Sponsored Links
Hausa NovelsJarababben Namiji Hausa Novel

Jarababben Namiji 18-19

Sponsored Links

*18 – 19*

(Bissmillahilladhi la yadurru ma asmihi shaiun fil ardi wala fissama wa huwas samiul alim)
بسم الله الذي لا يضر مع اسمه شيء في الارض ولا في السماء وهو السميع العليم
(A’udhu bi kalimatullahi tammah min sharri ma khalaƙ)
اعوذ بكلمات الله التامة من شر ما خلق
“`Addu’ar kariya daga dukkan sharri“`

*JUMU’A KAREEM*

___Cikin oya² Baba mai shara ta wuce gidanta ,tun a tsakar gida take ƙwala kiran “Lateefa!…Lateefa!!”
Wata kyakkyawar budurwa mai matsakaicin tsawo da kewayayyen fuska ne ta fito daga ɗakin kunnenta manne da earphone ,tana fitowa ta gantsare a bakin ƙofa tana miƙa tareda jan hamma,saida ta natsa kafin tace

“Mom meya faru kike ta ihun kirana tundaga waje , kardai kicemun kin kuma yayibo bashin kine ,masu bashin sun biyoki don in hakane wallahi saidai a tafi dake don banida ko sisi a bank harda pos sai fifty Naira!😏”

Ƙarasowa tayi da sauri ta rungume ta “ke dallah ja can ko sannu da zuwa baki iya yimun ba? To yau alkhaeri nazo maki dashi amma mushiga daga ciki” tafaɗa cikin sigar raɗa² kamar marasu gaskiya

Saida tashiga wani wahalallen falo mai ɗauke da leda tiles da kujeru masu hannun katako yadin jikinsu sunji duniya sai table ɗin katako a tsakiya
Zama tayi akan kujera ta saki tumbi tareda ɗaura ƙafa akan tebur ɗin

Da sauri wacce aka kira da lateefan taje gaban wani tsohon firinji daya dafe yazama brown brown tsabagen tsufa ta buɗe ta ɗakko ruwan famfo dasuka ɗuɗɗura a gorina me sanyi da cup ta kawo mata ta ajiye

Ɗauka tayi taɗan kurɓa kafin ta ajiye tana faɗin “Wash!”
Cikeda Zaƙuwa Lateefa tace “mom meke going ne nasan ke ɗin gindin resit ne komai a bakinku akeji ,halan kinji fanshan babanmu marigayi zasu sakar mana ne?”

“Ke dayalla wani fensho ai wato wani hanyar samun kuɗi na samo mana ,Hmm wato indai kikayi aiki mai kyau cikin ƙanƙanin lokaci zaki fara fantamawa kizama babban yarinya me tunkaranki sai ya tara😹”

“Wu wu Allah ya bar manake momy akwai cika baki,menene ɗan shafamun inji”

Tasowa tayi ta soma kalle kalle kafin taje kunnen ta ta raɗa mata.

Ɓata rai tayi kafin tace “kai mom Ni bazan iyaba” tafaɗa taba kumbura baki .
“Ke ƴar ƙauye zauna nan ,to inma baki saniba kisani wai in don mazane ,kike ƙunƙume kanki Gara ki saki jikinki ,karwai ki aureshi yayi maki wulaƙanci ko yace you’re not a virgin ,to se me?😏 Ni fa yanzu kaina ya waye naje naga yanda mata ke karakaina wajen yaron nan suna bada jikinsu suna kwasan nairori, ke infa kinada kuɗin ki saikiyi komai ,inkin tashi auran iyaka aje wajen likita yayi maki kwaskwarima ,to wa ze gane?… amma inkince baki yardaba ruwanki , saidai fa kisani sarai nasan keda idi ƙwaƙular juna kuke shiyasa yike Maki wannan hidimar, kuma in ance ya fito ba aurenki zaiyiba.kingako gwara kije wajen mutumin nan in kintara ƴan matsabbanki sai aje ayi gyaran gabaɗaya”

Dariya ta sheƙe da shi”Hmm momy har kinsa naji kunyarki🙈 amma aikema inasane da Bello mai kilishi dake zuwa da daddare wajen ki , kuma nasan ne ku keyi”.
“Ke ja can rufamun baki,… kin san Allah sai kinyi shiri inba hakaba kallon banza baki ishesa ba , don ɗan rainin wayone ga yarfi da miskilanci”
Karki damu mom nine fa ,barima ki gani”

Miƙewa tayi tashiga gyagyara na shanun ta cikin bra suna daɗa zillo
“Ai mom indai munada wainnan ba mu ba jin kunya” tafaɗa tana daɗa watsalosu.

Thumb up tayi mata kafin tace”kinga yimun irin tafiyar da xakiyi in kun haɗe،”

Miƙewa tayi da sauri ta gyara riganta ta soma haɗe ƙafa ɗaya cikin ɗaya tana balance tareda yarfe hannu

“Woooouu yarinya kinyi ,kawai saita fara mata waƙa A beutiful lady doing cat walking on the street wiuuu” ta kama tafa mata
“Saidai ya kamata kina ɗan gantsaro ƙirjinki tareda ɗiwawunki at d same time , wannan tafiyar shi ake kira da cat walking if i gues well”
Hakane mom saima nayo hayan fitinannun kaya a wancan boutique ɗin wallahi ke kanki bazaki ganeniba …mom? Kije kawai kuɗin nan sai mun cisu bar mun sauran aikin”
“I trust You Latee” tafara mata waƙa tana tafa hannu
“Lateeti Lati ,lati ƴan mata lati ,lati an girma lati,lati sai aure latee”
Turo baki tayi “mtsww mom nace maki banason waƙannan yanzu haba”

(Allah ka kare mu da irin wannan hali, hattara gareku iyaye masu tunanin iya kaiwa likita ƴarsu din ya dawo mata da budurcinta ba wannan likitan komun kwaskwarima bayi original ,na Lye inji inyamuri🥴)

*****
Daga Ruggar dabo kuwa harɗo ne ya fito daga bukkan su shatu cikin tausayawa da jimami ya tadda ƴan uwan shatun a daga waje.
Da hillonci yake basu haƙuri kafin yace “inaga mai zai hana akira mijin shatu ,yazo daga kudun yaga halinda matarsa take ciki ,tunda suna Maraya ai inaga bazasu rasa kuɗi a hannun suba,don gaskiya wannan ciwon yafi ƙarfin maganin gida”

“Toh babansu fatsime bari a kira lawwali yaje wajen ƙauyancan yasamu masu salulan kuɗi ,yasa lambansa yayi kiransa a shaida masa”

“Wannan kam shine shawarar da tafi”

*****
A wajen business Centren ƙauyen ne lawwali ya cancano kekensa yina tafe yina zuƙar rake
Yina isa wajen ya miƙo masu takardar numbern wayan baba mai gadi
“Ku rafkawa wannan numbern kira zuwa birnin ikko in kuna iyawa”
Tsuki suka ja kafin su karɓa aiko tuni ya fara ringing

“Woohoohuuu sun ɗano masa kira ”
Sai gab da zai katse ya ɗauka.
“To ai saika riƙe don kuɗinka ke tafiya ,don in ɗari kaci baka barin wajen nan saika biyasa cas ,ko in tafi da kekenka don ku ƴan rugarku Allah ya zuba maku zafin san abin duniya”

Karɓa yayi ya kanga wayan a baki yina ihu a dole yina waya .
“Baban Mairo ,shatu ba lafiya rai ga hannun rabbana ,kai maza ka taho gida kar a rasata”
Yina gama faɗa masa baijira ta cewarsa ba ya miƙa masu wayar .faɗi yake “Nawanaci”
Aka faɗa masa ya biya ya daɗa cancanan kekensa yayi gaba.

Yina barin wajen kiran baba mai gadi yashigo dayike ba kati a wayarsa saida yaje yasayo

Amsar ɗayane wanda yakira ya tafi wajen masu hayan wayane.

Ciikeda zullumi yafito ɗaki yina mai cire malfarsa tareda sharce zufa damuwa fal fuskarsa

Adaidainan baba mai shara ta dawo gidan.ganin baba akan bencin sa tace”sannu da gida baban Mairo?”
Shiru ba amsa hankalin sa na can wani wajen
Matsowa kusa dashi takumayi ta ƙwala masa kira a firgice ya ɗago ya kalleta
Cikin jimami take tambayarsa meke damunsa

Bai iya ɓoye mataba ya shaida mata halinda ake ciki

Har ga Allah ta tausaya masa ,cikin fuskar tausayi tace”to pah munshiga uku mu yaya zamuyine?…kanama da kuɗin motan zuwa Yola kafin ayi taɗin na zuwa ƙauyen ku?”
“Wallahi banidashi Hajiya ina ganin ,zan sa a roƙanmun me gidane ya bani albashi na iya na kwanakina inyaso ko a Boot ɗin motane inyi maleji har inkai”
“To ya za kayi da Mairo anyae?”
“Nabarta hannun Babanta (yina nufin ita)”
“Shi kenan da ikon Allah zaka yabama riƙona ,zan riƙe amanar Mairo…ai Mairo ƴace ,uhm Mairo ?😁 Karma ka damu gobe kayi sammakon shirinka Ni zan roƙi oga yabaka na mota ai laruri ya huce komai” Tafaɗa tana washe baki
[3/14, 06:45] Bamalli✌️: *Typing…✍️*

 

*JARABABBEN NAMIJI*

 

*Na…Oum Aphnan🌸*

________________________________

*ALHERI WRITERS ASSO.🖊️*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button