Sponsored Links
Duk Karfin Izzata Book 1Hausa NovelsHausa Novels and Love Stories

Duk karfin Izzata Book 1 Paga 5

Sponsored Links

Episode 5*

DON

Misalin karfe 5 na yamma jirginsu yayi landing a malam Aminu information Airport kano, wasu dan kare dan karan motochi 5 sukazo ɗaukansu ga motochi 3 chike da sojoji, basu wani ɓata lokachi a chikin jirgin ba suka fito tare suka jera, sai wani kara ɗaure fuska suƙe da ka gansu kaga wayan da akawa zuwa dole, musamman DON nashi daban ne, Abdol da Shahram suna biye dasu a baya,rike musu da trolley sojojin nan na ganin fitowar su suka jinro daga nasu motochin suka nufe su, Fahad na ganin fitowar su ya nufesu da sauri, yana ɗan murnushi hugging na DON yaje yayi yana faɗin “Wellcome back bro, hannu DON yasa yayi taying ɗin yana faɗin “missed U my blood “missed U too yayi maganar yana zare jikin sa daga jikin DON, yajuya yayi rungume Aryan ma, yana faɗin yaya Aryan nayi kewar ku sosai, rungume sa sosai Aryan yayi yace “nima nayi kewar ka sosai my blood, ganin DON yayi gaba ya barsu ne yasa Fahad ya saki Aryan da sauri sukabi bayan DON wajen motochin nasu suka nufa,nan take su Haidar suka fara musu sannu da dawowa ko kallan in da suƙe DON bai yiba bare su saran zai amsa musu, ya shige motar ya zauna yana yamutsa fuska, Aryan ma shiga mota yayi riƙe da hannun Fahad sai da suka zauna san nan ya dubi kannen nasu yace “yauwa to ku shiga mota muje gd koh sai mu gaisa a chan zaifi, da sauri suka koma chikin mota, drivers su kama motochin key da gudun gaske suka bar Airport ɗin gudu suƙe shararawa sosai a kan mikakkiyar titi, sai da suka kusa da bakin gate ɗin gida suka rage gudun motochin, batare da ɓata lokachi ba security daƙe tsaron gate ɗin su wangale musu gate ɗin a nitse suka kutsa chikin gd, kai tsaye parking space suka nufa suna kashe motochin, Shahram da Abdol suka fito daga nasu motar da gudu su kazo suka buɗewa DON da Aryan kofar motar, a nitse DON ya zuro kafafun’sa waje kafin ya fito gaba ɗaya bai bi ta kan kowa ba yanufi ɓangaren sa, Aryan ma ɓangaren sa yanufa riƙe da hannun Fahad suna tafiya suna hira, Yusuf ya karɓi trolley DON daga hannun Abdol yabi bayansa da shi Ahmad ma ya karɓi na Aryan daga hannun Shahram ya nufi ɓangaren Aryan ɗin, su Haidar kuwa kowa yakama kansa yayi part nasa

Ammi na zaune akan kujera a palan’ta tasha kwalliya chikin wata ɗankarekiyar lace baki da ratsin ja mai shegen kyau ga wasu gwala gwalan data zuba a wuya da hannu ta,ba karamin kyau tayiba inka ganta kace bata,wuce 25 years ba, Aunty farida tashigo da sallama ɗauke a’bakinta, da fara’a Ammi ta amsa mata sallamar, shigo chiki palon tayi ta zauna saman sofa mai zaman mutun 2,tana fuskantar Ammi “feeda dayake haka Ammi ke kiran Aunty farida feeda,ina junior yake “Junior yana wajen mardiya chewar Aunty farida ” ok kawai Ammi tace tana kallan face ɗin Aunty farida “Ammi magana nakesan muyi dan Allah “ae feeda tun shigowar’ki Na fahimchi hakan, badamuwa ina jinki “Ammi daman, magana che a kan price, tun!bata kai karshen maganar ba Ammi ta ɗaga mata hannu, tana faɗin a’a feeda, kinsan dai bazan saka bakina a maganar bako,babu ruwana, dan kuwa kinsan mai martaba idan yayi magana baya chan’zawa “Ammi mun san Abba idan yayi magana baya sau’yawa, amma ae ke ki nasashi ya sauya magana koh, dan Allah Ammi, ki samana baki pls takarisa maganar kamar zatayi kuka “aa feeda babu ruwa’na wai ni ina ruwa da wani prince, ae wan nan ɗan Ummi ne ba ɗa naba kije kisamu Ummi ita tashiga masa amma ban dani “dan Allah Ammi kinfasan Abba yafi sauraren maganarki fiye da kowa a gidan nan” Feeda kin dai san in nache bazanyi abuba tofa bazanyin bane koh dan haka kibar maganar kawai,”to shike nan Ammi na barta barinaje namusu sannu da zuwa “baki Ammi ta taɓe tana faɗin eh lallai feeda ɗaure wa karya gindi,su da suke kannenki basu zasuzo su gaida kiba ke zakije ki gaida su lallai yaran nan suna abun dasu ka gadama
Aunty farida tamike tana faɗin kai Ammi kedai babu ruwan ki tsakanina da yan uwana ko inche yayyuna dan yanzu nabasu girma takai karshen maganar tana kokarin fita daga pallan bata tsaya ta jira amsar Ammi ba ta wuche abunta tana fita tayi part ɗin DON

Da sallama tashiga palan nasa babu kowa, kai tsaye betroom ɗin sa tanufa, yana tsaye gaban mirrow yana gyara gashin kansa,sanye yake da bakar jallabiya, da alama wanka yayi, jin sallaman ta yasa yaɗago green eyes nashi ta chikin miron yana kallan’ta, batare da ya juyo ba “yace Aunty babba yanzu nake tunanin inje in ganki, kafin inyi barchi
Harara wasa Aunty farida ta wurga masa tana fadin “daka ganniba dole kafaɗi haka nasan da banzoba ba zuwa zakayi ka nemeni’ba, slowly ya juyo ya zuba mata green eyes nashi nan kafin yace “a’a Aunty farida ae kema kinsan dole na nemeki

Karisa shigowa chikin ɗakin tayi tai, a bakin katafaren gadansa dake shinfiɗe da White bet shit ta zauna tana faɗin,”to ya hanya “Tafiyar da bada san ranmu mukayotaba Tafiyar dole,ya kae karshen maganar yana ɗaure fuska , guntun murmushi Aunty farida tayi kafin tace, “hmmm yanzuma nagama magana da Ammi kafin nazo nan, kara ɗaure fuska yayi yana faɗin “ai dama baki mata magana ba, da baki ɓata bakin ki bama dan nasan baza ta saurare mu ba jinjina kai Aunty farida tayi kafin tache,mudaiyi addua karkadamu inshaa allah komai zaitafi yadda kakeso,tana kae karshen maganar tamike,bari na dubo Aryan, batare da ta jira amsar saba tayi waje dan tasan ba amsa war zai yiba,”juyawa yayi yachi gaba da abun daya’keyi

Tana fita ɓangaren DON tanufi ɓangaren Aryan bakin ta ɗauke da sallama tashi palon babu kowa a palon sai sanyi A.c dake ratsa jikin betroom nashi tanufa, sallama tayi a bakin kofar kafin ta tura kofar tashiga kwanche ta same sa akan katafaren gadansa,idon sa a lumshe da alama barchi,yafara ɗaukan, jin an taba kofar ne yasa ya buɗe idon’sa da kyar, yana ganin ta ya dan saki fuska yana da kyar ya buɗe baki da murya irin na mai barchi yace “Allah ya barmana ke aunty mu wlh naso nazo,na dubaki amma barchi ya hanani, murmushi tayi tana faɗin “an dawo lfy my tagar “lfy lau lovely Aunty “to bari na kyale kayi barchin ka daman dai ina san inzo inji an iso lfy ne tun da lfy ba wata matsala ayi barchi lfy sai mun haɗu awajen chin abinchin dare ahuta gajiya,tana kae karshen maganar ta juya tanufi waje juyawa yayi shima yana fuskantar gefen dama yachigaba da barchin daya fara”

Misalin karfe 8 nadare gaba ɗaya family Abba sun haɗu a palon, dan chin abinchin dare, banda Aryan DON da kuma Fahad, sun zauna shiru suna jiran fitowar Abba, Ammi che ta katse musu shirun da chewa “nikoh meyasa mairo da salma basu zo bane kodai basu da lbr meeting martaba ya shirya
A tsiyache Aunty amarya tace ke Aisha kidaina ɓatamin su nan yarinya, kuma ina ruwanki da zuwar ta inba muna furchiba
“haba Aunty amarya daga tambaya chewar Ummi “ke Ummi baa kasa dake ba idan kemaɗin muna furchinne sai naji akule Aunty mardiya tache “a’a wlh ya isheki haka gaskiya bazaki zauna kina zagin iyayen mu, a gaban mu’ba tayi maganar tana nuna Aunty amarya ta hannu, hannu Aunty farida tasa ta ɗan buge bakin Aunty mardiya, tana faɗin to ke ina ruwanki ae dukkan’su iyayen’mune wan nan fadar’sune tsakanin’su
Umar ya ɗago rai a ɓache yana faɗin “to ae gashi muma Aunty mardiya rashin kunya kike neman kiyiwa mahaifiyar tamu, A’kule haidar yache “haba Umar kai bakaji abun da Aunty amaryan ke faɗe bane, dafe kai Khalid yayi yana faɗin, to ya isa haka ae kuyi shiru, amma ina ba wan da ya saurari Khalid sunki yin shiru wan nan ya faɗa wan nan ya faɗa abun hat’tafara zama kamar faɗa
Dafe kai kawai Ammi da Ummi sukayi suna kallan ikon Allah kowa kokari yake yakare ma haifiyar’sa wan nan abu dame yayi kama” sai faman kache na che suke abu har ta fara zama kamar faɗa

Kamar daga sama sukaji gyaran murya daga bayan su nan take, sukayi tsit dan kuwa ko basu juya ba sunsan mai wan nan voice ɗin tsaye yake a bakin kofar shigowa palon, yazura hannu a aljihun wandan,sa’ yana kallon su fuskar nan tamkar batasan menene dariya’ba a daure take tam, a nitse yafara takowa izu chikin palon,wajen table ɗin yanufa,da sauri Haidar yamike, yaɗan jamasa kujeran zaman, baya tayadda zaiji daɗin zama gaba ɗaya matasan suka mike,ban da Khalid da Aiman da Yusuf jiki na kerma sukafara “faɗin sannu da fitowa yaya Aryan zama yayi batare daya amsaba yana binsu da ido jiki ba kwari suma suka koma suka zauna, murya na rawa Zahra tache “sannu da dawowa yaya Aryan
ko kallan in da take bai yi ba bai kuma amsa sannu nata ba ita ma,nan take kowa a chikin su yasha jinin jikin sa kallon fiskokin su yake sosai kamar mai karantar wani abu a tattare dasu

“me za’a zubamaka ne Aryan Ammi ta tambaya tana kallan fiskar sa, sai lokachin yadawo da kallansa kan Ammi kana yaɗan saki fuska calmly yace “abun daya dache kawai “ok to bintu kuzuba masa ferfesu kayan chiki da fraid rice Ammi tabawa masu aikin umarni, da sauri suka fara zaran plate dan su zuba masa,hannun su har rawa yake dan tsoran sa da sukeji suna kokarin zuba masa abin chin’ne
Aunty amarya ta daƙa musu tsawa “bashi zaku zuba masaba dan babu wanda ya isa ya zabawa ɗa na abun, da zai chi sai ni dana haife’sa kowa a gidan nan yana da nashi ɗan ae to kowa ya kula da nashi ba ruwan shi dana wani,dan haka tuwon shinkafa zaku zuba masa
Shiru yan aikin sukayi sun rasa umarnin wa zasu bi “kamar daga sukaji Aryan yana faɗin ku bar’shima kawai am ok, Aunty amarya zatayi magana sukaji takun tafiya ta bayan su dukkan su suka juya ban da Aryan, tafiya suke chikin kwanchiyar, hankali sun jero kamar ,sanye suke chikin jallabiya dukkansu Fahad bakin DON kuma fari tas, fiskar sun nan dukkansu babu wasa a ɗaure taku suƙe irin na chikakkun maza, kamar wasu yan biyu haka suka jero dan dai kawai DON yafi Fahad tsawo dakuma chika sai kuma kalar kwayar ido daya ban ban tasu Fahad kwayar idon sa baki ne DON kuma green amma ban da haka kaman’nin su ɗaya

A take palon yayi tsit suka kara nitsu wa dan duk gidan idan ka chire Abba Ammi da Ummi Aunty farida sai Aryan to kowa na gidan tsoran DON yake, har Aunty amarya tsoran sa take kamar me dan tasan DON ba wasa ba’a kawo masa wargi yanzu zai sumar da mutun, bakaramin tsoransa Aunty amarya ke jiba, da sauri Haidar yamike ya gyara musu kujerar da zasu zauna, a nitse suka zauna slowly DON ya ɗago yafara gai da iyayen nasu, da fara’a suka amsa masa, da sauri kannen nasu suka fara ɗaga masa gaisuwa, bai amsa gaisuwar kowa daga chikin su ba sai ma wayar sa daya chiro daga aljihun sa yafara latsawa
“prince me Za’a zubama,Ummi ta tambaya tana kallan face nashi, shiru ya ɗanyi kamar mai tunani sai kuma ya dawo da kallan sa kan Aunty farida,batare dayayi magana ba, Aunty farida ta gane me yake nufi da sauri tace,da masu aikin “ku zubawa kowa ferfesun kaji da chips kawai
Chikin sauri, suka fara zaran plate suna zubawa suna mika musu

A hankali Aryan ya ɗau spoon yafara shan ferfesu, wani kululun bakin chikine ya tokare wa Aunty amarya makoshi tana san tayi magana tana tsoran DON a zuchiyar ta take faɗin wai komai farida tace a gidan nan ko, basaso sai sun yarda, gashi dai ni tana haifi yaran nan amma bani da wani iko da su, maganar farida tafi nawa muhim manchi dole nayi maganin abun wlh bazayyiwu’ba

Da Sallama Abba yashigo palon yana sanye chikin jallabiya fara tas kai tsaye table ɗin yanufa,tun bai karisa zama ba suka fara gaishesa,Sai da duk suka gama gai’dashine ya haɗesu yabasu amsa ɗaya da sauri bintu mai aiki ta rari plate ta zuba masa abinchin zaɓin Aunty farida wato ferfesun kaji da chips
Tunda Abba yaga irin abinchin’ne a plate ɗin kowa dake wajen yagane zaɓin Aunty farida ne dan haka shima karba kawai yayi yafara chi

(sai yanzu nasan a inda yan gidan suka gado rashin magana dan kuwa shima Abba baya magana shiru shirune)

Shiru kake jin palan ba mai magana sai karan spoon kawai zakaji,da sautin A.c dake tashi

Bayan sungama chin abinchin ne DON ya mikewa ya nufi hanyar fita daga palon, harya kai bakin kofar sai kuma ya juyo yana faɗin “dukkan ku mazan nan kusameni a ɗaki,ke kuma Zahra karfe 10 dai dai ina bukatar ganin ki bai jira amsar su ba yayi waje, da sauri suma suka muke sukabi bayan’sa
Suna fita Abba ya dubi su Ammi yana faɗin “sun aikata wani abun da ba dai dai bake nan,Ammi dai shiru tai bata bashi amsaba hakama Ummi
aunty amarya che tache “zagina mana sukayi, Shiru Abba yayi dan yasan halinta sarai yanzu haka ita ta takalo faɗan “ranka shidade inasan magana dakai chewar Ammi, Abba zaiyi magana
Aunty amarya tarigashi dache’wa “to ae yau ba ranar ki bane bake kike dashi ba sai ki bari sai yadawo dakin ki, shiru Ammi tai dukkansu ba wanda yasake magana

DON na shiga dakin sa ya zaune a gefen katafaren gadon sa yana jiran kannen nasu
Da sallama suka shigo gaba dayan su
Aryan ya wuche ya zauna a kusa da DON a bakin gadan, shi kuma Fahad hayewa yayi kan gadon abunsa ya kwanta ya dauko wayarsa yafara latsawa,domin kuwa yariga da yasan dalilin kirannasu to shi baya chiki maganar

Dukkan su zama sukayi a saman sofan dake ɗakin Khalid ma agefen gadon yazauna suka sa DON a tsakiya shida Aryan ryan
Almost 10mnt DON bai che dasu komai ba kamar ma baisan da zaman su a ɗakin ba, shiru sukayi suna tunanin me yasa ya kira’su kodai yaji abun daya faru a palo ne calmly yafara magana “daga yau sai yau duk wanda ya sake,idan iyayen mu suna magana a tsakanin’su yasa baki kunsan me zai biyo baya ina ruwan ku da faɗan su
Shiru sukayi bawanda yache kala
DON yachi gaba dace wa “last warning nake muku idan kuka bari nasake kama’ku da irin wan nan dabiar bama sai nayi magana ba, kai Haidar da kai da Umar kuje wajen kwallo bayan nan kufara frog jump ina zuwa ya kai karshen maganar yana kallansu Haidar da Umar ɗin

mikewa sukayi suka fita jiki ba kwari suna fitowa Umar ya dubi hadar yafara magana “mun shiga uku wlh, yau zamu gane kuren’mu wayyo sheidan baka mana adalchi ba daga dawowar big bro muzai fara yiwa hukunchi ke nan wayyo Allah,
Chikin nar kewar murya Haidar yache “waima daman meyakai’mu shiga fadar matane yanzu gashi zamu karbi hukunchi,wlh ni nasan yau sai munkasa mikewa da kafafun’mu
Haka’dai sukayi ta surutai suna tafiya har suka isa wajen kwallan dukawa sukayi suka fara frog jump ɗin.

Miƙewa Yusuf Aiman Ahmad sukayi suka musu sai da safe suka fito nuka kowa yanufi part nashi ɗakin yarage daga DON Aryan Khalid Fahad, shiru suka zauna kowa na latse latse a wayar sa almost 10mnt Khalid ma yamiƙe ya musu sai da safe yayi waje, Khalid na fita Aryan ya ajiye wayarsa ya dawo da kallon sa da kuma hankalin sa kan DON yafara magana “zanje nayi magan da Aunty amarya batare da DON ya ɗago ba yace “a kan me fa “akan abun daya faru dazun a palo mana kasan komai kaji komai da kunnen ka,kasan wayafara taɗa rikichin to yakamata mu dakatar da abun tun bai yi nisa ba sai lokachin DON ya ɗago green eyes nashi yana kallan Aryan ɗin kafin yache “a’a ka kyaleta to idan ma kaje me zakache mata itafa ta haifemu bamu muka haifetaba dan haka kabar abun zamu’san abunyi a kai “a’a DON duk da ita ta haife mu amma ai idan tana kuskure addini ya halakta mana mu mata gyara,amma tun da kache in bari to shike nan zanjira matakin dazaka ɗauka
DON bai sake magana ba shiru suka zauna na dan lokachi kafin Aryan yamike ya musu sai dasafe yanufi waje
juyowa DON yayi yana kalli Fahad dake kwanche yana latsa waya “kai wai a nan zaka kwana ne, da sauri Fahad yace “a’a yanzu zan tafi ya kai karshe maganar yana miƙewa, “sai da safe yache da DON batare daya jira amsar DON ba ya sauko yanufi waje

Karfe 11 nadare

Sau kowa yake a nitse yana sanye da kayan barchi dogon wando da riga mai dogon hannu yan shara shara marasa nauyi white colour jikinsa sai kamshi yake, ya tara gashin kansa ya ɗaure a baya sosai kayan suka fito masa da surarsa na chikakke kuma jarumin namiji mai ji da lfy da karfi,taku yake irin na jaruman maza masu jini ajiki, kofar baya ya buɗe ya fito waje kai tsaye wajen kwallo yanufa

Frog jump yasamu sukeyi da kyar da kyar suƙe iya ɗaga kafa duk sun galabai ta sama sama suke numfashi sun jiƙe sharkaf da zufa
da kak’kausar murya yache “kutashi ku tafi ɗaki a gala bai che Umar yace “sorry bro wlh bazan iya miƙewa ba da kyar Haidar ya iya buɗe baki shima yace “wlh yaya prince nima bazan iya tashiba
Chikin tsawa DON yafara magana “zaku kwana a nan ke nan, zaku tashi kutafi ɗakine ko sai nayi kwallo daku ai tun bai kai karshen maganar ba suka tattara sauran karfinsu gaba daya suka miƙe, har jiri suke gani rungume juna sukayi suna ɗungisa kafa da kyar da kyar suka nufi hanyar part nasu, shi kuma DON ya juya ya koma ta in da ya fito

jimeta yola

Jama’a ne zaune a kofar gidan su diyana suna karɓan kai suwar rasuwar bappa chikin gida kuma matane zaune suna yan koke koken su, hiyana diyana Amrat lamrat kuma suna zaune a kusa da rafe kasan wani bishiyar mangoro suna kuka, duk fuskar su ta kunbura kuka suke sosai kamar ransu zai fita chikin kuka da dashewar murya diyana ke faɗin “shike nan bappa ya mutu ya bar mu munshiga uku ina zamusa ranmu wayyo allah “da kyar hiyana ta iya buɗe baki muryan ta duk ya dashe saboda kukan data sha tafara magana “a’a diyana ki daina chewa munshiga uku gaskiya bamu shiga uku ba tun da mun rike Allah inshaa Allah, Allah bazai kyalemu muchigaba da wulakantaba chikin shessheka lamrat tace “eh hakane Aunty hiyana addua kawai bappa ke bukata, duk kansu suka haɗa baki su kache Allah yajikansa da rahma
Diyana tache “hmmm jiya fa Bappa yarasu amma baza abar’mu mu dan huta ba muji da rasuwar bappa ba inna tace, dan Allah yanzu muji da wanne muji da rasuwar Bappa ne ko kuma muji da ɗebo ruwa
Mikewa hiyana tayi tana faɗin “kutashi ma mukarasa ɗeban ruwan nan kar inna ta buge’mu da kyar suka mike suka nufi rafin suna rike da cups a hannunsu
Sun ɗebo ruwan zasu wuche ke nan sai sukaji muryan yaya bello na kiran’su daga chikin gona, chikin gonar suka nufa, a zaune a inda yasaba zama suka same sa ga tulu sababbi guda 4 a gabansa
A gaban sa suka duka suka gaidashi ya amsa chikin faraa san nan yamusu taziyar mutuwar bappa tare da adduar Allah ya jikansa suka amsa da ameen, kana yache ku ɗauki tulu nan nan dasu zaku rinka deban ruwa dan ku nasaya, duk da kukan rasuwar bappa dasuke hakan bai hana’su yin murna da ganin tulun ba ɗauka sukayi suna murna sai godiya suke masa suka fito gonar suka nufi rafi, ruwa suka ɗeba a sabon tulun su sai murna suke,suka nufi hanyar gida

One day later

yau Bappa yachika kwana uku da rasuwa, jama’a sun watse babu kowa a kofar gidan kowa kama kansa

diyana hiyana da lamrat sunbar amra a gida tana tikar aiki duk kansu suna dauke da tulun da yaya bello yasa musu suka nufi rafi suna tafiya suna yar hirarsu
Diyana tache “wai ya akayi inna batayi magana akan tulun nan bane Girgiza kak hiyana tayi tana faɗin “hmmm ai bata lura bane inda ta lura ai da saita tambayi waya bamu ko kuma ma ta fasasu
Lamrat tache “to yanzu idan inna ta tambayi waya bamu tulun me zamu’che mata,dogon tsaki diyana taja kafin tace “sai muche muma ba mu san mutumin daya bamu’ba,yaga muna ɗeban ruwa da kofine sai yabamu “yauwa diyana gaskiya kin kawo shawara daman sai tunani nake idan inna ta tambaye mu me zamu’che chewar hiyana,tayi maganar dai dai lokachin da suka iso bakin rafin ruwa suka debo,a tulun suka juya suka nufi hanyar gd,

“hiyana wai yan zu haka zaki Auri buba diyana ta tambaya, buɗe baki hiyana tayi zatayi magana sai taji an ture tukun dake kanta ta baya ya faɗi ya tar watse, asukwa’ne buba tagani tsaye yana mur mushin mugunta diyana naganin buba ta kwasa a guje tayi hanyar gida, gudu take iya karfinta har ta iso dai dai zata shiga ke nan tayi tun tube da dutsen kofar gidan ta faɗi kasa tulun ya faɗi kasa ya tar watse, wani kukan bakin chiki ta sake kuka take kamar ranta zai fita
a wan nan yanayi Hiyana da lamrat suka zo suka sameta tai maka mata Hiyana tai tamike tsaye ga goshin ta sai jini yake, dukkanbsu sai hawaye suke haka suka shiga gida

inna dake zaune a tsakar gd tache ina ruwan, kuma tun dazun na zauna a nan nake jiranku zan dora ruwan shayi
Chikin shesshekar kuka lamrat tace “wlh inna buba’ne ya kifar da ruwan
Da sauri inna tamike tana faɗin buba na zakuwa sharriko ai nama buba ya ganku bare ya kifar da ruwan to wlh yau zaku yabawa aya zakin’ta, suna tsaye awajen suna matsar kwalla, har inna tashiga ɗaki ta daukoh wasu manya manya bulalin bishiyar dalbejiya

Ta nufosu gadan gadan baji ba gani tafara sauke musu zabga zabgan bulalun nan ajiki babu ko imani bare tausayi, ihu suƙe hiyana da diyana suka haɗu suka kare lamrat, duka inna ta musu sosai sai da ta kutun suna iya kuka har kukan nasu ya daina fita sosai, sai da ta bugesu iya san ranta san nan ta kyalesu tana faɗin kutashi tun kafin na rufe ido na buɗe ku ɗauki kofi ku tafi ku ɗebo min ruwa,yanzun nan kugama kuzo ku jemin tallah tana kai karshen maganar ta nufi ɗakin ta, da kyar suka mike suka nufi Kichin suka ɗauki cups suka fice daga gidan, Amrat dake duƙe a wajen wanke wanke tana wanke kayan inna sai kuka take kamar ranta zai fita ba abun da take tunawa sai mahaifiyar su a zuchiyar ta take faɗin yanzu da umman mu bata rasu’ba da tana nan inna bazata musu haka ba wayyo Allah ka jikan umma da bappa haka dai Amrat wunin ranan ta wuni tana kuka su diyana kuwa suna jidan ruwa da kofi ga yinwa ga nisan rafi ga zafin rasuwar Bappa.

Misalin karfe 11 nadare zaune suke a dakin’su dukkan’su ba wan da yayi barchi saboda yinwar dasuke ji ta hanasu barchi diyana che ta dubi hiyana tafara Magana “hiyana yaufa tun safe jinin nan yasake dawowa na chanza zani har nagaji duk kayana sun kare jinin kuma bai daina fitowaba
A ɗan tsorache Hiyana tache “bari na lallaɓa naje na tambayo innar yaya bello sai muji kodai akoi wani abun da zakisha sai ya daina zuwa a razane lamrat tace “Aunty diyana wani jini kuma, diyana zatayi magana hiyana ta rigata da chewa ina ruwan’ki dake ake magana ne, shiru lamrat tayi taba sake magana ba
Amrat dai takasa magana jimamin mutuwar bappa har yanzu bai saketa ba, dan kuwa duk tafisu shakuwa da Bappa su basu yawan zama dashi sosai saboda aikin ɗeban ruwa da tallah, wani lokachima sai sufi kwana uku basu samu damar ganin saba saboda balai inna,shiya ita amrat tafisu shiga damu dan kuwa ita kullum tana gida idan tagama wa inna aikin gida sai tatafi ɗakin bappa, ta kwanta ajikinsa suyita hira.

Mikewa hiyana tai tana faɗin, bari dai na lallaba naje wajen innar yaya bello dan nasan itama batayi barchiba,tana kai karshen maganar ta fiche daga ɗakin, lallaɓawa take kamar wata ɓarau’niya ta fiche daga gd tana fita ta kwasa da gudu dan tsoro dare yayi ga duhu, sai data shiga gidan su yaya bello san nan ta ta tsaya tafara tafiya a hankali hankali dan kar wani yaji ya ganta ya faɗawa inna

Da sallah ta shiga ɗakin innar yaya bello sai wani sanɗa take innar bello na zaune a tsakiyar ɗaki ta tasa dakkere a gaba tana chi ganin Hiyana yasa tamike tana tambayar ta “lfy hiyana me yafito dake chikin daren nan “lfy inna daman nazo tambayar ki wani abune “to menen faɗi, hiyana tasanar da ita komai abun da yafaru da diyana har fyaden da buba yaso yayi mata san nan taɗora da chewa kuma inna jinin fa kwana binyu da suka wuche ya dai na zuba sai yau kuma ya dawo
Shiru inna ta ɗanyi kafin tace “kai buba Allah dai yashirya mana shi batun jini kuma al’adane bari nabaki pant da tsunmma guda 2 kibata tasa summa daya yanzu dasafe sai tachire ta wanke ta shaya, sai ta dauki dayan tasa, ba’a ajiye summar jinin kinaji na da an chire za’a awanke, to wakai hiyana tace, inna tanufi kwallar kayan sawar’ta ta buɗe ta dauko pant da tsunmma guda biyu ta mikawa Hiyana, amsa tayi tana fadin “to inna tayaya zatasa, inna tasake amsar summar tasa a chikin pant ɗin ta nuna mata yadda zatasa, san nan ta miƙa mata, Hiyana ta ansa tana faɗin mungoɗe inna,tanufi hanyar fita har takai bakin kofa sai kuma ta juyo tache inna “menene al’ada kuma
Inna tache “idan mace ta girmane yake zuwa mata kuma alokachin da mace tafara al’ada to karta yarda wani namiji ya sake tabata idan kuma tabari ya taɓata tofa zata samu chiki
Zaro ido waje hiyana tai jin an ambachi su nan chiki murya har rawa yake tache inna to meyasa ni banyi al’adan ba kuma ai niche babba, dafe kai inna tayi tana faɗin “kai hiyana sarkin tambaya to ai kowa da irin halittarsa ne shiyasa wata zakiga shekara 13 take farawa wata kuma sai takai shekara 16 to kowa da irin tasa halittar “to inna kullun yake zuwane dan naga na diyana fa yanzu kusan sati 1 ke nan kuma diyana tache kwana biyu dasuka wuche ya daina zuwa yau ne kuma yasake dawowa, shiru inna ta ɗanyi kafin tace “ina gani diyana na da sanyi’ne shiyasa al adan ke mata rikichi, yanzu dai dare yayi kije gd inkin samu lokachi idan azzalumar innan kun nan bata nan sai kizo in baki maganin sanyi kibawa diyana, yanzu kinga dare yayi kuma ban haɗa maganin bama tukun nan Hiyana tache “to inna mungoɗe sai da safe ta nufi waje tana fitowa kofar gdsu yaya bello, da gudu tayi gidan su chikin duhu dan dare yayi tana tsoro
In da ta barsu diyana a nan tadawo ta samesu zama tayi gefen Amrat tafara yiwa diyana bayanin da inna tamata
Diyana kam tunda akafara bayani take sauraro anazuwa wajen da akache intabari namiji yataɓata to zata samu chiki a tsorache tache
Hiyana yanzu ko yaya bello tab nashiga uku na wlh yanzu ke nan zan samu chiki tun da kunga ko jiyama na kama hannun yaya bello,wayyo Bappa na dan Allah meyasa katafi kabar mu yanzu ni ya zanyi da raina ni diyana da chiki
Girgiza kai hiyana take tana faɗin “ki dai na kuka diyana kinji kibari dasafe sai muje mu tambayi inna muji kina da chikin ne ko babu, da kyar hiyana tasamu diyana tayi shiru, san nan to koyawa diyana yadda zata yi amfani da tsumma da pant ɗin kamar dai yadda innar yaya bello ta koya mata, mikewa diyana tayi hiyana ta taimaka mata tasa pant ɗin san nan tasa tsunmar, suka kwanta shiri babu wan da yasake magana da haka har barchi ya ɗauke su

3 days later

Zaune take a tsakar gida ita kadai diyana ta tafi tallah amrat tatafi wanki kayan inna a rafi lamrat kuma tana debo ruwa ita kuwa inna ta bartane tamata girki
Shigowa gidan inna tayi babu koh sallama tache “ke hiyana ko ki shirya ko karki shirya gobe za’a ɗaura auren ki da buba
Hiyana dai bata che da inna ko mai ba amma a chikin zuchiyarta tana tunanin yadda zata gudun wa Auren, wunin ranar kuka hiyana ta wuni yi dan yau rasuwar bappa ya dawo mata sabo fill tasha kuka har blue eyes nata suka kumbura suka kankan che.

Da daddare bayan su diyana sun dawone suna zaune a dakinsu kamar yadda suka saba
Hiyana ta dubi su diyana tafara magana “lokachi yayi da zamu bar gidan nan
A tsorache diyana tace “to muje ina muda bamu san kowaba bamusan ko inaba “ko bamu san ko inaba yazama dole mu bar gidan nan, dan gaskiya bazan Auri buba ba wlh na tsanesa bansan ganinsa mugune, gaskiya bazan tsaya a ɗaura mana Aure ba hiyana ta karisa maganar kamar zatayi kuka “to yanzu idan mun bar gidan nan ina zamuje diyana ta tambaya fiskarta chike da damuwa “kidai na damuwa diyana, zanyi tunani a kai dole na nemo mama inda zamuje chewar hiyana da sauri lamrat tace “to ko zamu nemo addan (yaya) bappa ne ba yataɓa faɗa mana yana da adda ba (yaya)
Hiyana tache “to ai na zamuganta kenifa baruwana da kowa, yauwa birni zamu tafi muje munemi aiki har musamu kudi
Taɓe baki diyana tayi tana faɗin to yanzu muda bamu san hanyar birni ba ta ina zamu tafi, karfa mu bar gidan nan muje mu haɗu da masu yan kan kai suyan ke mana kai, da sauri Amrat tace “wlh bappa yataɓa faɗamin akoi masu yan kan kai a birni, kara zaro ido lamrat tayi, tana faɗin “tab nikam ba zanje ba wlh gara na zauna a nan ta karisa maganar kamar zatayi kuka, kallon hiyana diyana tayi tace “to yanzu ya zamuyi Shiru hiyana ta ɗan yi kafin tace ke dai karki damu zansan yazamuyi, yanzu kan mu kwanta muyi barchi, da safe in munje ɗeban sai mukarasa maganar a rafi, har suna haɗa baji wajen chewa to

Suna kokarin kwanchiya kenan sukaga inna ta faɗo musu ɗakin kafin su ankara tafara sauƙe musu bulalun hannun ta ajiki, bugun su taƙe tana faɗin “buba ne bakiso ko to wlh koki mutu ko kiyi rai sai kin auri buba daga yau ba mai sake fita a gidan nan a chikin ku rufe ku zanyi a dakin nan ke hiyana gobe za’a kai ki gidan buba kukuma sauran yin’wache zata kashe’ku a chikin dakin nan dan kulle’ku zanyi ba inda zaku sake zuwa
Kuka suke sosai sun manne da juna diyana da hiyana sun haɗu sun karewa lamrat da Amrat ajikin su kawai bulalan ke sauka, inna kuwa bugun su take baji ba gani da iya karfinta,sai da ta farfasa musu jiki tukun nan ta kyalesu ta fiche daga ɗakin, kankame juna sukayi suna kuka a haka barchi ya ɗauke su

Kano ta dabo

Ammi na zaune a gefen katafaren gadan Abba shi kuma Abba yana kwanche a nitse da sanyayyiyar murya tace “ranka yadaɗe inasan muyi magana, mikewa Abba yayi daga kwanchiyar da yake ya zauna yana fiskantar ta “ina jinki Aishstu na manene yayi maganar yana kallan chikin idon ta, kasa da kai Ammi tayi chikin ladabi da girmamawa ta fara magana ” daman inasan zuwa Yola ne wlh kwana biyun nan,bana jin daɗi ina ganin kamar akoi damuwa ina yawan mafarkin Ahmadu kasan shi ya ragemin kuma gashi na yaddashi, abun yana yawan damuna sosai, inajin a jikina kamar Ahmadu na chikin damuwa,tunaninsa har tafara yimin yawa, dogon numfashi Abba yaja kafin yace “ba’damuwa Aisha ae kin jima baki jeba kusan shekara 7 ke nanfa gaskiya yakamata kije, ki shirya sai kuje da su Safras su rakaki
“da murna Ammi ta juyo ta rungumi Abba tana faɗin ilove U ilove U
rungumeta sosai Abba ma yayi yana faɗin “eyeeee yau kam ba fullanchi ke nan,kara shigewa jikinsa Ammi tayi tana murmushi

( Nikoh nache oh ka jimin tsofaffin nan gaskiya Abba da Ammi kuna shaaninku tsufa bata hana soyayya)

Misalin karfe 4 na yamma gaba ɗaya ilahirin family alhaji Abubakar saraki ne zaune a fada
Abba na zaune a kugerar sarauta gasu, Ammi a gefensa gefe guda kuwa sarkin fada’ne dasu waziri ga uncle Aliyu ma a gefe DON da Aryan suna zaune saman sofa mai ma zaunin mutun 2 duk kansu fiskokin’su babu alamar wasa a ɗaure taƙe tam kamar basu san menene dariya ba kallo ɗaya zaka musu ka gane suna chikin baƙin chiki, Khalid da Yusuf suna zaune suma a saman sofa ɗaya mai ma’zaunin mutun 3 ko ajikin su sai ma murmushi mugunta da suƙe wa DON da Aryan

gyaran murya Abba yayi yafara magana a nitse gaba ɗayansu suka tattara hankalin’su suka maida kan Abba suna sau raron’sa
” Dalilin dayasa na tara’ku inason sanar daku lokachi yayi da zan sauka a kan kujerar murki in mikawa ɗana Safras asukwa’ne DON ya ɗago kamar zai yi kuka nan take fuskar sa ta sauya sosai jiyake kamar yayi ihu shi gaskiya baya san mulki ai sojan shi kawai yake so, chigaba da magana Abba yayi “gaba ɗayan’ku ina mai baki umarni ku’nemi transfer a wajen aikin’ku kudawo kusa dani kuchiga da aiki a kasar ku Aryan Ahmad Aiman Khalid Yusuf a sukwane suka ɗago suna kallon Abba, Abba ko ajikinsa sai ma chigaba yayi da magana,”yau azumi saura wata 2 bayan Sallah da sati 1 zan sauka daga kan kujerar mulki na a naɗa sabon sarki Safras, buɗe baki DON yayi zai yi magana sai idon sa ya sauka a kan face ɗin Aunty farida, girgiza masa kai tayi alamar yayi shiru kar yayi magana shiru yayi, yafasa maganar ya mai da kansa yana kallon kasa, “akoi mai magana a chikin kune chewar Abba yayi maganar yana kallon fuskokinsu shiru sukayi gaba ɗayansu Almost 10mnt ba wanda yayi magana “ok tunda bakuda magana kutashi kuje sai bayan Sallah da one week

Da sauri DON ya mike ya fice daman kamar a kan kaya yake da sauri Aryan ma ya miƙe yabi bayan DON da ɗai da ɗai suka watse kowa yayi nasa ɓangaren

Aunty amarya na fita tayi part nata sai huchi take, tana shiga ɗaki ta ɗau wayarta tafara neman hajiya sadeeya, bugu ɗaya hajj sadeeya ta ɗaga tana faɗin hello aunty amarya tache “hajjiya sadiya kina ina “ina nan kano mana meyafa “akoi matsala hajj ya sadiya ae bama abun da bai faruba, kinaji wai Safras za’a bawa mulki ba Aryan’ba “what? gaskiya bazai yiwuba dolene musan abunyi wlh dole Aryan ne zai karbi mulkin nan karki damu gobe zanzo mu tattauna chewar hajj sadiya “to shike nan sai najiki amma dan Allah kiyi sauri dan jinake kamar zuchiyata zata buga “kar ki damu hajj Hajara ae damuwar ki damuwa tache inshaa Allah zan shigo da wurima,”to kawai Aunty amarya tace san nan ta katse kiran ta haye gado tanata kunkuni

Zaune yake a Katafaren palon sa saman sofa mai mazaunin mutun 3 yana fuskan tar sofar da Aunty farida ke kai a zaune ga Aryan zaune a gefensa sun zubawa Aunty farida ido, Khalid da Aiman suna zaune saman sofa mai mazaunin mutun 2 sai Ahmad da Yusuf suma a kujera ɗaya suke zaune dukkansu sunyi shiru sun zubawa Aunty farida ido suna jiran suje me zatache ita maɗin dai shiru ta zuba musu ido DON ne ya katse musu shirun da chewa “Aunty farida yanzu me mafita wlh bazan iya rike mulkin nan ba, mulki baya chikin tsarin rayuwata aikin sojana kawai nakeso bayan shi bana bukatar wani abukuma,dogon numfashi Aunty farida taja kafin tache “kar’kadamu nan da bayan sallah fa Abba yache kaga da ɗan sauran lokachi zamu shawo kansa a hankali, shiya dazun na hanaka magana domin kuwa kokayi magana ba sauraran’ka zai yiba amma zansan yadda zamuyi kafin lokachin inshaa Allah ka kwantar da hankalin’ka duk yadda zanyi naga ba’a baka mulkiba sai nayi, da sauri Aryan yache “dan Allah Aunty farida kada’fa kibari idan Abba ya yarda akan bazaa bawa DON mulkiba Ni kuma a dawo kaina, dan Allah kar’kibar hakan tafaru,wlh nima banaso mulkin nan a bawa Aiman ko Yusuf ” da sauri Aiman yache “tab wlh banaso sai dai Yusuf, wani harara Yusuf ya wurgawa Aiman kafin yace kaima dakake likita kache bakaso to inaga ni soja kuma me soja zaiyi da wani mulki sai dai abawa yaya Khalid ko Ahmad, da sauri Khalid ya buɗe baki zai yi magana, Aunty farida ta dakatar dashi da chewa “a’a Me abun rigima bayan ga uncle Aliyu yana nan da ransa ae shi yadache ya karbi mulkin “good my lovely aunty ina sanki wlh akoi ki da basira chewar Aiman harara wasa Aunty farida tamasa zatayi magana sukaji sallama
Dukkan su suka juya da gudu Aunty mardiya tazo ta rungumi Aunty farida tana faɗin “nayi missing naku sosai Aunty farida tache “sai yanzu kuka iso “eh yanzu shigowar mu Ammi ke sanar dani kuna nan Mikewa DON yayi shi da Aryan da Yusuf suka nufi hanyar betroom ɗin DON, jiki a sanyaye Aunty mardiya tache “bro kufa nazo gani ina kuma zakuje, tun bamu gai’saba tayi maganar kamar zatayi kuka,kuma dakaji muryan kasan a tsorache tayi maganar
Dukkan su ba wanda ya juyo bare ya tanka mata sukayi shige warsu chikin betroom ɗin, har ita kanta Aunty farida bataji daɗin abun da suka yima mardiya ba, a hankali ta dawo da kallanta kan Aunty Mardiya daniyar tabata hakuri, sai taga hawaye wani na bin wani a kan kumatun Aunty mardiya “kiyi hakuri Mardiya bai kamata kiyi kukaba duk da nasan basu kyau ta miki’ba amma kimu’su uzuri watarana sai lbr Chikin kuka mardiya tache “wai Aunty farida me namu’su ne dan Allah meyasa ni basa sona eh why? “suna sanki mana sudai haka halinsu yakene kawai amma suna sanki,wani dogon tsaki Aiman yaja kafin ya miƙe yanufi hanyar fita daga palon, chikin jin haushi Aunty farida tace “kai ina zaka kuma, a ta kaiche Aiman yace “ɗaki zanje batare daya jiya amsar Aunty farida ba yafiche da sauri, Aunty farida zatayi magana Ahmad ma yamiƙe da sauri yayi waje baki Aunty farida ta taɓe, girgiza kai kawai Khalid yayi ya mike ya dawo kusa da Aunty mardiya ya zauna yana bata hakuri, da kyar Khalid da Aunty farida suka shawo kanta tayi shiru, Aunty farida ta miƙe ta riko hannunta tana faɗin “muje ɗakin Ammi, koh, to kawai Aunty Mardiya tace san nan ta miƙe suka fice daga palon shikuma Khalid ya miƙe yabi bayan su DON ya shige chikin betroom ɗin shima,

Yola

Jama’a sun chika gidansu hiyana sai faman shirye shirye ake ga maza a kofar gida suna zazzaune a kan tabarma,liman ya miƙe yana faɗin “kowa ya nitsu yanzu za’a ɗaura Auren ina wali amarya daya daga chikin dattijan dake zaune awajen yace gani nan liman yace to ina waliyin ango Baban buba yace gani na to kumatso kusa zama malam liman yayi kana yache “malam audu kayarda kabawa dan wajen malam sani auren yarka hiyana malam audu yache…✍️

more comments an share *💫STAR LADY💫*

 

*DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star Lady*

 

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button