Sponsored Links
Hausa NovelsJarababben Namiji Hausa Novel

Jarababben Namiji 8-9

Sponsored Links

*8-9*

A wani ritsitsin Anguwa suka kutsa kai , wajen jaɓajaɓa yike ,inda mafiya yawan mazauna unguwar hausawa ne .
A wani gidan sama suka kutsa kai mai jerin ɗakuna sama da ƙasa fiye da talatin,gidan daga gani kaga irin daɗaɗɗun ginin nan .ta wani fatattakakken gareji suka bi zuwa farfajiyar gidan .

Aiko danƙam yacika da kaf mutan gidan dama ƴan waje wato dai ƴan kallo,shikuwa mai hayan yasa wasu ƙarfafan Almajirai sun karye ƙwaɗon ɗakin sunata watso masu kayan waje

Jiki na rawa mairo tashiga ɗakin ta zuba gwuiwoyinta a ƙasa faɗi take “oga land lord kiyi haƙuri ga babana nan zai biya ka kuɗin ka ” tafaɗa da tsatsaman hausan ta da ba’a cika fahimta ba

Tsaki yayi ya hamɓareta da take ƙoƙarin kamo masa ƙafa “uban naki tun yaushe yike alƙawarin zai biya amma yaƙi biya ,fiye da wata uku ,to nagaji nima kubar mun gidana dama naji labarin uwarki ma ta gudu dajinku neman magani ciwon yunwa na shirin aikata lahira…ku kafaffu kunƙi tafiya,saboda raina usuli da kwaɗayin zaman Lagos to ai gaku gayinan a zauna mugani…kai kuwatso mun sauran waje” ya ɗaga murya yina magana da yaran .

Tagumi baban mairon yayi saiga hawaye shaushau,tunda ya kife kansa a gwuiwa bai ɗagoba har ya ƙarike cin mutuncin sa suka sama ɗakin sabon kwaɗo suka futa suka bar masu tulin kayan su a tsakar gida, mutane ƴan kallo haka suka watse suna masu dariya da Allah ya ƙara

Zuwa mairo tayi a hankali ta ɗago kan baban nata kafin tace”Baba ina zamu yanzu?”
cikin makyarkyatan murya yace bansaniba mairamuu…ƙur yayi mata da ido kafin yace “Mairamuu mai kikaci yau kinajin yunwa ko?”
“Baba nasha wani sauran koko na shekaran jiya ɗazu da safe, Amma Ni yanzu ma na daina jin yunwa kawai ina tunanin inda zamu kwana ne yau”
“Mairamuu muje gidan da nike aiki sai mu roƙesa ya bani kuɗin watan nan munema ko shagone mu zauna”
“Cibtsi ai garin nan yagama siremun kawai ka amshi kuɗin ka mugudu rigarmu”
Jim yayi cikin ɗan tunani saidai ganin ba mafita ya miƙe yina harhaɗa masu kayansu da kaf bai cika Ghana must go ba ,ya tattara tabarminsu ya haɗa ya ɗaure ya ɗaura akai yace “zo muje ƴar Baba”
Maƙe kafaɗa tayi cikin sangartacciyar muryarta tace “uhm…uhm Ni sai ka ɗaura mun kayan meye amfanin kaina ,inbar Baba na yina ɗaukan kaya”
Murmushi yayi kafin yace”Mairo mairamuu ƴar albarka Ubangiji Allah ya baki mai jin ƙanki… amma kibarni in ɗauki kayan nan kinga Ni tsohone inna wuce bamai kallona kukuma ƴan mata bai kamata ba”

“A’ah naƙi wayon Baba kaifa kake cewa Ni yarinya ce saurin girma nayi,kuma mama tace shekara ta sha shida ana sha bakwai”
“To ba’a ƙin ta ɗan yau ɗauki muje” haka ya Aza mata suka kama hanya zuwa gidan julayb.

****
Julaybib fitowarsa kenan maƙale da sabuwar budurwan da yayi bayan yasamu ya rabu da wata data liƙe masa kusan kwana biyar ta hana masa saƙat wai ita a dole aurensa take son yi ,duk inda zaije suna tare inma baifita da itaba saita biyosa,sex kuwa tutur ana aikinyi ba a office ba balle gida sam tayi masa kaka gida da kula wasu ƴan mata ,though yinajin daɗinta saidai an ce rai dangin goro shima zaiso ya ɗanɗani wasu ƙoraman daɗin ko banana ta samu canji,ai kamar abincine bakullum ake cin shinkafa ba,ana bukatar canji acewarsa fa😅

Saidai tahanasa sukuni don tuni takwaso kayanta ta tare masa a gida ,shikam shine da abu ya ishesa jiya yazo da wata budurwan wato wannan kenan suka kwana suka hantse suna sheƙe ayarsu harma tayo masa gayyan ƙawayenta biyu ,ya ƙwaƙula yacika masu aljihu,itakuma yabarta ta kwana . shine kuwa tsohuwar budurwan tasa mai suna Zakiyya tana ganin yashiga toilet ta kullosa sukayi dambe na mutuwa da yarinyar tako yima yarinyan jina jina daƙyar ƴan aiki da mai gadi suka ƙwaceta haka tafita yarkace yarkace batare da ta tsaya karɓan haƙƙinta ba.

Sosai ya ɗauki zafi akanta aikuwa bayan ta buɗe sane yayi mata kacakaca ya koreta a gidan sa.
To shinefa Allah ya basa ikon kubce mata har yaje ya roro wata inyamura suka shigo tare so,shine bayan sun gama abinda zasuyi ya rakota waje inda zaimagana da driver ya Kaita gida

Marvelously(cikin mamaki) yaga gate a wangale.
Cikin zafinsa ya fara ƙwallawa mai gadi kira saidai shiru bai amsaba,gaban ɗakinsa yaje nan ma shiru sai cukurkuɗaɗɗen labulansa da tasha datti da take karkaɗawa a iska yina buɗe cikin ɗakin da bakowa a ciki
Anan ya tabbatar da ba kowa
Waigowa yayi yina kiran sunan driver .
Da gudu ma’aikatan suka shiga fiffitowa daga inda suke suna rurrusunawa kamar dukkan su ya kira , sakamakon basu taɓa jin faɗarsa ba

Ya ɗaga baki zaiyi magana kenan saiga Baba mai gadi da ɗiyarsa mairo a baya da tulin kaya aka.

Cikin tsawa yace”From where Are You?…You stupid he goat? You went and leave my get opened what kind of nonsense is this?”(Daga ina kake…kai ɗan akuya kafita kabarmun get a buɗe wannan wani irin rashin hankali ne?) Ya faɗa cikin ƙanƙance ido da tsananin jin haushi
Tsurutsuru masu jin turancin cikin su suka yi sai wannan ya kalla wancan su sunkuyar da kai

Shikam Baba ɗan fillo jiki na ɓari ya ƙaraso gabansa yina pleading (roƙonsa) amma ina shi baima san abinda yikecewa ba .waigawa yayi wajen jama’an yina
“Jama’a kuyi mun rai ku shaidawa oga mai hayanmune ya kore mu kar shima yace zai koramu bamu da wajen zuwa ya taimake mu ko zai koreni ya bani ɗan kuɗin aikina”

Tausayin shine yakamasu haka suke girgiza kai ba mai iya tamka wa
Tambayar su julaybib ɗin yayi “what’s he saying ?”(me yike cewa?)
Jan numfashi dattijuwan da aka kawo masa da zatana kula da gidan tayi mai suna Baba rabi
Cikin rawar baki tace”oga wai ankore sa ne a gidan haya ,plz ayi masa haƙuri albarkacin budurwan ƴansa gata can tsaye” ta nuno Mairo dake tsaye da ƙullin kaya

Duk da Mairo bata fahimtar komai tana ganin annunota ,ta taho gabansa da sauri ko ina najikinta na saɓal saɓal kamar kazar boloras
A gaban sa ta tsuguna tana sharɓan kuka cikin hausan ta da baya fita tace
“Malam don Allah kayima babana haƙuri kabasa kuɗin sa gida zamu ka haɗiye faɗanka zaimaka amfani wajen wani mutumin don Allah”
Dukkan su dariya tabasu yanda take magana batareda tsoro ba .duk masu hausan ciki ƙunshe dariya suka shiga yi don dukda hausanta ba futa yikeyiba
Sarai sun gane taji haushin faɗanda akewa mahaifinta ne.
Waigowa julaybib yayi yina kallonta ,dukda bai fahimtar hausan nata .
Buɗe baki yayi zai magana amma a take Yamun bakinsa ya ƙafe ganin wasu lafiyayyu , cikakkun lumtsuma luntsuman na shanun ta da suka hargitso waje ta wuyar rigarta.

Tuni idonsa suka kaɗa a take ya
Ɗaga hannunsa yayi mata alamun nuni da tamiƙe.
“Ku wuce ɗakin ka zan nemeka inna dawo” yafaɗa da turanci

Zuru baba ɗan fillo yayi masa da ido ,itadai haka Mairo ta miƙe tana cinciɗa wuyar rigarta sama ta koma baya fakatan fakatan tana jujjuya ɗima ɗiman ɗuwawukanta wanda suka zauna das a ƙugunta mai yalwa.

Saka halshensa yayi yana laso halshensa na ƙasa.
“Seems like he didnt understand Please who can interpret ”
(Kamar bai fahimci abinda na faɗa ba wazai fassara masu)

Dukkan ƴan aikin suka haɗa baki wajen gaya masu abinda yace
Aikuwa zullo Mairo ta daka a take suma nonuwanta suka hau tsalle

Cikin murmushi wanda har ya bayyanar da dimple ɗinta takuma saka gwuiwoyinta a ƙasa
“Mun gode malam”

 

 

Oum Aphanan ce ✍️
[3/14, 06:42] Bamalli✌️: *Typing…✍️*

 

*JARABABBEN NAMIJI*

 

*Na…Oum Aphnan🌸*

________________________________

*ALHERI WRITERS ASSO.🖊️*

*A .W. A*

https://www.facebook.com/Alheri-writers-association-100452175039849/

________________________________

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button