Sponsored Links
Hausa NovelsKurkukun Kaddara Hausa Novel

Kurkukun Kaddara 73

Sponsored Links

*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

قصة خائفة ومتعاطفة للسجناء💔🥺

*Daga alƙalamin Hafsat Boss Bature✍️*

Dedicated to Aunty kubra💘🌹

*Gargarɗi!!!*

_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube, ba tare da an nemi izni a wurina ba. Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!_

E73 Last free pages of Takun farko

💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫

*_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K’ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WATO DR MAMAN YUSUF LIKITAR MATA SOKOTO TANA FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE A FADIN NIGERIA DA NIGER HARMA DA WASU K’ASASHEN BAKI DAYA, KU SANI A DADE ANAYI SAI GASKIYA KUMA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI , INA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI_* 08133079957

*_munada zafafan kaya kamar haka ,_*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*Hadin amarya budurwa ko zawara*

*Hadin uwar gida Mai taken (Maida tsohuwa yarinya)*

*Maijego package (virgin gain)* 📦

*Hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji*

*Sahihin maganin sanyi na Maza Dana Mata Wanda yake fatattakar sanyi cikin Dan lokaci*

*Maganin gyaran nono Wanda zai gyara maki nononki cikin Dan lokaci komai lalacewarsa*

*Maganin hips Wanda zaisa shape dinki ya fita kiyi kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji*

*Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko kiyi kiba yar dai dai misali kema adinga binki da kallo Idan kin juya Sam rama batayi ba yar uwa*

*Hadin mallaka ba boka ba malam , akwai taimakon da muke bayarwa ga Mai butsarin namiji Wanda cikin ruwan sanyi Zaki dinga juya abunki , haka akwai Hadi na musamman Wanda komai rowar namiji sai kin samu alkhairin a wajanshi,*

*Muna da kalolin gumbuna masu Saka ni’ima sha’awa da dandano*
*Kalolin garrika mash gyara gaban mace da jimawa ajiki*
*Kalolin Zuma masu saukar da ni’ima Nan take da gamsar da maigida*
*Kalolin tsumi Wanda cikin sauki zasu Baki ni’ima da dandano irin wadda akeso*
*Kalolin matsi Wanda suke ciko da gaban mace matse gaban mace da bata Wani irin dadi da dadano*
*Akwai set kala kala Wanda yawansh ya wuce na zayyanasu anan ga Mai bukatar kayana zata iya mun magana Kai tsaye ta hanyar Kiran ko Kuma Whatsapp* 👉🏻 08133079957

*Muna dahuwar zabo ,dahuwar kaza ,dahuwar kifi ,dahuwar zuciya ,dahuwar Yan shila ,dahuwar tsoka Tara ,dahuwar Kwan mallaka, dambun nama ko na kaza Wanda yake saukar da ni’ima da jimawa sosai ajikin mace*

*Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha’awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha’awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura* 08133079957

*Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto*

💋PRISONERS💋

 

 

Cike da ƙwarin gwiwa ta yi maganar, Nazari sosai batul tayi dangane da kalaman da Angel ta furta mata, Na ɗan wani lokaci babu wanda ya furta wani abu a cikinsu, can batul tace”Kamar fa akwai ƙamshin gaskiya a maganarki, Amma idan har ta tabbata dagaske ne tsohuwa tamira ta yi kalaman hikima don ta fahimtar damu hanyar da zamu ku6uta, Tayaya zamu iya ganin ƙopar da zamu gudu? Sannan taya akai muka zama makullai

Zama Angel ta yi dirshan a saman floor, ta jingina bayanta jikin bango, Hannayenta Biyu Dafe da kanta, Ganin ta zauna yasa itama batul ɗin ta zauna, Ya kasance suna fuskantar Juna ita da Angel, Kowa Da abunda Ya ke nazari a cikim kanshi duk a ƙoƙarinsu na su gano fassarar kalaman tsohuwa Tamira,

Sun ƙurawa Juna ido Kamar Malaman Duba, tsawon mintuna kafin Angel ta soma ƙoƙarin motsa bakinta wurin furta”idan ya kasance ƙopa ce, to kuwa mun rasa Makullin da zasu Iya buɗe ta ko da ace mun gano ta, saboda adadin makullin da zasu iya buɗe ta basu Cika ba, Babban makullin ma baya a cikin mu, idan mu ka gano ƙopar tayaya zamu iya tattara makullan da basa atare damu”? ta jefa ma batul tambayar, numfasawa batul ta yi kafin tace”Shi ne Abunda nima nake tunani amma anya kina ganin kalaman tsohuwa tamira suna nufin ƙofa ce ke akwai? Kodai kawai tana nufin mu zamu haɗa hannu don mu ku6utar da kan mu”? Fuskarta da alamun ruɗu ta yi maganar, Angel tace”Abin da zaki lura anan shine, Cewa ta yi mu ne makullan buɗe ƙofar, that mean ƙofar daban ta ke bamu bane ƙofar, sai dai mu zama makullan buɗe ta, ni dai a hasashe na kenan” kowa kanshi ya ɗauki zafi, Girgiza kai batul ta yi”A’a ni nafi hasashen Mu ne zamu sama ma kanmu ƙopar fita idan muka haɗa hannu, Ba wai tana nufin Akwai ƙopa a cikin ɗakin mu ba, kaina ya fara rikicewa, Ko dai inje in yi ma su Hannah magana Su zo mu haɗu Kowa ya faɗi nashi ra’ayin? Kinsan abokin shawara nada daɗi, wata’ƙil acikin su asamu wanda zai faɗi ainihin me ma’anar ta ke nufi tunda mu kan mu ya kulle, Amma idan aka kira su wanda su ka fi raja’a akan cewa ƙopa ce kin ga sai mu fara binciken inda zamu ganta, Idan Allah yasa muka gano ta sai mu yi ƙoƙarin tattara makullan da muka rasa!”

Angel ta gamsu da bayanin da batul ta yi mata.

“Kina ganin mu tayar da su daga bacci yanzu ko mu bari sai gobe da safe”? Batul ce ta jefa mata tambayar.

“Wani irin gobe? ai yanzun nan zamu farkar da su, Babu zancen 6ata lokaci, zuciyoyin mu da fargaba su ke buga wa, duk daƙiƙa ɗaya na rayuwar mu a tsorace mu ke yin shi don haka bamu da lokacin 6ata lokaci, wannan dama ce agare mu, ba zamu yi wasa da ita ba, dama tsohuwa tamira ta faɗa mana cewa Ba zamu fahimci me ta ke nufi ba sai nan da wani lokaci da muka fita hayyacin mu, wasu ma su ka rasa ransu, A yanzu mun rasa mutun biyu, bamu da tabbacin ma Ƴan uwan mu maza da aka ɗauka zasu dawo mana da su dukkan su ba tare da an samu wanda ya rasa ran shi ba acikin su, fita hayyaci kuma mun yi sau ba adadi, Yanzu ne yakamata mu nema wa kan mu mafita tun kafin su ƙarar da mu don inaji araina Bamu ga komai ba, domin kuwa har yanzu muna a TAKUN FARKO na kurkukun ƙaddara, Idan har muka kai TAKUN TSAKIYA a cikin Kurkukun nan ba tare da mun ku6uta ba, bana tunanin za’a samu rai ɗaya da zai rayu acikin mu In ba wani iko na Allah,’ muryarta asanyaye ta ƙarasa maganar, Batul da ke sauraronta ganin ta ƙare maganarta yasa ta yunƙura ta miƙe tare da cewa”Ki taso muje mu tashe su daga baccin”! Miƙewa Angel tayi tare da kallonta.

“Batul duk wani motsi namu akan idon su! Dole sai mun yi takatsantsan idan ba haka ba Garin neman gira zamu rasa ido.

“Ya zamu Yi kenan”? Acewar batul
Angel tace”Ni aganina, mu kashe hasken ɗakin mu wata’ƙil idan mu ka yi hakan ba zasu Iya ganin mu ba, Sannan Ba kowa zamu tayar daga bacci ba, Mu za6i kamar mutun uku sun isa, Kinga mun cika mu biyar kenan, Sai mu ji ra’ayoyinsu.”

“Ni nafi tunanin atada su duka saboda kowa da irin baiwar da Allah ya yi mashi, musamman Azeeza da Deeja ga kuma Parveen sannan Hannah bayan ita sai sarah zata taimaka mana Tunda tana da tsawo sosai wani abun da ba zamu Iya hangowa ba zata iya hango shi.

Girgiza kai Angel ta ɗanyi”Gaskiya baza a tada azeeza ba, kinmanta bata gani idan dare yayi? Ita kuma Jamimah tayi ƙaranta ba abunda ta sani”

“Shikenan, Zan je na kashe hasken ɗakin, Kafin mu dawo tare dasu Ki Buɗe ƙofofin kowani toilets saboda mu samu hasken Fitilun da ke a cikin su Ya haskaka sashen,’
Angel ta amsa mata da toh, Juyawa batul ta yi tare da fuce wa daga Cikin sashen.

Ajiyar zuciya Angel ta sauke tare da kifa kanta Jigin bango tana jiran dawowarsu, Ɗuff Taji hasken ɗakin su Ya ɗauke duhu ya gauraye ko’ina, A hanzarce ta lalubi ƙofofin Toilets ɗin ta buɗe su duka, Hasken Fitilun cikinsu Ya haskaka Sashen Duk da bai wadata sosai ba”

Jin motsin shigowar su Yasa ta yi saurin fuskantar su, sai faman murza idanuwansu su ke da yatsun hannayensu, Parveen sai hamma ta ke Yi bakinta hada miyan bacci.

“Sai da nace maki ban da Azeeza meyasa kika tado ta”? rai a6ace ta yi maganar idonta akan Azeeza, da Batul ta ruƙo hannunta

“Bani na tada ta ba, Ina cikin tada su Deeja ta farka tana Jin fitsari shi ne na ruƙo hannunta muka shigo atare” mayar da idanuwanta tayi akansu, Kusan su dukane banda Jamimah ita kaɗaice basu Tada ta ba, tana can ƙudundune Cikin bargo saman shimfiɗar su.

“Wai lafiya aka tayar da mu daga bacci? Ko an kawo abinci ne”? Parveen ce ta yi tambayar fuskarta a yamutse,

Harara Angel ta watsa mata”Halan mafarkin shi ki ke cikin Yi aka tada ki, shiyasa kike tambayar ko an kawo abinci” Kwa6e fuska ta yi ba tare da tace komai ba, Sai faman murza ido su ke yi, fuskokin su a tur6une.

“Hakanan muna yin baccin mu mai daɗi an tada mu,” hannah ce ta yi maganar tana murgaɗa ƙaramin bakinta.

Jan hannun Azeeza Batul ta yi zuwa cikin toilet su ka shige.

“Ganin Yadda su ke ta kwa6a magana ransu a6ace saboda an katse masu bacci, har suna cewa ta tsare su da ido, idan ba abunda zata gaya masu zasu koma ɗaki su kwanta ne” Har sun yunƙura zasu Juya muryar batul ta katse masu hanzarinsu da cewa”AN SAMU ƘOPAR DA ZAMU GUDU” A ruɗe Suka dakata da yin tafiyar suna kallonta, tamkar saukar aradu Haka maganar ta dirar masu acikin kunnuwan su, wani irin kallon rainin wayau su ke binta da shi, ƙarasa fitowa ta yi daga Cikin toilet ɗin hannunta ruƙe dana Azeeza.

“Idan ku ka natsu zamu Yi maku bayanin komai” ga dukkan alamu sun shiga ruɗani duba da irin kallon da su ke yi mata.

“Wannan maganar daga jinta a cikin mafarki ake yinta ba’a gaske ba” Hibba ce ta yi maganar, idanuwanta kamar na mashayin giya.

Sarah tace”Nima nafi tunanin mafarki ne mu ke yi, idan har ta tabbata dagaske mu ke ganin batul da ta yi maganar to kuwa tabbas Ganyen da muke ci ya fara zautar da ita, shiyasa ta fara mana sambatu”
Sarah na rufe baki Hannah tace”ni bazan tsaya sauraron wannan shirmen ba, Kun ga tafiyata”

ta yi magnar tare da nufar ƙopa zata fuce da sauri batul ta saki hannun azeeza tai wuff ta ruƙo wuyan rigar Hannah ta janyo ta tare da dawo da ita ta jinginar jikin bango.

Angel ta kasa kunne tana sauraron su, gani ta ke kamar ba za su iya fahimtar su ba koda ace sun faɗa masu, saboda basu ɗauki abun serious ba.

“Kun tasa mu agaba kuna kallo kamar kun samu madubi, idan ba za ku buɗe baki ku yi magana ba, Ni zan koma ɗaki” acewar Rubina.

“Ki yi masu bayani mana ko ni zan yi masu”? Batul ce ta yi ma Angel magana.

Gyaran murya tayi Kafin ta sassauta muryarta ta yadda sautin ba zai fita sosai ba, kamar maiyin gulma, ta soma fayyace masu komai dangane da hasashen da su ke yi akan Kalaman tsohuwa tamira.

Sun natsu suna sauraronta, Yadda suka tattara hankulan su akanta sai ta yi tsammanin ko sun Fahimci inda zancen nata ya dosa ne, sai da ta kai ƙarshen Maganar, kusan atare suka haɗa baki wurin jan tsoki.

“Kawai don ta yi kalami sai asamu ƙofa, sai ka ce ba ku san wacece tsohuwa tamira ba, In banda ma rainin wayau taya za’ace mune makullan buɗe ƙopa? Ƙanzon kure ge ne wannan” Parveen ce ta yi maganar tana hura hanci ita ala dole an 6ata mata rai.

“Da nasan abunda zaku gaya mana kenan Allah da ban farka ba lokacin da batul taje tada ni daga bacci” acewar Eve

“Ni dama kwanakin nan ban yarda da ku ba, Ku biyun nan Batul da Angel, damuwa tasa kun fara zaucewa,” Yasmince ta yi maganar , kamar zasu rufe su da duka Kowa Da abunda ya ke furtawa, Mutun Biyu ne a cikin su basu yi magana ba, Deeja da ta jingina kanta Jikin bango ta lumshe idanuwanta sai Azeeza da ke a tsaye bakin ƙofar toilet, Ta kasa kunne tana sauraronsu duk bata ganin su.

“Koda ace baku yarda da maganar mu ba, Inaso ku bamu dama, Mu fara neman ƙofar da ke a cikin ɗakin mu. Idan ba’a ganta ba ni na yarda Ku yi min duk abunda ya dace dani,” cikin sanyin murya Angel tayi masu maganar.

“Deeja! Banji kince komai ba? Ke baki faɗi naki ra’ayin ba, dangane da kalaman tsohuwa Tamira,”

Daƙyar deeja ta iya buɗe idanuwanta masu ɗauke da bacci ta ɗaura su kan fuskar Batul da ke Yi mata magana, da buɗar bakin ta sai cewa ta yi”Oh wai da ba mafarki bane? Baki asake Take kallon su, Dafe kai batul tayi da hannu ɗaya”Wai meye haka? Idan har ba ku ɗauki maganar nan serious ba kun bamu haɗin kai tayaya zamu Iya ganin ƙofar….”

Tun kan ta ƙarasa maganar Rubina tace”Ae ba za ku ta6a ganin ƙofa ba, hasashen ku akan kalaman tsohuwa tamira Wasiƙar jaki ce wadda bazata ta6a zama gaskiya ba, in banda wahalar da kai ta ya tsohuwa Tamira zata Taimake mu? Ku yi amfani da kwakwalwarku mana, koda yake dama ba cikakken hankaline damu ba, ” Murmushin takaici Angel tasaki Jin abunda Rubina tace, wato dama basu da cikakken hankali.

Muryar azeeza ce ta janyo hankalin su ga kallonta.

“Ni ina goyan bayan maganarsu Angel, tsohuwa tamira tana son taimakon mu, kafin tabar cikin mu, Ta yi mana abubuwan da zata faranta mana rai wanda ke nuni da za ta yi kewar mu sanna ta faɗa mana cewa tana so wata rana mu tuna da ita acikin rayuwar mu, duk mutumin da ya furta maka wannan kalami dole asamu ƙaunarka da tausayinka acikin zuciyarshi, yakamata muyi nazari sosai, Koda ace bazamu yarda da maganar su Angel ba dangane da hasashen su akan kalaman tsohuwa, Kada muƙi bin maganarsu Mu jaraba duba ko’ina na cikin ɗakin, kafin mu yanke hukunci, Sannan inaso na tuna mana wani abu, kamar yadda Angel ta faɗa mana ba’a ganin wanda ya halicce mu, That mean idan zamu samu taimako daga wurin shi ba kai tsaye zai bayyana ba don ya taimake mu, sai dai Ya haɗa mu da wanda zai taimaka mana, ko ya fahimtar damu ta wata hanyar Kamar dai yadda Angel tayi mafarki da kalaman tsohuwa tamira……….” tun da Azeeza ta soma Yin magana Hankalinsu ya dawo kanta, Ko ƙyafta idanuwan su basa yi, Sun natsu suna sauraronta, Musamman Angel tsabar mamaki yasa ta saki baki tana kallonta, Yarinyar Allah ya yi mata baiwa, Ita takasa fahimtar dasu yadda zasu gane sai gashi kalaman Azeeza sun yi ta’asiri acikin zukatan su.

Nauyayyiyar ajiyar Zuciya kowan nan su ya sauke, sarah tace”yanzu abunda za’ae mu fara neman ƙofar! idan Allah yasa aka same ta sai mu fara tunanin ta yadda zamu tattara makullan buɗeta,”

Atare suka haɗa baki wurin cewa”Haka Ya dace, ”
“ita fa azeeza da bata gani? Ko dai in kai ta ɗaki ta kwanta”? Deeja ce ta yi maganar.

Tun kafin Wani ya bata amsa Azeeza ta bubbuga ƙafafuwanta Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace”wlh ba in da zan je, dani za’ayi komai kawai don anga bana Iya gani shine za’a ware ni” ganin zata ja masu hayaniya yasa Angel yin saurin kai hannu ta janyota zuwa jikinta, ta rungumeta tana faɗin”Its okey azeezata, Ai dole ma ayi tafiyar nan da ke, kwantar da hankalin ki” ajiyar zuciya azeeza ta sauke tare da sanya hannayenta Biyu ta ƙanƙame Angel.

“Kafin Mu fara bincike, Yakamata Mu fara Yin addu’a akan Allah ya bamu Ikon ganota Cikin sauƙi,” Angel ce ta basu shawarar Yin hakan, atare suka ɗaga hannayen su Sama ta dinga jera masu addu’o’i suna amsa mata da ameen, bayan sun kammala Hibba tace”Bafa lallai yakasance ƙofa ta ke nufi ba, A kalamanta, ” Batul tace”ae shiyasa zamu fara dubawa, Kunga idan ba’a samu ƙofar ba, sai muyi wani tunanin na daban”

Gyaran Murya Angel ta yi Hankali ya dawo kanta.

“Zamu Raba kan mu wasu zasu shiga toilets, wasu ɗaki, Amma na ɗaki dole su ɗaga gadajen mu, don ina hasashen ƙofar ta sirri ce, ta in da bamu tsammani zamu Iya ganinta, don haka mu sanyawa ran mu cewa har cikin Tukunyar fulawa zamu Iya samunta, kota jikin bango, kota ƙarƙashin gado, kai harma ta inda ruwa ke bi ya wuce, amma fa Wanda zasu duba Ƙarƙashin gadajen mu dole su yi taka tsantsan saboda ana ganin duk wani motsin mu, don haka Na ɗaki mu bari sai gobe zan shirya mana wasan Ƴar 6uya, zamu dinga shigewa da sunan mun 6oye kunga zasu yi tsammanin wasa muke Yi, ba wani abu muke nema ba”

Murmushi su ka saki gaba ɗayan su, kafin daga bisani Batul ta rarrabasu zuwa gida uku, Nan fa suka baza cikin toilets ɗinsu suna neman ƙofar nan, Angel tana ruƙe da hannun Azeeza saboda makantarta, Uban gumi suka haɗa akan fuskokin su, Sun bada himma sosai, wurin neman ƙopar ba inda basu ɗaga ba, hatta tukunyar fulawar da ke a toilet ɗinsu saida batul da Deeja suka haɗa ƙarfi wurin ɗaɗɗagota amma basu ga komai ba, Bangon da aka jingine ta dashi ashafe Ya ke haka ƙasantama Ashafe Yake babu wata ƙofa, Kamar zasu fashe da kuka su ka sauke tunkunyar, furennin cikin ta ma duk sun bushe babu mai lafiya, Ko’ina Ciki da bai na sashen toilet ɗinsu saida suka bincika amma babu ƙopa, A ƙarshe sarah Ta hango masu Tagogin nan da ke a saman ceilling waɗanda tun farkon zuwan Angel ta yi tozali dasu a garƙame da kwaɗo, Kowani toilet akwai tagogin saman ceilling guda biyu, hankalin su gaba ɗaya ya karkata akan tagogin ransu ya gama basu cewar Za’a samu hanyar da zata 6ullar da su wajen kurkukun, Sai dai basu san ta yadda zasu Iya kaiwa gare su ba saboda basu da tsauni tsayin su kuma ba zai kai su ba, hatta Sarah Da tafi su tsawo bazata Iya koda ɗaga hannu ta ta6a jikin su ba, Bayan haka kuma basu da Makullin da zasu Iya buɗe tagogin, daga bisani tunani su ya canza akan Su nemo makullan buɗe tagar, A daren ranar basu koma bacci ba, Saboda Aikin neman makulli, Sunci baƙara wahala ga bacci a idonsu amma Sun nace akan neman makullai, wasa wasa har Gari Ya waye suna aikin neman makulli, A ƙarshe da su ka galabaita, don dole suka haƙura, Ga yunwa suna Ji ga bacci a idanuwansu.

A saman floor na sashen toilets ɗinsu, Kowan nan su Ya samu wuri ya zauna suka fuskanci juna, Sai haki suke Yi kamar waɗanda suka Sha Gudu, Baccin wahala ne Ya ɗauke su mai nauyi, duk sun ɗaɗɗaura kawu nan su saman kafaɗun Junansu, Baka Jin sautin komai saina minsharin su.

Daga cikin ɗakin su muryar Jamimah ce ke ta ƙwala masu kira, babu mai jinta, farkawarta kenan daga bacci, Hankalinta atashe ya ke ganin babu su asaman gadajen su, saukowa ta yi daga saman gadonta, tare da nufar Sashen toilet ɗin su, shigar ta keda wuya ta yi arba dasu zazzaune suna bacci, Mamaki ne ya kama Jamimah, ganin su anan maimakon saman gadajen su, ƙarasa shiga ciki ta yi a yayin da ta ke leƙa fuskokin su don taga Idan baccin gaske su ke yi ko kuwa tsokanar ta su ke Yi, Kallon ƙurulla jamimah take binsu dashi, adai dai saitin fuskar Angel ta tsayar da eye balls dinta, muryar ta ƙasa ƙasa ta furta”My Genie” shiru bata amsa mata ba, da ta fahimce cewa dagaske baccin su ke yi, Sai ta zauna tare da kwantar da kanta saman laps ɗin Angel ta lumshe idanuwanta kamar maiyin bacci, Tsawon Lokaci babu wanda ya farka, Sun saki baki suna bacci.

A firgice Parveen Ta farka tana ambaton”Nagansu wlh nagansu” Sautin muryarta ne Ya farkar dasu Angel a fujajen su ka wawware Idanuwansu masu ɗauke da bacci suna kallon Parveen, Har suna haɗa baki wurin tambayar Ta”Makullan kika gani? a ina su ke”? Yawu ta haɗiya tana faman Zare ido, tare da ƙare masu kallo, Sam babu natsuwa atattare da Ita, Muryarta Ashaƙe tace”Kamar mafarki na yi nagan su a cikin ƙasar tukunyar fulawar nan, Makullan……..”

Tun kan ta ƙarasa maganar Zumbur suka mimmiƙe har suna bangaje juna wurin shiga toilet ɗin Saboda tsabar sauri, Jamimah batasan Kan me suke magana ba, binsu kawai ta ke Yi kamar bindi.

A Gaban tukunyar fulawar Su ka zuzzuƙunna, Deeja da batul na ƙoƙarin tsoma hannu cikin ƙasar Angel ta dakatar dasu ta hanyar yi masu magana”Bana so acire furennin nan saboda raine dasu, Ina gudun kada silar cire su su mutu……” Bata kai ƙarshen maganar ba, Deeja ta tari numfashinta”A halin da muke cikin yanzu bamu buƙatar furanni, ganinsu ma ƙara tayar mana da hankali ya ke yi, don haka cire su zamuyi” ba tare da 6ata lokaci ba, Mutun Biyar ne su ka tsoma hannayensu Ciki, duk suka tsige furennin tare da jefar dasu ƙasa.

Hankalin Angel sam ba akwance ya ke ba, Saboda ta yi believing da furannin rai Ne dasu, Ko da su Deeja su ka jefar dasu Ƙasa da sauri ta zuƙunna ta sanya hannu ta ɗauki furen daddynta dana Aunty aneelerh hada ƙaramin furennin nan, Har zata miƙe idonta Ya sauka Akan Dogon furen nan da ganyen shi ya koma baƙi, yanzu ya koma asalin colour din shi, Punch pink Ya ciza sosai, hakanan ta dinga jin gabanta Na faɗuwa, Ayayin da ta ke kallon shi, Kasa miƙewa ta yi har saida ta ɗauke shi ta hada da sauran furennin da ke a hannunta, tukunna taji Hankalinta Ya kwanta.

Fasa ƙara Azeeza Tayi tare da faɗin

“Mun samo shi! Gashi nan Makulli ne” jin muryarta Yasa Angel matsowa kusa dasu, Hankalin kowa Akan hannun Azeeza Ta damƙe wani abu dake a nannaɗe Cikin ƙasa, Wani irin farin Cikine Ya bayyana akan fuskokin su, Tun kafin Ta buɗe masu tafin hannun nata su ga menene.

A hankali Azeeza Ta ware tafin hannunta, Ta soma kakka6e ƙasar da ke nannaɗe da abunda ta damƙo, ko da ta kammala Kakka6e ƙasar jikin shi, Murnar da su ke yi ta koma Ciki, Ashe jijiyar fure ce, tsabar takaici Yasa kowaccen su ta dafe goshin ta da hannu, Ƙululun bakin Ciki Ya tokare masu maƙoshin su, Ji su ke kamar su rufe Azeeza da bugu, don ba ƙaramin sanya rai su ka yi ba, Kamar masu zaman makoki Haka suka zazzauna Cikin toilet ɗin Abun duniya ya ishe su, Jamimah ce kaɗai a tsaye ta ruƙe qugu Tana bin su da kallo.

“Wai ni kun barni aduhu me ake nema ne? Duk kun cire mana furennin mu, Genie Ki fada mini,” hada ƴar shagwa6arta

Ɗago da ido Angel ta yi tare da kallonta kafin ta miƙa mata hannu”Zo nan” matsawa ta yi kusa da ita, Ta sanya hannu biyu ta janyota zuwa jikinta

“Yaushe kika farka daga bacci bamu sani ba”? Yatsina fuska ta yi”tun ɗazu na farka ina ta kiran sunayen ku babu wanda ya amsa mini, Sai da nazo sashen toilet tukunna nagan ku kuna bacci, ni kun barni a ɗaki”

Harara Azeeza ta watsa ma Jamimah kafin ta soma kwaikwayon maganarta, salon jan faɗa, Hakan ba ƙaramin dariya ya basu ba.

“Yanzu fa ba lokacin Yin nishaɗi bane, Yakamata Mu nemi mafita, Ni dama tun farko raina bai bani cewar Akwai wasu makullai ba, Mu ɗin dai mune makullan, Ƙofa ce kaɗai zamu gano, Saboda a jawabin da tsohuwa Tamira ta yi mata cewa ta yi Mu ɗauka cewa mu ɗin makullan Wata ƙopa ce guda ɗaya wadda zata sama mana farin ciki, To kunga anan tana nufin we’re the keys da zamu buɗe ƙofar” Angel ce ta yi jawabin

“Ni kuma aganina akwai makullan, Ma’anar abunda ta ke nufi, Mu zamu haɗa hannu don mu gano su, Sa’annan waɗannan munafukan tagogin da suka zuba mana ido suna kallon mu, Ina zargin ƙofar tana A cikin su,” Deeja ce ta yi maganar, Kowa sai tofa albarkacin bakinsa ya ke yi kamar masu gabatar da shirin wasa ƙwaƙwalwa.

“Ni ma nafi hasashen acikin su ne za’a samu ƙofa, saboda su kaɗai ne hanyoyin da zasu Iya 6ullewa wajen ɗakin nan” Acewar Hibba.

“Ku dakata, Kada Mu ɗaura buri akan waɗannan Tagogin, Har yanzu fa akwai wuraren da bamu Bincika ba, Na farko akwai ƙarƙashin gadajen mu, Da kuma ɗakin tsohuwa Tamira” Yasmin ce ta yi maganar, Rubina tace”Ai babu ta yadda za’ai mu iya buɗe ɗakin Tsohuwa Tamira, tun da mu ke bamu ta6a shiga ɗakin ba, saboda kullum agarƙame ya ke kuma babu makulli ta waje balle muyi tunanin balle shi mu shiga”

Gaddama ce ta 6alle atsakanin su kamar za su yi faɗa kowa Ya kafe akan tashi shawarar, Sai tada jijiyoyin wuya suke Yi, Ko yunwar cikin su basa Ji ga Jikinsu da ke ta tsami saboda rashin wanka, Hayaniyarsu ta cika ko’ina, ganin zasu hargitsa mata lissafine yasa ta dakatar dasu ta hanyar daka masu tsawa, Nan fa kowa yaja bakin shi yai shiru, Hankalinsu ya koma kanta, Miƙewa tayi tsaye kamar malami agaban ɗaliban sa, A tsanake ta soma magana.

“Idan har mu ka rasa natsuwar mu to kuwa ba zamu ta6a Iya gano ƙofar nan ba! Mu kan mu hankalin mu ba a kwance ya ke ba, ta ya ya ku ke tunanin zamu Iya gano ƙofar bayan mun ƙi haɗa kan mu, mu sanya natsuwa wurin bincikota”? Ta jefa masu tambayar tana ƙare masu kallo, duk sunyi ƙuri da idanuwansu,

“Maganarki gaskiya ce Angel, komai yana buƙatar kwanciyar hankali da natsuwa, Yanzu ki faɗa mana me ya kamata mu yi? Tun da kinfi mu kaifin basira”

Murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, Jin an wasa ta, Miƙa ma Jamimah furennin dake a hannunta tayi tare da cewa”Ruƙe mini su My little sis” Kar6ar furannin Jamimah ta yi a hannunta.

“Abu na farko da yakamata Mu fara yi shine mu tsaftace jikin mu, ta hakanne zamu Ji daɗin Jikin mu brain ɗinmu ta yi fresh, mu samu natsuwar fara yin bincike na hankali, nasan kafin mu kammala Yin wanka Giants sun kawo mana Ganye, Idan mu ka Ci mu ka ƙoshi Sai mu fara wasan Ƴar 6urun 6urun kamar yarda na tsara mana, don kada ayi zargin wani abu tunda suna kallon duk wani moving ɗin mu”

Tun kan ta ƙarasa yin maganar, murmushi ya bayyana akan fuskokin su, gaba ɗaya sun yi amanna da maganarta, without wasting time kowan nan su ya miƙe tsaye, ɗaya bayan ɗaya suka fuce daga cikin toilet ɗin, Ya rage saura Angel da Jamimah, Kallon Juna su ka yi atare suka sakar ma Juna murmushi”My Genie, Ƙofar da zamu gudu ku ke nema mana?

Ɗaga mata kai Angel ta yi alamar eh, Dariyar Farin Ciki Jamimah ta saki har fararen haƙoranta sai da su ka bayyana, Bin ta da kallo Angel tayi dariyarta ba ƙaramin burgeta ta yi ba, sai da ta tsagaita da yin dariyar ta kuma cewa”Genie Zamu Koma Gidan ku da zama ko? Kuma can babu giants sannan ba zamu ƙara cin ganye ba ko”? Maganar da jamimah ta yi ba ƙaramin ta6a mata zuciya tayi ba, yadda suka ƙwallafa rai akan son zuwa gidan daddynta ba ƙaramin karya mata zuciya ya ke yi ba, duk idan ta tuna cewa ba lallai bane su samu damar tsira dukkan su ba koda ace sun samu ƙopar, wata’ƙil ma babu wata ƙofa tunda hasashene kawai suke yi basu da tabbaci akanta.

“My genie kin yi shiru, pls ki amsa mini, inaso inji a ƙagare na ke,” yadda ta ke yin maganar farin cikine tsantsa akan fuskarta, tuni idanuwan Angel sun cicciko tab da ƙwalla, sam ta kasa buɗe baki ta amsa mata.

“Genie Am talking to u pls ki amsa mini, idan ba haka ba zan cinye furannin da ke a hannuna” Ta yi maganar tare da yin kamar zata cinye su, Nauyayyiyar ajiyar zuciya Angel ta sauke tare da cewa”Kada mu 6ata lokaci My little sis, Zan yi maki wanka amma kafin nan ki taya ni mu mayar da ƙasar tukunyar nan sai mu mayar da furennin” Amsa mata tayi da toh.

Ba tare da ta ƙara tambayar Angel ba, Atare su ka zuƙunna jamimah ta kwantar da furennin a ƙasa, kafin su ka sanya hannu Suna ɗibar ƙasar da ke a ƙasa suna zubawa cikin tukunyar fulawar bayan sun kammala Angel ta ɗauki furennin ta tsirasu Cikin ƙasar, har ta yunƙura zata miƙa Karaf idanuwanta su ka sauka akan wasu furenni guda biyu da ke yashe ƙasa, ƙura masu ido ta yi tana kallonsu Jamimah sai magana take yi mata amma sam bata Jinta,

Wani irin faɗuwar gaba taji tamkar zuciyarta zata faso ƙirjinta, a matuƙar ruɗe ta ke kallon Furennin, Ganyen jikinshi ya bushe ƙasa ya mutu, bakomai ya faɗo mata araiba face Majnoon da Unaiza da suka rasu, Zazzare idanuwanta tayi Hannunta ɗaya dafe da ƙirjinta, Nan take ta fahimci cewa furennin su ne suka mutu, Tun da basa araye that mean sauran furennin dukkan su rayukan ƴan uwansu ne akai, A hanzarce ta ɗaura eye balls ɗinta kan Dogon furen nan Muryarta Na rawa ta furta”DA…NISH!”

Zungurar hannunta jamimah tayi hakan yasa tayi firgit ta dube ta

Fuskarta a ɗaure tace”Kin shanyani Genie, ko ba za ki mini wankan bane? Inje inyi da kaina” Yawu ta haɗiya zuciyarta duk ba dadi, Furen Danish ya tsaya mata aranta, musamman da ta tuna da Lokacin nan da ta tarass Ganyayyakin jikinshi Sunyi baƙi sosai, tana ji aranta cewa wani mummunan abune ya faru dashi wanda silar hakan yasa furen shi canza launi,

“Genie!!” jamimah ce ta ambaci sunanta da karfi ganin ta ƙara shiga zurfin tunani, Numfasawa tayi tare da ruƙo hannun Jamimah, Cikin sanyin murya tace”Am sorry Muje inyi maki wankan” Tayi maganar tare da janta zuwa gaban fanfo, Ta cika bokiti da ruwa ta ɗauko kwandon soso da sabulu, Bayan ta cire mata kayan Jikinta ta ɗaura su saman igiya, wanka ta ke yi mata amma hankalinta gaba ɗaya yana akan dogon Furen nan, A shiririce ta gama Yi mata wankan hada sumar kanta ta wanke mata, bayan ta kammala bata mayar mata da uniform ɗin jikinta ba, saboda sun yi datti, sai tace mata ta koma ɗaki ta Ta lullu6e da bargo kafin kayan da zata wanke mata su bushe saita maida su a jikinta, bayan fitar Jamimah daga Cikin toilet ɗin, komawa Angel tayi gaban tukunyar fulawar ta zuƙunna tana ƙarewa Dogon furen kallo, Yayin da zuciyarta ke harbawa da sauri da sauri, Yatsun hannayenta na kerma ta ɗaurasu kan furen tana shafa leaves ɗinsa, Har cikin zuciyarta ta ke jin kamar sumar kan Danish ta ke shafawa, A hankali ta rufe idanuwanta a yayin da ƙwaƘwalwarta ke tariyo mata Rayuwar su ta baya dashi, baza ta ta6a manta Rana ta farko da ta fara Yin tozali da kyakkyawar fuskar shi duk da bata a cikin kwanciyar hankalinta sai da gabanta ya faɗi ganin irin baiwar kyan da Allah ya yi mashi, Tana matuƙar ƙaunar danish, Jin shi ta ke yi tamkar oxygen ɗin da ta ke shaƙa don ta rayu, taya hankalinta zai kwanta? Bayan ta riga da ta gane furen Masoyinta ne, idanuwanta sun yi maraicin shi, zuciyarta sai azalzalarta ta ke akan ta nemo shi aduk inda ya ke, don taga awani hali ya ke ciki, ya idon shi ya ke? Meya faru dashi da har furen shi Ya canza Launi…………”

💔PRISONERS💔

Hankalin su Yaƙi kwanciya Jin shiru Angel bata fito daga Cikin toilet ɗin da ta shiga ba, Tun suna saran fitowarta har sun fara tunanin Anya kuwa lafiya? Ita kaɗai ya rage ta fito su fara wasan Ƴar 6urun 6urun, don su gano inda ƙofar nan ta ke, tun ɗazu Giats sun kawo masu Ganye kamar kullum tare da ruwan zafi, babu wanda yasan da cewa An kawo masu abinci.

Jamimah kaɗai ta rage a cikin ɗakin nasu, kwance saman gado ta lullu6e jikinta da bargonta, Jin motsin shigowar Giants, ta yi hanzarin yaye bargon data lullu6a dashi ta yi ɗaurin gaba har yana jan ƙasa saboda rashin tsawonta, Ahaka ta nufi ƙarƙashin gadon batul ta ɗauko kwandon abincinsu taje ta zuƙunna agaban dining Carpet ɗinsu, ta kwashe ganyan Ta zuba masu Acikin kwandon, bayan ta kammala kwashewa, Giants suka Ɗauki farantan tare da fucewa daga Cikin ɗakin, Zama Jamimah tayi saman carpet ɗin, ta soma ɗibar ganyen tana Ci yadda kasan ƴar akuya, Kunnuwanta har motsawa su ke yi saboda daɗin da ya yi mata.

“Angel ke fa mu ke jira! Tun ɗazu kowa ya fito daga wanka, Saura ke kaɗai kin shige toilet kin garƙame ƙofa kin barmu a tsaye” Deeja ce ta yi magnar

Batul tace”Ko dai ta fito daga wankan ne bamu sani ba? ta yi tambayar tare da yin saurin juyawa ta shiga ɗakinsu, Jamimah ta hango zauna tana cusa ganye abakinta, babu alamun Angel acikin ɗakin, dawowa ta yi sashen toilet ɗin tun kafin su tambayeta ko ta ganta, ta riga su cewa Na duba bata a ciki,

Nan fa hankalinsu Ya ɗungunzuma

Sunanta suka dinga kira shiru bata amsa masu ba, Atare suka haɗa ƙarfi wurin bugun ƙofar sai dai ga dukkan alamu An garƙame ta da Jamlock, Tamkar zasu fashe da kuka suka dingayi mata magiya akan tayi masu koda tari ne don su san cewa tana acikin toilet ɗin, saboda su samu hankalinsu ya kwanta amma shiru Angel bata tanka masu ba, kamar zasu 6alle ƙofar saboda Yadda su ke kai mata zazzafan naushi da hannayensu, a ƙarshe da suka Gaji agalabaice suka zuzzuƙunna Haɗi da jingina bayansu Jikin bango, jin motsin shigowar mutun cikin sashen Yasa suka kai idonsu ga mai shigowa,

Jamimah ce ta shigo hannunta ruƙe da kwando ta ajiye masu shi a tsakiyarsu, Bakinta a cunkushe ya ke da kingin ganyen da bata ƙarasa taunewa ba ahaka ta ke yi masu magana,

“Ku ci naku ne na kawo maku” kallonta kawai su ke yi, Ta zumbula bargo ajikinta sai ja da ƙasa Yake yi, jin sunyi shiru basu tanka mata ba, yasa ta haɗe girar ta”Ni ba ruwana Idan ba ku ci ba, Ku yunwa zata kama, Sannan Ina GENIE ɗina ta ke? Ko haryanzu bata fito daga wankan bane?

……………….. WHERE’S ANGEL❗❓

*Ayi min afwa bazan samu damar Yi Weekend ba kamar yadda nace zanyi maku, Zan haɗa maku two pages Ranar monday Complete kenan Takun farko, In Allah yakaimu da rai Da Lafiya, daga Monday zan ɗauki hutu, kafin acigaba da middle step, saboda in samu natsuwa kafin in dasa, ba jimawa zanyi ba, ƴar tazarace, Ga masu son cigaba da Karanta Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne kacal, Labarin yanzu nake Cikin rubuta shi babu Complete sai dai ka biya asanyaka agroup inda zaka dinga samun update akai akai, Inka biya za’ayi adding naka a paid group kuma za’a sanyaka a comment section, Sa’annan Ba’a share Ko yin forwarding duk wanda yayi gigin fitar da littafin, akwai ta inda zamu ga sunan shi da alamar yayi forwarding to zamu cire shi a group ne👌 Kuma yaja ma kanshi zamu ɗauki mataki👌*

*Littafin Kurkukun ƙaddara 3 part ne, Yanzu muna gab da ending na Takun farko free kenan, Sai kuma Takun tsakiya wanda ya kasance na kuɗi ne, da takun karshe duk akan 500 zaku karanta shi*

*Ga wanda ya shirya Yin payment, ga details nan, Idan ka tura kuɗin zaka bamu shaida, Bamu kar6ar kati, Ta bank ake turawa ko ta pos, In yaso saika ɗauko hoton reciept ka tura mana*

*3196407426*
Bature Hafsat Muhammad
First bank

*Zaka tura da shaidar Biyanka ta wannan Numbers ɗin (0816985 6268) ko kuma ta (08103884440)*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button