar qorafinsa na jiya da yaketa gujewa shi yakeson sokowa a yau din,saiya dan sunkui da kansa,kana ya daga kan nasa,yana muradun rushe wannan maganar,don baida sha’awar ci gaba da yinta,don haka cikin girmamawa yace da ita
“Kome akayi yau din zanci mommy,ki zauna ki huta….zan zuba da kaina,ina sauri ne ma,jiya akwai taron da zanyi da ma’aikata,ban samu zama ba nasa aka maidashi yau”ya fada yana miqa hannu zai hada tea.

jawahir ce ta miqe da hanzari ya dauka cup din ta soma hada masa,mummy tadan kalleta saita dauke kanta
“yi a hankali sarkin rawar kai,kada ki zuba masa a jiki”mummyn ta fadi sanda jawahir ke aje masa tea din,murmushi yayi ya dauka yana.kaiwa bakinsa,shi yasa yakeson autar tasu,sosai take nuna kumawa kan dukkan wani abu daya shefeshi,ba kamar ‘yar uwarta ba,wadda har yanzu bai fuskanci inda ta sanya gaba ba,shegen sin jiki gayunbanza,izgili da yiwa.mutane kallon banza hadi da rashi iya magana dukka najwa ta hadasu,abu daya da yasa bata iya wani kyakkyawan abu a gabansa ko a kansa shine,baya daukar raini,kamar yadda baya raina kowa,tafi kowa sanin ainihin wayeshi,wannan shine ya ke mata waigi a kansa.

miqewa prof yayi yana yagar tissue
“idan ka dawo yau din bayan sallar isha’i,ka sameni zamuyi magana dakai”
“ok daddy”ya fada da muryarsa mai dadi,sannan yaci gaba da kurbar tea din a nutse.

cup din ya ajjiye bayan ya gama amsa wata waya,mummy ta dubeshi
“bakaci komai bafa samir?”
“mommy,am late”
“a maka packaging ka tafi dashi mana,ya zaka fita aiki babu cikakken abinci a cikinka”
“ba komai mommy,zan nemi wani abun naci idan na samu break”
“a’ah..,.najwa……maza,shiga kitchen ki cewa baraka ta baki warmers qanana”fuska tadan bata
“Mommy…..yace a barshi fa”idanu ta fitar mata gaba daya
“ni kuma nace ki dauko…..”tuni ta miqe ma kafin mummyn ta qarasa bayani,saboda wani kallo da samir din ya jefeta dashi,harta soma takawa tajishi yana fadin
“dawo ki zauna,jawahir…..jeki dauko,guda daya ma is ok”taf tsoro ya cika cikinta,saboda ba kasafai yake bi takanta ba,tana tsoron irin wannan kallon nasa,saita ci gaba da tafiya ta miqe zuwa kitchen din,wata tsawa ya watsa.mata wadda ta sanyata tsaiwa,ta kuma kasa juyowa,har jawahir tazo ta wuceta da saurinta kuwa kamar yadda ya umarceta

bata motsa ba har sai dataji fitarsa yana cewa idan an zuba jawahir din ta miqa masa yana cikin mota.

koda ta koma harara Mommy ta bita da ita,sannan ta rufeta da fada,tana kallon fuskar jawahir,da alama taji dadin yadda mummyn ta balbaleta da fadan,sai tayi sakato,mamaki fal ranta,me yasa mummy ke mata fada da zafi har haka?,bata tanka ba har jawahir ta fice daga parlour din,saita dauki jakarta dake gefe wanda dama shirin makaranta tayi,kawai ta fice a falon.

yana daga zaune a driver seat ta buda gidan baya ta sanya warmer din sannan ta rufe,saita zagayo inda yake zaune din,fuskarta da murmushi
“a dawo lafya yaya”
“Allah yasa”ya amsa yana shirin rufe murfin motar,saidai jawahir din bata matsa ba tana tsaye still a wajen,kansa ya daga bayan ya sauke glass din motar yana dubanta
“ya akayi auta?”murmushi ta sakeyi
“kayi haquri yaya da abinda ya najwa keyi….ni kaina bansan meya canza ba”qawataccen murmushin gefan baki ya saki
“karki damu, she’s still my sister…..ina tunanin tana da damuwa,but we will talk later”kaita gyada kawai kana taja baya,ya tada motar a nutse,ya qarasa bakin gate ya danna horn,idanunsa saman fuskar mai gadinsu da yaketa marmashe gyada yana zubawa cikin jiqaqqen garin kwaki,ya taso da hanzari ya durfafi qofar zai budeta,sai samir ya yafitoshi da hannu,don haka yabar bude qofar ya iskoshi da sauri ya iso bakin window inda samir ke zaune
“Allah ya taimaki saraki”
“an tashi lpy baba”
“lafiya qalau dana”
“abinda aka dafa ne yau baba bai maka ba,na ganka da garinka harda gyada?”samir ya tambayeshi yana dan murmushi,murmushin shima yayi,a ladabce yace
“ko daya mai gida,yau dai bamu samu abun karin bane”fuskarsa cike taf da mamaki bayan yadan yamutsata yace
“kamar yaya?,kune baku da sha’awar ci?”da sauri ya girgiza kai
“ko daya,Allah ya taimakeka wazaiqi abinci irin na gidan professor?,inajin dai yau da gobe ne irin ta bahaushe,wani lokaci ku samu,wani lokacin kuma saidai kowa ya siya abinda yake dashi”baice komai ba saiya duba agogon hannunsa,bashi da lokaci da cikin gidan zai koma,bai zaci wasu cikin gida dake rayuwa tare dasu ba’a basu abinci ba,saiya bude aljihun gaban motarsa ya aciro yan dubu dubu guda biyu ya miqa masa
“gashi,ka ajjiye wancan ka siya wani abun me dumi kaci”hannu bibbiyu yasa ya amsa kudin yana zabga masa godiya,sannan ya tafi qofar ya dage masa gate din,yaja motar da dan hanzari ya fice.

 

09
*zafafa biyar na kudine,tuntubi wadan nan numbers din don samun naki copy din ki karanta cikin aminci*

08184017082
Ko
09134848107

*_follow us @ instagram_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1h9y2qgfg67x5&utm_content=nj79azb

Or facebook
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

___________________________

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button