Sponsored Links
Hausa NovelsJarababben Namiji Hausa Novel

Jarababben Namiji 101-102

Sponsored Links

*101 – 102*

Ranar wata weekend ne ya shigo d’akin nata,tana zaune da riga iya cinya ruwan sky blue ta k’ure fanka ga a c na aikinsa ,ta mimmik’e kafa tana shan romon kaza da irish.gashin kanta yayi kwance lam6ar a gadon bayanta sai sheki yakeyi,hannunta na dama da spoon d’ayan kuma handout ne tana karatu….ga d’an matashin cikinta daya dan fara turo rigar wanda yasa takuma bubbud’ewa.

Cikeda tsokana ya shigo yina “mai ciki…ehemm ganinan tafe”
Yunk’urawa tayi ta mik’e ta fara bubbuga k’afarta
“Ba nace ka bariba ,wallahi saika goyani ”
“Haba mai cik… sorry sorry na manta” zuwa tayi da gudu tayi sufa ta kamo wuyarsa ta sargafe hannunta
“Cincid’ani”
“Naga banu ”
Ya fad’a yina zunkud’ata saida ya gama kewayawa da ita kafin ya sauketa akan 3seater yina nishi
“Sai a ramawa kura aniyarta”
Kada idanuwarta tayi hmmm no way out….ammm baby inaso in kira mama tunsafe wayarta bayi shiga nakira na baba yayi ringing yafi sau nawa baa d’agaba…ko zaka kira mun su?”

“Topah subhanallah bari ingwada in gani”

Numbern baban ya cigaba da kira still baa dagawa daga karshe ma ,sai wayar in ankira a kashe.

Aikuwa tuni mairo ta burkice
“Na shiga uku, akwai matsala wayyo Allah na shiga uku… julayb ka kaini inga iyayena kar ka raba ganawarmu”

“Haba baby ya haka…daga rashin daukar waya sai zancen mutuwa …baki tunanin basu kusane”
“Eh nidai naji saidai wallahi kwana biyun nan ina mugayen mafarkai da ruggarmu plz ka kaini in gansu don soyayyan dake tsakanin mu🥲”

Rungumeta yayi yina Sha fa bayanta cikin sigar rarrashi “cool down ok?
Ki bari zamu cigaba da trying in har bamu samuba zuwa gobe zan shirya mana tafiya…”
Godiya tai masa takoma ta kwanta ranta a dagule har sauke wani zazzafan ajuyar numfashi takeyi mai had’e da fidda zazzafan huci.

Cikin k’ank’anin lokaci ta fara rawan zazza6i ,hakoranta har suna had’uwa a na juna.

Rud’ewa yayi ,tuni ya fyalla cikin gida yakira oumma ,tana zaune tana azkar da finger counter ,yarinyar dake mata aiki tana
Aikin matsa mata k’afa .a rude yike shaida mata Mairo ba lafiya.

Figar dan kwali tayi ta yafa saman tungujejen gashinta ,sukayi part dinsu da gudu..

Sun tarradda ita numfashi na fita sama²

A guje ya cunkuceta sukayi parking lot,oumma ce mai karfin halin tsayawa dauko mata doguwar riga da takalmi

Cikin urgent driver yaja suka tafi ,a accident and emergency aka wuce da ita…da sauri likitoci suka rufa a kanta bayan dogon intervension suka bata magunguna harda na barci

Suna fitowa julayb yabi bayan babban likitan

“Likita me ke damunta? Ja taimakeni kar in rasata,da yarona plz itace rayuwata”

Dafa kafadarsa yayi kafin yace “ka kwantar da hankalinka kawai stress ne da tension yayi ma kwalwanta yawa ,kaga kuma tanada juna biyu wanda yasa vericous vein dinta kumbura shine ya haifar mata da hakan…amma ko nan da ‘yan awanni zata iya dawowa daidai”

Godiya yayi masa a sa6ule yaje ya lek’ata tana kwance a gadon baccinta take haik’am…take wani tausayinta ya rufesa,baita6a lura da girman cikinta ba sai yau,ashe dama nonone da hips yake shanye girman? Ga abu rim a gaba har yanzu bai shiga 6 months ba….gaskiya in ta gama wannan makarantan bazata cigaba da wani ba sai allah ya sauketa lafiya.kuma dole in rage jarabannan don kar yazama ina shiga hakkinta”

A reception kuwa saida oumma taga ammata setting drip kafin ta koma gida tasa ‘yan aiki su hada abincin asibiti ,nihla da laylerh kuwa daketa damunta da waya tace su shirya su tafi kafin ta dawo.

Saida su nihla sukazo kafin ya wuce masallaci.

Fitarsa ba dadewa ta farka ,sheshekanta ya ankaraddasu “mamana ,babana karku mutu ku barni ,in hakan ta kasance wallahi nima binku zanyi”

Dagudu sukazo suka hau jijjigata

“Anty ….sorry…anty bazaki mutu ki barmuba muna sanki da fine baby da zaki haifan mana kinji”

Sai sannan ta dakata da samvatun ta bud’e ido tana tararar da hawaye…ana hakan sai gashi ya shigo

“Yaewa uncle zo tana kuka wai zata mutu tabi su babanta…dama babanta ya mutune?”

“A’ah wallahi”
A hankali ya karaso ya fara mammatsa mata kafarta dasuka soma tasawa

“Baby ki kwantar da hankalinki maki alkawarin ranar da kikaji sauki shagargari zan kaiki kiga baba kinji?”

Jinjina kai kurum tayi ta juyar fa kai ,tana shararar da wasu hawayen.

Tashin hankali kam sai wanda ya dad’u
A furgice yasa driver ya wuce dasu airport ,saida ya shirya masu tafiya kafin ya dawo ,still tana barci

Oum ya kira ya shaida mata zasubi flight din safe zuwa nigeria gobe.

Tambayarsa tayi lafiya? Nan ya shaida mata komai da ta fad’a masa .

Ajiyar nimfashi tayi “Julayb ,baa 6atawa mai ciki rai ,don haka dole kakaita taga iyayenta ai tayima k’ok’ari…don haka harda ni da su nihla duk zamu je”

Shikenan oum nagode”

Aikam tunda taji maganar tafiya ,ta mike zaune,sai fara’a karshe a daren ranar aka basu sallama.

****

Da sassafe tariga kowa tashi,ta fara hada kayan sarkokinta sai dogayen riguna masu fad’i yaji aiki da stones da6ada6a ,kudinsu kam kar ka tambayi tsadarsu,sai veil d’insu da takalma masu rufin gaba da budaddiyar baya masu asalin kyau.duk yawancinsu masu aljihune ,sune kayanda oum tasai mata a matsayin maternity gown.

Sai kusan 10 kafin duk suka fito cikin dogayen riguna da ita da oumma ,nihla da layla kuwa riga da wando suka saka jeans da tsadaddun top iri daya banbancinsu colour ,na nihla ja na layler pink

Har airport driver ya kaisu ,saida abby dasu asim suka ga tashinsu kafin suka juya gida tare da masu fatan sauka lafiya.

 

****

A dole jirginsu tayi branch a lagos ,kafin daganan su samu wacce zata kaisu adamawa ,but unfurtunately ba jirgin da zata tashi sai goben ranar .aikuwa sai suka kama expensive hotel suka sauka…

Kamar wasa ta dakko layinta na nigeria ta maida a wayanta ta kama dialing numbern su mama ringing biyu a na uku aka daga…saida gaban mairo yabada das ! Kafin tace “Assalamu Alaikum mamace?”
“Eh nice mairona kuna lafiya?”
Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke “mama ina babana?”
“Babanki na can vabban gida allah yayiwa liman rasuwa…ki kirashima ki masa gaisuwa”
“Innalillahi wainna ilaihir rajiun ,yaushe?”
“Yau kwana 2”
“Subhanallah …” Su nihla ne suka dameta da tambayan lafiya.
Dole ta katse wayar ,ta shaida mata baffanta ne yarasu

Sun jajanta mata ,dariya ta saki mai had’e da zubowar kwalla “nagode allah da ba su baba bane”
Yamma lis sukayi wanka suka sa hotel driver ya kewaya dasu suga gari.

A gaban wani filling station ne,suka sauka tareda balle taxi drivern hotel da masifa “kasan zaka sha mai ba sai ka shawo ka dawoba,kawai sai ka kama d’akko mu,kajamuyi ta amai ” hak’uri yayi ta basu ,amma tsaki sukayi suka fito daga gaban wajen shikuma ya shiga ciki.

Habawa saiga mutane sun masu yuuu an baibayesu da kallo
“La wallahi larabawa ne”
Wata gurguwace ta karaso inda suke cikin makyarkyatan murya tace “hajji sabil lillah”(hajiya sadaka saboda allah )

K’uri mairo tayi mata da ido kawai saita fashe da kuka,yi take harda shesheka da jan hanci kamar zata shide

Juyawa matar tayi zata gudu ,mutane kan fadi suke allah sarki ,tausayi gareta basu saba ganin musakan mabarata ba,yooo suda awakan kasansune ake basu buredi ina zaa ga nakasasshe a titi ,sai mu en nigeria”

Cikin gudu ² ta bi bayanta,jajayen idonta ta sauke akan matar ,kafin ta rankwafa da kyar daidai saitinta tana nishi.

“Kiwa girman allah hajiya karki cutar dani ,banda kowa sai kaina don allah da yarona ki taimaka” cikin murya mai karaji tace “Baba mai shara baki gane niba?…Nine mairon baba mai gadi nagidan oga julayb balarabe”
“K’alu innalillahi,mairo kece sauyin rayuwa tazo maki hakan ban ganekiba ,wallahi danaganku na aza larabawa ne…aina kike aure mike kinji ‘yata karki wahala da duk’uno”
Sharce hawaye tayi tana tuno tainakonta da tayi a rayuwa ,wai yau itace a nakas she ba k’afafu,duk iliminta ,wayewa iya girki sun tashi abundant.

“Mairo nace ina kike?”
Firgit tayi kawai saita kuma kecewa da kuka,su nihla ne sukazo suna rarrashinta ,tareda tambayar ta santane da larabci
Cikin harshen turanci tai masu magana

“Baba nayi aure ,kuma oga julayb na aura,wainnan kanninsane munzo gida paying visit ashe rabon zan gankine…Nihla wannan tareda ita mukayi aiki a gidan yayanku ta taimakeni ta rikeni tsakani da allah sanadiyyarta zan iya cewa na samu shiga wajen yayanku,ta koya mun karatu; girki;kwalliy;turanci kai bazan iya fadaba. ..oh my god”

Rungumeta sukayi suka jata gefe suna rarrashi .
Kan wani benci sika zauna bayan sun roki drivern ya jirasu.

“Baba ya haka ta kasance? Ina latifanki da ta barki kina bara?”
“Hmmm mairo na horeki da zama uwa ta gari,da fari nasan ni na saka latefa a hanyan bin maza ,saboda son abun duniya fararriya kararra ,saidai bayan mun bar gidanku,ta hadu da wani saurayinta yawwa wannan ahmadun abokin mijinki, ashe dan fashine,yana kashe mata kudi maras gaba don in sukayi sata in suka rasa yanda zasuyi da kudin saidai su zuvashi a ruwa,ni karan kaina na mallaki gidaje da motoci sanadiyyarsu ban saniva ashe bayan lateefa ta kasance karuwansu,harda ita ake fashin.har sai watarana suka fasa babban bankin GT aiko akayi tracing aka ganosu su basu saniba…cikin wani bakar rana yazo gidana zance saidai aka ritsasu anso su tsaya suka nema guduwa shine aka bude masu wuta a sanadiyyar kare lateefa aka dagargaza mun kafa da harsashi ,itakuma suka faffasa mata kirji da harsashi ko shurawa batayiba….”oushhhhhh ta dafe kirji tana amvalar da hawaye😭 kafin cikin dasashiyar murya ta cigava…..”sanadiyyan haka na zama gurguwa ,kuma banki ba tausayi suka kar6e komai nawa harda gidan da muke ciki muka dawo kwana a kasan gada…😭😭😭

 

Hawayene ya rinjayi
Maganarta “kiyi hakuri baba ,wannan shine kaddararki ,kuma ina fata zaki kar6eshi da hannu bibbiyu ,kicigaba da neman gafarar allah dayiwa lateefa addua allah maji rokon bawan sane.
Nihla sun tausaya dikda vajin abunda suke fadi suke yiba….

Rasa me zata bata tayi kawai saita tsinko zinaren wuyarta ta mika mata da dankunnen duka set din….ta ciro kudi ‘yan dubu rafa biyu ta bata,suma da sauri su nihla suka tsinko nasu zasu mika mata

“Aah mairo inna kar6a bina za ayi akwace kiyimun kwatancen inda zan ganki sai inzo”

Cikin kuka ta fada mata ,yawonda suka fasa kenan suka dawo hotel din da suka sauka,dama ba wanda yasan sunzo…

Cikin kuka suka shaidawa julayb da oumma incedent dinda ya faru harda mutuwar ahmad da lateefa.

Allahu akbar rayuwa kenan. Julayb yaji mutuwar ahmad ,har yanxu yina jin sonsa a ransa in bacin mace da ta shiga tsakaninsu…kuma ai itama taga wadarinta tunda ta kare da kanjamau ,ko yanzu tana raye ko a mace allahu aalamu

****
Dako sassafe Baba ta dako sammako ,duk da an hanata shiga haka ta zauna a bakin get har dagawan rana….
Cikin damuwar rashin zuwan baba su mairo suka fito zasu wuce,hannu sukaga ana daga masu…

 

 

 

 

 

 

Oum Aphnan✍️
[3/14, 07:16] Bamalli✌️: *JRRB NMJ*

 

 

*Na…Oum Aphnan🌸*

 

*ALHERI WRITERS ASSO.🖊️*
*A.W.A*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button