Sponsored Links
Hausa NovelsJarababben Namiji Hausa Novel

Jarababben Namiji 87-88

Sponsored Links

*87 – 88*

Zuciyarta ne tahau bata wannan shawarin
Tuni ta hau shashek’an kuka
D’aga muryansa yayi “driver to teaching hospital”

“Me zamuje yi a asibiti?”
“A’ah ki tabbatar da we are safe kawai”
“Ni bazani ba mu tafi gida”
“Allah sai mun je, Nari ga da na ganoki tunda if baki yarda da had’ubar shed’aniyar nan ba ,da banga kina mun asaran hawayenki ba a banza”
Gaddaman nan bai k’areba har Saida sukazo asibitin koyarwan dake kusa da company d’insa.

Don dole ta bisa saboda itama tana buk’atar sanin dahir d’insu ko zuciyarta zata natsu.

Saida aka d’auki blood sample d’insu kafin akace suje su jira a reception.

Cikin k’ank’anin lokaci result yayi out, likitan hannu ya kawo sukayi musabiha “congratulations result is negative so bakuda wata matsala… Amma in kuna tantama still zaku iya dawowa bayan wata uku ,sai ku k’ara sakeyi.”

Sayayyar tsarabar da ba ayi ba kenan,tace abarshi in sunje can adamawan a siya.
******

Tunda suka isa hanyar garinsu take ganin certain changes .
Koina solar ga kwalta shar har rugarsu ,tuk’atuk’a har biyu ,banda wutar nefa da aka jawo masu

Cikeda murna da mamaki take kallon julayb
“Hmmm bae jibi,aikin da mukasamu wannan gomnatin ta tuna damu…mun zama kamar cikin gari ,kai allah ya shiwa wannan gomnatin da albarka”
“Amin ,amin baby gaskiya kam waje yayi kyau”
Suna fitowa mutanen k’auyen sukayi masu caaaa

Kowa nayi wa julayb godiya tareda shi masa albarka.

Kallon rashin fahimta tayi masa.kawai sai ya kauda Kai,ya mik’a mata Jakarta da ya cika mata da ‘yan dubu² vatareda ta sani ba,don yasan zataso rabon kud’i.

“Kishiga daga ciki ganinan shigowa nima,sai ayi mun iso”
Dalo ido tayi,to ai ba gidan namu
“To ki fita ki tambaya😊”
“Na shigesu kardai iyayena sun Mutune gomnati ta gine filin mu😢”
“Come on ,nan shine gidan baba nima nasha mamaki da nazo naga ya chanza”
“Kai yaushe kazo baka sanar daniba”
“Baby kije zan gaisa da mutane kinga suna taruwa”
Jan jakarta tayi ,tafito waje sukuku , cikin tsoro da mamaki

‘yan gidansu ne sukaji labarin zuwansu aiko saigasusu fito da gudu ,kaci6is sukayi da ita

Da sauri suka kar6a jakanta cikin d’oki sukayi cikin gidan dashi

Shikuwa saida yagama rabon kud’insa na k’aida kafin ya kirata waya ,wai tazo ta shigo dashi.

Lokacin kuwa an gama koro mata labarin aikin da yayiwa k’auyen Ashe duk shine yagyara garin ya kuma k’era ma babanta wannan k’erarren gidan .

Cikin zakuwa taje ta shigo dashi ,kafin ayi haka angama cika mata gabansa da cimmakatai iri iri ,banda soyayyen naman zabbi da dafaffen k’wai.

Yaci sosai kafin ya bi d’aki d’aki ya gaishesu ,sannan yayi masu sallama with intention gobe zai zo da wuri su wuce.

Har taxi d’in da sukayi tasha ta rakasa dukda bata kai ga yimasa godiya abunda yayi masu ba,kawai she reserve it ,sai sunje gida.

Anyi firar yaushe gamo ,saida suka k’ure a daki da mamanta kafin take shaida mata sun zo yimasu sallama ne zasuje gayar da dangin mijin ta da hutun amarci.

Shiru maman tayi tana jujjuya abun a ranta ,tsoronta d’aya Kar zancen mutane ya tabbata,dasuke cewa sun yi cinakin ‘yarsu sun kar6i kud’in harda canji

Ta6ata tayi “mama akwai damuwa ne?”
“Aah , dama dai inata jin tsorone ,amma kiyi hak’uri zan fad’a maki ,amma karki zargeni da rashin yiwa mijinki adalci watau abun ne yina bugamun kai,mun zama abun tsegumi a cikin karkaran nan ,nima kuma na fara tsoro saidai inda Allah ba komai…watau kinsan meke faruwa…yanzu haka bayan wannan gyaran garin da yayi Mana,ya bud’ewa babanki k’atuwar masana’anta daga wajen gari…ana fidda madaran shanu ana maidashi ta kanti ana d’urewa a buhu…man jikin sa d’inma suna wasu amfanin dasu na davam… Ya zuba masa maaikata harda wainda ba ‘yan kasan nan ba ,wai duk a k’ark’ashin sa suke ya bashi wajen halak malak,yanzu haka babanki gini yike yi daga cikin garin yola wai zamu tashi anan mu koma can yanda zai fi masa kusa da wajen aikinsa.
Anya haka zatayiwu babanki jahilinsa dashi ,ba zaginsa nike son yi ba amma a basa irin wannan waje ,ai dole mu shiga zargi …shikuwa ko a jikinsa fantamawansa kurum yikeyi…amma bakomai na barwa Allah za6insa.

“Ayya mama na yarda da julayb dari bisa dubu ,saidai mugu bayida kama,don haka zan hak’ura da tafiyan nan kurum,ni dama bason zuwa wajen danginsa nikeyiba,don na lura basu sona”

“Akul d’inki…kije ba abunda zai faru inshallah, sannan gameda danginsa zan baki addu’oin tsari da na mallaka amma ki tunamun in zaki tafi zan rubuta maki wannan zantuttuka da mukayi , Ina so suzamar mana sirri”

“Shikenan mama allah ka shige mana gaba.”

*****

Washegari suka wuce Lagos cikin kewar iyayenta ,kwana biyu tsakani suka wuce egypt tanan suka fara ,dama yayi masu scheduling daga Egypt ne su wuce America,sai Australia ,china sai su sauka a dubai daga nan su wuce saudiyya…tunda Egypt yafi kusa damu Africa ne,sai ma su tsaya suyi umrah da aikin hajji kafin su dawo.

Aikuwa maryam ta shana taga gari sun 6arji soyayya ,anan ne tayiwa julayb godiyan duk kyautatawan da yayiwa iyayenta batareda ko sanin taba.duk ko k’asar da sukaje sai tayi hotuna tayo tsarabar irin abubuwan k’asan da ita kanta… status kam kullum yina kar6an sababbin pix na amarya da ango.

Saida sukayi sati biyu da kwana hud’u kafin suka wuce sa’udiyya ,a lokacin batajin ko shayin turanci , abunda ta gane shine ka kwakwa6a indai zaa gane ai shikenan.

Garin sa’udiyya
‘karfe goma na daren garin suka sauka a k’asar.

 

 

 

Ouk Aphnan
[3/14, 07:13] Bamalli✌️: *JARABABBEN NAMIJI*

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button