Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 53

Sponsored Links

53
DZ

“Ina hanya,yanzu zamu iso,koma meye idan nazo ka tambaya” abunda ya fada kenan sanda yake jingine da motarsa a farfajiyar gidan saukar baqin,saiya latse wayar kawai sanda yaji amirun nason masa cari,ya soma sanya wayar a aljihun wandon shaddarsa,lokaci guda kuma yana daga kansa.

A kanta idanunsa suka sauka,tana sanya da atamfa riga da zani,sai mayafi wanda yayi matuqar dacewa da kayan jikinta.

Kyakkyawar kalar fatarta ta haska tarwai cikin kalolin kayan jkinta,kwantaccen gashinta me santsi ya fiti ta gefe da gefan kunnenta,da kuma qeyarta inda ta nadeshi kamar alkaki.

Baisan sanda ajiyar zuciya ta kubce masa ba,yana tuna yadda hannunsa ya dinga yawo a jikinta daren jiya cikin mafarkinsa,wani abu ya tsarga masa sanda ta daga fararen idanunta suka sauka akansa,saiya sanya hannayensa duka cikin aljihun wandonsa yana qyara tsaiwarshi da kyau.

Faduwar gaba taji sosai,karon farko data ganshi da shigar da bata taba ganinsa da ita ba,shigar shadda fara sol sai maiqo da walqiya takeyi,wadda akayi mata aikin zare baqi,takalmi sau ciki wanda shima yake nashi kalar qyallin,hannunsa sanye da Rolex me asalin tsadan,sumar kanshi wadda bata da wani yawa sai sheqi takeyi saboda hularshi dake aje saman motar bai sanya ba.

Hardewa taji ta fara yi saboda takalman qafarta masu dan tsinin dunduniya da sukayi mata kyau suka kuma sake qawata kwalliyarta.

Tana dab da isowa inda yake ya sanya hannunsa saman motar ya.janyo hularsa ya aza a kansa,har a sannan bai fasa kallonta ba.

“Kinyi kyau” kalmar data subuce masa a bakinsa kamar fitar kibiya,hakan ya qara aza mata nauyinsa.

A hankali ya kutsa da motar cikin layin gidan ya dikko,duk kuwa da saurin da ya dinga yi amma hakan baisa ya iso a sanda yaso ba,saboda wani laziness da yakeji a jikinsa gaba daya,a hankali ya dannan wani madanni dake gefansa ya dage dukka gilasan motar sama sanda yake yiwa motar gun tsaiwa,hannu tasa zata bude motar

“Wait” taji ya fada,hakan yasa ta tsaya din kamar yadda ya buqata,ta qagauta ne su raba jaha,don ita kadai tasan wanne yanayi take riskar kanta a ciki duk sanda suka kadaice irin haka,wani mugun nauyi da kunyarsa takeji fiye da kowanne lokaci.

Wayarsa ya ciro ya dannan numbers din jawahir, ringing biyu ta daga,zata barke masa da surutun nan nata ya dakatar da ita,yace ta fito ya sameshi a waje,sannan ya aje wayar .

Daga nesa ya hangi fitowarta,tayi duru duru tana nemansu,saiya dan danna mata horn sannan ya bude motar ya fita,dai dai nan ta iso,saiya dan saka kansa kadan yace da kaltum din ta fito.

“Wai a ina kuka kwana kaltum?” Ta tambayi kaltum din cikin mamaki da kokwanto,saidai kafin tace komai samir din ya tsaidata

“Ba’a sani ba tambaya,ku wuce muje” bata qara tambayar ba,saidai tana mata susa a rai,tare da tambayar kanta inda sukaje suka kwana,kuma su biyu,ba muharraman juna ba,duk da cewa ta yarda da hali da dabi’ar yayan nata,dama ta kaltum din.

Suna gaba yana biye dasu a baya,duk da jama’a na tsaidashi suna gaisawa,duk inda ya wulga sai ya dauki hankalin jama’a,farinji da kwarjini gareshi,uwa uba yadda yake kyautatawa al’umma ya siya masa soyayyar jama’a me yawan gaske,a haka suka isa babban falon yadikko,wanda yalwar gidan da wadatar guraren zama ya sanya babu yawaitar mutane,kusan suna dakuna……

“A ina kika samo wannan beb din……ban santa ba a cikin danginmu” daya daga cikin samarin dake xaune a falon ya fada,abinda kuma kunnuwan samir suka jiye masa sanda yake shigowa,idonsa ya sauka kan yaron wanda ake kira da muntasir.

Sallamarsa yasa maganar da yake shirin yi ta yanke,duka suka waiwaya,sannan suka miqe cikin nuna girmamawa suna masa sannu da zuwa kafin su fara gaidashi.

Fuskarsa a hade tsam ya kalli jawahir

“Ina mummy?”

“A gidan haj shuwa ta kwana,amma munyi waya tace min ta taho,duk yadda akayi ta kusan qarasowa” ido ya lumshe kana ya bude cikin sakannin da basu wuce biyu ba,haka kawai cikin zuciyarsa jininsa baya son matar,kuma bazai iya tuna wani laifi data taba yi masa ba,koda na kallon banza kuwa

“Ki rakata wajen hajiya qarama”

“To” ta amsa masa tana yin gaba,kaltum tabi bayanta,saiya tsinci kansa da rakasu da ido.

Muntasir ya tabo dan uwansa

“Kaga guy din nan,ashe shima ya iya kallon mata?” Boyayyar dariyar ciki ya sake

“Waye baison mace dama?,aisu sunfi qarfin zuciya da qwaqwalwar kowa,saidai idan bai samu ba,bare wannan….ta wanku fa,kalar fatarta ta musammance wlh,ga wani kyau mai sanyi alaji,wanda saita matsoka kake ganinsa”,dif sukayi sanda ya waiwayo ya dubesu,don kalamansu na qarshe sun shiga kunnensa,baisan me yake taba zuciyarsa ba duk sanda sukayi magana irin wanann,dukansu ba sa’ansa a cikinsu,don haka ya miqe ya nufi bangaren dakin ya dikko don su gaisa,tun kafin daddy ya qaraso yaji basu gaisa din ba.

Fara’a fal fuskar hajiya qarama,farincikin ganin kaltum ya bayyana sosai

“Lale maraba da diyata,ina nan inata kewarki,dama yanzu nake shirin kiran saraki naji can gidan abokin nasa zaku yita zama ne?,sai amirun yacemin matar abokince bata jin dadi sosai,kin dan tsaya kin taimaka mata ta kintsa gidan” itadai murmushi kawai take,kanta a qasa tana jinjina yadda amiru ya iya tsara irin wannan qaryar,duk da tayi mata dai dai,don bata da kowacce amsa da xata bata.

“bari naje mu qarasa packaging abincin ‘yan daurin aure…..ina zuwa kaltum” ta fada tana juyawa gami da ficewa daga dakin,zuciyarta dai na tantamar labarin da amiru ya bawa haj qaraman kan rashin kwanansu gida,tunda a gabanta ne yake neman shima inda suka shiga,ture batun tayi,sabida batason baiwa shaidan qofa akansu,ta yarda da kowa a cikinsu.

Sai data zauna sosai sannan ta daga kai da niyyar gaida hajiya qarama,saidai gaisuwar taso.maqale mata a maqogaro,saboda sauka da idanunta sukayi kan wani hoto dake maqale a bangon dakin da yake tamkar na hajiya qaraman,saboda duk sanda tafiya ta kawosu azare a nan take sauka,idan zata tafi kuma ta rufe ta bawa ya dikko maqullin.

Hoto ne dauke da taswirar fuskar matar dake a jikin hoton data taho dashi zuwa azare,wanda tayi masa duban duniya amma ta rasa inda ta yada shi,gabansa kadan wani hoton ne irinsa,tana sanye da atamfa da akayi mata riga da xani,ta yane jikinta da mayafin atamfar,wadda ta haskata ta kuma fidda kyanta sosai.

Tattaro kalaman bakinta tayi tana gaida hajiya qarama,amsa mata tayi tana waiwaya bayanta don duba abindan ya dauki hankalin kaltum din haka,sai taga hotunan,hotunan da a kullum idan ta kallesu sai taji wani abu mai qarfi ya motsa mata,takan ji karyewa zuciya qwarai,har yau zuciyarta ta kasa gasgata abinda aka fada akan raihana,har yau ta kasa jin nutsuwa da kalaman da akayi a kanta,har yau zuciyarta tana gaya mata cewa tana raye.

“Suna kama ne da samir?” Hajiya qarama tayi mata tambayar tana murmushi gami da duban fuskar kaltum,maganar hajiya qarama ya sanyata janye idanunta daga kan hoton,murmushi yana subucewa daga fuskarta ta girgiza kai gami da saukar da kan nata qasa.

Shuru ne ya ratsa dakin na wasu sakanni kamar ba kowa a dakin,ajiyar zuciyar da haj qarama ta sauke yasa kaltum kallonta,suka hada ido,sai hajiya qaraman fa gyara zamanta

“Shekara kusan ashirin da takwas,amma har yau zuciyata ta kasa gasgata bacewar raihana…..wadda ta bace rana tsaka,sama ko qasa,a lokacin samir nada shekara biyar a duniya,bayan ana tsaka da wata hatsaniya,ba’a gama kamo bakin zaren ba,a yadda jidda tace…..a gaban samir akayi,tace ne ta gaji da zama da rashid,dama kara take mishi,ita ba sa’ar aurensa bace,akwai maza da yawa dama dake dakon fitowarta,ta bashi wata wasiqa data tabbatar da dukka abinda ta fadi cewa raihana tace,kuma tabbas kowa yasan rubutun na raihana ne,hatta da ‘yan uwanta sun tabbatar da hakan.

Hatsaniyar da ake tsaka da yi da kuma wannan abun daya faru ya haifar da gagarumar tsanar raihana a zuciyar rashid,abinda yasa ya karkade hannunsa daga batun nemanta,wannan ne kuma ya hasala danginta,wadanda ‘yan asalin qasar sudan ne,sukaga koba komai ai matarsa ce,kuma shine silar zuwanta qasar nan,bugu da qari su basu da ido a nigeria,shine zai shige musu gaba waje batun neman raihana,amma ya qeqasa qasa yaqi,yace dama can yana da hujjojin dake nuna cewa ita din bibiyar maza take,haquri yayi da ita,maimakon ya zauna a duba matsalar batanta,sai saki da ya rubuta mata ya baiwa ‘yan uwanta takardar,yace idan sun ganta su wuce da ita qasarsu” shuru hajiya qarama tayi tana sauke numfashi,da alama har kwanan gobe abun yana tabata bai wanke daga zuciyarta ba,yayin data jefa kaltum cikin zuzzurfan tunani.

“Tun kawo raihana qasar nan babu wanda ta shaqu dashi irina,hasalima a sannan tare muka qarasa karatu ni da ita,bani da aminiya kamarta saboda mu biyu mahaifiyarmu ta haifa,kamar yadda nima ta maidani ‘yar uwarta,a sannan ina gidana,ni naso karbar baquncin dangin raihana da suka shiga nemanta babu ji babu gani,amma saboda fusatar da sukayi sukaqi sauka,suka kama hotel…..lamarin da yayi matuqar girgiza mu shine,iyakar nema me sunan nema mun yiwa raihana amma babu ita babu dalilinta,cigiya kafafen yada labarai babu inda ba’a kai ba shuru maqatau,yan uwanta sun share watanni suna nema amma babu nasara,har suka koma qasarsu suna zuwa lokaci bayan lokaci amma har yau da nake baki labarin nan babu labarinta,wannan daliline yasa muka saddaqar cewa an sace raihana ne an kuma kasheta,amma inda tana raye ko da bata kawo kanta ba yadda cigiyarta ta watsu a na qasar dama waje….ba shakka ba za’a rasa wanda zai kawo rahoton ganinta a wani waje ba….”

Yan uwa raihana sun jima da sarewa,sunma tattara sun bar koda leqo qasar nan,lefin rashid ya sanya suka daina koda waiwayar samir,wanda shima bansan dalilin daya sanya tun tashinsa bai sha’awar yaje dangin mahaifiyarsa ba,tun ina masa maganar lokaci bayan lokaci nima harna haqura na qyale…..tabbas jikina har yau yana bani jidda tana da hannu kan bacewa da mutuwar raihana,har yanzu na kasa jin qaunarta a raina….kuma zuciyata ta kasa gamsuwa da soyayyar da take nunawa samir” maganar hajiya qaraman ta katse,da alama tana hadiyar dacin daya taso mata ne.

Dubanta kaltum keyi,itama tana jin wani abu cikin zuciyarta,tana kuma sake kallom hoton dake maqale,ba shakka itace a jikin hoton biba data dauko,to meye alaqar biba da mahaifiyar samir din?,meye haka yayi tasiri a ran samir daya sanya ya nesanta da dangin mamarshi?,meye alaqar matar dake gidan masu lalurar hankali da wannan matar?,tabbas akwai kamanni a tsakaninsu,saidai akwai wasi banbamce banbamce kuma data kasa ganesu,meye alaqarta da mummy harta ziyarceta a wanacan lokacin?.

“Na jima banyi wannan maganar da wani ba sai ke kaltum,bansan me yasa ba hakanan naji ina sha’awar baki wannan labarin,qila zaki tayamu da addu’a,addu’ar da har kullum mu masoya raihana mukeyi,kan koda kabarinta ne Allah ya nuna mana shi” qas tayi da kanta tana jin tunaninta na hautsinawa,yana son hada mata fuskokin nan uku waje daya

“Allah ya shiga lamarin?”

“Amin don nabiyyur rahmati” hajiya qarama ta amsa tana janyo wayarta,yayin da kaltum taci gaba da son daidaita makamar wadan nan zantukan da dukka hasashen zuciyarta a mizani guda,yadda zasu bata cikakken bayanin da take so.

“To ya rashid kodai suna hanya har yanzu bai qaraso ba?,gashi an kusa fara daurin auren,kuma wayarshi a kashe” hajiya qarama tayi maganar tana sauke wayar daga kunnenta,saita tashi ta na nufar qofar fita daga dakin.

A babban falon ya dikko sukaci karo da mummy,wadda ke keto falon cikin shigar alfarma ta wani baqin material daya haskata sosai,sai sheqin duwatsun da aka masa qawanya dasu yakeyi,tun daga wuyanta zuwa hannunta designers ne na jewelry daketa sheqi suma,bayanta kuma photocopy din tata ce wato najwa biye da ita,tana hura hanci tare da yiwa kowa kallon daya daya,kusan wannan din halayyarta ce,kada ma taga ‘yan son zuciya da neman gindi zama….hadi da masu ganin kimar mummyn saboda yawan kyautarta na miqa gaisuwa da girmamawa.

Cikin salon nan nata da koda yaushe take amfani da shi wato fara’a da sakin fuska take amsawa kowa,kafin ta maida hankalinta ga hajiya qarama ta soma gaidata,ba tare data damu da cewa ita dince matar yaya ba,ita ya kamata ta gaida.

Kamar ko yaushe ta amsa mata babu yabo ba fallasa,tayi gaba zuwa dakin ya dikko,mummyn na biye da ita a baya.

Tsohuwa ce sosai,don gaba daya kanta ya cika da furfura,saidai kuma yadda tayi quruciya me cike da nagarta da bin Alla sai tsufan nata yaxo mata da kyau,bata rasa baqora ba kamar yadda bata rasa hankalinta ba,hannu biyu ta karbi mummy kamar ko yaushe,saboda yadda mummyn ta maidata,kamar itace ta tsugunna ta haifi professor rashid.

Hajiya qarama na daga gefe tana ta gwada wayar professor din amma still dai taqi shiga,saboda sun riga da sunyi magana da ita kan cewar,zai iso nan da awa biyu ne,akwai ganawar da zasuyi shi da ita da ya dikko kan auren samir.

Tsaki ta danja sai duka suka kalleta

“Ya dikko na kasa samun yaya rashid,bansan ko matsalar network bane irin na qasar nan”

“Muna daya ashe,nima tunda na fito daga gidan hajiya shuwa nake gwada kiran nasa amma ban sameshi ba” mummy ta fada fuskarta na nuna damuwa,ajiyar zuciya hajiya qarama ta saki,ta duba agogo

“Amma yaci ace ma ya qaraso,indai ba fasa zuwan yayi ba”

“To Allah yasa lafiya” yadikko ta fada

“Ameen” duka suka amsa a kusan tare.

Ba kasafai ta fiya zama waje daya ita da mummy ba,amma wannan karon sai ta kasa tashi,taci gaba da zama a wajen.

Turo qofar da akayi ya sanyasu daga kai,kowa ya bawa qofar hankalinsa.

Samir ne ya bayyana,kana duban fuskarsa zakasan cewa cikin tsantsar tashin hankali yake,saidai yanata qoqarin dannewa da kuma boyewa,amma hakan bai boyu ba a idanun hajiya qarama,don haka sai ta miqe tsaye.

Cikin dakiya da qarfin zuciya yace

“Yanzu aka kirani a waya,su daddy sun samu hatsari a hanya,cikin bauchi” dukkansu suka miqe tsaye suna zabga salati,hajiya qarama hannu a ka a matuqar rude,mummy hannunta bisa qirjinta,idanunta a waje,hannu ya daga musu cikin son kwantar musu da hankali

“Karku daga hankalinku,ba wani mummunan abu bane ya faru dashi din,ban gayawa kowa ba,kuyi addu:a,zanje na duba yanayin da yake ciki nida amiru”…..

*_KOMAI NISAN JIFA….KUMA KOMAI NISAN DARE….SHARRI KARE NE…..ME SHI YAKE BI…. muje zuwa yanzu zaren zai soma warewa_*πŸšΆπŸΎβ€β™€οΈπŸšΆπŸΎβ€β™€οΈπŸšΆπŸΎβ€β™€οΈπŸšΆπŸΎβ€β™€οΈπŸšΆπŸΎβ€β™€οΈπŸšΆπŸΎβ€β™€οΈπŸšΆπŸΎβ€β™€οΈ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button