Sponsored Links
Hausa NovelsKurkukun Kaddara Hausa Novel

Kurkukun Kaddara 72

Sponsored Links

*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

قصة خائفة ومتعاطفة للسجناء💔🥺

*Daga alƙalamin Hafsat Boss Bature✍️*

Dedicated to Aunty kubra💘🌹

*Gargarɗi!!!*

_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube, ba tare da an nemi izni a wurina ba. Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!_

E72 Last free pages of Takun farko

💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫

*_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K’ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WATO DR MAMAN YUSUF LIKITAR MATA SOKOTO TANA FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE A FADIN NIGERIA DA NIGER HARMA DA WASU K’ASASHEN BAKI DAYA, KU SANI A DADE ANAYI SAI GASKIYA KUMA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI , INA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI_* 08133079957

*_munada zafafan kaya kamar haka ,_*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*Hadin amarya budurwa ko zawara*

*Hadin uwar gida Mai taken (Maida tsohuwa yarinya)*

*Maijego package (virgin gain)* 📦

*Hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji*

*Sahihin maganin sanyi na Maza Dana Mata Wanda yake fatattakar sanyi cikin Dan lokaci*

*Maganin gyaran nono Wanda zai gyara maki nononki cikin Dan lokaci komai lalacewarsa*

*Maganin hips Wanda zaisa shape dinki ya fita kiyi kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji*

*Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko kiyi kiba yar dai dai misali kema adinga binki da kallo Idan kin juya Sam rama batayi ba yar uwa*

*Hadin mallaka ba boka ba malam , akwai taimakon da muke bayarwa ga Mai butsarin namiji Wanda cikin ruwan sanyi Zaki dinga juya abunki , haka akwai Hadi na musamman Wanda komai rowar namiji sai kin samu alkhairin a wajanshi,*

*Muna da kalolin gumbuna masu Saka ni’ima sha’awa da dandano*
*Kalolin garrika mash gyara gaban mace da jimawa ajiki*
*Kalolin Zuma masu saukar da ni’ima Nan take da gamsar da maigida*
*Kalolin tsumi Wanda cikin sauki zasu Baki ni’ima da dandano irin wadda akeso*
*Kalolin matsi Wanda suke ciko da gaban mace matse gaban mace da bata Wani irin dadi da dadano*
*Akwai set kala kala Wanda yawansh ya wuce na zayyanasu anan ga Mai bukatar kayana zata iya mun magana Kai tsaye ta hanyar Kiran ko Kuma Whatsapp* 👉🏻 08133079957

*Muna dahuwar zabo ,dahuwar kaza ,dahuwar kifi ,dahuwar zuciya ,dahuwar Yan shila ,dahuwar tsoka Tara ,dahuwar Kwan mallaka, dambun nama ko na kaza Wanda yake saukar da ni’ima da jimawa sosai ajikin mace*

*Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha’awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha’awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura* 08133079957

*Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto*

💋PRISONERS💋

 

Ba ta kai ga ƙarasa cire wandon ba, sautin dariyar Batul ta janyo hankalin ta ga kallon fuskarta, tsabar mamaki ne yasa Angel ta sakar mata trouser ɗinta, ta tsaya tana kallon ikon Allah sai tiƙar dariya ta ke yi kamar ba ita bace ta ke ku ka.

“Batul bana son iya shege, menene haka? Dariyar me ki ke yi mini? Kin fara sanya mi kokwanto akan ki” ta yi maganar tana binta da kallon tuhuma yunƙurawa batul ta yi tare da miƙe wa ta zaune, Sumar kanta duk ta tarwaste har ta saman fuskarta, tana dariya ta sanya hannu tare da yaye sumar ta mayar da ita bayanta, A hankali ta ke bin fuskar Angel da kallo, ta haɗe rai har wani huci ta ke yi.

“Meyasa ki ke yi mini haka? Ko dan saboda kin ga na damu da ke ne? rai a6ace ta yi maganar, shiru batul taƙi magana sai kallonta ta ke yi,

Gyaɗa kai Angel ta yi”shikenan tunda na zama abun tsokana a wurin ki zan tashi in koma ɗaki, don’t ever expect me to worry about you anymore.”

Ƙoƙarin miƙewa ta yi da niyar ta fuce daga cikin toilet ɗin, muryar batul ce ta dakatar da ita.

“Ba za ki iya daina damuwa dani ba, that’s why ki ka sanya mini ido, ko bacci nake yi idon ki a kaina, duk wani motsi idan na yi sai kin ji ba’asin shi, irin wannan ƙauna haka……..” ta yi maganar da zolaya, hakan ba ƙaramin 6ata ran Angel yai ba.

“Nifa ba abunda ke damuna, lafiyata qalau, don kin ga ina bincikar trouser ɗina shiyasa ki ka ɗaga hankalin ki nasan me ki ke tunani nima abunda na ke tunani kenan, sai dai abun da mu ke hasashe bashi ba ne, It’s just a rash
ya fito min a wurin, ya addabe ni da ƙaiƙayi, ɗazu dana kwanta bacci, nayi mafarkin Unaizah, hankalina na ya tashi, a lokacin bansan ƙurji bane nadai ji zafi a wurin, gani nake kamar zai yi irin na unaiza, kin ji dalilin dayasa na shigo toilet ina shessheƙar ku ka tare da bincika wandona don inga menene awurin daya haddasa min jin ƙaiƙayi, ban yi tsammanin za ki biyo ni ba, amma tunkafin ki shigo naji motsin mutun nan take raina ya bani cewar Ke ce, shiyasa na ƙara sautin kukan nawa don in firgitar da ke…….” bata ƙarasa maganar ba, ta tuntsire da dariya ganin irin kallon rainin wayon da Angel ta ke Yi mata, tana a tsaye ta ruƙe qugu.

“Idan ba ki yarda da magana ta ba, zan nuna ma ki” ta yi maganar tare da sanya hannu tana ƙoƙarin zame wandon jikinta.

“Bana so ba sai na gani ba” ta faɗa tana harararta

“Idan ban nuna maki ba hankalin ki bazai kwanta dani ba, ” bata jira jin me zata ƙara ce mata ba, ta yi saurin zame wandon kaɗan ta yadda tsiraicinta bazai baiyana ba, ƙaramin ƙurjine yayi jawur dashi daga gani ba ƙaramin zafi ya ke yi mata ba, Ajiyar zuciya Angel ta sauke hankalinta har ya kwanta, gyara wandon batul ta yi ba tare da ta ɗauke idon ta daga kan fuskar Angel.

Zuƙunnawa Angel ta yi agabanta”Idan har ba ki so raina ya 6aci to ki faɗamin me aka yi maki tsawon time da Giants su ka ɗauke ki,” ganin irin kallon da batul ke yi mata ne yasa ta kuma cewa”Kada ki ce zaki 6oye mini komai batul, idan har baki so nima wata rana in 6oye maki wani abu dangane dani, ”

A tsanake ta soma magana tana kallon cikin idonta

“Angel bayan an ɗauke ni daga cikin ku, kamar yarda na faɗa maku, ɗaki ne su ka kaini ni kaɗai, a saman gadon su ka kwantar dani, bakomai zan iya tunawa ba, na dai san sun cire min kayan jiki na, sannan Naji ana shafa jikina ta ko’ina, ba tare dana iya motsawa ba, kafin daga bisani naji ana tsotse…….” bata ƙarasa ba ganin yadda Angel ta runtse idanuwanta, muryarta ƙasa ƙasa tace mata ina sauraronki ki ci gaba da magana

“Jinin da ke fitowa ta gabana shi naji ana tsotse shi”

Zuciyar Angel tuni ta soma tashi.

“Naji zafi sosai kamar zan zauce, tsawon lokaci Ana tsotse shi har zuwa time da naji bacci ya ɗauke ni, daga nan bansan me ya faru ba, lokacin da na farka banga komai ba, sai kayan abincin da aka ajiye mini Saman table, a bunda ban yarda dashi ba a cikin kayan abincin akwai wani luluyayyan abu fari fat guda ɗaya aka ajiye shi a tsakiyar tsokokin Nama…….”

Ba ta kai ƙarshen zancen nata ba, Angel ta yi saurin katse ta da cewa” Allah yasa ba ki ci ba” jin haka yasa ta haɗiyi yawu fuskarta da alamun damuwa tace”Naci Angel, yunwa nake ji sosai a lokacin, komai sai da na ci”

Angel tace”amma bayan kinci sai me ya biyo baya”?

Numfasawa Batul ta yi kafin taci gaba da cewa”bugun zuciyata ne ya ƙaru, na dinga jin faɗuwar gaba, yanzu haka da na ke yi maki magana, akwai Jan tabo saitin zuciyata, zan nuna ma ki shi idan na gama baki labarin abunda ya faru, tsawon 4 days da inayin menstruation abunda ake yi min kenan kamar na ranar farko, Bayan jinin ya ɗauke, saina samu sassauci, sai dai kewarku da ta addabe ni, damuwa ta hana ni yin walwala, haka zan zauna ni kaɗai a ɗakin ina ƙwala maku kira babu mai jina, kamar zan yi hauka Angel, tun ina kuka har na gaji na daina, Sai na koma ina yin addu’o’in da ki ka koya mana, idan na karanta su sai inji sanyi a cikin raina, har ma in shiga toilet in yi wanka, idan na fito sai in kwanta saman gadon da ke a cikin ɗakin, kullum sai an kawo min abinci amma ban ta6a ganin waɗanda su ke kawo min shi ba, sai dai in gan shi A jiye saman table, sannan duk in a ka kawo min abinci sai naga wannan Abun dana faɗa maki luluyayye, Ina jin daɗin cin shi, cikin wata uku da bana atare da ku sau Uku ina yin jinin nan akowani ƙarshen month, kuma duk in nayi abunda su ke yi mini kenan, tsotse jinin da ke fitowa…….” hawaye ne kwance a cikin idanuwan ta, ita kanta Angel ɗin idanuwanta A cike suke fal da hawaye gani take kamar Akwai wani abu da su ka yi mata ta hanyar abincin da su ke bata tana ci, musamman da ta ji ta ambaci luluyayyen abun nan fari da a ke sako mata cikin abinci, hankalin ta bai kwanta da shi ba.

“Batul inaso ki faɗamin ko kin ta6a gudowa daga Cikin ɗakin da aka kai ki?” ɗaga mata kai Batul ta yi alamar eh kafin ta ɗaura da cewa”Na ta6a samun damar durawa ta window ɗin da ke a cikin toilet ɗin ɗakin, na watso da gudu Ina neman hanyar da zata dawo dani cikin ku, A tsorace na ke a lokacin bani acikin hayyacina bansan meya faru ba, na dai ji kamar na faɗi ƙasa, kaina ya bugu, Bansan wanene ya mayar dani ɗakin da aka kai ni ba, lokacin dana dawo cikin hayyacina acan na ganni kwance saman gado, tsabar takaici yasa Na fashe da kuka har na kai ga zazzaga masifa ni kaɗai kamar mahaukaciya, a ƙarshe na haƙura na koma na kwanta, ina kukan zuci…….” dakatawa ta yi da yin maganar tare da sanya yatsun hannunta ta share ƙwallar da ke gangarowa ta cikin idanuwanta.

“Ina so insan a hawa na nawa ne aka kai ki, Na ta6a yin mafarki da ginin kuma ni idan nayi mafarki yana zama gaskiya, a yadda aka tsara mini ginin hawa Uku ne, a cikin su wannene aka kai ki’?

Girgiza kai Batul ta yi tare da cewa”Ae bazan Iya tunawa ba, amma inaji kamar ginin dana na biyo time dana gudo Acan sama Ya ke,” jinjina kai Angel ta yi”shikenan Iya abunda ya faru da ke? Wanene ya dawo da ke? Ko giants ne? Kamar ƴar jarida haka Angel ta tsare ta da tambayoyi.

“A ranar ina zaune tsakiyar gado, ina ta kuka ina ambaton sunyen ku, ina faɗin ni na gaji amaidani wurin ƴan uwana, idan ba haka ba zan haɗiyi zuciya in mutu, saboda na gaji da maraicin ku gani na ke kamar mutuwa zanyi, Angel shiru babu wanda yazo gare ni, hakan ya ƙara hasala zuciyata, Dama akwai wata ƙaramar wuƙa ta fruit da aka sako min cikin kayan abinci, sai nayi tunanin in ɗauke ta in yi kamar zan kashe kaina wata’ƙil asamu wani yazo gare ni tunda suna ganin komai da na ke yi, na sauko daga saman gadon na ɗauki wuƙar tare da buɗe murya ina faɗin”ko dai su zo su maidani wurin ƴan uwana ko in kashe kaina, kowa ya huta,” ina kammala yin maganar Na watsa da gudu na shige toilet ɗin ɗakin naja ƙopa na rufe, ina jiran ganin ko zasu zo gare ni, jin shiru yasa nayi tunanin in ɗan yanka hannuna Jini Ya fito ko sun gani su zo, Ina ƙoƙari ɗaura wuƙar saman hannuna da niyar in yanka, ba zato ba tsammani kunnuwana su ka soma jiyo min takun tafiyar mutun a cikin toilet ɗin, a tsananin tsorace na ɗago don inga wanene ya shigo bayan na rufe ƙopa, Tsabar tsoro Yasa na jefar da wuƙar dake a hannuna Yayin da nake kallon Shi, Giant ne sanye Cikin baƙaƙen Kaya, dogo ne yana da faffaɗan ƙirji sai dai tafiyar shi ta banbanta dana sauran Gaints da su ke kawo mana abinci, kuma shi wannan Yana magana Don har ce min yai yazo ne ya taimake ni ya maidani cikin ƴan uwana idan inaso” cikin shessheƙar kuka nace mashi kada ka cutar dani, idan har dagaske za ka iya taimaka mini, ka nuna min hanyar da zan bi in koma wurin su, ko ka ɗauke ni ka kaini.”

Tun da na ambaci hakan sai naji wani irin bacci acikin idanuwana, daga nan ban ƙara sanin me ya faru dani ba, sai dai na farka na ji kin rungume ni.

Ajiyar zuciya Angel ta dinga saukewa, Hankalinta ya kwanta sosai, jin cewa ba su yi mata irin na Unaiza ba, sai dai akwai wani abu da ya ɗaure mata kai dangane da labarin da batul ta bata, shin meyasa ita basu yi sex da ita ba kamar yadda su ka yi da Unaiza? Kuma har abinci su ke bata lafiyayye, basu cutar da ita ba ko kaɗan, Iya jinin al’adarta ne su ka tsotse, after that Angel ta yi mamakin Giant ɗin daya taimaki batul ya dawo da ita cikin su, a iya saninta Giant basa magana, sai dai ko tsakaninsu da manyan su zai iya yiwuwa suna magana, Amma ita Batul Giant ɗin ya yi mata magana har ya nemi taimakonta!! lamarin ya ɗaure mata kai.

Ta yi zurfi acikin tunaninta, muryar Batul ta katseta da cewa”Rabin raina, Me ki ke tunani ne? Allah yasa labarin dana baki bai ɗaga maki hankalin ki ba, dama saida nayi fagabar hakan”

Girgiza kai Angel Ta yi”a’a hankalina bai tashi ba, just na ɗanyi mamakin wasu abubuwa ne, Yanzu dai nuna min Jan tabon da ke a saman ƙirjin ki inaso na gani” da sauri batul ta sanya hannu ta soma nannaɗe ƙasan rigar da ke a jikinta har zuwa saman ƙirjinta, daga ƙasan boobs ɗinta da suka fara tasawa, Angel ta yi tozali da Jan tabon da ke a wurin, kasancewarta fara sosai, fatar wurin ta yi jawur.

“Yana yi maki zafi”? Angel ce ta yi maga tambayar, batul tace”A’a, bana jin zafi,” jinjina kai Angel ta yi”zan yi maki addu’a, in tofa maki saman fatar wurin a yanzu, sannan da Anjima kafin mu kwanta zan ƙara yi ma ki, don inaji araina cewa Jan tabon nan ba alkhairi bane, dole akwai wani abu da ya ke nufi” ba tare da 6ata lokaci ba Angel ta karanto addu’o’i tare da tottafa mata saman fatar wurin, bayan ta kammala yin addu’ar ta ɗago su ka kalli juna.

“Allah ya tsare min ke ya kare min ke tare da sauran ƴan uwana daga sharrin waɗannan azzaluman mutanan” fuskar Batul ɗauke da murmushi ta amsa mata da ameen, ruƙo hannunta Angel ta yi acikin nata”taso mu koma Ɗaki, kada ajimu shiru, ”

A tare su ka miƙa tare da nufar ƙopar fita daga cikin toilet ɗin, sam ta manta da zancen ainihin abunda ya kawota Cikin toilet ɗin.

Shigar su ɗakin keda wuya, kunnuwan su su ka soma Jiyo masu motsin buɗe ƙopa, ras! gaban su ya faɗi, Azeeza da jamimah jiki na kerma su ka sauko daga saman gadagen su, atare su ka shige ƙarƙashin gado, Hankalin su sarah ba ƙaramin tashi yai ba, Kowan nan su Zuciyar shi ta hau harbawa da ƙarfi da ƙarfi, Deeja da ke kwance saman gadon Haris tuni ta zabura ra miƙe zaune, Gaba ɗaya idanuwansu na akan Matakalar benan, A bakin ƙopar fitowa daga sashen toilet ɗinsu Batul da Angel su ka dakata da yin tafiya Hannunsu ruƙe Cikin Na juna, Kowa Jira ya ke yaga wanene zaya shigo.

Jin takun tafiyar ta yasa hankalin su ya ƙara tashi, A hankali ta ke saukowa daga saman matakalar benan hannunta a ruƙe da sandarta, Kamar kullum Cikin jar shiga ta doguwar riga, Takunkumin da ke akan fuskarta Iya saman tsinin hancinta Ya tsaya, blue eyes ɗin ta, sai ɗaukar ido su ke Yi, Daga bayanta Giants ne masu take mata baya, Majiya ƙarfi dogaye masu ƙirar dakarun Yaƙi, Tuni kowan nan su yasha Jinin jikin shi.

A tsakiyar Ɗakin nasu tsohuwa zafreen Taci burki, tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, Babu wanda yai tunanin ya gaishe ta a cikin su saboda tsoratar da su ka yi, a ƙalla ta ɗauki mintuna tana ƙare masu kallo, kafin ta soma magana da kakkausar murya

“Ba ku Iya gaisuwa bane? Ko jira ku ke yi ni in fara gaishe da ku”? Muryoyin su na rawa su ka soma gaishe da ita, banda mutun ɗaya Angel da su azeeza waɗanda su ka 6oye a ƙarƙashin gado ita da jamamah, sun rungume juna jiki na kerma saboda tsoron da ke gare su.

“Ba haka nake so ku gaisar dani ba, saukowa za ku yi daga saman gadajen ku, Ku russina min,” da sauri Sarah dasu hibba da ke zaune saman shimfiɗa su ka miƙe tsaye su Deeja su ka sauko saman gadajensu ita da parveen, a tsananin tsoroce su ka ƙarasa gabanta, Da niyar su zuƙunna mata kamar yarda ta buƙata, muryar Angel ce ta katse su

“Karku kuskura ku russina mata! Ae ita ba Allah bace, banga dalilin da zaisa mu girmama ki ba, because you don’t deserve it!”

A firgice su Deeja ke kallon Angel da ta yi maganar cikin ƙwarin gwiwa, tsabar mamaki ne yasa tsohuwa zafreen Saurin wurga ƙwayar idanuwanta kan fuskar Angel tamkar zasu faɗo ƙasa, Tun da take arayuwarta wani mahaluƙi bai ta6a yi mata katsalandan ba kamar yarda Angel ta yi mata ayanzu ɗin nan, Sam ta kasa magana sai kallonta ta ke yi haɗi da jinjina kanta.

Hankalin su Deeja idan yai dubu to ya tashi, muryoyin su na rawa su ka soma ambaton sunan Angel suna bata haƙuri akan ta daina magana karta ja masu bala’e.

Dogon tsoki Angel taja mai sautin gaske, Tare da cewa”Ku ku ke jin tsoronta, Ni bana tsoron kowa sai Allahn da ya halicce ni shi nake tsoro, amma ba wani bawa ba, mai hannu biyu irin nawa mai ƙafafuwa biyu, wanda in mutuwa tazo ɗaukar shi bai isa ya kubce mata ba”! Idanuwan zafreen azazzare ta ke ƙarewa Angel kallo tun daga ƙasa har sama, Giants ɗin da ke a bayanta Har sun yunƙura zasu motsa tsohuwa zafreen ta dakatar da su ta hanyar ɗaga masu hannu.

“Angel dan Allah ki rufa mana asiri, Mu za ki jamawa ki yi shiru ki daina magana, Na roƙe ki badan halin mu ba,” Batul ce ta yi mata maganar

Atare su Hibba su ka haɗa baki suna yi mata magiya akan ta yi shiru, ita kanta Angel ɗin ƙarfin haline kawai amma can cikin zuciyarta a tsorace take, sai dai bakinta yaƙi mutuwa, tana ƙoƙarin cigaba da yin magana Batul ta sanya hannu ta toshe mata bakinta, hannu ta sanya tana kiciniyar 6an6are hannayen Batul.

Ido cikin Ido Su ke kallon Juna ita da tsohuwa Zafreen, Abunda wani bai ta6a gigin yi mata ba, ba’ayi mata magana ana kallon Cikin idanuwanta, Yau sai ga wata ƴar ƙaramar cikin prisoners tana yi mata fitsara da rashin kunya akan idonta.

A hankali tsohuwa Zafreen ta ɗaura hannunta ɗa ya saman fuskarta, tare da zame takunkumin da ya rufe fuskarta, Kowa yasha jinin jikin shi, muryarsu na kerma suka zuƙunna saman gwiwowinsu agabanta suna roƙonta akan ta yi haƙuri kada ta cutar masu da Angel ɗin su.

Tuntsirewa tsohuwa zafreen ta yi da dariya tamkar bakinta zai 6are, duk su ka bi su ka ruɗe, a lokacin Angel Ta samu damar 6an6are hannun Batul data toshe mata baki da shi, Sai faman haki ta ke yi tana zare ido.

“Well done Unaiserh!” ta ambaci hakan tare da yi mata alamar jinjina da hannunta ɗaya.

“Dole in yaba ma ki, saboda Ke ce prisoner ta farko da kika fara gaya mini magana ido cikin ido, ba tare da jin shakkata ba, sannan ke ce mutun na farko da kika fara furta min kalmar cewa ni baiwa ce kamar kowa, sa’an nan baki jin tsoro na” Bazawarin murmushi tsohuwa zafreen tasakar mata, kafin ta ɗaura da cewa”Wuyan ki Ya isa yanka, tun da har kika iya gaya mini magana, Ina jinjina maki, kin kafa tarihi a zuciyar tsohuwa Zafreen” ta ƙarasa maganar fuskarta ɗauke da shu’umin murmushin nan nata mai wuyar fassaruwa.

“Ni bana hukunta mutumin da ya nuna baya jin tsorona, sai dai in ta6a zuciyarshi, ta hanyar cutar da wanda ya mutu akan ƙaunarsa”! ras gaban Angel ya faɗi, Hankalinta Ya tashi, ta zazzaro idanuwanta akan fuskar zafreen, saboda ta fahimci me ta ke nufi, hatta su Deeja sun gane me ta ke nufi, gwiwowin su a sage, su ka mimmiƙe tsaye suna ja da baya, yayin da hawaye ke bin fuskokin su.

“Dan Allah kada ku cutar mu, Ku ƙyale mu mu yi rayuwarmu, Lafin me mu ka aikata ma ku ne, da ku ke son ƙarar da mu…..” Kafin Deeja ta ƙarasa maganar tsohuwa zafreen ta buga sanar hannunta, muryarta a kausashe tace”Ban baku iznin Yin magana ba, ” tun da ta ambaci hakan babu wanda ya ƙara magana, A hankali ta ɗaura idanuwanta kan fuskar Angel ta soma magana yayin da take tunkararta

“ZA6I UKU ZAN BAKI! A CIKI DOLE KI ƊAUKI ƊAYA, SAKAMAKON RASHIN KUNYAR DA KIKA YI MINI”! runtse ido Angel ta yi Jikinta na kerma zuciyarta a tsorace ta ke da fargabar jin Za6in da Tsohuwa zafreen za ta furta mata.

A tsanake tsohuwa Zafreen Ta ci gaba da cewa” za6i na farko shi ne I will order the giants to do terrible things to your sisters while you watch, or I will kill two of your sisters. The last option is that you will no longer get healthy food. From now on, you will only have to eat leaves like animals, Sannan ruwan shan ku zai koma na zafi,”

Tsabar tashin da hankalin ta yai batasan sa’adda ta furta Innalillah wa’inna ilaihirraji’un! Muryarta adisashe .

Haƙiƙa ta yi danasanin maganar data gaya wa tsohuwa zafreen, Wasu irin zafafan hawaye ne suka wanke fuskarta, Muryarta A raunace ta soma magana

“Idan har maganar dana faɗa maki ce tasa kika bani wannan za6in, ina neman alfarma a wurin ki, Ba dan hali na ba, zan zuƙunna akan gwiwowina dan in nemi yafiyarki, saboda ni na yi maki laifi bai kamata hukuncin da za ki yi mini ya shafi ƴan uwana ba.

Girgiza kai tsohuwa zafreen tayi tare da cewa”kin ƙara tabkar wani kuskuren, Ni Ba’ayi min jayayya, sannan idan na zartar da hukun ci, babu wanda ya isa yasa in canza, Bayan haka kina yi min magana idanuwanki a cikin nawa, Anya kuwa kinsan wacece tsohuwa zafreen? Ta yi tambayar da izza, Angel dai bata ce komai ba, Jikinta duk yai sanyi.

“Idan ba ki za6i ɗaya daga cikin za6in dana lissafa ma ki ba, zan aiwatar da duka uku” fuskokin su Deeja tabi da kallo bayin Allah, Jikin su sai kerma ya ke yi, da yatsun hannayen su su ke yi mata nuna da ta ɗauki za6i na uku, duk da basu san menene ganyan ba hankalin su yafi kwanciya da shi tunda abin ci ne.

Zuciyar Tsohuwa zafreen ta hasala sosai Jin yadda ta yi shiru bata amsa mata ba, har ta buɗe baki zata zartar da hukunci muryar Angel ta katse ta da cewa”Za6i na uku amma duk da haka ina baki haƙuri, akan ki cire ƴan uwana daga horon da zaki bani” Girgiza kai tsohuwa zafeen ta yi fuskarta babu sassauci rashin imani ne tsantsa,
Juyawa tayi tare da nufar Benan ɗakin da sauri gaints ɗin dake take mata baya su ka bi bayanta, atare su ka fuce daga cikin ɗakin.

Zubewa Angel ta yi saman gwiwowinta, sosai ta fashe da matsanancin ku ka tamkar ranta zai fita, takaici duk ya ishe ta, ji ta ke kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu saboda baƙin cikin halin da ta jefa ƴan uwanta.

Tsananin tausayinta ne ya kama su Deeja, Jiki asanyaye su ka nufo wurinta hada su azeeza da ke a 6oye ƙarƙashin gado, A kewaye da Angel suka zuzzuƙunna suna lallashinta, Cikin shessheƙar kuka tace”Na tsani kaina, nayi danasani, zuciya ta ja mini na gaya mata magana, ga shi yanzu naja ma ku Cin ganye, Duk laifina ne, ni da ya kamata ace ina taimakon ku sai gashi ni nake ƙara jefa maku cikin matsala, ” daƙyar ta ƙarasa maganar.

“Angel Ki yi haƙuri ki daina zubar da hawayen ki, ki daina ɗaurawa kan ki laifi, Allah ya riga da ya ƙaddara faruwar hakan, pls kidana kuka bamu san ganin hawayen ki na zuba” Deeja ce ta yi maganar, Sarah tace”tun farko banso kika tanka mata ba, da duk hakan bata faru ba” idanuwanta jawur ta kalli fuskar Sarah da ta yi maganar ta mayar mata da martani”wlh zuciyace ta ɗebe ni, bansan ma na furta mata maganar ba, amma meyasa zata hukunta mu, mu duka bayan nice mai laifi”? Cikin ƙunar rai ta yi maganar, Batul tace”Saboda zalunci! Dama ai ba zata ɗauki mataki akan ki ke kaɗai ba , saboda kin nuna baki tsoronta, shiyasa ta haɗa damu don ta ƙuntata ki, kuma in sha Allah ba abunda zai faru damu, Ki kwantar da hankalin ki Angel, su ci gaba da kawo mana ganyen zamu ci, ruwa kuma ai muna da shi a cikin toilet sai mu koma muna shan na fanfo, ba dole sai wanda su ke kawo mana ba, ‘

Idanuwanta arauna ce ta ke bin su da kallo mai nuni da tsantsar tausayin su da ta ke ji, ta lura basu san me ganyen ya ke nufi ba shiyasa su ka aminci za su ci, duk da acikin za6in da tsohuwa zafreen ta bata shi ne mafi sauƙi agare su.

Muryarta asanyaye tace”Amma ae ba ku saba cin ganyen ba, ba mu san wani irin ganye zasu kawo mana ba, ina jin fargabar su kawo mana wanda zai cutar damu”

Cikin kwantar da murya Hanna ta soma magana” kada ki damu kan ki, Da daɗi da ba daɗi zamu ci”

Ta yi mamakin kalaman su agare ta, maimakon su ji haushin Abunda taja masu amma sai ga shi suna lallashinta.

A hankali ta ɗaura idanuwanta akan fuskokin su Azeeza da Jamimah da Parveen tun kafin ta yi masu magana parveen ta riga ta cewa “ba sai kin ce komai ba Angel, kwanciyar hankalin ki yafi mana komai, tabbas naji ba daɗi saboda ƙaunar da ke a tsakanina da abinci amma na haƙura tunda bamu da za6i, ƙaddarar mu ce tazo mana a haka, zamu jure muci ganye…..” runtse ido Angel tayi yayin da hawaye ke cigaba da tsastsafo mata saman kuncin ta.

Cikin sanyin murya Azeeza tace”Nima bani da matsala Angel, zanci ganye da babu ƙwara ba daɗi, sannan duk runtsi duk wuya idan Allah yaso mu rayu ba wanda ya isa ya hana, nidai fata na shine Allah ya ba ki ikon ku6utar damu daga Cikin kurkukun ƙaddarar nan, wlh banaso in mutu acikin shi, ” maganar Azeeza ta yi matuƙar ta6a zuciyoyin su, su kansu basu fatan suyi wulaƙantacciyar mutuwa a gidan kurkukun kamar yarda ƴar uwarsu Unaizah ta yi, idanuwan Angel jaga jaga da hawaye ta ke kallonsu ɗaya bayan ɗaya.

Muryar jamimah tamkar zata fashe da kuka tace”Nidai banason ganye, na saba da cin nama, amma in dai Genie ɗita zata daina kuka to nima zan haƙura inci ganyen” Murmushi ne ya bayyana akan fuskokinsu, Da sauri Angel ta miƙa hannu ta ruƙo Jamimah zuwa jikinta ta rungumeta sosai tamkar zata mayar da ita cikin cikinta.

“Nima bani da damuwa Angel, duk idan na tuna abunda kika faɗa mana dangane da irin tanadin da Allah yayiwa bayinsa salihai, waɗanda suka yi imani dashi sannan su kayi tawakkali, basu sa6a mashi ba, Sai inji daɗi araina, wahalar mu a gidan duniya ne, idan muka mutu zamu ji daɗi,” sosai Angel ta kuma fashewa da wani kukan jin abunda Yasmin tace.

“Yana daga cikin rukunan Imani mutun yayi imani da ƙaddara mai kyau da mara kyau, kamar yarda kika koyar damu, don haka munyi imani da ƙaddararmu, zamu rungume ta hannu bibbiyu, har zuwa lokacin da Allah zai ɗauki ranmu mu huta, amma duk da haka bamu sare ba, sannan bamu fidda rai da rahamar ubangiji ba, wata rana zamuji daɗi sai dai bamu sani ba, jin daɗin namu daga gidan duniya zai fara ko kuwa sai mun koma gare shi Allah wa’alamu,” eve ce ta yi maganar, hibba tace”ai ni tunda Angel ta faɗa mana cewa kowa zai mutu harda waɗanda suka cutar damu da waɗanda suka sadaukar da mu, wlh sai naji daɗi araina, tunda ba dawwama za mu yi acikin duniyar nan ba, dukkan mu zamu koma ga mahaliccinmu ne, Allah zai yi mana hisabi tsakanin mu dasu zaibi mana haƙƙin mu, aranar da basu isa su ƙwaci kansu ba, ” Maganganun dasu ke yi sun yi matuƙar faranta ma junansu, Musamman Angel taji daɗi da su ka yi imani da ƙaddarar rayuwarsu, a shirye su ke da su fuskanci kowani irin ƙalubale da zai zo masu acikin arayuwarsu a mutu ko ayi arai.

Tun daga wannan ranar ba’a ƙara kawo masu abinci mai rai da lafiya ba, Faranti Biyu ake cuko masu Da ganye ganyen ma mai ɗaci, ga ruwan zafi har tiriri ya ke yi, saboda tsabar mugunta haka ake kawo masu shi don su sha, Rana ta farko da aka fara kawo masu ganyen babu wanda ya iya ci, ga yunwa suna ji kamar suci ƴan hancin cikinsu, suka rasa ya zasuyi, saboda bai ciyuwa agare su, basu saba cin ganye ba, Yadda aka kawo shi haka giants suka koma dashi, a cikon kwana na biyu ne da yunwar ta kusa yi masu Illah Kamar dabbobi suka zauna suna cin ganye, saboda mugun kamun da yunwa ta yi masu kamar zasu zauce, suna ci suna kuka maƙoshinsu na ƙaiƙayi ahaka suka cinye shi tass, Basu sha ruwan zafin da a ka kawo masu ba, sai dai su ka koma suna amfani dana fanfon da ke a cikin toilet ɗinsu,
Ganyen da su ke ci ba ƙaramar illa ya ke yi masu ba, saboda basu saba ba, hakan yasa cikinsu ya dinga 6aci, babu wanda bai yi gudawa ba a cikin su, duk sun rame sun fita hayyacin su, sun zama mahaukatan ƙarfi da yaji, addu’ar da suke samu suyi yanzu sun daina saboda Rashin lafiyar da suke fama da ita, Kullum ne sai an samu wanda zai kwanta jinya acikin su, sun jigata sosai, kamar ba za su rayu ba, tun suna ci yana 6ata masu ciki har ta kai ga yanzu sun daina yin gudawa idan su ka ci ganyen, sun fara sabawa da cin shi, cikin nasu ya daina 6acewa, Idan aka kawo masu shi zama suke yi suci shi kamar dabbobi, ruwan kuma Basu iya shanshan shi da tsafi don zai iya yi masu illah, sai sun hura shi da bakunansu kafin su samu su kora shi ta cikin maƙoshin su, yaushe rabon da su wanke uniform ɗin jikin su yau tsawon wata ɗaya kenan, babu mai yin wanka a cikin su, damuwa da baƙin cikin halin da su ke aciki sakamakon canza masu abinci da akayi da kuma rashin dawo masu da ƴan uwansu yasa duk sun rasa kwanciyar hankali.

Sai da Angel ta yi dagaske wurin ƙoƙarin danne zuciyarta dake shirin bugawa ta hanyar dagewa dayi masu addu’a tukunna suka ɗan samu salama, natsuwa ta shiga jikinsu, yanzu suna samun damar runtsawa su yi bacci sosai, amma fa dukkan su bana tunanin za’a iya samun ɗaya wanda bai fama da depression, wani lokacin idan ƙirjinsu yayi masu zafi zuciyoyinsu suka yi masu nauyi, haka zasu zauna su dinga karanta duk wasu addu’o’i da su ka san zasu Sanyaya masu zukatansu, kuma cikin ikon Allah da zarar sun yi komai su ke samun sauƙi, harma su samu damar yin bacci, yanzu sun fidda rai da za’a dawo masu da ƴan uwan su duba da irin tsawon lokacin da aka ɗauka babu su, Danish Yana acikin wata na biyar a hannunsu, Su haris suna acikin wata na huɗu, basu san awani hali su ke aciki ba, Allah kaɗai yasan irin azabtarwar da ake yi masu, suna raye ko sun mutu basu da tabbacin hakan…………………”

💔PRISONERS💔

Dare ya nutsa sosai, babu mai motsi acikinsu, Bacci su ke yi kamar matattu, numfashin Angel ne ya soma canzawa, zufa ta soma wanke fuskarta, bugun zuciyarta ya ƙarfafa, yatsun hannayenta dana ƙafarta suka soma Yin kerma, Ga dukkan alamu mafarki ta ke Yi, wanda yasa ta shiga wannan yanayin da take a ciki, su uku ne a kwance saman shimfiɗar da ta yi masu a ƙasa, Ita da Jamimah sai Azeeza.

Sai faman yin sambatu ta ke yi tana ambaton Sunan tsohuwa Tamira!

Wata irin firgita ta yi Sakamakon Ta6a jikinta da akayi, a hanzarce ta yi wuff ta miƙe zaune tana faman zazzare idanuwanta, gashin kanta duk ya tarwatse saman bayanta.

“Angel ni ce! Meyasa kike sambatu kina ambaton sunan tsohuwa Tamira? A tsananin tsorace ta ɗaura idanuwanta kan fuskar batul da ke yi mata magana, Farkawarta kenan daga bacci, fitsarine ya matse ta bayan taje toilet ta yi shi ne ta dawo ɗakin har zata kwanta sai taji muryar Angel tana sambatu acikin baccinta, wannan dalilin ne yasa ta nufi shinfiɗar su don taga meke faruwa da ita.

Bata amsa mata tambayarta ba, saboda bata a cikin natsuwarta, ganin ta miƙe tsaye ne yasa itama batul ɗin ta miƙe tana tambayarta lafiya meya faru? Babu alamun zata tanka mata, sai faman bin ɗakin su ta ke yi da kallo kamar ranar ta fara ganin shi.

“Angel dare ne fa, Me ki ke kallo? Magana fa na ke yi ma ki amma kin share ni…..” tunkan batul ta ƙarasa maganar, Angel ta damƙi hannun batul tare da Janta da sauri ta nufi sashen toilet ɗin hannunsu aruƙe dana juna, bayan sun shiga sashen ne Angel ta saki hannunta, aruɗe batul ke kallon fuskarta gani take kamar angel tafara haukacewa ne shiyasa ta janyota a tsakar daren nan zuwa sashen toilet ɗinsu.

Fuskarta da alamun ruɗi tace”kiyi min magana mana, meyasa kika kawo ni nan”?

Sai da ta fara tattara natsuwarta guri guda kafin ta soma magana

“Batool na yi wani mafarki da ban ta6a yin irin shi ba, dangane da wani kalami da tsohuwa Tamira ta ta6a furta mana……” daƙyar tayi maganar tana faman haɗiyar yawu, batul duk ta gama ruɗewa
“Wani kalami kenan”!? Ta jefa mata tambayar.

“Zan faɗa maki amma kafin nan inaso ki sanar dani, Kafin zuwana gidan kurkukun nan, a ina ku ke yin rayuwa? Meyasa aka canza maku ɗaki daga asalin wanda ku ka baro”?

“Angel meyasa kika tambaye ni”? A tsiwace tace”nidai ki bani amsar tambayata”! Yawu batul ta haɗiya kafin tace”Ni kaina bansan dalilin dayasa aka dawo damu nan ba, kawai dai nasan tsohuwa Tamira tace zata sanya a canza mana ɗaki saboda asalin wanda muke aciki yayi mana ƙanƙanta, babu wadataccen filin da zamu sakata mu wala……..” A dabarbarce take yin maganar saboda yadda Angel tayi mata rumfa kamar zata rufeta da bugu.

“Amma ranar da aka kawo ni kurkukun nan, Na tsinci kaina nikaɗai acikin ɗakin nan, sai daga bisani aka buɗe ƙopa sai gaku kun shigo Ciki, daga ina ku ke”!? girgiza mata kai Batul tayi”bazan iya tunawa ba Angel, bansan inda aka kaimu ba, ” numfasawa Angel tayi tare da sanya hannunta biyu cikin sumar kanta, kamar akwai wani abu da take son ganowa, ganin yadda duk tabi ta ruɗe ne yasa Batul tambayarta”meke damun ki ne? meyasa ki ka tambayeni”?

“Saboda ina hasashen Akwai ƙopar da zamu Iya guduwa ta cikin ɗakin nan da muke rayuwa………” batul bata fahimci inda zancen nata ya dosa ba.

“Angel ƙopa fa kika ce a cikin ɗakin nan ta ina kenan? Anya kuwa kinsan me kike faɗa kuwa”?

Jinjina kai ta ɗanyi kafin ta soma magana” akwai wata magana da tsohuwa tamira ta ta6a furta mana, ban tashi tunawa ba sai Acikin mafarkin da na yi yau, abun tace mana shi ne tana so mu ɗauka cewa mu kamar

*MUKULLAI NE NA MABUƊIN WATA ƘOFA GUDA ƊAYA WADDA ZATA SAMA MANA FARIN CIKI ACIKIN RAYUWARMU, TABBAS MUNA DA DAMA*

Amma fa dole sai Mun yarda da kan mu, mun haɗa hannu, domin kuwa Ƙofar farin cikin nan tana atare mu Sa’annan

*MU NE MAKULLAN DA ZAMU BUƊE TA*

Numfashi Angel taja tare da cigaba da yin magana

“Kalamaine tayi mana cikin hikma, a hasashe na, dama tun fil azal tsohuwa tamira tana son taimakon ku, shiyasa tayi silar da aka canza maku ɗaki aka kawo ku nan, bayan haka tasan da zuwana gidan kurkukun nan……..”

Ba ta kai ga ƙarasa maganar ba, Batul ta tari numfashin ta da cewa” kin manta wacece tsohuwa tamira, itama fa muguwace kamar sauran, banbancin kaɗan ne sannan ma’aikaciya ce ita agidan kurkukun nan, taya kike tunanin zata iya taimakon mu? ta yi mata tambayar tana bin da kallo.

“Mutun koda dutse ne a ƙirjin shi ba zuciyaba, idan Allah ya so ka da rahama sai kaga Ya rikiɗa daga mara tausayi zuwa mai tausayi, Zai iya yiwuwa tsohuwa tamira taji tausayin halin da ku ke acikine shiyasa ta nemi hanyar da zata ku6utar daku, Ita da kanta ta faɗa mana cewa tun da ta ke rainon prisoners bata ta6a samun waɗanda su ka kwanta mata aranta ba irin mu, da alama tun kafin zuwana kurkukun nan take so ta taimake ku sai dai tagaza gudun kada taja ma kanta, Shiyasa ta dakata har zuwa lokacin da aka kawo ni sai tayi amfani da kaifin basirar da nake dashi wurin sanar dani cikin hikma akan hanyar da zamu bi don mu gudu daga prison!”

Cike da ƙwarin gwiwa ta yi maganar, Nazari sosai batul tayi dangane da kalaman da Angel ta furta mata, Na ɗan wani lokaci babu wanda ya furta wani abu a cikinsu, can batul tace”Kamar fa akwai ƙamshin gaskiya a maganarki, Amma idan har ta tabbata dagaske ne tsohuwa tamira ta yi kalaman hikma donta fahimtar damu hanyar da zamu ku6uta, Tayaya zamu iya ganin ƙopar da zamu gudu? Sannan taya akai muka zama makullai

……………………❓❗

Dai dai nan Na ajiye alƙalamina, Shin kuna ganin dagaske ne hasashen Angel akan kalaman tsohuwa tamira?

 

*Weekend zan kammala Takun farko, zan ɗauki hutu, kafin acigaba da middle step, saboda in samu natsuwa kafin in dasa, ba jimawa zanyi ba, ƴar tazarace, Ga masu son cigaba da Karanta Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne kacal, Labarin yanzu nake Cikin rubuta shi babu Complete sai dai ka biya asanyaka agroup inda zaka dinga samun update akai akai, Inka biya za’ayi adding naka a paid group kuma za’a sanyaka a comment section, Sa’annan Ba’a share Ko yin forwarding duk wanda yayi gigin fitar da littafin, akwai ta inda zamu ga sunan shi da alamar yayi forwarding to zamu cire shi a group ne👌 Kuma yaja ma kanshi zamu ɗauki mataki👌*

*Littafin Kurkukun ƙaddara 3 part ne, Yanzu muna gab da ending na Takun farko free kenan, Sai kuma Takun tsakiya wanda ya kasance na kuɗi ne, da takun karshe duk akan 500 zaku karanta shi*

*Ga wanda ya shirya Yin payment, ga details nan, Idan ka tura kuɗin zaka bamu shaida, Bamu kar6ar kati, Ta bank ake turawa ko ta pos, In yaso saika ɗauko hoton reciept ka tura mana*

*3196407426*
Bature Hafsat Muhammad
First bank

*Zaka tura da shaidar Biyanka ta wannan Numbers ɗin (0816985 6268) ko kuma ta (08103884440)*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button