Sponsored Links
Hausa Novels and Love StoriesJahilci Ko Al'Adah Complete

Jahilci Ko Al’Adah Hausa Novel

Sponsored Links

 

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃 🕊️

🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁

𝘽𝙮 Uwar batooler 🕊️

Bismillahirrah manirraheem

Duk abunda da zan rubuta wanda yake dede Allah alfarman Rasulullahi Sallallahu Alaihi laihi Wasallama Rabbi kaban ladan masu karantawama kabasu ladan wanda yake badede ba astagfirullah allah kayafeni kayafemu duka

Allah karabamu da abun da zai ruɗemu dazamubar ibadanmu danshi
Inkina karanta littafina aka qira sallah baki tashi kinyi ba, nide ban yafeba indai har hakan ya shafeni
Mijinki
Iyayenki
Yayanki
Baqonki
Dukwani mai haqqi akanki dan darajar Allah kada sanadin littafina ki tauye masa wannan haqqin 👏plsss

banyardaba asauyamun littafi kokuwa asayarmun dan wannan nacikin 𝙛𝙧𝙚𝙚 𝙗𝙤𝙤𝙠𝙨 don haka inma ance na sayarwa ne ba da yamun 𝙝𝙖𝙧𝙚𝙚𝙮𝙝 ba
Ayi karatu lafiya

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍

 

 

𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚’𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 – 250 𝟏𝐆𝐁 – 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 500
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 750

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎……

💋💋 امى بتولة💋

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 1_2

 

Yarinyace qarama wacce ataqaice ba zata haura shekara 14 da haihuwa ba, take ta aikin kwarara amai a tsakiyar ɗan madedecin gidan nasu.
Gidane madedeci mai ɗauke da ɗakuna huɗu 4 sai kuma ɗan rumfa haka da alama na dabbobinsune sai madafi(kitchen) a gefe sai kuma bayi(toilet).
Amai take kan yi, wata mata ce naga ta futo daga banɗakin nasu, ta ajiye butan dake hanunta sai ta wuce ɗaya daga cikin ɗakunan gidan, tayi kaman ba taga yarinyar dake ta kakarin amai ba. can wata mata a ɗaya ɗakin ta ɗaga labule ta leqo, da taga shigewan wannan matar ɗaki sai ta taɓe baki tace “dangin jarababbu kawai haka zaku fama ta mutu ma kece da asara” sauqe labulen tayi ta koma cikin ɗalibta.
Wata yarinyace yar shekara 12 ta shigo gidan tana ɗan tsallenta da alama daga aika take, ganin ƴar uwar tata a halin da take a saba’in ta yasar da ledan hanunta tayo wajan yar uwar tata tana cewa “Addah me ya sameki? ina Inna da Mama? Sai ta fashe da kuka ganin yacce ƴar uwar tan ta galabaita, ɗakin Innar tasu ta shiga na wacce ta futo daga bayi amma ba jimawa can ta fito tana kuka tayi ɗakin ɗaya matar.
Muryar matar naji tana cewa “ta mutu mana ina ruwana ita uwar ta bata kallonta ne dangin jarababbu kawai ba zan fito ba, ke hassu zaki ficemun a ɗaki ko sai na ɗau samira nayo kanki dashi” sai yarinyar ta fito tana kuka wanda qarshe ficewa tayi a gidan gaba ɗaya tana kuka.
Wannan yarinya mai aman kuwa sulalewa tayi qasa ta faɗi dan da alama suma tayi dan ta jikkita sosai.
Ba jimawa wannar yarinya da matar tacewa hassun ta shigo gidan ita da wata stohuwa, Salati wannan tsohuwan tayi ta ɗaura hanu akai tace “na shiga uku ni merama daso uwar isa, yanzu dan tsabar rashin kirki da mutanen gidan nan ke fama dashi ace akwai mutane a gidan amma akabar mun jika zata mutu” sai ta nufi wajan yarinyar da ta jima da sumewa.
Mama ce ta futo ɗaki tana cewa “baabaa sannu da zuwa yanzu nima nakeson fitowa dubata naga ko lafiya ina sallah naji kaman ana amai”
Kota kanta stohuwar bata bi ba tace “ke hansai zoki kamamun ita mu kaita ɗakinku” hassu tazo ta tallafawa stohuwar suka kaita cikin ɗakin nasu jikinta gaba ɗaya ya sake kaman babu rai ajikinta, ita dai hassu sai hawaye ita kuwa stohuwa sai masifa take yi”
Shigowa ɗakin Mama take qoqarin yi ita kuwa stohuwan na qoqarin fita, kallonta tayi tace “kinsan Allah da girma yake lami in kika shiga ɗakin nan sai na gwada maki ke qaramar ƴar daba ce, munafuka kawai wato indai ita indon bata san zafin haihuwa ba ke da aka bawa yarinyan bakisan zafin rashin ɗa ba, kuna gidan nan amma jikata na qoqarin mutuwa”
Sanin halin stohuwar ya sanyata ja da baya bata ce komi ba.
Ruwa ta ɗebo a randa tazo ta wuce Mama lami a qofan, qwafa tayi ta shige ɗakin.
Yayyafa mata ruwan tayi tana cewa “ke takwara tashi kinji ta Allah ba tasu ba, tambaɗaɗɗun iyaye kawai”.
Dogon numfashi yarinyar taja, ganin haka sai stohuwar taji sanyi a zuciyar ta tace da Hassu “ke kuma kin wani tasamu gaba kina hawaye kaman ance maki ta mutu tom takwarata ba mai mutuwa yanzu bace kema aniyar ki ta biki, tashi ki kawo mun ruwa a roba me ɗumi maza-maza yi saura”.
Tashuwa tayi ta fice a ɗakin, inda tayi sa’an samun tukunya cike da ruwa akan murhu wanda har ya tafasa, roba ta duba ta ɗiba ruwan ta surka sannan ta kaiwa kakar tasu a ɗaki.
Gefen kayansu stohuwan taje ta jawo wani ɗan-kwali babba, ta cirewa jikar nata kayan jikinta ta lullubeta da wannan ɗan-kwalin. Share mata jikinta tayi tass duk inda ya ɓaci da aman da tayin, ta goge ta tass sannan ta ɗauko wani kayan hassu na taimaka mata suka sanya mata.
Yarinyar ko ido bata buɗe ba, dan tana jin jiki gashi jikinta yayi zafi jau-jauu kaman wuta.
Stohuwar tace “ke hansai tashi kije ki qiramun malam ko magaji duk wanda kika gani nan qofa, kice yazo ya ɗauka mun ita muje gidana tunda nan gidan neman ranta suke basa sonta, to ya isa ni bazan iya ba ina sonta, in su suna gani zasu barta ta mutu to ni duk wata marar mutuncin da ta cika zan nuna mata nawa yafi nata, tambaɗaɗɗun iyaye kawai”.
Fita Hassu tayi ta nufi qofan gidan, cikin sa’a ta haɗu da Magaji, tana ganinsa tace masa “Hamma wai inji baabaa Mero kazo” amsa mata yayi suka shigo cikin gidan tare, suka nufi ɗakin su Hassun.
Jin shigowan Magaji gidan Mama Lami da sauri tayi dakinta ta turo qofar.
Da sallama ya shiga ɗakin, ganin kakar tasu tsaye kan yarinyar da mamaki yace “baabaa me yasami Innai kuma?
Cikin hasala stohuwar tace “to ubana Magaji zaka tsaya tambaya na ne ko zakamun abunda naqira kamun?”
Sanin masifar stohuwar sai yace “Allah baki haquri stohuwa” harara ta aika masa da shi tace “nace in ya bani kabi dare ka kwace, ɗan bokon tsiya kawai ni ka ɗauka mun jika mu tafi da ita gidana ba lafiyane da ita ba kuma in nabarta a gidan nan duka maqiyantane kashemun ita zasu yi ɗan gwanda hansai ma abunka da ƴar uwa har da qwalla tayi na tausayin Addan ta”
Qafa tsohuwar ta kuma yi tace “Magaji ina dalili in haifi abu in kasa ko kallonsa balle kulawa da shi, ko mutuwa zai yi, amma nide matar nan Indo abunda take yi yana cimun tuwo a qwarya aradu ji nake wataran inbi dare inshaqeta kowa ya huta da wannan kayan ciwon zuciyan, wai dan Allah ka haifi ɗa kai ga shugaban masu kunyan ɗan farko sai kaqi kula dashi tun yaushe akabar wannan jahilcin ai al’adar ma taci qaniyar ta, mu dai a zamanin mu ba wannan tambaɗewan zagewa ake a kula da ɗa in baka kula dashi ba ubanwa ya maka naqudan sa da zai kula maka da shi? Allah dai ya bawa takwara miji nagari tayi aure ko ta huta da taqaicin wannan tambaɗaɗɗiyar uwa da Allah ya bata”
“Ameen” Hassu da Magaji suka amsa wa baabaa Mero.
Ɗaukanta Magaji yayi kaman baby suka fita a gidan suka kama hanyan gidan baabaa da yake basu da nisa stakaninsu, suna tafiya sai sababi take har suka isa gidan nata ɗan madedeci, ɗakin ta Magaji ya shige da Innai ya kwantar da ita a ɗan qaramin gadon ciyawan dake ɗakin wanda dama na Innai ne dan mutuniyar baabaa Mero ce.
Baabaa tace “nagode ɗan nan Allah dai ya maka albarka duk da dai dama ba wani nauyin kirki ne da ita ba, yo to yaushe ma ta samu kwanciyan hankali da farincikin da zata yi nauyi yarinya kaman a hure ta faɗi, watarana ma aka yi iska mai qarfi inba sa’a ba sai ya ɗauke ta, Allah ya saka miki takwara”
Magaji yace “Allah qara sauqi baabaa bari muje lokacin salllah yayi”
Tace “to angode, kema hansai jeki gidan kigyara ɗakin naku ko da yake ke ai ɗiyar so ce, takwarata ce ba’a son ta” qwafa tsohuwar tayi ta ɗauki buta ta shige ban ɗaki”.
Hassu kaman ba taso haka ta kama hanyan gidan nasu ita kanta da take yarinya qarama abun na damun ta yacce mahaifiyar tasu ke nuna halin ko inkula akan ƴar uwar tata haka ma Mama Lami, “Allah baki lafiya Adda” cewar Hassu tana share ƙwalla ta shige gidan.
Ta samu mahaifiyarta ta idar da alwala kenan ta shiga ɗaki, Mama Lami ce ta fito dan itama tayi alwalan. Kallon Hassu tayi tace “munafuka ƴar munafukai dangin jarababbu hankalinki ya kwanta ke gaki me ƴar uwa ba kin qira tsohuwar nan ta zage mutane burin ki ya cika, Ita uwar taku bata kula da ƴar ta ba sai ni a gayyan soɗi da shishishigi mtswwww” ɗaga murya tayi dan mahaifiyar su Hassu ta jiyo ta “wai shi mutum gashi bafulatani a haka dai ƴar mutum za ta mutu indai nice zan kula da ita aikin banza anjiqa ba’a tsame ba” Buta ta ɗauka tayi bantdaki tana ta mita dan taji zafin faɗan baabaa Mero.
Ita dai Hassu ba tace komai ba ta nufi inda Addan nata tayi aman ta kwashe ta gyara gurin taje ɗakinsu ta gyara ta ɗauko kayan da aka cire wa Addan nata ta wanke su, Aikin da take kai kace ba yarinya ce ba.
Bayan ta kammala gyara komai ta ɗau buta tai alwala ta shige ɗakinsu dan itama tayi sallahn

💋💋 امى بتولة💋

𝗔𝗟𝗛𝗔𝗠𝗗𝗨𝗟𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜 𝗔𝗟𝗔 𝗞𝗨𝗟𝗟𝗜 𝗛𝗔𝗟𝗘𝗘𝗡, 𝗔 𝗬𝗔𝗨 𝗡𝗘 𝗤𝗨𝗡𝗚𝗜𝗬𝗔𝗥𝗠𝗨 𝗧𝗔 𝗖𝗜𝗞𝗔 𝗦𝗛𝗘𝗞𝗔𝗥𝗔 𝟮 𝗗𝗔 𝗔𝗦𝗦𝗔𝗦𝗔𝗪𝗔
𝗜𝗻𝗮 𝗿𝗼𝗾𝗼𝗻 𝗮𝗱𝗱𝘂𝗼’𝗶𝗻𝗸𝘂 garemu👏

ƳAR UWATA KUMA KOMAI TAWA
𝗔𝗨𝗡𝗧𝗬 𝗨𝗠𝗠𝗜
Ina tayki murnan kammala makaranta ina addu’an Allah yasa al’umman Annabi SAW su amfana da shi

Masoya al’qalamin Uwar batoorl 😁🤝 inayinku
Inasonku
In ji da ku
Ina fatan alkairi gareku ako ina

Wannan littafin kyauta ne dan ku dan farincikin ku, dan tabbas naga soyayya a littafin ‘YAR SARKI CE kuma ance yaba kyauta tukuici so ga TUKUICIN ku♥️🤝

Ayi karatu lfyh
Ina fatan samun qwarin guiwa daga gareku
Dan tabbas zan cigaba da posting ne in naga kuna buqtaan hakan

 

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Uwar batoorl 🕊️

𝘄𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝗹𝗮𝗯𝗮𝗿𝗶 𝗾𝗮𝗴𝗮𝗴𝗴𝗲𝗻 𝗹𝗮𝗯𝗮𝗿𝗶 𝗻𝗲 𝗯𝗮 𝘄𝗮𝗶 𝗮 𝗴𝗮𝘀𝗸𝗲 𝗯𝗮 𝘀𝗮𝗶 𝗱𝗲 𝗶𝗻 𝘆𝗮𝘇𝗼 𝗱𝗮𝗶-𝗱𝗮𝗶 𝗱𝗮 𝗹𝗮𝗯𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗸𝗶/𝗸𝗮 𝘁𝗼 𝘆𝗮𝗻𝗮𝘆𝗶𝗻 𝘁𝗮𝗳𝗶𝘆𝗮𝗻 𝗻𝗲 𝗻𝗮 𝗺𝗮𝘁𝘀𝗮𝗹𝗼𝗹𝗶𝗻𝗺𝘂 𝗮𝗸𝗮𝗻 𝘄𝗮𝘀𝘂 𝗮𝗹’𝗮𝗱𝘂𝘂 𝗻𝗮𝗺𝘂 𝘆𝗮𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 𝘆𝗮𝘇𝗼 𝗵𝗮𝗸𝗮 𝗯𝗮𝘄𝗮𝗶 𝗱𝗮 𝗸𝗲/𝗸𝗮𝗶 ɗ𝗶𝗻 𝗮𝗸𝗲 𝗻𝘂𝗳𝗶 𝗯𝗮.
𝗗𝘂𝗸 𝘄𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘆𝗮 𝘀𝗮𝘂𝘆𝗮 𝗺𝘂𝗻 𝗹𝗮𝗯𝗮𝗿𝗶 𝗸𝗼 𝘆𝗮 𝘀𝗮𝗶𝗱𝗮𝗺𝘂𝗻 𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗳𝗶 𝗯𝗮𝗻 𝘆𝗮𝗳𝗲 𝗯𝗮☹️

𝗡𝗔 𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥 𝗗𝗔 𝗪𝗔𝗡𝗡𝗔𝗡 𝗟𝗜𝗧𝗧𝗔𝗙𝗜 𝗚𝗔𝗥𝗘 𝗞𝗨 𝗠𝗔𝗦𝗢𝗬𝗔 𝗔𝗟𝗤𝗔𝗟𝗔𝗠𝗜𝗡 𝗨𝗪𝗔𝗥 𝗕𝗔𝗧𝗢𝗢𝗟𝗘𝗥𝗛 🕊 𝗙𝗥𝗘𝗘 𝗕𝗢𝗢𝗞 𝗗𝗢𝗠𝗜𝗡𝗞𝗨 𝗔𝗞𝗢 𝗜𝗡𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡 𝗞𝗨𝗝𝗜 𝗗𝗔’𝗗𝗜𝗡𝗞𝗨 𝗗𝗔 𝗦𝗛𝗜
𝗧𝗨𝗤𝗨𝗜𝗖𝗜 𝗚𝗔𝗥𝗘 𝗞𝗔 𝗔𝗞𝗢 𝗗𝗔 𝗬𝗔𝗨𝗦𝗛𝗘 𝗦𝗜𝗥 𝗔𝗕𝗨𝗕𝗔𝗞𝗔𝗥 𝗦𝗔𝗗𝗘𝗘𝗤 (𝗖𝗘O 𝗟𝗔𝗙𝗔𝗭𝗜 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗧𝗘𝗥’𝗦 𝗔𝗦𝗦𝗢𝗖𝗜𝗔𝗧𝗜𝗢𝗡)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍

 

JINJINA DA GAISUWA GAMI DA GODIYA GA MUTANE MASU DARAJA 🤝
QAWAYE NA
MUMMIES
SISTER
QANNENA
DAUTER’S
FAN’S 😁

QAWAYE NA MARUBUTA 💙
ƳAN UWA NA ƊAUKA CIN MEMBER’S NA lafazi writer’s association

Uwar batoorl na matuqar qamnar ku duka 🤝❤️

💋💋 امى بتولة💋

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 3_4

Bayan ta idar da sallah ta gama addu’a muryan Innar su taji tana cewa “Hassu zo ki ɗauki abincin baabaa ki kaimata in kin dawo kici naki”
Girgiza kai Hassu tayi wato dai ita Inna ko a jikinta wai an yakushi kakkausa, rashin lafiyan Adda Innai bai dameta ba.
Tashuwa tayi tayo waje ta ɗauka kwanon abincin baabaa Mero ta wuce dan kai mata.
Da sallama ta shiga gidan, amsa mata baabaa Mero tayi, har ɗakin ta isa ta ajiye kwanon abincin.
Baabaa Mero ta kalleta tace “wannan fa” sai Hassu tace “abincinki ne wai inji Innanmu”
Kice mun inji tambaɗaɗɗiyar uwarku ai dai Allah wadaran naka ya lalace ni Indo na ban mamaki wato ma ki kawo mun abinci na ita takwarata kuma dama ta cike mata fili a gidan mijinta tunda na taho da ita ta huta shikkenan zata koma gidan ubanta bari ta warke ai gidan bana uban wani bane” bala’i take tayi tace “ki ɗauki abincin kikai mata kice ba zanci ba nima ta haɗa ta cinye wataqila tayi jiki kamar shashashar nan Lami”
“Kiyi haquri baabaa” cewar Hassu.
Mai neman kuka an jefe shi da kashin akuya, stohuwa kam kaman jira take sharr sai ga hawaye a idonta tana cewa “yanzu dai duk da ke yarinyace hansai amma dole nayi maganar nan dake ko zanji sanyi a zuciyata, ki duba fa kiga abunda Innar ku keyi wannan Adda taki in kinsan irin wahalan da uwarku tasha da cikinta mu mun ɗauka ma ba zata yi rai ba amma sai Allah cikin ikon sa ya yaye maka ya baka lafiya ka haihu lafiya, yarinya mai hankali da tarbiya da tausayi irin takwarata sai kuma dan gaka kaika kawo kunyan ɗan fari duniya kana gani ɗan ka na neman mutuwa amma ko ah jikinka, nima fa nan bafulatana ce usul ma amma baruwana da wannan al’adah ta shashanci, nasan anayi ana kunyan ɗan fari amma ba irin na Innar ku ba, dan ita nata yabar al’ada ya koma rashin sanin ciwon kai, baiwar Allahn nan Indo tana fa gidan nan har na shiga har na fito ko leqowa bata yi ba gwanda wannan tambaɗaɗɗiyar munafukar ma ta leqo wai itama da bata taɓa haihuwa ba a ɗauki kyautan yaro a baka ka wulaqanta, ina na taɓa jin wannan tambaɗewan ni meramu daso amma dai malam bai yi sa’an mata ba wallahi”
Hassun ta qara cewa “kiyi haquri baabaa Allah bawa Adda Innai haquri nima abun ba yamun daɗi amma zai wuce”
Tashi kije to badon halinta ba zamu ci abincin kuma Allah zai saka wa takwara, ke kuma Allah miki albarka Allah qara tausayi da qauna tsakaninki da ƴar uwan ki” Da “Ameen” ta amsa ta tashi ta fice a gidan.

Baba mero sai fama take da jikar tata akan cin abinci tace “ke kuma ja’ira tunda kin samu kin farka sai ki tashi kisha wannan furar ko ƴan hanjin ki zasu yi qwari kisamu kisha magani”
Hawaye take tana yarfe hannu tana cewa “nikam baabaa na qoshi Allah”
Baabaa tace “Kin qoshi dan ubanki Isa nace kin qoshi uwar ki Indo kika ci?ba ki da lafiya amma sai shegen taɓara to in baki rufemun baki kin tashi kin karɓa kinsha ba zan hau ruwan cikin ki na zauna tunda kinsan yacce kike kamar taliyar murji yanzu sai na qarisa ki kowa ma ya huta”. Yarfe hannu take tana hawaye taqi amsan furar balle magani.
Baabaa Mero ta ɗaura hanu a ka tace “ooh ni Mero ƴar Amadu yanzu takwara da ace Indo ta jaki jiki kam bansan ya zaki zama ba mutum kaman narkakken tuwon da bai nuna ba gaskiya duk wanda ya aureki ya kwasawa kansa jaraba da taɓara yarinya kin kai zaman ɗakin miji amma tsabar fitinan ki qanwarki har ta fiki auki da kazar-kazar na masu lafiya kullum ke kamar wacce masu tanɗe lashe suke kame da kurwar ta, Allah na tuba maka ni jikar mai allo”
Ganin dai ba karɓan zata yi ba sai ta koma rarrashi dan tasan abarta “haba takwarata shalelen babanta Meramu uwar Isa Maryam farar zinariya mai alkairi kinfi qarfin uban mutum balle ɗan mutum, Maman babanta ƴar gaban goshin baabaar ta”
Turo baki tayi dan bata son yacce take ce mata Meramu suna ba ko daɗin ji.
Da lallaɓa da lallami dai a haka har ta samu tasha furan ta kuma shan maganin amma hawaye kam in zaka kawo drum to zaka cika da hawaye, tana gamawa ta koma ta kwanta bacci yayi awun gaba da ita”
Kama haɓa baabaa Mero tayi tasa jikar tata a gaba da kallo tace “ooh ni Allah na nagode maka Allah ka rayamun wannan zuria’a nawa Allah ka shiryamun su, yarinya jiki a sake kaman sakakken roba abu kaɗan sai kwanciya kaman kiste, duk mutum ba auki kaman ruwan aski to Allah dai ya baki lafiya Meramu”
Itama baabaa kishingiɗewa tayi a kan nata gadon.

Can dare bayan sallahn magrib wani dattijo ya shigo gidan bakinsa ɗauke da sallama.
Inna A’i da Mama Lami suka yi da suke zaune suke cin tuwo suka amsa masa suna masa sannu.
Hassu ta tashi ta amsa ledan da ya shigo dashi tana faɗin “sannu da shigowa Baffai” Amsa mata dattijon yana shafa kanta yace “sannun yar Baffai”.

Bayan Hassu ta kai masa ledan ɗakin Innar ta kasancewan ita ce da girki sai ta wuce ɗakin su, ganin ba ƴar uwan ta a ɗakin sai taji ya mata girma.

Inna ta tashi ta bisa takai masa ruwa tana sannu da dawowa malam.
Baffai yace “yauwa matar aljanna sannun ku da gida kuma ya aiki?
“Alhamdulillahi” ta faɗa tana murmushi sannan tace “malam a kawo maka abincin nan ɗakine ko-ko zaka ci a waje nasan kayi sallah kam”
Yace “a kaimun waje wannan zafin ɗakin sai a hankali”
Tashuwa tayi ta ɗauki taburma tayi waje.
Shumfiɗa masa taburman tayi ta ɗauko tiren kwanun abincin da ruwa duka ta kawo kan taburman.
Komawa ɗakin tayi tace “malam an kai komai”
“To Allah miki albarka matar aljanna ina futowa” ya faɗa yana miqewa.
Komawa tayi wajan Mama Lami suka ci-gaba da cin tuwon nasu suna hira sama-sama.
Bayan ya gama abunda zai yi ne ya fito da bismillahirrahmanirrahim ya zauna, Tashuwa Inna tayi tazo ta sa masa ruwa ya wanke hannu ta buɗe masa kwanon tuwon, Bismillah yayi ya fara cin abincin.
Mama Lami dai taɓe baki tayi ganin abinda Inna ke yi.
Bayan yaci abincin ɗan dai-dai ya wanke hannu yayi hamdala yana sanya musu albarka sai ga sallaman Magaji yana shigowa.
Ganin dattijon sai ya nufo wajansa yana faɗin “Baffai ka dawo ne sannu da dawo wa”
“Eh baban Baffai na dawo, yauwa dai nikam ina uwata ce tun dawowa na banji mostinta ba lafiya kam?”
Inna dai bata ce komi ba kaman ma bata wajan aka yi tambayan, dama kowa dake wajan ya tsammani haka dan sanin halin nata.
Lami ba kiji bane? baffai ya qara maimaitawa.
Ehm ɗan kame-kame ta fara “malam dama bamu son ɗaga maka hankali ne tunda jikin ba har can ba dan bata ɗan ji daɗin jikinta ba, to ɗazu dai tace zata gidan baabaa tana can bata dawo ba”
Magaji ya buɗe baki ganin ikon Allah shararo qarya ba ko tsoro kaman boka, duk da dama yasan matma Lami da iya lauye magana za tayi fin haka ma.
Sai kawai yace “eh Baffai bata da lafiya tana gidan baabaa Mero”
Baffai yace “to Allah ya sauwaqa ya bata lafiya, sai kaci tuwo muje muyi sallahn isha’i mu biya naga yaya jikin nata”
“To Baffai” ya faɗa a taqaice ya tashi ya shige ɗakin da yake mallakin sa.
Ɗaki 1 na Magaji
Ɗaki 1 nasu Hassu
Ɗaki 1 na Inna A’i
Ɗaki 1 na Mama Lami

Shigewa yayi yana qara ganin qoqari irin na mama lami wajan iya zagewa ta laftowa Baffai qarya duk da bai san mene asalin abunda ya faru ba amma dai yasan shigowan sa bata tsakar gidan ma kuma ba ita takai Innai gidan baba mero ba sannan ba ita taje da kanta ba tunda dai shine ya kaita, Inna dake nuna halin ko inkula akan ƴar tata tana basa mamaki ba ɗan kaɗan ba, Shima dai gashinan shine ɗan fari agidansu amma ba ruwan gwoggonsu da wannan abun al’ada-al’adan.
Zaunawa yayi yaci tuwonsa bayan yag ama ya fito da kwanukan.
Alwala yayi yace “Baffai mu tafi masallacin ko”
Fita suka yi a gidan suka wuce masallaci suka yi sallah sannan suka wuce gidan baabaa. Da sallama suka shiga gidan, samunta suka yi itama ta idar da sallahn kenan tana jan carbi.
Innai ce ta fito a ɗaki tana cewa “sannu da zuwa Baffai na” ta shumfiɗa masu tabarma.
“Sannu maman baffanta ya jikin? A taqaice tace “da sauqi baffai” .

Suna zaune sai suka ji sallaman Baba. Duk suka amsa masa ya shigo ya samu waje ya zauna.
Magaji ne ya gaishe sa ya amsa sai Baffai da yace masa “sannu da shigowa yaya” suka gaisa.
“Baba sannu da zuwa” cewar Innai da kanta ke qasa.
“yauwa maman Baba da Baffai sannunki ko, yau kuma a gidan takwara ake hirane” faɗin Baba cikin kulawa.
Langwaɓar da kai tayi tace “a’a fa Baba banda lafiya ne shiyasa”
Ashshaa! sannu maman Baba Allah baki lafiya ko
“Ameen” cewar baabaa Mero da ta shafa addu’a.
Kallon su tayi duka, gaisheta Baba yayi ta amsa Magaji ma ya gaidata ta amsa sannan Baffai ya gaidata amma tayi kaman bata kallesa ba ma.
Kansa aqasa yace “baabaata me nayi amun afuwa”
Cikin karaji tace “Au tambaya kake mevkayi bayan ka tara marassa tausayi da imanini a gidanka wai matanka”
“Ayi haquri baabaa Inshà Allahu ba zasu qara ba” cewar baba cikin sigar rarrashi.
“Bawani ba zasu qara ba Musa ka qyaleni da me sunan mallam na zaure, wato shi dai ba zai wa Indo nasiha da faɗa ta gyara halinta ba, ace mata suna gani suna ji yarinya ta kusa mutuwa amma ba mai temaka mata dan tsabar jaraban mugunta ai ba amfanin zaman su a gidan, Ita kuma wannan gulmammiyar Lami sanda ta ganni wai ta fito duba yarinyan wai duk wannan lokutan da yarinya ta kwasa a zube a qasa wanwar a sume duka walha take yi dan ta maida waye sha-sha-sha, Walha a gidan wa inba ganin arahan gabas da kuma renamun hankali da tayi ba yaushe ta tsaida sallah biyar 5 a rana ma bare ta qara da nafila, ni dai waɗannan marassa imani da ka tara a gida basu da amfani a wajena” baabaa ke maganan kaman zata rufe Baffai da duka.
Haquri suke ta bata dukan su, ita dai Innai ba tace komai ba saima tashuwan da tayi ta wuce ɗakin tsohuwar.
Da qyar suka lallaɓa stohuwar tasu sannan tabar faɗan da take yin, Baba yace “Insha Allah za’a gyara baabaa sannan kai kuma baffan Magaji ka musu faɗa sosai dan nima abun nan da Innar su keyi bayamun daɗi”
Baabaa tace “Ka qyaleshi dai tunda shi sha-sha-sha ne sha-giri girbau sun maida shi mijin tace, yana zaune zasu kashe masa ɗiyar sa da Allah ya basa, tom ni dai bazan bari haka ta faru ba daga shi ɗin har su zan yi dai-dai dasu”
Haquri Baffai ya bada akan za’a gyara zai musu faɗa.
Magaji yana zaune gefe be ce komi ba a zanceb iyayen nasa.
Baabaa Kallon magajin tayi tace “to kaima zan dawo kanka, wai kana boko kana nan ka gama girme mana a gida sai ka rasa wacce zata auri tsoho irinka ai”
Haɗe fuska yayi yasan dama tijaran stohuwar nan da yawa bata qyale kowa.
“Yauwa baabaarmu a faɗa masa ya nemo mata” cewar Baba.
Baffai yace “a dena takura wa yarona bai gama girma ba tukun”
taɓe baki baabaa Mero tayi tace “wannan zindiqin baligun yaron ne bai girma ba? Shikkenan zan kuwa bada shi sadaka wa wata baiwar Allah ba da jimawa ba”
Qwalawa Innai qira baabaa Mero tayi “takwara, takwaraa, takwaraaa zo nan”
Zuwa tayi ta zauna gefen baabaa Meron.
Baabaa tace “niifa banson zaman ɗakin nan kaman munafuka”
Baba ya kallesu yayi murmushi, cewa yayi “baabaarmu kar dae mu jiki da takwararki”
Baabaa tace “Allah sauwaqa a jimu”
Baba ya maida kallonsa kan Innai yace “mamar baba meke damunki?
take idonta ya kawo ruwa, cikin shagwaɓa tace “Kai na ke ciwo sai ciki na”
Salati baabaa Mero tayi tace “kunga ja’irar ƴarku ko tun da rana nake binta ta faɗa mun amma taqi faɗin meke damunta sai yanzu dan taga iyayenta shikkenan zaki tashi ki bisu dama ba za’a bar Hassu ita kaɗai ba tun da dai ke ma munafurcin kike son koya yarinya kaman narkakken tuwo, nan yanzu ma daga tambaya sai kuka, ooh ni Mero Allah nagode maka shikkenan ai kema ɗin tattara ki zamu yi mu aurarki”.
Suka ci-gaba da hiransu da baabaar tasu cikin raha, ita kuma Innai ta kwantar da kanta a qafan baabaa mero.
Magaji ya tashi ya fice yace da iyayen nasa in sun gama yana waje.
Baabaa Mero ta bisa da harara tana cewa “mutun sai jarababben baqin hali ai zaka ji dashi dan ni dai ba kayo halin miji na ba”.
Can su Baffai suka wa baabaar tasu sai da safe suka fice a gidan.
Magaji bayan ya fito wucewa yayi dandalin dake qauyen direct abunsa, Baffai da suka fito basu gansa ba sunsan za’ayi haka daman dan haka tafiyansu suka yi suna hira na yan uwa.
Baba ya qara jan kunnen Baffai akan abinda matansa keyi, lallai ya musu faɗa su gyara hakan bai kamata ba inba dai basu son zaman lafiya da baabaa Mero ba.
Bayan ya gama jaddada wa ganin nasa sai suka yi sallama Baffai ya shige gidansa kasancewan basu da nisa da baabaa Mero, Baba ma ya wuce nasa gidan dake gaba da na Baffai ba sosai ba.
Ya shigo gidan ya samu duk basu tsakar gidan, ɗakin Innar su Hassu ya wuce da sallama ya shiga, samun ta yayi ita da Hassu suna taɗi tana haska mata tana homework nata( kasancewansu fulani kuma waɗanda ke qauye bai hanasu karatun boko ba tunda yanzu duniya a waye take).
Ganin Baffai ya shigo ta tashi ta tattara littatafan nata dan dama da gama ta masu seda safe, albarka Baffai ya sanya mata. Ɗakin mama Lami ta wuce dan ba zata iya kwana a ɗakinsu ita ɗaya ba tsoro take ji in ƴar uwanta batanan.

Dasallama ta shiga,amsa mata mama Lami tayi.
Bata dai ce mata komi ba ta haura gado qarami dake ɗakin bayan ta kakkaɓe ta kwanta ta lulluɓu abunta, mama lami ba tace mata qala ba kawai ita ma lulluɓuwan ta tayi sai bacci kuma.

Baabaa Mero ta lallaɓa Innai taci tuwo ta qara shan magani, suna hiransu baabaa mero na mata ta-tsuniya, har suka kwanta zuciyan ta cike da tunanin ƴar uwanta zata kwana ita ɗaya a ɗakin nasu gaba-ɗaya sai taji ba daɗi, a haka suma har baccin ya ɗauke su.

Baffai tunda ya zauna nasiha yake mata akan inba zata daina wannan halin ba to ta rage don kuwa bai kamata ba, Allah zai mata hisabi tsakaninta da ƴar da ya bata.
“Aishatu su yara da kike gani da Allah ya bamu amana ne ya bamu ba wayonmu ko dabarar mu ba, amana kuwa kinsan ko ɗan adam ne ya baka to dubi abunda sakaci da amanansa keja maka balle wanda ya haliccemu da kansa ya bamu amana muyi sakaci dashi me kike tunani a kai? Tabbas wannan ba al’ada bane A’ishatu dan naki ya wuce a qira sa da hakan, dan girman Allah ki aje wannan abu a gefe ki rungumi abunda Allah ya azurtaki dashi, dan su ‘ya’ya arziqi ne babba ma kuwa, ko kina ga a wannan duniya tamu in uwa ba taja ɗan ta a jiki ta soshi ba wani zai so mata shi ne? Ko ɗaya dan wannan alhaqi ne dake kan uwa kuma duk abinda wani zai nuna wa ɗan ki na soyayya ko tsangwama(hantara/qiyayya) to kece sila dan kece malamar da kika nuna hakan a koyarwanki. Dan girmam Allah ki gyara A’ishatu kamun lokacin hakan ya qure miki”.
Inna kanta a qasa bata ce komi ba illa iyaka “ayi haquri malam”
Tashuwa tayi ta haye gado ta kwanta
Shima baffan hawa yayi dan ya lallashi matar aljannan sa, tunda yaga abun sai a juya ɗayan sigan dagann sai…….

 

𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚’𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 – 250 𝟏𝐆𝐁 – 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 500
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 750

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎

***
RUGAN HAMMAN
Shine sunan rugar tasu, ruga ce da takenan kaman gari ba ruga ba sakamakon cikan da tayi da kuma cigaba da ake samu a rugar ta hanyan asibiti da makarantu etc…
fulanine mafiya yawa a rugan sai ɗaɗɗaya-ɗaɗɗaya dags wasu yaruka kaman bolawa, terawa, wajawa har da hausawa.
Rugan ya xama kaman garine sakamakon fulanin rugan mazaunane ba matafiyaba, suna gudanar da rayuwansu cikin nasarorin cigaba Alhamdulillahi.
Suna karatun muhammadiya sosai da boko duk da basu da na gaba da primary, rugan nasu na qarqashin qaramar hukumar 𝘼𝙨𝙝𝙖𝙠𝙖 dake garin 𝙜𝙤𝙢𝙗𝙚 state.
In mutum ya gama yaqi da jahilci da primary a rugan sukan fito cikin qaramar hukumar ashaka dan ci-gaba da secondary….

ZANCI GABA DA POSTING NE KAWAI IN NAGA YAWAN COMMENTS NAKU

09161720046
Mrs big barbieyh ✍️

 

💋💋 امى بتولة💋

𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
09161720046
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
07015870735
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁

NOTED : karku nemeni a wannan layi 08146292652 domin yanzu baya aiki both whatsapp and call.

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

 

𝗝𝗔𝗛𝗜𝗟𝗖𝗜 𝗞𝗢 𝗔𝗟’𝗔𝗗𝗔𝗛? 🥺

Al’qalamin

Uwar batoorl 🕊️

Na sadaukar da wannan shafi sukutum gare ki TATTAƁA KUNNE NA fatan farinciki a rayuwanki da na iyalanki har abada.

Masoya na ababen qaunata ba zaku irgu ba♥️ fatan alkairi gare ku

Adama Umar marubuciyar – halak ɗina (inayin wannan littafi naki Allah qara basira da ɗauka ka)

𝗙𝗮𝗻’𝘀 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗸𝘂𝗻𝘀𝗮𝗻 𝗸𝘂 𝗻𝗮 𝗱𝗮𝗯𝗮𝗻 𝗻𝗲 🤙 𝘀𝗮𝗶 𝗱𝗮 𝗸𝘂𝘂𝘂𝘂
𝗨𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗻𝗮 𝘆𝗶𝗻𝗸𝘂𝘂𝘂𝘂 𝗼𝘃𝗲𝗿! 𝗢𝘃𝗲𝗿! 𝗢𝘃𝗲𝗿

𝗠𝗮𝘀𝘂 𝗰𝗼𝗺𝗺𝗲𝗻𝘁’𝘀 𝗱𝘂𝗸 𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵 𝘆𝗮 𝗯𝗮𝗿𝗺𝗶𝗻𝗶 𝗸𝘂 😘
𝗠𝗮𝘀𝘂 𝗯𝗶𝗻𝗮 𝗽𝗿𝗶𝘃𝗮𝘁𝗲 𝗱𝗮 𝗮𝗱𝗱𝘂’𝗼𝗲 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗯𝗼 𝗱𝘂𝗸𝗮 𝗶𝗻𝗮 𝗺𝗮𝘁𝘂𝗾𝗮𝗿 𝗴𝗼𝗱𝗶𝘆𝗮 𝘄𝗮’𝗱𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗯𝗮𝗻𝘀𝗮𝗺𝘂 𝗻𝗮 𝗱𝘂𝗯𝗮 𝗺𝗲𝘀𝘀𝗮𝗴𝗲’𝘀 𝗻𝗮𝘀𝘂 𝗯𝗮, 𝗶𝗻𝗮 𝗺𝗮𝘁𝘂𝗾𝗮𝗿 𝗯𝗮𝗸𝘂 𝗵𝗮𝗾𝘂𝗿𝗶 𝗮𝗯𝘂𝗯𝘂𝘄𝗮𝗻 𝗻𝗲 𝘀𝘂𝗸𝗮 𝘆𝗶 𝘆𝗮𝘄𝗮 𝗮𝗺𝗺𝗮 𝗸𝘂 𝘀𝗮𝗻𝗶 𝗸𝗼 𝗱𝗮 𝗯𝗮𝗻𝗴𝗮𝗻𝗶 𝗯𝗮 𝗸𝘂𝗻𝗮 𝗿𝗮𝗶𝗻𝗮 🥺💯

𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍

 

 

 

💋💋 امى بتولة💋

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 5_6

 

Tana tashuwa da safe bayan sunyi sallah sun idar ta ɗau stinstiya ta share ɗakin ta gyara musu sannan ta fito tana share tsakar gidan.
Baabaa Mero da fitowan ta kenan daga banɗaki ajiye butan hannunta tayi tace “ke dai takwara Allah kawo miki sauqi ko kaɗan bakya gajiya da wahala shiyasa gakinan ba auki kaman taliyar murji dan nemawa mutane wata jarabar ba ki da lafiya kin kama aiki, yarinya sai son manyance kaman wata babbar mata”
Innai tanajin stohuwar amma ko a jikinta sharan ta gama ta tattara kwanuka tace “baabaata bari nakai kwanukan gida na dawo”
Baabaa Mero taɓe baki tayi ta karyi goronta sannan tace “in kinga dama karki dawo sai bayan shekara 100, wahalalliya kawai ai so kike kije ki aikatu da jikin da ba kiji sauqi ba, yarinya sai shegen jarabar rashin ji, ni dai Allah ya gani ba haka halina yake ba wai ance mutum yakan iyo halin takwaransa to aradu baki biyo halina ba dan ni nan bana barin ko ta kwana sannan bana ɗaga qafa ba ruwa na da jarabar haukan stiya amma ke a masu suna Maryam ɗin ma kamata yayi ace maki damo(sarkin haquri) yarinya zuciya kaman kare ya lashe, ni ɓacemun daga gani kamun na qarisa ki da kaina” ficewa Innai tayi tana murmushi bata tsaya sauraran baabaa Mero ba dan tasan duk da sonda take mata yanzu zata iya kwaɗa mata abu.
Baabaa Mero ta ci-gaba da mitan ta kaman zata daki babu sannan ta ɗauko kwanon madaran da ta ajiye dan ta bawa takwarar tata tasha da magani sai kuma ta bostare ta tafi gidan nasu da zata mutu bamai kallonta, zama tayi ta shanye abunta tass sannan tace “Allah ganar da ke mai qaunanki takwara”.
Fitowa tayi daga gidan baabaa Mero tana murmushi, tafiya take cikin nustuwa wanda wasu sukan ɗau tafiyan nata akan rigima ta keyi.
Yarinyace yar kimanin shekara 14 da haihuwa amma in ka ganta sai kace takai 16 year’s, domin halittan da Allah ya mata. Fara ce sol kuma Siririya ce ba mai jiki ba(qiba) abunka da bafulatana, amma rashin jikinta da qarancin shekarunta bai hana halittar da Allah yayi mata bayyana ba dan tun bata gama girman ba maqerin budurci ya bayyana gare ta.
Tana da qugu(mazaunai), kuma duba da gashin dake kwance gaban goshinta da kuma sajen fuskanta hakan ya isar da cewan Allah ya mata baiwan gashi Masha Allah! Round face take dashi mai ɗauke da dara-daran idanunta (golden eyes) farare ne tass kaman madara kai kace idon jinjirine haka baqinma baqi wuluk, tana da yalwan cikan gashin gira wanda har ya haɗe hakan kuwa sai ya bada wani sirri a kyau nata, Tanada dogon hanci wanda shi da biro banbancinsu kawai rubutu ne, ɗan madedecin bakinta wanda inka gani za kayi mamakin anya tana ma cin abinci kuwa tsabar qanqantarsa, tabarakhallah Masha Allah don kyakkyawace ta ajin qarshe wanda qarancin shekatunta basu ɓoye ni’imomi da baiwan da Allah ya azurta ta dasu ba, duk da bawai girman ya gama bayyana a gareta ba.
Innai kenan wacce asalin sunanta shine Maryam takwara ga mahaifiyar Baffanta wato baabaa Mero.

A nuste tayi sallama ta shiga gidan nasu ta kuma yi sa’a baffanta na nan, ta samu Innar su na aikin ɗumame qanwarta Hassu kuma na shara.
Kallon Innar tasu sai jikinta yayi sanyi amma a haka ta qarisa wajanta, durqusawa tayi har qasa tace “jamɓanduna Inna”
Inna A’i kanta a gefe tana ayyukan ta ko juyowa ta kalli yarinyar nata ba tayi ba kawai ta girgiza kai alaman ta amsa gaisuwan.
Daman in da sabo ta saba da hakan tasan iya abunda Innan tasu za tayi kenan, kanta a qasa haryanzun jiki a sanyaye kaman kullum in hakan ya faru ta wuce ɗakin mama lami.
“Jam ɓanduna mama”
(Antashi lafiya mama)
“Jam innai noi ɓandu ma”
(Lafiya innai ya jikin ki)
“Ɓandu waɗu dama”
( jiki dasauqi)
“To Allah hokke en jam”
(Allah qara sauqi) Mama Lami ta faɗa tana jera kwanukan ta.
Da “Ameen” Innai ta amsa sannan ta miqe ta fito a ɗakin.
Hassu ta gaishe ta cikin fillanci tana tambayan ta jikin nata “Adda Innai noi ɓanduma?” “Ɓandu waɗu dama Hassu am”.
Mawanki ta wuce dan tayi wanke-wanken, Hassu tace “Adda zanyi wanke-wanken ki bari ki huta abunki kinga baki da lafiya”
Murmushi kawai tawa qanwar nata ba tace komai ba. Haɗa kwanukan wanke-wanken tayi da wanda ta shigo dasu daga gidan baabaa duk ta wanke su, bayan ta kammala ɗakinsu ta wuce ta gyara musu.
Tana kammala ayyukan ta Hassu ma ta gama sharan da take yi dai-dai Baffan su ya fito a ɗakin Innar su sai dukansu suka nufe sa, suna zuwa suka stugunna suka gaishe sa cikin fillanci.
Amsawa yayi yana sanya musu albarka sannan ya tambayi Innai jikinta, da sauqi ta amsa masa, duk gaisuwan da suke yi da fullanci suke magana.

Magaji ya fito a ɗakin sa shima ya tsugunna ya gaida Baffan nasu, Baffai ya amsa cikin fara’a. Gaishe da shi Innai da Hassu suka yi ya amsa masu sannan shima ya tambayi ya jikin Innai ɗin, da sauqi ta amsa masa.

Albarka baffa ya sanya musu duka yace kowa yaje ya karya.
Inna ke madafi tana raba musu abun karyawan, Innai zuwa tayi tace “Innan mu bari in qarisa miki”
Ba tare da Inna tace komai ba ta tashi ta fice a madafin.
Qarisa wa Innan ta aikin tayi ta raba komi har da madaran da Hamman su magaji ya kawo ta raba ta sawa kowa nasa, ta kaiwa Hamman su nasa har ɗakinsa sannan ta qira Hassu kuma takai na Baffai, ita kuma ta miqawa su Inna nasu, Hassu ta ɗauka musu nasu suka yi ɗakinsu da shi.
Ɗumamen tuwon surfaffen masara da aka wanke yayi haske sosai da miyar ɓaskoje bushashshe(bushashshen kuɓewa) da yaji nama da man shanu, sai naman zabbi da kuma madaransu mai ɗumi.
Karyawa suka yi sannan suka haɗa kwanukan Hassu ta wanke masu bayan ta dawo kai wa baabaa Mero nata.

Ɗakinsu suka shige ko waccen su ta kwanta dan hutawa amma kowa da abunda take tunawa a ranta.
Innai da ta faɗa duniyar tunani hawaye ne ya gangaro a idonta wanda ke nuni da damuwan da take ciki, sai tace “Duk da kasancewana yarinya amma abun na damuna anya Inna ce ta haifeni anya ba tsintata suka yi ba suke ɓoye mun” sai kawai ta fashe da kukan da bata san ma ya qwace mata ba.
Hassu ta tashi tana cewa “Adda Innai ɗume?”
Innai cikin hawaye tace “Hassu jam, wala ko ɗume”
Itama hawayen ta fara tana magana cikin harshen fillanci “Adda Innai ki faɗamun bana son ganinki cikin damuwa in baki faɗa wa ƴar uwanki abinda ke damunki ba wa zaki faɗa wa?”
Cikin Kukan tace “Hassu ba zaki fahimta ba ko na faɗa miki, Hassu inajin kaman zan mutu bansan me nawa Inna ba bansan me yasa Inna bata qauna ta Inna bata sona kaman ba ita ta haifeni ba” ta faɗa tana hawaye
Haquri take bata itama tana kukan “Adda kiyi haquri Allah Inna na sonmu kinji” cewar Hassu tana rungume ƴar uwanta
Haka suka rungumi juna tana taya Addan nata kuka kai kace marayu ne ko kuwa mutuwa aka musu.

Baffai ne a ɗakin Inna bayan ya gama karyawa yace “tom A’ishatu yanzu ke me shawaranki akan makarantan Innai da nake son tayi gaba, dan gaskiya wannan al’ada ta aurar da yara da wuri ba ruwa na, ni ba wani al’adan da zan gwada wanda yake kaman jahilci ya sanya na cuci rayuwan yara na”
Shiru Inna tayi ba tace komai ba, Baffai cikin hasala da quresa da halin ta ke yi yace “wai ke A’ishatu me yasa kika zaɓi haka ne? Ko kaɗan baki son gaskiya na jima da fahimtan ki, wannan ƴar taki baki tunanin da qanqantan ta ciwon zuciya zai iya kashe miki ita، wannan kalan banzan al’adan naki zai sanya ki tafka babban asara tunda kina uwa amma zai sanya uwa ta gagara ceton rayuwar ɗiyarta sannan ta kasa mata abunda zai zama ci-gaba a gare ta har da ita uwar kanta tunda komi ɗa ya samu a rayuwa ba mai amfanuwa ko morar sa irin uwarsa barin ma dai ɗiya mace, A’ishatu yanzu ke baki tunanin Innai zata fara tunanin ba kece kika haifeta ba shiyasa kike mata haka? Yarinyar nan ki godewa Allah da yayo ta da haquri sannan ki kiyayi ranar qarewan haqurin ta ɗan aje-aje zata daina kallonki matsayin mahaifiya irin halayen da kike nuna matan nan” ita dai Inna kanta na gefe bata ce komai ba har yanzun.
tsaki Baffai yaja a hasale ya miqe ya fice a ɗakin dan in ya cigaba da zama zasu iya samun mastala.
Ɗakin magaji ya wuce, ganin Baffai sai Magaji ya tashi ya zauna yana cewa “Baffai da kanka ba ka qirani ba”
Baffai cikin murmushi yace “bakomi baban baffa, yanzu dai shawara nazo muyi game da yar uwanka, yanzu kaga sunyi wannan jarabawa wai na gama firamare(primary) to kana ga ya za’ayi ta wuce gaba ina tunanin zai fi ba”
Magaji yace “Baffai gaskiya ya kamata kam ta wuce gaban inya so sai a lallaɓa baabaa ta ajiye batun aure a gefe tunda ko saurayi bata da shi, kuma sai dai a nemi na zuwa a dawo dan makarantan kwanan nan sai a hankali”.

Baffai yace”amma Magaji samun abun hawan da zai ke kai ta ya dawo da ita ba matsala ba”
Magaji yace “babu matsalan komai Inshà Allah Baffai, kawai a nema mata wanda zai ke kai ta yana dawo da ita nasan za’a samu ko yawale aka wa magana sai ake biyansa duk sati ko wata”
“Shikkenan in taji sauqi sosai sai kuje kuyi komai anan cikin Ashakan” cewan Baffai cikin gamsuwa da shawaran yaron nasa.
Magaji yace “to Baffai Allah ya qara mata lafiya ya kuma qara buɗi da girma”
Da “Ameen” Baffai ya amsa sai suka ci-gaba da tattaunawa kamun can Baffai ya miqe yana faɗin “Magaji ba na fita to kasan akwai wani ruga nan gefen mun nan tom akwai wata baiwar Allah ba taji daidiba an aiko naje”
Miqewa shima Magajin yayi yana cewa “a dawo lafiya Baffai Allah bata lafiya” Tare suka fito a ɗakin.
Suka bi gidan baabaa mero suka gaisa kamun Baffai ya fice ya tafi rugan dake gefen nasu.

Baabaa mero ta kallesa tace “yanzu kai Magaji ka gaya wa kanka gaskiya biyewa baffanku kake yi ko, in na maka maganan aure sai ka haɗa fiska kaman shanun huɗa(garma), kaman wani mara ishashshen lafiya, to dan Allah in ma lafiyan ne baka da shi ai ka gaya mun na nema maka magani, yo me abun kunya a ciki ni da na haifi ubanka mene ban sani ba, kawai kace mun Baabaa abun baya tashi ko bakajin buqatuwa, shikkenan magana mai sauqi niko na bazama na nema maka magani yacce zaka koma kaman doki dan qarfi, amma ka girma ka riqa ka balage kaqi aure wai kai boko ba bokoko a wuta aradu sa’annin ka akwai masu yara huɗu wasu har shida ma, shikkenan ya rage maku kai da Baffan naku in ma baqin ciki yake wa kansa na ganin jikokin sa to kansa ya wa sai nan gaba zaku san soyayyace nake muku shi yasa na matsa kuyi aure….

𝗜𝗬𝗔 𝗬𝗔𝗪𝗔𝗡 𝗦𝗛𝗔𝗥𝗛𝗜𝗡 𝗞𝗨 𝗜𝗬𝗔 𝗬𝗔𝗪𝗔𝗡 𝗣𝗔𝗚𝗘 🙃

ZANCI GABA DA POSTING NE KAWAI IN NAGA YAWAN COMMENTS NAKU

09161720046
Mrs big barbieyh ✍️

 

💋💋 امى بتولة💋

𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
09161720046
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
07015870735
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁

NOTED : karku nemeni a wannan layi 08146292652 𝗱𝗼𝗻 𝘆𝗮𝗻𝘇𝘂 𝗯𝗮𝘆𝗮 𝗮𝗶𝗸𝗶 𝗯𝗼𝘁𝗵 𝘄𝗵𝗮𝘁𝘀𝗮𝗽𝗽 𝗮𝗻𝗱 𝗰𝗮𝗹𝗹

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

𝘽𝙮

UWAR BATOORL 🕊️

𝗪𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝗹𝗮𝗯𝗮𝗿𝗶 𝘀𝘂𝗸𝘂𝘁𝘂𝗺 𝗻𝗮𝘆𝗶 𝘀𝗮 𝗸𝘆𝗮𝘂𝘁𝗮 𝘀𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝗻𝗮 𝘀𝗮𝗱𝗮𝘂𝗸𝗮𝗿 𝗴𝗮 𝗺𝗮𝗵𝗮𝗶𝗳𝗶𝘆𝗮𝘁𝗮 𝗶𝗻𝗮 𝗳𝗮𝘁𝗮𝗻 𝗱𝘂𝗸 𝘄𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘆𝗮 𝗸𝗮𝗿𝗮𝗻𝘁𝗮 𝘆𝗮 𝗺𝗮𝘀𝗮 𝗱𝗮𝗱𝗶 𝘆𝗮 𝗮𝗺𝗳𝗮𝗻𝗮 𝗱𝗮 𝘀𝗵𝗶 𝘀𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝘆𝗮 𝗱𝗮𝘂 𝗱𝗮𝗿𝗮𝘀𝗶 𝗮 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝘀𝗮 𝘇𝗮𝗶 𝘄𝗮 𝗺𝗮𝗵𝗮𝗶𝗳𝗶𝘆𝗮 𝘁𝗮 𝗛𝗔𝗝𝗜𝗬𝗔 𝗠𝗔𝗥𝗬𝗔𝗠𝗔 𝗮𝗱𝗱𝘂’𝗮 𝗱𝗮 𝗯𝗮𝗸𝗶𝗻 𝗸𝗮/𝗸𝗶 𝗺𝗮𝗶 𝗮𝗹𝗯𝗮𝗿𝗸𝗮 𝗶𝗻𝗮 𝗺𝗮𝗶 𝗿𝗼𝗾𝗼𝗻 𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵 𝘆𝗮 𝗮𝗺𝘀𝗮 𝘆𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗷𝗶 𝗾𝗮𝗻 𝗶𝘆𝗮𝘆𝗲𝗻𝗺𝘂 𝗴𝗮𝗯𝗮 𝗱𝗮𝘆𝗮 𝘄𝗮𝗱𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘀𝘂𝗸𝗲 𝗿𝗮𝘆𝗲 𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵 𝗾𝗮𝗿𝗮 𝗺𝘂𝘀𝘂 𝗹𝗮𝗳𝗶𝘆𝗮 𝘆𝗮𝘀𝗮 𝗺𝘂 𝗿𝗮𝗯𝘂 𝗱𝗮 𝘀𝘂 𝗹𝗮𝗳𝗶𝘆𝗮
𝗔𝗹𝗹 𝗺𝗮𝗿𝘆𝗮𝗺’𝘀 𝘄𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗳𝗶 𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝘀𝗵𝗮𝗳𝗶 𝘀𝗮𝗱𝗮𝘂𝗸𝗮𝗿 𝘄𝗮 𝗴𝗮𝗿𝗲 𝗸𝘂, 𝗶𝗻𝗮 𝗳𝗮𝘁𝗮𝗻 𝘇𝗮𝗸𝘂 𝘀𝗮𝗻𝗶 𝗮 𝗮𝗱𝗱𝘂’𝗼𝗲𝗻𝗸𝘂 𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵 𝗮𝘇𝘂𝗿𝘁𝗮 𝗻𝗶 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗿𝗶𝗻𝘆𝗮 𝗺𝗮𝗰𝗲 𝗺𝗮𝗶 𝗮𝗹𝗯𝗮𝗿𝗸𝗮 𝗻𝗮 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 𝗺𝗮𝘁𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝗯𝗮𝗯𝗯𝗮𝗻 𝘀𝘂𝗻𝗮 𝗡𝗔𝗡𝗔 𝗠𝗔𝗥𝗬𝗔𝗠𝗔
𝗛𝗔𝗕𝗜𝗕𝗧𝗬𝗡 𝗛𝗔𝗬𝗥𝗔𝗧𝗢𝗨 𝗮𝗸𝗼 𝗶𝗻𝗮 𝗶𝗻 𝗻𝗮 𝗮𝗺𝗯𝗮𝗰𝗶 𝘄𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝘀𝘂𝗻𝗮 𝘁𝗼 𝘁𝗮𝗯𝗯𝗮𝘀 𝗸𝗲𝗰𝗲 𝗱𝗮𝗹𝗶𝗹𝗶 𝗱𝗮𝗻 𝗵𝗮𝗸𝗮 𝗻𝗮 𝘀𝗮𝗱𝗮𝘂𝗸𝗮𝗿 𝗱𝗮 𝗹𝗮𝗯𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗻𝗮𝗻 𝗴𝗮𝗿𝗲 𝗸𝗶 𝗳𝗮𝘁𝗮𝗻 𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵 𝗯𝗮𝗿𝗺𝘂 𝘁𝗮𝗿𝗲 𝗵𝗮𝗿 𝗮𝗯𝗮𝗱𝗮 𝘆𝗮 𝗾𝗮𝗿𝗮 𝗺𝗮𝗻𝗮 𝗵𝗮𝗾𝘂𝗿𝗶𝗻 𝘇𝗮𝗺𝗮 𝗱𝗮 𝗷𝘂𝗻𝗮 𝗤𝗔𝗪𝗔𝗥 𝗦𝗛𝗜𝗚𝗔 𝗔𝗟𝗝𝗔𝗡𝗡𝗔𝗛

Tukuici gare ka SIR ABUBAKAR SADEEQ CEO LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION da ɗaukacin membobin mu

Free book
Kyauta bada kudi ba duk wanda akasayarwa to ycn baruwana nide littafina na kyauta nayosa sabo da Allah da kuma masu suna Maryam

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍

 

 

𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚’𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 – 250 𝟏𝐆𝐁 – 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 500
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 750

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎……

 

💋💋 امى بتولة💋

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 7_8

 

Sai nan gaba za ka san gaskiya nake faɗa maka kuma ni mai sonka ce, in ka girma ka stofe ka rasa mai yarda ta aure ka, ka ci-gaba da biyewa Baffan ka wai baka girma ba gaka shagiri-girbau ko? To dan ma ka sani shi Baffan naka ma auren wuri yayi dan dai kawai Allah bai kawo haihuwan da wuri bane amma ai da yana da yaro kusan sa’an ka, yo ni Meramu Allah na tuba maka ba don kar na karta saɓo ba ai Magaji da cewa zanyi da ma bai haihun ba kaga fa tsakani da Allah yacce Allah ya dube su yai musu kyautan da bakowa ke samu ba, yarinya nustaststiya kuma kyakkyawa gata da sunan manya, nifa wannan ɗan banzan AL’ADAN ba dani ba in faɗa maka ji nake kaman in kama Indo in shaqeta kowa ya huta, dan cin fuska irin na baffanku ya ɗauki sunana ya sawa yarinya sannan anuna qiri-qiri anason kashe yarinya dan hassada da baqin ciki, shi kuma sha-sha-shan gashi solo-ɓiyo ya kasa tsawatar mata wai ita kunyan ƴar fari to Allah wadaran wannan kunya da jahilallen al’ada, kalla fa hankali irin na takwarata da tausayi da sanin ya kamata, tana tashuwa ita gata mai son uwarta yarinyar nan fa bata warke ba ta tashi ta tafi gidan can ina mata magana ko ta saurare ni kuma nasan aiki za taje tai ta yi kaman jaka dan abinda suka ɗauke ta kenan ita ma ƴar buhun uba, amma Allah wadaran naka ya lalace wannan rashin zuciya na Innai na sani jin watarana kaman na zaune ta gata ba auki ba sai kuma naji tausayinta ƴar qaniya kawai”.

goro ta gustura kamun ta ci-gaba da surutun ta “kaga fa Magaji wallahi ina jiyewa mutanen nan hisabin Ubangiji, sunan ta Maryam fa suke mata wannan ɗanyen jaraba su basu san lukutin al’haqi suke ɗauka wa kansu ba Kuma kwaran-kwatsa duk in suka yarda suka yi sanadin mutuwan takwara ta sai nayi shari’a da su har shi uban nata isa sai hukuma sun shiga tsakanina da su, dukan su jarababbu tambaɗaɗɗu ƴan buhun uba”.

Dariya yaso kwace wa Magaji ganin yacce take yi kaman suna gabanta, danne dariyan yayi yace “yanzu dai stohuwa naji magananki amma dan Allah kar kice mun in kayi wa mai suna Maryam abu zunubin ka dabanne kuma lukuti ne?”😂

gyara zama Baabaa Mero tayi, dan kuwa abun nema ya samu an sosawa Baabaa Meramu inda yake mata qaiqayi, tace “Yauwa Magaji kaga kuwa gwanda da kayi tambayar nan dan nasan duk karatun muhammadiyan ka da bokoko awuta baka sani ba dan ba mai sani wannan sai wanda Allah ya nufa da arziqin rahaman sani, NANA MARYAMA, Maryama daban ce a cikin mata ka duba fa irin girma da darajan Qur’ani amma ba wata mace da Allah ya ambaci sunanta kai staye a ciki sai Nana Maryam Uwar isah”.
Murmushi stohuwa tayi dan in tana wannan labari daɗi take ji “ita Maryama komai nata daban ne
Hankali gareta
Ga haquri
Ga nustuwa
Ga iya zama da mutane
Ga addini
Ga kyau
Ga ilimi
Ga tarbiyya
Ga tausayi
Ga iya soyayya
Uwa uba baiwa gare ta wanda ba kowa ke sani ba sai wanda Allah ya nufa da ikon sani barinma dai wanda ya auri mai wannan suna
Allah dai yayiwa duk wata mai suna Maryam albarka a duk inda take” ( nace ba baabaa Mero mu kuma da ba maryam sunan mu ba sai ki stine mana nace a stine mana😬).

Magaji sauraran Baabaa mero kawai yake yi yana cewa a ransa “kaga aku gidan surutu daman ke kullum a yabon sunanki kike” amma a zahiri sai yace “aikuwa Maryam ta wuce haka ma baabaa”.

Washe haqora tayi tace “kaga ɗan albarka shiyasa nake sonka nake faɗa maka gaskiya kayi aure, ai ni duk wanda zai yaba mun takwara tom banda kamarsa sonsa nake da qaunarsa, Allah dai ya muku albarka ya nuna mun auranku da yaranku” Murmushi Magaji yayi bai ce komai ba.
“Kunga ja’irin yaro ba zaka amsa da Ameen ba wato ance maka bansan murmushin na son aure bane kayi” cewar baabaa Mero tana washe baki.

Magaji yace “haba ni me zanyi da wata bayan ina da ke yar tsohuwata ta, kinsan fa da stohon zuma ake magani”.

Hararansa tayi tace “kaga ɗan ƙwal uba da yaudara, zai cuceni tom ni bana sonka kaje ka kawoman kishiya kawai shi nake so, in kayi sa’a ka samo Maryama dan ina faɗa maka Magaji samun Maryama sai me rabo da sa’a irin rantsanstar rabon nan dan ko kana sallan dare da bada sadaka kai har ma da raba zakka kuma qarshenta ko makka kake zuwa duk juma’a sai da rabon ka samun mesuna Maryam ko da kuwa da kuɗin ka”.

<nace ba baba mero ma tsohuwa ta yaba Maryam bare mu tom muma dai ba mu gwada
Waqan umar m shariff maryama🎶

Nayi soyayya kala-kala amma banga ya naki ba
Naga yammata iri-iri a kyawu ba zasu kai ki ba
Kalamun so kashi-kashi banji salo irin naki ba
Kyawun halinki ba’a faɗa na baki hanya wuce gaba
Gatanan tafe masoyoyiyata gatanan tafe tana zuwa
Maryama zooo maryama zooo maryama zooo masoyiya…..
Amincin Allah ya tabbata a gareku masu suna Maryam>

Zan juya kenan na fice kamun Magaji ya ganni ba sai aka yi sa’a muka haɗa ido da Baabaa mero ba ni ko na qara tamke al’qalami na, baabaa Mero cewa tayi “Allah dai ya miki albarka Hariratu ourmmarhn batooler Allah kawo batoolerh lafiya mu kwaso shoki mu zuba qara’i, tattaro kayanki a inda kika sauqa a qauyen nan daga yau kin dawo gidan nan da zama tunda kika waqe Maryama, inga uban da zai takura miki ko ya koraki” ta faɗa tana hararan Magaji
Godiya nake baabaa mero🙌
Fan’s ɗin baabaa Mero azo atayani Godiya jama’a dan kuwa labari yanzu aka fara, Baabaa Mero har da ɗaki ta bani muje zuwa ✍️.

Hiransu suka ci-gaba dayi da Magaji anan yake ce mata zai nemowa Innai makaranta a cikin Ashaka kuma suna son na taje ta dawo.
“Na shiga arba’in da uku ni Meramu yanzu sabi da Allah wannan jarabar bokon har da takwara ta, Magaji yanzu ina laifin kace zaku mata aure amma wai boko, wanne kalan boko ne haka nikam gaskiya bason bokon nan naku nake ba dan so nake takwarata tayi aure ta haihu tunda raina naga yaranta inyaso kai ka stofe ma a gida bai dame ni ba”.

Taɓe baki Magaji yayi yace “ke kika jiyo ni dai makaranta zan turata”.

Cikin masifa Baabaa Mero tace “tunda duk kunnenku a hure yake baku ɗauke ni a bakin komai ba kun cike carɓin mun fistara tsaff to shikkenan ba komai, sai abinda kuke so za kuyi ko? to billahillzi bari shi uban nata Isa yazo ya same ni kowa ya shaida kuma ya ji in dai takwara ta taje makaranta ta dawo ta rasa mijin aure ko zaka mutu kai zaka aure ta”.

Haɗe fuska yayi ya miqe yana cewa “kamun a jimu bana yi tafiya ta”.

Taɓe baki tayi tace “kaima kai ka jiyo tambaɗaɗɗen yaro kawai ko itama bata sonka takwarar tawa sai me sallan dare kai ko farillahn ma nasan da qyar kake miqawa balle nafila”

Dariya ta basa yace “nidai ƴar stohuwa byee”

Cikin masifa tace “na bayoo maka qafan ubanka Musa ɗan buhun uba ni zaka wa wannan banzan yaren da kuke zagi dashi yaren ƴan wuta yaren jarababbu tambaɗaɗɗu, to to ni Meramu me ya haɗani da wuta ina masoyiyar Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam, Allah mana tsari da wuta ban da nima da shirme na Magaji ina da suna Maryam kam ai ma mune farkon shiga aljnna”.

Murmusawa yayi yace “ai kuwa dai gaki sunanki Maryam ga ɗanki Isah Annabi guda ai kece ma a gaba”.

Washe haqora tayi tace “Allah dai ya maka albarka Allah qara mana son Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam”.

Murmushi yayi dan ko ba komai yawan ambatan Annabi da take yi yana sanya sa jin dama-daman surutun ta “ƴar stohuwata Malama Maryama mai kama da hurul-eyn na tafi” ya faɗa yana ficewa a gidan, Allah tsare ta yi masa.

Ganin ana neman qarfe sha-ɗaya 11 tashuwa Baabaa mero tayi dan tayi sallan walha.
SALLAHN WALHA

من فضلة الصلاة الضحى

عن ابي هريرة رضي الله عنه قال ، قال رسول الله صلى الله عليه والسلام ” إن فى جنة بابا يقال له (( الضحى )) فإذا كان يوم القيامة نادى مناد: أين الذين كانوا يداومون على الصلاة الضحى؟ هذا بابكم فادخلوه برحمة الله ” رواه الطبراني

و في قول ابي هريرة ايضا أوصاني خليلي بثلاث :
” صيام ثلاثة أيام من كل شهر، ركعتي الضحى ، أن أوتر قلبل ان انام”

Daga falalar sallar walha

FASSARA :

An karɓo daga Abi huraira Allah ya ƙara mishi yarda yace, Annabin rahama sallallahu Alaihi was- sallam yace ” a cikin Aljanna akwai wata kofa ana ce mata (( DUHA )) idan Alƙiyama ta kasance mai shila zai yi ƙira, ina waɗanda suka dauwama a sallar walha ? Wannnan kofar kuce ku shigeta da rahamar Ubangiji ”
Ɗabarani ne ya rawaito

2: A cikin faɗin Abi huraira kuma,
Masoyina ya min wasiyya da Abubuwa guda uku:
Azumin kwana uku a kowani wata, yin sallar walha, da na ringa yin sallar wuturi kafin nayi Bacci
WALLAHU A’ALAM.

Inna bayan sun gama kukansu da Hassu har bacci ya ɗauke su, farkawa tayi tana mai karanto addu’an tashuwa a bacci, ganin 11 har yayi da sauri ta tashi ta fita a ɗakin.
Da sallama abakinta ta shiga ɗakin Innan su, Amsa sallaman tayi.
Samunta tayi tana naɗin kaya sai ta stugunna tace “Inna kawo in tayaki” ba tace mata qala ba kuma ko kallonta ba tayi ba ta tashi ta zauna a bakin gado.
Kan Innai a qasa tana jin wani iri a haka har ta kammala mata naɗin kayan ta gyara ɗakin sannan ta koma gabanta ta stugunna kaman ɗazu tace “Inna me za’a ɗora na rana? Duk cikin harcen su na fillanci take maganan.

Kau da kai Inna tayi ba tace komai ba, ganin haka jiki a sanyaye ta tashi ta fita a ɗakin.

Ɗakinsu taje ta tashi Hassu tace “Hassu tashi kije ki tambayi Inna me za’a ɗora na rana sai na ɗaura”.

Kallon Addan nata tayi ta turo baki tace “Adda me yasa ke ba za ki tambaya da kanki ba? In kina qara nisanta kanki da ita ne fa bakwa shaquwa”.

Murmushi tayi ta zauna gefen gadon nasu na kara(ciyayi) tace “ke dai jeki tambayo kizo muyi tare ko kuwa kiyi wanka ki huta abinki”.

Tashuwa Hassu tayi ta fice, ɗakin Innan su ta shiga da sallama.
Amsa mata tayi, ta qarisa ta stugunna gabanta kaman yacce ɗazu Innai tayi
( tarbiya ne gare su duka mu kula da tarbiyan yaran mu ko da ba cikin gida ba, ko dan mutanen waje abun ba daɗi ya zama na ana cewa yaranka ba tarbiya dan Allah iyaye mu kula)
“Inna me za’a yi na rana?

Innan su tace “a dafa fara da yaji uwata”

“Uhmn!” Hassu tace kawai.

Inna kallonta tayi tace “ya akayi uwata?
“Inna kiyi haquri in wani laifi Adda ta maki ki yafe mata kinji” Hassu ta faɗa kaman za tayi kuka
Murmusawa Innan su tayi tace “Yaro Yaro ne! tashi kije kuyi aikin”.

Kasancewan basu kasance masu musu da iyayensu ba tashuwan tayi kaman yacce ta umurceta ta fita a ɗakin.
Aikin suka haɗu da Innai suke cikin qanqanin lokaci suka gama, wanka Hassu ta shiga ta fito itama Innai ta shiga tayi suka shirya.
Duk da tasan ba amsawa Inna za tayi ba amma ta mata sallama tace “Inna zamu tafi gidan baabaa”.

Ɗakin mama lami suka je dan suce mata sun shiga gidan baabaa kar ta neme su shiru amma suka tarar tana baccin asara (inji kakata baccin mutuwan rai).
Ɗaukan abincin baabaa Mero Hassu tayi suka kama hanyan gidan baabaa bayan sun gama komi a gidan nasu.
Tafiya suke suna hira inda Innai ke cewa “Hassu kar ki damu kinji, ki daina takura Inna kar kema tayi fushi da ke kaman ni da bansan me na mata ba, komai zai wuce zan cigaba da haquri”.

Da sallama suka shiga gidan Baabaa Mero, ta amsa musu tana faɗin “kunga ƴammatan Malam da Inna
Jikokin Meramu Allah muku albarka ƴammatan aljanna”
Murmushi suke dukansu Innai ce ta faɗa jikin Baabaa mero tana cewa “washhhh! baabaalle ta na gaji Allah”

Baabaa Mero kaman mai jiranta ta kalleta tace….

Wannan page sadaukarwa gareki habibtynah nana maryamatou nah💋 masoyiyar shiga aljannah nima tun da ina da masoyiya Maryama mune ƴan shigan farko😂
Masoyan Rasulullahi SAW♥️

Ina gaisuwa masu suna maryam

Muje zuwa fan’s ✍️

𝗜𝗬𝗔 𝗬𝗔𝗪𝗔𝗡 𝗦𝗛𝗔𝗥𝗛𝗜𝗡 𝗞𝗨 𝗜𝗬𝗔 𝗬𝗔𝗪𝗔𝗡 𝗣𝗔𝗚𝗘 🙃

ZANCI GABA DA POSTING NE KAWAI IN NAGA YAWAN COMMENTS NAKU

09161720046
Mrs big barbieyh ✍️

 

💋💋 امى بتولة💋

𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
09161720046
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
07015870735
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁

NOTED : karku nemeni a wannan layi 08146292652 𝗱𝗼𝗻 𝘆𝗮𝗻𝘇𝘂 𝗯𝗮𝘆𝗮 𝗮𝗶𝗸𝗶 𝗯𝗼𝘁𝗵 𝘄𝗵𝗮𝘁𝘀𝗮𝗽𝗽 𝗮𝗻𝗱 𝗰𝗮𝗹𝗹

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

By

Uwar batoorl 🕊️

INA MIQA SAKON GAISUWAN TA’AZIYA TA GARE KI pharteemah, Allah yawa baffa rahama Allah sa ya huta.

Masu exam’s Allah bada sa’a ya kuma taimaka ya albarkaci karatu da sakamako.

SADEE-BEB MARUBUCIYAR
Dr. SULTAN (sadiya ka’oje)
Ni Uwar batoorl da ɗauka cin fan’s na JAHILCI KO AL’ADAH?🥺 Muna matuqar Godiya Allah bar zumunci Allah saka da alheri.

MARASSA LAFIYANMU gida da asibiti Allah bamu lafiya mai amfanarwa🤲 masu ciki Allah raba lafiya yawa yara albarka.

FAN’S ina mai baku haquri na rashin ji daga gare ni kwana 2 sakamakon banji daɗi ba amma da sauqi yanzukam Alhamdulillahi.
JUMA’AT KAREEM FAN’S mutanen Uwar batoorl, ina fata da addu’an alkairin Allah ya kai gare ku a duk inda kuke Alfarman wannan rana da kuma Annabi SAW ♥️

INAYINKU
INA JI DA KU
INA SOYAYYAR KU
INA QAMNAR KU
INA MUKU FATAN ALKAIRI AKO INA KUKE A FAƊIN DUNIYA.

FREE BOOK
Kyauta bada kudi ba duk wanda akasayarwa to ycn baruwana nide littafina na kyauta nayosa sabo da Allah da kuma masu suna Maryam

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍

 

 

𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚’𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 – 250 𝟏𝐆𝐁 – 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 500
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 750

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎……

 

💋💋 امى بتولة💋

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 9_10

“Takwara keko kiji tsoron Allah da shegen son jikin dake damun ki ɗaga ni kar ki karya stohuwa”.
cunno baki Innai tayi tace “baabaata ba kiga fa aikin da nayi ba duk na gaji”.

Baabaa Mero tace “ni tashimun a jiki kamun ma taqaici yasa na surfa ki na kirɓa ki, shagiri-girbau kawai dama can uban wa ya sanya ki aikin da zaki faɗo man a ka kaman gini, mutum banda gulma da kini-bibi ba abinda ya iya wai baka gama samun sauqi ba sai shegen son aiki kaman ba jini ne ajikinki ba, to kyaji dashi stunstun da yaja ruwa shi ruwa ke duka dan haka ɗagani banson jaraban sakalci”.

Hassu tana dariya tace “Baabaa kuma fa tare muka yi aikin bama ita kaɗai tayi ba”.
Baabaa tace “Allah dai ya miki albarka Hansai dube ki da qwarinki kaman ba kiyi komai ba”.

Tura baki itama Hassu tayi tace “nifa Baabaa ki dena cemun Hansai ɗin nan, duk kun ɓatamun suna wai Hassu wai Hansai ni fa gwanda ku dinga cemun Hafsatu na yafi daɗi aradu”.

Danqwalo ta mata tace “nace dan matar ubanki Lami baza’a ce ba Hansai zance, wato kema kin renani kamar qannan mai zubin kajin mayun nan ko?”

Hira suke da raha abunsu kaka da jikokinta.
Tashuwa suka yi suka ce “Baabaa kici tuwo ba muje gidan baba mu dawo”.

“To ku dawo lafiya ku gaidamun su Shatu da halimatu” cewar Baabaa Mero tana jawo Radion ta.

“Zasu ji baabaarmu”.

sai tace “ƴan kwal uba iyayen kalen dangi tunda kashe taku uwar kuka yi zaku qwacewa ubanku nasa, ni baabaar iyayenku ce ba ku ba”.

Fita suka yi suna dariya sanin halin ta “Allah ja kwana ya bar mana baabaar iyayenmu” faɗin su.

Murmusawa tayi tace “Allah maku albarka kuma”.

Tafiya suke abinsu suna hira sai Hassu tace “Addah gaskiya yau nikam muje dandali in anjuma yayi”
Waro manyan idanunta tayi tace “Hassu ki rufa mana asiri mu mutu a gida maza su mana sutura, Hamma Magaji ya ganmu acan ko ya samu labarin munje kashinmu ya bushe dan haka ni ba ruwana kinsan gobe monday kuna da school ko?”
Hassu kaman za tayi kuka tace “Kai de Addah nikam muje dan Allah please”
“to ki dawo lafiyah ni dai Innai ba ruwana ba dani ba gaɗa a kotu, kuma in an ganni a lahira kaini aka yi” Innai ta faɗa suna qarisa shigewa gidan baban nasu.

“Assalamu’alaikummm⁴ Maamaaa³” suka haɗa baki suka yi sallama, mama da ke fitowa banɗaki tace “ai tun da naji anata kwala sallama da qiran nan nasan sai ke aikin ki ne Innai Allah shiryamana ke”.

Innai na dariya tace “Mamata nayi kewanki ne fa”.

“A’a kam ba wani kewa yanzuma nasan wajan su Shatu kukazo ba waje na ba” mama ta faɗa tana ajiye butan hannun ta.
Dariya Hassu tayi tace “laa Mama kaman kinsani nice kawai nazo gaishe ki”.

Mama tace “au wai ke ɗin Hassu ai gwanda Innai ma akan ki, dukan ku dai kunsan wajan su wa kuka zo”.

Suna dariya suka durqusa suka gaishe da mama ta amsa ta tambayesu ya su Innansu da lami? Duk suna lafiya suna gaidaki har da Baabaa ma.

Mama tace “ashe kuce mun daga gidan Baabaa kuke, to fatan tana lafiya?” suka bata amsa da “tana lafiya lau”.

“Masha Allah to gacan su Shatun suna sallah a ɗaki” mama ta faɗa.

Wucewa ɗakin su shatu suka yi, Innai tace “uwata sannu da ibada”.

Shatu na murmushi tace “sannu Adda Innai”.

Hassu tace “Shatu ba magana ne ina hali take?

“Ke dai Hassu aiki ya ganki sunan Inna gareni amma baki ko sakayawa sai dai kice Shatu gastau-bajau” yarinyan da ta kusa sa’an Innai ta faɗa.

Hararanta Hassu tayi tace “na sakaya akan me? Ai Inna daban ke daban ah to dan sunanku iri ɗaya ba wai kece Innan tawa ba ai”.

“Za kiji dashi dai” Shatu ta faɗa.

Alwala Hassu da Innai suka yi suma suka yi sallahn.
Abinci shatu ta ɗauko musu dukan su ukun suka zauna suka ci suka cika cikin su, bayan sun gama ci sai kuma hira har hali ta dawo aike ta jona su.
Har sai can bayan la’asar sannan Innai tace “Hassu kinga tashi mu tafi naje nai wa mama lami sanwan dare”.

“Kai Adda ke dai bakya gajiya Allah to ni ba inda zani yanzu ehe ai bamu gama hira ba ko Shatu? Hassu ta faɗa tana kallon Shatu.
Shatu tace “eh Addah Innai please ki tsaya sai anjuma kaɗan sai mu tafi duka ai dai mama lamin lafiyan ta lau zata iya yin aiki ta”.

Innai tace “Nikam ku rabani da jaraban surutun mama Lami dan sai ta kusa cinye ni ɗanya, kuma kunsan gobe dukan ku zaku school dan haka maza-maza tashi mu tafi Hassu”.
Hassu ba yanda ta iya haka ta tashi tana aikin turo baki, Sallama suka yi wa mama tana Allah musu albarka suka wuce gidan Baabaa mero.

Kwanuka suka ɗauka kawai suka nufi qofan dan komawa gida.
Baabaa Mero ke magana muryanta a ɗage “wato dai takwara ke de baki gaaji kirki ba ko kaɗan, Haka zaki barni nai ta zama ni ɗaya agida kaman mayya to ban yarda ba”.

Innai tana dariya ta juyo tace “Kai de baaballe ta kefa jaruma ce”.

Baabaa Mero tace “nabi jarumtan da gudu dan buhun ubanki Isa”.

Turo baki tayi tace “ni banson zagi baabaa”

Baabaa Mero tace “na zage ki zo ki ɗau mataki shi uban naki ba nice nan na tsugunna na haifesa ba har ya haife ki ƴar ƙwal uba”
Qara turo baki Innai tayi, sai baabaa tace “ki tura in kinga dama yakai gidanku”
Cikin lallashi Innai tace “tom baabaata kiyi haquri zan dawo nima fa kinsan bazan iya kwana ba’a kusa dake ba”
Washe baki baabaa tayi tace “shiyasa nake sonki takwara ta, tunda kin zama ƴar aiki aje ayi aiki lafiya Allah muku albarka Allah qara miki lafiya ko”
“Ameen baabaata” ta faɗa a taqaice suka juya suka fice a gidan.

Sun isa sun samu har mama lami ta ɗaura sanwan dare, tana hangan ta a madafi tace “naga ta kaina yau kuma da surutun mama lami, kinga Hassu je kiyi wanke-wanke da wuri ki gama ki kama shara ni kuma zan karɓi girkin”
Zuwa madafin tayi tace “sannu da aiki mama lami”.

Harara ta mata tace “wato dai ɓaro-ɓaro a gidan nan kike nunamun ba nice uwarki ba Innai, kinsan ba uwarki ce da aiki ba kika kama figaggun qafanki kika tafi yawo to yana da kyau bari kiji ko uwarki bata miki riqon da na miki ba dan ni nan da kika rena ɗin to nono ne kawai ban baki ba da kuma haifan ki amma duk wahalanki nice nan na shanye su tass nice komi naki, ko mutuwa za kiyi kuka ko kallo baki isa uwarki ba bare har ta baki nono”.

Kanta aqasa tace “kiyi haquri mama” dan in da sabo ta saba duk randa ta mata laifi wannan gorin kam sai tasha shi har da wanda yafi wannan.
Tsaki mama Lami taja ta wuce a wajan, duk abun nan da suke yi har da maganganun mama Lami Inna dake waje kusa da madafin tana gyaran ɗan akurkin dabbobi tana jinsu amma ko juyowa ta takallesu ba tayi ba kuma ko a fuska baa alaman maganganun da akayi ya dame ta.

Hassu ke qunquni tana wanke-wanken tana cewa “ai de wallahi Inna kece kika jawa Adda” a haka Hassu ta gama wanke-wanken ta kama sharan gidan.
Innai ta qarisa girkin ta raba ta sawa kowa nasa, ta kai na Baffai ɗakin mama lami sannan ta kai na Hamman su ɗakinsa.
Hassu ta ɗau nasu ta kai musu ɗakin nasu, Innai ta kaiwa su Inna nasu qofan ɗakin mama lami.

Bayan sun kammala komi Magrib yayi dukansu alwala suka yi kowa ya shige ɗaki dan yin sallah. Bayan sun idar ita da Hassu duka suka ɗauki Qur’ani suna karatu kamun a qira isha’i.
Masha Allah! shine kawai abun furtawa saboda daɗin muryansu sannan karatun na fita zar-zar, a haka har aka qira isha’i sannan suka rufe Qur’anin suka tashi suka gabatar da sallahn.
Tuwonsu suka ja suna ci suna fira, can suka jiyo muryan baffansu alaman ya dawo kenan.

Bayahn sun gama cin tuwon kowa ya wanke hannunsa, sun tabbatar Baffai ya gama cin nasa tuwon yana zaune a taburman saqa a tsakar gidan.
Zuwa wajansa suka yi suka stugunna gefensa, kallon su Baffai yayi yace “Mamana ku zauna ko”

Zama suka yi a tabarman baffan nasu.
Gaishe sa suka yi ya amsa yana sa masu albarka.
Kallonsu yayi yace “yaran Baffai ko akwai wani abun ne?
Kan Innai a qasa ta girgiza kai, Hassu kuma tace “bakomi baffanmu”
Baffai yace “To Allah muku albarka, yauwa mamana munyi magana da yayanki za’a kaiki makaranta gobe in Allah ya kaimu tunda naga kinji sauqi sosai”
Kanta a qasa tace “Allah kaimu Baffai”
Sai Yace “Ameeñ ƴar Baffai, sannan na kwana kike so ko na aje a dawo?”
Haryanzu kanta a qasan tace cikin nistuwa “ko wanne Baffai zaɓinku shine nawa”.

Murmusawa yayi aransa yace “dattakuwa yarinya mai halin manya Allah rayamun ke yai maki albarka Maryam uwata” a fili kuwa yace “to shikkenan dama dan naji ta bakinki ne amma tuni Hamman ku yace za kike zuwa ki dawo”.

Hassu tace “ai yafi Baffai dan nikam bazan iya kwana ni kaɗai ba”
Murmushi yayi yace “Allah muku albarka”
Suka amsa “Ameen₦”.

Yace “Tom kowacce taje ta kawo Qur’anin ta naji haddanta kamun Hamman ku ya dawo”.
Hassu ta tashi taje ta ɗauko musu.
Karatun suka yi, ya qara musu yace “a dage yaran Baffai Allah maku albarka Allah taimaka ko”
Suka amsa da “Ameen baffanmu”
Sallamansu yayi sannan suka tashi suka bar wajan.

Innai tace “nikam zan koma wajan baabaata”
Hassu tace “to Adda sai da safe”.

Innai sai da safe tawa su Baffai da su Inna, Hassu ta raka ta amma basu isa gidan ba ta dawo ita kuma ta qarisa.

Ɗakin Innar su Hassu ta shige ta ɗale gado, Kallonta kawai Inna tayi ta murmusa tace “Uwata tashi maza kije kiyi alwala kizo kiyi adduan bacci”.
“Tom innanmu” alwala taje tayo tazo tayi addu’a takwanta saboda gobe zuwa makaranta monday.

Da sallama ta shiga gidan ta samu Baabaa na zaune akan ƴar tabarmar ta da abun goron ta a gefen ta.
Amsa mata sallaman baabaa tayi tana washe baki tace “Sannu takwara ƴar albarka”.
“Sannu baabaalle ta” cewar Innai da ta kwanta ta ɗaura kanta a cinyar stohuwan.

“Yauwa baabaata in tambaye ki” cewar Innai.

Baabaa Mero tace “tambayeni ƴar nan ina jinki”

Baabaa ta nikam me yasa ba ki cika son a kawo miki tuwon dare bane?
Murmushi baabaa Mero tayi tace “yo ina za ki gane ke yarinyace takwara”.

Turo baki Innai tayi tana cewa “nidai faɗamun”.

Tom takwara tuwo da dare cinsa sosai ai bai kamata ba balle ga mu stofaffi, saboda ba’a son mutum na cin abu mai nauyi in zai kwanta sannan kuma gani tsohuwa kinga bakina sai da kayan maƙwalashe.
Dariya Innai tayi tace “ga gaskiyan nan ya fito baabaata kawai kice kwaɗayi gare ki”
Make mata baki baabaa tayi tana cewa “wato ma nice ke kwaɗayi, to ba dole nayi kwaɗayi ba na stufa shekaru nawa ni Meramu”.

“Uhmn” kawai Innai tace.
kallonta baabaa tayi tace “takwarata ya akayi?
Cunno baki tayi tace “ni fa Allah nagaji da karatun nan baabaa kice abarni nayi zama na haka”.
make mata baki Baabaa Mero ta kuma yi tace “dan ubanki Isa kin gaji da karatu dan gidan ku uban wa zai miki? Ki godewa Allah ma zaki dinga nesa da uwarki ko taqaicin ta zai ragu miki, ko so kike ki zauna ba ki zuwa makarantar baqin cikin halin Indon ya kashemun ke dan buhun ubanki, ai ko ni nan ba qaunar maganan bokon nan nake ba amma tunda wannan balagaggen mai jarabar taurin kan yace zaki to ko baki na zai kai cikin Gombe tsayi sai kinje gwanda na haqura na biki da addu’a dan zuwan naki yafimun, ke ba saurayi ba balle ayi maganan aure gwanda kawai kije ko hankalina ya kwanta, domin Indo na tabbatar gaba(haushi) take yi da ni da gan-gan take laɓewa dake, amma dai ni take nufi tunda ta ga ba sunan uwarta gare ki ba shiyasa take mun wannan cin fiskan, Allah de ya saka miki takwarata”.

Murmushi Innai tayi ba tare da tace komi ba domin ta saba da irin wannan magana, kuma yana qara mata zafin da take ji a zuciyan ta, duk da zuwa yanzu yaci ace ya zama soso da sabulun ta.
“Baabata kimun tastuniya mai daɗi har nayi bacci kinji” cewar Innai da idanuwan ta ke kan farin-wata tana murmushi.

Baabaa tace “dan gidanku tunda ni manguwanku ce(mai aiki) ubanki na biyana duk wata dole kice na miki tastuniya, tashi maza kiyo alwala muyi nafila mu samu mu kwanta ki huta gajiyan ayyukanki”.

Innai kaman za tayi kuka tace “ayya de baaballe ta ki bari sai anjuma ki tasheni muyi nafila” ta faɗa tana lumshe ido kaman mai jin bacci.

Washe gari Monday
Hassu ta shirya ta wuce makaranta da wuri dan suna daf da fara exam’s na fita a aji biyar 5.
Innai ce tayi aikin komi kaman kullum kama daga ɗumame shara wanke-wanke duk, sannan ta shirya ta yiwa Mama Lami da Innan su sallama ta wuce gidan baabaa Mero dan ta jira Hamma magaji acan
Bayan ya karya shima wanka yayi ya shirya dama already sunyi magana da Baffai tun da asuba.
Ɗakin Inna ya nufa “Assalamualaikum” ya furta ya tsaya neman izinin shiga ɗakin.

“Wa’alaikassalam Magaji burtu on”

Innan mu jamɓanduna.
Jam Magaji, noi fewel?
Alhamdulillahi Inna.
Noi shungullajo?
Alhamdulillahi Inna, noi kugal?
Kugal ɗon Magaji sai miyetti Allah….
Magaji yace “Inna ba muje cikin Ashaka sai mun dawo”.
“to a dawo lafiya Magaji am Allah ya tsare hanya Allah kaiku lafiya ku kula sosai ko” cewar Inna cikin kulawa.

Da “Ameen” ya amsa ya fice a ɗakin, ya wuce ɗakin mama lami ya gaishe ta ya fice yayo gidan Baabaa Mero.

Da sallama ya shiga gidan ya tarar da su a tsakar gida, gaisawa suka yi da Baabaa Mero sannan tace masa “to wallahi Magaji na baka amanan takwarata bana hana ku kaita makaranta inkun so har bangon duniya amma dai karka manta da maganata kaji da kyau, duk da ma dai tafi qarfin irinka”.

Haɗa fiska yayi yace “Ke fito mu tafi”.

Baabaa hararan sa tayi tace “kai Magaji zanci buhun ubanka banson jaraban tijara da subahin Ubangiji in ban da tambaɗewa da cin fuska duk kaima bansan yaushe ka koyo baqin hali ba aradu banson cin fuska dan kaji sunanta Meramu ba ke ba ka ji ni ai, fistara kawai sunan Uwar ubanka Musa sai kace ke”.
Ko kallon baabaa bai yi ba yace da Innai “ina jiranki a waje kika jima kuma ki tafi ke ɗaya” yana faɗan haka ya fice a gidan.

Baabaa Mero tace “takwara ki kula sosai ko Allah maki albarka ya tsare ku duka”.

Innai tace “Ameen baabaa ta byeee sai mun dawo”.

“Oh ni Mero kema yaren ƴan wutan kike son koya na shiga ɗaki na kasa fita to Allah ya staremu da wuta mukam ai masoyan Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam ne ba mu ba wuta da yardan Allah” cewar baabaa tana shigewa ɗakin ta.

Fita tayi ta samu Hamman su na jiranta, sai lokacin ta gaishe sa ya amsa yana faɗin “mu tafi ko”.

Sanye take da kayansu na fulani riga da zani fari tass ta sanya milk color hijab iya guiwanta Masha Allah tayi matuqar yin kyau.
Shi kuma Magaji sanye yake da jamfa milk color da hulansa, sun sha kyau ba kaɗan ba kaman ba ya da qanwa ba.
Mashin suka hau ko wanne da nasa ya kaisu bakin hanya dan samun motar da zai kai su cikin Ashaka.

Baffai ne zaune a fadan rugan da yaje shi da Arɗon wannan rugan suna magana.
Kaman an jefo mutum daga sama haka wani ɗan matashin yaro ya shigo fadan a guje ya zube gaban Arɗo kaman zai faɗi yana haqi yace “Arɗo! Arɗo! Arɗo! aradun Allah mutumin shan ya falka”.

A tare Baffai da Arɗon suka miqe da sauran jama’an dake fadan.
Arɗo yace “ke belloji mene kike shewa haka?”
Yaron yace “Arɗo aradun Allah kuwa wanshan mutumin ta falka”.

Da Arɗon da Baffai hanyan da wannan matashin ya fito suka bi da ɗan sauri-sauri, Da sallama suka shiga ɗan madedecin gidan Wanda yake mamallakin Arɗon.
Wani ɗan bukka suka shiga suka tarar da wata dattijuwan mata ana rirriqe ta tana fisgewa.

Ganin haka sai Baffai yace “su sake ta”
Addu’a yake karantawa yana tofa mata can sai ta daina fisge-fisgen ta yi baya luuuu zata faɗi aka rirriqe ta aka kwantar da ita.
Arɗo dake gefe sai hamdala yake yana cewa “Aradu Malam mun gode maki yau kwana 3 gaci wannan mutumi ta falka mu mun ɗauka ma ya mutu ashe kaɗo kam da ran shi”.
Murmusawa Baffai yayi yace “Arɗo mu dai godewa Allah, Allah kuma ya qara mata lafiya, Allah yasa in ta farka yanzu ta faɗama na daga inda take” da Ameen aka amsa duka mutanen dake cikin bukkan.
Ruwan rubutu Baffai ya bawa matan Arɗo akan a qara shafa mata sannan a bata tasha.
A wannan ruga Baffai suka wuni jikin matan Alhmdlh.

Sunje Ashaka sunyi komi sun gama zata fara zuwa school Monday mai zuwa,
Suka kamo hanyan komawa gida.
Mota ya kawo su har inda suke sauqa sannan su samu mashine su hau su qarisa gida.
Direct gidan baabaa Mero tace a ajiyeta, haka kuwa aka yi.
Da sallama ta shiga gidan tana kwalawa baabaa Mero qira.
“Baabaata maganin kukana ina kike na dawo”.
Baabaa Mero dake kwance a gadonta na qarfe ta ɗaga kai ta kalleta tace “ke dai Allah shirya ki, mutum sai qira kaman makahon da bashi da sanda Allah ya taro mun ke takwara”.
Zaunawa tayi a kan gadon ta na ɗakin baabaa Mero tana faɗin “washh baabaata na gaji wallahi kaman anmun duka, nifa gaskiya zan fasa karatun nan”.
Baabaa Mero ko kula ta taqi yi sai cewa tayi “sannunku da dawowa ƴan bokoko a wuta”.
Madara me ɗumi baabaa Mero ta bata, ta amsa ta sha ta ɗauro alwala tayi sallah sannan taje ta watsa ruwa ta kwanta sai bacci.

Hassu sun dawo makaranta da yamma, ganin Addan ta bata nan sai ta kama ayyukan gidan duka cikin qanqanin lokaci ta kammala.

Bayan kwana uku baiwar Allahn nan da Baffai ke wa magani taji sauqi ta warware sosai dan ta iya tuno sunanta da kuma tana da aure sannan tana da yara amma kuma ta kasa tuna garin da take. Ganin ta tuno waɗan nan abubuwa sai su Baffai suka yi hamdala, ya kuma bayar da wasu maganin da ruwan rubutu a ci-gaba da mata aiki dasu Insha Allahu nan da ƴan kwanki komai zai koma dede.
A kwana a tashi ba wuya a wajan Allah, yau take monday ranar da Innai zata fara zuwa School a cikin Ashaka.

FAN’S YA BANA JIN TA BAKINKU? KO LABARIN BAI YI BANE A AJE SA, IN LABARI YA MUKU DA GASKE INGA RUWAN COMMENTS KAMUN NA CI-GABA.
WANNAN LABARI KYAUTA NE DAN KU MASOYA AL’QALAMIN UWAR BATOORL KU KARANTA KU NISHAƊANTU KU FAƊAKANTU SANNAN KU QARU DA YARDAN ALLAH, NAYO SA KYAUTA NE DAN SOYAYYAN DA KUKA NUNA MUN A LITTAFIN 𝗬𝗔𝗥 𝗦𝗔𝗥𝗞𝗜 𝗖𝗘𝗘 AMMA KUMA RASHIN COMMENTS NAKU KAN IYA MAYAR DA WANNAN LABARIN ZUWA NA KUƊI.

MUJE ZUWA ✍️ SAI NAJI TA BAKINKU KAN NA CI-GABA

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
CALL
TELEGRAM

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

Ayi enjoying weekend lafiya sai kuma Monday.

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

By

HARIRA SALIHU ISAH

(Uwar batoorl) 🕊️

UWAR BATOORL FA BA LAFIYA🥺ina fatan samun addu’oee daga bakunan ku masu albarka fan’s, duk marassa lafiya gida da asibiti Allah azurtamu da wadatacce amfanennen lafiya 🤲
Masu bina private da masu gaisheni a cikin groups har ma da masu qira na, tabbas ina matuqar Godiya da addu’oenku da kulawanku gareni, na yarda da soyayyan ku ga wannan labari Insha Allahu iya iyawata da yardan Allah littafin JAHILCI KO AL’ADAH? Zai ci gaba da zuwan muku ako da yaushe banda weekend kaman yanda muka yi da ku, in kuma rai yayi halinsa to ina fatan samun addu’oen Rahamar Ubangiji daga gare ku 🥰

Uwar batoorl
Tana yinku
Tana ji da ku
Tana soyayyar ku
Tana qamnarku
Sannan tana muku fatan alkairi a duk inda kuke a faɗin duniyar nan

Dan Allah a kula da HAQQOQIN jama’a dake kawunanmu kar karanta littafi ya ɗibemu yasa muyi aikin dana sani a gaban mahaliccin mu, mu kula mutanena na AMANA 👍 SAI DA KU

 

𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚’𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 – 250 𝟏𝐆𝐁 – 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 500
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 750

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎……

 

💋💋 امى بتولة💋

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 11_12

 

Da asussuba Baabaa Mero ta tashi Innai tana mita “Ke takwara tashi ki shirya da wuri kamun Magaji yace nice ban tashe ki ba kin sansa da fiska kaman na uwarsa Habiba, Ni Mero wannan jarabar karatun yaren ƴan wutan da kuka ɗaurawa kanku kam ai kunga ta kanku da tambaɗar stiya babu ku babu hutu ba qanin ubanku da yaja muku da kuɗin ku kuka nemawa kanku tangaɗi a hanya” Baabaa Mero ta faɗa tana shumfiɗa darduman ta.

Tashuwa Innai tayi da salati ɗauke a bakinta da kuma addu’an tashuwa bacci, fita tayi a ɗakin ta samu buta cike da ruwa Baabaa Mero ta aje mata.
Ɗauka tayi ta zaga bayi ta fito tai alwala ta koma cikin ɗakin nanma ta samu darduma a shumfiɗe sai ta tada sallah ta idar ta ɗau carɓi tayi lazumin ta da azkar nata sannan ta miqe ta gyara ɗakin.

Ta fita ta share tsakar gidan tana qoqarin haɗa kwanukan da suka ci abinci jiya ta wanke sai Baabaa Mero ta fito ɗaki tana cewa “ke takwara wai me kike shukawa ne tun……..”
Maganan bakin Baabaa Mero ne ya maqale ganin abinda Innai ke yi sai ta zuba salati ta ɗaura hannu a kai tace “Aradun Allah takwara in baki tashi ba zan zaune ki kinji na ranste har Aradu, yanzu dan tsabar neman fitina da bala’i ana zaune lafiya zaki nema min jarabar tamɓadan Magaji ni Mero na shiga ɗaka na kasa fitowa”.
miqewa Innai tayi tana tura baki ta ɗau bokati tana ɗiban ruwan wanka, Baabaa Mero kaman zata kifu a qasa haka ta nufo ta tana cewa “dan ubanki Isa ina magana kina abu kaman wata hawainiya ko wacce ƙwai ya fashewa a cikin hanjayenta ko, to zaki zaunu kuwa”.
Innai ganin da gaske Baabaa Mero ta tunkaro ta da gudu ta ɗau bokatin tayi banɗaki, Baabaa Mero ta tsaya tana qwafa “Hmmn! Da kin tsaya na nuna miki iya qarfi na ai ja’irar yarinyar mai nemawa mutane jaraba kuma saura karki fito a bayin nan da wuri ki zauna kaman wacce aka aiki bawa garinsu ko aka bawa mace filo da tabarma tana naquda”.

Baabaa ta lelashe kwanuka ta ɗuma mata madara, cikin mintuna kaɗan ta gama wankan ta fito sumui-sumui ta wuce ɗakin ganin hararan da Baabaa Mero ke binta da shi don tasan halin stohuwar yanzu sai ta zaune ta ba ruwanta da maganan jika ko kaka.

Ko minti biyar bata yi ba ta shirya staff cikin uniform nata da yayi matuqar amsan ta kai kace dan ita aka fitar da colorn uniform ɗin, fitowa tayi stakar gidan Baabaa Mero ta ɗago kai ta kalle ta sai lokacin ta sake fuska tayi murmushi tace “takawarar arziqi kar kice zaki tafi ba ki karya ba, dan haka tsaya kisha madaran da na ɗuma miki ga wannan naira ɗari ne ki sayi abu a makaranta ko”.
miqa hannu Innai tayi ta karɓa ta sanya a aljihun ta kamun tace “baabaata zan sha amma ba naje na gaishe da su Baffai kamun sai nazo na karya na tafi kar na ɓata lokaci na haɗu da Hamma ya buge ni”.

Baabaa Mero tace “shikkenan ki dawo lafiya kuma kiyi sauri tunda dai kuma kinsan baqin halin jarababben Hamman naku, saura kuma ki tsaya ɓata lokaci dan ita uwar taki ba ta amsa gaisuwanki ba kinji ai”.
Innai na murmushin tace “Baabaa ta yanzun nan zan dawo” ta faɗa tana fita a gidan baabaa Mero ta nufi gidansu.

Da sallama ta shiga gidan, Hassu ta samu a madafin nasu sai tace mata “sannu da aiki surbajo am kiyi haquri na barki da aiki” tana gama magana ta wuce ɗakin Innar su sallama tayi, Baffai ya amsa mata yace “shigo uwata”.

Shiga ɗakin tayi kanta a qasa tana murmushi ta stugunna tace “Baffai jam ɓandu na”
“jam dada Baffai mako noi sare? noi baabaa am?
“jam Baffai am noi shungullajo noi fewel?
“Fewal alhamdulillahi shungullajo ɗon miyetti Allah daadaa Baffai mako” murmushi ta yiwa Baffai bayan sun gama gaisawa cikin fillanci yana ce mata har an shirya kenan.
Ta juya wajan Innar su dake gyaran gado tace “jam ɓandu na Inna”.
“jam” a taqaice Inna tace haka bata kuma cewa komai ba kuma bata ko kalli inda Innai take ba taci gaba da aikinta.

baffai ya kalle ta ya girgiza kai dan baima san menene zaice ba tunda dai ko kunyar idon sa bata ji.
Innai tace “Baffai yau ne dama zan fara zuwa makaranta”
Baffai da murmushi yace “to-to yaune shiyasa naga uwata ta shirya tayi kyau sosai to ki maida hankali sosai kinji, a dage sosai Allah miki albarka ya albarkaci karatun ku yasa al’umman Annabi SAW mu amfana da shi”.
“Ameen Baffai na” ta faɗa tana murmushi.
“Inna na tafi sai na dawo” ko juyowa Innar tasu ba tayi ba balle ta mata wata addu’ar.
Haka ta tashi ta fice, bayan Baffai yace taje wajan Hammansu kamun ta tafi.

Tana fita a ɗakin ta shiga ɗakin mama lami da sallama, amsawa mama lami tayi fuskanta a sake tace “ƴar ɗaki na sai yanzu aka shigo?
Gaishe da ita tayi tana murmushi haka itama ta amsa, sannan tace “Mama lami na yau zan fara zuwa makarantan da aka nema mun a Ashaka”.

“To yau ne dama, amma dai za kike dawo wa ko? mama Lami ta tambaye ta sai tace mata “eh mama lami zan ke dawowa Insha Allah amun addu’a”.

“To Allah bada sa’a ya albarkaci karatu tashi kije kar kiyi latti ko, ta ɗau murtala ta miqa mata gashi ki sayi abu”.

Murmushi tayi ta amsa tace “Nagode Mama Lami sai na dawo”.
fita tayi a ɗakin ta wuce ɗakin Hamma Magaji.

Tsayawa tayi a bakin qofan tayi sallama, amsawa yayi yace “wacece?” sai tace “nice Hamma”.
ya qara cewa “ke wa?
turo baki tayi kaman yana ganinta tace “Innai ce fa Hamma”.
yana daga ciki ya murmusa yace “ok come in”.
Shiga tayi ɗakin ta same shi daga shi sai vest da threequater, ganin sa haka sai ta sunkuyar da kanta qasa ta gaishe sa ya amsa yana cewa “sai yanzu kika shirya kenan kin tsaya biyewa stohuwar nan ko, to gwanda ita taci zamanin ta karki dage kanki za kiwa ita ba ruwanta, yanzu ba’a auran matan da basu yi karatu ba ko basu waye ba gwanda ki dage in kinason samun miji kaman yacce kullum take faɗa”.
kanta a qasa, ba tace komi ba sai wasa take da bakin hijab nata dan maganan sa ya bata kunya ita ina ma take ta aure.

Miqewa yayi yace “kin sani a gaba ba zaki fita na sa kaya ba ko so kike ki kalli jikina ne kam? Maza Je waje ki jirani gani nan zuwa muje ki hau abin hawa ya kaiki na riga nawa Rabe (rabiu) magana zai ke kaiki yake dawo dake har makarantan”.
Tana tura baki ta rufe fuska tace “to Hamma Nagode Allah saka” bai qara cewa komi ba ta tashi ta tafita.

Hassu ta samu ta fito wanka itama ta shirya zuwa makaranta, ganin Addan nata sai tace “Adda a dawo lafiya Allah bada sa’a ko, muma muna zuwa soon” murmushi Innai tayi tace “to Ameen ya Allah kuma Allah taimaka hassu a dage ayi karatu ayi exams lafiya”.

“Ameen Adda”.

Wucewa waje tayi tana fita sai ga Magaji tace “Hamma zamu bi gidan Baabaa ko?
Wani kallon da ya mata shi ya sanya ta zuge bakinta bata qara cewa komi ba, Allah yaso already kominta na tare da ita madaran ne kawai kuma tasan akwai buga match da Baabaa Mero in ta dawo.

Sunje sun sami Rabe dama yana niyan zuwa ɗaukanta har gida ganin shiru bata zo ba har lokacin sai kuma gata, gaisawa ya yi da Magaji yana cewa “Magaji dama yanzu nake niyan zuwa na jiku shiru”, “Ba komi kai kam inba matsala in shida da rabi tayi 6:30 ka dinga zuwa har gida” faɗin Magaji fiska a sake, sai Rabe yace “to Magaji”.

“Innai hau mu tafi” cewan Rabe yana qoqarin ta da mashine, hawa tayi kanta a qasa.
Kallon ta yayi yace “ke kuma ki kula sosai kar naji kar na gani in ba haka ba kinsan sauran, sannan ya ciro kuɗi ɗari biyu ya miqa mata yace a dawo lafiya” Rabe yaja mashine suka kama hanyan Ashaka, Feeeeee haka suke tafiya gudu yake sosai ganin lokaci yaja gudun kar tayi latti farkon zuwanta.

Magaji ganin sun ɓace wa ganinsa juyawa yayi ya koma, gidan babansa ya wuce.
Da sallama ya shiga gidan dede baban nasa ya fito zai fice dan tafiya kasuwa, ganin Magajin sai yace “A’a yaron Baffan sa ne a gidan mu da sassafen nan?”
Murmushi yayi ya tsugunna har qasa yace “baba antashi lafiya? Gaisawa suka yi sai ga Mama ta fito suka gaisa itama.
Baba yace “Magaji kai de kam ina ga yanzu ma wataqila baka jin yaren ka daga hausa sai yaren yahudawan nan to Allah shiryaku ya maku albarka kawai”.

Shatu da hali suka fito a ɗaki da shirin makaran ta, ganin Hamman su duk sai suka stugunna har qasa suka gaishe sa, amma sai yayi fiska a haɗe yace “me kuke yi a gida har yanzu baku tafi makaran ta ba? Zan fa ɓalla ku akan maganan karatu” da sauri suka wa Mama da baba sallama suka fice a gidan, suna fitowa suka haɗu da Hassu nan suka kama hanya sai makaranta.

Baba yayi murmushi yace “ai gwanda ka dinga tsawatar musu yaran nan ko kaɗan basa ji sai a hankali” sallama baba yawa mama suka fice tare da Magaji yana rakasa suna tattauna wa.
Baba yace “Magaji kai kuma ya ake ciki ne ka ji fa maganan Baabaa ko?
Sosa qeya yayi yace “baba a ɗaga mun qafa a ɗan qyale stohuwan nan tukun nikam ma na kusa komawa zamfara maganan karatun kuma in dai naje zan iya kai shekara huɗu 4, kaga in na dawo sai nayi auren”.
Murmushi baba yayi yace “Magaji shekara huɗu 4 akan shekarunka shekara 30 kenan fa, so kake ka stofe ka rasa matar aure ko ta maganan Baabaa?”
Magaji kansa a qasa yana murmushi yace “Baba a dai sa mana albarka Allah tabbatar ma na da alkhaeri nan da lokacin”, “To Ameen ya Rabbi Magaji” faɗin baba.
Raka baba yayi har wajan da motor ke ɗaukansu da dabbobinsu zuwa cin kasuwa sanda suka tafi ya juyo ya koma gida dan shiryawa shima yau yana son shiga cikin Gombe.

𝘽𝙀𝙎𝙏 𝙒𝘼𝙔 𝙄𝙉𝙏𝙀𝙍𝙉𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉𝘼𝙇 𝙎𝘾𝙃𝙊𝙊𝙇 𝘼𝙎𝙃𝘼𝙆𝘼

Rabe ya kawota sun iso lafiya ya ajiyeta ya juya akan sai yazo ɗaukan ta in an tashi.
“Bismillahirrah manirraheem
يا رب انى اسعلك كل ما خير فى هذل بلد و هذل مدرسة، و اعوذ بك من كل ما فيه شر،بجح رسو لله صلى الله عليه و سلم
يارب ارزقن بل علم نفع….”
Addu’oee tayi sosai kamun nan tayi stepping qafanta a cikin makarantar.
Makaranta ce babba sosai ɗalibai ne ko ta ina kowa ka gani sauri yake da alama assembly za’a fara.

💋💋 امى بتولة💋

𝙏𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃 𝙏𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃
𝙄𝙣𝙖 𝙪𝙬𝙖𝙮𝙚𝙣 𝙮𝙖𝙧𝙖, 𝙪𝙬𝙖𝙧 𝙜𝙞𝙙𝙖𝙮𝙚 𝙠𝙖𝙞 𝙝𝙖𝙧 𝙢𝙖 da 𝙖𝙢𝙖𝙧𝙚 𝙙𝙖 𝙮𝙖𝙢𝙢𝙖𝙩𝙖𝙮𝙚, 𝙟𝙖𝙠𝙖𝙣 𝙩𝙖𝙛𝙞𝙮𝙖, mai 𝙜𝙞𝙧𝙢𝙖, 𝙢𝙖𝙙𝙚𝙙𝙚𝙘𝙞 da qarami 𝙠𝙤 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙚 𝙨𝙞𝙯𝙚 𝙙ai-𝙙ai 𝙮𝙖𝙘𝙘𝙚 𝙠𝙖𝙠𝙚/kike 𝙨𝙤 𝙙𝙖𝙮𝙖 𝙣𝙚 𝙠𝙤 𝙨𝙖𝙧𝙞 𝙢𝙪𝙣𝙖 𝙢𝙖𝙧𝙖𝙗𝙖 𝙙𝙖 𝙠𝙪 𝙖𝙠𝙬𝙖𝙞 𝙦𝙖𝙣𝙖𝙣𝙖 𝙙𝙚𝙙𝙚 𝙣𝙖𝙮𝙞𝙣 𝙬𝙖𝙣𝙠𝙖 akwai wanda z𝙖 𝙠𝙞𝙮𝙞 𝙩𝙖𝙛𝙞𝙮𝙖𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙠𝙞 𝙨𝙖 𝙠𝙖𝙮𝙖𝙣 𝙠𝙬𝙖𝙡𝙡𝙞𝙮𝙖𝙣𝙚, 𝙯𝙖 𝙠𝙞 𝙨𝙖 𝙠𝙖𝙮𝙖𝙣 𝙮𝙖𝙧𝙖𝙣𝙚 duka akwai available at affordable price farashi mai rahusa ga sauqi ga inganci
𝙌𝙞𝙧a 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮𝙞
👇
08162862038
Domin qarin bayani da kuma sayan naka/naki, sannan ana delivery zuwa ki wanni gari kai karma qetaren qasa in an buqata
👜 MAMAM NANA BAG DEALER 👜

 

 

⭐⭐⭐
ba tare da ta ankara ba tayi karo da mutum, Littatafan dake hannun wannan yarinya suka zube.
Haquri ta shiga bata suka stugunna tare suna kwashewa, yarinya ce ƴar kimanin shekara sha uku 14 dan bata wuce sa’ar Innai ba.
Tattarewa suka yi tare yarinyar na murmushi tace “ba komi sister muje assembly ko, wani aji kike?
“SS 1” Innai ta faɗa tana gyara zaman jakan bayanta.
wannan yarinyan tace “Ok ajinmu ɗaya muje layi ko”.
Layin ƴan SS 1 suka je suka tsaya, aka yi conducting assembly for almost 30 minutes before aka sallami students kowa yayi aji.
Da yake yarinyar ɗazu na tsaye bayanta ce mata tayi “muje class our new commer” murmushi Innai tayi suka wuce aji.
Da Bismillah ta shiga, jan ta yarinyar tayi suka zauna a kujera na 3 a layin mata.
Kallonta tayi tace “ke new commer ce ko kaman yacce nace dan ban taɓa kallonki a ajinnan ba? Ta faɗa ta stigar tambaya.
Murmushi Innai ta kuma yi tace “eh yau na fara zuwa”.
yarinyar ta juya za tayi magana sai ga Malami ya shigo, tashi suka yi duka ajin “gud morning Uncle”.
suka haɗa baki wajen cewa.

“Morning”.
ya amsa musu a taqaice ya musu alama da su zauna.
Black board aka goge ya rubuta subject ɗin da ENGLISH LANGUAGE topic
PART OF SPEECH
juyowa yayi kamun yayi komi yace “class can someone help us tell what he knows about part of speech ,or can someone just explain?

Wani yaro ne ya ɗaga hanu
malamin yayi pointing nasa yana cewa “ehem am getting you”.

Naa naaa nounn is a name of things, objects or…. Tsayawa yayi ya gagara qarisawa yana in-ina, Malamin ya kalle sa yace “can you please sit down, any other person class?

Kowa yayi shiru ganin malamin na da zafi kar wani ya tashi yace ba haka ba.
Hankalinta gaba ɗaya na kan Black board kaman mai tunanin wani abu daban, yarinyar ɗazu ce ta taɓa ta tace “sister malamin nan fa na kallonki”
Sauqar da kan ta qasa tayi jikinta na rawa tace “Hande kam mi boni, nifa ina copyn rubutun da yayi ne”.

“Heeyyyy youu!!!” suka ji ya musu tsawa, a take jikinta ya fara rawa kaman wacce aka wa duka idonta ya tara hawaye.
Malamin yana nuni da su yace “am asking question and you guys are busy making noise right? Oya be on ur fit”.
Yarinyar ta tashi ta kama hannun Innai suka tsaya tare, malamin yace “you should tell class what u’re discussing about or else..”

Haquri yarinyar ta bada amma da qyar malamin yace “ok you get ur sit” yana nuni da yarinyar, sai ya juya kan Innai yace “so you can’t apologize right?

“Sir she’s a new commer” cewar yarinyar.

Tsawa ya daka mata “can you please shut up ur mouth my friend, am talking u’re talking idiot”.
Innai da kaɗan take jira ta fashe da kuka jikin ta har yanzu rawa yake kaman ace firit ta kwasa a guje haka take ji sai kulle idon ta kawai tayi, ƴan aji na kallonta saura na dariya qasa-qasa saura na jin tausayin ta.

Kallonta yayi yaja qaramin tsaki yace “have ur sit” da sauri yarinyar taja hanunta ta zaunar da ita tana hamdala, ita kuwa Innai tana zama sai hawaye da qyar ta seta kanta har ya kammala karantarwan sa ya fita bata gane komai ba. malamin Islamic ya shigo musu
Sosai take gane lectures en ,hankalinta duka na kan malamin har ya basu Home work
Akan su lissafo masa adadin annabawan da aka lissafa a Alqur’ani
Yana fita aka fice musu break.

Yarinyar ɗazu ne har yanzun suke tare, kallonta tayi tace “sister ba ki faɗamun sunanki ba”
Murmushi Innai tayi tace “sunana MARYAM ISAH MUHAMMAD”. Yarinyar tace “Wow! suna mai daɗi sosai nake son sunan Maryam dan sunan mommy na kenan” murmushi kawai Innai ta mata.

“Ni kuma sunana FATIMA NURA MUHAMMAD amma ana cemun AFRAH” murmushi Innai ta mata tace “kema sunanki me daɗi”.

Ni ƴar cikin garin Gombe ne iyayena ma na can kawai an baiwa kakata ni ce shiyasa muke zaune anan ni takwarar ta ce, Innai tace “la nima takwarar kaka ta ce ai kuma nima nafi zama a gidan kakata”.

Afra tace “ke me ake ce miki a gida?”

“Innai haka ake qira na” ta bata amsa tana murmushi.

“To nidai ba zance Innai ba zan dinga ce miki Habibty tunda sunan mommy gare ki” Murmushin Innai ta kuma yi kawai, sai Afrah tace “habibty ke kam ba dai murmushi ba kam ai sai ki qarar da murmushin naki ki rasa nawa angonmu”.

Dariya Innai tayi tace “Wow! So dama murmushi na qarewa bansani ba?”
Afrah tace “za kiji da shi ni dai yanzu kinga tashi muje wajan break mu sayi abu inason cin awara yau naqi karyawa, muyi sauri kuma an kusa komawa aji”
Murmushi kawai ta mata suka fice a ajin suka yi wajan break ɗin.

Bayan fitan Innai a ɗakin baffai ya dubi Inna yace “A’ishatu zo ki zauna”.
Inna zuwa tayi ta zauna gefen baffai tana murmushi tace Baffan Magaji ganinan”.
Kallon ta Baffai yayi yace inason zan miki magana a matsayina na mijinki kuma uban yaranki indai kin ɗauke ni da muhimmanci kinajin maganata kuma kina ganin mutunci na to inaso na sani”.

“Ina jinka malam” Inna ta faɗa.

“Aisha kinsan ma’anan haihuwa kuwa?
Kinsan bakin uwa kuwa akan ɗanta?
Ko dai wani abun da kike yi ta maganan Baabaa mero ne don na sawa Innai sunan ta shiyasa kike haka?
Ashe mahaifiyata ba mahaifiyar ki bace?
Ko ban sawa Hassu sunan Gwaggo ba? Ki dubi girman Allah kiwa kanki faɗa ko sau ɗaya ne dan ina guje miki aikin ɗan da na sani, makaranta fa yarinyar nan zata tafi amma bakisan tana buqatan addu’an ki da sa albarkanki ba?
wai duk me yasa kuma akan me kike hakan?
A’ishatu ina guje miki ranan da na sanin abubuwan da kike aikatawa wannan baiwar Allah ranar da wannan nadama bazai haifar miki ɗa mai ido ba, dan wannan ba AL’ADAH bane JAHILCI ne A’ishatu, al’adu da yawa a yanzun an daina su kaman su SHAƊI, AURE DA QANANUN SHEKARU, GUDUN KARATUN ZAMANI, RASHIN AUREN BARE IN BA YARENKA BA KUMA BA ƊAN UWANKA BA, DA KUMA TAKI AL’ADAN TA KUNYAR ƊAN FARI da dai sauran AL’ADUNMU da yawa amma ke me matsalanki A’ishatu?
Kanta a qasa tace “kayi haquri malam dan ko ɗaya ba haka nake nufi ba, Baabaa mero a wajena mahaifiyata ce ko da kuwa ba aure tsakanina da kai balle har da jikoki, kuma ai na mata addu’an Allah ya ba da sa’a”.

“Hmmn! yana da kyau, ni dai ina guje miki ranan nadaman da ba abunda zai haifar miki sai ɗa mara ido don in lokaci ya qure miki alhaqin abinda kikewa yarinyar nan kaɗai ya isheki ba sai da wani abun ba” cewar baffai yana ficewa a ɗakin dan baison qara sauraran ko me zata ce.
Inna bin bayan sa tayi da kallo sai tayi qasa da kanta dan gaba ɗaya ita ma abun na damun ta na rashin wanda zai fahimce ta da kyau.

Ɗakin mama Lami Baffai ya shiga suka gaisa, sai ta kallesa tace “malam ashe uwar masu gida anfara zuwa makaranta?”

“Eh wallahi se dai mu ta musu addu’a kawai” cewar baffai.

Mama Lami tace “to Allah ya basu sa’a yasa a gama lafiya a kuma ci riban karatun”
Da “Ameen” ya amsa ya sallame ta zai fita, tare suka fito tana faɗin “a dawo lafiya”.
ko ɗakin Inna bai koma ba ya fice dan dama ya gama shirin fitan sa.

Sun gama class na yau duka qarfe uku 3:00 aka tashe su, tare suka fito da Afrah ta samu Rabe yazo ɗaukanta. Sallama suka yi da Afrah ta hau mashine ɗin tana ɗaga mata hannu suka kama hanyan gida, Afrah ma drivern ta yazo ya ɗauke ta.

INA FATAN YANDA NA DAGE DUK DA BANDA LAFIYA AMMA NA MUKI TYPING SOSAI KUMA ZAKU DAGE KUYI COMMENTS SOSAI DAN NAJI DAƊIN QOQARTAWA NA MUKU🤝
UWAR BATOORL NA CIKA ALQAWARI IN BA DAI DA WANI QWAQWQWARAN HUJJA BA TO NAN NE ZAKU MIN AFUWA, AYI KARATU LAFIYA MUTANEN UWAR BATOORL

Dan Allah ayi sharing 🥺 wasu na buqata kuma banda lfyh ku kawai anan na samu daman turowa.

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Amma banda Call

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

Free book
Kyauta bada kudi ba duk wanda akasayarwa to ycn baruwana nide littafina na kyauta nayosa

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

Jeddatulkair, Maman muh’md, babyn baby, doterlo, hindat, Umme Aliyu, pharteemah etc Wannan page naku ne 💃 Uwar batoorl taji daɗin comments naku

MARASSA LAFIYA GIDA DA ASIBITI ALLAH BAMU LAFIYA.

MRS ISHAM
Marubuciyar
NI DA PATIENT NA
Uwar batoorl da ɗaukacin membobin group na JAHILCI KO AL’ADAH muna matuqar Godiya da fatan alkairi Allah bada sa’a a abinda aka sa a gaba Amaryar Hero

LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION 🤝 shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 💃 2 YEAR’S ANNIVERSARY

FAN’S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

 

💋💋 امى بتولة💋

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 13_14

 

Tana shiga gidan baabaa tun daga bakin qofa ta cire hijab tana kwalawa stohuwar qira “baaabaaallle taaaaaa!!.
Baabaa mero dake stugunne tana gyara akurkin kajin ta juyowa tayi tana faɗin “yau ni Mero naga cikakken carɓin jaraba da stiya, ke dai takwara makaho ma ya ganki ya sara miki a iya qwalawa mutum qira kaman yaci bashin ki da hanci kaman stinken balangun kwaɗi”.
Tura baki tayi tace “Baabaata ko kice mun sannu da dawowa mana kin hau ni da surutu, to ni nayi fushi ma gidanmu zan tafi” ta faɗa tana juyawa cikin burga.
Baabaa Mero qaramin stoki taja ta sunkuya ta ci-gaba da abinda take yi ko ta kanta bata bi ba. Innai ganin haka tana tura baki ta juyo ta shige ɗakin ta cire uniform nata ta sanya na gida ta ɗau kwanon abincin da ta gani da madaran shanu a gefe ta hau ci.
“Ke dan rawanin mai anguwan garinku banson kwarzaɓa, ni na baki abincin ne ko uwaki mara zuciya Indo? Daga ganin abinci kika hau ci kaman wata almajirar garin munafukai, yo Allah na tuba dama uban wa ya baki wannan mugun shawara ta ki tafi boko ba tare da kinci komai ba sai kace mai zuwa neman aljanna ko kuwa ance Annabi ake gani acan, ni Allah na tuba inba Annabi zanje gani ba bance akwai abinda zai sa na stallake ɗumammen madara mai amfani da qara lafiya jikin mutum na ɗibi jiki suɓutun-suɓutun kamar shanuwar huɗa wai na tafi wata wajan jarabar ba, inbanda gayyan jaraba ba komai a boko mutane su ta fama da biro da farar fefa kaman masu aikin Allah” cewar baabaa Mero da ta shigo ɗakin yanzu.

Sai da ta gama ci ta ɗau madaran da sanyin sa kaman ansa a firiji(fridge) ta kwankwaɗa tayi hamdala sannan ta kalli baabaa tace “nifa ba da son raina na tafi ba Hamma na ne ya sani a gaba wai mu tafi lokaci na qurewa kuma a hakanma na kusa yin letti”, harara Baabaa ta aika mata tace “shi Magajin ai shine hanjayen cikinki dole ya sa ki gaba ke kuma ki bisa jagwab-jagwab kamar tinkiyar sa za’a kai kasuwa, to Insha Allah zai zo har gidan nan ya sameni zanci mutuncin sa ba qidaye ɗan bani na iya da wuyansa kaman lagwanin risho, ke kuma tunda ya zamo mala’ikin mutuwa gare ki dole ki biye masa ki tafi haka, in nice tun yaushe na bostare nace ban karya ba amma ke shegen storon kin nan kar ki daina sai an rainaki ai sha-sha-sha kawai”.
Innai tashuwa tayi tace “nikam ba nayi sallah na tafi islamiyya gwanda ke kinyi naki”.
tashuwa tayi tayo alwala tayi sallah sannan ta wuce makaranta, Baabaa Mero sai sababi take “ja’irar yarinyar wataran tayi abu uwa babbar mata uwar gardaye”.
Baabaa ta haɗa uniform na Innai ta wanke mata, yana bushewa ta naɗo mata ta ajiye tana faɗin “na miki mai wuyan ƴar gwafan uba kyazo ki goge abunki.

Yau watanta curr tana zuwa makaranta inda cikin watan wani shaqiqin shaquwa ya shiga tsakanin ta da Afrah duk inda kaga qafan Innai a cikin makarantar to za kaga na Afrah, a wata gudan nan duk ajin ba wanda baisan qawancen su ba. Malamin English nasu kuwa wanda Afrah da sauran ƴan aji suka sawa suna “Malam ba-wasa” sam basa jituwa da Innai wanda karan-zuqan da ya sawa Innai itama Afrah ta sa mishi, sai dai duk yin su basu rena shi ba dan bai bawa ko wacce ɗaliba fiskan hakan ba.
Kaman kullum yau ma an tashe su breakfast kowa da ke cikin ajin ya fita sai ɗai-ɗai ku sai kuma Afrah da Innai da suke zaune suna hira Afrah na copyn note.
Innai tace “ni banga amfanin note da kike ta aikin yi ɗin nan ba, mu da zamu dage da karatu tunda za’a fara test ina muke ta copyn note”, Afrah barin rubutun da take yi tayi tace “habibty ke ba zaki gane ba fa, bakisan note ma da kansa C.A bane kuma kinsan na Malam ba-wasa ne dama yaqi jininmu rashin note sai ya sanya shi mana repeat tunda dai kinga yanzu shine sabon formmastern mu” faɗin Afrah tana ci-gaba da rubutun ta.
“Uhmn ni dai ba wani note da zanyi in yaga dama ya maidani Nursery” faɗin Innai tana ɗan tura baki.
Afrah abun ma sai ya bata dariya “habibty kin ganki kuwa kaman baby-doll dama aka ce su Maryam sun iya shagwaɓa to naga ɗaya yau, amma maganan note ko baza kiyi ba ni zan miki dan banson sa mana ido da yake ɗin nan especially ke..” qaran bell da suka ji wanda ke nuni da break-time ya qare shi ya sanya su gyara zaman su Afrah ta rufe littafin gabanta tana cewa “Alhamdulillahi saura naki in na koma gida na miki”.
Malamin P.H.E ne ya shigo musu (physical and health education) ya koyar na tsawon mintuna arba’in ya gama ya fita, malamin Arabic 1 ya shigo shima yaci lokacin sa ya fita.
Classes aka dinga musu har qarfe biyu ya buga kamun aka tashe su dan yin Sallahn azahar.
Tafiya suke ita da Afrah dan zuwa masallaci suyi sallah. “me kike sauri haka kaman zamu tashi sama?” Afrah girgiza kai tayi tace “kefa habibty zan miki na yarenku wai a ɗonmari problem(kina da damuwa) kinsan muka koma lokacin Qur’an ne kuma kinsan Ustaz na uzuri amma banda na latti gwanda ke nasan kin iya haddan da ya bayar ni ko ban iya ba dole nayi sauri”.
Suka qarisa masallacin suka yi alwala suka gabatar da sallahnsu sannan Innai ta ji wa Afrah haddan ta har sanda uku saura yayi kamun suka tashi suka koma aji.
Suna shiga ustaz ya shigo, Afrah lumshe ido tayi tana hamdala a zuciyarta, nan aka fara karɓan hadda. Duka layin benci biyu dake gabansu mutum kusan takwas kwata-kwata mutum uku ne suka ba da haddan dai-dai duk wanda ba suyi dai-dai ba Ustaz ya tsayar da su, aka iso kan Innai ta miqe cikin nistuwa ta fara karanto Suratul-Maryam wanda aka basu shafi guda.
Tana kammala karatun cikin yabawa da haddan nata Ustaz yace “attakbir” ƴan aji suka amsa da “Allahu Akbar!” Ustaz yace “jamil-jiddan barakhallahu feeki, ijlis” Innai zama tayi tana hamdala dan bata zaci zata iya kawo haddan dai-dai ba duk da dai tayi nacin karatu har sai da Baabaa ta qwace Qur’anin tace ta kwanta dare tayi.

Afrah miqewa tayi jikinta na ɗan rawa, ganin haka sai Innai ta kama hannunta tana magana qasa-qasa “Qawa fell comfortable okay” ajiyan zuciya Afrah ta sauqe nan ta fara rera nata karatun cikin nistuwa har ta kammala ko gyara ɗaya ba’a mata ba, itama kabbara Ustaz yasa aka mata sannan ya umurce ta da ta zauna.
“Habibty jazakhilla bikhair ta shiga aljanna Nagode” Afrah ta faɗa qasa-qasa dan kar Ustaz ya jiyo ta.
Duka ajin sanda aka karɓi haddan su sannan waɗanda basu iya ba aka bisu da bulala goma-goma kuma ustaz yace ranar Monday su tabbatar sun kawo masa haddansu, ganin rabi da kwatan ajin basu iya ba sai bai musu qari ba kawai aka yi muraja’a ya gama ya fita qarfe 3:20.
Yana fita Afrah ta rungume Innai tace “habibty ba dan ke ba da wallahi yau na tabbata sai nasha bulala kuma anamun bulala nasan sai ciwo dan ni tun ina yarinya ana duka na sai nayi rashin lafiya, Allah saka miki”.
Lokacin tashi nayi suka fito suka tarar masu ɗaukan su duk sun zo nan suka yi sallama kowa aka yi gida da shi.

Arɗo ya kalli matar nan cikin hausansa da bai nuna sosai ba yace “yanzu kai bawan Allah maimunatu ka she ja ka tahi to ya ja kayi ka gane jida ɓandu wala jam ko saɗɗa, ka bari idan ka walke duka hai ka koma gidanka”.

Kanta a qasa tana sauraran sa duk da ba duka abinda yake faɗa take ganewa ba amma tasan akan tafiyanta ne, cikin sanyi da yake yanayin ta tace “Baba na gode sosai but an apologizing because I have children’s and I know they’re in serious need of me two months is not easy” ta faɗa da harcenta da kusan turanci ya cinye sa don kanaji kasan wannan ba cikakkiyar bahaushiya ba.
Matan fara ce sosai kuma kyakkyawa wanda kana ganinta kasan ba ‘yar Nigeria bace domin turancin nata ma pure one ne ba irin broken ko pidgin ko capin na Nigerian ba, ciwon da take ciki da raunukan jikinta bai hana kyawunta fitowa ba duk da kuwa shekarunta sunja dan zata kai arba’in da ɗori.

Arɗo da ba abunda ya fahimta a maganan ta sake baki kawai yayi yana kallon ta har ta gama tayi shiru sai yace “aradun Allah maimunatu ban gane duka abinda ka she ba wannan yare ta mashu janjayen kunnuwa ni muntala(Murtala) ina jan gane kawai ka bari ita malam isa in ta Jo hai ka mata inta iya to in bata iya ba hai ta nemo mai ji”, ba yanda ta iya haka tayi shiru kawai tana addu’a Allah ya kawo wannan bawan Allah lafiya.
Washe-gari Baffai yaje rugan, suka gaisa daɗi-daɗi da hausa duk da wani abun bata ganewa, ta masa maganan komawanta da Hausa da turanci, Baffai haquri ya bata kan shima ba yaji amma in Allah ya yarda in zai zo zai taho da yaronsa mai ji sai suyi magana.
Matan nan tunda taga Baffai taji hankalinta ya kwanta da shi kuma fahimtar da tayi shi yake mata magani sannan ba biyan sa ake ba sai abun ya matuqar burgeta har take tambayar kanta “dama har yanzu akwai masu irin halin nan? Ko da yake yanda nakan ji labarin waɗan nan yaren akan ce wasun su na da mutunci sai dai wasunsu AL’ADAR su ta sai su ya su basu mutunci wa bare” shigowan matar Arɗo ne ya dakatar da ita daga tunanin da take yi, kasko ta kawo mata da garwashi nan ta lulluɓeta tayi hayaqi sannan taje ta kawo mata abincin su wanda zuwa yanzu ta saba da shi barinma madaran shanu wanda yake dama ita masoyiyar sa ne.
Duk magungunan da zata yi aiki dashi matar Arɗo ta haɗa mata sannan ta fita, kaɗan ta stakuri miyan shima sabo da maganinta da ke ciki sai gasashshen naman rago da ta ci kaɗan shima, madaran ne ta sha sosai dan sanda taji kaman cikinta zai fashe kamun ta aje ƙwaryan.

Arɗo yace “malam Isha Allah ya biya ki hi kawai jamu she maki don kuwa kema kin taimaka, haka fa daga fita kiwo kawai hai ga belloji da gudu wai shun ga gawa hai na gama storita gawa kuma ana jaune hai lafiya, to muna juwa muka ga bawan Allahn nan maimunatu jina-jina Allah dai ya kare ahe bai mutu ba da ransa kaɗo kam hai muka qira ki”, “ba komi Arɗo ai yiwa kai ne fatan dai Allah daɗa karewa ya bata lafiya yanzu dai zamu zo da yaron waje na Insha Allah gobe inyaso sai suyi magana ya faɗa mana in ma komawan ne in Allah ya yarda ba zai gagara ba sai mu shirya mata tafiya” cewar baffai.

 

“Ke dai takwara Allah aiko miki da Manzon shiriya domin kuwa kina buqatan shiriya wai kullum na miki wanki goga kayan naki ya gagareki kindai san gobe ranar da kuke storo har shi mai jan kunnen da ya qirqiro muku jarabar karatun yaren ƴan wutan ko, in ba za kiyi ba shikkenan kiyi zamanki ni dama banso zuwanki makaranta ba naso kawai kiyi aurenki ki haifaman ‘yan yara kyawawa masu kama da ke, to Allah na tuba ai gwanda ma kiyi bokon wani shawaragin ne zai yarda ya aure ki yarinya shekara sha huɗu kike nema kin balaga ba ko alaman nunu (nono) a qirjinki ni bantaɓa ganin budurci irin naki ba ma takwara, ba sakaran da zai aureki ba ki da komai yo yanzu mazan duk sun zama ‘yan iska masu satifiket mu a zamanin mu saima mun kusa haihuwan fari muke fara nunu wata ma sai ta haihu nunun ke fitowa kuma haka muke zauna lafiya da mazajenmu ba ruwansu da iskancinku na yaran zamani, nasan Hansai ma ta kusa fara wa amma ke shiru qirji kaman an daɓe kwalta, Allah na tuba maka da wannan jarabar yarinya mutum yaqi yin nunu bare ace ya fara jini su dole na Samari suqi ki, kin wani rantaɓo tankin kashi (ɗuwawu) kaman babbar mata gaki dau ba jiki ba nunu amma sai tulin ɗuwaiwaya” cewar baabaa tana stefewa Innai kai.
Ita dai ko qala bata cewa Baabaa Mero ba sai ma karatunta da take kaman waqa.
Suna gama stifan ta bata ɗari da hamsin tace “gashi maza kaiwa maman lado ta miki tunda uwarki makistiya baqin ciki take da ke na tabbata watarana ma zata aske miki kai tunda taga kinfi ta gaban goshinta gashi, kema da kika wani yo wannan uban kayan nauyi da zafin bansan ina za ki kai ba, gashi kaman hauka”.
Tura baki Innai tayi tace “ni dai a daina zagarmun uwa ta” ta faɗa tana ficewa a gidan.
Ɗaukan buta baabaa tayi ta bita da shi da gudu zata wurgeta sai ta ga har tasha kwana, cikin gidan ta dawo tana cewa “ja’irar yarinya mai zubin aljanu yaushe kika fita har kin ɓace to zaki dawo ki same ni ko aljanar ce ke ma bai dame ni ba nice nan uwar aljanu Maryam shugabar su in muguntar inma kirkin duk masu suna Maryam na Aljanu halinsu ne to ma wa ya isa ya nuna musu mugunta, ooh ni Mero bakina dawo Allah shiga tsakanin mu da jinnu ai wasa nake muku Aradu” ta faɗa tana waige-waige can kuma taci gaba “har ni za ki nunawa halin ‘yan duniya ɗan wani bushashshen kashi, da ace uwar taki kaman ta kowa ce ai sai ya dame ni yo shawaragiyar uwa sha-tara sha-bakwai wacce bata san zafin haihuwa ba bata san Annabi ya kafu ba, inkin sake kin dawo gidan nan mai rabamu sai Allah jeki wajan tambaɗaɗɗiyar uwar taki jarababbu”.

 

 

𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚’𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 – 250 𝟏𝐆𝐁 – 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 500
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 750

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎……

 

Taje ta samu ba layi Allah ya taimake ta nan aka mata kiston da aka basu a makaranta na “flower in the garden” anayi tana raki har da hawayen ta, ana gamawa ta wuce gidan su dan tasan tabbas taje gidan baabaa to kashinta ya bushe.
Tana shiga taci sa’a ba kowa a cikin gidan sai ta wuce ɗakin su kai tsaye, samun Hassu tayi tana goge nata uniform ɗin nan ta lallaɓata taje ta ɗauko mata nata a gidan Baabaa zata musu gugan.

Da sallama Hassu ta shiga gidan tana cewa “baabaarmu wai inji Adda Innai a bani kayan makarantar ta”, “tunda kece fistararriya fitsaratun carɓin rashin ta idonki a fistare yake kin fitsare qafafuwanki har da qwaqwalwanki dole ta aiko ki, to gasu can ba kwaɗa su zanyi ba kuma tazo ta tattare komai nata a gidan nan ta kaiwa uwarta tunda dai halin ɗan wani zata nuna mun,kuma ni baabaar iyayenku ce ba ku ba, yara sai tulin kalen dangi tunda baku sai da taku uwar ba ku riqe ta ni ban haifi ja’irai ba, kukam sai Isa da Indo” cewar baabaa mero da ke kulle kajin ta ganin magrib yayi.
Hassu ɗaukan kayan Innai tayi tawa baabaa sai anjuma tayi tafiyan ta dan tasan tana stoma baki cikin rigimar su ita ce za taji kunya sun saba in da sabo.

***
“Fatu Allah Ubangiji yasa yau wani ɗan albarkan Malami ya daka mun ke tunda dai bakya ganin lokaci mutum sai shegen son bacci kaman man konti” cewar wata farar stohuwa da har gashin girar ta furfura ne.
Yarinya da ake tashi a baccin ne tayi miqa sannan ta tashi ta zauna idonta a rufe tana addu’an tashuwa bacci, sauqa tayi a kan gadon ta gama tsalle-stallen ta sannan ta tura qofan bayin ta dake cikin ɗakin ta shiga tayi wanka cikin minti biyu ta fito ɗaure da qaton towel.
Wayan ta ne ya ɗau qara tana dubawa taga “Dad” ɗan tura baki tayi dan tasan duk aikin kakarta ce, sanda wayan ya kusa yankewa ta ɗauka a hankali tace “Daddy good morning”
Morning too Afrah, mai kike yi har yanzu baki shirya zuwa makaranta ba? Kinaso na turo miki yayanki ko?
Cikin shagwaɓa tace “daddy Allah sharri take mun yanzu haka na saka uniform karyawa zanyi na tafi kuma yanzu 6:30 ne”
Afrah ungo naki, dan gidanku uwar tawa ke miki sharri maza-maza ki shirya yanzun nan kar qarfe 7 ya sameki a gida hope am communicating?
“Yes Daddy a gaishe da habibty” ta faɗa tana murmushi
Kitt ya kashe wayan.
Tashuwa tayi tana ƴar rawanta cikin mintuna biyar ta gama shiri komai da komai yau ma a hannu ta riqe takardun ta, qofan ɗakinta taja ta rufe.
Hango stohuwar nan tayi a palourn hakimce akan kujera da ƴar rakani kashinta a gefenta (Old Nokia), gaishetaa tayi tace “Hajja na tafi” harara stohuwan ta aika mata da shi tace “Fatu yanzu dan na fadawa ubanki gaskiya shine zaki gaisheni a tsaye kuma kiqi karyawa to baki isa ki fita gidan nan baki karya ba”.
Gudun ɓata lokaci kuma tasan time ya tafi bakin Hajja ya kamata a daka ta sai ta zauna ta karya sama-sama tace “kuma ni a daina cemun fatu in ba za’a ce Afrah ba ace Fatima kar mutum yaga kaman sunansa gare ni ba ruwa na da wata takwara” Afrah ta faɗa ta fice tana dariya dan tasan ta cokalo stuliyan dodo.
Hajja tana zaune tace “duk abinda kika ce kincewa uwarki Mairamu rasai akuyan jauro”.
Masu aikin gidan ne suka tattare inda Afrah ta ɓata suka gyara komi kaman ba’a taɓa ba dan duk sunsan halin Hajja akan tsafta.

Yau kusan tare suka iso makarantar dan drivern Afrah na juyawa Rabe ya iso da Innai, cikin farin ciki Afrah ta rungume Innai tace “habibty jaɓɓama” murmushi Innai tayi tace “kinfara koyan fillanci kenan halan bafulatani zamu bawa ke”.
Wucewa suka yi filin assembly inda aka yi inspection waɗanda ba suyi style na kiston da aka bada ba aka fitar da su, Allah ya taimaki Afrah da Innai sunyi nan Afrah ta dinga hamdala a zuciyarta ta godewa Hajja dan ita ce ta masta mata akan sai tayi kiston.

Sun gabatar da karatun yau inda wa’danda basu bada haddan sati uku da suka wuce ba suka bada kuma Alhmdlh kowa ya iya nan aka musu qari sannan wani sati ran labara za suyi C.A na Qur’an kowa ya tabbatar ya iya.
Ana tashin su suka fito tare har bakin gate amma yau ba wanda mai ɗaukan sa ya iso a cikin su sakamakon antashe su da wuri, Afrah tace “habibty yaushe za kizo gidanmu kiga hajjata? Innai na murmushi tace “nima yaushe za kizo kiga baabaa ta”.

Afrah ta buɗe baki za tayi magana sai ga drivern ta nan, tura baki tayi tace “baba driver zai kaste mana hiranmu dama kullum karatu na hanamu yi dan haka sai anzo ɗaukan ki zan tafi nima”.
Innai kawai murmushi ta mata dan tasan ko tace ta tafi ba yarda za tayi ba tunda ba yau ta fara yin hakan ba inda ba ita Innai aka fara zuwa ɗauka ba Afrah bata yarda ta tafi ta barta.
Suna staye har qarfe huɗu ya cika nan fa Afrah ta dage Innai ta bita gidansu, suna cikin ja’injan sai ga Rabe ya iso nan Innai tayi hamdala tace “case closed gashi ya zo”.
Hararanta Afrah tayi a wasa tace “dama nasan ba zaki je gidanmu ba ai tunda muna yanka mutane dole kice case closed” nan kowa ya hau abun ɗaukan sa aka yi da kowa gida, Afrah dai har suka rabu taqi yiwa Innai dariya, abun ya damu Innai.

MASU SHARHI UWAR BATOORL TAKU TA GODE🤝 DAN SHARHIN KU SHINE QWARIN GUIWANA
MASU GODIYA BANSON THANKS NAKU KUMIN SHARHI KAWAI SHI NAKE BUQATA
Masu sharhi waɗanda basa group na JAHILCI KO AL’ADAH Uwar batoorl na godiya tana yinku❤️

Ba posting ranakun qarshen mako amma nayo dan farincikinku so kuma kumin comments shine farinciki na

 

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

Free book
Kyauta bada kudi ba duk wanda akasayarwa to ycn baruwana nide littafina na kyauta nayosa

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

Wannan page naku ne masu daraja, sharhinku na qaramin qwarin guiwa 🤝
Surayyatou nah
Dr Seeyerth
qanwat ecleemah
doterlo
my dearest
ukhtynh… etc

LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION 🤝 shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 💃 2 YEAR’S ANNIVERSARY

FAN’S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

💋💋 امى بتولة💋

 

 

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 15_16

Innai na komawa gida ta wuce gidan baabaarta inda ta tarar da Baabaa tare da Baffai a zaune suna hira.
Tana shiga ta gaida Baabaa sannan ta gaishe da Baffai.

kallonta Baffai yayi yace “Uwata inkin cire kayan makarantar akwai inda za muje ki raka ni”.
Innai ta buɗe baki zata amsa sai Baabaa Mero ta rigata tace “amma baka storon Allah mai sunan Malam ace dan tsabar tsagwaran rashin tausayi balle ta-ido a gabana ba bayan raina ba kai ma zaka fara nunawa takwara baqin hali irin na uwatta Indo, ace yarinya daga dawowa ba ko hutawa ka hau ta da jarabar stiya, to in kayi wasa ba inda takwara za taje kai ɗin daa ubanwa ya hana ka iya yaren masu jan kunnen, jimun jaraba fa, ai sai ka bari baiwar Allah tayi sallah taci tuwo ta huta, ku kama ku tura yarinya jarababben boko sannan baza’a barta ta hutawa rayuwanta ba dan cikan rashin imani balle tausayi”.

Baffai yace “ayi haquri Baabaa”.

Innai ta miqe ta shiga ciki ta cire uniform nata sannan ta ɗau kwanon abinci da ta gani a rufe da kuma madaran shanu mai ɗumi, ta ci ta sha sannan ta fito ta watsa ruwa tayi alwala tayi sallah.
Fitowa tayi a ɗakin taje gefen baabaa ta zauna tace “baabaalle ta ina Baffai na?”
Harara Baabaa ta aika mata da shi tace “ja’ira, ubanki ya tafi koyan yiwa mutane sannu da gida, kullum na ajiye madara ta sai ki daqarqare ki shanye yo to ke da za kiyi bokoko a wuta ina ruwan ki da madara ai da aure kika ce za kiyi sai na daqarqare nima na dinga ɗirka miki madara dai-dai gwargwado da duk wani abun da nasan zai sa ki kece reni a wajan ƴan iskan mazan yanzu”.
Innai da bata fahimci me baabaa ke nufi ba tace “yanzu dai ina Baffai ba?
“Dan ubale ubanki ya tafi gidansa tashimun a gefe kamun na zaune ki ƴar ƙwal uba” .
Tura baki Innai tayi ta miqe ta sanya hijab ta fice a gidan.

Tana qoqarin shiga gidan Baffai ya fito, ganinsa sai ta masta gefe ta durqusa tace “Baffai dama zanzo qiran naka ne”.
Murmushi Baffai yayi yace “to uwata tashi mu tafi kar dare ya mana a hanya ko.

Tashuwa tayi suka kama hanyam rugan su Arɗo, suna tafiya suna hira har suka isa.
Cikin gidan ta shige shi kuma Baffai ya tsaya wajan su Arɗo suka yi sallar Magrib sannan suka shigo gidan tare.

Innai tayi sallah tana zaune a gefe su Baffai suka shigo nan ya umurce ta da ta biyo su, suka shiga ɗakin suka tarar matar ta idar da sallah.
Innai tsayawa tayi kallon matar duk da duhu ya fara amma hasken ɗakin yana haska su, matar fara ce kyakkyawa in ka ganta ba zaka ce babbar mata bace, kama take da larabawa.
Gaisawa da matar Arɗo da Baffai suka yi sannan Innai ma tace “ina wuni”.
Matar fuskanta da murmushi dan yarinyar ta shiga ranta tace “how are’u doing baby? Innai tace “am doing good”…
Bayan sun gama gaisawa cikin harshen turanci da Innai wacce ba wani sosai-sosai ta iya ba, nan matar ta faɗa mata komai dalla- dalla yacce zata gane dan tawa su Arɗo bayani.
Innai ajiyan zuciya tayi tace “Baffai wai ita a cikin Gombe take amma hastarin ya faru da ita ne tana dawowa daga Jigawa state dan acan suke zaune da yaranta, yanzu tana so zata koma Gombe ne saboda yaranta tasan hankalinsu a tashe yake amma in Allah ya yarda zata zo baza’a jima ba” Matar murmushi take dan tasan Innai ta fahimci zancen ta kuma yarinyar ta qara burgeta.

Arɗo duk da ba sosai yake jin hausa ba amma kasancewar Innai tayi wani maganan da fillanci shima ya fahimta nan dai yace ba komai Allah kaimu.
Bayan sun fito Baffai ya yi sallama da Arɗo suka kamo hanyan komawa gida ga dare yayi ga duhu, tafiya suke suna hira na ɗa da Uba.

Ihu Innai ta sanya “Wayyooo! Allah naaaaa, hande kam mi boni! Baffai qaya ya soke ni, Wayyo zafi!” cewar ta tana yarfe hannu dan azaba.
Da sauri Baffai ya laluɓo touchin da ya kunna yana haska qafan nata, wuff kaman walqiya yaga gimawan bindin abu, cikin sauri Baffai ya haska qafan Innai.
Salati yayi ganin abinda yayi tunanin ne ya faru, maciji ne ya cije ta ba qaya ba, tana yarfe hannu har ta fara kuka dan ciwon da take ji.

Abinda ya rataya a wuyan sa kaman ɗan-kwali ya jawo ya kama qafan nata ya ɗaure mata cinyan ta sannan ya ɗaga ta cikin sauri suka qarisa rugan nasu yana mata sannu.
Innai ba abinda take sai hawaye, suna shiga cikin gida Baffai yace “A’ishatu kawo mun tabarma”.
Inna ta fito da tabarma ta shumfiɗa masa ya ajiye Innai yace “zo ki mata fifita ba naje na qira Baabaa”.
Inna tana tsaye daga gefe har Baffai ya juya zai fice bata mosta ba.
Baffai juyowa yayi ganin ta tsaye bata mosta ba ransa a ɓace yace “A’isha ba dake nake magana ba?”
Inna sunne kai tayi qasa ta juya ta shige ɗakin ta.

Baffai har zai bita ɗaki sai kuma tuna yarinyar sa kar dafi ya haura mata sai ya fice da sauri ya je gidan Baabaa Mero, da sallama ya shiga Baabaa na kallonsa tace “kai mai sunan Malam lafiya na ganka haka ragaja-ragaja kaman an biyo ka? Ina ita takwarar tawa take?”
Baffai yace “Baabaa mun gamu da stautsayi ne ki taimaka mana da gadalin dafin maciji”.
cikin sauri Baabaa ta miqe daga zaunen da take ta ɗaura hannu a kai tace “kar ka ce mun takwara ta maciji ya ciza?”
Baffai yace “baabaa ita ce”.
Baffai bai ida rufe baki ba Baabaa Mero ta wawuri hijab tayi hanyan waje sai kuma ta juyo ta shige ɗakin ko minti guda bata yi ba ta fito da wani qulli a hannunta tayi waje ko takan Baffai bata bi ba.
Shigowa gidan tayi ba sallama dan ta manta da Sallaman ma, inda ta jiyo nishin Innai tayi ta same ta kan taburman sai zufa take yi numfashi sama-sama kaman zata sume.
Cikin hanzari Baabaa Mero ta riqo qafan da taga an ɗaure ganin babu haske ta ɗaga kai za tayi magana sai taga Baffai a gefenta, qaramin tsaki taja tace “kai Isa ka sanya ni gaba kaman mai neman tubarraqi ba zaka kawo mun haske ba dan tambaɗewa tunda ciwon ba’a jikinka yake ba ko?”
Touchi ya kunna ya haska mata qafan, nan ta murza gadalin ta manna mata a wajan ciwon.
“Miqo mun ruwa a kofi” cewar Baabaa tana duban Baffai, miqewa yayi ya wuce madafin gidan ya ɗu kofi ya ɗiba ruwa ya kawo wa baabaa, jiqa maganin tayi tana tallafo kan Innai sai gani tayi Innai ta sume.

Magaji ne ya shigo gidan da sallama ganin su Baffai sai yayi wajansu “me ya same ta Baffai?” Cewar Magaji ganin Innai a kwance a sume kuma baabaa na sharar qwalla kaman anyi mata mutuwa. Cikin masifa Baabaa tace “Ubanka Musa ne ya same ta dan rashin tausayi ko sannu ba zaka mata ba”.
Kallon Baabaa kawai yake yi tana bam-bami tana sawa Innai ruwan maganin da ta jiqa a baki amma yana zubewa ne kawai baya shiga bakin ta.
Ganin haka sai Magaji ya amshi kofin maganin ya riqe kan Innai ya ɗan buɗe bakinta yana stiyaya mata ruwan maganin.
Ruwan maganin na isa maqoshi ta ta buɗe ido tana haɗiyan ruwa, sai da ta shanye tass sannan ta rufe idonta ta koma tayi luff da kanta a cinyan Magaji.

Baabaa ido ta zaro tana salati tace “na shiga arba’in da uku ni Meramu yau me ya samu takwarata tasha maganin kuma ansa mata gadali sannan ba tayi amai ba sai faman lumshe ido take kamar mai shirin mutuwa, don Allah takwara bar wannan lumshe ido kamar wacce ke mashashshara ki buɗe idonki kiyi amai son ranki kinji”.
Ba ita Baabaa ba har Baffai da Magaji hankalinsu ya tashi ganin taqi yin amai sai ma lumshe ido da tayi tana bacci da ya ɗauke ta yanzu”.

“Wai nikam mai sunan Malam babu mutane a gidannan ne? Ko wata sabon salon baqin halin aka qutto gida shiru kaman ba halittan mutane ga yarinya bagatantan kaman wacce zata mutu amma ace ko ɗan stunstu bai fito dubamu ba kaman wanɗanda muka musu kashi akan gado jarababbu tambaɗaɗɗu marassa imani da tausayi” faɗin Baabaa Mero da ta miqe tayi hanyan ɗakin Inna A’i tana cewa “uwar jaraba mai sharɓa-sharɓan baqin hali kina gani yarinya ba lafiya cizon maciji na faman kashe ta kina zaune a ɗaki da hijab kamar mai takaba, wuce muje kiwa jikata tofin cizon maciji nikam”.

Inna dake zaune akan sallaya da carbi a hannun ta sai qasa kawai tayi da kanta tana jin maganganun Baabaa har ta gama bata mosta ba bata ce uffan ba.
Baabaa tace “Indo wai har halin naki ya balaga ya kai haka? Indo rashin storon Allahn ma ya girmama ya wuce misali? Ina magana kina zaune wato ta mutu? Kai subhanallahi tirr da wannan tambaɗewan rayuwa wai AL’ADA, Indo Sallahn ki ma ba karɓuwa zai yi ba dan alhaqin baiwar Allah dake kanki, ni Meramu wannan JAHILCI KO AL’ADAH za’a qira sa? To koma me yake Aradu nayi Allah wadai da shi, Mutum na da iliminsa amma ya cika carbin burbushin tunaninsa tsaɓ da JAHILCI” Baabaa na gama magana ta fice rai a ɓace.

“Kai Magaji ɗauka mun yarinyar nan mu tafi gida na dan in tana gidan nan tun ranar mutuwanta bai yi ba zasu qarisa kashe ta dukansu gaba suke da Allah da ya qaddara zuwan takwara duniya”.
Magaji miqewa yayi ya ɗauke ta a kafaɗa suka fice tare da Baffai sai gidan Baabaa Mero.

Suna shiga gidan tasa Magaji ya ajeta akan tabarman da dama take zaune a kai kamun Baffai yazo qiranta, mafifici ta shiga ɗaki ta dauko Baffai ya karɓa yana fifita Innai Magaji kuwa kanta na cinyansa.
Baabaa tagumi kawai ta zuba tana ganin ikon Allah dan duk iya sanin ta ko wani irin maciji ne ya ciji mutum muddin ta basa wannan magani ta manna masa gadalin shikkenan sai ya amar da dafin, dan a wajan mijinta ta gaji duka magungunan.
Miqewa Baabaa tayi ta shiga ɗaki can ta fito da wani qullin magani da qwai da kofi, tana zama ta fasa qwan sannan ta sanya maganin ta kaɗa, Magaji ta miqawa ya karɓa ya buɗe bakin Innai yana sa mata, sai ta kuma buɗe ido tana haɗiya kaɗan-kaɗan, yana gama bata ta wara ido tana ya tsine fiska sai lokacin ta fara jin tashin zuciya, in tayi kaman zata rufe ido sai taji amai na taso mata tana buɗe ido ya kwanta.
Baabaa tace “kai Magaji yanzukam ɗago ta kar ta ɓata maka jiki” sai ya ɗago kanta ya zaunar da ita amma yana riqe da ita. Sai lokacin Baffai ya tuna da maganan tofi nan take ya ɗau kofi da ruwa ya fara addu’a yana tofawa sannan ya sa mata a bakin ta sha, tana gama sha ko kofin bai gama barin bakinta ba sai amai, sosai take amai kaman zata harar da kayan cikin ta, ganin haka sai duk suka yi hamdala suna aikin jera mata sannu.
Sosai tayi amai ta galabaita, tayi luuuu! zata faɗi Magaji yayi saurin taro ta, nan Baabaa ta miqe ta ɗauko roba da ruwa sannan ta sanya Magaji ya gogewa Innai jikinta ta kawo wani riga tace ya sanya mata, kallon Baabaa yayi jin abinda tace na ya sawa Innai riga, duk da dai qanwar sa ce kuma yarinya ce tunda shekarunta sha-huɗu 14 kuma ba komai qirjinta amma baya jin zai iya sa mata rigan dan gudun mastala shi shaiɗan ba’a iya masa.
Ganin ya tsaya da riga a hannu sai ta harare sa ta karɓa zata sa mata shi kuma Magaji kau da idonsa yayi sai da ta gama da mata ya juyo, baabaa ta sanya shi ɗaukan Innai ya kaita ɗaki, ya ɗauke ta ya kaita ɗaki ya kwantar da ita akan gadon ta ya juyo ya fito.

Duk suna zaune zugum-zugum kowa yayi shiru ko wannensu da abinda yake tunawa a ransa yayinda shi kuma Magaji tunani yake wannan yarinya ko kaɗan bata da nauyi kullum ka ɗaga ta kaman ka ɗaga stinke.

Baabaa Mero tace “mai sunan Malam kana ji na?”
Baffai ɗaga kai yayi alaman yana sauraranra, sai ta numfasa tace “mai sunan Malam abun ya isa haka yau shekara ɗai-ɗai shekaru sha-huɗu kenan da haihuwan takwara sannan tun randa aka haifeta har yau ba abinda ya sanja na daga AL’ADAN da uwarta ta ɗaura wa kanta, abun ya isheni yau an qureni na tabbata nan gaba ko ba rai aka kawo takwara indo ba zata kalli gawanta ba balle batun ta mata addu’a ko ta wanke ta dan haka zan ɗau mummunan mataki a kanku duka abun ya ishe ni, ku tashi ku bani waje” ta faɗa tana kallon Baffai da Magaji.

Magaji kallon Baabaa yayi yace “baabaa kiyi haquri amma ni na tabbata Inna na son Innai irin matsanancin soyayyan nan ma, dan Allah kuyi haquri ku mata uzuri”.
harara baabaa Mero ta aika masa da shi tace “kai dan ubanka Musa tunda ba kai ake azabtarwa ba dole kace haka, bayan AL’ADA ta kunyan ɗan fari kasan akwai AL’ADAH ta SHA’DI kamun aure ko? To tunda kace haka ka tabbatar sai an maka za’a baka mata jarababben mara tausayi har za kayi magana ni da nasan ba dan an daina sha’di ba sai dai ka mutu ba aure, to ciwon da ake ji a shaɗi na ɗan awanni ko mintuna ka isa ka haɗa shi da irin ciwon da ake ji na rashin kulawa daga mahaifiya? Anbar duk waɗan nan AL’ADUN saboda zamani yayi kowa ya fahimci yawancin AL’ADU ba komai bane face JAHILCI da kuma ɗaukan alhaqin bayin Allah a banza da wofi abu ba aya ba bare hadisi kuma dai ba Mustahabbi ba ko sunna balle a qira sa farilla kaman yacce mutane ke jahiltan kan su suka aza a gaban goshi, ciwon da takwara ke ji ba ko wanne mai laga-lagan zuciya bane zai iya ɗauka ka godewa Allah uwarka Habiba ba ruwanta da wannan JAHILALLEN AL’ADA dan da kai ne na tabbata sai ka shiga duniya dan jaraba”.

Baffai kansa a qasa ya kasa cewa komai shi kaɗai yasan me yake kissinawa a ransa, dan sosai yau A’isha ta quresa.
Baabaa masifa take kaman zata ari baki barin dai in ta tuno rashin kunyan da Inna ta mata, cewa su Baffai tayi su tafi dare nayi tunda qarfe ɗaya na dare har ya gota, ficewa suka yi suka tafi gida, Magaji yawa Baffai sai da safe ya wuce ɗakin sa.
Baffai yana shiga ɗakin ya samu Inna a kwance da alama tayi bacci ma, qaramin tsaki yaja ya shumfiɗa sallaya ya kwanta a nan qasa.

Baabaa ɗaki ta shiga, cike da tausayi ta kalli Innai tace “takwara Inshà Allahu damuwanki ya kusa qarewa nasan me zan yi” nan ta kwanta a nata gadon bayan tayi addu’a ta shafawa Innai itama ta shafa nata.

Ina mai matuƙar baku haquri na rashin ji daga gareni jiya Monday sakamakon wani uzuri da ya riqe ni, amma Insha Allahu yau page’s 2 zan turo, amma fa ya danganta da sharhinku, dan in kukayi yamun to da yamma ma zakuga update inkuma shirune to sai gobe kuma.

MASU SHARHI UWAR BATOORL TAKU TA GODE🤝 DAN SHARHIN KU SHINE QWARIN GUIWANA
MASU GODIYA BANSON THANKS NAKU KUMIN SHARHI KAWAI SHI NAKE BUQATA
Masu sharhi waɗanda basa group na JAHILCI KO AL’ADAH Uwar batoorl na godiya tana yinku❤️

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

Free book
Kyauta bada kudi ba duk wanda akasayarwa to ycn baruwana nide littafina na kyauta nayosa

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

Wannan shafi gaba ɗayan sa sukutum nasa, sadaukarwa ne gare ki rabin rai na, my peace giver, tattaɓa kunnena, ecleeyhn Kakus mum ɗin ta♥️ ECLEEMAT ABDUL (Ummu khamaluddeen wa Sheikh Mufaddal).
Mum Noor wa batoorl a isarwa antyn Nana saqo.
Jama’a kuyiwa TATTAƁA KUNNE NA addu’a da fatan alkairi.

LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION 🤝 shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 💃 2 YEAR’S ANNIVERSARY

FAN’S GA NAKU

𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

💋💋 امى بتولة💋

 

 

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 17_18

𝗖𝗔𝗡𝗔𝗗𝗔⭐⭐

Zaune yake a katafaren office nasa wanda staruwa da haɗuwan office ɗin kai kace a ɗaki ne dan yafi ɗaki ma staruwa da haɗuwa ga ko ina qamshi ke tashi a office ɗin, waya ce qirar cammon 20+ a hannun sa yana magana kaman mai storon buɗe bakin sa.
DMD kenan haɗaɗɗen saurayi kyakkyawa ajin qarshe mai ji da kyau da kuɗi wanda ba zai haura shekara 29 da haihuwa ba, magana yake a wayan cikin harshen turanci yana cewa “look jay am not coming to Gombe again I wan rest serious cuz dis day’s the work’s are plenty am even tired with the company” ya faɗa yana yastine fiska.
Dariya Jay ya sanya a ɗaya ɓangaren yace “DMD kaji muryanka kuwa da yacce kake magana kaman mace gaskiya babe naka ta shiga uku dan nasan bata isa ta gwada maka rigima ba, shikkenan in baka shigo Gomben ba ni zan shigo Canada ɗin soon ba”.
“Ai ni ba’a haifi babe na ba tukunna ina tunani ma ba macen da zata burge ni kamun aje zancen gaba dan haka mata suyi rayuwan su nayi tawa rayuwa ba su yafi daɗi” cewar DMD.
Jay dariya ya kuma yi wanda kana ji kasan na shaqiyanci ne sai ya kwaikwai muryan DMD ya maimaita abinda ya faɗa kamun yace “wannan bashi ne kuma soon zan tuna maka abinda ka faɗa”.
Dariyan da Jay yayi ya qular da DMD dan ya stani yawan dariya kaman ba lafiya ba shi abu mai wuya ne kaga murmushin sa ma balle dariyansa, staki yaja cikin fushi yace “Jay kai ba’a dogon magana da kai sai ka ɓata wa mutum rai, so Ammi zata shigo Gombe in zata dawo sai ku taho tare”.
Qitt ya kashe wayan ya aje kan table dake gabansa ya busar da iska a bakin sai ya danna wani button akan table ɗin, sai kawai wata ta shigo tana rusunawa tace “Sir” nuni ya mata da first-aid box dake ajiye acan gefe wanda shi kanshi abun kallo ne.
Tana ganin haka tasan me yake nufi sai ta buɗe box ɗin ta ciro magani ta miqo masa tana rusunawa, amsa yayi ya ɓalla ya wasta a bakin sa ba ko ruwa ya haɗiye ya miqa mata saura ta mayar box ɗin sannan ta fita.
Sanda ta fita kamun ya buɗe idon sa yana unbotting na jacket nasa ya cire ya aje ya dannan wani button jikin kujeransa sai yayi kaman resting chair, ya ɗaura qafan sa kan table ɗin ya lumshe ido, wai ɗan maganan da yayi har kansa ya fara masa ciwo.

Jay na kashe waya yayi murmushi yace “gaskiya DMD kana fama da cuta” matar da ta shigo palourn ganin sa yana magana shi ɗaya yana dariya sai tace “kai jabeer lafiyanka kake magana kai kaɗai? Murmushi yayi ya sosa qeyansa yace “habibty lafiya lau kawai DMD ne yaban dariya”.
Taɓe baki tayi tace “kai da shi kam ai sai addu’an shiriya, fatan Amminsa na lafiya?
Jay yace “tana lafiya wai ma tana hanyan shigowa Gomben”, “to Allah kawo ta lafiya, dan gaskiyar baiwar Allah ya kamata ta leqo gidan mijinta duk da dai dan yaranta take zaune acan ɗin” cewar mummy tana zama a kujera.
Jay yace “ai wallahi Ammi na da qoqari mummy kullum fa tana sintiri a hanyan nan ita ce Gombe ita ce Canada Allah dai ya stare ta”.
da “Ameen” mummy ta amsa a taqaice.

Jay(jabeer) kenan matashi mai kyau da aji sannan ga kuɗi shi kuma babban likita ne a babban asibitin cikin garin Gombe FMC Gombe.

Sai da ya huta sosai ganin ba zai iya aikin ba sai ya danna button na ɗazu wannar matashiyar baturiyan ta kuma shigowa ya miqe yayi gaba ya fice a office ɗin, jacket nasa da ya cire da wayoyinsa ta ɗauka tabi bayansa da sauri, ta danna button na lifter ya buɗe sai ya shige ita kuma ta shiga na gefen, floor na qarshe liftern ya tsaya buɗe da kansa ya fito ita kuma baturiyar ta jima da fitowa a nata ta staya gefe, yana fitowa yayi gaba tabi bayansa.
Driver ne ya staya da mota a dai-dai qofan fitowa Companyn sannan ya buɗe wa DMD qofa ya shige sai ya kulle, baturiyan ta miqa masa jacket da wayoyin DMD ya amsa ya aje masa a gefen sa sannan yaja motorn.

𝗤𝘂𝗲𝗯𝗲𝗰 𝗖𝗮𝗻𝗮𝗱𝗮
Gaban wani tangamemen gida dake quebec area a canada baturen drivern yayi horn aka buɗe musu haɗaɗɗen gate ɗin gidan wanda kana gani kasan sai dai a qasar wajen dan gida ne iya gida, baturen na parking ya fito da sauri ya buɗe wa Ogan nasa qofa, DMD fito da haɗaɗɗun qafafuwan sa dake sanye cikin sandal’s wanda a qalla kuɗin su zai kai 700k a kuɗin Nigeria, sannan a hankali ya fito gaba ɗaya, ya juya zai shige cikin gidan ganin drivern a bayansa sai ya juyo yayi magana cikin harshen turanci “Christ na hana ka shigowa cikin gida na ina kuma zaka bini?” rusunawa baturen da aka qira da Christ yayi yace cikin turanci shima “Sir kayi haquri dama wayoyinka ne”.
Ba tare da ya kuma cewa komai ba ya amshi jacket nasa da wayoyinsa sannan ya miqa masa wani envelope yace ya kaiwa sakatariyar sa liliyan.
Karɓan envelope ɗin Christ yayi shi kuma DMD ya qarisa shigewa gidan da sallama a bakin sa.

Wata yarinya ce wacce ba zata wuce shekara 10 goma ba mai matuqar kama da shi banbancin su kawai ita tana da duhun fata amma ba har can ba dan tafi chocolate color skin kawai dai ba za’a ce mata fara irin hasken sa ba. Da gudu tazo tayi hugging nasa tana cewa “oyoyo Darling sannu da dawo wa” murmushi ya mata ya ɗaga ta sama yayi juyi da ita kamun yace “sweetie kin fara nauyi fa” tura baki yarinyar da ya qira da sweetie tayi ta fara hahharba qafa akan ya ajiye ta tunda ita ce ma ta fara nauyi yarinya da ita, ganin ta tura baki kuma yasan me take nufi dan bata so ace mata tana da jiki ko tana da nauyi, sai ya miqa mata waya yaja kunnen ta ya wuce kan step’s yabi hanyan da zai sada shi da sashin sa, duk maganan da suke da turanci suke yi dan kaman kwata-kwata basa jin Hausa.

Ya Ilahi! Inji masu karin zance suka ce wata miyar sai a makwaɓta, tabbas wata duniyar ko a mafarki sai mai rabo ke kallonta dan kuwa haɗewan sashin DMD ba zai faɗu ba dan duk staruwan office nasa in kaga sashin sa kai kace bola ne, duk haɗuwan wannan gida daga waje bai yi rabin kwatan haɗuwan sashin DMD ba, wasu arnun england-chair’s ne a palourn kusan set huɗu dan haɗuwa da girman palourn, akwai white, dark-blue, black and light-blue, daga gefe wasu haɗaɗɗun transparence labule ne masu kama da glass-door a dinning area wanda in mutum na zaune a dinning ɗin zai iya hangen komai na palourn amma in kana palourn ba lallai kaga komai na dinning ɗin ba, daga gefe kuma wani corridor ne wanda bai kai wajan gidan ba amma akwai swimming-pool mai ɗauke da shape na heart sannan ruwan cikin sa fari tass har kana iya hango qasan pool ɗin, daga gefe kuma qofa ne wanda zai sada ka da kitchen na palourn sai kuma step’s a gefe wanda DMD yabi dan haurawa ɗakin sa, a saman ma wani palourn ne wanda ya haɗu ya gaji da haɗuwa sai dai bai kai na down-stairs girma ba sannan akwai duk wani abun buqata a nan ɗin ma har da kitchen da dinning area.
A bakin ɗaya daga qofofi 6 na glass dake saman ya staya, sai da ya sanya yastan sa a jikin wajan fingerprint wani abu a jikin qofan kaman computer ya haska qwayar idon sa sannan a hankali qofan ya buɗe ya shige ɗakin nasa.
Wata arniyan gado ne a ɗakin wanda yasha shumfuɗi kai kace ba’a kwanciya a kai, gadon nada girma sosai daga jikin bangon kuma plasma ne mai girma a manne wanda kaman a jikin bangon aka qerosa sai wall-drop da ya cinye rabin ɗakin dan girma. Aje wayoyinsa yayi a kan bed side drawer sai ya cire kayan jikinsa ya rage daga shi sai short-nicker, kayan da ya cire ya rataya a hanger dake cikin Sip ɗin sannan ya nufi wani ɓangaren ɗakin, yana tsayawa a wajan sai qofa ya buɗe a wajan wanda inka gani da farko ka ɗauka duka bangon ɗakin ne.
Bayan mintuna ya fito ɗaure da guntun towel wanda iyakacin sa guiwansa sai wani qarami a hannunsa yana share ruwan jikinsa, qirjinsa mai cike da haiba da jarumta cike yake da kwantaccun gashi luf-luf jikinsa a mummurɗe kaman ɗan kokawa(restiling).
Gaban dressing mirror yaje ya staya sama-sama ya shafa mai ya shafawa gashin kansa da inka kama zai kistu staff dan stayi gashi baqiqqirin, ya taje kansa sannan ya taje gemunsa da gashin ba sosai ba, ya ɗau kayan da ya fitar ya saka, 3quarter sai armless, ya fice a dakin.
Main palourn ya dawo ganin ba kowa sai yabi hanyan ɗayan step’s ɗin, tun a bakin qofan ya fara jiyo hayaniyan su dafe kai yayi yace “Ammi ta tafi kuma tabar ɗan adam da ciwon kai ka dawo baka huta ba waɗan nan yara masu kai da kunnuwan su dame ka” cikin harshen turanci yayi maganan.

Yana ida shiga palourn sashin yaran na ganinsa sai duk suka yi shiru suka yi sturu-sturu da ido, yarinyar ɗazu da ya bawa waya da wata wacce daga gani sistern ta ce dan zata bata 5 year’s.
Ya buɗe baki zai yi magana sai yaji qaran qofa sai ya ɗaga kai, wata ƴar budurwa ce wacce a qalla zata kai shekara 20 da haihuwa ta fito a ɗaki sanye da t-shirt da legis ta tufke gashin kanta, sauqowa step’s ɗin tayi ta qaraso palourn fuskanta ɗauke da murmushi cikin harshen turanci tace “Darling sannu da dawowa kuma gwanda da ka shigo dan sweetie da sweerie zasu iya kashewa mutum dodon kunne tun ɗazu magana nake musu su bari sunqi ji” kamun ta gama rufe baki sweetie tace “sweedy ji storon Allah ki faɗi gaskiya yanzu fa muka far….”.
Kallon da DMD ya mata shi yasa ta haɗiye sauran maganan, sai yace “you’re very stupid sweetie, so u’re telling ur sister to fear god, who are you to tell her dis? She older u with good 10 year’s so watch ur word’s is sweedy not sweerie….” Faɗa ya mata sosai cikin harshen turanci kamun ya juya kan sweerie wacce zata kai 15 year’s yace mata “and you sweetie is not ur mate she’s ur junior sister you better take ur rank as a sister and maintain it idiot”.
Duk faɗa ya musu kamun ya qarisa shigewa ya samu waje ya zauna yace “sweedy bring coffee for me”.

Duk nistuwa suka yi kaman anyi ruwa an ɗauke sannan ya dube su yace cikin harshen turanci “littatafan makarantu laifi suka muko ko kuma kashe kuɗi ake yi ba dalili? Duk miqewa suka yi sweerie tayi ɗaki ita kuma sweetie ta miqo masa waya tana magana a shagwaɓe “Darling na qira Ammi layinta a kashe baya shiga” amsan wayan yayi yaja qaramin staki ya ajiye dan yasan ɗazu a office suka gama magana da ita ta isa Companyn su dake Jigawa tace zata bi mota ta shiga Gombe kuma in ta isa yasan zata qira sa ko Abiy ya qira sa.
Sweedy ta kawo masa coffee nasa yana kurɓa suna hira sama-sama dangane da school nata da zata koma a India, sweetie da sweerie suka ɗauko materials na makarantan su yasa sweedy ta duba shi kuma ya ɗau wayan sa ya buɗe data yana duba wasu abubuwa.

 

“Jabeer wai baka da hankali ko? Ba zaka je ka dubo mahaifiyata ba, kukam wai me ke damunku ne? Daga Kai har ɗan uwanka baku son zuwa wajan hajja, ita fa ta haifemu kamun Allah yasa muka haifeku to maza-maza karka yarda satin nan ya qare ba tare da kaje ka dubo ta ba inkuma kaqi na haɗaka da baffanka dan shine dai-dai da ku dukan ku har shi ɗan uwan naka, kuma kasa Afreen a gaba ku tafi fatan ka jini?
Jay yana sosa qeya yace “eh Daddy Inshà Allahu nan da Sunday zanje amma gaskiya ni bazan tafi da afreen ba tunda ta iya tuqi kuma itama tana da mota sai ta tafi tafiyanta dan Allah Daddy Afreen ta rena mutane”.

Matashiya budurwa ce ta shigo palourn sanye take da Arabian gown tasha rolling kyakkyawa mai kama da Daddy, jin abinda yayanta ke cewa sai ta fakaici idonsa ta harare sa ta wuce gefen Daddy ta zauna tana tura baki tace “dama nima bance zan bi mutum ba, ace yayanka ya tsaneka Allah kyauta rayuwan nan”.
Danqwalo mummy ta mata tace “ungo naki Afreen yayan naki kike faɗawa haka dan ba ki da kunyako?”
Tura baki ta kuma yi tace “habibty Allah baya sona” Daddy ne ya kaste maganan ta hanyar cewa “magana ya qare na gama magana ke Afreen za kibi yayanki kai kuma jabeer zaka tafi tare da Afreen”.
Mummy tace “Allah sarki Faɗimatu na, Allah duk Auta tafi ku hankali da jin magana kawai anyi rashin sa’a ta fito qaramarku amma ita ya kamata ta zama yayarku”.
Jay dariya ya saka yace “Habibty ni na haqura nabar mata girman zan koma field nata na zama ɗan Auta nima a dinga lallaɓani”.
hararansa Daddy yayi yace “gardi da kai zaka haɗa kanka da ‘yar jinjirar mu” dukan su a palourn dariya suka saka har Afreen.

 

Shiru-shiru DMD bai ga qiran Ammi ba balle na Abiy, abu duk yabi ya ishe sa Allah dai yasa lafiya.. qiran da ya shigo wayan sa ne ya yanke masa tunanin da yake yi, raɗau sunan “ABIY” ya fito, ganin mai qiransa hamdala yayi dan yasan Amminsa ta isa kenan.
Ɗaga wayan yayi ya kara a kunne “Hello Abiy ya…..” Maganan dake bakinsa ne ya maqale jin abinda Abiy yake cewa cikin faɗa-faɗa, miqewa yayi yace “Whatttttt!!!!!!?………..

 

MASU SHARHI UWAR BATOORL TAKU TA GODE🤝 DAN SHARHIN KU SHINE QWARIN GUIWANA
MASU GODIYA BANSON THANKS NAKU KUMIN SHARHI KAWAI SHI NAKE BUQATA
Masu sharhi waɗanda basa group na JAHILCI KO AL’ADAH Uwar batoorl na godiya tana yinku❤️

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

 

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

Free book
Kyauta bada kuɗi ba duk wanda aka sayar wa to ba ruwana nidai littafina a kyauta nayi shi.

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

Wannan page naku ne masu daraja, sharhinku na qaramin qwarin guiwa 🤝
Surayyatou nah
Dr Seeyerth
Jeddatulkair
Basira montakha
Ummeey Aliyu
Momsi
Maman kausar
my dearest
ukhtynh
Duk mai SHARHI dole Uwar batoorl ta ambato sunansa.

LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION 🤝 shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 💃 2 YEAR’S ANNIVERSARY

FAN’S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

💋💋 امى بتولة💋

 

 

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 19_20

Washe gari Innai ta tashi da mugun zazzaɓi ga ciwon ciki, hankalin Baabaa Mero in yayi dubu to ya tashi.
Hanata zuwa makaranta tayi tunda bata da lafiya ta huta, amma Innai ta tirje sai taje dan suna da test.
Sai da Magaji yazo da kansa kaman zai mata duka tukunna ta haqura da maganan zuwa makarantan amma idanuwanta har da qwalla tana tunanin test na yau da zasu yi.
Baabaa ta kalleta tace “ja’irar yarinya shawaragiya wai ace baka da lafiya ka huta zuwa boko hakanan ka sanya mutane a gaba kana sheshsheqa da gulmammen kuka dan staɓar tijara, kai kace uwarku da ubanku ake raba muku a makarantar, Aradu takwara kika yi wasa daga yau kinbar zuwa makarantar sai na aurar dake in yaso kije can mijin yayi haquri ya raineki kiyi nunu a gidan sa” .
Tura baki Innai tayi tace “nikam tunda an hanani zuwa makarantar a bar damu na da magana”.
Buɗe baki baabaa tayi ta jero salati tace “eh tabbas ya tabbata bayan yaren ‘yan wuta har da halayyar ‘yan wuta ake koya muku yanzu wai du yaushe kika fara zuwa makarantar? Inaji baki cika wata biyu ba amma har kin koyo fistara yarinya shiru-shiru sanyi-sanyi ba ruwanki kaman kazar da aka sanya a ruwan sanyi amma yau ni kike cewa na dameki da magana to takwara kinyi da uwaki Indo, shashashar yarinya kawai ai inba tambaɗanci ba da rashin kunya baki gayamun magana, to Allah kawo ubanki daga yau an daina karatun da zuwa makarantar tunda rasar kunya ake koyowa a can”.
Innai fashewa tayi da kuka ta tashi tana riqe ciki ta shige cikin ɗakin Baabaa Mero, binta da harara tayi tace “ja’ira ‘yar kutun-kutun dubi yacce take tafiya kaman stohon da yasha sanda a baya amma wai ki dage zaki makaranta”.
Fitowa tayi a ɗakin tana share hawaye ko qala bata cewa Baabaa Mero ba ta fice a gidan, da kallo Baabaa ta bita ta tafa hannu tace “kai amma in akace yaro da kare basu da banbanci to haqqun anyi gaskiya, yanzu sabida Allah dan rashin sanin ciwon kai yarinya ta kwashi figaggun qafanta kaman wanda aka stoma kaza a ruwan sanyi tace zata je wancan gidan dan kawai anfaɗa mata gaskiya to Inshà Allahu ni Meramu ba ni binki kuma ba ni qara shiga tsabgarki da ta uwarki kayan kunyan ya ishe ni kuje ku fama in suka barki kika mutu su binneki ko gawan kar a gwada mun ‘yar ƙwal uba Allah baki lafiya, kuma makarantar ne nace ba zaki je ba babu zuwa sai Aure”.

Da sallama ta shiga gidan tana riqe da cikin ta, tafiya take tana layi kaman zata faɗi idonta na hawaye tayi hanyan ɗakin su, Inna na zaune qofan ɗakinta tana gyaran shinkafa tunda ta ɗaga kai sau ɗaya ta kalli Innai sai ta kau da kai ta cigaba da aikin ta, Innai na tafiya a duqe tayi tuntuɓe tana qoqarin faɗuwa Baffai da fitowansa bayi kenan da Mama Lami da itama fitowan ta ɗaki kenan kusan rige-rigen tare Innai suka yi lokaci guda Baffai na cewa “subhanallahi Uwata jikin ne har yanzu?” hutar da mama Lami Baffai yayi ya ɗaga Innai caɗak ya kaita ɗakin mama lami ya kwantar sannan ya fito, kallo ɗaya yawa Inna ganin ko mostawa ba tayi ba ya kau da kai ya juya yana ayyana irin hukuncin da zai ɗauka wannan karon, zai fita a gidan sai ga Magaji, ganin Baffai sai yace “Baffai za ka fita ne?.
Baffai yace “eh baban Baffai zan sayowa qanwarka magani ne zazzaɓi na damunta” kallon Baffai Magaji yayi yace “dama Hassu ba taje makaranta ba? Girgiza kai Baffai yayi yace “ba Hassu ba Innai ce”.
Da mamaki Magaji yace “Innai de da yanzu na barta gidan baabaa? “Eh ita dai yanzu shigowanta”.
Karɓan kuɗin maganin yayi ya juya sayo wa shi kuma Baffai ya koma cikin gidan.
Ɗakin mama Lami ya ɗage labule ya shige ya zauna gefen Innai yana jera mata sannu.
Magaji yaje ya sayo magani ya kawo Baffai yayi-yayi da ita tasha maganin amma sai taɓara take taqi amsa, da Magaji yasa baki sai ta fashe da kuka. ganin haka sai mama Lami ta bawa Baffai haquri akan ya bari sai anyi abincin rana taci sai ta sha, Baffai ba dan yaso ba ya qyale ta.

—–
Afrah tunda ta shigo makaranta take zuba ido ta inda zata ga ɓullowan habibtynta dukda dai sun rabu tana fushi da habibtyn nata amma ta mastu ta kalleta dan bata jin zata iya fushi da ita.
Wasa-wasa har aka yi assembly aka gama aka shiga class malam ba wasa ya shigo ya gama ya fita shima sai leqawa yake amma bai ga idon mutumiyar sa ba, Afrah tun tana ɗaukan abun wasa har taga da gaske ne dan gashi har an fita break an dawo an kuma fita sallahn azahar, nan dai duk gaba ɗaya yanayinta ya sauya sai take jin kaman ta dinga ihu rashin ganin Innai, Allah ya taimake ta ba’a musu test ɗin ba dan da kuwa bata san me zata rubuta ba balle ma tayi tunanin yiwa Innai.
Har aka tashe su aka zo ɗaukan ta amma ta roqi drivern ya jiraata, zaman dube-dube tayi sune basu baro makarantar ba sai da ɗaliban day gaba ɗaya suka waste na hostel ma suka shige hostel kamun tawa drivern magana su tafi idanuwanta cike da qwalla qiris take jira tayi kuka gashi gobe Saturday ba makaranta har sai Wednesday dan ranan Monday da Tuesday hutun Esther.

Driver na parking ta sauqa ko jakan makarantar bata ɗauka ba ta tura baki ta shige cikin gidan, hanyan ɗakinta tayi ko kallon palourn bata yi ba balle tasan ko akwai mutane ko babu.
Kaman daga sama ta jiyo muryan yayanta yana cewa “Afrah ba magana ne? Juyowa tayi sai kawai hawayen da take riqewa suka gangaro suna bin kuncinta ta wuce wajan yayan nata ta shige jikinsa.
Afreen ce ta taɓe baki tace “ke dai kinga ta kanki kuma in haka ake Auta to baki more ba duk anbi an sakalta ki kalli abinda kike yi fa kayan amai”.
kamun Jay ya buɗe baki Hajja ta riga sa tace “ke maimuna banson rashin mutunci fa daga zuwa zaki addabi baiwar Allah, wai ubanwa yace kizo ne ma, kai kuma jabiru baka san hanya bane ka ɗauko wannan fitsaratun?
Jay bai kalli Hajja ba balle Afreen hankalinsa na kan damuwan da suke ciki yace “Auta me ya same ki? Cikin kuka tace masa “BB (big brother) ba Habibty na ce taqi zuwa makaranta yau ba” da mamaki yake kallon ta yace “wacce habibtyn? dan nasan mummy dai tana gida”.
Tura baki tayi tace “qawata ce mai sunan mummy shine nake ce mata haka, jiya da zamu rabu mun ɓata yau kuma ban ganta a makarantan ba kuma ina kewanta”.
Afreen cikin taqaici tace “amma Allah wadaran naka ya lalace aka bincika ma wata ‘yar talakawa ce har da zubar da hawayenki a kanta dan ganin arahan gabas karuwa da sallahn walha”.
Hajja ma guntun tsaki taja tace “fatu ke dai kin cika abin taqaici kaman mutum yayi kashi” Jay kuwa murmushi yayi cikin sigan rarrashi yace “to tashi kije ki shirya kici abinci na kaiki gidan su ki dubo ta ko”.
Tura baki Afrah tayi tace “nifa BB sunan ta kawai na sani bansan gidansu ba kuma kaman ba’a cikin Ashaka take ba amma dai ban sani ba, Allah BB sai ka ganta ga kyau ga hankali itama takawarar kakarta ce kaman ni kuma itama a gaban kakarta take zaune, BB Allah nikam ka aure ta ai sai ka ganta kaman ni take amma ta fini kyau dai sai bata da um’um” cikin jin kunyan abinda takeson cewa ɗin tace “kawo kunnenka na gaya maka” kunnensa ya kawo ta faɗa masa maganan tana miqewa tayi ɗakinta da gudu.
Murmushi Jay yayi yace “wannan yarinya kin girma soon kema zamu nemo miji mu aura miki”.
Hajja tace “fatu faɗi ba’a tambayeki ba, shikkenan har ta gama rigiman ta gudu saura kuma na anjuma in ta fito”.
Afreen ta jawo wayanta tana lastawa tace “anjuma kuma ke da ita dan mukam mun jima a Gombe”.
Jay kallonta yayi yana murmushin mugunta a ransa cewa yake “ina Gombe ba muna Gombe ba dan barinki anan zan yi”.
Nan Hajja ke tambayan sa batun mastalan da ake ciki.

Numfasawa yayi yace “Hajja har yanzu dai shiru ba wani labari cikiya ba irin wanda bamu bada ba har DMD ya bada kyauta akan wanda ya ganta amma shiru”.

Qwafa Hajja tayi tace “wancan fitinannen yaro da ya gagari kowa, ina ma yake da baku zo tare ba?

“Mun taho yana bacci Hajja”.

“Ya masa kyau ya fama da baqin halin sa, ita kuma uwar su Allah bayyana ta”

Da “Ameen Jay ya amsa”

Afreen ta tashi ta shige ciki tana “cewa bari na huta kamun lokacin komawa”.

Harara Hajja ta bita da shi tana cewa “sai inga gidan uban da zaki koma muna nan dake ja’ira”.

Jay yayi murmushi yace “Hajja ba na dawo zanje wajan wani freind na”.

“To a dawo lafiya ɗan albarka” faɗin Hajja tana murmushi

Tashuwa Jay yayi ya fice.

 

𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚’𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 – 250 𝟏𝐆𝐁 – 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 500
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 750

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎……

 

⭐⭐

DMD Miqewa yayi yace “Whatttttt!?
“Eh uwarku bata iso ba kuma na qira layinta baya shiga maza-maza ka nemeta ka faɗa mata inma a ina ta staya ko me take yi ina buqatan ganinta a gida yanzun nan” kitt Abiy ya kashe qiran yana gama magana.
Layin Amminsa ya ke qira both na Nigeria da na Canada amma duka abu ɗaya ake faɗa masa “switch-off” huzar da iskan bakinsa yayi yana cewa “shittt! Na rasa me Ammi ke ɗaukowa a Nigerian nan har na tsani qasar kullum cikin matsaloli” zama yayi ya ɗau wayansa yayi dialing wani number ana ɗauka aka ce “hello Sir” cikin magansn sa mai kama da rigiman yace “Mark zan turo maka layuka yanzu ka bincika mun su” yana gama magana ya kashe qiran ya tura masa, can sai numbern ya qira sa ya ɗauka yace “Yes ina jinka”, “am sorry Sir amma a binciken mu layin na kashe kuma ba yanda za’a yi mu bincika sai dai a samu qwararru a Nigerian su bincika da kansu, sannan layin Canada kuma anjima da sauqe shi” mutumin da ya qira ya faɗa, ba tare da yayi magana ba ya kashe wayan qittt.
Main palourn ya sauqo ya tarar da sweedy na zaune riqe da waya a hannunta, kallonta yayi yace “ya aka yi” tashuwa tayi ta dawo gefensa ta zauna kaman za tayi kuka tace “Darling ina ta qiran layin Ammi baya shiga kuma fa tun da rana da muka yi waya bamu qara yi ba yanzu ga can sweetie sai kuka take wai za tayi waya da Ammi yanzu haka na barta da sweerie tana rarrashinta ne na fito na yi knocking qofanka baka ji ba” duk maganan da take cikin harshen turanci take yi sannan izuwa yanzu hawaye ya fara wanke fatan kumatun ta dake yalqi kaman na jarirai.
Ɓoye damuwan da yake ciki yayi ta hanyar cewa “karku damu Ammi na lafiya nafi tunanin wayanta ne ba chaji so ki turomun sweetie ke da sweerie kuma ku kula sosai sannan in Allah ya kaimu gobe zan tafi Nigeria karki faɗa musu ke dai ki kula da kanki da su sosai”.
kallon sa tayi tana hawaye tace “Darling Nigeria dai? Kai da kace ba zaka qara komawa Nigeria ba sannan yanzu kace zaka je kuma kace mun lafiya, please inda wani abun ka faɗamun zanfi samun nistuwa dan na qira Abiy yaqi ɗauka” murmushi yayi ya shafa kanta yana share mata hawayen yace “da akwai wani abu zan faɗa miki ki yarda da yayanki ko, ki kula da kanki da qannenki kaman yanda nace in naje kuma zan haɗaku da Ammi yanzu je ki rarrashi sweetie in na dawo zanzo na ɗauke ta”.
Ba dan taso ba ta haura sama sashin su taje ta samu sweetie tayi bacci idanuwanta duk bushashshen hawaye, sweerie kuma tana zaune gefenta tayi tagumi, kallon su da tayi ya sanya jikinta ya qara mutuwa nan dai ta daure tayi yanda yayansu yace mata ta nunawa sweerie komai lafiya wayan Ammi ba chaji ne kawai sannan itama ta zauna gefen su dan yau basa jin kowa zai iya kwana shi ɗaya a ɗakin sa.

Ɓangaren DMD yana ganin haurawan qanwan sa sama ya sauqe ajiyan zuciya yana fita driver yazo da mota ya buɗe masa ya shiga yaja motan suka fice a gidan, a taqaice kawai yace ma drivern “airport”.
Suna zuwa airport suka samu ba jirgi mai tafiya Nigerian sai gobe, yaso biyan kuɗin jirgin gaba ɗaya a tafi da shi yau amma sai ya fasa tuna sweetie dan in ba shi ya rarrasheta ba baza taji rarràshin sweedy ko sweerie ba. Juyawa suka yi suka koma gida lokacin ma dare yayi amma abinka da qasar turawa kuma babban qasa ko ina kaman rana ga jama’a ga haske.
Sama ya haura ya shiga ɓangaren su, ɗakin sweetie ya nufa dan yasan ba zasu wuce can ba, yana murɗa handle ɗin sweedy ta zuba mishi ido, sweetie tayi bacci kanta na cinyan sweerie ita kuma sweerie kanta na kan cinyan sweedy, duk sai yaji sun basa tausayi rana guda kawai na rashin jin Ammi har sun rame.
Qarasa shigowa yayi ya qara kwantar wa da qanwar tasa hankali, sannan ya ɗauki sweerie ya kaita ɗakin sweedy yace suje su kwana a can shi kuma ya ɗauki sweetie ya fito ya nufi ɓangaren sa da ita.
Har bedroom ya kaita ya kwantar da ita akan faffaɗan gadon sa, shi kuma yaje ya ɗauro alwala yayi sallahn isha’i da bai samu yayi ba ya kuma yi shafa’i da wutiri sannan yayi addu’oen sa ya kwanta gefen qanwar tasa yayi addu’a ya shafa mata shima ya shafa.

Sama-sama yake ji ana bubbuga shi ana sheshsheqan kuka, idanuwansa ya buɗe ya kalli sweetie na tukuikuya shi, tashuwa yayi ya zauna ya riqo ta yana tambayan ta menene? Cikin sheshsheqan kuka tace “Darling Ammi na nayi mafarkin bata da lafiya kuma banji muryanta ba tun jiya ka qiramun ita” shafa kanta yayi alaman rarràshi ya miqa hannunsa ya ɗauko wayan sa ganin har 3 na dare yayi sai yace “sweetie ki bari sai gobe da safe kinga yanzu dare yayi kuma kinsan wannan lokaci Ammi na bacci kar mu tashe ta” da qyar ya samu ta haqura har bacci ya ɗauke ta, tashuwa yayi ya ɗauro alwala yayi nafilfilu da addu’oe sannan ya sha dai-dai ana qiran sallan asuba, jan carbi ya dinga yi har aka shiga ya tashi yabi masallaci.
Yana idar da komai a gaggauce ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya shirya cikin qananun kayan da suka karɓe sa sosai, ganin sweetie bata farka ba sai ya barta a ɗakin ya fice yaja mata qofa.
Yana shiga mota driver yaja sai international airport Canada.

Suna isa komai ready, driver ya ajiye sa ya juya shi kuma cikin mintuna biyar jirgin su ya tashi sai Nigerian.

Jirginsu na sauqa ya qira jay “Hello jay ina airport ka turo mun mota” qitt ya kashe wayan.
Bai kai minti talatin ba sai Jay da kansa yazo ya ɗauke sa, da mamaki ya kalle sa yace “jiya kawai muka yi waya ba zaka zo ba yau kuma sai gaka akwai wani abun da ya faru ne?
Lumshe ido yayi dan yama rasa ta yaya zai fara sai kawai yace “Jay bansan me ke faruwa ba amma dai Ammi tun jiya bata je gida ba” da mamaki Jay ya kallesa yace “shine har ka shigo Nigeria akan hakan me yasa ba zaka qira layinta ba ko ka qirani naje na ɗauko ta?
Cike da gundura da magana dan kansa har ya fara ciwo yace “Jay ka fahimta mana an qira layinta both baya shiga kuma nasa ayi tracking tun acan amma ba wani labari ga su sweedy duk sun ɗaga hankali qarshe ma jiya sweetie a ɗaki na ta kwana dan rigima wallahi har sun rame jiya kawai basu ji muryam Ammi ba”.
Jay kansa ya ɗaure ga tausayin su sweetie dan yasan irin sanya ta a jiki da Ammi tayi, cikin ɗaurewan kai yace “to yanzu ina muka nufa?
DMD yace “wai Jigawa fa jirginta ya sauqa tabi Companyna na can duba yanayin ayyukan sannan ta ɗau mota wai za tayi driving da kanta har Gombe nace mata a’a amma Ammi taqi ji”.

“Yanzu ita ɗaya ce ko tare da driver? Cewar Jay….

 

MASU SHARHI UWAR BATOORL TAKU TA GODE🤝 DAN SHARHIN KU SHINE QWARIN GUIWANA
MASU GODIYA BANSON THANKS NAKU KUMIN SHARHI KAWAI SHI NAKE BUQATA
Masu sharhi waɗanda basa group na JAHILCI KO AL’ADAH Uwar batoorl na godiya tana yinku❤️

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION 🤝 shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 💃 2 YEAR’S ANNIVERSARY

Qawas 🤣 to masto kusa ga naki page ɗin, ABEEDATOURH (OUM INAYAH)
marubuciyar IZINAH

JINJINA GARE KI : Asma’ul Husnah (favorite) asmabaffa ❤️

FAN’S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

💋💋 امى بتولة💋

 

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 21_22

DMD cikin yanayin damuwa yace “Jay yanzu dai bansani ba sai dai mu tambayi Managern Companyn”.
Laluɓo wayansa yayi ya fito da shi ganin wayan dake hannun sa sai ya lumshe ido, kaman zai yi kuka yace “shitttttttttt! Jay ba wayana mai layukan Nigeria na taho da shi ba”.
Kallonsa yayi yace “to ya za muyi? Dai-dai sun iso qofan gidan Abiy dake cikin GRA kusa da gidan governor.
Jay zai yi horn DMD ya dakatar da shi yace “ina zaka kai ni?
Kallon sa Jay yayi mai nuni da banson tambayan renin wayo sai yace masa “in kawo ka gidan ku kace ina zan kai ka kaga banson irin tambayan nan”.
Qaramin tsaki yaja yace “to daman wa ya gaya maka nazo gidan mu ne? Nazo neman Ammi na ne kawai kuma kasan bana shiga gidan nan in bata ciki so ko ka juya mu tafi ko kuma ka sauqa ka bani mota nayi gaban kaina”.
Dariya Jay yayi yace “in sauqa in baka mota ni kuma na ɓace kenan na koma gida? Hararansa DMD yayi yace “yauwa na tuna layin nasa na kan ɗayan Gmail account na bari nayi loggin.
Jay jan motan yayi suka tafi gidan su dake Tunfure, suna isa ya kammala komai ya qira Managern ya ɗauka suka yi magana.
Cikin palourn suka shiga tare da sallama a bakin su duka, Jay yayi sama ɗakin sa yace bari ya sauya kaya yazo su fita, shi kuma ya wuce ɗakin mummy.
Sallama yayi a qofan ɗakin, mummy ta amsa masa tace “shigo”. sai ya murɗa handle ɗin ya shiga.
Waro ido tayi cikin mamaki tace “yaron Ammi kai ne da sassafen nan? Iso ka zauna” zama yayi a bakin gadon mummy sannan ya gaisheta nan yake faɗa mata abinda ke faruwa cikin tashin hankali ta kalle sa tace “yanzu maimakon ku wuce jigawan ko wajan ‘yan sanda shine ka biyewa jabeer, ba’a tafiya da jallabiya ne? Ko kuwa a qafa zaku tafi ba mota ba? Qasa yayi da kansa dai-dai Jay ya shigo ɗakin da sallama.
Shima gaishe da mummy yayi ta amsa tana cewa “jabeer baka da hankali ashe? Sanja kayan me zaka yi zance za kaje ko neman uwarka? Shafa kai Jay yayi yace “afuwan habibty yanzu zamu tafi, tashi mu wuce DMD”.
Miqewa DMD yayi yace “habibty sai mun dawo” mummy tace “Allah bada sa’a ku dawo lafiya ubangiji Allah yasa lafiya ne ya riqe ta Allah sa komai yazo da sauqi kuyi sauri maza zan faɗawa Daddyn ku”.

Ficewa suka yi suka ɗau wani motan DMD yace shi zai yi driving jay in yana driving kaman mai storon hanya.
DMD ya ja su sauka ɗau hanyan barin Gombe, sun bar cikin Gombe sun isa Kwami local government har suka fita.
Sun fita a kwami ba jimawa Jay yace “dude tsaya na rage mara” ba tare da yace komai ba ya ci-gaba da driving.
Jay ganin zai jaza masa aiki sai ya danna birki, kaman za su gangara wani rami haka motan ya tsaya DMD yaja guntun tsaki yace “malam yi sauri bamu da enough time yau nake so mu dawo” Jay na sauqa ya gangara zai yi fistari sai yaga wani mota kaman wanda aka yi hastari kaman kuma ba hastari ba, fasa fistarin yayi ya qarisa wajan motan da mugun sauri ya dawo wajan motan su yace “dude zo kaga wata mota kamar ta Companyn ka”.
Ba shiri ya fito a motan suka gangara hanyan da Jay ya fito, tun daga nesa DMD ke mamaki wannan ai motar Companyn sa na Jigawa ne.
Jay fistarin sa yayi kamun ya dawo wajan DMD ya samu yana waya da Managern sa.
Yana kashe wayan ya dubi Jay muryan sa a raunane kaman zai yi kuka yace “Jay wannan ne motan da su Ammi suka taho da shi”. da qyar DMD ya buɗe qofan motan nan ya samu handbag na Ammi da wayoyinta da komai a ciki, yana buɗewa yaga tana cikin WhatsApp akan layin sa, dubawa yayi yaga ta fara typing amma bata qarisa ba.
Abinda ta rubuta ya maimaita cikin harshen Indianci ta rubuta “Darling ina fatan za kaga saqon nan muna hanyan shiga Gombe wasu suka tare mu za..” bata qarisa rubutun ba.
Wani gigitaccen qara ya saki da qarfi cikin harshen turanci yace “koo kai ne shugaban Aljanu you most pay for this sai ka biya taɓa mahaifiyata” Jay kallonsa yayi ya sa hannu ya amshi wayan amma sai ya samu da Indianci aka yi rubutun kuma bai iya ba, kallon sa yayi yace “me ke faruwa DMD?
Idanuwan sa jajir ya faɗa masa abinda Ammi ta rubuta, ba tare da ɓata lokaci ba Jay ya fitar da waya dan qiran ACP(assistant commissioner of police) da yake abokin sa sai kuma qiran Daddy ya shigo, ɗagawa yayi suka gaisa yake tambayan su ya ake ciki? Nan Jay ya faɗawa Daddy komai sai Daddy yace ya bari zai qira commissioner of police da kansa yanzu ya lallaɓa ɗan uwansa su dawo gida.
Jay yayi yayi da DMD su tafi ga abinda Daddy yace amma sam yaqi, suna staye a wajan kusan fin awa sai ga jiniyan motan ‘yan sanda.
Da qyar DMD ya yarda ya shiga mota suka koma cikin Gombe, sanin halinsa da kuma yanayin da yake ciki sai bai kai sa gidan Abiy ba yayi gidan Daddy.
Gaba ɗaya bincike ake ko ta ina neman Ammi da drivern ta, lamari dai har yakai gaban governor sakamakon aminin Abiy ne governorn Gomben, al’amari yayi stamari tun ana ganin kaman komai zai zo da sauqi amma ina ba su Ammi ba labarin su, sai da aka kwashe sati guda gaba ɗaya DMD ya fita hayyacin sa a ɓangaren su sweedy kuwa kullum cikin kuka take qira tana masa itakam Ammin ta, tun yana ɓoyewa Muhseena (sweedy) har ya faɗa mata abinda ake ciki amma tayi haquri ta ci-gaba da kula da qannen su.

“Duk wannan magana da kake bai taso ba fa Mustapha yanzu abun damuwan shine Maimuna Allah Ubangiji ya bayyana ta ba maganan surutu ko wani magana daban wa zai so haka kawai yabar iyalansa dan son ransa? Kasan babu wannan mutum ɗin sai dai in ta kama ba yanda aka iya Allah ne ya aiko da hakan” faɗin Daddy da fuskansa ke cike da damuwa.
“Hmmn! Yaya kenan duk da nasan ba mai son hakan amma in ba ganganci ba me na tsayuwa a jigawan da tayi, me zai hanata qarisowa gida inyaso daga baya ba sai taje jigawan ba, kuma mai ya hanata bin jirgi ta dawo Gomben, ita sai dai a mota gaskiya ɗaya ce yaya kuma ba’a sonta Wallahi Maimuna bata ji bata kiyayewa yanzu gashi duk tasa hankalin mutane ya tashi”.
DMD da ya cika yayi fam idanuwan sa suka kaɗa suka yi jajir har fiskan sa jaa yayi dan ɓacin rai dake ƙwarzaban sa ji yake kawai kaman ya tashi ya shaqe Abiy ya huta da irin maganan da yake faɗan nan, tashuwa yayi zai haura sama ɗakin Jay sai maganan da Abiy ke yi ya tsayar da shi “yaya ka gani ko yaron nan ba abinda yake damunsa sai reni, gani yake kanmu ɗaya yanzu ina magana ya tashi zai tafi ko qala bai ce ba wato ga mahaukaci na magana hmmn duk Maimuna tabi ta lalata tarbiyyan yara basa ganin girman kowa dama sai da aka hanani auren ta amma na dage, gashi nan abinda ake jiyemun”.
Juyowa DMD yayi a fusace ya dawo palourn gaban Abiy yaje ya tsaya yana huci kaman zai maqure sa, wani malalacin kallo yake wa Abiy, ya buɗe baki da niyan yin magana “….
“Kul son karka soma mahaifinka ne shi” cewar mummy da ke qarasowa palourn.
Abiy da kana ganin sa kasan ya girgiza dan kuwa ba wanda ya kaisa sanin halin ɗan nasa “a’a ki qyale sa yayi abinda zai yi ba gashi nan ba inba reni ba har zai tsayamun a kai yana huci kaman wani maciji, kasheni za kayi ko? To shaqeni ka kasheni dan ba zan taɓa kallon laifinku ba komai kuka yi ku yara ne nuna muku aka yi, Maimuna dai ta cuce ni bata gwada wa yarana rayuwan ‘ya’yan musulmai ba dan duk musulmi na qwarai yasan ba’a ja da iyaye” Abiy ya faɗa ransa a ɓace.
Daddy miqewa yayi ya dafa kafaɗan sa yace “son calm down ka nustu kaji kayi haquri” jan hanunsa yayi ya zaunar da shi kamun ya dubi Abiy yace “Mustapha magana ya qare ba wanda zai so a dinga zagin mahaifiyarsa ko da a bayan idon sa balle a gaban idonsa”.
Qwafa DMD yayi ya tashi ya fice a gidan gaba ɗaya.

Wasa-gaske sanda aka kwashe wata guda ba Ammi ba labarin ta, abun duniya duk ya taru yawa DMD yawa, bincike ba irin wanda ba’a yi cikin Nigeria har da kewayen Nigeria ba gidan TV da ba’a bada cikiya ba haka jarida duk wata kafar sada labari ba inda ba’a bayar ba kuma tare da garaɓasa duk wanda ya kawo ta ko ya ganta yana da kyautar gida da million biyar, amma duk da haka ba labarin Ammi.
Kan DMD ya qulle ga su sweedy sun dame shi zasu zo Nigeria shi kuma baya jin zai iya komawa Canada ba tare da Ammi ba kuma baya jin zai iya bari su Muhseena su shigo Nigeria dan a yanzu ji yake ya qara tsanar Nigeria dan da Ammi na Canada ba mai taɓa ta balle sace ta.

Jay kallonsa yayi yace “dude kayi haquri mana dan Allah dubi fa yacce ka koma har dishewa kayi, addu’a ya kamata mu dage da shi ba damuwa a rai ba”. Lumshe ido yayi cikin yanayin damuwa ya buɗe baki kaman mai ciwon baki yace “Jay ba yanda na iya abun yamun yawa, da rashin Ammi zan ji ko da maganganun Abiy dan bana ta Hajja ita matsalar stufa gare ta na sani sannan ga su sweetie sun dage zasu zo Nigeria in su ma suka shigo aka sace mun su ya zanyi ai sai dai a ganni bushe a tsaye dan sune rayuwata”.
“Kayi haquri da lamarin Abiy ka san ba laifin sa bane duk aikin Aunty Amarya ne da zugi amma Abiy na son Ammi duk sonta ke sanya shi wannan hargagin”.
“hmmn! Jay kana son magana, Abiy a da ne yake son Ammi amma tun da ya auri wannan matar ya daina son Ammi tunda yana ganin ita ta haihu ta tsufa, ni babban damuwa na su sweetie”.
“To dude ka barsu suzo mana inyaso sai su zauna nan tare da Afreen ko ka kaisu Ashaka gidan Hajja tunda kasan tana son su sosai kuma suna shiri in sweetie ta ga Hajja nasan zata rage damuwanta” kallon Jay kawai yayi ya girgiza kai yace “Jay zuwansu ba zai yiwu ba bazan taɓa barin su suzo ba ko Abiy zai kashe ni ne duk da su yaransa ne”.

Abiy zaune a palourn sa yana waya wanda daga gani mai muhimmanci ne ganin yacce ya staya yana sauraro da kyau.
Aunty Amarya ce tayi sallama ta shigo palourn cikin shiganta na alfarman jikinta sai tashin qamshi yake, gefen Abiy ta zauna ta kwantar da kanta a kafaɗan sa har ya gama wayan kamun ya dube ta yace “sweetheart irin wannan qamshi da kyau ɗin haka”.
Murmushi ta masa tace “baby duk wa kai dan nustuwarka da farinciki ka” ta faɗa tana masa fari da ido, Abiy susucewa yayi yana faɗi a ransa “gwanda da abun ya tsaya iya kan Maimuna kar ya taɓa mun Amarya tunda dai ta zaɓi yaranta a kaina farinciki na bai dame ta ba” yana murmushi ya kalli Aunty Amarya zai yi magana sai qira ya shigo wayan sa “baby ana qiranka ba na ɗauko ma” faɗin Aunty Amarya cikin kissa, Abiy riqeta yayi yana guntun tsaki yace “sweetheart qyale mai qiran kawai baqin ciki ake mun da son yanke mun jin daɗi”.
Murmushi tayi ta zille ta miqe ta ɗauko wayan tana cewa “lah-lah baby Hajja ke qiranka fa lallai ka faɗawa Hajja magana” ta faɗa tana rufe baki ta miqa masa wayan.
Amsan wayan yayi yana murmushi yace “ai na ɗauka ko maganan maimuna ne” fakan idonsa tayi bayan ya ɗau wayan tayi murmushi a ranta tace “ni bansan inda ta shige ba amma addu’a nake gaba-gaba harrr kar ta dawo ta barmun mijina” a fuska kuma ta ɗan ɓata fuska taqi komawa jikinsa.

“Assalamualaikum Hajja an tashi lafiya? Ya gidan ya Afrah?

“Duk muna lafiya Alhamdulillahi Mustapha, ya yayanka da yaranku ya labarin maimuna?

“Uhmñ Hajja har yanzu dai shiru ba labari sai kan bincike ake”.

“To Allah Ubangiji ya bayyana ta, yarannaka fa?

“Hajja suna can Canada shi kuma yayansu yana nan gidan yaya Nura suna tare da jabeer”.

“Ashe Mustapha baka da hankali? Dan lalacewa da rashin imani sai ka bar yaran mata har su uku gatsal-gatsal a qasar turawa su kaɗai to maza-maza kayi gaggawan ɗauko su ka kaiwa Rabi’atu su in kuma ba zata iya ba ka kawo mun su nan na riqe su kamun Allah ya bayyanar da uwar tasu”.

“Hajja ba naqi ɗauko su bane yaron nan ne ya dage ba zasu zo Nigeria ba”.

“Mustapha nace ubanka kai da yaron naka, jimun shashanci kana ubansa sai ya faɗa maka abinda za kayi, wai shi ya haifa maka su ko kai ka haifi kayanka? Duba banason rashin hankali ka wuce kaje da kanka ka ɗauko yaran nan in ba haka ba ni da kai ne tunda kai kana storon ɗan cikinka ni ba storon ka nake ba balle ɗan da ka haifa, banson rashin mutunci da rashin tausayi”.

“Kiyi haquri Hajja in Allah ya yarda a cikin satin nan zanje na ɗauko su”.

“Mustapha ince ka ɗauko yara da gaggawa sai kace mun cikin satin nan? To nabi satin da gudu in kayi wasa yanzun nan zaka tafi wallahi ai kaji na ranste ba?

“Eh kiyi haquri Hajja Insha Allahu zanje jibi dan gobe akwai wani abun da zamuje dubawa tare da governor game da mahaifiyar su”.

“Mustapha kaji na ranste ba to wallahi gobe-goben nan karka yarda mangariba yayi ba tare da yaran nan suna cikin Gombe a gidan ubansu ba sha-sha-sha kawai ba, ni zaka faɗawa wani gomna ba gomna ba ubansa shugaban qasa karka kuskura na jefo qafana a cikin Gombe dan haɗuwanmu ba zata maka daɗi ba, fatan kana ji na?

“Eh Hajja ina ji Allah huci zuciyanki in Allah ya yarda goben zan ɗauko su”

“To yafi kam Allah muku albarka duka ya bayyana uwar su, ina ita Rabi’atun?

“Gatanan Hajja ba na miqa mata wayan”.

Abiy ya miqawa aunty Amarya waya ta kara a kunne tana sallama.
“Assalamualaikum Hajja anwuni lafiya?

“Lafiya Alhmdlh ƴar nan fatan kuma kuna lafiya? Ya kuma fargaba ya haquri?

“Alhamdulillahi Hajja”.

“To Masha Allah, za’a kawo miki yaranku sai ayi ta haquri da yara ko kinsan yaro sai a hankali…. ata haquri kamun Allah ya bayyana uwar ta su”.

“Lah…. Ba komai Hajja ai shi ɗa na kowa ne fatanmu Allah ya bayyana ta lafiya”.

“Ameen… Ameen Rabi’atu Allah miki albarka ya qara miki haquri kema in da rabon to Allah baki yara masu albarka, kici gaba da zama zuciyanki fari karki damu ko kaɗan da kowa kinji?

“Insha Allah Hajja, Allah qara girma ya qara lafiya”.

“Ameen ƴar nan”.
Kashe wayan Hajja tayi daga ɓangaren ta sai Aunty Amarya ta ajiye wayan ta juyo tana fuskantar Abiy tace “baby kaje ka ɗauko su yanda Hajja ta buqata inson samu ne ma ka tafi yau in yaso zuwa gobe sai ku dawo da wuri”.

Kallon ta Abiy yayi yace “sweetheart to ko zaki raka ni? Kinsan ba zan jure kwana bakya tare da ni in ba kamawa yayi ba”.

Murmushi ta masa tace “wannan ma kamawa tayi baby, Allah kaika lafiya ya dawo da ku lafiya dama nayi missing na yara na kaga zan gansu kamun Amminsu ta dawo ta qwace abunta, Nima dai Allah ya bani” tayi maganan idonta cike da qwalla har da sheshsheqa na kissa.

Abiy rungumeta yayi yana rarrashinta da maganganu masu daɗi.

Aunty Amarya ta taya Abiy shiryawa har airport ta raka sa bayan jirginsu ya tashi driver ya juyo da ita gida, tana shiga tayi jefi da mayafinta kan kujera tana huci tace “wannan stohuwa da kini-bibin stiya take dan Allah in ba kini-bibi ba kana zaune lafiya da mijinka ace za’a ɗibo ƴaƴan kishiya a kawo maka in ba cin fiska da son takurawa ɗan Adam ba, amma ba komai su da kansu zasu nemi komawa inda suka fito ko kuma duk suji a jikinsu ƴan iskan yara masu kama da aljanu ai wallahi ba don yayansu ba sai na kashe su duk na huta miji ya mutu dukiya tawa na fancama iya son raina” qaramin tsaki taja bayan ta gama zancenta ita ɗaya sai ta tashi ta shige ɗakin ta..

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

𝗙𝗮𝗻’𝘀, 𝗻𝗶 𝗨𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝗯𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗸𝗮𝗹𝗮𝗺𝗮𝗻 𝗱𝗮 𝘇𝗮𝘀𝘂 𝘄𝗮𝗱𝗮𝘁𝗮𝗿 𝘄𝗮𝗷𝗮𝗻 𝗯𝗮𝗸𝘂 𝗵𝗮𝗾𝘂𝗿𝗶, 𝗮𝗯𝘂𝗻 𝘆𝗮𝗳𝗶 𝗾𝗮𝗿𝗳𝗶𝗻 𝗮 𝗾𝗶𝗿𝗮 𝘀𝗮 𝗸𝘄𝗮𝗻𝗮 𝟮 𝘀𝗮𝗶 𝗱𝗮𝗶 𝘀𝗮𝘁𝗶 𝟮, 𝗸𝘂𝗻𝗷𝗶 𝗻𝗶 𝘀𝗵𝗶𝗿𝘂 𝗻𝗲 𝗯𝗶𝘀𝗮 𝗱𝗮𝗹𝗶𝗹𝗮𝗶 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝘄𝗮 𝗶𝗻𝗮 𝗳𝗮𝘁𝗮𝗻 𝘇𝗮 𝗸𝘂 𝗺𝗶𝗻 𝘂𝘇𝘂𝗿𝗶 𝗱𝗮 𝗮𝗳𝘂𝘄𝗮 𝗸𝗮𝗺𝗮𝗻 𝗸𝗼 𝘆𝗮𝘂𝘀𝗵𝗲, 𝘁𝗮𝗯𝗯𝗮𝘀 𝗜𝗡𝗡𝗔𝗜 𝘁𝗮𝘆𝗶 𝗸𝗲𝘄𝗮𝗻𝗸𝘂 𝗳𝗶𝗻 𝘆𝗮𝗰𝗰𝗲 𝗸𝘂 𝗸𝗮 𝘆𝗶 𝗸𝗲𝘄𝗮𝗻𝘁𝗮.
𝗠𝗮𝘀𝘂 𝗻𝗲𝗺𝗮 𝗻𝗮, 𝗾𝗶𝗿𝗮 𝗱𝗮 𝗺𝗲𝘀𝘀𝗮𝗴𝗲𝘀 𝗱𝘂𝗸 𝗻𝗮 𝗴𝗮𝗻𝗶 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗻𝗮𝗴𝗼𝗱𝗲, 𝘄𝗮’𝗱𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗯𝗮𝘀𝘂 𝗴𝗮 𝗿𝗲𝗽𝗹𝘆 𝗻𝗮𝘄𝗮 𝗯𝗮 𝗸𝘂𝘆𝗶 𝗵𝗮𝗾𝘂𝗿𝗶 𝗶𝗻 𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵 𝘆𝗮 𝘆𝗮𝗿𝗱𝗮 𝗱𝘂𝗸 𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘇𝗮𝘁𝗮 𝗮𝗺𝘀𝗮 𝗺𝘂𝗸𝘂.

𝘞𝘢𝘯𝘯𝘢𝘯 𝘱𝘢𝘨𝘦 ‘𝘥𝘪𝘯 𝘯𝘢𝘬𝘶 𝘯𝘦 𝘑𝘈𝘏𝘐𝘓𝘊𝘐 𝘒𝘖 𝘈𝘓’𝘈𝘋𝘈𝘏? 𝘍𝘈𝘕’𝘚 𝘊𝘓𝘜𝘉
𝘒𝘺𝘢𝘶𝘵𝘢 𝘨𝘢𝘳𝘦 𝘬𝘶
𝘛𝘶𝘬𝘶𝘪𝘤𝘪 𝘨𝘢𝘳𝘦 𝘬𝘶
𝘠𝘢𝘣𝘢𝘸𝘢 𝘨𝘢𝘳𝘦 𝘬𝘶
𝘚𝘰𝘺𝘢𝘺𝘺𝘢 𝘨𝘢𝘳𝘦 𝘬𝘶
𝘑𝘪𝘯𝘫𝘪𝘯𝘢 𝘨𝘢𝘳𝘦 𝘬𝘶
𝘎𝘰𝘥𝘪𝘺𝘢 𝘨𝘢𝘳𝘦 𝘬𝘶
𝘒𝘶𝘺𝘪 𝘺𝘢𝘯𝘥𝘢 𝘬𝘶𝘬𝘦 𝘴𝘰 𝘥𝘢 𝘴𝘩𝘪 𝘥𝘢𝘨𝘢 𝘵𝘢𝘬𝘶 𝘢𝘬𝘰 𝘺𝘢𝘶𝘴𝘩𝘦 𝘜𝘸𝘢𝘳 𝘉𝘢𝘵𝘰𝘰𝘭𝘦𝘳𝘩.

𝘓𝘈𝘍𝘈𝘡𝘐 𝘞𝘙𝘐𝘛𝘌𝘙’𝘚 𝘈𝘚𝘚𝘖𝘊𝘐𝘈𝘛𝘐𝘖𝘕 shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 𝘠𝘌𝘈𝘙’𝘚 𝘈𝘕𝘕𝘐𝘝𝘌𝘙𝘚𝘈𝘙𝘠.

𝘑𝘈𝘏𝘐𝘓𝘊𝘐 𝘒𝘖 𝘈𝘓’𝘈𝘋𝘈𝘏? 𝘍𝘈𝘕’𝘚 𝘊𝘓𝘜𝘉 🤝💙one lurv masu daraja habibties, Uwar batoorl na matuqar qamnar ku da sharhinku da soyayyan ku ga wannan littafi.
Dama waɗanda basa group ɗin amma suna sharhi to tabbas Uwar batoorl 𝘯a soyayyan ku🤝

𝘍𝘈𝘕’𝘚 𝗚𝗔 𝗦𝗔𝗤𝗢𝗡 𝗨𝗪𝗔𝗥 𝗕𝗔𝗧𝗢𝗢𝗥𝗟 𝗭𝗨𝗪𝗔 𝗚𝗔𝗥𝗘 𝗞𝗨 𝗔 𝗞𝗢 𝗗𝗔 𝗬𝗔𝗨𝗦𝗛𝗘.

𝘚𝘖 𝘚𝘖 𝘕𝘌 𝘈𝘔𝘔𝘈 𝘚𝘖𝘕 𝘒𝘈𝘐 𝘚𝘏𝘐𝘕𝘌 𝘈𝘚𝘈𝘓𝘐𝘕 SO🤙 𝘛𝘖 𝘛𝘈𝘉𝘉𝘈𝘚 𝘕𝘐 𝘏𝘈𝘙𝘌𝘌𝘠 𝘈𝘚𝘈𝘓𝘐𝘕 𝘚𝘖 𝘕𝘈𝘒𝘌 𝘔𝘜𝘒𝘜, 𝘒𝘜 𝘏𝘜𝘛𝘈 𝘒𝘜𝘑𝘐 𝘋𝘈’𝘋𝘐𝘕𝘒𝘜.
𝗜𝗡𝗔 𝗬𝗜𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

💋💋 امى بتولة💋

 

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 23_24

Abiy ya isa Canada inda ya shiga taxi ya kai sa gidan yaronsa.
Mai taxi na horn gate man ya leqo ganin Abiy sai ya buɗe suka shigo Abiy ya sallami mai taxi da kuɗin qasar mai yawa, suka gaisa da gate man sannan ya shige cikin gidan.
A main palour ya samu sweedy na aikin rarrashin sweetie rigimanmiya. Ganin Abiy da gudu sweetie ta taso ta rungumesa tana sakin kuka cikin turanci take magana “Abiy ina Ammi na?

Shafa kanta Abiy yayi ya ɗagata sama suka qarisa cikin palourn ya samu kujera ya zauna, sweedy na masa sannu da zuwa cikin turanci, kallon sweetie yayi yace “Muheebbahn Abiy Ammin ki na gida yanzu ma nazo na ɗauke ki na kai ki wajan Ammin ki ne, amma kinsan me?

Girgiza kai sweetie tayi tana murmushi, jan kumatun ta Abiy yayi yace “good girl Muheebbahn Abiy sweetien Ammi, ina so kar wanda ya ɗau qiran yayanku ko da ya qira ku karku ɗauka inaso mu masa surprise shi da Ammi”.

Cikin gamsuwa da batun Abiy sweetie ta rungumesa ta masa peck a kumatu itama sweedy rungumesa tayi ta masa peck ɗin dan sun yarda da Abiyn su.

Sweerie ke sauqowa a benen da zai sada ka da ɓangaren su tana magana cikin harshen turanci “sweedy me kika bawa rigimanmiyan Ammi tayi shir… Maganan bakinta ne ya maqale ganin Abiy zaune a palourn, da mugun gudu ta gangaro ko takalmin hill’s da ta saka bata damu da shi ba tana isowa ta faɗa jikin Abiy tana cewa “Abiy surprise! sannu da zuwa”.

Rungume ta Abiy yayi ya mata peck a goshinta yace “Munawwaran Abiy ya school?

“School lafiya ba daɗi Abiy dan ma an bamu hutu”.

“Yauwá good dai-dai kenan kunga sai mu tafi Nigeria tare wajan Ammi”.

Waro ido tayi tace “Abiy! Darling fa ya hanamu yace kar ya kama qafanmu a Nigeria har sai sun dawo tare da Ammi in ba haka ba zai saɓa mana”.

“Wasa yake muku sweerie, yanzu zamu tafi gobe da wuri in Allah ya yarda amma kar ku faɗa masa muma mu masa surprise”.

Ɗaga kafaɗa tayi tace “shikkenan Abiy Allah ya kaimu amma tunda kazo Abiy ka kaimu yawo”.

Murmushi Abiy yayi yace “duk kuje ku shirya ba na wasta ruwa mu tafi”.

Sweerie tace “ni dai a shirye nake Auta da sweedy ne zasu shirya”.

Abeeyh sama ya haura, ɗakin da yake mallakin sa a gidan ya shiga ya wasta ruwa ya sanja kaya.
Qananun kaya yasa inka gansa ba zaka ce ya haifi DMD ba dan kaman matashi haka ya koma kayan ya amshe sa kuma Abiy ba dai kyau ba dan kusan a wajan sa yaran suka ɗauko rabin kyawun su.

Suka fita Abiy ya kaisu Park ne restaurant ne etc yawo suka dinga yi sune basu dawo gida ba sai bayan isha’i, suna dawowa kowa ta shiga ɗakinta sweetie kuma tabi Abiy dan ta dage a wajansa zata kwana.
Sallolin su suka yi kamun kowa yabi lafiyar gado ya kwanta tunda Abiy yace musu gobe da wuri jirginsu zai tashi.

 

𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚’𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 – 250 𝟏𝐆𝐁 – 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 500
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 750

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎……

 

⭐⭐

“Wai me yasa ba zaka ci abinci ba son? Ko bai maka ba ne na dafo maka da kaina” cewar mummy da idanuwanta ke kan DMD.

Shafa kansa yayi mai cike da baqin gashinsa mai stayi yace “habibty na qoshi ne fa”.

“Ka qoshi me kaci?

“Uhmn ɗazu munje gidan Abiy to na ci a can”.

Mummy kallonsa take da mamaki domin kuwa qaryan ma bai amshe sa ba tunda kowa yasan ba shiri yake da matar Abiy ba balle yaci abincin ta, kallon Jay tayi tace “jabeer kunje gidan Abiyn naku?

Jay sosa qeya yayi yana kallon DMD dake lumshe masa ido alaman yace eh, hararan sa yayi kamun yace wa mummy “eh Habibty munje”.

“Shikkenan to” mummy ta faɗa a taqaice suka ci gaba da cin abincin wanda a qarshe shikam miqewa yayi ya haura sama.

Bayan Jay ya gama cin abinci ya tashi yana sunne kai dan yasan mummy ta san qarya suka mata, ya haura saman shi ɗin ma. Yana shiga ɗakin ya tarar da DMD na ta aikin jan tsaki sai ya kalle sa yace “ka sa ni yiwa habibty qarya kai kuma kazo nan kana aikin tsaki kaman tsaka kai da waye?

Hararansa yayi yace “ni inba dalili ba har banson zuwa Nigeria kuma kai ma har da kai a masu hanani, surutu kaman parrot, ni da rabuwa da ciwon kai nasan sai nabar qasar nan”.

Jay ya taɓe baki yace “tunda ance maka bansan hanyan Canada ba dole kace haka, yanzu dai me kake wa staki?

“Layin sweedy nake ta qira baya shiga duka layukansu a gidan baya shiga na driver na kuma ba’a ɗauka, so bansan ko lafiya ba”.

“To ka bari zuwa safiya mugani amma nasan Insha Allahu lafiya lau ne”.

DMD tashuwa yayi ya fita a ɗakin ya tafi nasa dan shi baya iya kwana da wani a ɗaki ɗaya balle gado ɗaya in ba sweetie ba.
Yana shiga yayi shirin kwanciya ya kwanta dan so yake ya tashi da wuri ya samu yayi nafila anjuma.

Abiy da sassafe ya sako su a gaba suka dawo Nigeria inda qarfe sha biyu ya same su a cikin garin Gombe.
Da sallama ya shigo palourn riqe da hannun sweetie, Aunty Amarya na murmushi ta fito sashin ta tana musu sannu ta ɗaga sweetie tana cewa “my baby girl nayi kewanku”.

Sweetie dai taqi sake fiska dan damuwan ta taga Ammi.

Sweedy suka yi hugging Aunty Amarya ta musu peck a goshi tana cewa “babies nawa nayi kewanku”
Duk murmushi suka sakar mata taja hannun su har sashin ta, tasa mai aiki ta kawo musu komai suka ci tare da Abiy suka gama.

Sweetie ta kallesa tace “Abiy ina Ammi fa?
Murmushi ya mata yace “ku kwantar da hankalinku Ammi na Ashaka gidan Hajja jibi zata dawo okay”.

Sweedy da sweerie miqewa suka yi zasu fice a sashin sai Aunty Amarya ta kallesu cike da kirsa tace “babies na ba zamu zauna anan kamun Ammi ta dawo ba?

Kamun su buɗe baki yin magana Abba ya rigasu yana washe baki yace “a’a ki qyale su suje can su huta, Muhseenan Abiy kuje sashin Amminku ku huta ko”.

Qarisa ficewa suka yi ba tare da sunce komai ba, sweetie ta kalli Aunty Amarya ta harare ta sannan ta kalli Abiy tana tura baki tace “ni dai Abiy da kai zan zauna har sai Ammi ta dawo”

Abiy ba yanda ya iya da rigiman sweetie dan sun sakalta ta daga shi har Amminta da yayyunta dan haka dolen sa ya mata murmushi yace “sosai ma Muheebbahn Abiy gaki ga Abiyn ki har Ammi ta dawo my ƴar lukutan yarinya ta”

Tura baki tayi tace “Abiy bana so”.

Aunty Amarya dake zaune ta cika tayi fam ji take kaman ta rufe ta da duka amma sai murmushin yaqe take musu a ranta kuwa ayyana abinda za tawa Muheebbah in Abiy ya fita take “sweetie a wajan Aunty zaki zauna ma ba Abiy ba”.

“A’a ni dai wajan Abiy na tunda banga Darling ba halan shima yana tare da Ammi” ta faɗa tana shagwaɓe fuska.

“Karki damu Muheebbahn Abiy kina wajan Abiyn ki ko!
Sai sweetie ta gyaɗa kai alamun “eh”.

Aunty Amarya murmushin yaqe kawai take amma ji take kaman ta kamata ta cinye ta ɗanya dan tasan yarinyar da shegen sakalci yanzu ko ina Abiy zai je zata ce zata bi sa in dai ta bari yayi nesa da ita to sai in zai shiga banɗaki, shiyasa bata son suzo kuma ta gwammace yayyun ta suzo akan ita tazo gwanda ma in da Ammi ta zo.

DMD sakamakon nafilfilun da yayi tun da ya dawo sallahn asuba ya kwanta shine bai tashi ba sai wajen qarfe sha-ɗaya 11, yana ganin time da mugun sauri ya sauqa a kan gadon sannan ya shige bayi wasta ruwa yayi ya fito ya shirya sama-sama ya leqa ɗakin Jay bai gansa ba sai ya sauqo palour nan ma bai tarar da kowa ba, hanyan ɗakin mummy yayi yana isa yayi sallama aka masa izinin shiga ya shiga ya tarar da ita tana gyara ɗakin nata sai ya stugunna ya gaishe ta yana cewa “habibty kawo na gyara miki”.

Murmushi tayi tace “aikam son ni sheda ce yanda kake gyarawa Ammi ɗaki yayi kyau ɗin na amma dai na hutar da kai zauna abinka na gama ma”.

Zama yayi a bakin gado yace “habibty Jay fa ban gansa ba kuma na qira layinsa bai shiga ba”.

“Yanzu dama bai faɗa maka ba, ɗazu Afreen ta dawo kuma sun tafi Ashaka dan kana bacci ne ma dama Daddyn ku yace aje da kai dan tun ba yau ba yake binsu suje”.

Taɓe baki yayi yace “Alhamdulillahi ina bacci ma suka tafi dan ba inda za ni, yanda halin stohuwar nan yake haka halin Abiy yake ina zuwa za tabi ta isheni da surutu tana zagin baiwar Allah bata ji ba bata gani ba”.

“Allah shirya ka son, mahaifiyar mu ce ke masifa ko?

Shiru yayi bai ce komi ba ya miqe yana cewa “habibty ban karya ba” ya qarisa ficewa.

Tashuwa mummy tayi ta biyo bayansa ta same har ya shiga kitchen da mamaki take kallon sa tace “son ba dai girkin za kayi da kanka ba?

“Eh Habibty yanzu zan gama inaso na fita da wuri naje masallaci akan lokaci na bada abun sadaka a tayamu da addu’a”.

“Oh to shikkenan, amma je ka zauna zan dafa maka me kake so?

“Habibty Allah ki huta indomie ne yanzu-yanzu zan gama nazo muci sai na tafi”.

Mummy tayi-tayi amma yaqi bari ta dafa masa, haka ta haqura ta koma palourn ta zauna tana jiransa.
Indomie ya dafa sai ya soya qwai ya juye duka a plate ya kashe gas ɗin ya fito, a kujera ya samu mummy na zaune, sai ya jawo center table ya ajiye plate ɗin yaje fridge ya ɗauko wa mummy abun sha ya ɗauko nasa.
Mummy tana 1 spoon ta kalle sa tace “son wai kai ka dafa?
Yana murmushi yace “eh habibty ai har rice na iya dafawa”

“Eh lallai in-law tamu ta huta wannan iya girki kace in kana amarci na ɗan 1 month da ake kai abinci ka hutar da mu zaka dinga muku, indomie har da hanta da kifi ga cabbage ni Maryam ina na taɓa gani gwanda in Afreen ta dafa nakan ga tasa hanta wani lokacin amma bansan ana sa wannan duka ba”

Murmushi yayi yace “habibty ki staya santi zan cinye ne yanzun nan”.

Suka gama ci ya tattare komai ya kai kitchen ya dawo palourn suka ɗan taɓa hira kamun ya mata sallama zai je gidan Abiy, mummy ta masa a dawo lafiya.

Yana fita yasa driver ya kai shi gidan Abiy, suna isa ya sallami drivern ya dawo dan dama so yake yazo ya ɗau motan sa dama da na Jay suke yawo kuma ya tafi Ashaka.

Ba tare da yayi knocking ba ya tura qofan palourn ya shiga dan Sallaman ma a ciki-ciki yayi shi.
Hanyan da zai sada shi da sashin sa ya nufa sai kaman ance juyo ya kalli qofan sashin Ammi a buɗe, da mamaki yake kallo yasan dai Ammi ke da key sai Abiy kuma shigowansa bai ga motan Abiy ba dan shiyasa ma ya shigo da qarfin guiwansa don baison abinda zai sa ya haɗa hanya da Abiy gudun kar a samu mastala.

Sharewa yayi ya wuce sashin sa ya bari akan ko Abiy ya sa a gyara sashin ne tunda dama ko bata nan ana mata shara.

Yana shiga ya kullo qofan sa, kallo ya qarewa sashin nasa ganin duk qura alaman anjuma ba’a shigo ba.
Kwaɓe fiska yayi yace “yanzu da Ammi na nan nasan da an gyaramun tunda ita kam na bata key na kuma na hana kowa shigowa in ba ita ba, da ace ma Ammi nanan me zai kawo ni wannan trouble Nigerian rashin Ammi ya kawo ni, Allah ya bayyana ta mu koma”.
Duba time yayi ganin har 12 yayi sai ya ɗauko mooper da abun shara sama-sama ya gyara palourn nasa ya wuce cikin ɗakin sa ya share ya gyara shima da kyau ya shiga banɗaki ya wanke tass, shine bai gama aikin ba har qarfe ɗaya da rabi 1:30 sannan ya cire kayan jikin sa ya ɗaura towel ya shige toilet.
Yana gama wanka ya fito ya je gaban dressing mirror ya shafa mayukan sa ya shafawa kansa ya taje ya taje gemun sa duba lokaci yayi yaga qarfe biyu saura sai ya wuce ya ɗauko manyan kaya wata dakakkiyar jamfa milk color ya saka ya ɗau hula ya kafa.
Masha Allah! Manyan kaya ba qaramin kyau suke masa ba wanda shima kanshi ya sani kawai yanayin rayuwan outside ne da kuma shima bai dame sa ba yafi son qananan kaya.
Ya gama shirin sa da komai qarfe biyu ciff 2:00pm ya feshe jikin sa da turarukan sa iri da kala wanda sanyin qamshin su da daɗin su har hawa kai suke ga kuma sanya nistuwa ga mai shaqan su.

Sweerie na zaune a palourn Ammi sai taga kaman giftawan mutum yayi hanyan sashin yayansu, kamun ta fito kuma ba taga kowa ba taje jikin qofan ta murɗa handle nan ma taji a kulle sai ta juya tana cewa may be idon ta ne kawai.

Aunty Amarya da fitowanta kenan a sashinta tun da taji an buɗe gate kuma ta ga shi ya shigo sai tayi sauri ta fito amma sai ta tarar sweerie ce kawai a palourn, qwafa tayi fuska a haɗe tace “Munawwara tashi kije kitchen ki taya mai aiki girki, ko so kuke mu aurar da ku a dawo mana da ku baku iya komai ba mun sakalta ku?

Sweerie kallon Aunty Amarya tayi kawai ta miqe ba tare da ta mata musu ba tayi hanyan kitchen dan dama ita girki bai dame ta ba ko a can Canada suna girkinsu Ammi ta hana masu aiki yin girki, sai share-share da sauran ayyukan.
Aunty Amarya cije leɓe tayi dan taso ace ta tanka mata ta koya mata hankali amma abun haushi yake bata ko tayi abu basa tanka mata balle ta samu daman ce wa sun mata reni dan yaran staff halin uwar su gare su na haquri da kawar da kai ba ruwan su, juyawa tayi cikin jin haushi ta koma ciki.
Sweerie sun gama girkin tare da mama mai musu aiki sai ta fara jidowa tana kawo wa dinning, ta ɗauko kulan qarshe me cike da ferfesun naman zabuwa(Abiy baya cin kaza) tana fitowa a kitchen kaman daga sama aka jefo sa ta kalli mutum a stakiyan palourn ya nufi waje sai kawai ta sake kulan hannun ta tace “Darling!!

Ɓangaren DMD fitowa yayi ya kulle sashin sa ya nufi hanyar fita har ya kusa qofan palourn ya jiyo qaran faɗuwan abu sai kuma yaji muryan sweerie na faɗin “Darling!
Juyowa yayi mamaki fal ransa yace “sweerie, ke kuma a Nigeria ke da wa?

Qarasowa tayi tace “Darling kayi kyau, Abiy ne yaje ya ɗauko mu sweedy na ciki sweetie kuma sun fita da Abiy ta bisa masallaci”.

Maimaita kalman “Abiy ne ya ɗauko mu” yayi sannan ya kalle ta ransa a matuqar ɓace yace “yaushe kuka zo?

“Ɗazu da safe muka zo, Darling wai kuna tare da Ammi ina take? Ko ka baro ta acan ne?

Kallon ta yayi kawai bai ce komai ba sai ya duba agogon hannun sa yaga ya kusa yin latti, cikin sauri yace “before na dawo ku tabbatar kun shirya” yana faɗa ya fice.

Ko ta kan kulan da ta yasar bata bi ba ta juya ta shige sashin Ammi tana qwala wa sweedy qira “sweedy! sweedy! sweedy!”

Fitowa tayi a ɗakin su tana cewa “irin wannan qira lafiya?

“Sweedy yanzu na ga Darling zai tafi masallaci”.
Da mamaki take kallon ta tace “Darling dai sweerie ba Abiy yace mana suna tare da Ammi ba?”

FAN’S KU RIQE GODIYAR KU, UWAR BATOORL SHARHI KAWAI TAKE BUQATA.

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR’S ANNIVERSARY

Ƙawalliya Dija k’aya ga naki page ɗin (Fulanin Royal Star) marubuciyar KAINUWA DASHEN ALLAH.

JAHILCI KO AL’ADAH? FAN’S CLUB 🤝💙one lurv masu daraja habibties, Uwar batoorl na matuqar qamnar ku da sharhinku da soyayyan ku ga wannan littafi.
Dama waɗanda basa group ɗin amma suna sharhi to tabbas Uwar batoorl na soyayyan ku🤝

 

FAN’S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

💋💋 امى بتولة💋

 

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 25_26

 

“Allah shi ne kuma nima naji mamaki na tambaye sa Ammi fa sai yace bari ya dawo daga masallaci zai yi latti”.

“To Allah dawo da shi lafiya dan na mastu na kalli Ammi”.

“Amma fa inaga shi kaɗai yazo dan yace mun mu shirya kamun ya dawo wataqilan zai kai mu wajan Ammin ne”.

Yana ficewa a gidan ya ɗauki motan sa qirar Toyota mai tinted glasses ya mata key sai babban masallacin juma’a na qofan Sarkin Gombe.

Yana zuwa Allah ya taimake shi ba’a fara salla ba nan ya samu ya lallaɓa har wajan liman da ya idar da khuɗuba suka gaisa cikin mutuntawa ya faɗa masa buqatan sa, nan limamin yace masa mahaifin sa ya jima da masa magana kuma suna kan addu’a, godiya yawa limamin sannan ya bada kuɗi a sayi abun sadaka 2million ya basa check dan dama tun a gida ya rubuta check ɗin.

Suna gama magana da liman ya koma wajan zaman sa ya zauna jiran a tada Salla yana danna counter (carbin qirge) zuciyansa cike da tunanin dama Abiy ya damu da ɓatan Ammi ne da har ya bada ayi addu’a? Inda gefe ɗaya kuma yaje cike da taqaicin zuwan su sweetie Nigeria.
Ajiyan zuciya ya sauqe jin ana qiran sallah sai ya miqe shima ana idar da Qiran kamun a tada iqama ya jero addu’oeen sa ya shafa aka tada sallah.

***
Manzon Allah SAW yace “ku kasance masu miqa addu’oeen ku ga mahaliccin ku Allah maɗaukakin Sarki a ko wanni lokaci sannan mafi soyuwar lokaci ita ce yayin da liman yake tada iqama na sallahn asuba da kuma ranar juma’a domin kuwa a ranar juma’a akwai wani lokaci wanda ke ɗauke da sa’a wanda duk wanda Allah ya nufa yayi addu’ansa a wannan lokacin ta sa’ar to ba hijabi tsakanin karɓuwan addu’an sa ga Allah”.

To sai malamai ke cewa wanne lokaci ne wanda Annabi stira da amincin Allah su tabbata a garesa ya ambata? Wasu daga cikin malamai ke cewa sa’ar na nan lokacin sallar asuba ta ranan juma’a, wasu kuma suce tana nan a lokacin da liman ke qiran sallah kamun kuɗuban farko wasu kuma suce kuɗuba na biyu wasu kuma suce yayin ta da iqaman sallahn juma’a.

Mu qwata wunin juma’ar mu da zikiri da ambaton Allah da kuma yawaita salati ga shugaban Annabawan Allah Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ♥️

WALLAHU A’ALAM.
***

Suna idar da Sallah, aka ɗaura aurarraki aka yi addu’a sannan liman ya roqi jama’a da a taya su da addu’a akan ɓatan wata baiwar Allah, nan aka kuma addu’a aka shafa.

Yana fitowa yayi ta aikin raba sadaka, dama halinsa ne kyauta duk ranan juma’a kuma yana sadakan kuɗi wani bin har da abun ci.
Yayi wa masu Dabino da Alewa juye kowa ya raba sadaka sannan ya shiga motan sa ya ja ya nufi anguwansu GRA.

Mama mai aiki tana fitowa kitchen tayi mummunan gani, dan a wajan ta wannan mummunan gani ne dan tulin jarabar da yau zata kwasa akan wannan aika-aikan, kulan ferfesun Abiy a yashe a qasa.
Cikin hanzari take qoqarin tattare wa kamun aunty amarya ta fito ta gani ta fara mata tijara, amma sai aka yi rashin sa’a tana cikin share wajan Aunty Amarya ta fito.
Kallon mama mai aiki tayi sama da qasa tace “me wannan ya zube?

Cikin in e na tace “ha…ha… Hajiya ayi haquri nima wa…wall….wallahi bansan da.. da wannan aiki ba sai yanzu na gani”.

Malalacin kallo ta wasta mata sama da qasa dan ko ba’a faɗa ba tasan ferfesun Abiy aka zubar kuma daga maganan mama mai aiki ta gane Munawwara ce ta zubar, dan haka rai a ɓace tana huci ta nufi sashin Ammi.
Ba sallama ta tura qofa ta shiga tana haqi tana huci kaman za taci babu, tana qwala wa sweerie qira “Keeeee! Keeeee! Munawwara”.

DMD da ya iso gidan ya buɗe qofan palourn kenan ya shigo sai yaga bayanta ta shige sashin Ammin sa kuma ta banko qofa, rai a ɓace ya buɗe qofan sashin ya shiga amma sai ya tsaya a bakin qofa yana qare mata kallo jin irin qiran da take wa sweerie kaman ita ta raɗa mata sunan, tsayawa yayi ganin iya gudun ruwanta.

Bata san da shigowan sa palourn ba ta ci-gaba da cewa “Munawwara! Munawwara! Keee Munawwara ba ke nake qira ba?

Cikin sauri Munawwara ta fito a ɗakin, sanye take cikin dogon riga wanda bai kama jikinta sosai ba bai kuma mata ruwa sosai ba, idanuwan ta akan Darling dake staye bakin qofa suka sauqa amma sai ya mata alama da kar ta nuna ta gansa.

Cikin qufula Aunty Amarya tace “ke dan uwarki ba ke nake qira ba kika yi banza da ni? Ina wasa da ke ne zaki zubar da abincin miji na dan nace kije ki taya ta girki wato gaki fistararriya ko? Tunda ba Uwarki ce ta sanya ki ba dole kimun ta’adi tunda buri kuke ubanku ya sake ni ya zauna da uwarku kawai kuna taya ta kishi ko?

“Kiyi haquri Aunty ba da sanina bane ya faɗi a hannuna kiyi haquri” Munawwara ta faɗa idanuwanta cike da ƙwalla sakamakon masifan Aunty Amarya, dan su basu saba da masifa ba balle stawa, Ammi bata musu Abiy ma haka Darling ma haka.

Tsabar masifa Aunty Amarya har qanqance ido take kaman zata rufe sweerie da duka, cewa tayi “Har zaki ce bada saninki ba dan uwarki” ɗaga hannu tayi zata sharara mata mari amma kamun hannunta ya kai ga sauqa sai taji an riqe hannunta an buge gefe, cikin taqaici ta juyo za tayi ashar amma ganin waye ne sai ta haɗiye zagin tace “kai har ka isa ka hanani hukunta yarinya tamun laifi ina matar ubanka ni sa’arka ce da zaka riqe hannuna?

Kallon sama da qasa ya mata ya watsar da kashin ta kamun ya juya ga sweerie yace cikin Indianci “dama bance ku shirya bane ko reni ne? Wuce ki qira sweedy ku fito yanzun nan” ya faɗa yana zama a kan ɗaya daga lumstuma-lunstuman kujerun palourn Ammi.

Cikin taqaicin rashin ida nufinta ta juyo ta kalle sa tace “ina maka magana ka maida ni mahaukaciya amma ai kasan nima uwarka ce b….” Wani kallon da ya mata ne ya sanya ta haɗiye maganan dake bakin ta tana ja baya dan ta storita ganin yanda lokaci guda ya sanja fiska da irin kallon da yake mata.

Yatsa ya nuna mata kaman wanda bakinsa ke ciwo yace “watch ur tongue” iya abinda ya faɗa kenan ya fidda wayansa yana lastawa.

Cikin stiron masifa da ke cinta da ayyana irin abinda zata faɗa wa Abiy ta fice a sashin fuuuuu ta banko qofa.

Guntun tsaki yaja “mstwwww! Idiot human being bansan shima me ya gani a wajan ya burge sa ya auro ta ba” ya faɗa yana taɓe baki.

Sweerie da sweedy suka fito yace musu “ina key ɗin Ammi?

Sweedy ne ta miqa masa ya karɓa ya sasu gaba suka fice yaja sashin ya rufe ya jefa key ɗin a aljihun sa suka fice a gidan.

Suna fitowa a palourn a compound na gidan suka ci karo da Abiy da sweetie sun dawo hannunta da ledodi alaman siyayya ya mata.

Sweetie da gudu tayi wajan Darling ta rungume sa tana cewa “Darling ina ka baro Ammi” kallon ta yayi kawai ya kau da kai ya juya dan zuwa yanzu ya fahimci me Abiy ya faɗa musu ba sai ya tambaya ba.

Abiy ganin ko kallon sa be yi ba sai ya kai kallonsa kan su sweedy yace “Munawwara where are you going?

” Darling ne yace mu shirya ya kaimu mu gaishe da mummy” qarya ta sharara masa dan ita ma bata san ina zasu ba kawai ta faɗawa Abiy hakan ne.

“To ku dawo lafiya ku gaida mummynku” Abiy ya faɗa yana shigewa cikin gida.

Dukansu ɗuruwa suka yi seat na baya, har ya sawa mota key sai ya fasa tayarwa da Indianci yace “waye drivern ku?
Ba shiri sweetie da ke gwalalo ido ta fito dan tasan ko yaushe ita ce da zaman gaba, yanzun ma dan taga ransa a ɓace shiyasa ta storita ta shige baya.

Qwafa yayi yaja motan suka fice a gidan sai Tunfure.

A bakin gate yayi parking dan sharp-sharp yake so su gama su fito, cikin gidan suka shiga suka tarar mummy na saving Daddy da abinci.
Da gudu sweetie tayi wajan Daddy ta rungumesa, yana murmushi yace “manyan mata yaushe a gari?

Sweetie na dariya na farincikin ganin Daddyn ta washe baki tace “Daddy yau da sassafe”.

Mummy na murmushi ta rungume su sweedy tana tambayansu wa ya kawo su?
Sweedy tace “Habibty Abiy ne ya kawo mu”

“Masha Allah Abiy ya kyauta sannunku da hanya”

Daddy sai biyewa sweetie yake, ta ɗau cokalinta suna cin abincin da aka saka masa tare.
Sweedy ma mummy ta saka mata ita kuwa sweerie tace ta qoshi dan ta gama cika cikinta a kitchen da ta taya Mama mai aiki girki.
DMD ma yace ya qoshi, sanin hali ya fi sanin kama dan haka mummy bata masta masa ba mutumin da kaman bai da halittan ƴaƴan hanji a cikin staɓar rashin son cin abinci kuma Allah ya taimake sa ulcer bata kama sa ba.

Sanda suka gama cin abincin suka ɗan huta dan sunyi awa a gidan kamun ya duba lokaci ganin yamma na yi ya dube su yace “maza ku tashi mu tafi”.

Daddy ne ya kalle sa yace “har za ku koma gida son? Ni na ɗauka kwana za suyi kuma ai ko ba kwana ba ka barsu sai zuwa dare ko?

Kaman baison yin magana yace “Daddy ba gidan Abiy za mu tafi ba kar dare ta mana a hanya”.

“To ina zaka kaisu son? Cewar mummy da idanuwanta ke kansa.

“Habibty Ashaka zan kai su kuma a yau nake so na dawo”.

“Ashaka dai son? Shi Mustaphan ne yace ka kai su ko kuma me daga zuwan yara basu huta ba ka sanya su a hanya”.

“Daddy gidan Abiy ne sai a hankali kasan abinda ya ajiye a gidan”.

Mummy tace “duk da haka dai son bai kamata ba shi mahaifinku ne kuma gidansa naku ne ba matar da zata sanya hijabi tsakaninku da abinda yake mallakin ku, ka dinga haƙuri don dama mu mata sai a hankali”.

Shiru yayi bai ce komai ba sai Daddy yace “shikkenan son na fahimce ka ku dawo lafiya amma ka kasance mai haquri da kuma biyayya ga iyaye kai ne babba abinda kayi shi suma qannenka za su gani su bi”.

Sallama suka wa su Daddy ya sa qannensa a gaba suka fice, suna shiga motan yaja da mugun gudu dan so yake ya kaisu ya dawo da wuri ɗaga waya yayi ya qira layin Jay.

 

𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚’𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 – 250 𝟏𝐆𝐁 – 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 500
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 750

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎……

 

Jay na ficewa a gidan Hajja ya ciro waya yayi dialing layin abokinsa da yayi saving da “Farooq” qiran na bugu ɗaya aka ɗauka.

“Hello freind yau kayi mafarki nane?

Jay dariya yayi jin abinda abokin nasa ya faɗa sai yace “kaman kuwa ka sani, yanzu dai kana ina?

“Ina gida”

“So na shigo Ashaka ne mun kwatancen inda kake nazo dan nasan gida na bajoga”

“Okay ba kasan best way international school na nan cikin Ashaka ba?

“Yeah! Na sani”

“Okay in ka shigo makarantar ka qira ni”

Jay yace “okay freind” sannan ya kashe wayan ya juya kan motan sa yayi hanyan makarantan su Afrah.

Yana isa yayi dialing layin abokinsa ya faɗa masa ya iso ya kashe wayan, yana tsaye ba jinawa sai gashi ya iso yana murmushi ya miqa masa hannu suka tafa yace “freind ashe ka shigo Ashaka shiyasa ka qira ni, amma wa ya gaya maka ina Ashaka”

“Munyi magana da Waleed ne yake faɗamun kazo service Ashaka to banma san a nan makarantan kake ba ai da na baka aikin yi domin anan Auta ke karatu kuma bata ji”

Quarter’s suka qarisa, Farooq ya buɗe qofan ɗakin sa, room and palour ne sai kitchen, ko ina a share fes-fes gwanin sha’awa, suka qarisa shiga yana cewa “dama anan Auta take karatu kenan? Amma wani class take?

Jay taɓe baki yayi yace “kaman dai a Jss 1 take ne ko SS 1 tsakanin biyun dai”

“Ai kuwa in SS 1 take to a ajina take dan yanzu presently ni ne form-mastern su, amma me sunan ta?

Hararansa Jay yayi yace “za kace baka san sunan Hajja Afrah take da shi ba ko kuwa sunan Daddy ne baka sani ba?

Farooq na dariya yace “sorry freind na tuna FATIMA NURA right? Amma ba mai sunan sai dai wata me suna FATIMA NURA MUHAMMAD”.

“ɗan renin hankali ita ce to tunda baka san tana aiki da sunan Alhaji ba”.

“Ai kuwa sai yanzu ma ta faɗo mun kasan ba cika kallon students nake ba yanzu ɗalibai renine da su in ka sake kaɗan su renaka wasu suce suna sonka wasu kuma su maka sharri a wajan qawayensu akan kace kana sonsu alhali ba haka bane”.

Murmushi Jay yayi yace “kai dai faɗa gaskiya kasan dai na sani wannan AL’ADA ce ta malamai soyayya da ɗalibansu to kai faɗamun akwai wacce ta maka a students naka?

Farooq hararan Jay yayi yace “taɓɓ JAHILCI KO AL’ADAH? Kana Malami kayi soyayya da ɗalibar ka ba dai AL’ADA ba sai dai ko JAHILCI dan reni ne zalla gwanda ma in ɗalibai suka gama ka bi yarinya har gida in ta maka, thought akwai wacce suke zama da ita Afrah a class ina tunanin qawarta ce yarinyar nistuwan ta da hazaqanta na burge ni amma ba ina nufin wani abu ba dan duk ajin qwailaye ne irin nata ma yayi muni don ko Afrah ta fita cika ido”.

Dariya Jay ya saka har da kama ciki yace “kaji ɗan iskan malami ba, wai qwailaye wato ido kake sawa ɗaliban ka?

Hararansa Farooq yayi yace “in nasa musu ido in kalli me? Ko ita ma wannan yarinyar ba wai sonta nake ba dan karkaji nayi magananta, ni ba ruwa na da soyayya da ɗaliba dan malamai masu irin haka ke ɓata ma saura suna, kaga malami yana bin ɗalibansa ba kunya balle storon Allah wani ma har yaje ya ɗirkawa yarinyar mutane ciki sannan a haka ya qira kansa a malami wanda aka bawa amanan ɗalibai, ai Allah shirya mana al’umma kawai amma wannan halin malaman namu da wasu ke masa kallon AL’ADA tamu ta malamai to bai haɗu ba dan bakomai ciki face cikakken JAHILCI, kuma abun haushin sai kaga sun manta da suma iyaye ne su dinga bin yaran wasu wanda suma in akawa nasu ba zasu ji daɗi ba, sai dare kaga malamai suna shigowa ɗaukan yaran hostel kaman wani College ko University dan tsabar lalacewan zamanin mu ta yau, to Allah kyauta ya shirya mu amma ni Umaru ba ruwana da harka da ɗalibai dan bana qaunar reni ma”.

Jay cike da shaqiyanci ya ce “to in ba sonta kake ba me kake? Kaga in ta maka kawai faɗamun muje har gidan su in yaso sai ka rene ta kar ka damu da rashin girman ta, kawai ta girma a hannunka in kana zuba mata takin asali (sperm) tun yaushe zata girma kaman kazar gona, kai soyayyan aure zaka mata ba na lalacewa ba dan haka kai daban sauran malamai daban, Allah shirya mu duka”.

“Kai dai ɗan iska ne Jay Allah kawo maka sauqi dan fa baka ga yarinyar ba ta haɗu kam amma ba komai a wajan ni kuma tsakani da Allah yacce na balaga na balagen nan ai duk wacce na samu kasan ba aikin wasa zan mata ba balle akai ga maganan reno, sai dai ko in kai zaka iya haqura kayi renon tunda ɗalibata ce sai ka fara kamun qafa”.

Jay ya buɗe baki zai yi magana sai qiran da ya shigo wayansa ya kaste sa, ganin mai qiransa DMD sai ya ɗauka ya kara a kunne yana cewa “hello dude an tashi baccin ne?

Guntun tsaki DMD yaja yana driving, a taqaice yace “kana can har yanzu?

“Eh inanan amma bana gidan Hajja naje wajan freind”.

Da yake DMD yasan wanda Jay ke qira freind sai ya kaste qiran ba tare da yace komai ba ya ci-gaba da driving da gudu, ba jimawa suka isa.
Gidan ba za’a ce masa babba har can ba amma duba da ba’a cikin gari yake ba to zai iya amsa sunan babba kuma stararre wanda a kaf anguwan babu irin sa.
Bai ko shiga gidan ba ya tsaya a bakin gate ya juyo ya kallesu yace “ku sauqa ku shiga kuma kar naji kar na gani fatan kuna ji na?

Duk amsa masa suka yi sannan suka sauqa, sanda yaga shigansu kamun nan yaja motan sa yayi gaba.
Layin Jay ya qira ya masa kwatancen inda suke, yana shiga makarantar ya tarar da su suna jiransa, dan sanin halin DMD basu bari ya iso ya qirasu ba suka fito jiransa.

DMD kallon Farooq yayi yace “yanzu kai a nan kake rayuwa? Service ɗin nan dole ne?

“DMD ba zaka gane bane”.

Taɓe baki yayi ya shige cikin ɗakin ya ɗauro alwala ya dawo palourn ya same su suna hira sai ya shumfiɗa darduma ya ta da sallah.
Yana idarwa ya kallesu kaman wanda aka sa dole ko aka shaqe yace “kunyi sallan ne ko kun tsaya hiran mata?

Jay hararansa yayi cikin wasa yace “ba zancen mata ba cin mata muke ɗan renin hankali mutum sai kace mata-maza nikam anya dude lafiyan ka? Anyama kana jin feelings?

Ko kallo Jay bai ishe sa ba balle ya tanka ya juya yaci gaba da qirga countern sa.

Farooq dariya yayi har da kama ciki ya ce “kai fa Jay shahararren ɗan iska ne baka da magana sai na mata ai kam matarka ta shiga uku, yanzu angaya maka su mata-mazan basa jin feelings ne? Suma feelings gare su mai qarfi ma dan kaji kuma DMD irin su da kake ga suke shirun nan kaman abun bai damesu ba to sune oganni in suka kama mace sai sun sumar irinka kuma kuna good 5mints kun gama”.

Wani kallon banza kallon bakasan me kake faɗa ba Jay yayi wa Farooq ya ce “amma tabbas in nace baka ci tuwo akaina ba to nayi qarya dan tsaban renin hankali ka dubeni jibgege da ni kana qiran 5mints ai wallahi yanda nake ji na ɗin nan in mace ta shiga hannuna sai an ɗinka ta, muga wannan kala muga wannan duk muyi ittaqillah mu haƙora ai in muka samu namu ta sunna da lada to sai mun qarar da arna dan kisa, kai dai kawai ayi shiru, ɗazu Afrah ke ban labarin wata qawarta inaga ma ita kake nufi Afrah yarinyar nan dan staɓar tana ji ta fara girma har da cemun wai na auri qawarta tana da hankali amma kuma na kawo kunne ta faɗamun wata magana, duk ɗauka na wata serious magana ta arziƙi za ta faɗa mun ashe yarinyar nan cewa za tayi qawar tata bata da ko nono, to sai ka tuno mun da Afrah nima kaman DMD nake da ra’ayi sai qosashshiyar mace kuma nunanniya wacce tasan ta amsa suna budurwa dan yarinya ba za ta ɗauki buqatar Jay ba”.

“Hhhhh! Jay Allah kawo maka sauqi” faɗin Farooq yana miqewa.

DMD kallon Jay yayi ya aika masa da harara dan maganganun nasu sosai ya cika sa fam da haushi amma rashin son hayaniya yasa bai yi magana ba.

 

FAN’S KU RIQE GODIYAR KU, UWAR BATOORL SHARHI KAWAI TAKE BUQATA.

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR’S ANNIVERSARY

Ameerah, jeddatulkair (oum abdusamad), Besty(Dr Seeyerth) wannan page ɗin naku ne kuyi yanda kuke so da shi.

JAHILCI KO AL’ADAH? FAN’S CLUB 🤝💙one lurv masu daraja habibties, Uwar batoorl na matuqar qamnar ku da sharhinku da soyayyan ku ga wannan littafi.
Dama waɗanda basa group ɗin amma suna sharhi to tabbas Uwar batoorl na soyayyan ku🤝

 

FAN’S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

💋💋 امى بتولة💋

 

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 27_28

Ɗage kafaɗa Jay yayi irin ko a jikina ɗin nan, yace “uban masu jin kai ai wallahi tun wuri ka rage wannan ji da kan ko kuwa kasha wahala a hannun ‘yar mutane don na tabbata za’a wahalar da kai kamun a baka haɗin kai kuma kai kaja, sannan za ta qeraka staff ka shiga hankalin ka dan mata dai sun wuce duk tunaninka a seta maza duk mulkinka a waje a gida sune masu mulkin ƴan aljanna ba Allah dai ya qarawa mata albarka da ni’ima mu kuma ya qara mana qarfin kwasan ni’iman”.

“Mtssswww! Kai fa Jay iskancinka bai da uban gida, yaro qarami sai son maganan banza” cewar DMD da ya ciro wayansa yana lastawa kaman ba shi yayi magana ba.

Wani wawan dariya Jay yayi kaman wanda akawa kyauta yace “dude kai cikakken ɗan renin hankali ne Wallahi nine yaro? Inaji shekara biyu zuwa uku ka bani to ba banbanci sannan kuma maganan banza dole nayi ta atou harka ce ta sharholiya kuma ta jin daɗi da samun nistuwa, ni wallahi zama haka ma ya ishe ni dole amun aure a wannan shekara dan bazan yarda na cika shekara talatin na stofe kaman kai bansan wancan hanyan ba, ni ko classic bazawara zan aura dan ban cika son gargada ba dama indai garin akwai ni’iman damuna sannan ko ina da damshi ga daɗi to an wuce wajan muje zuwa kawai kwasan albarkatun gari ba kakkautawa harka ta sharholiya, a shekara guda kuma za kaga yaro ya haifo yaro”.

DMD dubansa ya kai kan stadadden agogon dake maqale a kakkauran hannun sa, ganin time sai ya miqe yana faɗin “in ka gama maganan yarantan taka sai ka taso mu wuce dan ba kwana a garin nan zan yi ba, in kuma baka gama ba sai ka dawo”.

Hararansa Jay yayi ya miqe yana qwalawa Farooq qira, nan ya fito a shirye staff cikin qananun kayan da ya yi matuqar amsan sa.
Farooq (malam ba wasa) chocolate color ne amma ba mai duhu ba, yana da saje da gashin gemu, fiskan sa mai ɗauke da dogon hancin sa da idanuwansa ƴan dai-dai, yana da stayi amma ba sosai ba dan DMD ya fisa stayi sannan ba za’a ce masa stiriri ba kuma ba za’a ce masa mai jiki ba saɓanin DMD da Jay da jikinsu kenan kaman na mata waɗan da ake ce musu ƴan duma-duma abinda ya ɓoye jikin DMD kuwa stayin sa dan yana da stayi dai-dai burin ko wacce mace ga kuma faffaɗan qirji, shi Jay kuma stayin ba sosai ba sai jikin sa ya ɗan nuna.

Fita suka yi duka har inda suka Parker motocin su, Jay da Farooq suka shiga na Jay shi kuma gogan ya shiga nashi ya mata key.

Sweedy da sallama suka shiga palourn, Hajja da ke zaune tana kallon tashan kung-fu kaman tana jin Chinese, jin sallama sai ta juyo tana ganin su ta fara washe baki tana faɗin “maraba lale da kyawawan jikokin Hajja”.
Sweetie ce ta qariso ta faɗa jikin Hajja tana magana da turanci “Hajja ta nayi kewanki”.
Dundu Hajja ta mata tace “kindai san ke ƴar lukuta ce ba kamar sauran ba to ɗaga ni karki karyani da wannan yaren mutane da kuke satowa ba za ku iya naku ba”

Tura baki sweetie tayi dan ta stani ace tana da jiki, tashuwa tayi ta koma gefe tana magana da Indianci.

Gaishe da Hajja su sweedy suka yi ta amsa da fara’a dan Allah ya gani tanason yaran Mustaphan ta ba kaɗan ba barin ma dai yayansu babban jikanta.
“Halan ku da wa kuka zo? Naga ku kaɗai ku ka shigo.

Sweedy tayi shiru sanin tana faɗa Hajja za ta hau surutu amma sai ta ji muryan sweerie na faɗin “ai Hajja Darling ne ya kawo mu yanxu ma ya tafi wajan big bro ne zasu dawo tare” ajiyan zuciya sweedy tayi jin abinda sweerie ta faɗa tasan ko ba komai yanxu kam albarka zata saka masa.

Hajja jin haka sai ta washe baki tace “ban dai so qanin miji yafi miji kyau ba amma ba komai Allah kawo su lafiya ƴan albarka, shi kuma jabiru zai zo ya faɗa mun Maryam ce ko Nura suka ce ya fita da har zai ja mun jika wajan shirmen sa.
Da qyar ta lallaɓa sweetie ta haqura har ta sake suna dariyansu dan dama babbar abokiyar shirin ta kenan.
su sweedy suka tashi suka shige ciki ɗakin da yake nasu ƴammataye amma banda sweerie dan ita ɗakinsu da Afrah ne sai sweetie kuma wajan Hajja take tarewa muddin tazo ba tare da Ammi ba.
Samun Afreen suka yi tana kwance tana chat, ganin sweedy kaman daga sama ba shiri ta miqe ta rungumeta tana cewa “sweedy yaushe kuka zo? ke da wa? Ina Darling?
Sweedy hugging nata tayi tana murmushi dan daman tasani wannan wajibi ne sai ta tambayi Darling dan mutuwan sonsa take yi shi kuma Darling ko a jikin sa.
“Yau ɗin nan muka zo ko hutawa ba muyi ba aka kawo mu nan kuma aikin Darling ne amma ya tafi wajan big bro” sweedy na faɗa tana ɓata fiska dan gajiya.
Afreen tace “sorry my dear, sannunku da gajiya”.

Sweerie ma ta gaida Afreen kana ta juya ta fice dan zuwa ɗakin su ita da Afrah su ma.

Da sallama ta shiga tana faɗin “qanwata Afrahty my love ina kike?

Afrah dake cikin banɗaki dan tashuwanta bacci kenan, jin muryan sweerie dan tasan ita kaɗai ke qiranta haka, barin wankan tayi ta ɗaura towel ta fito da gudu tana faɗin “oyoyooo sister sweerie”.

Hugging juna suka yi suna dariya Afrah tace “ke kullum ba zaki ce Afrahty kaɗai ba sai kince qanwarki kuma shekara guda kawai fa kika ban, shiyasa inajin qiran nan nasan kece, ina mintin zuciyata? Ina yaya sweedy? Yaushe a gari? Wa ya kawo ku? Ina Darling?

Hararanta sweerie tayi tace “kede baki sauya ba kullum tambaya kaman ƴar jarida”.

Dariya Afrah tayi tace “naji daɗin zuwanku dama ina missing na habibty na thank God gaku nan weekend zai yi daɗi, yanzu dai bani amsa ta”.

Sweerie murmushi tayi tace “1 mintin zuciyarki na wajan Hajja, 2 yau ɗin nan muka zo, 3 yau muka diro Nigeria,4 Darling ne ya kawo mu amma daga Gombe daga Canada kam Abiy ne, 5 Darling yana tare da big bro”.

Dariya Afrah ta sanya tace “kin bani duka kenan? Shikkenan sannunku da zuwa ba nayi wanka nazo na baki labarin Habibty ta” ta faɗa tana shigewa banɗaki ita kuma sweerie ta qarisa kan gado tana kwanciya.

“Hajja ina tambayanki ina Aunty masoyiya kinyi shiru ko? Faɗin sweetie tana tura baki.

“Sakalatun sakalalliya iyayen taɓara gaba ɗaya yarinya kin girma kin zama budurwa amma sakalci uwa sakakken mara, ni ina nasan kina da masokiya ne ko masogiya”.

Tura bakin ta kuma yi tace “Hajja yaya Afrahty fa nake nufi”.

“Au ai sai kice mun Fatu ni ina nasan wani masokiya, tana can ɗaƙin su”.

“Shikkenan Hajja na barki ke ɗaya na tafi wajan Fatu” ta faɗa tana dariya ta shige hanyan ɗakunan.

Hajja danqwalo ta bita da shi tace “tijararriya sakalalliya zaki dawo ki same ni ai ba dai sunana kika qira gastau-gastau kamar ba sunan uwar ubanki ba”.

Jay har sun iso qofan gidan Hajja sai ya waiga bai ga motan DMD a bayansa ba, cikin sauri ya ciro waya yayi dialing layin sa.
“Hello dude ya banganka ba ina ka tsaya?

“Mtsww! Ni ba zani gidan Hajja ba ku same ni a inda nace maka zan je”.

“Dude please ka zo wallahi kuwa za mu bika can ɗin ka ji” Jay magiya ya dinga wa DMD har dai cikin ɓacin rai ya kashe wayan ya juyo motansa hanyan gidan Hajja.

Farooq na dariya yace “gaskiya DMD ko mace ta basa hanya a rigima da jan rai”.

“Ai wallahi freind ba iya jan rai ba har da na aji kaman ance masa nima ba al’qalamin ne da ni ba kaman shi”.

“Amma ai zai zo ko?

“Tunda ka ji ya kashe waya to zai zo amma xansha surutu kam dan kasan halin sa da ya dinga yawaita magana ya gwammace yayi abinda bai yi niya ba”.

Murmushi Farooq yayi dai-dai suna qarisa shiga palourn bakinsu da sallama.
Ganin ba kowa a palourn sai suka zauna kawai suna kallo, Jay yace “gwanda da Hajja bata waje dan da taga shigowana bata gansa ba ta farawa mutane aiken surutun ta”.

Bai ida rufe baki ba ta fito sanye da hijabin ta hannunta da carbi tana cewa “munafiki wato ma uwar ubanka ce mai surutu kai amma yaran nan kun renani uwayenku duk basu muku tarbiya ba” nan ta fara masifan kuwa tana tambayan bata ga Muhammadu ba?

Farooq ya gaisheta ta amsa tana tambayan sa ayyuka da gidansu ya amsa lafiya.

Ta buɗe baki zata qara tambayan sa sai sallaman sa da ta jiyo yasa tayi shiru ta hau washe baki.

𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚’𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 – 250 𝟏𝐆𝐁 – 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 500
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 750

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎……

 

Abiy yana shigewa gidan yayi mummunan gani dan kuwa Amaryan sa ya gani da mayafi da qaton akwati tana kuka ta taho zata fita ko kallon sa ba tayi ba (dama tana jin qaran motan Abiy ta haɗa kaya ta hau kukan kirsa).

Kallonta yake cike da mamaki yama kasa cewa komai har ta fice a palourn, da qyar ya iya ɗaga qafansa a inda yake staye yayi waje ganin har ta shiga mota tana qoqarin tayarwa, da sauri ya qarisa jikin motan yana mata magana “sweetheart me ya faru? Me aka maki? Ke da wa? Ina kuma za kije baki gayamun ba gashi kina kuka?

Aunty Amarya ko kallon Abiy taqi yi sai aikin kukan da take yi ta qara volume ta kau da kai (kana gani kasan kukan munafurci ne).

Abiy sai aikin rarrashin yake da tambayan ba’a si dan ba qaramin tashin hankali ya shiga ba, babu maimuna itama wannan tana qoqarin tafiya ina zai sanya kansa da yawan buqatan sa? Ai dagewa yayi yana rarrashi Aunty Amarya wacce da abun ya mata yanda take so ganin har da cewa zai saya mata mota sai ta buɗe murfin motan ta fito nan ma bata ko kallesa ba kuma bata ɗau kayanta ba ta shige cikin gida har ɓangaren ta direct ɗakinta ta shige tana kan kukan ta.

Abiy ajiyan zuciya yayi ganin dai ta koma cikin wanda yasan yanzu lallashin zai zo masa da sauqi tunda ta fasa tafiyan, shima bin bayanta yayi yana ƴar waqan soyayya.
“Rabi’atul adawiyya masoyiya ta Amarya ta ƴar aljanna mai haquri ga kawaici ga hankali(Abiy ya faɗa sosai😂).
Har cikin ɗakin ya bita, yana shiga ya cire babban rigar sa ya masta kusa da ita ya jawo ta jikin sa yana bubbuga bayanta yana qoqarin laluɓo bakinta ta fiske cikin kukan kirsa tace “Ni a gidan nan ba’a ɗauke ni a bakin komai ba iya amfanina kenan a biya buqata da ni duk sanda aka so amma wai ace dan ban haihu ba baza’a girmama ni ba aban matsayin uwa ko da zanji sanyi a raina, kowa ya tashi bai da mareniyar wayo sai ni har ɗan ciki na ya mare ni” duk maganan da take cikin kuka.

Abiy da yake mamakin wa zai mare ta sai yace “sweetheart ke da wa?

Hararansa tayi tana kuka tace “Ni da wa kuma ina banda yaronka wai ace har yaronka yayi girman da zai mari matar ubansa ina a matsayin uwar sa dan ni ba mazaunin yadikko nake zaune da su ba yaro na kowa ne”.

Abiy da mamaki da ɓacin rai suka cika sa yace “wai har kina nufin MUFADDAL ya mare ki? Yaushe duk rashin kunyan nasa ya kai haka akan me zai mare ki?

Cikin taqaici Aunty Amarya tace “wato baka yarda ya mareni ba? Zanwa yaronka sharri ko? Hmmn! Ba komai dama nasan iya mastayina kai ma baka qaunata kawai amafanina gare ka biyan buqatan ka tunda har kana tunanin duk irin qaunar da nake wa yaran nan zan musu sharri, wai kana tambaya akan me ya mare ni ko? Hmmn! To akan gaskiya kawai dan ita gaskiya ɗaci gare ta, yarinyar nan sweerie na samu ta kunna waqa tana aikin tiqan rawa sai na kashe nace bai kamata ba tana ɗiya mace ga can mama mai aiki a kitchen taje ta tayata wani abun yafi wannan rawa dan ita mace ce kuma aurar su za muyi, kar a dawo mana da su basu iya komai ba, amma yarinyar nan tan tashuwa buɗan bakinta ba zata yi ɗin ba ina ruwa ai ni ba uwarta ba balle na sanya ta aiki. Na fito na dawo ɗaki bance mata komai ba sai can fitowa na na samu an juyemun gaba ɗaya ferfesun da na shiga kitchen na maka da kaina ina mamaki sai ga yarinyar nan ta fito tana faɗamun ita tayi na ɗau mataki, cikin ɓacin rai na fara mata faɗa nace nima mahaifiyar su ne bai kamata ba, ban ida rufe baki ba MUFADDAL ya wanke mun fiska da mari wai na daina haɗa kaina da Ammin su dan ita ba sa’a ta bace” Aunty Amarya na gama magana ta fashe da kuka mai qarfi wanda in kaji ka ɗauka ko uwatta ce ta sheqa.

Abiy cikin tsananin fushi ya miqe zai fice amma aunty amarya ta riqo sa tana kuka tace “nikam kayi haquri na yafe musu Allah shirya mana su dan kaga sun riga sun fita bai kamata ka fita cikin fushi ba banso komai ya samarmun kai mijina kayi haquri kaima ka yafe musu”.

Kallonta yayi ransa a ɓace yace “Rabi’a har zaki ce na yafe musu kin yafe musu to wallahi ba za’a yi haka da ni ba na auro mata yara su hanata sukuni dan suna taya uwarsu kishi to zan ɗau mataki dole da shi MUFADDAL ɗin da ita MUNAWWARA su san nine na haife su ba su suka haife ni ba renin yaron nan ya fara wuce gona da iri”

Aunty Amarya murmushi tayi ganin Abba baya ganin ta amma sai ta lanqwasa murya tace “komai suka yi kai ne ka ja dan ya kamata tun farko ka nuna musu ni ma uwarsu ce amma baka yi hakan ba dan haka haquri gare ni ya zama dole tunda yaran mijinane kuma ina sonsa matuqa dan haka dole gare ni na qaunace su suma”

Abiy na huci ya dage zai bi DMD amma Aunty Amarya ta hana sa nan dai ya bata haquri kan zai ɗauki mataki da ta nuna bata so ta haqura sai yayi fushi ya tafi ɗakinsa wanda ganin haka tayi hamdala a rai tasan komin yaya sai ya ɗau mataki dan shirin nata ya tafi yanda take so.
Wata ƴar iskan dogon riga ta sanya shara-shara ta tamke nononta da ya fara kwanciya a bresia tayi hanyan ɗakin Abiy, tana shiga ta same sa da waya a hannu yana aukin qira ana gaya masa “not reachable” alaman ba network, qwafa yake kan jerawa dan har yanzu cikin ɓacin rai yake, jin qamshin Amaryan sa ya sanya shi juyawa duk da kuwa fushin da yake yi da ita, wanda kallo ɗaya ya mata ya kau da kai.

Aunty Amarya ganin haka sanda ta girgiza da fushin Abiy tasan shi koma menene tayi wannan shiga da wannan qamshi zai haqura dan haka ta qarisa ta zauna kan cinyan sa tana qara basa haquri tana shafa sa.

Abiy da Allah yayo sa da qarfin sha’awa duk da kuwa manyantan sa amma garau yake dan haka lokaci guda ya biyewa Amaryan sa suka lula duniyan ma’aurata.

DMD qarisa shigowa palourn yayi da sallama a bakin sa qasa-qasa dan ko ka kasa kunne ba jiyowa za kayi ba sai dai in ka kalli laɓɓansa waɗanda ke mostawa a hankali kaman mai rigima da su, fiskan sa a haɗe kana gani kasan a cike yake qiris yake jira ya juye akan mutun, ba tare da ya kalli ko su Jay ba balle Hajja ya samu waje ya zauna ya fidda wayan sa ya sa Bluetooth.

Hajja kallon sa tayi ta kalli su Farooq ta kuma kallon sa, cike da masifa tace “Muhammadu uwaka maimuna”

Ɗago idanuwan sa yayi da har sun sanja kala, rai a ɓace ya wastawa Hajja wani mugun kallo, kallon karki sake qiran Uwata.

Hajja qwafa tayi ganin irin kallon da yake mata ta ce “an faɗa uwarka maimuna tashi ka cinye ni ɗanye ɗan gidan marassa ji yaro sai aukin zuciya kaman na fir’auna uwarka ta fi uwar wa? Dama wa ya kawo ka gida na tunda kasan rashin kunya ka ɗibo ka taho da shi ba kirki ba?

Cikin fushi ya miqe ya juya zai fice dan yasan muddin ya buɗe baki to abun ba zai yi daɗi ba dan kasancewarta kakarsa bai dame sa ba, kawai tayi kaɗan ya tamka mata shi yasa ya miqe ya fice.
Yana fitowa ya wuce ɗayan sashin da yake nasu yara maza yana ji kaman ya kamo Jay ya shaqe sa dan shi ya jawo masa shigowa gidan.

DMD na barin palourn Afreen ta shigo, jin hayaniyan Hajja ta san tabbas DMD ya shigo nan ta baza maganenta (idanuwanta) amma baya palourn, idonta har da qwalla ta haɗa fiska tace “ke dai Hajja wallahi kin cika masifa da surutu an samu ya zo shine kika kora sa da halinki, big bro Ina yake?

Jay da shima ya cika da surutun Hajjan hararan Afreen yayi dan shima yaji haushi yace “igiyar ajiyan sa da kika ban ya ɓata idiot kauce mun a gani”

Murguɗa baki tayi ta fice, tana fita kuwa ta ga motan sa wanda ke nuni da yana cikin gida bai tafi ba dan haka cikin sassarfa ta tuni sashin yayyunta mazan.

Hajja ma da ta cika da baqin halin jikan nata da ke damunta ga ta masa faɗa kuma bata jin daɗi duk da kuwa irin kallon renin da ya mata amma sonsa da take yi yasa take jin haushin faɗan da ta masa dan haka miqewa tayi itama ta fice dan tasan ba zai wuce yana sashin su ba.

Afrah da sweetie ne suka fito daga ɗaki inda suka baro sweerie a ciki.
Sweetie na ganin Jay ta yi wajan sa da gudu tana cewa “oyoyo big bro”

Afrah kuwa ganin wanda ke zaune gefen big bro ai sai ta storita ta waro ido a ranta tace “Malam ba wasa!”….

 

FAN’S KU RIQE GODIYAR KU, UWAR BATOORL SHARHI KAWAI TAKE BUQATA.

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR’S ANNIVERSARY

JAHILCI KO AL’ADAH? FAN’S CLUB 🤝💙one lurv masu daraja habibties, Uwar batoorl na matuqar qamnar ku da sharhinku da soyayyan ku ga wannan littafi.
Dama waɗanda basa group ɗin amma suna sharhi to tabbas Uwar batoorl na soyayyan ku.

*Wannan page ɗin naki ne NAFEESAH*

FAN’S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

💋💋 امى بتولة💋

 

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 29_30

Afrah qasa tayi da kanta ta qarisa cikin palourn wanda shima Farooq idon sa ke kanta yana danne dariyan sa dan yasan bata san me ya kawo sa gidan ba.
Qarisowa palourn tayi ta durqusa ta gaishe shi sannan tayi wa big bro sannu da dawowa.
Jay yace “yauwa qawar qwailar budurwata”.
Afrah tura baki tayi tare da yin qasa da kanta duk a tunaninta ba wanda yasan abinda ta faɗa bata san Jay kam ya jima da juyewa malam ba-wasa.

Afreen tura qofan palourn nasu tayi ta shiga da sallama, ganinsa yana zaune yana danna waya sai taji sanyi a ranta ta qarisa ciki zuciyanta na dukan uku-uku dan kuwa tasan halin sa sarai.
Tun shigowanta yaji mostinta har qarosowan da tayi palourn da kuma idanuwan da ta zuba masa duk yana sane amma sai ya basar.
“Darling kayi haquri da halin Hajja” ba tare da yace komai ba ya lumshe idon sa gami da jinginar da kansa a jikin kujeran da yake zaune, yana sauqe ajiyan zuciya.
Haquri taci gaba da bashi tare da masa sannu da zuwa amma ko kallonta bai yi ba balle ya tanka mata, har sai da ta yi addu’an Allah bayyana Ammi kamun cikin sanyi ya buɗe bakin sa yace “Ameen ya Hayyu ya Qayyum” iyaka abinda ya faɗa kenan ya kuma rufe bakinsa gum kai kace baya magana.

Hajja da sallama ta shigo, inda ta hange sa zaune ta nufa tana faɗin “Malam Muhammad Mufaddal, yaro mai sunan larabawa, babban mutum a daina fushi da Amarya mana”.
Tun shigowan stohuwar yaji ransa na qara ɓaci, duk surutun ta kuwa bai ko haɗa shi da qasa ba, sai ma earpiece nasa da ya maida kunne.
Zama tayi gefensa tace “haba Angon Hajja mijin Hajiya fushi kake da Amaryan ka?
Duk surutun Hajja ko kallonta bai yi ba bare kuwa ya kai ga mata magana dan DMD sosai yake da zuciya ga rashin son surutu, amma kuma bashi da riqo.

Hajja rarràshi tayi kaman wacce ke rarràshin yaron goye amma ko kulata yaqi yi sai da qyar kamun ya buɗe baki yace “Hajja komai za kuce ku daina sako Ammi ba ruwanta ba abinda ta sani”.
Hajja jin ta samu ya kulata ai cikin kwantar da murya ta ce “ai ni tsakanina da Maimuna baiwar Allah sai addu’a da fatan alkairi barin ma dai da ta haifamun ku, karka damu an daina Angon Hajja, amma kai ma ka dubi girman Allah da Manzon sa ka rage wannan halin naka”.
Sai lokacin yayi ajiyan zuciya yace “kuma kiwa yaronki ma magana komai za suyi shi da matarsa su daina sako Ammi kowa ya staya iya mastayinsa ya zauna iya mazaunin sa”.

“Ai karka damu tsaff na ɗauki mataki na gama dan na sani Rabi’atu cikakkiyar munafuka ce ga kirsa, ai ita abin nata ma yayi yawa yo gaki ba kyau ba ga kuma munafurci, kuma fa damuwan ta duka dan bata haihu bane, ai ni nagode wa Allah da ban haɗa jini da ita ba, kaikam kayi haquri ko Allah ya bayyana maimuna”.

“Ameen” ya faɗa a taqaice yana miqewa zai fice a sashin, da Hajja da Afreen duka miqewa suka yi suka bi bayansa.
Motansa ya shiga ya zauna ya mata key kamun ya juyo a daqile yace wa Afreen “ki gayawa Jay na tafi”.

Hajja salati tayi kawai ta tafa hannu dan ita tama rasa irin zuciyan wannan jikan nata ko na uban wa ya ɗauko oho, ubansa Mustapha nada zuciya amma ba irin wannan baqar cin rai ɗin ba “to Allah ya shirya” ta faɗa tana shigewa sashin ta.
Afreen kaman za tayi kuka haka tabi bayan Hajja bayan taga fitan motan sa, sosai take mugun sonsa amma ko kallo bata ishe sa ba, ta rasa ta ina ma zata fara ɓullo wa ta nuna tana sonsa kuma gashi ba wanda yake saurara balle ta sama da maganan “Allah dawo dake lafiya Ammi nasan kece kawai zaki mallaka min masoyin raina” cewar ta tana shigewa palourn.

Jay na jin dirin motan DMD nan suka fito shi da Farooq, kusan karo da Afreen suka yi nan ta faɗa musu abinda yace, tana gama magana ta qarisa ta ciki dan lallashin kanta, su kuma suka shige nasu motan.
Jay yaje ya ajiye Farooq sannan shima ya kamo hanyan komawa cikin Gombe.

 

𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚’𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 – 250 𝟏𝐆𝐁 – 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 500
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 750

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎……

 

⭐⭐
Anci hutun qarshen mako an suɗe amma har yanzu qafan Innai bai warke ba har da ɗingishi take yi, baabaa da idanuwanta ke kan Innai da tayi hanyan banɗaki girgiza kai tayi tace “Allah Ubangiji ya yaye wa ɗan mutum jarababben raki da son jiki irin naki takwara, dan kekam abun sun taru sun miki yawa, kece qan-jiki kuma kece raki to wai ma ta ina ciwo zai sake ki in ya kama ki? Ai ranar da za ki haihu akwai kwasan ƴan kallo, Allah dai ya kawo miki da sauqi ya yaye miki, amma tabbas duk shawaragin mijin da ya aureki takwara sai dai a bisa da kondunan haƙuri cikin akori-kura, yarinya gaba-ɗaya kaman wacce nono bai isheta ba, uhmñ ni Allah na tuba ai ma nonon ba isanki yayi ba babu laifinki Allah shiryi uwaki Indo”.
Har Innai ta fito banɗaki baabaa na kan mita, kallonta baabaa tayi tace “wai yau har rana ta fito gasto-gasto kina ta yan-yana qafa halan baza ki bokokon ba?

Innai zama tayi gefen baabaa tana faɗin “washh! Qafata, baabaa sai jibi za muje makarantan yau da gobe babu”.

“Uwar masu sakalci yanzu wannan ɗan tafiyan shine har da wani washh, na washo miki kan baabaarki Indo, ‘yar shawaragin buhun uba”.

Duk tsawon kwanakin nan da duk abunda ya samu Innai har taji sauqi Inna ko sau ɗaya bata taɓa gwada ce mata sannu ko ya jiki ba, tun Baffai na fushi har ya gaji ya sauqo yana bin ta da addu’an Allah kyauta dan ya tabbatar lamarin Inna sai a hankali, tun yarinya na stumman goyo har ta girma ta zama budurwa amma babu soyayya da kulawan mahaifiya, sai dai ya qudure a ransa tabbas zai ɗauki mataki kuma itama Baabaa Mero tana nata shirin daban, don abun ya kai su bango zuba mata ido da suke yi shi ne laifin su.

A ɓangaren DMD kuwa zuwa yanzu ko magana baya yi da Abiy akan abinda Aunty Amarya ta faɗa wa Abiy, wanda saura kaɗan Abiy ya stine masa Daddy ne ya taka masa burki, sai Hajja da tace ya dai bincika dan zai yiwu sharrin Rabi’atu ne ko kuwa gaskiyanta fitsaran shi yaron ne.
DMD dai duk zuba musu idanuwa yayi yana kallon su dan shi damuwansa Ammin sa, in ta dawo duk zai koma kan maganan ya ɗau mataki dan ya fahimci matar Abiy na buqatan qarin hankali.

Su sweerie sun gama fahimtan Amminsu ɓacewa tayi kawai Abiy lallaɓasu yayi.
sweetie kuwa kukan yau daban na gobe daban kullum dai ita Ammin ta, gashi Darling tunda ya kawo su bai dawo ba har dai yau da ya kama Monday.

Hajja zaune da jikokin nata a palour, sweetie ke kukan darun da ta saba “Ammiiii naaah! Wayyo Ammiii naaaah! Whmmmmm!…. Ammiiii….” Kuka take da gasken-gaske dan har muryanta ya dishe.
Sweerie tashuwa tayi taje gefen sweetie ta zauna, idanuwan ta cike da qwalla tace ” Muheebbah please kibar kukan nan haka za kisa Ammi yin shaquwa kiyi haquri kinji zata dawo” ta faɗa tana qoqarin jawo ta jikin ta, amma sweetie sai ta zille tana kan kuka tana qiran sunan Ammin ta.
Sweerie ganin haka sai itama ta fara hawayen, Afrah dake kallon su itama kukan ta kama dan sosai take son sweetie bata son ganin ta cikin damuwa balle kuma sweerie abokiyar ta, Hajja da ta cika tayi fam kaman ta fashe cikin jin haushin kukan nasu tace “Wai nikam ance muku uwar taku mutuwa tayi ne? Kun maida mun gida gidan makoki to bazai saɓu ba, ubanku yazo ya ɗauke ku ya maida ku gidan sa dan wannan kukan mutuwan ba’a gidan Fatuma ba”.

“Eh ɗinnn an…an..anyi kuuu kann.. ai dan ke maaa..maaaan..kii bata duniya shiyasaaaa.. Wayyo Allah na Ammi na!” Sweetie ta faɗa cikin kuka.

“Eh lallai kukan munafurci kike yi muhibba, yau dan staɓar carbin fistaranki a cike yake ni zaki cewa Uwata ta mutu? Yau dama uwar waye ba zata mutu ba, Uwar kowa ma sai ta mutu dan haka zaku barmin gida na bana uwaku ba, yarinya qarama sai cikakken rashin kunya, waye baisan haquri ba inbanda rashin hankali da ke damunki”.

Sweedy da ke zaune gefe damuwa ya taru ya mata yawa ga kukan sweetie da yake ci mata zuciya ga kuma labarin Ammi shiru sannan Darling tunda ya kawo su bai waiwayo su ba.
Afreen da ta shigo palourn yanzu wajan sweedy ta nufa tana faɗin “lafiya da tagumi? Cikin harshen turanci.

Sweedy kaman mai shirin kuka tace “komai ma ba lafiya ba ni banma san ya zanyi ba wallahi gaba ɗaya duniyan tamun zafi, gashi layina na Nigeria na nemeshi na rasa Darling bai zo ba bai neme mu ba”.

Hajja da take ta aikin hararan sweedy tace “ai dole duniya ta miki zafi tunda a bakin kura kuke, shi yayan naku ai stakar dokan daji ya aje ku dole kice bai waiwayo ku ba, ooh ni fatuma na shiga aljanna na kasa fita wai yau ace jikoki na neman maida ni zabiya ko stigai rana tsaka abinda banyi tun tale-tale ba sai yau rana tsaka, gaba ɗaya jikoki sunbi sun buwaye ni”.

Sweedy ko kallon Hajja bata yi ba balle ta mata magana dan ita bata cika hayaniya ba, indai stiwa kake so to ka samu sweerie ko sweetie dan halin DMD da sweedy ba banbanci basuson yawan magana.
Afreen da idanuwanta ke kan sweedy tace “yanzu ki amshi wayata ki qira Darling inyaso sai ya rarrashi sweetie da kansa, zuwa gobe sai mu nemo miki layi”.

Murmushi Kawai sweedy tayi bata ce komai ba ta amshi wayan tayi dialing layin Darling, ganin sunan da Afreen tayi saving sai abun ya sanya ta murmusa sosai har fararen haqoranta suka bayyana tace “Wow! Sunan yayi daɗi ina aure haka zan dinga qiran mijina da shi Insha Allahu”.
Ta qira yakai sau 3 bai ɗauka ba sai kawai ta tura message ta rungume wayan a qirjinta idanuwanta akan su sweetie.

DMD dake zaune gaban Daddy kansa a qasa yana sauraran faɗan da Daddy ke masa sai jin qira ya shigo wayan sa yayi, bai kalli wayanba balle ya duba har akayi qira uku duk suka kaste, Daddy yace “son ba qiranka ake yi bane?

Ya buɗe baki zai yi magana sai yaji shigowan message, ɗaukan wayan yayi ya duba ganin abinda aka tura sai kawai ya lumshe ido ya aje wayan yayi shiru.

Daddy ganin haka sai yaci gaba da maganan sa “son shi fa mahaifinka ne, baka da kaman shi ko madadin sa a duniyar ka, ka daina gaba da mahaifinka akan abinda bai taka kara ya karya ba dan nasan baka mari Rabi’atu ba”.

DMD dai kansa a qasa baice uffan ba har Daddy ya gama, godiya kawai ya masa ya tashi ya fice a palourn yana ciro wayan sa dan qiran qannensa.

Mummy da kallo tabi sa har ya fita kamun ta sauqe ajiyan zuciya tace “gaskiya lamarin Mufaddal sai addu’a, Rabi’atu bata kyauta ba haka shima Abiy bai kyauta ba duk da yaron sa ne amma kuma Mufaddal bai yi dai-dai ba akan ɗauke yiwa mahaifinsa magana, Ammi shiru ba labarin ta shi Abiy da kuke tare ai sai ku dage ku rabu lafiya da shi”.

“Ai ni rasa abun faɗa nake habibty addu’a na kawai Allah dawo da Maimuna lafiya dan har da rashin ta ya qara ta’azzara wasu abubuwan a halayyar sa duk da dama dai Mufaddal bauɗaɗɗen mutum ne” cewar Daddy yana ciro wayan sa dake qara a aljihu.

Sweedy na zaune riqe da waya shiru tana tunani kawai ta ji qaran shigowan qira har sai da ta razana, ganin Darling ne mai qira sai ta ɗauka ta kara a kunne “Hello”.

Cikin Yaren Indianci ya mata magana a ɗaya ɓangaren “Sweedy ya aka yi?

“Darling, sweetie kuka sweerie kuka ni na rasa ya zanyi sunqi bari na naji da abu guda ɗaya ga layina na Nigeria ya ɓata”.

Ajiyan zuciya ya sauqe yace “kuyi haquri Ammi ta kusa dawowa in Allah ya yarda, sa wayan a handsfree”.

Sawa tayi a handsfree kaman yanda ya umurce ta cikin yaren hindi.

“Sweetyn Ammi kukan me kuke?

Sweetie da ke aikin ajiyan zuciya jin muryan Darling da sauri ta fara magana da Indianci cikin dashashshiyar muryanta “Darling, Abiy yace Ammi na gida amma munje gida ba Ammi sai yace kuna tare a gidan Hajja, mun ganka ka kuma kawo mu gidan Hajja yau kwanmu 4 ba Ammi bamu ganta ba kuma Hajja tace Ammin mu ta ɓace”.

Dafe kai kawai DMD yayi jin irin surutun da take korowa bata ko jan numfashi ga kuma ciwon kai dake kan addaban sa “sweetie kina ji ba, to kuyi haquri ba yau Monday ba to Ammi zata dawo ranan Thursday kinji ki dena kuka kiyi shiru okay”.

Sweetie tura baki tayi kaman tana gaban sa tace “Darling kai kuma yaushe za kazo to nayi missing naka kuma Abiy ma yaqi zuwa”.

Busar da iska yayi kamun cikin gajiya da magana yace “zanzo Wednesday” kittt ya kashe wayan, yana qarisawa wajan da ya Parker motansa ya fice yayi wajan Jay dake asibiti.
Yana isa direct office na Jay ya nufa, qwanqwasa qofa yayi nan aka basa daman shiga, ya tura qofan ta shiga ko kallon Jay bai yi ba ya nufi wani qofa ya tura ya shiga, Wow! Kai ka ce ɗakin wata Amarya ne dan kuwa kujeru ne set guda ga kuma fridge ga kuma wani madaidaicin gado a gefe.
Jay buɗe qofan yayi ya shigo, ganin DMD akan dogon kujera mai ɗaukan mutum uku sai ya qarisa ya zauna akan 1seater yana faɗin “dude lafiya kuwa?

“Normal” abunda ya faɗa kenan a taqaice yana mai lumshe ido.

Murmushi Jay yayi sanin stokana zai yi, sai yace “dude ko dai abun ta mosta ne?

Wani banzan kallo DMD ya wasta masa sannan ya kuma maida idon sa ya kulle.

“Dude in abun ne in nemo magani ko kuma na qira maka ɗaya daga Nurses namu” ya faɗa yana danne dariyan sa dan yasan tabbas ya nemo magana.

Tashuwa zaune DMD yayi rai a ɓace kaman wanda aka stare da bindiga dai yayi maganan ya ce “Jay kasan bana son maganan banza ko? In abinda kake yi kenan ance maka ni kai ne da ko wacce qazamar zata taɓa? Mind ur word’s, u know i hate this, mutum ko da yaushe ba shi da magana sai na mata to za su kashe ka, in kuma batun magani ne kai ka sani na fika sanin maganin mastalata dan kai ne babban ciwo na, mutum kullum surutu ka dinga saka mun headache, ina barin Nigeria ciwo na ya warke” faɗin Darling yana komawa ya kwanta.

Jay dariya yayi dan ko kaɗan kalaman DMD basu damesa ba “dude nima dai saurayine gal a leda kaman kai…..” Knocking da ake wa qofan office nasa shi ya sanya shi miqewa ya fice dan dama akwai patient nasa da ya tura yin scanning su dawo.

DMD gyara kwanciyan sa yayi ya lumshe ido dan bacci yake buqata ko kansa zai yi masa dai-dai.

Ayi Haquri da ƙarancin page ɗin nan.

FAN’S KU RIQE GODIYAR KU, UWAR BATOORL SHARHI KAWAI TAKE BUQATA.

A yi sharing dan girman Allah.

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR’S ANNIVERSARY

JAHILCI KO AL’ADAH? FAN’S CLUB 🤝💙one lurv masu daraja habibties, Uwar batoorl na matuqar qamnar ku da sharhinku da soyayyan ku ga wannan littafi.
Dama waɗanda basa group ɗin amma suna sharhi to tabbas Uwar batoorl na soyayyan ku🤝

 

FAN’S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

💋💋 امى بتولة💋

 

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 31_32

Jay ne ya shigo ɗakin ya nufi inda yake kwance yana qiran sunan sa “Dude! Dude! Dude…”
Kasancewan bashi da nauyin bacci tun shigowan Jay qaran qofan ya tayar da shi, idanuwan sa a kulle yace “Jay meyasa ka cika rashin ji ne? Ka qira mutum sau ɗaya bai yi ba sai ka qarar min da suna” yana gama faɗa ya miqe ya zauna yana laluɓo wayansa.

Jay taɓe baki yayi yace “daɗin abun ba sunanka na qira ba, koma dai mene tashi mu tafi gida”.

DMD bai ce komai ba ya miqe ya shiga toilet ɗin dake ɗakin, can ya fito yana gyara hannun rigansa da ya nannaɗe.
Bai ko kalli Jay ba ya shumfiɗa darduma ya tada Salla, sai da ya idar ya naɗe darduman sannan ya kalli Jay yace “let’s go” yana gama magana ya fice a ɗakin.

Jay miqewa yayi ya bi bayansa bayan ya kulle qofan office nasa.
Kowannen su motansa ya shiga suka yi gidan Daddy.

Ɗaya na bin ɗaya haka duka taho har suka iso gida gate man ya buɗe musu gate suka shigo kowa yayi parking suka nufi cikin palourn da sallama.
Mummy da ke zaune tana waya wanda daga ji kasan akan business nata ne, tana gama magana ta kaste tana amsa sallaman yaran nata fiskanta ɗauke da murmushi “wa’alaikumussalam sannunku da dawowa mazajen Hajja”.

Jay ne ya fara magana “habibty gaskiya nidai ba zan iya da fitinan stohuwar nan ba, nabar wa dude kyauta”.

DMD hararan sa yayi sannan ya buɗe baki kaman baison magana yace “Habibty yunwa” da Indianci yayi maganan.

Mummy na murmushi tace “yanzu son ai ko sayar da ni kayi niyan yi sai dai ka saida ni har ka amshi ƴan canjinka, dan ban fahimci ko kalma ɗaya a maganan ka ba, wannan yaren sai ku ai tunda Amminku taqi koyamin”.

DMD murmushi yayi jin abinda mummy tace, sai ya tuno rigimansu da Ammi watarana akan indiancin
** Ammi ce tayi magana cikin harshen Indianci “habibty wai Hajja na magana mune muka hana yaranmu yin aure sun girma suna gaban mu”.
Mummy idanu ta zubawa Ammi kawai bata ce komai ba.
Ammi ta kuma magana cikin harshen turanci “wai baki ji me nace ba habibty?
Sai sannan mummy tayi magana da turancin itama “ta ina zanji abinda kika ce Ammin su, bayan kinqi koyamun kuma dai so kike muyi gulmanmu amma kinqi koyamun yaren da za muyi gulman gashi ke kuma bakya jin yaren mu duka”.
Ammi murmushin ta mai stada tayi tace “karki damu yaronki zai koya miki tunda shi yana jin yaren ku yana jin Indiancin” cewar Ammi da turanci.**

Muryan mummy ne ya kaste masa tunani “Son me kake tunani tun ɗaxu ina magana shiru? Mummy ta faɗa tana kallon DMD da ya faɗa duniyar tunanin mahaifiyar sa.

Lumshe ido yayi ya buɗe su a hankali yace “ba komai habibty”.

Mummy ba dan ta yarda ba tace “shikkenan, kai kuma jabeer maza-maza kaje ka ɗauko min yarinya tunda gobe Wednesday hutun ya qare akwai school”.

Jay langwaɓe kai yayi kaman mace yace “Habibty zan ɗauko ta dole na, amma nima ki dinga cemun yaronki, kowa daga son sai daughter sai yarinya na, nine kawai ake qira da sunana jabeer”.

Hararan sa mummy tayi ta wuce dinning tana faɗin “son zo kaci abinci shi kuma in ya gama kishi da yaran nawa sai yazo ya ci shima”.

DMD kallon sa yayi tare da yin murmushin gefen leɓe “ka daina kishi da mu”.

Jay taɓe baki yayi yace “ayi kishi da kai akan me? Ni wuce muje muci abinci”.

“Kaci abinci a ina bayan baka yi sallah ba”.

Jay hararansa yayi yace “in kai ke amsan sallahn in tawa tazo ka dawomun da ita, kana sharar baccinka nayi sallah kace banyi ba”.

Dukansu miqewa suka yi suka nufi dinning ɗin, mummy tayi saving nasu duk suka yi shiru suna cin abinci.
Bayan sun kammala suka miqe suka haura sama kowa yayi ɗakinsa dan ya wasta ruwa.

DMD yana shiga ɗakin sa ya cire kayan jikinsa sannan ya ɗaura towel ya shige toilet, can ba jimawa ya fito ɗaure da towel ɗin a qugunsa daga leman ruwan dake jikin sa kasan wanka yayi.
DMD namiji ne iya namiji wanda kana ganinsa kaga ingarman namiji domin ya tara duk wani abu da mace ke buqata a wajan mijin aure, Allah ya hore masa kyau ga kuɗi sannan mutum ne mara hayaniya, yana da tsayi amma ba stayi mai muni ba sannan yana da jiki wanda tsayin sa ya ɓoye jikin sai komai ya tafi dai-dai, qirjinsa mai cike da haiba a cike yake da kwantattun gashi wanda kai kace gashin kan jariri ne ba kaman na wasu mazan kaman quda-quda ba, yana da haske sannan yana da yalwan gashin kai da na gemu waɗanda suka sha gyara, gashin kansa kuwa kai kace mace ce, yana da hanci mai stayi dai-dai da kuma bakin sa wanda bai da girma sosai mai tafiya da yanayin sa na rashin son yawan magana, DMD kyakkyawa ne ajin qarshe kana ganinsa kaga wanda ya haɗa jini da larabawa ko kuma indiyawa.
Ba tare da ya staya shafa mai ko kuma sanya kaya ba ya nufi kan gadon da towel dake qugunsa, kishingiɗa yayi kansa akan fillow dake jingine da kan gado, ya sanya hannayen sa duka biyu ya tallafo ƙeyarsa yana tunanin rayuwan da suke ciki da kuma qaddaran da ya sauqa kan mahaifiyar su.
Lumshe idanuwan sa da suka koma jajaye yayi a hankali ya furta “Ammi nayi kewanki sosai, ki dawo gare mu Ammi mu koma Canada muyi rayuwanmu kaman baya hankali kwance, I soo much miss you Ammi”.

 

𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚’𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋’𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 – 250 𝟏𝐆𝐁 – 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 500
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 750

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 – 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 – 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 – 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 – 75𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎……

 

WAIWAYE ADON TAFIYA!
Cikakken tarihin DMD!
Asalin labarin…

Alhaji Muhammad Nura mai fata shine asalin sunan kakan su DMD, haifaffen garin Maiduguri ne a local government na Wuba anguwan Askira, Alhaji Muhammadu ya kasance yaro ɗaya tal da Allah ya bawa iyayen sa Malam Nura mai fata da kuma mahaifiyar sa Zainabu wacce ake qira da Yah-gana, ya taso cikin soyayya da qaunan iyaye wanda suka kasance daga cikin yaren bare-bari waɗanda aka fi sani da Kanuri.
Iyayen Alhaji Muhammadu auren dangi suka yi wanda hakan yake AL’ADAH a gare su, mutum ba zai yi aure ba sai ƴar dangin su kuma ta kasance Kanuriya gaba da baya haka ma mace sai mijin ya kasance Kanuri, Alhaji muhammadu tun da ya mallaki hankalin kansa ya nuna yana son wata yarinya a wani yanki Magumeri itama Kanuriya ce amma ba a familyn su take ba, iyayensa sun yarje masa neman ta amma da suka je wajan kakannin sa sai suka nuna basu amince ba an masa mata kuma ƴar gidan yayan maman sa. kasancewan sa yaro mai biyayya da jin magana ba musu ya amince kuma ya rabu da wacce yake so inda ba jimawa aka masa aure da FATIMA da ta kasance yarinyar kawun sa.
Bayan auren su bai wuce da shekara guda ba mahaifin sa da mahaifiyar sa suka yi hastari inda ko shurawa basu yi ba suka ce ga garinku nan (Allah musu rahama).
Kakan sa ya nemi da ya koma cikin Maiduguri ya zauna da Fatima wacce suke qira da Hajja a family house amma sai ya nuna ba haka ba shi yana son zuwa qaro ilimi, kakansa yayi-yayi ya zauna tunda anan Maidugurin ma suna da wadatattun makarantu amma yaqi dan haka sai suka bisu da fatan alkairi sannan ya tabbatar suna zuwa duba dangi, nan Alhaji muhammadu ya kamo hanyar Gombe tare da matar sa Hajja wacce har zuwa wannan lokaci bata taɓa ko ɓatan wata ba.
Sun shigo Gombe cike da sa’a inda basu staya ako wanni yanki na Gombe ba sai Ashaka, kasancewan yana da rufin asiri dan mahaifansa suna da qadarori kuma kamun ya taho ya buqaci wasu daga qadaran gadon sa kuma kakan sa baba-alhaji bai hana sa ba ya basa tunda garin mutane zai je ga kuma iyali.
Gida ya saya musu na rufin asiri, inda yake shiga cikin Gombe dan duba makarantar kaman yanda yayi niya, ya samu wani babban sangaya a nan cikin Gombe yana qara karatun sa in yayi kwana biyu a cikin Gombe ya dawo Ashaka yayi kwana biyu zuwa uku, a cikin wannan halin Allah yasa ya fara sana’ar fata inda Allah ya sawa abun albarka kuma ya karɓe sa, har dai ya siya fili a cikin Gombe.
Bayan dawowarsa Ashaka ya huta suna zaune tare da matarsa Hajja sai ya dube ta yace “Yah-gana na saya mana fili a Gombe saura ginawa in Allah ya yarda kinga sai mu koma can da zama abunmu, ke kin huta kewa na nima na huta kewanki da kuma jigile a hanya”.
Hajja sai tace masa “a gaskiya nikam Alhaji nafi son zaman nan garin sai dai in ka sayawa yaranka amma dai ni zaman nan yafi min”.

Ganin Hajja ta dage sai Alhaji muhammadu ya qyaleta ya cigaba da kaiwa da komowa tsakanin cikin Gombe da Ashaka, wanda ana cikin haka a shekarar su ta farko da zuwa garin Gombe kenan Allah ya azurta Hajja da samun juna biyu, wannan ciki ba qaramin farantawa Alhaji muhammadu rai ya yi ba, sosai yake kulawa da Hajja da abunda ke cikinta.
Tunda cikinta ya girma ta shiga watan haihuwan ta sai Alhaji ya kuma tunkaran ta da maganan komawa cikin Gombe amma nan ma taqi ganin haka sai yabar maganan gaba ɗaya shima ya daina yawaita zuwa Gombe dan ko harkan fata yanzu yana da yaran gida daga Gombe har nan Ashaka da sauran local government na Gombe har ma da wajen Gombe.
Ranar da naquda ya tashi wa Hajja ya ɗauke ta suka tafi asibiti, da zuwansu da haihuwanta duka bai fi minti biyar ba ta santalo yarinyar ta mace mai matuqar kyau dan tana kama da Alhaji kuma shi kyakkyawan gaske ne duk kyawun Hajja bata kama qafan sa ba, suka dawo gida da farinciki nan ƴan barka ke shigowa kowa ya shigo sai ya yabi kyau na yarinyar, ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar Alhaji wato Zainabu amma sai suka ɓoye sunan suna qiranta Yaanah, bayan suna da kwanaki dan har sun fita arba’in nan ciwo ya kama yarinya, ciwon ciki ba ji ba gani duk kyawun yarinya cikin kwanaki ta koma abun tausayi kuma a cikin wannan halin wani cikin ya qara bayyana a jikin Hajja nan dai abubuwa suka taru suka musu yawa sai gaba ɗaya ya ajiye shiga Gombe komai kawai ana masa yana daga gida yana kula da iyalan sa.
Yarinya taji sauqi inda zuwa yanzu take da kusan wata 7 cikin jikin Hajj na wata 6, kwastan suka wayi gari yarinya babu rai wannan rashin yarinya ya damu Hajja inda har ya janyo ta rasa cikin jikin ta, Alhaji yayi jimami na rashin cikin da kuma yarinyan amma ya miqawa Allah lamarin sa dan Allah ne mai bayarwa kuma shine mai karɓa.

Sai da Hajja ta shekara da yin ɓari sannan ta kuma samun wani cikin ta haifi yaranta ƴan biyu duka mata aka sawa ɗaya sunan Zainab ɗayan kuma sunan mahaifiyar Hajja wato Hajara, har yara suka kai shekara 2 Hajja bata kuma haihuwa ba inda ta masta ma Alhaji akan suje Maiduguri ba tare da ya mata musu ba ya miqa amanan ayyukan sa a hannun yaran gidan sa, suka wuce Maiduguri da ƴan biyun su inda suka isa lafiya kowa yayi farincikin ganin su stoho Alhaji-baba yayi ta sa musu albarka sannan yace su kula da bakin mutane akan yaran su, satin su biyu da zuwa zazzaɓi ya bugi ƴan biyu wanda ko lokaci bai ɗauka ba a ranan da Magrib zainabu tace ga garinku, an barta zuwa safe a mata sutura amma kamun gari ya waye itama Hajara tace ga garinku, Hajja tayi kuka har kaman zata bi yaranta dan sosai take qaunar ƴan biyun ta.

Sai da suka kwashe wata guda a Maiduguri kamun suka juyo garin Gombe, suna dawowa basu yi sati ba ciki ya bayyana jikin Hajja nan ta dinga addu’a da amfani da magungunan da baba-alhaji ya bata, wata tara ciff ta haifo yaronta namiji mai kama da ita inda ranan suna yaci sunan kakansa Nura, Alhaji sosai yake son wannan yaron nasa yana da shekara 2 ya ɗauke sa ya kaisa cikin Gombe yana karatun Alqur’ani a sangaya kuma yana zuwa boko, Hajja har da kukanta an rabata da yaronta qarami amma ko takan magananta Alhaji bai bi ba tunda ba zata zauna a cikin Gombe ba to shikuma yaransa za suyi karatu.
Ciki ne ya qara bayyana a jikin Hajja inda bayan wata tara ciff ta kuma haifo yara biyu mace da namiji, ranan suna mace aka sa mata maimuna takwarar matan baba-alhaji namijin kuma aka sa masa Mustapha, yara suna cika shekara biyu Alhaji ya ɗau Mustaphan ya kai cikin Gombe ya sanya shi a makarantar da yayan su Nura yake wanda shi Nura a lokacin shekarun sa huɗu 4.
Hajja haka ta zauna daga ita sai maimuna a Ashaka duk da Maimuna ma ba zaman gida take ba Alhaji ya sata a makaranta a nan cikin Ashaka.

Nura na da shekara goma ya sauqe Qur’ani mai girma kuma lokacin yana qoqarin shiga secondary, Mustapha ma a lokacin yana da shekaru 8 amma ya sauqe kuma yana qoqarin shiga junior secondary shima, Maimuna ta kusa sauqewa kuma itama tana qoqarin shiga junior secondary, Hajja bata sake haihuwa ba shi kuma Alhaji dukiya sai gaba-gaba yake dan zuwa lokacin filayen sa a cikin Gombe ba zasu irgu ba kuma tun bayan barowansu Maiduguri basu koma ba har yanzu da Nura ke neman shekara 11.
Nura ya kasance yaro ne mai sanyin hali da jin magana ga gudun zuciya, haka Maimuna akwai gudun zuciya ga ta shiru-shiru, saɓanin Mustapha da yake yaro mai hazaƙa fa qoqari amma yana da zuciya ga kuma kafiya, ba shi da reni amma ba ya storo kuma ba maganan kowa yake ji ba.
Maimuna na gama primary Alhaji ya ɗauko ta ya kawo cikin Gombe makarantar kwana ta fara secondary, Hajja ganin haka sai ta saduda ta yarda zata zauna cikin Gomben ita ma ganin za’a rabata da yaranta duka.

FAN’S KU RIQE GODIYAR KU, UWAR BATOORL SHARHI KAWAI TAKE BUQATA.

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR’S ANNIVERSARY

JAHILCI KO AL’ADAH? FAN’S CLUB 🤝💙one lurv masu daraja habibties, Uwar batoorl na matuqar qamnar ku da sharhinku da soyayyan ku ga wannan littafi.
Dama waɗanda basa group ɗin amma suna sharhi to tabbas Uwar batoorl na soyayyan ku🤝

 

FAN’S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

💋💋 امى بتولة💋

Not edited ayi haquri da mistake’s.

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 33_34

 

Hajja na dawowa cikin Gombe Alhaji ya sauyawa Maimuna makaranta daga na kwana zuwa na aje a dawo, Nura ma ya dawo gida amma shi Mustapha yaqi yace a makarantar zai zauna.

Rayuwa na tafiya abubuwa da yawa sun faru masu daɗi da marar daɗi inda a cikin wannan halin Allah yawa matar Alhaji-baba rasuwa inda saqon na riskar Alhaji ya tarkata iyalansa duka suka nufi Maiduguri cikin motan su na kansu dan yanzu Alhaji ba abinda bai mallaka ba,sun isa lafiya sai da suka share wata guda har da ɗori kamun suka juyo kasancewar hutun yaran ya qare inda a hanyar su ta shigowa Gombe suka yi hastari kuma duka sunyi rauni, kwanansu biyu 2 a asibiti Allah yawa Maimuna rasuwa, wannan rashin ya jijjiga gaba-ɗaya iyalan Alhaji barinma Mustapha da ke staninin qaunar ƴar uwar sa kuma shaquwa mai qarfi ne tsakaninsu duk da kasancewar basu zauna mai stayi a waje guda ba.

Mustapha na kammala secondary Alhaji ya basa zaɓin inda yake son cigaba da karatun sa, shi kuma sai ya zaɓi India.
Alhaji ganin zuwa lokacin ya girma tunda ya kai shekaru sha biyar 14 sai ya amince ita kuma Hajja ba abinda tace sai addu’an Allah bada sa’a kuma ya kula, Nura dai ya zaɓi qarisa karatun sa a Maiduguri kuma Alhaji da Hajja sun amince da hakan sannan sunji daɗin hakan inda ya tafi Maiduguri yana karatun sa yana zaune a family house kuma hakan ba qaramin daɗi yawa baba-alhaji ba duk da zuwa yanzu ya stufa kucuf.
Mustapha anshirya masa komai ya tafi India yana karatun sa hankali kwance, Hajja zama ba yaranta abun bai mata daɗi ba amma kuma ba yanda ta iya a yanzu kuma tasan bata isa tace zata koma Ashaka ba haka ta haqura.

Sai da aka shekara biyar kamun Mustapha yazo gida inda ya tarar yayan sa ya jima da dawowa gida dan ya kammala degree da master’s nasa akan kasuwanci((business), Hajja tawa Mustapha faɗa sosai akan rashin zuwansa amma ya bata Haquri abinka da uwa da ɗa tuni ta haqura, nan suka ɗugunzuma suka tafi Maiduguri, suna zuwa baba-alhaji yace sam sai sun zaɓi mata a cikin yaran dangi sunyi aure kowa ya koma da mata barinma dai Mustapha dake garin mutanan da basu damu da AL’ADUN musulunci na rufe jiki ba, tunda ya kai shekara ishirin to ya kai riqe mata, Nura tunkan a iso kansa ya bayyana cewar yana son yarinyar Gwaggon sa mai suna Maryam dan tunkan ya koma suke soyayya, wannan abu ba qaramin daɗi yawa baba-alhaji da iyayen su Nura ba nan kuwa aka tsayar da komai tunda abu na gida ne kowa yasan AL’ADUN yaren nasu da yanda suke gudanar da biki sai aka aje nan da wata huɗu kamun Maryam ta kammala secondary.
An kaɗa an rawa da Mustapha amma yaqi yace shi dai a masa uzuri tunda saura masa shekara guda to sai ya kammala zai dawo ya dubi mata inyaso sai ayi auren, saboda qaunar da Hajja kewa yaron nata nan ta tayasa roqon baba-alhaji da mijin nata wanda da qyar baba-alhaji ya amince sannan ya jaddada masa kada ya wuce shekara 1 dan ba yanda za’a yi ya ɓata mata sunan zuria’a.

Sai da suka yi mako biyu sannan suka shirya suka dawo Gombe, Nura cike yake da kewar sahibar sa Maryam wacce yake qira da Habibty, amma kasancewan wayayyen zamani muke sai ya saya mata waya wanda zasu dinga gaisawa.
Mustapha tunda suka dawo yayan sa Nura ke masa magiya akan baya so ayi bikin sa bayanan, ganin yayan sa ya damu kuma shima daman yafi qaunar yaga bikin wan nasa sai kawai ya tura saqo makaranta zai qara 2 months aka hutun su, to abinka da harka ta kuɗi nan take makarantar suka yarda tare da bashi daman yin komai na attending class a online.
Akwana a tashi asaran ma rai yau auren Nura da Maryam saura sati biyu, baba-alhaji ya buqaci da su koma cikin dangi ayi auren acan in aangama sai su dawo, suka tattara suka tafi Maiduguri.
Angudanar da shagulgula da AL’ADUN yaren nasu na kanuri kama daga events na Amarya da kuma Ango su Wushe-wushe da dai sauran su, an ɗaura auren NURA MUHAMMAD NURA & MARYAM TIJJANI ɗaurin auren da ɗumbin jama’a suka halarta kama daga abokanayen Nura har da na Mustapha da kuma manyan masu kuɗi jama’un Alhaji, aka kai Amarya ɗakinta wanda yake nasu aduk sanda suka zo garin Maiduguri.
Bayan mako guda ankammala komai Amarya tayi bankwana da mutan Maiduguri suka kamo hanya da su Hajja duka, anan gidan Alhaji dake anguwan federal-lowcost Nura ya zauna da Amaryar sa Maryam a sashin da dama Alhaji ya gina wa ko wannensu sashin sa a cikin gidan.
Bayan sati 1 da dawowan su Mustapha ya shirya ya koma India yaci gaba da karatun sa, mutan Gombe kuma rayuwa suke cikin farin ciki da girmama juna.

Bayan komawan Mustapha India garin Hyderabad, Telangana ana makarantar da yake take.
Watarana ya fito class da abokanan sa yana tafiya ba tare da ya kula ba sai ya buge wata baiwar Allah, juyowa yayi da niyan bata haquri amma kamun ya buɗe baki guard’s nata suka riqe sa suna surutu cikin Indianci wanda duk abinda suke faɗa yana fahimta, idanuwan sa ya ɗago dan ganin wacce ya buge “fatabarakhallahu ahsanul kaliq” shine abinda bakin sa ya furta ganin yarinya kyakkyawar gaske wacce kana ganinta kaga ba-indiya kuma ƴar mai kuɗi.
Fara ce sol, mai dogon hanci da kuma stayin gashi ga qaramin bakin ta, kayan dake jikinta kaɗai ka gani kasan ita musulma ce ba hindu ba, sanye take da riga da wando indian dress mayafin da yake babba ta rolling nasa yanda ba bar shape nata ko gashinta a waje ba, shigarta komai na mutunci ne sai dai abinda baza’a rasa ba abinka da AL’ADAR qasar da take.
Mustapha bai ce komai ba sannan guard’s nata basu sake sa ba, buɗe baki yarinyar ƴar kimanin shekaru 15 tayi tace “ku sake sa bada saninsa bane” cikin harshen Indianci.
Guard’s ɗin sake sa suka yi suna nuna sa da yasta alaman jan kunne, shi dai har lokacin bai ce komai ba dan Mustapha akwai zuciya, yarinyar ce ta dube sa da murmushi fiskanta tayi magana da English “kayi haquri da abinda suka maaka”.

Sai lokacin Mustapha ya samu daman magana, cikin harshen Indianci yace mata “bakomai”.

Cike da mamaki ta dube sa tace “Wow! So kai ba-indiye ne?

Girgiza kai yayi yace “Nigerian” ya miqa mata hannu alaman su gaisa.

Kallon sa tayi a karo na biyu da mamaki ganin shi ɗan Nigeria kuma yana bata hannu bayan ita ba muharrmar sa ba, a zuciyar ta tace “wannan dabi’an qasar tamu JAHILCI NE KO AL’ADAH oho musu duk wanda yazo sai ya ɗau banzan AL’ADAN su.
Maganan da yayi ne ya kaste mata maganan zuci da take yi.

“am i not welcome?”

Murmushi ta masa tace “you’re welcome, amma addini na ya hana gaisawa da namiji”.

Wani abu ne ya dirar masa a zuciya tare da mamaki dan tabbas ta burgesa ya buɗe baki zai yi magana sai qira ya shigo wayanta, ɗauka tayi ta kara a kunne tayi magana cikin Indianci wanda kana ji kasan da mahaifiyarta take magana, tana gama wayan ba tare da ta bi takan Mustapha ba ta juya ta tafi guard’s nata na take mata baya.

Tundaga wannan rana har aka kwashe wata ɗaya, biyu har uku bai qara ganin giftawanta ba, kuma gashi soyayyan ta ta riga ya masa mugun kamu dan yarinyar ta shiga ransa shi ko takan AL’ADAN su na dole sai ka auri ƴar dangi kuma Kanuriya ba bi ba son baiwar Allahn nan yake bilhaqqi, ana haka kwastan ranan ya fita yawo da abokanan sa sunje wani Cafe suna zaune kowa yayi ordern abinda za’a basa, waitern ne ya tambaye sa mai yake so? Buɗe baki yayi ya faɗa sai dai da mamakin sa muryan ta ya jiyo a gefe itama tana faɗin “biryani” juyawa yayi yaganta tare da qawayen ta amma duka cikin su ita ce mai shigen mutunci dan yau ma irin shigan ranan tayi.

Yana zaune yana cin biryanin sa ganin suna qoqarin barin wajan sai ya miqe ya qarisa wajan su yana musu sallama, ita kaɗai ta amsa dan sauran kallonsa suke da mamaki, murmushi tayi tace “You again? Sorry that day i gone without saying byee, my Ammaah called me that’s why”.

Murmushi Mustapha yayi yana mamakin meeyasa take son masa turanci bayan ya nuna mata yana jin Indianci, roqon ta yayi ta basa numbern ta, ba tare da tayi musu ba ta basa dan tun kallon sa da tayi ya burgeta, domin Mustapha ya ɗauko kyawun Alhaji da na Hajja duka.

Cikin watanni huɗu masu kyau soyayya mai mugun qarfi ya qullu stakanin Mustapha da Maimoon, mastalan da suka fara samu tun farko daga mahaifiyar ta Hindu ce, dan Maimoon yarinya ce ga shugaban makarantar da Mustapha ke karatu, University of Hyderabad, Telangana.
Dr.Mufaddal shine sunan mahaifinta, babban mai kuɗi ne da India gaba-ɗaya keji da shi ba iya Hyderabad ba, matar sa ɗaya Hindu da yarinyar su Maimoon wacce suke wa soyayya ta duniya gaba-ɗaya kasancewan ita kaɗai suka haifa, su musulmai ne duk da asalinsu ƴan India ne amma ilimin addini ya sanya ba suyi wasti da abinda addini ya umurta ayi ba.
Mahaifiyar Maimoon ta dage nan duniya yarinyar ta ba zata auri ɗan Nigeria ba, dan ita a AL’ADAN su basa auren baqin fata, hukuncin mahaifiyar ta shi mahaifinta yabi yace ba zata auri ɗan Nigeria ba, wannan hukunci na iyayen nata ba qaramin tashin hankali ya haddasa mata ita da Mustapha ba dan har sai da ta kwanta ciwo, kusan wata guda tana asibiti akan soyayyan Mustapha wanda mahaifinta Dr.Mufaddal ganin yana qoqarin rasa yarinyar sa akan abinda bai taka kara ya karya ba nan yace ya amince, da amincewar mahaifinta ko kwana biyu bata qara yi a asibiti ba ta warke nan yasa ta aiko masa Mustapha, cike da ladabi ya amsa qiran Mahaifin Maimoon nan ya faɗa masa ya basa yarinyar sa inyayi ya turo iyayensa ayi baiko(saka rana), cike da farin ciki ya tashi ya tafi.

Yayan sa Nura ya fara qira ya sanar masa da komai cike da ɗimbin damuwan jin irin son da yarinyar kewa Mustapha ya ce “kana da hankali kuwa? Zaka sa yarinya ta faɗa sonka bayan kasan irin AL’ADAN mu, kaima ka sani ko mutuwa za kayi ba iya baba-alhaji ba ko Alhaji da Hajja ba zasu yarda ba, daga ni ba mai goyon bayan ka akan wannan lamari da ka kawo”.

“Yaya gaskiya nikam bazan iya da wani AL’ADA ba, wacce nake so ita zan aura inma menene sai su bari daga baya insunga bata da hali mai kyau sai su saka ni auren Kanuriyan, wannan yarinya yaya da ka ganta ba kaman sauran ƴammatan indiyawa bane ba ruwanta da wani AL’ADUN indiyawa da ya saɓawa addini, ranan na taɓa gwada ta amma har muka kusa samun damuwa tayi ta surutu wai wannan abinda nake yi JAHILCI KO AL’ADAH za’a qira sa”.

Nura a ɗaya ɓangaren yace “shikkenan fatan alkhaeri Allah kawo komai da sauqi ya kuma tabbatar da alkhaeryh”.

Bayan kwana biyu ya qira Hajja ya sanar mata, nan ɗin ma wani faɗan ya tarar.
“Hajiya wallahi yarinyar na so na kuma mahaifanta sun amince, ai ko dan amincewar su ya kamata ku amince min tunda dai AL’ADUN su sunfi naku stauri kasancewar su indiyawa” faɗin Mustapha da ke kare da waya a kunne.

“Mustapha ba indiyawa suke ba koma menene ni ba ruwana kuma karka bari maganar nan yaje kunnen mahaifinku balle akai ga kunnen baba-alhaji, kana gani dai kuma kana sane sai da nasa baki kamun ya barka kai ma ba’a yi aurenka ka koma da mata ba, kuma ko tafiyanka wannan qasar sai da aka sha daru da shi, to karka yarda magana ya kai kunnen sa ni bansani ba kuma karka sako ni ciki, nasan duk abinda kake qullawa ɗan uwanka yana sane to kuje ku fama” Hajja na gama magana ta kashe waya kittt.

Dafe kai Mustapha yayi gaba ɗaya ya rasa yaya zai yi kansa ya qulle, qira ne ya kuma shigowa wayansa ya duba ganin ita ce sai yaqi ɗauka.
Abubuwa sun taru sun masa yawa ga kuma final-year exam’s nasu dake kusantowa wanda bai wuce watanni biyu ya rage musu ba kuma sunayi ba jimawa makaranta zata sallamesu kowa ya kama hanyar sa.

Wasa-wasa har aka yi sati guda baya ɗaukan qiran Maimoon, abubuwa ne suka kacame masa dan ko ya ɗau qiranta baisan me zai ce mata ba.
Yana zaune a wani ɓangare na cikin makarantar kwastam yaji an rungume sa, juyowa yayi amma bai sha mamakin ganin ita ɗin ce ba, nan ta dinga masa kuka akan me yake shareta? Ba tare da ya ɓoye mata komai ba ya faɗa mata halin da ake ciki, nan suka rarrashi juna suka yi hira ya rakata har gida ya wuce gidan da yake.

Bayan Papanta ya dawo ba tare da ta ɓoye masa komai ba ta faɗa masa abinda iyayen Mustapha suka ce, Dr. Mufaddal nan ya lallaɓata ganin tana kuka.
Ko da mahaifiyar ta taji abinda ke faruwa nan tayi hamdala tace “shikkenan kowa ya huta, ita ta auri ba-indiye ɗan uwanta shima yaje can ya auri ƴar Nigeria ƴar uwar sa”.
Papanta ya qirata ya bata haquri saboda abinda mahaifiyarta ta faɗa, su haqura Allah bai yi zasu auri juna ba. Nan fa hankali ya tashi dan ko makaranta taqi zuwa qarshe ma ba tare da kowa ya sani ba har guard’s nata ta fice ta tafi gidan kakarta mahaifiyar mamanta dake cikin Bangalore.
Dr. Mufaddal suka neme ta suka rasa, har ya kori wasu daga cikin masu staronta dan aganinshi basu da hankali tunda zata fita ba tare da sun sani ba, ya nemi Mustapha ko tana wajan sa shima yace baisan bata gida ba, nan fa hankalin su ya tashi dan duk basu kawo wa ransu tana Bangalore ba.

 

FAN’S KU RIQE GODIYAR KU, UWAR BATOORL SHARHI KAWAI TAKE BUQATA.

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

Wannan shafi gaba ɗayansa sadaukarwa ne gare ku iyayenmu mata❤️ Allah saka muku da aljanna, Allah ji qanku ya muku rahama, Allah qara ma ko wacce mace haqurin zama da mijinta ya kuma bata dama da ikon masa biyayya, Allah ya albarkaci zuri’a duniya da lahira.

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 35_36

 

Ko da taje nan ta faɗawa kakarta duk abinda ake ciki na abunda mahaifiyarta take faɗa.
Faɗa kakarta ta dinga yi kaman zata ari baki.
Sai da tayi sati biyu a gidan kakanta, ba tare da tayi waya da iyayen ta ko Mustapha ba dan wayan nata kashe shi tayi ta baro sa a gidan su, saboda tasan in tana waya da Mustapha za’a san inda take ta wajan shi.
Shiryawa suka yi suka kama hanyar Hyderabad da kakarta, ko da suka isaa kakarta ta dinga aikin surfawa yarinyarta masifa tunda tasan ba laifin Papa bane Ammaan ta ke hanawa, nan tasa Papa ya aika qiran Mustaphan saboda shi da kansa take so yaje Nigeria akan maganan auren.
Qiran Mustapha tayi bayan ya gama mata faɗa akan tafiyanta ya ɗaga masa hankali sai ta bashi haquri nan ta faɗa masa Papa na nemansa, suka yi waya suka yi sallama.

Mustapha yazo ya samu Papa nan ya tambaye sa halin da ke ciki ba tare da ɓoye-ɓoye ba ya faɗawa Dr. Mufaddal komai akan abinda iyayen sa suka faɗa, nan yace ya basa address na gidan nasu zai je, amma sai kakar Maimoon tace ya bari in Mustaphan ya gama exam’s su tafi tare har da ita, sannan ta kuma yiwa iyayen Maimoon faɗa “shi aure da kuke gani nufi ne na Allah, in Allah yaso kuma rabo ya ranste sai ku mutu ayi, ko ayi ba yanda kuka iya kunya ta kasheku daga baya”.
Sallaman Mustapha Papa yayi, sannan ya sanya aka maida kakar Maimoon (Aliyah) Bangalore.

Bayan wata biyu su Mustapha sun gama exam’s, nan aka dinga shirin graduation nasu wanda kowa iyayensa zasu halarta, mutanen Nigeria sun samu isowa suma, Nura, Hajja, Maryam(matar Nura) sai Alhaji.
Tunda suka zo Hajja ke qara jaddada masa jan kunne akan kar ya kuskura yayi wannan magana balle mahaifin sa yaji, Nura da yasan duk abinda ake ciki har da maganar da yayi da Papa nan shima yake kaffa-kaffa yake addu’an Allah kawo wa ɗan uwansa komai da sauqi.

Ranar graduation akayi hidindimu, kama daga yaye ɗalibai da wasanni da al’adun makarantu yayin sallaman ɗaliban su.
Mustapha da familyn sa suna zaune a qayataccen wajen zaman da yake nasu shi da iyayensa, Alhaji ke magana “yanzu tunda an kammala komai yau gobe zamu wuce kai kuma yaushe zaka biyo mu?

Qasa yayi da kai yace “Alhaji sai nan da wata guda zamu gama kammala komai”.

“To Allah ya kaimu, ka tabbatar ka gama komai akan lokaci ka dawo tunda kana sane da batun baba-alhaji kuma so ake a hada bikin naka da na ƴan uwanka acan Bornon…”
Maganan da Alhaji yake yi ya dakatar ganin wata yarinya da tazo ta tsaya gefen Mustapha.

Ba iya Mustapha ba, hatta Nura da Hajja sai da suka sha jinin jikinsu domin kana ganin yarinyar kasan ita Mustapha ke so, Maryam matar Nura tayi qasa da muryanta tace “mijin habibty wannan baiwar Allahn tamun kyau Allah sa budurwan Mustapha ce”.
Nura dai ya kasa bata amsa dan dukan su idanuwan su na kan Alhaji da jin abinda zai faɗa.
Maimoon da ta tsaya gefen Mustapha ganin dukansu su kalleta su kalli babban mutumin da ta bashi matsayin mahaifin Mustapha, sai kawai ta stugunna tana gaida Alhaji, shi kuma ya amsa cike da mamaki yanawa Mustapha kallon neman qarin bayani.
Gaishe da Hajja tayi ta amsa ba yabo ba fallasa, Nura ma suka gaisa fuska a sake, Maryam ma suka gaisa tana mata murmushi dan ita Maryam har zuciyarta Maimoon ta burge ta.
Mustapha yasha jinin jikinsa sosai dan kallon da Alhaji yake masa kaɗai yasan akwai yinta, miqewa yayi ya bar wajan sai Maimoon ta biyo bayansa, su Alhaji kuma binsu da ido suka yi duka.

Kallonsa tayi ta fara magana cikin indiyanci “iyayenka dama sunzo baka gayamun ba?

“Kiyi haquri, yanzu kije gida za muyi magana daga baya”.

Kallon sa tayi sai ta juya tayi tafiyanta, shi kuma ya koma wajan zaman nasu.
Alhaji kallonsa yayi yace “ina sauraranka”.

“Alhaji me ya faru? Faɗin Mustapha da ya waske kaman baisan abinda Alhaji ke nufi ba.

“Mustapha mun fara wasan reni da kai? Inajinka wacece ita?
Hajja kau da kai tayi, Nura kuma yayi qasa da kai ya ciro wayan sa yana dannawa, Alhaji duk yana kallon su kuma ya fahimci sun san komai da ke tafiya “Mustapha ina sauraranka”.

“Alhaji ba komai dama…dama…”.

Cikin qufula Alhaji yace “Mustapha dama me? Ko ba zaka iya magana bane?

“Alhaji wacce zan aura ce, kuma dama babanta ya…..”

Cikin ɓacin rai Alhaji ya dakatar da shi “Mustapha dama abinda kake qullawa anan qasan kenan? Dan na baka damar zuwa nan karatu ko? To bari kaji tun wuri ka aje maganan nan a gefe kana komawa kaje borno ka zaɓi mata a haɗa aurenku ayi da ƴan uwanka, karka bari ma baba-alhaji yaji zancen nan”.
Juyawa yayi yana qarewa Nura da Hajja kallo, ƙwafa yayi yace “duk abinda Mustapha yake qullawa da saninku da kuma goyon bayanku da ɗaurin gindi da kuka masa, kai Nura ka fita idona ka kama kanka, Hajiya karki bari labari yaje kunnen baba-alhaji da ba zaku kwashe ta daɗi ba kema kin sani” yana gama magana ya miqe yabar wajan.

Sai sannan Hajja ta samu daman yin magana “kaga abinda nake gudu ko? Ni na sani kome zaku aikata za’a ce nice na ɗaure muku wajan zama barin ma dai kai Mustapha amma babu komai”.

“Hajiya kiyi haquri ki bimu da addu’an alkairi” faɗin Nura da ke cike da tausayin ɗan uwansa.

“Nura in banyi haquri ba ya zanyi da ku? ‘ya’ya ne Allah ya bani duk kuma sun tafi sai ku biyu kawai kuka tsaya Allah ya nufa, to ai haquri da ku ya zamamun dole Allah dai ya jiɓanci lamuranku ya tabbatar da alkairi a rayuwanku, amma Nura ka dinga yiwa Mustapha faɗa, dan hanyar da ya ɗauko ba mai ɓullewa bane”.

Washegari su Hajja suka tattara suka koma Nigeria inda suka baro Mustapha akan zai taho daga baya amma da qyar Alhaji ya yarda bayan ya kuma ja masa kunne.
Sai da ya ɗiba sati basu yi magana da Maimoon ba tana fushi akan bai faɗa mata iyayensa sun zo ba, da qyar dai yaje har gidan su ya lallaɓa ta sannan ya mata bayanin halin da ake ciki ba tare da storo ko fargaba ba tace bákomi ita dai tana son shi.
Mahaifinta ta faɗa wa abinda ke faruwa amma kasancewar sonta da yake yi shima ya amsa ba komai zasu tafi Nigerian tare da Mustapha.
Bayan ya kammala komai da komai da zai yi suka kamo hanyar Nigeria da Mahaifin Maimoon da kuma kakarta.

Bai ma tunkari garin Gombe da su ba dan ya tabbata ba za su shirya da Alhaji ba dan haka sai suka yi Borno state, sun isa lafiya inda baba-alhaji yaji daɗin ganin sa amma yana mamakin mutanen da yazo tare da su.
Tarba mai kyau akawa kaka-Aliyah da Dr. Mufaddal duk da ba wanda yasan me ke tafe da su, sai bayan sun huta sannan washegari suka nemi yin magana da baba-alhaji.
Bayan sun gaisa Dr. Mufaddal ya fara zayyano abun da ya kawo su, cike da haquri yake magana dan Mustapha ya faɗa masa komai daga wajan stohon ne.
Baba-alhaji da ya zauna turus kaman an shuka dusa kallo kawai yake bin Dr. Mufaddal da shi na jin zancen da yake yi.
Baba-alhaji, farin dattijo stoho wanda ya stufa cukuf amma kana ganinsa zaka san da sauran qwarin sa, buɗe baki yayi ya fara magana “To to madallah naji zancen ku da kuma buqatanku amma ina mai baku haquri anriga an masa mata”.
kaka-Aliyah ce tayi saurin taran numfashin Dr. Mufaddal dake qoqarin magana ta hanyar cewa “ai kuwa sai dai a haɗa masa biyu dan kuwa jikata ta gani tana so, mu nan da ka ganmu ma da shirin mu muka zo”.

Baba-alhaji cike da masifa yace “sai inga mai aurawa yaro na wata can ƴar garin kafurai”.

“Yanda kake musulmi a wajan Allah haka muke duk ɗaya wataqila ma mun fiku imani dan haka in Allah yasa za’a yi bikin nan sai ka mutu anyi ni da ka ganni nan ba ruwana da shiga tsabgan abinda Allah ya qaddara dan in yazo da qarar kwana sai mutum ya mutu kuma qudurar Allah ta tabbatu” kaka-Aliyah ta faɗa itama cike da masifa dan kana ganinta kaga masifaffun tsofaffin indiyawa”.

Baba-alhaji masifa ya dinga yi, daga qarshe dai kwana kawai suka yi suka yi shirin tafiya, Mustapha ko haɗuwa da baba-alhaji yaqi yi tare suka fito da su kaka-Aliyah suka nufo Gombe kuma, kaka-Aliyah sai sababi take a mota tana bawa Mustapha haquri ya kwantar da hankalinsa in dai da ranta sai ya auri Maimoon, Dr Mufaddal da ido kawai yake binsu dan ba shi da ta cewa.

Suna isa cikin Gombe suka yi gidan Alhaji cikin rashin sa’a kuwa suka tarar Alhaji na gida, Hajja ta karɓe su hannu bibbiyu, Maryam matar Nura da take ji kaman Amaryan aka kawo dan daɗi sai nan-nan da su kaka-Aliyah take yi.
Alhaji dai da ido yake binsu bai ce komai ba dan yasan kwanan zancen amma bai da labarin zuwan su Maiduguri.
Bayan sun huta da dare nan ma kaka-Aliyah ce ta fara magana, tunda ta fara bayanin ta mai kama da masifa dan haushin baba-alhaji da take ji, kowa a palourn ido ya zuba mata, Nura kuwa sai raba ido yake ya kalli wannan ya kalli wannan.
Sai da ta gama jawabin ta sannan Alhaji ya numfasa yace “ina mai baki haquri maama amma tunda har yaron yayi dabaran kai ku can Maiduguri amma baba-alhaji yaqi aminta to banda yanda zan yi dan dukkanmu masu biyayya gare sa ne kuma wannan AL’ADA tamu tun kakanni ban isa nace a’a ba”.

Cikin taqaici kaka-Aliyah da idanuwanta ke kan Alhaji tace “aikam dama gado ba karambani ba dole dai kace haka amma ko kunqi ko kunso in Allah ya nufa auran nan za’a yi sa kuma sai duk ku mutu, amma jikata inda alkairi to sai ta auri wanda take so”.

Sai yanzu Hajja ta buɗe baki tayi magana “kuyi haquri Allah ya bata miji nagari” wani kallo Alhaji ya wasta ma Hajja wanda ya hanata qarisa maganan dan tasan cike yake fam da haushinta, duk a ganinsa itace ta ƙulla komai ko kuwa da saninta yaran suke komai.

Dr. Mufaddal da kansa ke gefe ba abinda yake tunani sai yarinyarsa ɗaya tilo da irin soyayyan da take wa Mustapha, numfasawa yayi kamun ya fara magana “Alhaji ina mai baka haquri dan Allah dai a dubi lamarin nan, yarinyar mu tanada ilimi dai-dai gwargwado boko da addini duk da kasantuwar mu ɗin indiyawa ne amma ba inda muka gaza ta neman sanin addinin Musulunci, yaro na sonta itama tana son shi dan Allah a duba lamarin, inma kuɗin aure ne ko wani abu mu mun yarda zamu biya sadaki kaman yanda ake yi a al’adance a qasar mu”.

Kamun Alhaji yace wani abu kaka-Aliyah ta tari numfashin sa nan ma, ta hanyar cewa “a’a kaga Mufaddal karka wani roqesa duk ka qyale su, in Allah yace za’a yi auren nan to in Allah yaso ya yarda za’a yi kuma su mutu, to dama rabo kam wa ya bari? Ai in Allah yaso sai kaga su da kansu sun ladabtu sun ɗaura”.

Alhaji da zuwa yanzu ya fara qufula sai yace “na baku haquri Allah ya mai da ku lafiya” yana gama magana ya miqe ya fice a palourn.

Hajja ce ta basu baki ta basu haquri sannan ta qirawo Mustapha yawa Dr Mufaddal jagoranci har zuwa ɗakin da aka ware masa masauqin sa, itama kaka-Aliyah aka kaita nata masauqin.

Tunda Hajja ta shigo ɗakin Alhaji ya haɗe fiska ya juya mata baya,ganin haka tasan dama za’a rina wai kwando da zubar da ruwa, zama tayi ta fara basa baki akan batasan abinda ke faruwa ba, Alhaji tashuwa yayi ya dinga mata masifa da faɗa ita ta ɗaure wa yaran wajan zama “Fatima kece kika basu wannan fiskan, tunda baba-alhaji ya nemi ayi auren Mustapha ya koma da matar sa amma yaron nan yaqi to nasan akwai abinda yake shiryawa, kema kika zo kika sanya baki har aka barsa ya tafi haka nan kinga kuwa da saninki yake aikata komai dan kece kikama nuna masa hanyar tunda mastayinki na uwa kamata yayi ki sanya ayi bawai a bari ba, to ki buɗe kunnuwanki kinjini da kyau dan in anyi duniya dan Manzon Allah SAW to Mustapha bashi da mata sai Asma’u dan tunda ya nuna nashi yarintan da rashin hankalin to ya daƙilewa kansa damar zaɓar mata kenan, baba-alhaji ya zaɓa masa kuma in Allah ya amince aure nan da sati Uku masu zuwa ko ya shirya ko bai shirya ba, ina fatan kin fahimta?”

Ajiyan zuciya Hajja ta sauqe sannan ta miqe ta haura gadon ta kwanta abunta ba tare da tace komai ba “dan wannan inda sabo to tabbas an saba wai karuwa da cutan qanjamau, indai muddin mace zata tsugunna ta haihu to fa sai dai ta toshe kunnenta kuma ta kau da ido dan akan yara ba abinda ba za taji ba wai ɗan kuka mai jawa uwarsa jifa, wani uban daga randa kika ɗauki ciki shikkenan halayya daban-daban za ki dinga gani, salo iri-iri kama daga hantara, wani rashin kulawa, wani daga ranar an qaurace miki kai wani ma ya dinga jin haushin ki kamar kece kikawa kanki cikin dan wannan AL’ADA ce mai kama da JAHILCI ta maza, a yayin da kika haihu kuma shikkenan duk laifin duniya ke za’a ɗaurawa in yaro yayi ba dai-dai ba dan babu mai miki uzurin cewa ba halinki bane koko ke kina naki ƙoƙorin, amma a haka in Allah bai shirya maka ba sai kaga wani ɗan ya tashi amma kuma ba shi da abin renawa irin mahaifiyar sa, to Allah ka kyauta mana ka bamu shiryayyu, dan mazajenmu sai a hankali kawai sai addu’a ko kaɗan ba ko wanni namijin ne yasan wannan zafi da ciwo na ɗaukan ciki da haihuwar ciki ba, su yara kawai suke gani basu san ita uwa tasan mai ta ɗan-ɗana ba, mu mata sai dai godiya ga Allah da yayo mu kuma ya mana wannan baiwa ta ɗaukan ciki, haihuwa da kuma ciwon al’ada(period) sannan ya jarabce mu da mazaje daban-daban wanda wasu daga cikin su basa duba wannan raunin namu, Allah ka qara mana haquri sannan ka ci-gaba da bamu dama da ikon cinye waɗannan jarabtar tamu ta hallayar wasu mazan..” muryan Alhaji ne ya katsar mata da zancen-zuci da take kan yi.

“Fatima nayi magana kin mini shiru, wato ga mahaukaci na zance ko? Cewar Alhaji da zuwa yanzu ya sake fiska ya kuma tashi ya zauna.

Miqewa Hajja tayi tace “kai ne mahaifin sa sannan kuma ka yanke hukunci, ko so kake na ja da hukuncinka na kuma yin wani laifin? Ai magana ta ƙare Allah kaimu nan da sati uku ya kuma tabbatar da alkhaeryh ya basu zaman lafiya da zuri’a masu albarka shine kawai”.

“To su kuma mutanen da ya yayuɓo yazo da su ya za’a yi dasu?

Murmushi Hajja tayi tace “to ai kuma aikin gama ya riga ya gama wai karuwa da cikin shege, ba wani sauran magana tunda ka sallame su kuma ka basu haquri”.

Kallonta yayi yace “yanzu dai wani shawara za ki bada? Ga lamari ya isa gaban baba-alhaji, gaskiya yaran nan akwai rashin hankali yanzu sunsan mutum da stufa Allah kaɗai yasan me baba-alhaji zai yanke”.

Wannan karon ma murmushin Hajja tayi tana faɗi a ranta”sai da lamari ya lalace sannan za’a nemi shawarata maza, maza kenan to Allah ya kyauta” a fili kuwa cewa tayi “Alhaji banda abun cewa sai dai fatan alkairi Allah rufa asiri”.

“Ameen Fatima, nikam ma maganan stohuwar nan nake qara juyawa da kyau fa”.

Kallonsa tayi da alaman tambaya “wacce stohuwa?.
“Haba Fatima kema kinsan wa nake nufi fa, akwai wata wacce ta wuce baqin da Mustapha ya yayuɓo, amma fa kinsan gaskiyar matar nan na cewa rabo na iya kisa, yanzu in Allah ya qaddara sai mu mutu kuma ayi su zauna, yanzu dai sai mun saurari baba-alhaji”.

“To Allah ya kyauta” faɗin Hajja da ta kwanta cike da alhinin abinda ke faruwa.

Washegari sassafe Dr. Mufaddal ya fito a shirye akan kaka-Aliyah ta fito su tafi amma tace bata san zancen ba, ai gidan surakanen jikarta ce ba ita ba tafiya da sassafe haka kaman an korata, Papan Maimoon ba don yaso ba ya tsaya suka karya har sai da hansti tayi kamun suka yi sallama da su Hajiya da Alhaji inda kaka-Aliyah ke kan maimaita ma Alhaji sai jikarta ta auri wanda take so, har airport Mustapha ya kai su, gaba ɗaya kunyan su yake ji amma Dr. Mufaddal ya nuna bakomai haka Allah ya qaddara dama.
kaka-Aliyah kallon Mustapha tayi tace “jikana kar ka damu in Allah yayi duniya dan Manzon sa to ba mai hanaka auran jikata sai shi Allah da kansa, dan haka ko ma sunqi yarda ni nan zan sanya a ɗaura maka aure da jikata in yaso su kashe auren in sun isa”.
Cikin girmamawa da aminta da maganan stohuwar yace “to kaka Allah ya mayar da ku lafiya”.
Jirginsu na tashuwa mustapha ya juya gida, yana shiga Alhaji na qoqarin fita shi kuma, kallo ɗaya ya yiwa Mustapha ya kau da kai ya shige motar sa aka buɗe masa gate ya fice, sai da Mustapha yaga fitan mahaifin nasa kamun ya shige cikin gidan.
A palour ya tarar da Hajja sai qarasawa yayi gefenta ya zauna kansa a qasa, Hajja kallonsa kawai tayi ta girgiza kai ta miqe ta bar palourn, mustapha kuma ganin haka sai shima ya miqe ya wuce ɗakin sa zuciyansa cike fal da damuwa ga kuma shawari da zuciyarsa ke kista masa.

Su kaka-Aliyah sun koma India lafiya inda guard’s na Papa suka zo ɗaukan su tare da Maimoon, tun a mota Maimoon ke ta ɗaukin jin ya su Papanta suka qare da dangin Mustapha, kaka-Aliyah cikin tausayin jikar nata da soyayyan da take wa Mustapha ta dubeta cikin harshen su ta ce “Maimoon na raba ki da ɗaurawa ‘da namiji soyayyan duniya, ba wai na hanaki soyayya ba a’a amma dai ki sassauta dan kaman yanda kika ga network ba shi da tabbas to gwanda network akan namiji ki tsagaita Maimoon”.
Kallon kaka-Aliyah tayi idonta cike da ƙwallah ta ce “nima so nake na rage amma na kasa kullum cikin qara jin sonsa nake a zuciyata, in Mustaphan bai aure ni ba zan iya mutuwa”.
Tausayin Maimoon ne ya cika zuciyan kaka-Aliyah da kuma Papa dake mazaunin gefen driver, duk addu’a suka bita da shi a zuciyansu dan abun sai dai addu’a.
Sun isa gida, Hindu ta tare su da ya ake ciki? Amma daga kaka-Aliyah har Papa ba wanda ya bata amsa, ganin haka sai taja baki tayi shiru, har aka kwana biyu kaka-Aliyah ta tattara ta koma Bangalore tana mai addu’an Allah ya kawo wa yaran ɗauki cikin lamuran su.

Tsakanin Alhaji da Mustapha kuwa ko gaisuwan sa baya amsawa kuma yanzu haka auren sa da Asma’u saura sati da kwanaki, Maimoon kuma suna waya sannan tasan halin da ake ciki dan ita auren sa bai dame ta ba damuwanta ya aureta itama ko da mata uku zai qaro.
Baba-alhaji gaba ɗaya ya sanya a hau shiri tunda yaran da za’a haɗa bikin nasu tare komai sun kammala sai aka bar watannin aka ce duka a sati mai kamawa za’a yi, duk shirin da ake yi Mustapha ko a jikin sa kuma zuwa yanzu ya gama yanke shawaran abinda zai yi, Hajja dai ta zubawa sarautar Allah ido tana binsu da addu’a.
A can India Maimoon wasa gaske ta fara rashin lafiya wanda ya kai su har asibiti, Papa ya rasa yanda zai yi haka kaka-Aliyah ma, mahaifiyar ta kuwa zuwa yanzu itama ta saduda so take yarinyarta ta auri wanda take so.

Anshiga satin biki, ana hidima ba kama hannun yaro, su Alhaji duka sun tattaro sun dawo Maiduguri har da Mustapha da aka sha daru da shi kamun ya biyo su dan sai da Alhaji ya nuna ɓacin rai sosai, anyi hidima an gama an ɗaura aure ya kai 6 duka na jikokin baba-alhaji, an kai ko wacce Amarya ɗakinta.
Sai da suka kwashe sati guda a Maiduguri kamun suka tattaro suka dawo garin Gombe, duk kwanakin nan da aka ɗiba Mustapha ko kallo Asma’u bata ishe sa ba balle maganan ya shiga ɗakinta, sai da suka kwashe wata guda da dawowa Gombe amma bai bi ta kan Asma’u ba, ko da Hajja ta fahimci hakan sai ta qira sa.
Zaune yake a gaban Hajja wacce ke zaune a bakin gadon ta, kansa a qasa ya ce “Hajja ganinan”.
Kallonsa tayi da kyau kamun ta buɗe baki ta fara magana “Mustapha meyasa ba ka ji? in har kasan ba za ka iya kula da yarinyar mutane ba meyasa ka aure ta, su fa mata da kake gani ƴan lallashi ne kuma masu buqatan kulawa ne ba wai ka ajiye mace ka fita harkanta ba, haquri shine naka a matsayinka na mijinta, duk abinda kake yi ina sane ina kallonka ne kawai na maka shiru, dan haka tun kamun mahaifinku ya sa baki kayi ƙoƙarin gyarawa ka kula da matarka, ƴar uwanka kuma ƙanwarka fatan kana ji na?
Mustapha da yake ji kaman ya saka kuka ko magana ya kasa sai kawai gyaɗa kai da yayi yana ƙoƙarin miqewa, Hajja ce ta kama haɓa a ranta kuwa cewa tayi “nasan za’a rina wai an saci zanin mahaukaciya” da kallo kawai ta bisa har ya fice a ɗakin, yana fita a sashin su Hajiya ya wuce sashin yayansa Nura.
Da sallama ya shiga, Maryam dake zaune tana kallo ta amsa tana murmushi “sannu da shigowa Ango”, Mustapha taɓe baki yayi bayan ya qariso ya zauna.
Murmushi ta kuma yi tace “Angon Maimoon mijin Asma’u ya aka yi?
“Habibty ina mijinki?
Ta buɗe baki zata bashi amsa sai maganan Nura ya dakatar da ita, Nura da ke qarasowa palourn yana murmushi yace “ganinan Mustapha Autan Alhaji da Hajja” ya zauna gefen qanin nasa, suka gaisa Habibty ta kawo musu abun karyawa suka karya sannan ta miqe ta koma ciki ta basu waje dan ta ga qanin mijin nata so yake su zanta da yayansa.
Mustapha juyowa yayi a yanayi na damuwa yace “yaya Maimoon fa zuwa yanzu ko abu bata iya sawa a bakin ta wallahi storo nake kar soyayyata ta kashewa mutane yarinyar su kuma ita kaɗai suka haifa”, dafa kafaɗansa Nura yayi ya ce “Mustapha nima abun na damuna kuma bansan ta inda zamu ɓullo masa ba, kaga dai Hajja bata goyon bayanmu sannan Alhaji baya sauraran kowa, shi baba-alhaji kuma ya dage akan wannan al’adan, kai kam dai inaji Alhaji yana batun zai yi tafiya so sai muje mu dubo ta da jikin amma kuma ka fara bai wa Asma’u kulawan da ya kamata in har kanaso nasa hannu a lamarin nan”.
Mustapha da yaji sanyi a ransa tunda ɗan uwansa na goyon bayan sa sai ya amince ba komai zai kula Asma’u, bayan sun kammala magana sun yanke shawarar yanda zasu ɓullo wa lamarin sai Mustapha ya sallami yayansa ya bar sashin, amma bai wuce sashin sa ba ya ɗau mota ya fice a gidan gaba-ɗaya.

Asma’u yarinya kyakkyawa Masha Allah, a shekaru ba zata wuce sa’ar Maimoon ba, sanye take da dogon rigan zani wanda ya amshi jikinta, tana hakimce kan 1seater ta zuba tagumi wanda a zahirance TV dake maqale a bangon palourn take kallo amma a baɗinan ce hankalinta da tunaninta baya duniyar Gombe, ringing da wayanta ke yi ne ya kaste mata tunanin da take aikin yi, jawo wayan tayi ganin mai qiranta sai da ta share guntun ƙwallah kamun ta ɗauka ta kara a kunnenta “Assalamu’alaikum fanne an tashi lafiya?
Lafiya Alhamdulillahi Asma’u ya gidan naku? Ya maigidanki da iyayenku?
Asma’u jin an ambaci maigida wanda ita a zaman da take yau kusan wata 2 da aure amma bata ga ko giftawan ƙeyarsa ba sai Kawai ta fashe da kuka, cikin tashin hankali a ɗaya ɓangaren matar tace “ke Asma’u lafiya kuwa daga tambaya sai kuka waye ya mutu?
Cikin sheshsheqa ta ce “lafiya fanne ba wanda ya mutu”.
“Asma’u lafiya shine kike kuka? Faɗamun meke faruwa, me mijin yake miki yanzu na faɗawa baba-alhaji shine dai-dai kowa”.
“Ba komai fanne kawai kewanku nake yi”
Matar dai bata yarda da abun da Asma’u ta faɗa ba, nan ta sauya harshe ta fara magana mai kama da faɗa da yaren nasu, Asma’u dai tayi shiru tana sauraran matar tana kuma kan share hawayen dake sintiri a kumatun nata, jin matar ta tsagaita tana kuma tambayanta sai tayi ƙasa da kai ta fara faɗa mata komai duk abinda ke faruwa daga farko har qarshe, nan matar ta dinga surutu daga qarshe dai ta kashe wayan, Asma’u ganin matar ta kashe sai ta kifa kanta a cinya tana sakin wani marayan kukan.

Surutun da mata dattijuwa mai kama da Asma’u ke yi shi ya tashi mijin matar daga bacci yana faɗin “fanne lafiya ke da waye?
Cikin masifa ta fara magana “wai yanzu saboda tsabar muhammadu yaransa sunfi qarfinsa ace daga biki har yau wata har 2 amma yaron nan Asma’u bata taɓa sanya shi a ido ba wannan ai lalacewa ne, insun san haka yaron nasu ya gagara me na dagewa a ɗaurawa marainiyar Allah ciwon zuciya tun tana yarinya, gaskiya sashin baba-alhaji zanje in har yaron ba zai iya ba ya sakomun yarinya banson rashin mutunci tunda su iyayensa basu haifi mace ba balle su san zafin hakan..” masifa fanne ta dinga yi da qyar mijinta babagana ya rarrasheta ta haqura amma ta ɗau alwashi a ranta sai baba-alhaji ya ji abunda ke faruwa.
Bayan fitan mijin nata, farau-farau ta haɗa dan tasan baba-alhaji shi ya fi so, ta yafa mayafinta ta fice a sashin.
Gidan baba-alhaji stoho mai ran qarfe, babban gida ne iya ganin ka sashi-sashi shi da iyalansa, wanda a hakan ma wai wasu basa cikin gidan amma gida ne babba sosai, fanne da sallama ta shigo palourn baba-alhaji aka amsa mata sannan ta shige, zaune yake a kan kujeransa na gado da sandar sa gefensa, sai wani jikansa da yake zaune suna fira, gaishe su fanne tayi sannan ta ajiye abinda ta kawo wa baba-alhaji, yana gani ya fara washe baki yana sa mata albarka, ganin bata tashi ba sai yake tambayan ta ko da wani abu? Ba tare da ɓata lokaci ba fanne ta fara zazzagewa baba-alhaji qarya da gaskiya.

JUMA’AT KAREEM FAN’S 🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR’S ANNIVERSARY

JAHILCI KO AL’ADAH? FAN’S CLUB 🤝💙one lurv masu daraja habibties, Uwar batoorl na matuqar qamnar ku da sharhinku da soyayyan ku ga wannan littafi.
Dama waɗanda basa group ɗin amma suna sharhi to tabbas Uwar batoorl na soyayyan ku🤝

 

FAN’S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

💋💋 امى بتولة💋

 

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 37_38

Abinda aka yi da wanda ba’a yi ba duk sai da ta faɗa masa, baba-alhaji kuwa ransa in yayi dubu to ya ɓaci nan yasa aka qira masa Muhammadu.

Alhaji bayan fitan sa a gida, Companyn sa da suke aikin fata ya nufa dan yaga yanda ayyukan ke tafiya.
Yana zaune tare da wani abokinsa sai qira ya shigo wayansa, ganin mai qiransa yana murmushi ya ɗauka dan yasan ba zai wuce baba-alhaji yakeso su gaisa ba “Assalamualaikum stoho mai ran ƙarfe”
Baba-alhaji a ɗaya ɓangaren cikin masifa ko amsa sallaman bai yi ba shima ya fara zazzago nasa surutun daga qarshe ya ce “ka tabbatar yaron nan ya gyara kamun na sako qafana a cikin Gombe dan in yaga yayi auren nan to bayan rai na ne” yana gama magana kittt ya kashe waya, Alhaji ajiyan zuciya ya sauqe ya ajiye wayan yana auna rashin hankali irin na Mustapha da yarintan da ke damunsa, abokinsa ne ya dubesa yace “Alhaji Muhammadu lafiya kuwa?
“Ina lafiya kuwa Alhaji Ahmed kana gani yaron nan mustapha na ƙoƙarin jazamun magana”.
Abokin nasa ya ce “haba dai Mustapha kuma, yaro mai hankalin nan”.
Murmushi Alhaji yayi, nan take ya kwashe komai a taqaice ya faɗawa abokin sa ya ɗaura da cewa “in ba yarinta dake ɗawainiya da Mustapha ba ina shi ina ‘yar wata can qasa indiya bama anan Nigeria ba”.
Abokin Alhajin ma murmushin yayi yace “amma dai stoffi akwai rigima Alhaji in ba haka ba ai kai ne jikan sa ba yaranka ba kuma ko kai ai bai kamata ya hanaka abinda kake so ba balle kuma yaronka, gaskiya ba’a kyautawa Mustapha ba dan soyayya ba abun wasa ba, kawai ku barsa ya auro wacce yake so inyaso sai ya haɗa su biyu duka, kaga dai gaskiyan matar nan rabo yana kisa gwanda tun wuri ku qyale yara suyi auren su”.
Alhaji jin zancen abokin nasa sai ya sauqe ajiyan zuciya yana faɗin “nima dai tun da stohuwar nan tayi magana ina tunani amma kuma kaji yanzunnan shi baba-alhajin yake cewa in dai Mustapha ya auri bare to sai bayan ranshi ni kuma ban isa na musa ba, amma kuma ba komai Insha Allahu zan shiga Maidugurin da kaina na gwada tausan shi baba-alhajin ko zai sauqo ya amince”.
“To Allah kyauta ya tabbatar da alkhaeryh” faɗin abokin Alhajin yana miqewa ya bawa Alhaji hannu suka yi musabaha ya fice a office ɗin.

Alhaji ko da ya dawo gida surutu ya dinga yiwa Hajja akan tasan abinda ke faruwa tayi shiru, ita dai Hajja ido ta zuba masa har ya gama ya ciro waya ya qira Mustapha yana ɗauka ya ce masa “duk abinda kake yi ka tabbatar ka zo bayan sallahn isha’i” yana gama magana ya kashe wayan sa ya miqe yana kan mita.
Hajja da kallo kawai ta bisa, tana mamakin wani abun dan tasan ba’a yi ba amma ba komai Allah shige ma kowa gaba a al’amuran sa.

Mustapha shine bai zo qiran Alhaji ba sai wajan qarfe takwas, nan Alhaji ya dinga masa faɗa sannan ya ce “ka tabbatar ka kula da yarinyar mutane kar na kuma jin wani abun balle na gani”.
Shi dai kansa a qasa bai ce komai ba har Alhaji ya gama maganan sa ya sallamesa, kamun ya miqe ya nufi sashin sa, a palourn ya same ta zaune tana cin abinci, sanye take da kayan bacci riga da wando masu kauri da duhu ta tufke gashin kanta mai tsayi dai-dai gwargwado, kallo ya qare mata a taqaice yana taɓe baki ya ce “wannan ina ta kai Maimoon tawa” haka dai ya basar yayi sallama wanda a gefen Asma’u kaman sauqan aradu haka ta ji sallaman ba zato ba tsammani dan har ta storita, amsawa tayi tana masa sannu da zuwa shima ya amsa ya qarisa ya zauna.
Ruwa ta kawo masa da abun sha sai abincin da take ci ta kawo gabansa tana faɗin “kayi haquri bansan zaka shigo ba”.
Shi dai Mustapha bai ce komai ba ya taɓa kaɗan yana satan kallonta, daga qarshe ya umurce ta tazo suci tare ba musu ta dawo gefensa suna ci tare yana kallonta.
A wannan dare dai ya mai da Asma’u cikakkiyar mace sannan suka fahimci juna ya mata faɗa na haɗa sa da gida ita kuma ta nemi yafiyar sa.
Zuwa yanzu Mustapha da Asma’u suna zaune lafiya duk da dai Mustapha ba sonta yake ba kuma itama tasan da hakan amma tana son shi kuma a ɓangarenta ta amince ya auri Maimoon dan tana ganin za ta fi samun nistuwa itama.
Ana haka dai ciwo ya kama baba-alhaji ba ji ba gani, ciwo yayi tsanani wanda ganin hakan sai Alhaji da iyalansa suka tattara suka nufi Maiduguri, sunje lafiya sun duba shi, duk da dai baba-alhaji ya ga Mustapha da Asma’u lafiya kuma shima yana cikin zafin ciwo amma hakan bai hanasa yiwa Mustapha faɗa ba dan shi a ganin sa yana son ɓata masa tsarin rayuwan familyn sa ne, in da ya kuma jaddada musu ko bayan ransa bai yarda wani ya auro bare ba.
Shi dai Mustapha duk abinda baba-alhaji ke faɗa jinsa kawai yake yi.
Basu fi sati biyu ba suka tattaro suka dawo Gombe, Maryam matar Nura dai addu’a take Allah ya qaddara auren Mustapha da Maimoon duk da kuwa Asma’u ‘yar uwatta ce amma tan son Maimoon da Mustapha.

Basu fi wata guda da dawowa ba Maryam ta fara laulayi, wannan laulayin ba qaramin faranta ran iyalan Alhaji yayi ba kowa ɗauki yake yi barinma Mustapha duk da shima a kullum hango Maimoon da cikinsa yake yi.
Kwatsam Alhaji ya samu qira daga Maiduguri kan jikin baba-alhaji ya tsananta kuma yana buqatan kallon su shi da Hajja, ba tare da ɓata lokaci ba suka shirya suka tafi Maiduguri su biyu.
Bayan tafiyansu Mustapha da Nura suka shirya jirgi ya lula da su qasar India, suna isa suka nufi asibitin da aka kwantar da Maimoon, ganin yanda ta koma ba iya Mustapha ba har Nura sai da yayi ƙwalla ya tausaya masa, kaka-Aliyah taji daɗin zuwansu kuma jikin Maimoon har yayi dama-dama a kwana 2 da suka yi, nan dai Nura ya buqaci da a ɗaura auren Maimoon da Mustapha amma Dr Mufaddal ya nuna qin amincewar sa dan tunda dangi basa sonta kar aje yarinyar sa kuma ta qarisa mutuwa.
Anyi juyin duniya amma Papa da Ammaa sunqi, Mustapha har da kukan sa amma sunqi dan kowa a cikin su yasan sharrin qiyayya balle ma da suka ji yanzu Mustapha na da mata, har sai da kaka-Aliyah ta sa baki sannan Dr Mufaddal ya aminta dan sosai yake jin maganan surkuwar ta shi, ba tare da ɓata lokaci ba Nura ya biya sadakin Maimoon rufi dubu hamsin a kuɗin indiya, a kuɗin Nigeria kuma dubu ɗari kenan.
An ɗaura aure lafiya-lafiya ba tare da sun sanarwa kowa ba a gida, Maimoon kuma tun da aka ɗaura aure shikkenan sauqi ya fara samuwa gadan-gadan, ganin sun kwashe sati guda sai Nura ya buqaci da zasu ɗauke ta su dawo Nigeria tare amma kaka-Aliyah tace a’a su zasu kawo ta daga baya in ta gama samun sauqi, Mustapha ba don yaso ba suka baro India yana cike da farin ciki da kewar sahibar sa Maimoon wanda a gefenta itama hakan take.
Nura dai komai yake yi shahada ne dan zuciyar sa na cike da storon me zasu tarar a gida tunda ba wanda yasan zancen kuma gashi shine ya jagoranci komai, amma a gefen Mustapha ko wannan tunanin baya yi illa farinciki da yake ciki, sun sauqa lafiya sun tarar su Alhaji ma basu dawo ba.
Nura ya faɗawa Maryam abinda ake ciki, itama ba tare da ta damu da cakwakiyar da zai faru ba ta dinga farinciki har da murna, ɓangaren Asma’u ma Mustapha bai ɓoye mata komai ba ya faɗa mata, ko ba komai ta ji kishi tunda ita dai Allah yana gani tana qaunar sa amma sai ta danne zuciya. Bayan mako guda da dawowan su Mustapha su Alhaji ma suka dawo sun baro jikin baba-alhaji sai a hankali kawai.
Har aka kwana biyu da dawowan su tsakanin Nura da Mustapha ba wanda yayi qarfin halin tunkarar iyayen nasu ya faɗa musu abinda ake ciki, daga qarshe dai Nura ne yayi qarfin halin zuwa wajan Hajja ya faɗa mata komai da ya faru, cikin tashin hankali ta kalli Nura tace “ashe Nura baka da hankali? Har za kuje ku ɗaura aure wa kanku ba tare da sanya albarkan iyaye ba wato kun girma ko? To ba ruwa na dole mahaifinku yaji maganan nan tun da wuri asan yanda za’a yi kamun baba-alhaji ya ji tunda dai ku kunnen qashi gare ku, gaku marassa iyaye marassa manya kune iyayen kanku har za kuyi gaban kanku kuje ku ɗaura aure ba saninmu to maza-maza ku shedawa mahaifinku kamun na faɗa masa da kaina dan ba zai yiwu dan na haifeku sai ku dinga jamun magana ba, ni kuka raina komai ku ka yi ni za ku tinkara ku faɗawa tunda ni mareniyar wayo ce ba abinda na isa nayi to ku faɗawa mahaifinku shi da ta isa kuma kukejin storon sa dan baza’a ce nice na ɗaure muku wajan zama ba wannan karon”.
Nura kaman zai yi kuka ya ce “shikkenan Hajja Allah huci zuciyanki Insha Allahu zamu faɗawa Alhaji amma so kuke ki sanya mana albarka da addu’oenki, Wallahi Hajja ko kece kikaga halin da baiwar Allahn nan ke ciki sai kin tausaya mata amma ba komai kiyi haquri ki yafe mana”.
Harara Hajja ta aika masa “to ban tausaya mata ba a rufeni da duka, nidai na faɗa maka maza-maza kuyi gaggawan faɗawa mahaifinku, shi kuma Mustaphan tunda fitsarar sa har takai haka to ya tabbata ya rubuta wa yarinya sakinta kamun ya tunkaro mahaifin naku kuma kan magana take garin Borno, maza tashi ka ficemun daga gani “.
Nura haquri ya dinga bawa Hajja amma ganin ta bawa banza ajiyarsa sai ta miqe ya fice yana hamdala ko ba komai sun rage wani aikin saura na tunkaran Alhaji dan baba-alhaji basa ta shi tunda shi ba ubansu ba ba kuma uban iyayensu ba.
Hajja ajiyan zuciya ta sauqe Nura na fita ta ɗaga hannu sama tana faɗin “Allah ka sanya albarka a wannan auren, Allah ka musu albarka duka ka basu ikon haqurin zama da juna, Allah ka shiryamun su ka basu zuria’a masu albarka, Allah ka jiɓanci lamuran su ka kawo musu komai da sauqi” sannan ta miqe, haka kawai itama Hajja taji tana farincikin wannan auren duk da tasan akwai ƙura dan ko wannan zuwan nasu kan su dawo sai da baba-alhajin ya jaddada musu akan Mustapha ya kiyaye shi.
Sai da aka kwana ɗaya, biyu ana ƙoƙarin na uku Hajja ta dinga surutu in basu faɗawa Alhaji ba to yau zata faɗa masa, ganin haka a ranan da dare Alhaji na zaune palourn sa yana kallon labarai suka shigo, bayan sun gaishe sa sai duk suka yi shiru aka rasa mai fara magana, Alhaji kallon su yayi kamun ta tambaye su “akwai mastala ne?
Mustapha ya buɗe baki da niyan yin magana sai Nura yayi ya maza ya fara korowa Alhaji bayani kansu a ƙasa duka, Alhaji kuwa tun da Nura ya fara magana ya zuba musu ido ko kiftawa ba yayi.
Hajja da ta sako kai zata shigo palourn, jin abinda suke faɗa sumui-sumui ta juya ta koma ɗakinta tana musu addu’a kawai Allah kawo musu komai cikin sauqi.
Sai da Nura ya gama koro bayani kamun Mustapha ya buɗe baki ya ce “kayi haquri Alhaji”. wannan magana ta Mustapha shi ya bawa Alhaji daman iya haɗa laɓɓunsa ba tare da dogon zance ba ya ce “kun kyauta, ku tashi ku bani waje shashashshu kawai”.
Da mamakin iya abinda Alhaji ya furta suka kalli juna suka miqe suka fice a palourn tare, sai da suka gama magana sannan kowa ya wuce sashin sa.
Alhaji sai da ya gama nazari da tunani sannan ya nufi ɗaki inda ya samu Hajja har ta kwanta, qyaleta yayi ganin kaman tayi bacci ya kwanta shima, Hajja kuwa likimau tayi ba bacci ba dan har dai da taji sauyawan numfashinsa alaman bacci ya ɗauke sa sannan ta miqe ta ɗauro alwala ta tada nafila mai cike da addu’a ga yaranta rayayyu da matattun duka ( to Hajja Allah ya amsa).

Sai da aka shafe sati guda Alhaji bai ce musu komai ba, gefen Mustapha kuwa soyayya da Maimoon ruwa-ruwa kullum suna maqale da waya dan zuwa yanzu jikinta yayi sauqi sai abinda ba za’a rasa ba, dama shigan ciwo ne mai sauqi amma fitansa sai a hankali.
Asma’u tun tana dannewa tana haquri har abun ya fara isar ta, dan yanzu kullum Mustapha raba dare yake yana soyayya da Maimoon, magana Asma’u ta masa amma sai ya bata haƙuri shi gaskiya yana son Maimoon ba zai iya dannewa ba, sai kuma Asma’u ta fara ɗaga hankali tana masifa daga qarshe qiran fanne tayi ta faɗa mata komai, ita kuma fanne ta samu baba-alhaji ta faɗa masa qarya da gaskiya, duk da zafin ciwon da baba-alhaji ke ciki bai hanasa qiran Alhaji ba, sai aka yi rashin sa’a layinsa baya shiga, nan dai suka dinga gwadawa shiru, baba-alhaji dan masifa har jikinsa tashuwa yayi.
Alhaji kuwa har zuwa yanzu bai ce komai ba sannan bai tunkari Hajja da maganan na yayi shiru tunda yaran sun nuna masa bata sani ba itama kuma ya yarda.

Maimoon zuwa yanzu ta warke rass kaka-Aliyah ta gyarata dai-dai gwargwado nasu indiyawa, jikinta dai bai koma normal ba dan kana ganinta kasan tayi jinya amma duk da haka ta murmure tayi kyau abunta abinka da kyakkyawan mutum kuma ‘yar indiya, kaka-Aliyah tayi maganan tarewan ta amma Hindu ta tirje sam sai sunga ana son ‘yar su kamun ta tare, kusan samun damuwa suka yi da Dr Mufaddal amma sam taqi yarda, kaka-Aliyah tayi-tayi amma Hindu taqi ganin haka sai suka fita harkanta suka yi shiru maganan tarewan, ganin an kwashe wata amma shiru sai kaka-Aliyah ta dinga masifa sai yarinya ta tare in taso ta stine mata ai itama zaman gidan mijinta take, qarshe dai suka tsayar da ranar tarewan bayan sun tuntuɓi Mustapha shima ya faɗawa Hajja, nan aka dinga shiri Mustapha na gyaran sa amma duk shirin su da suke yi Alhaji bai sani ba.
Alhaji na zaune tare da Hajja suna fira sai qira ya shigo wayansa, ganin mai qiran sai da gabansa ya faɗi amma haka ya ɗauka, ai kaman yanda ya tsammani haka ya ji dan da masifa baba-alhaji ya fara ba ko sallama, muryansa ba fita yake ba sosai amma inda yake shiga ba nan yake fita ba “wallahi Muhammadu ka tabbatar yaron nan ya bawa ‘yar mutane talardan ta dan in ba haka ba wannan karon da kaina zan zo har Gombe daga kai har shi ba za kuji daɗi ba, kuma kar naji labarin wasu sunzo gidan ko shi ɗin yaje can qasar kafuran..” haka baba-alhaji ya dinga surfa tijara yana ganawa yasa fanne ta kashe masa wayan, nan kuma yasa ta qira Asma’u ya shaida mata ana kawo mata gidan ta faɗa masa, Asma’u bata so abun ya kai har haka ba amma ta amsa kuma dolenta dan tasan halin fanne, baba-alhaji tari ne ya sarqafe sa da qyar dai ya lafa.
Alhaji bayan baba-alhaji ya kashe waya dafe kai yayi yace “Fatima yaranki za su kashe ni lokacin mutuwana bai yi ba, yanzu ya aka yi magana yaje kunnen baba-alhaji?
Hajja itama da mamakin ta ce “Alhaji ni kuwa ina zan sani, nima mamakin ya aka yi ya ji nake”.
“Ni gaba-ɗaya yaran nan sun ɗaure ni da jijiyoyin jiki na, na rasa yaya zan yi, wallahi har naji da ban tura yaron nan wannan qasar ba, amma dai ya zan yi qaddara ta riga fata Allah ya sanya alkairi, amma maganan tarewan yarinyar nan dole a dakatar ba yanzu ba”.
Hajja dai shiru tayi bata ce qala ba tunda tasan sun riga sun gama magana.

Mustapha bai bi ta kan kowa ba ya tattara ya tafi India, ganin sa kuwa ba qaramin qwarin guiwa ya qarawa Dr Mufaddal da kaka-Aliyah sun san ko ba komai yana sonta kuma zai riqe ta, sai da ya kwana 2 suna soyayyan su sannan ya tattaro ya dawo yana jin kaman ta dawo da matar sa, Asma’u tunda ya dawo ta fahimci India yaje, nan ta qara saro sabon tijara itama wanda basu fi sati ba Mustapha abun na isar sa ya sake ta saki guda, Hajja ta masa faɗa tun Alhaji bai ji ba ya mayar da ita, amma da qyar ya yarda ya mayar da ita.

Mustapha ya kammala komai sai zaman jiran zuwan Amarya sati mai kamawa, yayi ordern kayan akwati ba wanda ya sani ya kawo gefenta ya ajiye, dama starin part na Mustapha da Nura main palour ne babba sai kuma gefe 2 bedroom da palourn ɗayan gefen ma 2 bedroom da palourn, to gefen da Mustapha yake akan nasa shi ya shiryawa Maimoon komai.
Ranar Alhamis mutan India suka tattaro da Amarya sai Nigeria, Dr Mufaddal, Hindu, kaka-Aliyah, Maimoon Amarya.
Sun sauqa lafiya lumui, Nura ne da kansa yaje ya ɗauko su, direct sashin Hajja aka yi da Amarya kuma anci sa’a Alhaji baya gida, nan Hajja ta musu tarba mai kyau wanda ya farantawa kaka-Aliyah, ita kuma Hindu taji dama-dama a ranta, Maryam mai fama da cikinta da zuwa yanzu ya tasa kusan wata 6 sai nan-nan take da Amarya wanda a take suka zama kaman ƙawaye.
Asma’u tunda ta gifta taga shigowan mutane, a sace ta shigo taga Amaryan, tunda Asma’u taga kyawun Maimoon hankalinta ya tashi ba shiri ta juya ta daqa waya ta qira fanne ta faɗa mata, itama ta sanar da baba-alhaji, ba ɓata lokaci shima ya qira Alhaji yana surfa masifa inda yake shiga ba nan yake fita ba kuma yau-yau ɗin nan zai zo Gomben sai Mustapha ya sake yarinyar kuma sun koma, Alhaji da baisan da wannan magana ba shima ransa ne ya ɓaci ya kamo hanyar gida.
Baba-alhaji da qyar aka dannesa akan ya bari gobe su taho kamun ya haqura.

Alhaji yana isowa gida, ya hau Hajja da Mustapha da masifa dan ko kula su Dr Mufaddal bai yi ba, qarshe ma saqon baba-alhaji ya basu sannan ya ce Mustapha ya tabbatar ya bawa yarinya takardan ta kamun gobe, wannan masifa har kunnen su kaka-Aliyah wacce ita kuwa tace jikarta taga gidan zama, Hindu kuwa an sosa mata inda yake mata qaiqayi ta dinga mita za’a rena yarinyarta za’a maida yarinya bazawara dan haka su yau zasu koma amma kaka-Aliyah ta hana tace sai sun jira zuwan baba-alhaji taga ta inda zai raba abinda Allah ya qulla, Dr Mufaddal dai nasa iso ya kasa cewa komai, domin shi mutum ne mara son hayaniya komai aka yi dai-dai ne, ba abinda yake ji sai yarinyar sa amma yana binsu duka da addu’an alkairi.
Mustapha da Maimoon a gefensu kuwa duk abinda ake yi bai dame su ba, su damuwan su ma su haɗu da juna amma an hanasu wannan daman Hindu ta kasa ta stare daga sashin Hajja sai India ba inda yarinyarta zata je salon a maida ta bazawara, shi ma Mustapha Alhaji ya kasa ya stare in har ya keɓe da ƴar mutane to bai yafe masa ba kuma sai ya sake ta, Hajja dai tausan Mustapha tayi sannan ta dinga bawa su kaka-Aliyah haƙuri amma kaka-Aliyah ta nuna ba komai dama duk wani aure wanda zai yi qargo ya gaji haka, yawan qalubale yawan qwari da qargon aure.
Maryam ma duk abinda ake tana maqale gefen Maimoon har dare kamun ta tafi sashinta.
Tunda ya shiga palourn Asma’u ke ruwan masifa da bala’i sai ya sake ta cin amana ai an ɗaura auren ma bai sanar mata ba sai daga baya, nan dai Mustapha yaji ita ce takai zance kunnen baba-alhaji, ba ɓata lokaci ya kuwa rubuta mata sakin da ta buqata, saki guda ya mata ya zama biyu da wanda aka yi kwanaki.
Nura dai ba shi da ta cewa sai zubawa sarautar Allah ido, dan yasan gobe baba-alhaji na dirowa Gombe to ta kansa za’a fara shine yayi wa komai jagora, amma Maryam ta dinga kwantar masa da hankali ta rarràshi mijinta suka lula duniyar masoya ta ma’aurata zuciyanta cike fal da addu’an Allah yasa kar a saki Maimoon.

Washe-gari baba-alhaji ya dinga fitina ba yanda aka iya haka aka sako shi a motan gida shi da jikokinsa 3 da fanne da kuma yayan Asma’u da suke uwa ɗaya uba ɗaya, suna hanya Asma’u ta qira ta shaida musu sakin da Mustapha ya mata da dare da kuma na kwanaki nan fa masifa ya ninku baba-alhaji ji yake babagana baya sauri a tuqin, dan ciwon dake damunsa ma neman sa yayi ya rasa ba abinda yake cinsa sai masifa da burin ya gansa a gidan Muhammad “in banda jarabar yara basu sa maka ciwon kai ba haka jikoki basu sanya maka ciwon baki ba dai yaran jikoki ne zasu sanya ka hawan jini, ni in ba azalzala da rashin ji irin na yaran zamani ba me zai kai ni wata gari can Gombe, banje sun samartaka ba sai da stufa kucuf-kucuf ina ƙoƙarin mutuwa, Allah kyautawa yaran zamani da kafiyar stiya wai soyayya” cewar baba-alhaji da yake magana da qyar.
Tunda garin Allah ya waye Mustapha ya fice a gidan ya qira Maimoon kawai suna soyayyan su ba ruwansu da fitinan da ake yi sanadin su, Hindu ko abin karyawa taqi masa kallon arziqi ita burinta kawai su tattara su koma yanzu karma rana ta fito ta same su a qasar jama’a, Dr Mufaddal dai ɗakin da aka basa yake ciki yana ayyukan sa da zai yi ta waya bai bi ta kan Hindu ba dan shi ko karan hauka yasha ba zai maida yarinyar sa bazawara da hankalin sa ba.
kaka-Aliyah kuwa fitowa tayi ta wane a palourn Hajja kai kace gidan ta ne tana faɗin ba ita ba barin gidan sai jikarta ta haihu, Hajja dai abun kaka-Aliyah ma dariya yake bata dan haka nan suka dinga hiran su kaman ba komai.
Alhaji dan ɓacin rai ko fitowa bai yi ba yana ciki yana jiran isowan baba-alhaji dan shima zuwa yanzu renin hankalin yaran nasa ya ishe sa tunda har yarinya zata tare ba’a faɗa masa ba, gefen Asma’u kuwa ta gama haɗa kayanta dan su fanne na zuwa suka gama abinda ya kawo su da ita za’a juya ba zata zauna da Mustapha ba a faɗin ta.

Alhaji na zaune a palourn sa idanuwan sa akan TV yaji muryan wayansa, ganin layin ɗan uwansa dai ya ɗauka, abinda aka faɗa masa ne ya sanya shi miqewa yana furta “INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI’UN! Kuna wani asibiti? Okay to ganinan zuwa yanzun nan” ya faɗa yana ficewa a palourn, tarar da Hajja da kaka-Aliyah yayi zaune amma bai bi ko ta kansu ba ya fice, ganin jiran driver zai ɓata masa lokaci sai ya ɗau mota da kansa ya nufi hanyan asibitin da aka ce masa.
Hajja dai tun fitan Alhaji hankalinta bai kwanta ba, nan ta wa kaka-Aliyah magana bari tana zuwa, ta miqe ta shige ciki.
Wayanta t ɗauka ta qira layin Alhaji yafi sau uku amma bai ɗauka ba haqura tayi ta koma palourn ta zauna, sai kuma ga Hindu ta fito riqe da hannun Maimoon, Hajja da kaka-Aliyah idanuwa suka zuba mata ganin ikon Allah, amma ba wanda yace ko ci kanki.
Hindu na jan Maimoon tana tirjewa har da kuka, Dr Mufaddal da muryan Maimoon ya fito da shi ganin abinda ke faruwa da abinda Hindu ke faɗi yana isowa ba ɓata lokaci ya ɗaga hannu ya kwaɗa mata mari yace “sake mun hannun yarinya kiyi tafiyanki”.
Idanuwanta a bushe tace “wallahi sai na tafi da yarinyata ba wanda ya isa ya hana ni” duka maganan da suke cikin harshen Indianci ne dan haka Hajja bata san ma me ke faruwa ba, ganin suna qoqarin yin abinda bai kamata ba Maimoon cikin kuka ta fara magana “shikkenan Papa kayi haquri mu koma na haqura da Mustapha, Ammaa kiyi haquri ki daina na haqura mu koma..”, Nura da ya shigo hankali tashe shi ya kaste maganan Maimoon, cikin damuwa Nura da tashin hankali yace “Hajja Alhaji yayi hastari suna asibiti”.
Dukkan su miqewa suka yi suna salati, Hajja da gudu tayi cikin ɗakinta ɗauko hijab, nan ta tarar da misscall na layin Alhaji.
Hajja, kaka-Aliyah, Nura, Dr Mufaddal duka suka fice za su yi asibiti bayan ya gama jawa Hindu kunne kar ta yarda ta fita da Maimoon a gidan nan.

Suna fita suka ɗau hanyan asibitin da aka kai Alhaji sun isa an shiga da shi accident and emergency dan yayi rauni sosai, nan Hajja ke tambayan Nura dama ina Alhajin zai je? Nura ya buɗe baki zai bawa Hajja amsa sai yaga qiran yayan babansu ya ɗauka, jin abinda baffa babagana ya faɗa sai ya sanya salati yana faɗin “okay gamunan zuwa Alhajin ma ya samu hastari muna asibiti a cikin Gomben”.
Hajja dubansa tayi ta ce “kai da wa?

MASU SHARHI UWAR BATOORL TAKU TA GODE🤝 DAN SHARHIN KU SHINE QWARIN GUIWANA
MASU GODIYA BANSON THANKS NAKU KUMIN SHARHI KAWAI SHI NAKE BUQATA.

 

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR’S ANNIVERSARY

FAN’S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

💋💋 امى بتولة💋

 

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 39_40

Nura ya ce “Hajja wai hastari su baffa suka samu a hanyar shigowa Gombe yanzu suna asibiti amma Allah yayi wa baba-alhaji cikawa”.
Innalillahi wa inna ilaihirraji’un! Shine abinda su Hajja duka suka furta dan sunsan baba-alhaji, Hajja hawaye ta fara tana maimaita sunan Allah a zuciyan ta da bakinta dan tasan wannan babban rashi ne, Alhaji kuwa har yanzu bai farfaɗo ba, nan Nura ya barsu shi kuma ya nufi asibitin da su baffansa suke yana qiran layin Mustapha baya shiga.
Ɓangare su Maimoon kuwa su Dr Mufaddal na fita Hindu taja hannun ta sai dai su tafi, ta tirje ta tirje amma tace zata saɓa mata ganin haka sai ta bita amma tana qiran layin Mustapha baya shiga kaman za tayi kuka haka suka fice a gidan, ba tare da sanin ina suka nufa ba kawai suka hau hanya.

“Mustapha ya kamata kaje gidan kaji ya za’a yi tunda ka ce baba-alhaji na hanya ya kamata kaje komai ayi ya wuce ko” faɗin wani matashi wanda da kaɗan ya girmi Mustapha a shekaru.
Cikin yanayin gajiya da kuma damuwa da yake ciki ya ce “Yusuf ba za ka gane ba, wannan stohon fitinan sa ya wuce duk tunaninka kuma Alhaji jin maganansa yake kaman shi ne babansa ba kakansa ba, nasan zai iya sanya Alhaji ya stinemin akan Maimoon ni kuma Allah ya gani ina qaunarta ba zan iya rabuwa da ita ba ko za’a stinemin, aurena da Maimoon har mutuwa ba saki Insha Allahu sai dai duk iya gwagwarmayan rayuwa a yita a jure, don baiwar Allahn nan qauna take mini bilhaqqi wanda a wannan zamani da muke ciki samun mace ta maka irin soyayyan nan ko a film albarka, domin su mata da kake ganinsu in suka ce suna son abu tsakani da Allah to hakan suke nufi har iya ransu, mata basa karya zuciyan namiji sai dai shi ya karya nasu, in har kaga namiji na zancen mace ta karya masa zuciya to kayi bincike da kyau zaka tabbatar da gaskiyar lamari ba hakan bane, mata daga kan ciwon da suke na al’ada zuwa ɗaukan ciki da renon ciki da kuma haifan ciki to daganan zaka fahimci suna da ƙawa-zucin da duk iya sheɗancin wasun su to tabbas wasun su imaninsu da tausayinsu da soyayyansu ba abu ne da za’a ɗauka a wasa ba balle ace zasu iya karya waɗannan abubuwa, Maimoon na qaunata kuma nima ina qaunarta, ina fatan zama da ita kaɗai amma tun kamun ayi nisa qaddara ta sanya nayi wata matar kamun ita, to wannan qaddaran ba ni da ikon guje mata inta tashi aiki a gaba, ni dai fatana Allah sanya duk wata qaddara da zata shigo rayuwarmu ta zama ta alkairi”.
Murmushi Yusuf yayi kamun ya ce “wato kai irin ga ka alaramma ko? Ba za ka mata ko da ɗan daɗin bakinmu na maza ba, ai dai kasan zaka sanyata farin ciki ko taji daɗi ta sake tayi maka qauna dai-dai gwargwado, domin su mata da kake ganinsu sai ana haɗa musu da ƙarya inba haka ba lamarin ba zai tafi dai-dai yanda ake so ba, ” ke kaɗai ce babu qari” sai kaga wannan kalmomi da basu wuce biyar ba su sanya mace haukacewa a kanka ta yarda daga ita babu watan, amma kai a gefenka kana samun hali da kuma wacce kake so sai ka auro abarka ai Allah ne ya halasta shikkenan tayi haukanta ta gama dole ta zauna da kai domin tana sonka”.
Taɓe baki Mustapha yayi ya ce “tabbas a JAHILALLEN AL’ADA tamu ta maza da muka ɗauka ba laifi ne faɗawa mace haka ba, amma ina so ace ba iya ni da kai ba so nake mazan duniya duka su fahimci wani abu guda ɗaya shi yiwa mace ƙarya akan daga ita ba qari bai da fa’ida domin wani daga nan yake jawa kansa reni a wajan matarsa tunda alqawari ya ce, kaga kuma duk wanda bai cika alqawari ba shi da Ubangiji kuma kimarsa da ƙwar-jinin sa ga al’umma disashewa take yi, sannan ka zama ba abun yarda ba ga mace wanda kuma in ana zaune tare to fa tabbas ana so a yarda da juna zama tafi inganci, sannan ka sani a addinance da ka yiwa mutum qarya ka sanya shi farinciki gwanda ka faɗa masa gaskiya ka sanyasa baqin-ciki ko da kuwa yaya abun yake domin ita ƙarya raminta ƙurarre ne kuma fure take bata ‘ya’ya, amma ita gaskiya komin daren daɗewa sai farinciki ya maye gurbin baqin-cikin da mutum ya shiga na ɗan wani lokaci, sannan da kake cewa dole mace ta zauna da kai domin tana sonka, amma ba ka san cewa soyayya na komawa qiyayya ba? Kuma gwanda qiyayya tun ranar farko akan qiyayyan da ya samo asali daga soyayya, akwai tashin hankali a ciki da rashin kwanciyan hankali wanda muke ganin laifin matan mu akan suna aikatawa dan mun ƙara aure amma a baɗinance mu munsani mune muka ja komai kuma mune muka haddasa komai amma sai muke maidawa kansu, tabbas Allah ne ya halasta amma karya zuciyar mace ta hanyan mata ƙarya mara amfanu wannan Allah bai halasta ba, ana so ne duk lokacin da kake neman mace da niyar aure to ku gina komai kan gaskiya duk da akwai wajaje da ɓoye wani abun ya halasta dan ka auri mace amma wannan abu baya ciki, sai dai kuma a wannan duniya tamu mun ɗauke sa AL’ADA wanda ni a gani na JAHILCI KO AL’ADA za’a qira sa oho, amma dai tabbas ba AL’ADA mai kyau bane, munsan wani abu qaddara ne da kuma jarrabawa amma tun ranar farko sai ka nunawa mace iya gaskiyanka sai kaga daga baya ko da menene zata fahimce ka Insha Allahu duk iya wuyan sha’anin mace a wajan kishi sai kaga Allah ya wanke ka ya fahimtar da ita, Allah kawai ya kyauta mana amma a gaskiya ni ba zan yi daɗin baki ko ƙarya a inda nasan in abun ya wuce za’a iya shiga tashin hankali ba”.
Yusuf na dariya ya bugi kafaɗan Mustapha cikin wasa ya ce “to shugaban masu faɗan gaskiya sai aje aji da baba-alhaji ko aji da Maimoon Allah kawo ciki da goyo, yau-yau ɗin nan Allah kawo rabo”, Mustapha na dariya ya miqe yawa abokin nasa sallama ya hau motan sa ya kama hanyan gida.
Yana tsaka da tuqi kaman ance masa kalli gefen can, kawai ya hangi Maimoon da mahaifiyarta, yana mamaki ya sauya aqalar motar sa zuwa side da suke yayi parking a gabansu, fitowa yayi a motan amma kamun yayi magana tuni Maimoon ta shige jikinsa, Hindu ta dinga surutu wanda daga qarshe Hajja ya qira ta haɗa su da Dr Mufaddal kamun Hindu ta haqura ta shiga mota suka koma gida, suna isa Hindu ta sauqa ta shige ciki, shi kuma ya kama hannun Maimoon suka nufi sashin sa.

Asma’u na zaune tana jiran isowan su baba-alhaji su Mustapha suka buɗe qofa suka shigo, ɗago kai tayi amma ganinsa da Maimoon ba ƙaramin ɓata mata rai yayi ba dan haka sai ta fara habaici “anyi ba’a yi ba wai anraka baƙo kuma baƙo ya dawo, domin yanda aka sake ni haka za’a saki mutum, kuma Allah na tuba wani dare ne jemage bai gani ba, ai sai dai daren mutuwarsa, da ɗi da ƙari ko a jikina wai an mari kakkausa..” hausa ta dinga yi wanda ita dai Maimoon ba hausan take ji sosai ba balle a kai ga baqaqen magana, shi kuma Mustapha ko a jikinsa sai ma rungumota da yayi suka shige ciki, ganin shigansu kaman za tayi kuka haka ta miqe ta shige ta ɗauko wayanta tayi ta aikin qiran layin fanne amma baya shiga balle a ɗauka har ta ajiye wayan sai ta tuno da kawunta da suka taho tare nan ta qira shi ta samu layinsa busy, sai can kamun ya ɗauka suka gaida sama-sama nan yake faɗa mata abunda ya faru da asibitin da suke, kuka ta sanya tayi jifa da wayan ta sanya mayafi ko ta kan su Mustapha bata bi ba ta fice ta nufi aisbiti.
A ɓangaren Mustapha kuwa fitowa yayi kitchen na sashin Asma’u ya sama musu abinda za su ci sannan ya koma ya lallaɓa Maimoon ta ci suka shiga farantawa junansu dan kusan sun manta da meke faruwa ma, suka lula duniyar su ta ma’aurata.
Hindu tunda ta shiga take ta surfa masifa qarshe ganin Maimoon bata shigo ba sai ta kishingiɗa zaman jiranta har dai bacci ya ɗauke ta, ɓangaren Asma’u kuwa asibiti ta nufa, nan ta tarar da Nura da kawunanta biyu da kuma jikinsu da sauqi suna zaune, amma fanne da yayanta da kuma kawunta dake jan motar duk sun samu rauni, kawunta ya karye a ƙafa, yayanta kuma kansa ne ya bugu sai fanne da ƙashin guiwanta ya goce hannunta ya samu karaya biyu sannan kanta ya bugu shima sosai, sai baba-alhaji da Allah yayiwa cikawa tun kamun a iso asibitin.
“Innalillahi wa inna ilaihirraji’un! Shi ne abinda itama Asma’u ke maimaitawa wacce tun ba’a je ko ina ba har nadama ta fara shiganta domin a ganinta ita ce taja komai sanadinta ne suka kamo hanya.

Anan Gombe aka wa baba-alhaji sutura aka kai shi hanyan bajoga (maƙabarta) aka zauna zaman makoki, da kuma jinyan su fanne dan Alhaji yaji sauqi shi kam, ɓangaren Maimoon da Mustapha soyayyar su suke sha duk da kuwa rashin da aka yi dan tun ranar da Mustapha ya kai ta sashin sa to kullum tana can sai in ta shigo gaishe da su Hajja da su kaka-Aliyah, Dr Mufaddal da Hindu tun da aka yi sadakam bakwai suka koma suka bar kaka-Aliyah.
Fanne ma zuwa yanzu taji sauqin jikinta, wanda ganin haka sai Alhaji yasa duka aka tattaru aka tafi Maiduguri dan saura kwana biyu ayi sadakan arba’in, sun isa lafiya da kwana biyu aka yi sadaka jama’a saura aka waste, family meeting aka haɗa wanda anan aka qara jajantawa juna na rashin babban bango tsayayye da aka yi, yayansu babba wanda yake ɗa a wajan baba-alhaji ba jika ba shi ya fara jawabi “da farko dai ina mai bamu haquri duka akan wannan rashi, kuma muna masa fatan samun rahama da gafarar Ubangiji, Allah haɗa shi da Annabin Rahama SAW, tun da abubuwan nan ke faruwa ban so sanya baki ba dan gudun mastala da yawan ka-ce-na-ce amma duk da haka a yanzu Allah ya sanya ni a matsayin da dole nayi magana, kai Mustapha ta kanka zan fara domin kuwa iyayenka basu da laifi sai dai abinda baza’a rasa ba, Mustapha tunda ka tashi iya rayuwarka kana zuwa cikin ƴan uwa kai kasan irin aure da muke ta AL’ADA wanda har shi mahaifin naka wannan AL’ADA tayi aiki a kansa, ya fara neman yarinya ƴar yare amma ba ƴar dangi ba an taka masa birki kuma ba tare da ja’inja ba ya amince ya auri mahaifiyarku gata nan Fatima ƴar albarka, wan ka shima ganin tsarin family sai ya nemi ya auri ƴar dangi dan aka ce ” zaman lafiya yafi zaman ɗan Sarki ” sannan tunda muke a zuria’an mu ba wanda ya taɓa gigin ko gangancin karya wannan AL’ADA tamu ta tun iyaye da kakanni sai kai Mustapha, tabbatas ba kayi dai-dai ba wanda garin rashin jinka ya jawo mutuwar hatsari ga mahaifinmu duk da dama mu munsani kowa da irin hanyar da tasa mutuwar zata ɓullo amma baka kyauta ba, ina fatan za ka gyara dan kai ma zuwa gaba ka samu ‘ya’ya masu jin maganar ka da kiyaye dokar ka?
Mustapha da kansa ke ƙasa haquri ya bayar bazai qara ba, numfasawa dattijon da ke magana yayi ya ɗaura da faɗin “madallah da mai babban suna, to Allah maka albarka ya albarkaci zuria’an ka, yauwá dai magana ta biyu duka wa kai, abinda ka aikata na saki bai kamata ba sam-sam, eh tabbas munsani Allah ne ya halarta saki amma fa shi ma Allah da kansa baya son sakin dan duk sa’ilin da aka furta saki ga mace to al’arshin Ubangiji sai ya girgiza, Mustapha baka kyauta ba ko ba komai ita ‘yar uwarka ce sannan kuma mu da ka ganmu bamu saki don yaranmu maza da mata masu biyayya ne da jin magana na magabatansu da mazajensu tun da nake a zuria’an mu na taso ban taɓa jin ga wani yayi saki ba a’a sai dai wance ta rasu sai mijinta ya auro wata qanwarta ko ‘yayarta, akan batun saki baka kyauta ba ko da me ta maka amma ba komai Allah sa haka ne alkairi gare ku da mu duka, sannan sai magana ta ƙarshe akan matsayin aurenka da Maimuna, ni na amince maka sannan ina binku da addu’an alkairi kuma ina fata kowa da ke nan wajan ya aminta da batun kuma ya sanya muku albarka” da idanuwa yake binsu dan jin ko akwai mai ja da batun auren.
Fanne da take ji kaman ta shaqe baffan nasu da ke magana ita ce ta fara buɗe baki tayi magana “gaskiya ni dai ban amince da maganan auren nan ba tunda har zai iya wulaqanta ‘yar uwansa akan bare tun ba’a je ko ina ba, inaga in abu yayi stamari? Ai muma sai ya wulaqanta mu akanta duk da yanzun ma ya wulaqanta mu ɗin”.
Murmushin manya dattijon yayi kamun ya ce “bayan ita babu wani mai magana?
A cikin mutane talatin da ɗauri da ke cikin babban palourn kwata-kwata mutum 2 ne suka yi magana da fanne da wata yarinyar baba-alhaji Mama-kumboji, ganin haka murmushi dattijon ya kuma yi sannan yace “to Alhamdulillahi! na ɗauka rabinmu basu yarda ba ashe kusan dukanmu za’a ce sun amince, to Masha Allah! Ke kumboji ke babbace ina so ne kiyi tunani da hankalinki ki yanke abinda ya kamata kamun kice wani abu kuma karki kawo son zuciya a cikin tunaninki, ke kuma fanne zan miki uzuri ke yarinya ce kuma kina tunanin duka mu bamu qaunar ‘yar wajan yayarki Asma’u, amma karki manta nine mahaifin baban Asma’u sannan ga Gambo ga Baana sune iyayen mahaifiyar Asma’u abun nufi iyayenki kenan kema ko, to duk da ke yarinya ce inaso ki duba me yasa su basu ce komai ba inkin dubo abun na tabbata kema za ki aminta, wannan aure na Mustapha da yarinyar nan maimunatu ina so ku sani duk mu ɗauke sa a Allah ya qaddaro ne ba yanda aka iya, kuma ina mai kyautata zaton akwai alkairi da kuma rabo wanda Allah ya ɓoye a auren dan haka ina umurtanmu duka da mu bisu da addu’an zaman lafiya, sannan ina so nayi magana ta ƙarshe wanda ba iya Mustapha ba dukkanmu da yaran da zamu haifa gaba ina so a kiyaye aikata irin wannan laifin, a stayar iya kan Mustapha ga dai yara nan Masha Allah kowa na haifa sannan ko mace guda ko mata 4 mutum yake buqata akwai su a dangi Allah ya hore mana haihuwa dai-dai dai-dai duk da dai yaranmu basa wuce uku biyu, to Allah musu albarka, Allah albarkaci zuria’an mu gaba-ɗaya Allah qara haɗa kawunanmu, Allah yajiqan magabatanmu ya rahamce su, to sai duk wani mai abun faɗa a shawara ko abinda ya kamata muna sauraro”.
Kumboji ce ta bada haquri sannan ta sanyawa auren albarka wanda hakan yayiwa kowa daɗi musamman iyayen Mustapha, nan dai aka tattauna abubuwan da suka kamata sannan taro ya waste, a ranan Alhaji, Nura, Mustapha, Hajja, Maryam mai stohon ciki da Maimoon da kaka-Aliyah suka tattaro suka dawo Gombe inda aka baro Asma’u acan tunda ba wanda yayi maganan komawanta.

Bayan kwana biyu da dawowan su kowa ya huta nan Alhaji ya zauna da dukka iyalan nasa, ya maimaita musu a kiyaye sannan ya sanya albarka wa auren wanda shi dama da jimawa ya sanya musu albarka, daga qarshe ya maida dubansa kan kaka-Aliyah ya ce “mama ina mai matuƙar baku haquri na abubuwan da suka faru ayi haquri a yafe mana”.
Murmushin manya kaka-Aliyah tayi sannan ta ce “bakomai Allah ya yafe mu duka, Allah basu zaman lafiya da zuri’a masu albarka sannan ina fatan kunga abinda nake guje muku na qoqarin ja da abinda Allah yake nufin qaddarawa, daga qarshe nima zan baku shawara guda, duk da dai munsani AL’ADA wani abu ne da mu mutane muka riqesa gam-gam kaman addini ko Farilla ko Sunna, eh tabbas akwai wasu AL’ADUN mu da suke zama halas a addinance daganan sai ya zama addini ba al’ada ba kaman ace a al’adanmu mace sai ta sanya hijab ta rufe jiki, babu yin zina, babu shan giya da dai sauransu to Masha Allah wannan ne AL’ADA da addini ma ta yarda da shi amma kaman hana aure da sauran su muma munsan me muke yi amma ba al’ada ba, to shawarata ita ce ko nan gaba wani abun ya ɓullo kar ku nemi jaa da hukuncin Ubangiji ku dai komai za kuyi kubisa da addu’a dan kaman yanda na faɗa tun farko in Allah ya qaddara abu barinma aure kuma ace da rabo ciki to fa s kiyayi Allah domin sai ya ɗauke mutum kuma ayi abun ba wanda ya isa ya hana, Allah ya kyauta to, da farko nace zan zauna da jikata amma yanzu dai ina buqatan komawa”.
Alhaji dai bai ce komai ba, Hajja ma kusan hakan sai rufe taro da addu’a da aka yi.

Bayan sati guda kaka-Aliyah ta koma India, inda Dr Mufaddal yaji daɗin abinda ya faru na amincewa da aka yi da auren yarinyar da haka a ɓangaren Hindu ma, bayan wani lokaci Maryam ta haiho yaranta tagwaye mace da namiji ranar suna yara suka ci sunan kaka-Aliyah da kuma mahaifin Maryam, wannan abu yayiwa Maimoon daɗi nan suka ci-gaba da zamansu cikin aminci.
Labari ne ya samu Maimoon na rasuwar kaka-Aliyah, tayi kuka har ta godewa Allah sannan suka tattara suka tafi ta’aziya amma acan suka baro ta sai an yi bakwai ita zata dawo, a wannan lokaci ne kuma Asma’u tazo har Gombe ta bawa Mustapha haquri sannan ta roqi su Hajja tafiya da kuma qoqon baran su roƙa mata Mustapha ya mayar da ita, ba tare da musu ba yace shi bai da matsala amma sai Maimoon ta dawo, bayan kwana biyu Asma’u ta koma Maiduguri.
Maimoon anyi bakwai ta dawo cike da kewan iyayenta, bayan dawowanta da kwanaki Hajja ta mata maganar Asma’u nan ta amince bakomai, ba ɓata lokaci aka qara ɗaura auren Asma’u da kuma Mustapha, rayuwa suke cikin kwanciyan hankali wanda a lokacin kuma aka gane Maimoon nada juna biyu kusan na watanni huɗu, kowa yayi farinciki, Mustapha ya dinga kula da ita da abun cikin ta, Asma’u ta sani Mustapha Maimoon yake so amma ganin itama tana sonsa sai ta kawar da kai tunda tasan Maimoon mai kirki ce kuma tana ƙoƙarin ganin sun zauna lafiya.
A lokacin da cikin Maimoon ke da wata 7 yaran Maryam na da watanni biyar a duniya kwastam aka wayi gari duk babu su, rashin yaran ya taɓa Maimoon sosai dan inka gansu tare kai kace ita ce ta haife su ba Maryam ba, abinda ke haɗa su da Maryam shan nono, cikin Maimoon na cika wata tara ta haifo santalelen ɗan ta namijin inda ya ci sunan kakansa MUFADDAL, sai Maimoon ta yiwa sunan alkunya da Darling. Maryam ta qara haihuwa yaro namiji ya koma ta qara haifo namiji lokacin Mufaddal na da shekara biyu sai akan wannan yaron mai suna Jabeer ya tsaya, tun Daga kan Mufaddal Maimoon bata qara haihuwa ba, har ya kai shekara biyar inda a lokacin Asma’u ta samu juna biyu ciki nakai haihuwa kuma a wajan naquda ita da yarinyar nata Allah ya amshi ransu, Maimoon tayi kukan rashin Asma’u sosai domin zaman lafiya suke yi.
Sai da Mufaddal ya cika shekara goma ciff a duniya sannan Allah ya azurta Maimoon da samun wani cikin wanda a lokacin kuma Maryam matar Nura ta haifi yara kusan 6 amma duk sun koma saura biyu, Jabeer mai shekara 8 sai Afreen mai shekara 2.
Maimoon ta haifo yarinyarta mace inda taci suna MUHSEENAN amma suna qiranta da sweedy daganan kuma bata qara haihuwa ba sai da yarinyar ta shekara biyar, nan ma mace ta haifa MUNAWWARA suna qiranta sweerie, wanda a lokacin bayan shekara guda Maryam itama ta haifo mace nan taci sunan Hajja suna qiranta Afrah, takwarar Hajja na da wata guda a duniya Allah yayiwa Alhaji rasuwa, wannan mutuwa ta girgiza alhalin Alhaji da ma ƴan Maiduguri dan kowa ya sanshi mutum ne mai haquri da kuma biyayya, bai kai mako guda ba tsakani mahaifiyar Maimoon itama Allah ya mata rasuwa, a lokacin Mufaddal na da shekara 16 kuma zuwa lokacin ya sauqe Qur’ani mai girma yana karantan business a India dan kusan acan ya tashi, Mufaddal yaro mai kyawu na wuce misali, ga haquri ga kuma zuciya sannan baya ɗaukan raini, tunda ya taso cikin soyayyan iyaye da kakanni duka ɓangare biyu sai dai Hajja da kawai suke kaman ‘yar stama kullum, ga shi dai tana sonshi sosai amma kullum cikin masa stiya take, shi kuma Allah ya wadata shi da saurin fushi ga zuciya sai dai yana da haquri da sauqa da wuri.
Sai da aka shekara biyar kamun Maimoon ta kuma haihuwan mace taci sunanta MUHEEBBAH suna qiranta sweetie, daganan kuma haihuwa ta staya wa Maimoon dan Maryam kam tana kan haihuwan amma tun daga kan Afrah yaran basa stayawa, ganin haka daga qarshe sai suka ɗaure mahaifan kawai, Allah yasa wa waɗanda suke da su albarka.
Tun da aka tura Mufaddal karatu a CANADA nan ya ce yaga wajan zama, ba tare da ansani ba takwaransa Dr Mufaddal ya saya masa gida ya buɗe masa babban Company, rayuwa yake hankali kwance yana Canada yana India in dai ka gansa a Nigeria sai an shekara, amma abun na damun Maimoon wacce suke qira da Ammi.
A ɓangaren familyn Alhaji kuwa rayuwa suke tsaftacciya, musamman Maimoon da Mustapha da yaransu ke qiransu da Ammi da Abiy, soyayya ne suke ma junan su ba na kaɗan ba, Abiy na qaunar yaransa da matar sa, da yaransa da yaran yayansa Nura da suke qira da Daddy inka gansu ba zaka banbance su ba, yaran duka kyawawa ne duk sun ɗauki kyawun kakansu Alhaji amma su sweetie sai nasu ya zama daban da suka haɗa da jinin indiyawa, shi Darling Mufaddal kuwa ya fita daban daga matan har mazan ba mai kyawun sa, Hajja duk tafi sonsa a jikokin ta sai kuma bi da Afrah takwararta, amma son da take wa yaran Mustapha daban ne ta rasa dalili, tun asali son da take wa Mustapha a cikin yaranta daban ne sai ya zama akan jikoki ma haka, amma bata nuna hakan dan gudun kawo rabuwan kai cikin zuria’anta.

Jabeer ma ya bi Mufaddal da abokanayensu ke ce masa DMD(Darling Mufaddal) suna Canada yana karantan likitanci, komai nasu tare suke yi, in ka gansu kace twins ne sai dai banbancin hali kawai, domin Jabeer da shi kuma abokanai ke ce masa Jay (Jabeer) mutum ne shi mai son surutu, ba shi da fushi ko kaɗan, akwai son kyauta ga son raha.
Dr Mufaddal da zuwa yanzu yayi ritaya kuma yake da tulin dukiya, ganin dai Maimoon mace ce sai komai nasa ya ɗaura Mufaddal wanda lokaci ɗaya Mufaddal ya zama babban attajirin mai kuɗi, rayuwarsu suke suna sharholiyan su amma ba ruwansu da harkan mata ko shaye-shaye barsu dai da yau ana nan gobe ana can, shi dai Mufaddal yana binsu ne dan yawanci komai shi yake biya amma ko yawan magana bayayi dan haka ya tashi surutu da yawa sai ya fara ciwon kai, akwai ranar da suka je wani club tun da suka matsa masa yayi rawa ya yanke jiki ya faɗi to tun daga lokacin ma ya daina binsu komai za’a yi yana gefe sai dai ya biya.

Kwastam wani zuwansu Maiduguri sai wata yarinya Rabi’atu ta maqalewa Abiy, duk da dai ba qaramar yarinya bace dan ta manyanta amma kuma bata taɓa aure ba, tun Abiy na basarwa har yaji shima ta masa, domin kuwa Rabi’atu ba qaramar makira ba ce ta kware a iya kirsa, Ammi tun da ta fahimci hakan sai bata nemi jan dogon magana ba da kanta ta samu Abiy ta ce masa gwanda ya aureta tunda tana sonsa kar ta sanya shi aikata abinda bai aikata da samartakan sa ba, Abiy dai yayi borin kunya daga baya ya sanar da Hajja, ita dai bata isa ta ce komai ba, dan abun ba qaramin karɓuwa yayi wajan dangi ba, masu haushin auren sa da Maimoon dama nan suka bada mubaya’a gwanda ya auri ƴar uwar sa tunda Allah yayiwa Asma’u rasuwa, ba jimawa aka ɗaura auren Abiy da Aunty Amarya (Rabi’atu).

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

 

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR’S ANNIVERSARY

FAN’S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

💋💋 امى بتولة💋

 

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 41_42

Tun da Abiy ya auro Aunty Amarya nan fa suka fara samun damuwa da Ammi, duk iya qoqari da haƙurin Ammi da kawar da kai amma sai Aunty Amarya ta kimsta mata munafurci.
A wannan lokacin ne kuma Hajja ta buqaci komawa Ashaka wai zaman Gombe ya ishe ta tunda babu mijinta, Abiy da Daddy sun-yi-sun-yi amma firr Hajja taqi zaman cikin Gombe, ganin haka ba yanda suka iya suka amince kawai aka gyara gidan su dake can Ashakan ya koma ginin zamani da komai da komai, suka nemo mata ‘yan aiki da driver da mai gadi, sai da aka zuba komai sannan aka sanya ranar komawanta.

Abiy zuwa wannan lokaci gaba-ɗaya ya sanjawa Ammi daga Mustaphan da ta sanshi ya koma wani Mustapha daban, a da dai ta san yana sonta amma a yanzu ba ta da bakin faɗan yana sonta amma kuma bata isa ta ce baya sonta ba, abubuwa ƙara kacamewa suke, akwai ranar da Hajja ta ga abinda Aunty Amarya ke yi na mugunta ga su Munawwara, faɗa ta mata sosai sannan ta stawatar wa Abiy da ya kwaɓi matar sa akan jikokinta ko su samu matsala, Abiy yama Aunty Amarya faɗa ita kuwa ganin haka sai ta nuna ta amshi laifinta duk da ba mugunta tayi ba amma kuma a gefe guda kistawa Hajja munafurci take yi, ba’a jima ba Hajja abun ya isheta ta koma Ashaka da zama, bayan Daddy ya bata Afrah su zauna tare.
Ammi dai komai aka yi sai ido take binsu da shi daga Abiy har Aunty Amarya ba um ba umn’umn, abu ɗaya ya isheta rashin zuwan Mufaddal, daga qarshe dai ta buqaci zuwa India amma Abiy da qyar ya amince bayan ya ce sai dai tabar masa yaransa ta tafi ita ɗaya, Ammi dai bata son ja’inja dan haka ta ɗauki Muheebbah kawai suka tafi, sun isa lafiya Dr Mufaddal da ya manyanta zuwa yanzu sosai yaji daɗin ganinsu, amma ganin yanayin yarinyar sa kaman tana cikin damuwa nan dai ya masta mata da tambaya amma ta ce ba komai daga qarshe fita harkanta yayi yana bin ta da addu’a, damuwan ta na rashin zuwan Darling gida kawai ta faɗa masa amma shima ya ce ba yanda baya yi da Mufaddal yaje Nigeria sai yaqi shiyasa ya fita harkan sa dan gaba kaɗan in ya mallaki hankalin kansa to zai je.
Cike da damuwa Ammi ta fara magana cikin Indianci dan sosai abun ke mata ciwo, Allah ya gani tana qaunar Mufaddal fin tunani “Papa yanzu Darling bai girma ba? Shekara ishirin da ɗori fa, yaro gaba-ɗaya baya son mu baya son zuwa wajan mu, ni abun na damuna dan kaman abun maita kullum qannensa cikin maganan sa suke yi, ni inaga qarshenta tattara su zan yi na kai masa su fama, ace yaro bazai waiwayi iyaye ba, gaba ɗaya yaja ana ganin laifi na, yaron nan ga mahaifinsa ga kakansa amma ba wanda yake tunanin zuwa dubawa sai ya dinga sanya ni damuwa kawai shi a barshi da iya qiran mutane kaman ance masa lokutan mu duka nasa ne ko da yaushe qira kawai..” cikin ɓacin rai Ammi ta dinga faɗa daga qarshe Dr Mufaddal da qyar ya danne zuciyarta bayan ya qira Mufaddal a wajan ya ce masa lallai-lallai nan da kwana biyu ko me yake yi yayi squeezing na sa ya zo, ganin yaron ya amsa zai zo ne nan hankalinta ya kwanta, suka dinga hira da mahaifinta har yake faɗa mata hukuncin da ya yanke na damqawa Mufaddal dukiyar sa, ba tare da taja ba ta ce “Allah ba shi ikon kula da dukiyan” da “Ameen” Dr Mufaddal ya amsa yana zolayan sweetie da ke kwance a jikinsa.

Ɓangaren Abiy da Aunty Amarya soyayya suke sha, dan Ammi na tafiya Aunty Amarya ta ji kaman ansarara mata an bata iska, ganin wannan sakewan ta qudurin aniyan koran Ammi a gidan, gefe guda kuma tana gallazawa Munawwara da Muhseena duk da dai ita Muhseena kusan halin Darling gare ta amma duk da haka Auntya Amarya sai da ta sanya mata karan zuqa.
Habibty (mummy) tana kallon duk abinda ke faruwa, amma ba ta da bakin magana dan akwai ranan da ta sanya baki amma abun ya zama magana har Daddy ya mata faɗa, ganin haka sai dai ta bar su a ɓangaren ta inkuma Aunty Amarya ta qira su to bata hanasu zuwa dan har dukan yaran tana yi kuma ta hanasu faɗawa kowa.
Sai da Ammi ta kwashe sati guda a India amma Darling bai zo ba, fushi tayi ta daina ɗaukan wayansa, ga hankalinta ya koma kan yaranta da mijinta da kullum sai ya qira yaushe za ta dawo, abun na bawa Ammi mamaki in dai tana gida kullum suna faɗan da babu dalili dan watarana haka kawai zai shigo ya dinga mata masifa batasan hawa ba balle sauqa, amma indai za’a ce yau ta ɗaga ƙafa ta fita to fa ko anguwa ne ya dinga qira kenan ta dawo, to abun na bata mamaki qarshe dai ta bar hakan akan yanayin rayuwa dan bata taɓa ɗaura alhaqin komai akan abokiyar zamanta ba.
Dr Mufaddal da dawowansu kenan daga zaga gari da yarinyar tasa da jikar sa, da mamaki yake kallon Abiy da ke tsaye cikin gidan kaman wanda aka ce wani nasa ya mutu, bayan sun shiga ciki sun gaisa Dr Mufaddal ya ja jikarsa suka basu waje, suna tafiya Abiy ya rungume Ammi wai yayi kewanta, qarshe ɗaki suka qarisa suka baza soyayyan su sannan ya fito ya sallami Dr Mufaddal ya koma Nigeria yana mata magiyan ta dawo, Ammi ko dan yaranta tasan ya kamata ta koma dan haka ta shiga shirin komawa duk da bata cika wata gudan da taso tayi ko dan ta hutawa rayuwanta, bayan tafiyan Abiy da mako guda ya kuma dawowa dan wannan karon da qyar ya yarda ya koma ba tare da ita ba, bayan kwana biyu da komawansa suka gama shiri zasu tafi har driver yasa kayansu a mota za su tafi kaman daga sama suka ji muryan Darling, sweetie wajansa taje da gudu ta maqale masa, Ammi dai fushi tayi zata tafi da qyar Dr Mufaddal ya rarrasheta suka zauna, nan kuma ta saki jiki da ɗan nata ya dinga zuba shagwaɓan sa kaman shi ne sweetie, tambayanta yayi “Ammi ina kika baro su sweedy?
Hararansa tayi a wasa ta ce “su kam suna gidan ubansu dan ba su da inda ya fi shi”.
Murmushi kawai Darling ya yi dan yasan nufin ta amma bai ce mata komai ba dan shi yasan dalilinsa na qin zuwa domin tun da Allah yasa Abiy ya auro figaggiyar matar sa shikkenan ya tsani gidan da kuma ganin cin kashin da akewa Ammi kuma bai isa yayi magana ba ita ta ce ba komai dan tana son mijinta, shagwaɓe fiska yayi kaman yaron goye ya ce “Ammi ku dawo wajena a Canada muyi rayuwanmu”.
Kallon yaro man kaza ba ka san me kake yi ba Ammi ta masa, sannan ta ce “in na bika wa zai zauna min a gidan miji na? Ko ka fara raba aljanna ba ni da labari?
“Please dai Ammi Allah hankalinmu kwance mu koma kinji, sweetie ai kina son zama a Canada ko? Ya faɗa yana kallon sweetie da ke cinyan Dr Mufaddal.
Sweetie washe baki ta yi ta ce “eh Darling ina so”.
“Please Ammi mu koma dan na tabbata su sweedy ma suna so”.
Hararansa tayi ta ce “tashi min a jiki nikam tunda aure na kakeso ka kashemun, in qannenka na so sai ka tattara su ba wanda ya hanaka kai ne babban yaya uba kuje can ku fama ni dai ina gidan mijina sai mutuwa kuma Insha Allah, hankalina a kwance a gidana ba inda zan je, kuma kai ma in kayi wasa ka gama zama a qasar waje kenan mu koma kayi aure muga jikoki”.
Tun da Ammi tayi maganan aure sai ya ɓata fiska ya miqe ya shige ɗakin sa, Dr Mufaddal dai yana kallonsu aikin murmushi kawai yake yi yana ƙara jin qaunar tilon yarinyar tasa da jikokinsa, haquri ya bawa Ammi akan ta qyale Darling a can ɗin da sannu a hankali zai fahimta, kuma batun aure in lokaci yayi zai yi.
Abiy ganin an kwana biyu ba idon Ammi nan ya qira ya dinga masifa sai ta dawo ko kuwa ya hanata qara zuwa Indiya, haquri ta basa kan cewa Mufaddal ne ya zo amma sam yaqi sai dai ta dawo shi kam tun da yaron baya qaunar su kar yazo yayi zamansa, abinka da uwa duk da haka sai da ta qara sati guda, Darling na komawa itama ta tattaro suka dawo, amma ganin yanda yaranta suka koma a zamanta na wata guda ma bai cika ba sai da ta tausaya musu, ga shi Abiy ya ce rashin lafiya suka yi, sai kawai ta yanke hukuncin da ta tafi ta barsu gwanda ta haƙura da tafiya kawai.
Rayuwa haka ta dinga tafiya ba daɗi da daɗi sai godiya ga Allah, zuwa yanzu kuwa Daddy ya koma sabon gidan sa da ke Tunfure kuma shi ma Abiy na ƙoƙarin komawa nasa sabon estate ɗin da ke anguwan manya GRA kusa da gidan abokin sa da ke takaran gomnan Gombe, Ammi dai tana ganin rayuwa amma duk da haka bata taɓa bari zuciyarta ta amince sharrin kishiya ne, komai barinsa take yi akan jarabawan rayuwa, tsakaninta da Abiy kuwa ya wuce misali kullum faɗa ba dare ba rana amma kaman kuran ƙarfe ko da ba ranar da yake ɗakinta bane za kaga ya shigo yayi masifa yayi soyayya, kuma duk abinda ke faruwa itama a ɓangaren ta baya damunta sai ma ƙara jin ƙaunar Abiy da take yi.
Hajja dai kullum cikin qiran Ammi take yi ta sauqe mata kondon masifa akan ta hana jikanta zuwa balle ya zo ya ganta, Ammi ta rasa ya zata yi dan ko da ta samu Abiy da maganan ya tsawatar masa ko zai dawo amma qarshe akanta masifan ya ƙaru domin Darling ko wayan Abiy da ya ɗauka bai ce qala ba har Abiy ya gama ya kashe, sai abun ya koma kanta ita ce ta sanya yaron ya rena kowa bata bawa yaransa tarbiyya ba, wannan rana Ammi tayi kuka domin Hajja ta goranta mata an aurota bare kuma Abiy ma ya goranta mata akan tarbiyya, dan haka qiran Darling tayi tana hawaye ta fara magana da Indianci “Mufaddal! Mufaddal! Mufaddal! Ka ji na qira sunanka sau uku ko, to wallahi na ranste in baka zo Nigeria ba babu ni babu kai, me yasa kake so a kanka adinga gayamun magana ne, ko haihuwanka da nayi shi ne laifin da na maka kai kuma, to tun raina bai ɓaci ba ka dawo dan baka isa na haifeka kuma kai ɗaya ka hanani zaman lafiya da mijina ba, in baka zo ba sai na saɓa maka kuma dolenka kayi aure kaji na faɗa maka” qitt tana gama magana ta kashe wayan ya share hawaye dan kar qannensa su shigo su gani, zama tayi tana mai bin yaran nata da addu’an shiriya da alkairi.
Bayan wasu kwanaki Ammi ta fita ta tafi gidan Daddy yara suna makaranta, hiransu suka sha da habibty tana faɗa mata yanda suka yi da Darling ta tabbata suna hanya, mummy murmushi tayi ta ce “amma Ammi kin kyauta dan kuwa wannan yaran zasu ja mana magana su kashe mana aure da girmanmu, na gaya miki jiyannan Hajja ta qira ta dinga surutu wai mun ɗaurewa yaranmu wajan zama basu son aure”.
“Ai Habibty yaran namu sai addu’an shiriya da stawatarwa irin nawa kam abun yayi yawa dan na rasa wani irin zuciya da hali ga Darling ko kaɗan baya storon kowa balle shakkan kowa, ko ni baya jin maganata”.
“To Allah dai ya shirya mana su ya kawo su lafiya” faɗin mummy.
Sai da suka gama shan hiran su har Afreen ta dawo ta mannewa Ammi kamun daga baya Ammi ta musu sallama ta shiga motan ta nufo gida, Afreen sai kuka take aikin yi za ta bi Ammi da qyar aka lallasheta sai weekend.
Ammi na isowa gida tun daga compound na gidan take jiyo muryan ihun Munawwara dan dama sun dawo makaranta ta sani, da sauri har tana tuntuɓe ta shiga gidan, abun ba qaramin mamaki ya bata ba ganin Aunty Amarya na aikin zane Munawwara, ko mostawa Ammi ta kasa sai muryan Darling da taji kaman daga sama ne ya dawo da ita daga hayyacinta, da mamaki take kallon sa yaushe ma ya zo har ya shigo gidan? Ganin abinda yake ƙoƙarin yi tayi saurin dakatar da shi tana faɗin “Darling Maman naka kake nunawa da yatsa tarbiyan da na maka kenan?
Ammi na rufe baki ta jiyo muryan Abiy yana faɗin “tabbas tarbiyan da kika musu kenan ba musawa dan haka kika nuna musu su tayaki kishi, in banda yaro ya zama fistararre matar tawa zai nuna da yasta to tabbas kuwa ka jawa uwarka”.
Da mamaki Ammi da sauran yaran ke kallon Abiy dan Darling ko ido bai ɗaura akan Abiy ba balle wani abun, kallon jan kunne kawai yake bin Aunty Amarya da shi, ita kuma kuka ta fashe da shi har da sheshsheqa tana faɗin “kayi haquri baby dan na hukunta yarinya akan tayi laifi shine laifi na amma ba zan qara ba komai ya wuce kuyi haƙuri” ta faɗa tana kukan kirsa ta wuce cikin ɗakinta.
Abiy da kallon za mu haɗu ya bi Ammi sannan ya juya ya bi matar sa, ita kuwa Ammi Darling ta zubawa ido, ta rasa me zata ce kawai ta shige ɗakinta ita ma.
Qannensa rungumesa suka yi suna kuka, haka ya ja su suka bi Ammi amma tayi fushi taqi sauraransa, suna zaune shiru can sai ga Abiy ya shigo a fusace ko me Aunty Amarya ta kista masa oho, yana shigowa ya kama faɗa ganin haka yaran suka fice a ɗakin, Darling dai yana zaune jikinsa sai rawa yake yana da-na-sanin shigowa Nigeria, bai gama dawowa daga duniyar tunanin da ya faɗa ba ya ji sauqar mari yana ɗagowa ya ga Abiy ne ya mari Ammi, idanunsa jawur ya miqe yayi kan Abiy amma Ammi sai ta riqe sa idonta ba ko ɗigon hawaye tana masa surutu “Mufaddal ba ka da hankali ne me za ka yi? Mahaifinka ne fa ko bayan wanda ka yi ɗazu wani abun za ka kuma yanzun? Da qyar da suɗin goshi ta riqesa qarshe dai kan gadonta ya faɗa a sume,hankalinta ne ya tashi tana jijjagasa, Abiy da ya storita yayi baya ko qala bai ce ba, ya ja staki ya fice, amma fa kana ganinsa kasan a storace ya ke da yanayin yaron nasa dan yasan da an barsa to fa akwai mastala.
Ammi ruwa ta yayyafa masa amma shiru, sai kawai ta sanya shi gaba ta dinga kuka, kaman wanda aka jefo haka Jay ya shigo ɗakin yana tambayanta me ya faru? Ganin Darling a wannan yanayin a take ya fara ba shi taimakon gaggawa wanda da ikon Allah da qyar ya dawo hayyacinsa amma yana riqe da kansa, qarshe sai da Jay ya ɗaura masa ruwa da allurori.
Ammi ta ga tashin hankali dan sai da ya ɗiba kwanki biyu kamun ya koma dai-dai, yana warkewa kuma ya tattara suka tafi Ashaka, sai da ya kwashe sati guda kamun ya dawo a ranan da ya dawo a ranan ya ce zai koma in yaso daga baya Jay ya bisa, Ammi kaman za tayi kuka haka ta lallashesa amma ya ai, daga qarshe dai barinsa tayi ya tafi tana jin kaman ta bi sa, sai kuma daga nan zuciyanta ya fara saqa mata zama da yaranta yafi wannan zaman tashin hankalin dan indai cutan Darling kenan akan ɓacin rai to tabbas yana buqatan mahaifiya ko mata a kusa da shi, amma kuma soyayyan Abiy sai ya danne wannan waswasin son bin yaron nata, haka ta dinga zama Abiy na fushi baya ko shiga harkanta.
Aunty Amarya buri ya cika nan ta dinga baza shagalinta, mummy dai komai aka yi sai dai ta bada haquri amma bata da bakin yin magana kar ace munafurci, Afreen da ke ɗawainiyan son Darling wannan abu da ya faru ya ja bata gansa ba sai ta yanke hukuncin qullawa Aunty Amarya gadar zare tunda taƙamanta takurawa mutane ga shi ta hanata kallon masoyinta, a gefen Hajja dai bata san me ke faruwa a Gombe ba dan yanzu a irin kirsan Aunty Amarya to ita ce ta gaban goshin Hajja sai dai abinka da soyayya da mai kula da kai na gaskiya, har lokacin tana jin Ammi daban a zuciyanta yanda tayi haquri ta dage har ta auri yaronta ta haifa musu kyawawan jikoki.

Sai da aka shekara biyu amma Darling ko ƙofa ta kashin Nigeria bai leqo ba, duk da tunanin qannensa da Ammi na azalzalansa amma da ɓacin ran da zai tarar gwanda masa zama anan yana kewansu, a gefe guda kuwa yana qara lallaɓa Ammi ta dawo Canada dan har kakansa sai da ya sanya a maganan amma Ammi dai ta ce gidan mijinta za ta zauna.
Ana haka Sweedy ta nemi da ta tafi India itama karatun ta amma sam-sam Abiy yaqi sai dai su yi a nan Nigeria, wannan abu ba ƙaramin ciwo yayiwa Ammi ba amma ta shanye tunda dai yaransa ne ba yanda ta iya, Sweedy na qiran Darling ta sanar da shi ba second thought ya shirya komai yanda ya dace, Abiy yayi tafiya zuwa China dan shigo da wasu kayaki na Companynsa masu yin hanya (kwalta) sai kawai Darling ya shigo Nigeria a ranan ya shirya sweerie da sweedy ba tare da ko Ammi ta sani ba ya tattara su suka koma Canada, ba karɓan transfer ba komai da yake kuɗi na aiki nan ya sanya sweerie a makaranta ita kuma sweedy ya fara mata duk wasu shirye-shirye da zata tafi India tayi karatunta bayan sunyi magana da kakansa.
Ammi dai tun fita yara shiru ba su ba labarinsu har dare, qarshe ta qira Darling amma layinsa baya shiga wanda hakan ke mata nuni da baya Nigeria, mamaki ne ya kamata ƙarara ta rasa ya zata yi, dan ko da ta qira layin Canada nan su sweerie suka ce su dai da Darling za su zauna, abun ya dameta ga shi bata san me zata faɗawa Abiy ba in ya dawo kuma ga shi yana dawowa za su koma sabon gidan sa na GRA.
Duk abinda ke faruwa Aunty Amarya na gani dan haka ta gama ƙulle-ƙullenta jira kawai take Abiy ya dawo ta juye masa dan ta ranste ba za’a koma sabon gida da Ammi ba, a gefen Ammi kuwa damuwa ya mata yawa ga kewan yaran ya qaru yanzu ba shi kaɗai ba har su uku, ga damuwan sweetie kullum ita dai yayyunta, ga kuma tunanin abinda Abiy zai yanke, duk abun Aunty Amarya dai Ammi kam baya gabanta dan har lokacin bata jin hausa sosai barta da English ko Indianci kuma yaren kanuri ko ka zo bata ji.

Abiy ba sanarwa kawai ya diro Nigeria, kallonsa ba ƙaramin girgiza Ammi yayi ba amma ta danne, kasancewan a ɗakinta yake nan ta tarbi mijinta, ba tare da ya lura da rashin yaransa ba suka sha soyayyan su, daga yanda Abiy ke tafiyar da Ammi insun haɗe zaka fahimci zallan soyayyan da yake mata amma sai ta rasa me yasa sukeeyawan faɗa.
Washe gari ya tambayi yara nan ta faɗa masa sunje hutu wai Canada, da mamaki yake kallon ta yana maimaita abinda ta ce “hutu a Canada! Yanzu lokacin hutu ne ko menene?
Ammi dai ta rasa ta faɗa daga qarshe dai ɓata mata rai yayi kamun ya koma ɗakin Aunty Amarya, nan kuma ya sanya su shirya za’a yi waliman buɗe gidan nan da two days sai a koma washe-gari in an gama waliman, ba tare da ɓata lokaci ba kowa ya fara shiri duk da dai komai na buqata an zuba a sabon gidan komai na zamani fin na wanda suke ciki, ba buqatan su ɗauki komai.
A ranar da aka yi walima, aka buɗe gida da addu’a da jama’a, sweetie ce ta yanka qyallen da aka sanya na buɗe gidan bayan ta sha kyaututtuka daga abokanan Abiy nan taro ya waste mutane kowa ya koma da takeaway banda wanda aka ci har aka bari.
A ranar da dare bayan dawowan Abiy yana zaune ɗakinsa, Aunty Amarya ta shiga ta kista masa ƙarya da gaskiya, aikam Abiy ya cika yayi fam, paper ya ɗauka yayi rubutu ya kai wa Ammi a daren kuma ya umurce ta da ta bar masa gida kuma kar ta tafi masa da yarinya, Ammi ta shiga tashin hankali a daren ta haɗa komai nata ba tare da ɓata lokaci ba da sassafe ta fito zata tafi, sweetie ta dinga kuka amma Ammi ta tsallake ta yi tafiyanta, Aunty Amarya daɗi ta dinga ji Abiy ya saki Ammi dan haka ta baje, washegari aka koma sabon gida.
Aunty Amarya taji daɗin sabon gida dan komai yayi sai dai baqin ciki take yi duk tulin wannan dukiya bata da ko kakkauran kashi balle ɗa ɗaya mai gada, nan ta fara damuwa ganin koma mene Ammi ce da riba.
Ammi na fita ba ta nufi Indiya ba dan kar ta ɗagawa Dr Mufaddal mahaifinta hankali, sai ta nufi Canada.
Su sweedy kaman daga sama suka ga Ammi, sunji daɗi amma rashin ganin sweetie abun ya dame su, Darling dai ya mastawa Ammi sai da ta faɗa masa komai yanda aka yi nan ya dinga farinciki Abiy ya sake Ammi sun huta, washegari ya shirya ya ɗauko sweetie ko ta kan Abiy bai bi ba.
Ammi taji daɗin ganin autar tata nan tayi murna ta rungumi yaranta suna rayuwa hankali kwance, bata kai wata guda da dawowa ba kawai suka ga Abiy wai ya zo su koma da Ammi da yaransa, ita dai Ammi ko sauraransa ba ta yi ba amma yaran kam abu da uba da ‘ya’ya sai Allah sunji daɗin ganin mahaifinsu, har Abiy ya tafi Ammi taqi kula shi.
Nan fa Abiy ya mai da Canada wajan sintirin sa duk bayan kwana biyu sai yazo kuma sai yayi kwana 2 ya koma, amma duk da haka Ammi ko kulasa ba ta yi duk da duk ranar da ya tafi sai ta ci kukanta a ɓoye, Allah ya gani tana qaunar mijinta kuma tasan shi ma yana sonta, a gefen Darling duk abunnan da ke faruwa yana gani kawai yaqi shiga harkan Abiy ne dan gudun ɓacin rana, kuma bai wa Ammi magana ba tunda yasan sun riga sun rabu to iya ƙoƙarin sa zai yi kar ma a mayar da auren.

Ko da mummy taji labarin nan ba ƙaramin mamaki tayi ba duk da tasan kaɗan kenan daga sharrin Aunty Amarya, kuma dama su kanuri zama da su a kishiya sai in Allah ya staga dan wasunsu basa zama banza, Daddy ma yayi bala’in shi sannan ya ce da Ammi kar ta yadda ta kula Abiy ta barsa ya gama haukansa tunda da girmansa yake biyewa munafurcin mace.
Hajja dai labari bai kai kunnenta ba, a lokacin kuma jay ya fara aikin asibitin sa, Afreen da suka samu huta ta dage sai ta je Canada dan haka ba wanda aya hanata tayi tafiyanta tunda kowa yasan soyayyan dake tsakanin Ammi da Afreen da yake Afreen takwarar Ammi ce.
Abiy fa tun yana ɗaukan abu wasa har ya zama gaske, Ammi taqi ba shi dama ya mata bayani balle yayi yunqurin bata umarni ta yarda ta bi, ɓangaren Aunty Amarya ba abinda ya dameta tana farantawa Abiy tana rayuwanta qalau, dan babbar damuwarta dama Ammi da yaranta ne kuma ga shi cikin ruwan sanyi sun tafi sun bar mata gidan.

Abiy Darling ya sama akan yawa Ammi magana ta sauraresa duk abun bai kai haka ba, amma ko kallon kirki Darling bai yiwa Abiy ba domin duk sanda ya ɗaga ido ya kalli Abiy ba abinda ke faɗo masa sai marin da ya yiwa Amminsa da kuma wulaqanci wai a sunan soyayya.

Wasa-gaske Ammi watanta 2 a Canada kuma Abiy bai bar sintiri ba, sannan ita kuma bata kulashi ba, ganin abun yaqi ci kuma yaqi cinye wa sai Abiy ya niqa garinsa ya kama hanyar India domin yasan in ba tanan ya biyo ba ba zata sauraresa ba.
Abinda Abiy bai sani ba kuwa ashe Aunty Amarya ta gama shafawa mutanen Maiduguri kan cewa ya saki Ammi, suna can suna ta farinciki har da ita ba wanda yasan sintirin da Abiy yake na ganin Ammi ta dawo gare sa.

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR’S ANNIVERSARY

FAN’S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

💋💋 امى بتولة💋

Wannan page naku ne masu daraja

Surayyatou (habibtyna)

Ummin karima

Amina khamil

Deejer nata’ala

Maman abdusamad (kakata jidda)

Ƙawata Salima(Maman unborn)

Ummu muhammad

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 43_44

Abiy na sauqa a India ya nufi gidan Dr Mufaddal, cikin Sa’a kuwa ya same sa a gida dan dawowansa daga ganin likita kenan.
Bayan Dr Mufaddal ya ma Abiy iso sun zauna sun gaisa sai ya numfasa yana magana ganin yanayin Abiy da ke nuni da akwai mastala, da hausansa da ba sosai ya nuna ba ya ce “Mustapha ince dai Maimoon ba wani laifin ta maka ba?
Cin girmamawa Abiy ya ce “Papa ba wani laifi ta mun ba illa iyaka nine mai laifi, Maimoon na iya ƙoƙarinta amma abubuwan sai a hankali, to kwana biyun nan nayi tafiya ina dawowa na tarar gaba-ɗaya yara sun tafi Canada ba tare da izini na ba, abun ya ɓata min rai har ya kai mun samu saɓani da Maimuna har dai na bata takarda to sai ta tafi Canada,to bayan an kwana biyu naje akan tayi haquri mu dawo amma taqi saurara na kuma shi ma yaron yaqi taya ni bata haƙuri, dan Allah a bata haƙuri ta dawo Papa dan na gane laifi na kuma Insha Allah ba za’a kuma ba”.
Murmushinsu na manya Dr Mufaddal yayi kawai ya girgiza kai dan mamaki yake har yanzu daga Maimoon har Mustapha kaman akwai yaranta a kansu, duban Abiy yayi ya ce “Asshhha! Asshhha! Amma wannan abu sam bai yi daɗi ba, Mustapha da girmanka sai ka biyewa Maimoon? Kun girma fa zuwa yanzu kuma kun tara yara bai kamata abinda ba kuyi a yaranta ba kuyi shi da girmanku da yaranku wanda na tabbata da Mufaddal yayi aure to da kunyi jika kuma, zan mata faɗa Insha Allah za ta koma amma fatan sakin dai auren bai ƙare ba? Kuma a dinga haquri da iyalai, domin su mata da kake gani ‘yan lallami ne da kuma rarràshi, mulki ne da su ba kaɗan ba, mu yi haquri mastayinmu na shugabanni samansu mu zauna lafiya domin ƙwaƙwalwan mace wani lokacin sai a hankali, a dinga haquri Mustapha, yaro kuma ku cigaba da masa addu’a Insha Allah zai gyaru duk yarinta ke damun Mufaddal daga zaran aka ce yau ya ajiye mata to komai zai daina ku dinga haquri”.
Abiy cikin jin daɗin maganan Dr Mufaddal da kuma mamaki wanda ya gauraye da jin daɗin ya faɗa duniyar tunanin “saki aure bai ƙare ba kuma?” Cikin mamakin abinda kusan kowa ke ɗaukan barin maimuna gidan ya dinga jujjuyan maganan Dr Mufaddal har sai da ya qira sunan sa kamun ya dawo daga duniyan tunanin yana faɗin “Papa ba wani sakin da ya shiga stakanina da Maimuna, bansani ba ko ta ɗauka a sakin ne amma ni ba haka na rubuta a takardan ba, kuma ina ta qoqarin bata haquri na fahimtar da ita amma taqi saurarana”.
Dr Mufaddal jinjina kai yayi kamun ya ce “to Masha Allah! Allah kiyaye na gaba ya ƙara muku haquri, Allah albarkaci zuria’anku, in Allah ya yarda za ta koma karka sa damuwan komai, irin tunanin matan kenan, kaga bata buɗe takarda ta gani ba ta hau dokin fushi, su mata guntun zuciya gare su, Allah muku albarka duka”.
Da “Ameen” Abiy ya amsa kamun suka ɗan tattauna daga bisani yawa Dr Mufaddal sallama, ya kamo hanyan Nigeria da nufin bayan kwana biyu zai koma Canada.

Ammi da yaranta zaune a babban palourn gidan nasu, Darling ne ya shigo sanye da suit wanda ke nuni daga office yake, zama yayi a kujeran da Ammi ke zaune mai ɗaukan mutum uku, kansa ya kwantar a qafan Ammi yana lumshe ido, sweedy ganin haka sai ta taso daga inda take zaune ta zo ta cire masa takalman sa sau-ciki tana magana cikin harshen Indianci “Darling sannu da dawowa”.
Gyaɗa kai kawai yayi bai ce uffan ba, Ammi ganin haka sai ta murmusa tana cike da mamakin halin wa Darling ya ɗauko dan dai iya saninta wasu halayyan nasa sun ɗarawa na mahaifinsa nesa ba kusa ba.. muryansa ne ya kaste mata zancen zuci da take saqawa.
Da Indianci ya ce “Ammi ya naga kina ramewa ko kewan Abiy ne?
Sanin halin sa sai ta murmusa cikin zolaya ta ce “to dama ta ya ba zanyi kewan mijina ba, kunbi kun kanainaye masa mata, ai na kusa komawa sai kuyi zamanku abinku amma nikam gidan mijina zan koma”.
Kwaɓe baki yayi kaman mace ya ce “Ammi cin fiska ba kyau, ai munfi Abiy buƙatan zama tare da ke”.
Murmushin ta kuma yi wanda ke nuni da yaro man kaza, tana faɗin “aikam dole ka ce haka tunda kai ka kasa yin matan, to ba da Maimoon ba ni gidan mijina ma zan koma gwanda kasan na yi tun wuri da qannenka tunda kai kaje ka ɗauko su duka, dan haka in na tashi komawa ma daga ni dai jakan kayana zan koma, in zaka nemo mata ta riqe maka qanne in kuma za ka mayar da su ka haɗu da Abiynku ba ruwa na, in kuma ka masta na koma da su to fa sai dai a koma da kai kaima kabar Canada kenan”.
Lumshe ido ya kuma yi bai ce uffan ba duk da kasancewar yana da abun faɗan, a haka ma dan yana tare da Amminsa ce domin in ba ita ba ba shi da lokacin dogon zance balle shagwaɓa ko dariya.
“Baban Amminsa” ta qira sa a yanayi na magana mai muhimmanci take so suyi.
Buɗe kyawawan idanuwansa yayi da suka rine zuwa ja, a hankali kaman zai yi kuka ya ce “na’am Ammina”.
Kallonsa tayi ganin yanayin fiskansa sai ta girgiza kai kawai ta ce “baban Amminsa me mastalanka da maganan aure? In wani abun na damunka ko in akwai wani mastalan ka faɗamun ni mahaifiyarka ce bayan ni ba ka da wacce ta fini inka cire mahaifinka da matar da za ka aura, me mastalanka da kake qin aure?
Qannensa ya kalla da idanuwan nasa da suka rine, ganin kallon nasa duk sai suka miqe suka haura sama, mai da idonsa yayi ya rufe kamun a hankali ya buɗe baki ya ce “Ammi lafiyana qalau”.
“Darling lafiyanka qalau, to ko matan ne ka rasa? Naga dai alhamdulillahi Allah ya horewa yarona kyau, ilimi, kuɗi, nasaba, duk wani abu da mace ke buƙata wajan mijin aure kana da shi dan ko halinka sai wanda bai fahimceka ba ne zai yi ƙorafi akan hakan amma Masha Allah! Kana da haquri, kau da kai, ko kayi fushi kana sauqowa da wuri, rashin magana ma na sani inhar ka samu mace to tabbas a gabanta wannan stohon zance ne dan sai abinda ta buqata za ka faɗa surutu sai ta ce kanari, please son kar na mutu banga jikoki na ba” ta qarisa maganan tana kamo hannun sa.
Jikinsa ne yayi sanyi amma duk da haka shi ya sani ba shi da yanda zai yi, ko kaɗan baya jin buqatan mace ko kaɗan baya ganin mace yaga ta burge sa, shi in mace tayi ƙoƙarin taɓasa ma ji yake kaman ya kashe kansa ko kaɗan mace bata gabansa baison maganan mata, shi kansa yayi gwaji yafi a irga amma lafiyansa qalau result ke nunawa amma ko kaɗan baya jin buqatan mace balle yayi kwaɗayin aure, wahalallen numfashi ya sauqe tare da furzar da iska mai zafi da huci ya miqe ya zauna tare da jingina kansa a jikin kujeran da suke zaune, idanuwansa a lumshe dan ya rasa amsan da zai baiwa Amminsa, qarshe miqewa yayi ba tare da ya ce qala ba ya nufi step’s da zai sada shi da ɗakin sa, Ammi kuwa bayansa ta bi da kallo tana murmushi kawai, tana faɗin “Ni Maimoon banda ta cewa sai dai fatan alkairi da binku da addu’a, Allah ya sanya jinkirin na alkairi ne kuma Allah qaddara min ganin jikoki na, Allah shiryamun ku ya muku albarka, qannenka ma Allah basu mazaje na gari da ma duk sauran yara da basu da aure, Allah stare mana ku ya stare mana mutuncinku” murmushin ta kuma yi a zuciyarta tana tuna mutanen Maiduguri da dokan su, qarshe dai itama miqewa tayi ta haura saman tana jinta cikin kewan Abiy sosai.

Yana shigewa haɗaɗɗen part nasa, direct akan kujera ya wa kansa masauqi, kwanciya yayi yana riqe kansa ya rasa me ke damunsa, qira ne ya shigo wayansa, ganin layin Jay sai yaja guntun staki ya kaste qiran dan in ya ɗauka to surutun Jay sai ya sanya shi zazzaɓi ya sani.

Ammi da haurawanta sama kenan wayanta ya ɗau kara, ganin layin Jay sai ta ɗauka tana faɗin “my boy ka qira Ammi bata kusa a mata afuwa ina can ina fama da ɗan uwanka da rashin jinsa”.
Murmushi Jay yayi a ɗaya ɓangaren ya ce “Ammi sai haquri da mu, dana Afreen ce sun kusa isowa wai za ta taho Hutu wajanki”.
“Ah! My boy shi ne sai yanzu za ka sanar min? Shikkenan kaste waya ba naje driver ya kai sweedy ta ɗauko ta”.
Kashe wayan Ammi tayi, ta laluɓo Numbern Sweedy, tana ɗauka ta ce “maza-maza ki shirya driver ya kai ki airport Afreen na hanya” tana gama faɗa ta kaste qiran ta wuce toilet, alwala ta ɗauro ta fito, tana ɗaga wayan ta ga misscall na Papa amma sai ta bari sai tayi sallah ta qirasa.

Sweedy shiryawa tayi cikin riga da wando ta ɗauko top ta ɗaura da hulanta, ta ɗau wayan ta ta fice.
Driver ta samu ta yiwa magana, ya ɗau mota suka nufi airport, suna isa ba jimawa jirgin su Afreen yayi landing, cikin farin ciki suka rungume juna suka shige mota driver ya kawo su gida.
Afreen tun da ta shigo palourn ta Lumshe ido, jin ƙamshin abun qaunanta, sai ta bi step’s da zai sadaka da part nasa ta kallo tana jin farinciki mara misaltuwa, Murmushin da take yi har sweedy sai da ta ankare sai kawai ta girgiza kai a zuciyar ta tana faɗin “Allah ya sa Darling ya aure ki dear”.
Sama suka haura har ɗakin Ammi, ba qaramin daɗin ganin Afreen Ammi ta ji ba nan ta rungumeta kaman za ta maidata ciki, har ta manta da misscall na Dr Mufaddal.
Da dare duk suna zaune a dinning a sashin su suna cin abinci, Ammice ta ce “wai nikam yau rashin cin abincin ya mosta wa yayanku ne bangansa ba?
“Ammi ai Darling kam ni rasa da ne yake rayuwa a cikin sa nake, ba ya cin abinci fa, gaskiya matar Darling aiki ya ganta sai ta dinga feeding nasa ko ɗura ma” cewar sweedy da ke saving na kanta.
Murmushi Ammi ta yi ta ce “to dai Karki sake ya jiki ba ruwana, yanzu ku kai masa wani abun sashin sa ko”.
Sweedy ta maida kallonta kan Afreen ta ce “dear ki kai wa Darling abinci”.
Ammi buɗe baki tayi ta ce “Muhseena ashe ba ki da kirki? Yaushe daughter ta huta da zata kai abinci, maza tashi ki kai masa yanzun nan kamun na saɓa miki”.
Sweedy tura baki ta yi za tayi magana sai Afreen ta kasteta ta miqe ta fara jera abincin dan tasan mai yake son ci da dare ko da ya je Nigeria, kuma maganan sweedy ya mata daɗi za ta samu ta ga “peace of mind” sunan da ta sanya masa.
Ammi ganin haka sai bata ce uffan ba ta ci gaba da cin abincinta, Afreen haɗa komai ta yi ta ɗauka ta fice a palourn, a hankali take haura step’s ɗin har ta isa bakin qofan, knocking tayi shiru ba’a amsa ba, jin shiru sai ta tura qofan ta shiga.
Wani irin lumshe ido tayi wanda tunanin da take yi ya sanya idanuwanta cika da qwallah, a hankali ta furta “Allah ka nunamin ranan da za’a kawo ni wannan sashin a matsayin matar Darling Mufaddal” mostin da ta ji ne ya kaste maganan nata tayi saurin saita nustuwarta.

Tun da ya kaste qiran shi ne bai mosta ba sai da ya ji MuslimApps da ke wayar sa na qiran sallah sannan ya miqe ya haura sama inda ɗakunan sa kenan, alwala yayi ya gabatar da sallahn sa sannan ya cire kayan jikinsa ya shige toilet dan ya watsa ruwa , ko da ya shiga jacuzzi ya sakarwa kansa shower sai da ya kwashe kusan awa 3 kamun ya fito dan bacci ne ma ya fara kamasa a cikin abun wankan jin ruwan ɗumi da ya sanya masa nistuwa.
Yana kwance daga shi sai towel a qugun sa ya ji kaman mosti sai ya nemi short ya sanya ya saka 3quater sannan ya nufo sauqowa palourn nasa na qasa dan duk zatonsa su Sweedy ne shiyasa bai damu da sanya riga ba.
Qarasowa palourn yayi ba tare da ya kalli wacce ke zaune ba, ya zauna a kujera mai ɗaukan mutum guda yana faɗin “empty tea” da harshen Indianci.
Afreen da tun isowansa palourn duk wani laƙa na jikinta ta neme shi ta rasa, faɗi take a zuciyanta “ya subhanallah!! Allah ka mallaka mun wannan haɗaɗɗen bawan naka da ko shi ya stara kansa ba zai kai haka haɗuwa ba..” maganan nata ne ya kaste jin daddaɗan sautin sa na magana da Indianci ita kuma ga shi ba ji take yi ba, ɗan yastine fiska ta yi kamun a hankali ta furta “peace of mind banji ba”.
Da mamaki DMD ya juyo yana kallon wacce ya ji muryanta, kallo ɗaya ya mata ya lumshe ido a ransa ya furta “yarinya ƙarama sai iyayi” dan ya ji sunan da ta qira sa da shi.
“Shayi empty” ya maimaita a taqaice.
Haɗa masa tayi ta miqa masa ya karɓa yana kurɓa idanuwansa na kan TV, ita kuma ta mai da shi TVn ta har sai da yayi kaman zai qware sannan ta dawo hayyacinta ta maida ido kan TV itama.
“Yaushe kika zo” kaman daga sama ta ji muryan sa yana tambayanta, sai kuma ta juyo ta kalli kaman ba shi yayi magana ba, murmushi tayi na jin daɗi sannan cikin kwantar da murya ta ce “ɗazu ne, big bro na gaisheka, mummy na gaisheka, Daddy na gaisheka”.
Jin yayi shiru bai ce komai ba ta ɗago ta kallesa, ta ga kaman dai ba da shi take maganan ba, kaman za tayi kuka haka ta qara zuba masa idanuwa.
Cikin gajiya da kallon da take masa ya ce “za ki iya tafiya” yana gama magana ya miqe ya haura sama.
Tattare cup’s ɗin tayi sannan ta miqe ta fito a sashin tana jin farinciki abinta ta koma sashin su Ammi.

Yana haurawa sama ya shirya sama-sama ya ɗau makullin mota ya sauqo, ganin duk basa palourn ya ciro wayansa ya qira layin Ammi yana faɗin “Ammi na fita sai na dawo”.
“A dawo lafiya Darling”.
Qitt ya kashe wayan ya fita, driver na ganinsa ya nufi ɗauko mota amma sai ya dakatar da shi, ya shiga wata arniyar mota qirar 2020 ya ja ya fice a gidan.

Washegari da wuri Ammi ta sanya su suka shirya breakfast, sweedy ta tura dan ta qira Darling ya fito yayi breakfast, amma ta dubo baya sashinsa wanda da alama bai ma kwana a gidan ba, mamaki Ammi ta dinga yi akan inda yaje tunda tasan ba halinsa bane yin dare a waje balle kwana a waje, amma sai ta share tana addu’an Allah yasa lafiya.
Bayan sun gama breakfast, masu aiki suka tattare wajan, Ammi da yaranta kuma duk suka koma bacci, sai Afreen kawai da ke dakon shigowan Darling.

Tuqi yake da mugun gudu duk da kasancewar safiya ce amma burinsa ya isa gida akan lokaci dan yasan Ammi nacan ta damu ya kwana a waje bai sanar mata ba.
Dai-dai lokacin da ya iso bakin gate ɗin gidan yayi dai-dai da isowan Dr Mufaddal shima, da mamaki Darling ke kallon sa yana murmushin sa mai stada, dan a rayuwansa bayan Ammi da ‘yan uwansa in akwai wanda yake mugun qauna da kuma iya masa dariya to kakansa ne.
Yana gama parking ya fito ya rungumi Dr Mufaddal ɗin yana magana da Indianci “landlord ka zo amsan kuɗin haya ne irin wannan sammakon” ya faɗa yana kan murmushin.
Dr Mufaddal girgiza kai yayi yana sansanyar dariya cikin qaunan takwaran nasa kuma jikansa namiji kawai ya ce “in ba’a biya ba kuma a bar mini gida yanzun nan”.
Suna murmushi duka suka nufi shiga cikin palourn, mostin qafan mutum da suka jiyo ana sauqowa daga kan step’s ɗin sai duk suka kai kallonsu wajan da tunanin ko Ammi ce, ganin mai sauqowa Darling kau da kai yayi yana faɗin “fitinanniyar yarinya”.
Dr Mufaddal na murmushi yayi magana da turanci “ah! Lallai na iya zuwa a dai-dai, ga Amarya ga ango an haɗu sai a ɗaura kawai mu koma India in kuma ɗan-kwali ya ja hula sai ku koma Nigeria” ya faɗa yana darawa, Afreen da ta qariso palourn tana murmushi itama ta ce “stoho mai ran qarfe sannu da zuwa, amma dai ni kamun stufa sabon jini nake so” ta faɗa tana satan kallon Darling da ya kusa shigewa sashinsa dan bai san ma suna yi ba.
Afreen ruwan sha ta kawo wa Dr Mufaddal da kayan kari ta ce “Angona bari na qira maka Amminmu” ta juya ta nufi sama wajan Ammi.
Tana isa shiga palourn sama dai-dai Ammi na fitowa a ɗakinta tana faɗin “daughter hayaniyan me nake ji, ko Darling ya dawo ne?
“Eh Ammi, ya dawo amma tare da stoho mai ran ƙarfe na gansu, yana palourn ƙasa ma na ce masa ne bara na qira ki”.
Ammi da sai yanzu ta tuno misscall’s na Papanta ai wara ido tayi tana faɗin “Papa dai?
Afreen na murmushi ta ce “shi ɗin dai Amminmu”.
Kamun ta ida rufe baki Ammi har ta fice a palourn, da sallama ta shiga palourn qasan tana faɗin “sannu da zuwa Papa”.
Dr Mufaddal yana murmushi ya ce “yauwa Maimoon”.
Qarisowa tayi ta zauna gefensa tana gaishe sa.

Darling yana haurawa sama, ya wasta ruwa sannan ya sanya kayan shan iska da suka yi matuqar ansan sa, palourn sa na qasa ya dawo sannan ya shige kitchen nasa, sama-sama ya samawa kansa abinda zai sanya a cikinsa sannan ya gyara komai ya fito ya kulle qofan ya nufi wajan su Ammi.
Ammi na kallonsa ta fara murmushi dan kullum gani take yaron nata na qara kyau “baban Amminsa sai yanzu aka shigo?
Dr Mufaddal na murmushi ya ce “ai Maimoon yaronki ya renani nima, halin ‘yan adam yake nuna min wai nazo amsan kuɗin haya ne da sassafe, ina laifi nazo naga lafiyansa tunda shi baya tuna kowa”.
Darling na Murmusawa ya zauna gefen Ammi ya gaisheta sannan ya fidda wayansa yana dannawa.
Dr Mufaddal girgiza kai yayi kawai a ransa yana faɗin “sarautan da bamu da ita ta mosta”🤣.
Ammi ne ta dubesa ta ce “yau ba zuwa office ne?
Lumshe ido yayi tare da jingina kansa a jikin kujeran yana faɗin “akwai zuwa office Ammi, sannan companyn da ke Jigawa ma suna buqatar gani na, ga kuma wanda ke Zamfara wai meeting kuma dole sai da ni, gaskiya ni sayar da companies da ke Nigeria duka zan yi banson headache da yawa ba son zuwa Nigerian nan nake ba”.
Da mamaki Ammi da Dr Mufaddal ke binsa da kallo, Ammi ce ta fara magana “kuma sai aka yi rashin sa’a a Nigeria aka binne cibiyanka ba, citizen of Nigeria by birth ba ka da inda ya fi shi, duka ka shirya zuwa ka tabbatar ko bayan raina baka sai da qadaranka ko guda ba a Nigeria”.
Dr Mufaddal ne ya numfasa ya ce “ka tabbatar ka halaccin meeting ɗin amma ka kula dan naji kaman Zamfara akwai issues a garin ga kidnapping ga sace-sace so ka kula”.
Darling kaman zai yi kuka kawai ya miqe ya fice a Palourn.

Sweetie ce ta fara fitowa ta kalli kakan nasu ai da gudu ta koma ta tashi sweerie inda hayaniyan nasu ya tashi sweedy ita ma a baccin, jin sweetie na faɗin kakansu ya zo duk ba shiri suka wanke fiska suka fito palourn suna qiran sunan sa.

Dr Mufaddal jin muryan jikokinsa sai ya fara washe baki, ya buɗe hannu duk suka zo suka shige jikinsa suna faɗin “grandpa yaushe ka zo? Sannu da zuwa, ina staraba?
Yana murmushi duk ya amsa musu, sannan sweedy tabar jikinsa, sweetie da sweerie suka maqalqalesa, Ammi ce tayi magana su tashi amma sweetie yaqi sauqa a jikinsa, ita sweerie kuma ta sauqa ta zauna gefensa suka sanya shi a gaba suna masa hira.
Ammi miqewa tayi tabar palourn, wanka tayi ta shirya sannan ta dawo ta korasu suyi abincin rana su bar Papa ya huta.
Dr Mufaddal ɗakin da yake mallakin sa a nan palourn qasa ya shige ya wasta ruwa sannan ya kwanta dan ya huta.

Sai da suka gama ayyukan abinci sannan duk suka yi wanka Ammi ta sanya sweedy ta qira Papa, Afreen kuma ta qira Darling, Papa sun fito tare da sweedy amma Darling Afreen ta samu baya sashinsa, qiransa Ammi tayi ya tabbatar mata yana office sannan suka wuce dinning duka, Afreen ce tayi saving nasu kowa ya fara cin abincin cikin nistuwa ba tare da surutu ba.

Zaune yake a office nasa hankalinsa gaba ɗaya na kan aikin da yake yi a system nasa, knocking da aka yi ne ya sanya shi mai da idanuwansa kan ɗan computer da ke jone da CCTV camera da ke wajan office nasa, ganin wanda ke staye a qofan sai ya buɗe baki kaman baison magana ya ce “come in”.
Mutumin ne ya buɗe ya shigo, sai da ya basa izinin zama kamun ya zauna, inaduwansa na kan system da yake aiki a kai ya ce “Yes”, jin haka sai mutumin da ya shigo ya fara masa bayani a nuste, sai da ya kammala bayaninsa sannan a nuste cikin girmamawa ya ɗaura da cewa “Oga akwai buqatan shiganka Nigeria dan kayan da aka kama ba kaɗan ba”.
Har mutumin ya gama magana ko mostawa bai yi ba balle ya kallesa, gaba-ɗaya idanuwansa na kan system nasa, sai da ya ɗau mintuna masu yawa sannan ya janye system ɗin zuwa gefe ya sanya hannu ya rage tied na wuyansa, kaman baison magana ya ce “ba mastala za ka iya tafiya” daga haka ya danna wani button akan table da ke gabansa, sai ga wata baturiya ta shigo, ba tare da yace mata komai ba ta wuce ta ɗauko masa magani a cikin wani haɗaɗɗen box ta miqa masa, sai da ya sha sannan ta mayar, mutumin ya fice itama ta fice, duba time yayi, ganin lokacin kaman zai yi kuka ya miqe ya shige haɗaɗɗiyar toilet nasa ya ɗauro alwala sannan ya fito ya shige wani daki da ya gaji da haɗuwa ya shumfiɗa sallaya ya gabatar da sallahnsa.
Da ya idar ya fito ya kuma jawo system ɗin ya cigaba da abinda yake yi.

Mutumin na fitowa daga office na DMD ya tsaya jin maganar abokin aikinsa “John daga ina?
Wanda aka qira da John ɗin ya ce “daga office na Oga, kasan wannan karon ansamu mastala”.
“Wai ai naji maganan, kaya ba kaɗan ba, Oga sai ya kasa zama”.
John na dariya ya ce “nima nayi tunanin hakan, amma bakasan abun mamaki ba, in kaga Oga kaman ba abinda ya faru, dan cemun yayi ba mastala, ni na rasa Oga wani irin human being ne ba’a gane yana farinciki ko akasin haka, kullum fiska ɗaya kuma ko ba shi yayi dogon magana ba indai aka masa sai ya sha magani”.
“Hhhh! John ai lamarin Oga sai a hankali, mu wuce eatery antashi break lokacin sallah yayi” suka nufi lifter suna kan hiransu, duk abinda suke faɗa da turanci suke faɗa.

Sai da ya kammala komai sannan ya fito, sect.liliyan tana binsa riqe da wayoyinsa da jacket nasa har sai da ya shiga mota sannan ta juya, driver ya ja suka nufi gida.
Suna isa driver na gama parking ya fito bayan ya tattare wayoyinsa, da sallama ta shiga palourn amma ganin ba kowa sai hakan ya masa daɗi dan dama a gajiye yake, kawai sai ya haura sama sashinsa, ruwa ya wasta ya bi lafiyan gadonsa ya kwanta.

Sai dare kamun ya sauqo palourn qasa, inda ya tarar da Dr Mufaddal da su Sweedy duka, Afreen na ganinsa ta miqe tana masa sannu da shigowa, ba tare da yace qala ba kawai ya ɗaga mata kai tare da zama gefen Dr Mufaddal yana faɗin “landlord yaushe za ka koma?
Dr Mufaddal abun ma dariya ya basa, sai ya ce “korana kake yi kenan? Dan ma nazo ganinku ko”.
Shiru Darling yayi bai kuma cewa komai ba illa wayansa da ya ciro yana laste-lastensa.
Sai can Ammi ta fito, suka yi dinner sannan ya tashi zai haura sama amma sai Dr Mufaddal ya dakatar da shi akan za suyi magana, su sweedy ya kora kowa ya je ya kwanta, dukansu haurawa sama suka yi inda suka kunna TV suna kallo, sweetie ce taqi binsu sama wai ita wajan Dr Mufaddal za ta kwanta, kallon da Darling ya aika mata da shi ne ya sanyata miqewa tana kuka ta haura sama itama, ganin haka sai ya taɓe baki kawai, Ammi da ke zaune tana jinsu murmushi ta yi tana faɗin “ka takurawa jinjirata, mutum da Angonsa za ka korasa ga shi ka sanya mun Auta na kuka, in na mutu zaka kula da sweetie kuwa Darling?
Shi dai shiru yayi bai ce komai ba, ganin haka sai Dr Mufaddal yayi gyaran murya tare da cewa “Maimoon je ki ɗauko min takardan da Mustapha ya baki”.
Ammi shiru tayi kaman wacce ruwa ta cinye ta, dan mamaki ya kamata na yaushe Papa yasan da maganar wani takarda, amma sai ta fuske ta ce “Papa wani takarda kuma?
Kallonta kawai yayi ya murmusa nasu na manya ya ce “Maimoon banson magana biyu ke kinsani, ina takardan da Mustapha ya baki? Inkuma bai baki takarda ba me ya dawo da ke Canada da zama? Ko kin manta me kika ce a India lokacin da Mufaddal ya buqaci ki dawo Canada ku zauna”.
Ammi qasa tayi da kanta ta kasa cewa komai, amma mamaki take wa ya sanar masa, tasan dai Abiy ba zai sanar masa ba kuma Mufaddal ma haka, sannan yaran ma ba zasu sanar masa ba, gaba-ɗaya kanta ya ɗaure, maganan Dr Mufaddal ne ya dawo da ita daga tunanin da take yi “Maimoon ba da ke nake magana ba?
Darling dai yana zaune shiru, yana danna wayansa bai ko ɗago ba balle ya ce musu uffan, Dr Mufaddal ne ya sake magana sai Ammi ta miqe ta haura sama, ɗakinta ta shiga ta buɗe drawern ta ta ɗauko takardan ta dawo da shi, cikin girmamawa ta miqawa Papa amma sai bai amsa ba ya mata nuni da ta zauna, zama ta yi sannan ya ce “inaso ki buɗe takardan nan da kanki ki karanta mun abinda aka rubuta, Ammi da yanayinta ya fara sauyawa kaman za tayi kuka ta ce “Papa kayi haquri amma bazan iya karantawa ba”.
Darling ganin har idanuwan Ammi ya fara tara ƙwalla sai ransa ya ɓaci kallon kakansa yayi ya ce “wai duk me amfanin karantawan? Ba dai ya sake ta ba ya zaɓi matar sa akan ta shikenan ku qyale ta muma mu huta munaganinta hankalinmu a kwance”.
Dr Mufaddal murmushi yayi tare da girgiza kai sai ya ce “Maimoon miqawa Mufaddal takardan”, Darling amsa yayi yana kallon kakan nasa ya ce “me zan yi?
Dr Mufaddal na murmushi ya ce “kai ka karanta mana”.
Darling cikin yanayin ko a jikinsa da abinda ke cikin takardan ya qarisa warwarewa, ganin abinda ya fara tozali da shi sai ya waro idanuwansa.
Tunda Dr Mufaddal ya ga haka sai ya murmusa, yayinda Ammi kuma tayi qasa da kanta jira take kawai Darling ya karanta domin tun ranar da Abiy ya miqa mata ta sanya a handbag nata to ko ta kansa bata bi ba balle ta duba domin bata son ganin abinda ke ciki zuciyanta zai karye da yawa.
“Mufaddal ka karanta kai muke sauraro” ya stinci muryan kakan nasa na faɗin haka.

 

MASU SHARHI UWAR BATOORL TAKU TA GODE🤝 DAN SHARHIN KU SHINE QWARIN GUIWANA
MASU GODIYA BANSON THANKS NAKU KUMIN SHARHI KAWAI SHI NAKE BUQATA.

 

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR’S ANNIVERSARY

FAN’S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

💋💋 امى بتولة💋

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 45_46

 

Darling fara karanta abinda ke rubuce a takardan yayi kaman haka “𝗠𝘆 𝗠𝗮𝗶𝗺𝗼𝗼𝗻 𝗶𝗻𝗮 𝘀𝗼𝗻𝗸𝗶 𝗶𝗻𝗮 𝗾𝗮𝘂𝗻𝗮𝗿𝗸𝗶 𝗵𝗮𝗿 𝗮𝗯𝗮𝗱𝗮, 𝗻𝗶 𝗱𝗮 𝗸𝗮𝗶𝗻𝗮 𝗯𝗮𝗻𝘀𝗮𝗻 𝗱𝗮𝗹𝗶𝗹𝗶𝗻 𝘆𝗮𝘄𝗮𝗻 𝘀𝗮𝗺𝘂𝗻 𝗱𝗮𝗺𝘂𝘄𝗮 𝗱𝗮 𝗺𝘂𝗸𝗲 𝘆𝗶 𝗯𝗮 𝗮𝗺𝗺𝗮 𝗸𝗶 𝘆𝗮𝗳𝗲𝗻𝗶, 𝗻𝗮𝗰𝗲 𝗸𝗶 𝘁𝗮𝗳𝗶 𝗯𝗮𝘄𝗮𝗶 𝗯𝗮𝗻𝗮 𝘀𝗼𝗻𝗸𝗶 𝗯𝗮𝗻𝗲 𝗮’𝗮, 𝗻𝗮𝗰𝗲 𝗵𝗮𝗸𝗮𝗻 𝗻𝗲 𝗱𝗮𝗻 𝗸𝗶 𝘀𝗮𝗺𝘂 𝗸𝗶 𝗵𝘂𝘁𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗸𝗲𝗺𝗮 𝗻𝗮𝘀𝗮𝗻 𝗸𝗶𝗻𝗮 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝗱𝗮𝗺𝘂𝘄𝗮𝗻 𝗿𝗮𝘀𝗵𝗶𝗻 𝘆𝗮𝗿𝗮𝗻 𝗻𝗮𝗻 𝗮 𝗸𝘂𝘀𝗮 𝗱𝗮 𝗸𝗲, 𝗸𝗶 𝘆𝗮𝗳𝗲𝗻𝗶 𝗮𝗸𝗮𝗻 𝗮𝗯𝘂𝗯𝘂𝘄𝗮𝗻 𝗱𝗮 𝗻𝗮𝗸𝗲 𝗮𝗶𝗸𝗮𝘁𝗮 𝗺𝗶𝗸𝗶, 𝗻𝗶 𝗱𝗮 𝗸𝗲 𝗺𝘂𝘁𝘂 𝗸𝗮 𝗿𝗮𝗯𝗮 𝗶𝗻𝗮 𝗾𝗮𝘂𝗻𝗮𝗿𝗸𝗶 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗿𝗮𝗻𝗺𝘂 𝗱𝘂𝗸𝗮”
𝗗𝗔𝗚𝗔 𝗡𝗔𝗞𝗜 𝗠𝗔𝗜 𝗦𝗢𝗡𝗞𝗜 𝗠𝗨𝗦𝗧𝗔𝗣𝗔𝗛𝗡 𝗠𝗔𝗜𝗠𝗢𝗢𝗡 (𝗔𝗕𝗨 𝗠𝗨𝗙𝗔𝗗𝗗𝗔𝗟).
𝗦𝗮𝗶 𝘇𝗮𝗻𝗲𝗻 𝗵𝗲𝗮𝗿𝘁 𝗱𝗮 𝗮𝗸𝗮 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 𝗸𝗮𝗹𝗺𝗮𝗻 𝗜 𝗟𝗢𝗩𝗘 𝗬𝗢𝗨, 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗸𝗲 𝗱𝘂𝗸𝗮 𝗿𝘂𝗯𝘂𝘁𝘂𝗻 𝗱𝗮 𝗶𝗻𝗱𝗶𝗮𝗻𝗰 𝗮𝗸𝗮 𝘆𝗶 𝘀𝗮.

Ammi kaman za ta fire, a take ta nemi duka damuwan da ke damunta ta rasa sai wani farinciki take ji mara adadi, amsan takardan tayi ta qara karantawa, hawayen farinciki da kewan Abiy ya zubo mata ta share sannan ta naɗe takardan.
Duk abinda take yi Papa da Darling suna kallonta, shi Darling ji yake kaman ya rusa ihu dan taqaicin Abiy ganin ya gama wulaqanta masa Amminsa sannan yazo yana faɗin wani abin daban, sai dai ba zaka fahimci hakan daga fiskan Darling ba domin wayansa ya jawo ya ci gaba da dannawa, Dr Mufaddal dai murmushi yayi dan ya sani tabbas yarinyansa soyayyan gaskiya take yiwa Mustapha da wuya ace wai rabuwan ne suka yi, sai kuma ya maida kallonsa kan Darling, ganin abinda yake yi sai ya murmusa kawai bai ce uffan ba, ya dubi Ammi ya fara magana “ina fatan kinji kuma kingani saqon mijin naki ba rabuwa da ke yayi ba?
Ammi na murmushi ta ce “eh Papa”.
“Okay! To Yana da kyau duk lokacin da abu zai haɗaki da mutum ki tabbatar kinyiwa mutum uzuri domin kinga yanzu da ace yayi fushi da ke to zaki tabbata cikin stinuwan Mala’iku ne domin ba rabuwa yayi da ke ba kina da auren sa a kanki amma kikaqi sauraransa balle kiji me zai ce miki, kuma kikaqi duba takardan balle kisan hukuncin da kika yanke dai-dai ne ko akasin hakan, kiyi haquri ako da yaushe shi ne abinda zan faɗa miki domin ke kinsan wani irin aure kuka yi kuma kinsan irin soyayyan da Mustapha yake miki, daga qarshe kuma inaso ki tattara ki koma gidanki daga zaran mijin naki ya buqaci haka, sannan ki kiyaye gaba fatan kina saurare na?
Ammi cikin farinciki ta ce “Insha Allah Papa”.
“Yauwá! Allah muku albarka ya raya zuri’a ya albarkace su, sannan maganan yara sai kisan yanda za kiyi, domin ita Muhseena wataqila ma tare zamu koma maganan makarantan su, sai Munawwara da ita Muheebbah duk yanda kuka yanke sai kuyi, don bana goyon bayan a barsu su kaɗai a gida ba kowa tunda shi Mufaddal ba aure yayi ba”.
Ammi dai komai Papa yace amsawa take yi dan farincinkinta ba misali, sosai tayi kewan Abiy dan a yanzu ba abinda take buqata kaman ta kallesa.
Dr Mufaddal idonsa ya mayar kan Darling da ke danna waya ya ce “my man ka rage zuciyanka akan mahaifinka domin shi ne wanda yayi sanadin zuwanka duniya ba ka da madadinsa, in kuma kanason fushin Allah da rashin albarkan iyaye ta tabbata a kanka sai ka ci-gaba”, Ammi ce ta tari bakin Papa ta hanyar cewa “indai dan ni kake wannan cin ran to ka daina Darling komai ya wuce, komi na duniya mai wucewa ne, sannan tare da kai zamu koma Nigeria wannan karon kuje Maiduguri wajan dangi”.
Darling dai a fiska ba zaka gane me yake ciki ba amma a zuciyansa ji yake kaman ya tashi ya tafi kar ya kuma dawowa, ga abun haushin wai har Borno kuma za suje ba iya Gombe ba, Lumshe ido kawai yayi ya ce “Allah kaimu”.
Nan Dr Mufaddal ya qara yi ma Ammi faɗa sosai sannan ya ce “gobe in Allah ya yarda zan koma”.
Da “Allah ya kaimu” Ammi ta amsa, nan duk suka miqe Ammi tayi sama, Darling ma ya wuce sashinsa, sannan Dr Mufaddal ya wuce ɗakinsa dan ya sanya haqarqarinsa ya huta.
Amma tararwa tayi duk bacci ya ɗauki yaran sun bar TV a kunne, sai da ta kashe komai sannan ta tashesu suka tafi ɗakunan su, sweetie kuma ta ɗauketa ta kaita nata ɗakin itama ta mata addu’a sannan ta fito ta ja mata qofa ta nufi nata ɗakin cikin nishaɗi yau za tayi kwanan farinciki.

Darling yan haurawa sashinsa ya jawo system nasa ya ci-gaba da aikinsa dan bayajin bacci ma, Burinsa ya kammala ayyukan kamun ace za su tafi Nigeria, sai dai gefe ɗaya na zuciyansa tunanin Abiy yake yi na irin yanda ya mayar da Ammi dan yaga tana sonsa.

Washegari da sassafe Dr Mufaddal ya shirya dan ya dage Darling ne zai kai sa airport ba driver ba, ba yanda ya iya yana gama shirin zuwa office suka kama hanyan airport Dr Mufaddal nakan masa faɗa cikin sigan rarrashi har suka isa, ya shiga jirgi zuwa India shi kuma Darling ya juyo driver yayi office da shi.

Abiy yana tashuwa da sassafe ya fara shirye-shiryen zuwa wajan masoyiyar sa, Aunty Amarya dai tana ganin ikon Allah sai dai sanin halin sa bai cika son yawan tambaya ba sai tayi shiru, sai da zai tafi ya ce mata “sweetheart na tafi Canada zan kai week sai na dawo”, Aunty Amarya da kallon taqaici da haushi take binsa, cike da kishi ta ce “me za kaje yi a Canada? Ina ka sake ta to me zaka je yi? In yaran ka kakeson kallo ba sai ka sanya shi ya kawo su ba tunda kai ka haifesa ba shi ya haifeka ba” surutu take yi ido rufe wanda kanaji kasan kishi ki azalzalanta.
Abiy kallonta kawai yayi bai ce komai ba, dan yana rasa dalili shi bayason ɗagawa mace murya amma duk da haka Maimuna da yake so yakan iya ɗaga mata murya, ba tare da ya damu da yanayin magananta ba ya ce “wanda ya faɗa miki na saki Maimoon to ki koma ki qara tambayansa, sai na dawo” yana gama magana ya fice.
Aunty Amarya bin bayan Abiy tayi tana surfa masifa, qarshe ganin driver ya fita da shi sai itama ta koma ta ɗau waya ta qira Hajj, “assalamualaikum Hajja anwuni lafiya?
“Lafiya Alhamdulillahi Rabi’atu ya gidan? Ya mijinku?
“Ba lafiya ba Hajja, gashinan ya kama hanya wai zai tafi Canada kuma bayan ta sake ta, nace in yaran yakeson gani ai sai ya ce a kawo su”.
“Rabi’atu wa aka saka? Ba dai kicemun Mustapha ya saki Maimunatu ba, INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI’UN! Wai yaran nan ina kukeson duniya ta kai ku ne? Mutum ya auri mace da wahala amma cikin sauqi ya rabu da ita, to dan ubansa zai dawo da ita dan wannan cin amana ba da Fatuma ba”.
Auntu Amarya jin ba abinda take so Hajja ke faɗi ba sai ta kaste waya tana faɗin “mstwwww! Duk bakinsu ɗaya wallahi Maiduguri zan je, ba ta isa ta dawo ba” tana gama magana ta shige ɗaki ta hau shirya kaya a akwati.

Abiy driver ya kaisa har airport jirgi ya ɗaga da su sai Canada republic, taxi ya hau har qofan gidan yaron nasa sannan ya sallami taxi ɗin, da sallama ya shiga palourn inda ya tarar shiru ba kowa kaman basa gidan, sama ya haura nan ya samu yaran suna aikin karatun Alkur’ani wanda ganin Abiy ya sanya su miqewa da gudu kowa ya je yayi hugging nasa har Afreen suna masa sannu da zuwa, amsawa yayi yana tambayan su ina Amminsu? Hanyan ɗakinta suka nuna mishi alaman tana ciki, cikin zumuɗi da son ganin matar tasa ya lallaɓi sweetie da daraba ya zille ya nufi palourn da zai sada shi da ɗakin Ammi.
Fitowanta wanka kenan ta gama shafe jikinta da turaruka masu daɗin qamshi, kayan da suke matuqar amsanta ta fitar ta sanya, Pakistan dress tana staye gaban madubi taji anbuɗe qofan ɗakin nata, duk ɗaukanta yaran ne sai bata juya ba ta cigaba da rolling nata tana faɗin “wai sweetie ban hanaki shiga ɗaki ba sallama ba…” Maganan bakinta ne ya kaste jin ta jikin mutum wanda ta tabbatar ba kowa bane face Abiy, shi kuwa cikin farin ciki ya rungumeta ta baya yanajin kaman yau ya fara raɓarta, Ammi farinciki ne da wani irin nishaɗi ya lulluɓeta amma sai ta waske ta ja aji taqi yin mosti balle ta ce qala, sai qoqarin tashuwa da take yi amma Abiy bai bata wannan daman ba.
Duk yanda ta so mostawa Abiy ya hanata wannan qoqarin ita kuma ga shi tabbas tayi kewansa dan bata qi su qare rayuwansu a haka ba, cikin danne abinda take ji ta ce “sake ni kar yara su shigo su ganmu haka”.
Abiy murmushi yayi dan yasan aji ake ja masa, kuma yasan me zai yi a wuce wajan amma sai ya nemi jan maganan dan so yake yau ta taɓa rigiman nata, muryanta ya kwaikwaya ya ce “babu ɗan albarkan yaron da zai shigo duk sun san Amminsu na kewan Abiynsu, sannan kuma nima ba sake ki zan yi ba dan da shiri na nazo wannan karon ya kamata a samawa Muheebbah qani tunda ta haura shekara biyar ɗin, kuma dama starin na shekara biyar-biyar ake yi”.
Ammi qara ɓata rai tayi jin abinda ya ce “hmmn! Wato ma planning nake yi kenan? Good inma shi ne ai magana ta wuce yanzu ba komai tsakanina da kai sake ni”.
“Aiko ni da ke muke da abu babba ma stakaninmu, yanzu dai fatan an buɗe takardan an ga me na rubuta kuma an yafe mini an karɓi tubana?
“Uhmñ! Na buɗe kuma naga saki uku, so na jima da yafe maka jeka wajan matar ka inma yaranka kazo ɗauka ka ɗaukesu Allah tsare hanya”.
Murmushi Abiy yayi jin rigiman nata da gaske take yi, sai kawai ya haɗe bakinsu cike da son nuna mata irin kewanta da yayi da kuma soyayyanta da neman afuwanta haka yake sarrafa ta, wanda a take Ammi ta amshi tuban nasa ta kuma yaba soyayyan sannan itama ta miqa nata qoqon neman yafiyan ta hanya maida masa martani mai nuni da tayi matuqar kewan sa.
Cike da soyayya da qauna suka sarrafa juna wanda na tabbata ko wasu matasan ma’auratan ba lallai su shumfiɗa irin wannan soyayya ba (shi yasa ake son in za kayi aure kayi dan Allah, domin in kayi dan wani abu daga lokacin da abun ya gushe to fa ba zaman lafiya balle soyayya sai a ta ɗaukan alhaqin juna).
Bayan komai ya lafa sun yi wanka tare, Abiy na zaune kan Ammi a qafansa nan ya dinga qara bata haquri da lallashi, wanda Ammi ba ɓata lokaci ta ce “na yafe maka, komai ya wuce ina fatan hakan kar ya sake faruwa, kuma za ka yafemun Nima?
“Ai na jima da yafe miki Maimoon, Allah miki albarka ya barmu tare, sannan ina so ki sani har abada kibar tunanin rabuwa tsakaninmu, domin ban taɓa son wata mace kaman ke ba kuma bana tunanin akwai wacce zan so nan gaba kaman ke, abubuwan da suke faruwa tsakaninmu kuma in Allah ya yarda zan ɗau mataki kinji..”
Kaste Abiy tayi ta hanyar cewa “komai ya wuce ka daina dawo da shi, sannan in dai ni ce Maimoon za ka ɗau mataki dan ni to na yafe duniya da lahira kar kayi wani abun dan in kayi ma ba zan yafe ba”.
Abiy na murmushi cike da son matar tasa ya ce “shikkenan angama ranki ya daɗe nustuwar Mustapha”.
Ammi ma murmusawan tayi ta ce “to ranka ya daɗe yallaɓoi ina neman wata alfarma”.
“Maimoon faɗi ko ma menene Insha Allah zan yi miki da yardan Allah in har bai fi qarfina ba”.
“Yallaɓoi dan Allah maganan Mufaddal, ka daina biye masa kaga dai yaro ne kuma komai zai wuce in ya girma, dan Allah kai mahaifinsa ne ka yafe masa, sannan maganan komawa Nigeria ina neman alfarman zama a Canada tare da yaran nan tunda ya sanya su a makaranta inyaso sai mu dinga zuwa Nigerian in sun samu hutu”.
Dogon ajiyan zuciya Abiy ya sauqe domin Allah ya gani baya jin akwai abinda yake qauna a duniya sama da yaran nasa amma kuma dan qara samun nistuwansu da faranta musu zai yarje da hakan, cikin murmushi mai nuni da gamsuwa da batun ta ya ce “kaman yanda na ce koma menene zan amince miki kuma zan miki, to na amince inyaso zan dinga zuwa akai-akai fatan zaki kula mana da su? Kuma ko ba’a yi hutu ba wani lokacin kema ki dinga leqowa tunda kinsan wani zubin muna busy sosai kuma ba zan jure har fin sati ba tare da na ganki ba”.
Cikin jin daɗi Ammi ta amince tare da qara rungume mijin nata, nan suka ci-gaba da farantawa junansu.

Aunty Amarya shiryawa tayi ta kama hanyan Maiduguri, inda tana isa ta sami mahaifiyarta ta sanar mata, amma da yake mahaifiyar nata ba ruwanta sai ta tsawatar mata akan ta koma gidan mijinta, Aunty Amarya dai hakan bai gamsar da ita ba, sai ta samu fanne, itama fannen cewa ta yi “amma tabbas Rabi’atu baki da hankali, ki godewa Allah Mustapha ya aureki shi ne har kike kawo wani maganan? Wannan auren su Mustaphan fa kaman an bisa da baki wallahi kana mastawa a lamarin ka baqonci lahira, yanzu ina baba-alhaji? Ina Alhaji surkinki? Ina Asma’u? Ko yarinyan da Asma’u ta haifa bata zauna ba dan haka ya isa kisan wannan auren nasu Allah ne ya haɗa, amma kuma tunda kince sakinta yayi ba mastala kya iya samun Alhaji babba amma dai ni fanne naga ayar Allah ba ruwana da lamarin Mustapha da ƴar qasar can”.
Aunty Amarya kaman za ta haɗiye zuciya haka ta yi kwana biyu a daddafe ta dawo bayan ta gama ɗaura aniya da sabon shirin shiryawa Ammi manakisa wanda sai ya rabasu na gasken-gaske.
Ɓangaren Hajja kuwa Daddy (Nura) ya qira ta dinga masa faɗa akan ya tabbatar Mustapha ya dawo da maimuna inba haka ba zata saɓa musu, shi dai Daddy haquri ya dinga bawa Hajja sannan suka yi sallama ya qira layukan Abiy baya tafiya sai ya bari akan zai qira daga baya.

Yau aiki ya sha ba kaɗan ba dan da qyar ya samu kayakinsa da aka riqe su suka fito, companyn Jigawa kuma ya seta komai dan shi ne dama dalilin aikin da ya hanasa bacci da wuri jiya, sai dai duk da haka akwai buqatan ya je dan duba sauran abubuwan ga kuma maganan meeting da ake jiran approval nasa, sai can yamma kamun ya fito ya dawo gida.
Da sallama ya shigo palourn wanda tun daga bakin qofa ya gama kallon farincikin da ke kwance a fiskan Ammi kuma yasan tabbas Abiy ne ya zo, ba tare da ya ce qala ba ya qarisa shigowa yana faɗin “sannu da gida Ammi” yana gama faɗa ya wuce haurawa sama.
Ammi dai amsawa tayi tana murmushi ta masa sannu.
Abiy ne ya sauqo ɗauke da sweetie tana ta aikin shagwaɓa, domin su ma yaran karan kansu sunsan yau Ammi na fatinciki kuma suma zuwan Abiy ya sanya su farinciki domin kewan mahaifin nasu suke.

Wasta ruwa yayi sannan ya jawo wayansa yana laluɓo Numbern Jay yau kusan kwana biyu bai qira sa ba, “hello dude yau ka tuna da ni ne? Cewar Jay da yayi picking call ɗin.
“Mtsw! Za ka fara surutun naka ko?
“Hhh ba dole nayi surutu ba Allah ya stagomin baki, ai kaikam sai tsagun bakinka ya manne tunda baka buɗewa kayi magana da kyau, salatin ma a zuciya ake yi, yanzu dai ya su Ammi? Ya kuma labarin Abiy? Ina su sweetie ina Afreen?
DMD dafe kai yayi yana faɗin “ko me kayi ba laifinka ba nine na qiraka, amma kaji wallahi ko ɗaya ba zan amsa ba, ka gaida gida” kitt ya kashe wayan yana jan guntun tsaki.
Jay na kan qiransa amma ko kallon wayan bai yi ba, ya shige toilet.
Ɓangaren Jay kuwa dariya ya dinga yi yana faɗin “Allah ka shiryi dude ka gwadamun ranan da zai sauya, ai wannan mace me zama da kai ta shiga uku”.

Sai da Ammi ta tura aka qirasa kamun ya fito, sama-sama ya gaishe da Abiy sannan ya zauna Ammi tayi saving nasa ta cika cikinsa.
Washegari DMD bai je office ba, Managern sa ya qira ya tura masa abubuwan da ya kamata, dan so yake ya huta aikin da yayi kwana biyu ko ishashshen bacci ba ya yi, inda ɓangaren Abiy da Ammi kuwa soyayyan su suke yi kaman sabbin aure, a ranan kuma Abiy ya sa duka suka shirya har Darling suka tafi shopping, kaya niqi-niqi kowa ya jida, aka wa sweedy sayayyan tafiya school Afreen ma aka mata na dawowa Nigeria, Abiy ma ya jida kayaki, shi dai DMD ba abinda ya ɗauka illa iyaka wani headband na mata da ya gani ya masa kyau, Abiy ne ya biya kuɗin komai suka kuma wucewa suka yi sayayyan kayan ƙwamulashe, yawo suka yi sosai sannan suka dawo gida, kowa ya jida nasa yayi ɗakinsa da shi, Darling a Waldrop ya jefa headband ɗin ba tare da yasan ma me zai yi da shi ba.
Washegari da sassafe sweedy ta kama hanyan India bayan Abiy da Ammi sun mata faɗa ta kula sosai, Afreen kuma sai da aka kwashe sati guda kamun suka juyo tare da Abiy da ke cike da kewan matar sa.

Abiy na dawowa Aunty Amarya cikin kirsa ta lallaɓasa ta basa haquri akan ba tayi dai-dai ba kuma ba zata qara ba, abinka da mata da miji nan suka shirya suna soyewansu, da farko sai yayi kwana biyar ko sati a Nigeria sai ya je Canada yayi kwana biyar ya dawo, ana rayuwa ana tafiya haka har dai Aunty Amarya ta fara kasa hali, sai yayi sati bai je Canada ba kuma in yaje baya wuce kwana biyu zai dawo, qarshenta kwana ɗaya yake yi ya dawo, daga baya kuma zai fi sati biyu bai je ba kuma a ranan da yaje a ranan zai dawo, ita dai Ammi duk haka bai dameta ba, ga yaranta na makaranta tana kallonsu suna kallonta hankalinta yafi kwanciya, a cikin wannan halin DMD yayi approval na meeting nasa a Zamfara inda yana shigowa ya gabatar da komai ya juya ya koma ko sauran companies ɗin bai leqa ba balle Gombe, Abiy da sai da ya raba hali domin faɗa ya dinga yiwa Ammi kaman ita ce ta yi hakan, qarshe sai da ya kwashe wata bai je Canada ba, Ammi kuwa duk tabi ta damu a wannan lokacin ne kuma yara suka samu Hutu har da sweedy da ta kwashe shekara a makaranta ta dawo dan haka sai Ammi ta sako su gaba har DMD duka diro Nigeria.
Aunty Amarya a fiska kuma a gaban Abiy nunawa take duk duniya ba wanda take so irin yaransa kuma bata kishi da Ammi, amma a bayan fage rashin kunya takewa Ammi ta ke kuma zuba mata munafurci, sai da suka kwashe sati biyu da zuwa sannan suka je Ashaka, Hajja farincikin rasa inda zata sanya kanta ta yi ganin jikokin nata, nan ta dinga zubawa Abiy faɗa kaman za ta ari-baki ” Maimoon kiyi haquri naji abinda ya faru, wato tunda shi Mustapha yanzu ya butulu ɗa namiji hankaka gabansa fari bayansa baqi shi ne har da saki nan Rabi’atu ta qiran tana faɗamun”.
Ammi da tayi qasa da kai cewa tayi “Hajja bakomai ba saki bane nice naje Canada”.
“A’a ‘yar nan karki wani rufa masa asiri ai na sani, shi Mustapha dan staɓar ya zama ciki ba Godiyan Allah balle tuna alheri ya mance yanda ya sha gwagwarmaya ya aureki har zai iya daukan hannu ya baki takarda tunda shi sha-sha-sha ne, to ya taimaki kansa dan da mun haɗu tabbas sai na saɓa masa”.
“Bakomai Hajja ya wuce, am nace ba Hajja dama munason zuwa Maiduguri da yaran nan”.
Washe baki Hajja tayi ta ce ” ‘yar albarka Allah miki albarka ai ya kamata kam zuwa Maiduguri dan za suce tunda Allah ya ɗauki Alhaji shikkenan kuma ni da ku bama zuwa, yanzu dai wannan tafiya duka za’a yi sa kowa da kowa”.
“To Allah ya kai mu”.
Ammi washegari tabar Ashaka su, DMD kuwa sai da yayi kwana biyu kamun ya dawo yabar su sweedy a can, dan sweetie indai gidan Hajja ne to ko babu Ammi za ta zauna.
DMD ya je ya dubo Companyn Jigawa, sannan ya wuce Abuja nan ma ya duba sabon shopping-mall da zai buɗe, komai lafiya sannan ya juyo. a ranar kuma duk suka tattaro da iyalan Daddy da na Abiy suka nufi Maiduguri.
Sosai family suka ji daɗin zuwan su Hajja, nan aka sauqesu a sashi na daban, dan duk da kasancewan basa zuwa amma duk wani dangi yana da masauqi a family house ɗin domin a yanzu yawansu ma ya sa an raba family house ya zama biyu, ɗaya stohon na iyaye da kakanni ɗaya sabon kuma na jikoki da yara, sannan duka gidajen manya ne iya ganin ka wane anguwa guda.
Zuwan su Hajja ya sanya an haɗa qwarya-qwaryar family meeting in da aka buɗe taro da addu’a sannan Alhaji babba da zuwa yanzu shima ya stufa sosai ya fara koyo bayani, sai da yayi ya gama sannan aka buqaci duk wani mai abun faɗa ya faɗa.
‘yar uwan Hajja da suka haɗa uba ne ta fara koro bayani akan abinda suka kista da Aunty Amarya na game da auran yaran kan cewa su Jay da DMD su zaɓi mata su sweedy ma anmusu miji.
Tun shigowan sa babban palourn ya samu waje ya zauna wayansa ya ciro yana laste-lastensa bai ko kalli kowa ba balle ya tofa musu qala har sai da ya ji abinda dattijuwan da Hajja za ta girmeta da kaɗan ta faɗa, ɗagowa yayi ya wasta ma matar da baisan wacece ma ita a wajansa ba wani malalacin kallo, har zai buɗe baki sai kuma me ya tuna oho ya maida hankalinsa kan wayansa, Daddy ne yayi magana “in Allah ya yarda Duk zasu zaɓi mata in yaso ba jima sai ayi auren tunda duk yanzu suna da aikin kansu”.
Jay idanuwansa ya baza a ɗakin ganin yaran mata basa palourn sai ya taɓe baki yana faɗi a ransa “in yaranku suna da kyau kuma sun nuna to ko huɗu ne ni Jabeer zan aura amma in kwailaye ne to tarihi zai maimaita kansa, mata zan nemo zuqeqiya” vibrating na wayansa ne ya kaste masa zancen-zuci da yake yi, ganin mai qiran sai ya miqe ya fice a palourn yana ɗaukan qiran.
Shi ma miqewa yayi yana maida wayansa aljihu tare da sanya ɗaya hannun a aljihun wandon jeans na jiginsa da yayi matuqar amsar sa, gaskiya DMD kyakkyawan qarshe ne dan yanda qananan kayan suka zauna a jikinsa kai kace ba ɗan Nigeria ba ne, ficewa yayi a palourn duk sai suka bi su da kallo Aunty Amarya da dattijuwan da tayi magana taɓe baki suka yi, Ammi kuma qasa tayi da kanta tana addu’an shiriya ga yaran nasu da maganan da suke ja musu, Abiy dai ko qala bai ce ba dan shi komai aka yi dai-dai ne baya qaunan ya kuma yin wani laifin.
Hajja dai tayi supporting na shawaran, Aunty Amarya ranta fari tass har aka yi addu’a aka waste, wasu na ta zancen DMD ya rena mutane ai gado yayi wajan Mustapha.

Jay yana gama wayan yabi bayan DMD da ya nufi ficewa a sashin babban palourn da ake meeting yana faɗin “dude Angon ƴar Maiduguri jirani mu fara shirye-shirye”.
Ko nuna alaman ya ji abinda yake faɗa bai yi ba balle batun ya jirasa, sai da Jay ya haɗa da gudu kamun ya iso sa yana faɗin “Allah nuna min randa zanga ƴar Maiduguri ta sanya ka wanke-wanke wallahi sai na sanya ta ramamin wulaqancin nan da kake mun”.
Kallon banza ya bi Jay da shi yana faɗin “ba’a haifi iyayenta ba balle ita, ni banda lokacin mace balle aure amma inaga tabbas zan yi dan waɗannan mutanen su san basu isa su sanya ni auran yaransu ba”.
Jay murmushi yayi ya ce “ashe kai ma ka gama yanke shawara? Ai ina gaya maka dude nikam in har suna da qosasssun yara kyawawa to ko huɗu suka ce zan aura amma aradu indai qwailaye ne to sai dai ayi wanda za’a yi inyaso a yafe ni daga family dama can bai damen ba, bare zan nemo na aura zuqeqiya nunanniya dan ni banson harka da qananun mata, dama muna can Gombe me ya haɗa mu da Maiduguri, Ni fa inaganin ta Abiy zan yi India zan koma na zaɓo mata nustaststiya mai kyau wacce ta iya soyayya kaman Ammi, matan Nigerian nan in ba sa’a kayi ba to duk shiru ne”.
Taɓe baki yayi yace “ɗauko mota ka kaini airport sai ka dawo musu da motan”.
Jay dubansa yayi ya ce “badai yau zaka koma ba dude?
“In na zauna ban koma ba aikin ne zan maka?
“A’a mai da wuqan jirani na ɗauko motan, amma gaskiya ba dan ina buqatan qarewa ƴammatayen kallo ba da na biyo ka mun tafi”.
“Mstww! Ai kai maganan mata shi zai kashe ka, za ka ɗauko ne ko na tafi da kaina kuje ku samu motar a airport?
Jay yana dariya ya juya dan yasan kaɗan daga halin DMD sai ya tafi ta motan ya barota a can yayi tafiyansa.
Motan ya ɗauko DMD ya shiga suka nufi airport, har suka isa Jay shi kaɗai ke surutun sa DMD hankalinsa duka na kan waya kai kace dan kallon waya aka halicci idonsa.
Sai da jirginsu ya tashi sannan Jay ya juyo ya dawo gidan, Ammi na ganinsa ta tambayesa Darling sai ya faɗa mata ya koma Gombe, addu’an a sauqa Lafiya da na Allah shirya ta bisa da shi, Jay kuwa baza idanuwa ya dinga yi yana qarewa ƴammatayen gidan kallo, kyau kam iya kyau Allah ya azurta wannan family da shi don kana ganin ko waccen budurwa za ka tabbatar tabbas Kanuriya ce gaba da baya, Jay yayi kallo iya kallo qarshe dai ya gama rawan idonsa ya rasa ta zaɓa.

Ammi da yaranta suna ɗakinsu a zaune, Jay ya shigo yana faɗin “Ammi gaskiya ni na gama dubawa sama da qasa banga wace ta mun ba kawai na yanke shawara zan jira sweetie ta girma”, ba iya Ammi ba har sweetie da bata cika shekara goma ba sai da tayi dariya duk da rashin wayonta.
Ammi ta ce “son Allah ya shiryaku, ai gwanda ku dage ku nema kamun a nema muku, ka bari kayi ta huɗu da sweetie lokacin ta girma”, tura baki sweetie tayi ta ce “ni Ammi banson ta huɗu ta ɗaya nakeso”.
Duk dariya suka sanya, Jay na faɗin “sweedy ku dage ku zaɓi ku darje duk da nasan ba zaku samu kyawawa irinmu ba”.
Sweedy na murmushi cikin rashin son yawan magana ta ce “big bro kai ma kasan mijina sai ya fika kyau, amma yanzu dai ba ta wannan ake yi ba”.
Hira suka ci-gaba da yi suna dariya, cikin dabara Ammi ke tausarsu tana nusar da su fa’idan bin magana da biyayya ga iyaye, amma sweedy dai ta tuɓure ba wanda ya mata dan abun kaman wanda suke jiran qiris samarin gidan kowa sai faman isar da saqon soyayyansa yake gare su barinma dai Sweedy, domin a duniya sweedy Allah ya hore mata kyau banbancin ta da DMD kaɗan ne dan da ta kaisa shekaru ko ta biyo sa kusa-kusa za’a iya qiransu twin’s.

 

MASU SHARHI UWAR BATOORL TAKU TA GODE🤝 DAN SHARHIN KU SHINE QWARIN GUIWANA
MASU GODIYA BANSON THANKS NAKU KUMIN SHARHI KAWAI SHI NAKE BUQATA.

 

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

 

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR’S ANNIVERSARY

FAN’S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

💋💋 امى بتولة💋

Ayi haƙuri da rashin update jiya sakamakon wayar tawa sai a hankali har yanzu ba ta farfaɗo sosai ba.

 

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 47_48

DMD bai nufi Gombe ba direct Abuja ya wuce dan ankammala komai na shopping-mall ɗin, wata arniyar hotel ya kama ta manyan masu kuɗi wanda daga masu mulki da manyan ‘yan siyasa sai manyan masu kuɗi ke zuwa hotel ɗin, kwanansa ɗaya washegari ya fito daga mall ɗin wanda ake shirye-shiryen buɗewa gobe ya dawo hotel ɗin, bayan yayi parking ya fito a motan ya kulle, tafiya yake hankalinsa na kan wayansa da aka turo masa saqo daga Canada yana dubawa, ba tare da ya kula ba ya ji ya yasar da key na motan sa, har ya shiga ɗakin da ya kama bai kula da ya yasar da abu ba, ruwa ya wasta sannan ya yi ordern coffee aka kawo masa.
Yana kurɓan coffee nasa yana ayyukan sa a waya sai ya ji knocking.

Wata haɗaɗɗiyar mota ne ta shigo hotel ɗin da mugun gudu, ana gama parking aka buɗe duka qofofin kusan a tare, wasu ƴammataye ne suka fito guda uku sai gefen da yake na driver ne kawai a buɗe ba’a fito ba, ɗayar da ta fito daga gefen zaman driver ne ta ce “reeysah me kike kallo ne ba zaki fito mu tafi ba?
Wacce aka qira da reeysah ce ta jefo qafafuwanta waje, wasu arnun hill’s ne a qafanta wanda daga takalmin qafan zaka tabbatar mai qafan ta haɗu, a hankali ta qarisa fitowa, sanye take da riga da wando iri ɗaya wanda ake qira da Up&down wanda a qalla kuɗin kayan zai kai 300k, inda take kallo duk ƴammatan suka bi da kallo, ganin guy ɗin sai duk suka shagala da kallonsa suma, ɗayar ce ta ce “reeysah amma guy ɗin nan ya haɗu fa”.
“Hmmn! Zee ba kaɗan ba, ai ni naga mijin aure dama excellency ya fara magana miji kamun ya bar villah” tana gama magana ta taka a hankali ta ɗau abinda ya faɗi a hannun guy ɗin da ta gani sannan ta bi bayansa, sai da ta ga ɗakin da ya shiga sannan ta juyo wajan freind’s nata tana faɗin “let’s go guy’s”.
Ɗakin da suka kama suka shiga sai da suka huta sannan ta ɗau key ɗin ta fito bayan tawa qawayen nata sai ta dawo, tana isa qofan tayi knocking.

Tashuwa yayi ya buɗe dan duk a tunaninsa ko waiter ne yazo amsan cup na coffee ɗin, kallo ɗaya ya mata ya ce “lafiya?
Cike da qwarqwasa ta ce “zan iya shigowa?
Ba tare da DMD ya ce komai ba ya juya ya shige ciki sai ta biyo bayansa, zama tayi a ɗaya daga kujerun palourn tana gaishesa cikin harshen turanci, har ta yi ta gama bai ce mata ko qala ba kuma bai kalleta ba, gajiya tayi ta ciro car key nasa ta ce “am dama key na motanka ka yasar shine nace bara na kawo maka”.
Hankalinsa da idanuwansa na kan waya ya ce “okay thanks! You can kept it”.
Yana gama faɗan haka ya juya ya shige bedroom.
Reeysah kaman za tayi kuka ta ajiye ta tashi ta fice, amma tana ayyana wa a ranta itafa taga mijin aure, ko da ta koma cewa qawayenta tayi ya amshi soyayyanta.
Fareesah(reeysah) kyakkyawan budurwa wacce a qallah za ta kau shekara 26 da haihuwa, yarinya ta uku ga present president na Nigeria, wacce tayi karatu a America bata jima da dawowa ba aka fara mata maganan aure, da farko ta nuna taurin kai tana yawon ajenan-ajenan da qawayenta sakamakon yarinyace da bata ji an sangartata, yayyunta biyu duka sun yi aure sai qannenta maza biyu da suke karatu a outside, yaran manya ministoci da ‘yan kasuwa na sonta amma ba maganan aure a gabanta, amma ganin DMD sai taji za tayi auren.
Yana jin qaran fitan ta ya ja guntun tsaki, ya rage hasken wutan ɗakin ya kwanta.
Washegari da sassafe ya shirya ya fice gaba-ɗaya a hotel ɗin, reeysah kuwa sai da rana ta fito gastal-gastal suka tashi da qawayenta, sunje ɗakin DMD suka tarar baya nan, kaman za tayi kuka haka suka tafi tana faɗin sai ta nemo shi dan ita ba ta da miji a duniya bayan shi, ko da kuɗi ko da mulki sai ta aure.
(😂 Jama’a kuwa fareesah fatan nasara).

Bayan sun qara kwana biyu suka tattara suka koma Gombe, bayan sun ajiye Hajja a Ashaka.
Maganan aure da aka yi kuma daga Daddy har Abiy ba wanda ya ce wa yaran komai, dan Hajja jira take su haɗu duka ta ja musu kunne kar su kuma jawo mata wani abun.
Ammi zamanta take hankali kwance bata shiga tsabgan Aunty Amarya dan zuwa yanzu Ammi ta fahimce ta amma tabar hakan a mazaunin kishi ba wai munafurci ko kissa ba.

Sai da aka kammala hidiman komai aka buɗe shopping-mall sannan ya kamo hanyan dawowa Gombe, cike da gajiya ya shigo gidan, ba tare da yayi part na Ammi ba ya nufi ɓangaren da yake nasa, yana shiga qamshi ya doki hancinsa sashin staf-tsaf ko ina a gyare sai qamshi, ganin haka sai ya murmusa yana faɗin “Allah barmana ke Ammi” ya shige ɗakin nan muna a a gyare har toilet, ruwa ya wasta ya ɗauro alwala yayi Sallah sannan ya bi lafiyea gado ya kwanta.

Fareesah tayi iya nemanta amma ba alama ko guda da zata samu daman samun ko da phone number na DMD balle sunansa, masu hotel ba abinda suka sani akansa sannan bata da labarin shopping-mall da ya buɗe, duk da haka dai kan nemansa take yi taqi haqura.

Hutu na qarewa suka tattara suka koma Canada, inda suke rayuwa cikin kwanciyan hankali sai Ammi kawai da aka barta da sintiri yau tana Nigeria gobe tana Canada, domin Abiy zuwa yanzu sai dai ya dinga leqosu lokaci-lokaci yakan shafe wata guda bai je ba, Ammi hakan dai bai dameta ba domin ita tana zuwa tayi sati guda ta koma in tayi sati biyu a Canada ta qara zuwa tayi sati guda ta koma.
Jay yana aiki a FMC Gombe sai Afreen da ke final-year semester a GSU tana karantan computer science, Afrah kuwa tana gaban Hajja tana secondary school.

Fitowa DMD yayi da shirin tafiya office amma sai ganin Ammi yayi ta fito da nata shirin ita ma, gaisheta yayi yana faɗin “Ammi sai ina?
Tana murmushi ta ce “sai gidan mijina, tunda ku kunqi gidan ubanku”.
Taɓe baki yayi yana gyara zaman suit nasa ya ce “adawo lafiya a gaishesu, and please Ammi inkin samu lokaci kamun ki dawo ki dubamun Companyn Jigawa”.
“Darling yai shekara nawa rabonka da Nigeria? In banyi qarya ba kafi 2 year’s ba kaje ba, tun last da muka je tare muka je Maiduguri kaqi ka koma, ina ji dai anfita harkanka akan batun auren tunda dama shi ne damuwarka, ka fita idona inba haka ba zan mugun saɓa maka, maza-maza nan da Friday anabawa su sweerie hutu ka tabbatar kun biyo ni dan wannan karon zamu kwana biyu acan tunda hutun su sweedy da yawa”.
“Ammi karki manta da zuwa jigawan please” iya abinda ya faɗa kenan yayi hanyan fita waje.
Girgiza kai kawai Ammi tayi tawa yaran nata bankwana sai sun zo, sweetie har da kukanta za ta bi Ammi ai saura two days a bayar da hutu inyaso sweerie ta karɓo musu hutun, da kuka ta bi Ammi har compound na gidan, kallon da DMD ya mata shi ya sanyata haɗiye kukan, Ammi ta shiga motan da ya shiga suka zauna tare a baya driver yaja su sweedy suna ɗaga mata hannu har motan ya ɓace sannan suka juya suka koma ciki.

“Darling sam-sam bana son irin wannan halin da kakeyi bai kamata ba”.
Kaman zai yi kuka ya ce “Ammi nifa bansan dalili ba gaskiya banson Nigeria, amma kiyi haquri zan je wani hutun, wannan karon in aka basu hutu dai zasu taho ko Abiy ya zo ya tafi da su”.
“Hmm! Ni Maimoon me zan ce in ba Allah ya shiryamin kai ba Darling, Allah kai mu in aka basu hutun inma Abiynku bai zo ba zan dawo na ɗauke su mu koma amma ba zaka turamun yara su kaɗai a jirgi ba inason yarana”.
Murmushin da ya qara masa kyau yayi ya ce “Allah bar mana ke Amminmu” dai-dai sun iso airport nan Ammi ta sauqa ta samu jirgin ya kusa tashuwa fasinjoji na shiga, ta gama bin step’s na jirgin har ta kusa shigewa ta juyo tana masa murmushi ta ce “ka kulamun da yarana Darling”.
Hannu ya ɗaga mata yana faɗin “Ammi Karki manta da Jigawa”.
Murmushi kawai tayi ta qarisa shigewa dan tasan dalilinsa na jaddada mata bai wuce baya son zuwa Nigerian ba, wajan zamanta ta wuce tana mai karanto addu’an shiriya ga yaran nata a zuciyarta.

Ganin jirgin nasu ya tashi sai ya koma cikin motan, driver ya ja suka wuce katafaren Companyn sa.

Ammi tunda ta zauna a cikin jirgin zuciyarta ke stinkewa, amma bata jin za ta iya haqura ta koma domin tabbas tayi kewan mijin nata, addu’oe ta cigaba da karantowa har jirgin nasu ya ɗaga zuwa Nigeria (ƙasar mu ta gado😂).
A Jigawa jirgin nasu yayi landing, tana sauqa ta wuce Companyn yaron nata dake garin, qiransa tayi ta sheda masa ta isa a Jigawa ta staya za ta duba kamun ta wuce, DMD kaman zai yi kuka haka ya dinga yiwa Ammi magana meyasa bata wuce Gombe.
“Please Ammi ki bari driver ya kai ki”.
“Kaga Darling ƙyaleni in naso driver ya kaini in naso kuma nayi driving da kaina nan da Gombe wani nisa ne?
“Ammi amma kinsan Nigeria ba Canada ba, hanyoyin nasu kaɗai ma ya ishe ki ciwon kai ba sai kin haɗa da driving ba”.
“To ubana! Ni dai ka kulamun da yarana” tana gama faɗa kitt ta kashe wayan ta yi duk abubuwan da ya dace a Companyn sannan ta fito da niyan tafiya amma Managern ya bata haquri ta huta tukunna.
A cikin motocin Companyn Managern yaɗau guda ya bawa Ammi driver akan ya kai ta Gombe, amma sai da yaja masa kunne ya kula sosai da tuƙinsa, sannan suka yi bankwana da Ammi driver ya kamo hanyan tahowa Gombe.
Hankali kwance suke tafiya, inda ta sanya drivern ya tsaya suka yi sallah a Bauchi sannan suka nufo Gombe, har sun fara shiga qauyukan Gombe dan sun kusa isa Kwami, gaban Ammi ne ya tsananta da faɗuwa dan haka sai ta ciro wayanta a haka dan qiran sweedy taji ko suna lafiya, gani tayi babu network dan haka sai ta aje wayan tana ambaton Allah da fatan Allah yasa lafiya.
Kaman daga sama ba zato ba tsammani driver yaji ya yi karo da wani abu kaman an aje akan kwaltan wanda hakan ya sanya shi kasa sarrafa stering motan, ƙwace masa motan yayi hakan ya sanya suka fara gangarawa gefe wanda da qyar drivern ya samu ya tsayar da motan, Ammi da ke bayan motan salati kawai take aikin yi, kamun ta dawo daga duniyan firgicin hastarin da suka kusa yi, kawai ta hangi mutane a gaban motan tasu da makamai, cikin storo ta jawo wayanta ta shiga WhatsApp, ita batama san layin wa ta shiga ba kawai rubutu take jikinta na rawa, tsawan da aka daka mata ne ya sanyata yin saurin kashe wayan ta tura a jakanta ta jefar a qasan motan wajan qasan seat.
Ƙattin maza ne baƙaƙe munana wanda kana ganinsu kasan babu ko ɗigon Imani a tattare da su, bindigu ne a hannun kowannen su kusan su rai bakwai 7, bindiga suka sanya a goshin driver wanda ya sanya shi dole ya fito, Ammi ma fitowan ta yi dalilin stawan da suka daka mata cikin yarensu da batasan me suke nufi ba.
Ammi da hausarta da ba sosai ba ta buɗe baki za ta yi magana amma kamun ta ma fara maganan wani a cikinsu ya buga mata kan bindiga, ai sai kawai Ammi ta faɗi ta sume, wanda drivern ganin haka sai ya fashe da kuka, amma mutanen nan ba imani balle tausayi haka suka dinga jan Ammi.
Jan Ammi suke ba tare da damuwa da gurjewan da take yi da buga kanta ba, kanta ne ya bugu da wani kututturen duste wanda ba shiri ya dawo da ita daga duniyan suman da tayi.
Tafiya mai nisa suka yi, nan kuwa mamaki ya kama Ammi duk da ba ta hayyacinta sosai, wasu mutanen suka tarar tare da waɗansu, munana ƙarfafan maza sun kai goma 10 tare da wasu mutane da suka kai Shida 6 wanda da alama suma kamosu aka yi kaman yanda aka kamo su Ammi.
Mutane biyar a gaba biyar a baya, uku a gefe da gefe suka sanya su Ammi a stakiya suka naushi jeji, tafiya suke iya tafiya ba tare da sun staya ba ko Hutu balle batun shan ruwa.
Abinda su Ammi suka fahimta mutanen basa jin hausa ko kaɗan kuma english ɗin ma sai caping suka iya basu iya brokin ba balle ordinary english.
Tafiya suke sai wata cikin waɗanda mutanen suka ɗauko ta gurgura caping ɗin ta ce “ina jin fitsari”.
Mutanen cikin faɗa da masifa suka yi yare, ganin matan na ƙoƙarin tsayawa suka sanya bindiga suka harbeta nan ta faɗi gawa, suka stalleke suka tusa su Ammi gaba aka cigaba da tafiya.
Wannan lamari ya storata sauran mutane huɗu da su Ammi su biyu, wani a cikinsu da alama tare yake da wacce aka harbe sai kuka ya sanya yana ambaton Allah.
Ammi ce tayi qarfin halin basa haquri da hausanta da bai nuna ba, sannan ta ce suyi ƙoƙari susan yadda za su yi su gudu, duk kallon bakisan me kike yi ba suka wurgawa Ammi domin Waɗannan mutane marassa imani masu fuskan kafuran da ko da kuɗi aka ce ka gudu ba zaka iya ba domin bindigun hannayensu da zubin halittansu kaɗai ya ishe ka shiga storo da tashin hankali.
Tafiya suke har yamma ta yi, Ammi abinka da ba sabonba har qafafuwanta sun kumbura kana ganinta kasan bata hayyacinta, ba abinda suke sai ambaton Allah ya kawo musu ɗauki domin su ba su ma san ko kidnapping nasu mutanen suka yi ko wani nufin daban.
Su Ammi su huɗu mata sai maza biyu, drivern Ammi da kuma ɗan uwan wacce aka harbe, mutanen nan ko alaman gajiya babu a tattare da su ko kaɗan tafiyan da suke yi bai dame su ba, su Ammi ne dai tafiyan ta jikkata su, musamman Ammi kana ganinta kasan duk tafi sauran kalan hutu bata saba da wahala ba.
Ammi kanta ciwo yake ga qirjinta na haka, jiri take gani qafafuwanta sun sunduma ga bugun da suka mata ɗazu ga kuma buguwan da tayi da suke janta, jinin da ya zuba a jikin Ammi shi ya haddasa mata wannan jiri da ciwon kai domin sosai tayi raunuka kuma ta zubar da jini, bibbiyu ta fara gani wanda kamun tayi wani yunquri tuni ta faɗa a jikin wani murɗeɗen qato a cikin waɗanda suka ɗauko su.
Wanda ta faɗa jikinsa cikin faɗa yasa qasan bindiga ya bugeta da shi wanda ya yi sanadin qarisawanta qasa babu numfashi.
Sauran duk stayuwa suka yi suna yare cikin fushi da stawa-stawa kaman za su kaure da faɗa a junansu, cikin yaren nasu wanda da alama shi ne babba stakaninsu ya ce “cap me de legit, oh she wan for her bodi woto-woto?(me ya faru ko bugu take buƙata?)
“Oga Pwade faɗuwa tayi a jikina kuma kaman bata numfashi”.
Wanda aka qira da Oga Pwaden ne ta masto ya sanya jibgegen qafansa yayi ball da Ammi amma ko mostawa bata yi ba dan kaman ta sandare ma da alama bata numfashi, qara naushinta yayi jin shiru sai ya stugunna ya sanya hannunsa a hancinta ya ji shiru ba numfashi, haka wuyanta da zuciyanta, jin shiru sai ya miqe yana masifa “kunsan dalilin ɗauko su, abinda za suyi baya buqatan kasancewan su da yunwa ko ciwo me yasa baku tambayi ne take so ba yanzu ga shi kunmana asaran mutum biyu kuma mata ga shi wannan kana ganinta kasan za ta fi burge Oga-kwata-kwata”.
“Sorry Oga pwade, to Ojonjo ya ɗauke ta mu tafi mana” sauran suka haɗa baki wajan faɗan hakan.
“Ku baku da hankali ne? Inmuka tafi da deathbody(gawa) muyi me da ita inba Oga-kwata-kwata ya kashemu ba, mu bar gawan mu tafi amma mu kula da sauran kar asaran tayi yawa ga shi ba mutane da yawa muka samo ba”.
“To Oga Pwade” suka haɗa baki suka faɗa, duk sai da suka naushi Ammi sannan suka tsallake gawanta suka tusa qeyar sauran a gaba suka cigaba da tafiya.
Tunda drivern Ammi ya ga haka sai shima ya kama salati yana kuka, dan duk stiya gwanda ace da ranta akan yanda suka mata ga shi ta mutu, baiwar Allah da gatanta amma dabbobin daji ne za su ci gawanta, kuka ya dinga yi wanda mutanen da suka ɗauko su sun zaci wani abu ne nan suka ciro biscuits suka raba musu, ai da gudu duk suka amsa kowa na korawa a cikinsa hannu baka hannu qwarya.
Ammi yanda suka barta a yashe kaman gawa ko mosti bata yi har can stakiyan dare wajajan qarfe biyun dare sai ga hadari da walkiya ba jimawa aka fara ruwa kaman da bakin qwarya, ruwa ake me qarfi kuma duka a jikin Ammi yake sauqa, kaman wacce aka stikara haka taja dogon numfashi tare da buɗe idanuwanta, jikinta ba inda baya mata ciwo ga kanta da ke sara mata kuma yana mata kaman jiri-jira, abu ta gani a hannunta kaman kwali, ba tare da ta tsaya duba menene ba ta sa a bakin zaninta ta tashi tanajin jirin haka ta sanja hanya ta kwasa a guje dan tabbas ta tuno abinda ya sa ta ganta a tsakiyan daji.
Gudu Ammi take yi ba ko waiwaye dan ji take kaman zasu biyota, ba tare da ta damu da kumburan qafan nata ba ko raunukan jikinta haka take kwasan gudu tana taka qayoyi jefa qafa kawai take yi bata san inda take nufa ba, jirin ne ya ci-gaba da damunta tana kan gudun amma abun fin qarfinta yayi tana gudu tana layi kaman wacce ta sha wani abu, ba zato ba tsammani lokaci guda ta taka wani mugun qaya da kuma kwalba, garin waywaye taci karo da wani ɗan bishiya tayi baya ta buga kanta akan wani qaton kututturen bishiya mai stini, shikkenan Ammi a gurin ta kuma mugun faɗuwa ba ta ko mosti dan ta bugu, qafafuwanta na jini kanta na jini.

Belloji ɗa ɗaya tilo ga Arɗo wanda Allah bai bashi haihuwa ba sai yayansa da ya haifa ya basa kyauta kuma ba jimawa Allah yawa iyayen belloji rasuwa, nan Arɗo ya riqesa gam-gam tunda shi baya haihuwa kuma ɗan yayansa sannan yayan nasa ya basa kyauta tun da ran sa, belloji na da shanyensa da mahaifinsa ya bar masa, Arɗo ma yana da nasa, sai belloji ya haɗa yana zuwar musu kiwo, tun yana yaro har ya girma.
Su bororaye ne na usul masu kiwon shanu, da ikon Allah dai suka ya da zango a wannan jejin har suka gina gidajensu na kara suka hayayyafa, amma sunqi shiga cikin mutane balle batun yin wani karatun zamani, sai ta muhammadiya kawai itama ba wai har can ba kawai na yin salla ɗan fatiha, Nasi da Falaqi.

“Hai belloji kam wei hai me shisheyi a shikin uwar ɗaka ba jaki hito hai ki tai kiwo ba, ko hai sho kike shaniyata ya mace da yunwa ce? Arɗo ke magana cikin harshen shi da fillanci ya cinye.
Yaron da ya qira da belloji ne ya fito daga wani ɗan madaidaicin bukka sanye da wando wanda suke ɗinkawa sama ya ɗame qasa ya buɗu da riga burgujeje da takalminsa wanda akewa laqabi da “tashi ka bi shanu”.
Belloji ɗan mastashin saurayi da ba zai haura shekara 17 ba siririne fari yana da ɗan tsayi sannan kyakkyawa ne dai-dai gwargwado, sandarsa ya ɗauka ya saqala a bayan wuyansa yana faɗin “yanju jan tai kiwon fa Arɗo, aradun Allah shaniyaki ya qi yin shauri aradu buge hegiya jan yi, na tai hai na dawo” ya faɗa yana ficewa a gidan.
Arɗo cikin fillanci ya zagi bellojin yana faɗin “cegiya belloji hai ki dawo da shanuwai na lahiya”.

Belloji yana fita ya kaɗa kan shanaye fin ɗari biyu suka yi jeji, yana tafiya yana ɗan waqar sa da fillanci.
Tafiya suka yi sosai shanaye na kiwo yanda ya kamata domin yanayin garin anfara ruwa ciyayi sun fito yanda dabbobi za su ci su qoshi, qasan wani bishiya belloji ya samu ya zauna yana ɓare gyaɗansa da ya taho da shi yana ci dabbobi na cin ciyayinsu su ma.
Har yamma ta yi sannan belloji ya fara kaɗo kan shanayen, wasu biyu ne suka yi kwana nan ya bisu yana taro kansu, da qyar ya samu ya haɗe su ya gangara da su rafi suka sha ruwa sannan suka nufi hanyan dawowa gida, belloji yana tafiya dai ya hangi bishiyan gwandan jeji yayi ‘ya’ya sun nuna, rasta wajan yayi yana faɗin “cege Arɗo jai washe matauni (haƙora), wanga gwandan da ta nune hai ka she kana taɓa hi kai fahe na shan jaqi jai yi”.
Kamun belloji ya qarisa wajan yayi tuntuɓe da abu, da yake kansa na sama miqawa kawai yayi zuwa bishiyan bai lura da me yayi tuntuɓe ba sai da ya gama ciki aljihunansa da gwandan jejin ya juyo kawai ya ga mutum jina-jina a kwance a qasa kaman gawa, cikin rashin storo ya masto kusa da ita yana faɗin “hai belloji ta shiga shaba’in Aradun Allah, wannan mutum ko aljan? Aradu ji cegen da cau dole na ɗauke sa hai muje na nunawa Arɗo me cau na shan Arɗo bata taɓa ganin mai cau ba aradun Allah”.
Belloji ɗago ta yayi ya saɓa a kafaɗa, qarshe akan shanu ya ɗaurata suka koma gida.
Suna shigowa gida ya bar shanayen a garekensu sannan ya ɗago matar da ta ɗauko yayo gidan Arɗo da ita yana shiga ya ce “Arɗo jo kiga aljana na shamo Aradun Allah yau, ai ni naga aljana mai cau Aradu”.
Matar Arɗo ce ta fito cikin fillanci tana faɗin “ke belloji ina kinka shamo wanga mutum?
Belloji ya buɗe baki zai yi magana sai ga Arɗo ya shigo “belloji kin higa uku kin lalashe, ina kika shamo aljana mai kyau? Cewar Arɗo yana qarisowa cikin gidan.
Matar Arɗo ce ta ce “haba Arɗo kur kuyi irin ta belloji mana, wanga ba aljani bane mutum she Aradu”.
Arɗo ne ya ce “Allah sarki bawan Allah dubi jikinshi hai duk shiwo, kai Maman belloji kawo tabarma”.
Matar Arɗo taburman ta ɗauko aka shumfiɗe Ammi, ruwan zafi ta ɗaura bayan ya ɗumu ciwokan fiskan Ammi da qafanta aka goge aka manna mata wani ganye da Arɗo yasa belloji ya daka.
Anan rugan tasu Arɗo ya aika aka qira wani mai magani, amma har aka kwana biyu ba alaman sauqi dan ga duk alama matar dogon suma ta yi, inka kalleta ma ba lallai ka gane da ranta ba.
Daga qarshe Arɗo ya aika rugan hamman aka masa magana da Baffai saboda dama kowa yasan Baffai a harkan magani dan ya gaji mahaifinsa ne mijin Baabaa Mero, anci sa’a Baffai ya amsa zai zo, inda ba ɓata lokaci ya je ganin matar sai ta basa tausayi kuma ya dage zai taimaka dan shi ma ya samu lada ba sai anbiya sa komai ba, kuma cikin ikon Allah ya mata magani ta warke.

CIGABAN LABARI.

Baabaa Mero ke rafka salati tana faɗin “ai nikam tunda Allah yasa Isa da Indo suka haifoki shikkenan sun haifomin jaraba, jarababbun iyaye koɗaɗɗu suna ganin na stofe sun turoki ki qarisa ni, da basa sonki suka haifeki ni Meramu naga rayuwa, Allah na tuba badan-badan ba ai sai nace da basu ma haiho ki ba, yarinya kullum abu guda jaraba akan bokon ‘yan wuta, to Aradu aure za’a miki a haka kije can ki fama in aka miki gori baki da ko nunu kece kika ja, shawaragiya shiyasa kullum ba ki da auki kaman hastin-bana”.
Innai tura baki tayi ta ce “ni fa ba iya zuwa zan yi ba baabaata”.
“Don yayan ubanki Musa ni baabaar ubanki ce ba taki ba, ja’irar yarinya kawai, Aradu in baki shirya ba kinfito yau sai nayi qasa-qasa da ke a garin nan, ko ma kija na ɗauke ki mu tafi masallaci naje can na bada sadakarki, ai ni Meramu aiki kuma ya qara samu na tunda jarababben hamman naku ya tattara komastansa wai ya tafi shima tasa karatun can wata uwa duniya ai ni aka bari da dogon baki akanki dan dama shi kaɗai kike storo kaman azara’ilunki,to bari kiji ubanki Isa zan sanya a nemomin salula duk randa kika buga min tijara nima na kamosa a salula na sanar masa yana miki adashe a littafi duk randa ya dawo ya ɓarzamin ke ‘yar buhun uba”.
Innai tura qaramin bakinta tayi tana qunquni ita qafanta na ciwo ba inda za taje, qarshe kuka ta sanya tana shura qafa “ni bazanje ba yau kuma ni na gaji da bokonma kuma Allah ba zan yi aure ba yiiiiiiiiiii yiiiiiiiiiii Wayyooo! Uwataa”.
Baabaa Mero wangale baki tayi tana ganin ikon Allah dan taqaici ta ma rasa me za ta yi wa jikartata ta huta, sai kawai ta rarumi daron kwano da yake gefenta tayi kan innai, ita kuwa ganin haka sai ta ruga a guje ta shige ɗakin ta turo ƙofa tana ihu ta rarumi kayan makaranta ta sanya ta fito ko mai bata shafa ba balle kwalli a ido, Baabaa ganin ta fito a shirye taɓe baki tayi ta ce dan uban mutum inyaga dama ya tafi tunɓur nidai abarmin gida a tafi koyo yaren ‘yan wuta, Allah yasa wancan qawar taki fatuma ta miki dariya”.
Innai tura baki tayi ta qi ko cin komai ta fice, gidansu taje ta iske Baffai ya fita, kaman za tayi kuka haka ta gaishe da mama Lami ta gaishe da Innarsu duk da ba amsawa take ba, Allah yaso ta Mama Lami ta bata Naira ɗari sannan ta fito ta samu Rabe na jiranta kawai ta ɗale mashine suka ɗau hanyan makaranta.

Kunce kunyi kewan Baabaa Mero 😁 to naga ruwan sharhinku ga Baabaa Mero.

MASU SHARHI UWAR BATOORL TAKU TA GODE🤝 DAN SHARHIN KU SHINE QWARIN GUIWANA
MASU GODIYA BANSON THANKS NAKU KUMIN SHARHI KAWAI SHI NAKE BUQATA.

 

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR’S ANNIVERSARY

FAN’S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

💋💋 امى بتولة💋

*Wannan page naku ne masu daraja ‘yan Amana Uwar batoorl na yinku*

Deejerh nata’ala

Surayyatou nah

 

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 49_50

Hajja ce ta tura qofan ɗakin Afrah ta shiga tana faɗin “wai Fatuma yau ba za ki je…” Maganan ta kasa qarisawa kawai ta sanya salati “La’ilaha illallahu Muhammadu Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam, ni jikar mutum huɗu me zan gani? Fatu baccin asara kuke yi tun ɗazu dama baki shirya ba kin biyewa Munawwaratu ita da ba uwar inda za ta leqa ko qofa ta-kashi, to tashi kamun na qira Nura yanzunnan” ta faɗa tare da zubawa Afrah bugu a cinya.
Afrah kaman za tayi kuka ta tashi dan ita sam duk ta mance yau Wednesday ne suna da school, sauqa tayi a gadon tana qunquni “ni wallahi na manta yau akwai makaranta kuma yanzu lokaci ya tafi ko naje nasan duka na za’a yi, ni ba inda zanje” ta faɗa tana shigewa toilet.
Taɓe baki Hajja tayi sannan ta juya ta fice a ɗakin tana cewa “sai kinje dan uban wani ne ya sanya ki yin bacci ko stabar samun waje wai karuwa da sallahn walha, to za ki fito ki tafi kuma yanzunnan zan qira Nura na sani shi ne dai-dai da ke ‘yar fatarin uba ta renani ina takwararta”, Hajja ɗakinta ta shige ta samu sweetie na game na maciji a Nokianta, zama tayi tana faɗin “ƙawar Hajja kamomin layin baffanki Nura dan in bai stawatar wa wannan sakalalliyan ba nasan ba inda za taje yaran zamani duk idanuwanku a tsai-staye kun fistare qafafuwanku bakwajin maganan kowa sai na iyayenku dan carɓin rashin ta idonku kun cike shi cass, mu a zamaninmu ai ko kakar kishiyar maƙociyar goggon mai anguwan garin su pendon uwar ubanka ce ta maka magana tsaff muke biyayya amma ku yaran yanzu sai addu’an shiriya domin wasu yaranma ko na iyayensun basa ji, to Alhamdulillahi tunda kunajin nasu Allah ya muku albarka ya shirye ku”.
Sweetie jin lissafin kalen dangi da Hajja ta surfa ai sai ta dinga tiqa dariya kaman za tayi kuka har sai da Hajja ta dundeta kamun ta tsagaita ta qira mata layin Daddy, yana shiga ya kashe ya qira ta miqawa Hajja ta cigaba da dariyanta.
“Nura ka qira yarinyarka yanzunnan ta shirya ta tafi makaranta ko na mata rashin kirki” faɗin Hajja cikin faɗa ko gaisuwan da Daddy ke mata bata amsa ba.
Daddy haquri ya bawa Hajja sannan ya gaisheta ta amsa suka yi sallama ta kashe wayan tana faɗin “Muheebbah kekuma taho mu karya”.
Sweetie tana dariya ta shirya tsaff suka fito da Hajja suka zauna dinning da aka gama jera kayan kari, ba jimawa sai ga sweedy ta fito, ta gaishe da Hajja itama ta zauna suna Indianci da sweetie.
Afrah wasta ruwa tayi ta fito ta shirya sama-sama ta juya zata fita qira ya shigo wayanta, tana ji tasan Daddy ne kaman za tayi kuka ta ɗauka dan bata isa taqi ɗauka ba.
“Hello! Daddy good morning”.
Daddy a ɗaya ɓangaren jinjina kai kawai yayi yana addu’an shiriya ga yaran nasu ya ce “Afrah morning daga ina? Har yanzu kina zaune baki tafi ba kina sane da exam’s za kuyi nan da kwanaki ko, ki fita idona Afrah maza-maza ki shirya ki tafi kar na saɓa miki”.
Kaman za tayi kuka ta ce “kayi haquri Daddy na gama shiryawa yanzu zan tafi”.
“Good a dawo lafiya kuma a mayar da hankali ayi karatu”.
Sallama tayi da Daddy ta kalli sweerie da ke shiryawa ta ce “sistor na tafi makaranta jaraba kai da hutawa sai ka mutu, kai ni Allah bani miji nayi aure na huta kuma Allah yasa ya ce bazan cigaba ba dan sai nafi murna, kuma Allah ko su Aunty Afreen ba suyi aure ba yin abuna zan yi tunda dai ban hanasu ba bari Allah ya bani miji kugani har Hajja sai tasha mamaki” ta faɗa tana ficewa a ɗakin.
Sweerie dariya ta dinga yi har ta kammala shirin ba jimawa itama tabi bayan Afrah.
Bakin nan a gaba an cunnon sa aka fito tana ta harare-harare, hanyan waje ta nufa za ta fice sai Hajja ta tsayar da ita “yunwa ba baffanki Mustapha bane dan haka sai kinsa abu a cikinki za ki tafi, ba zaki jawa mutane ja’iba cuta bayan rai ba, ulcer ta kamaki ki tashi hankalinmu” cewar Hajja tana wastawa Afrah harara.
Sweetie miqewa tayi cikin shagwaɓa ta ce “Aunty masoyiya zan biki school naku nima sai na tayaki karatu”.
Afrah da ta haɗa fiska jin abinda sweetie ta faɗa sai ta kama dariya tana faɗin “mintin zuciya dama ana raka mutum makaranta ne? Kiyi haƙuri yanzu zan dawo ba zan jima ba kinji”.
Sweetie bubbuga ƙafa ta kama yi tana kukan rigima ita sai ta bi Afrah, sweedy gajiya tayi da jin hayaniyan gashi ana ɓatawa Afrah lokaci dan zuwa yanzu kamun ta isa ma tayi latti, stawa sweedy ta dakawa sweetie akan in bata daina ba zata haɗata da Darling, qin yin shiru tayi, Afrah sama-sama tasha tea ta kama hannun sweetie ta ce “mu tafi in aka dakemu tare kin huta dan nayi latti” suka fice a Palourn sun samu driver na jiran Afrah kawai suka shiga ya ja su sau school.
Hajja da kallo ta bisu har suka fice a palourn sannan ta yi magana “gaskiya ni fatuma ina ganin abubuwa iri da kala, duk jikoki ace babu na yasarwa amma guda na Allah da Manzonsa mai jin magana kawai ke ce Muhseena sai dama-dama Jabiru, to ni mai zan ce in ba addu’a da fatan shiriya gareku ba, Allah rufa muku asiri kar jikokinku su muku abinda kuka min dan na tabbata sai kun haukace, yaran wannan zamanin ma ya aka qare balle na wani zamani, to Allah ka kyauta ka shirya mana zuri’a alfarman Annabi Muhammad SAW, Ameen”.
Sweedy murmushi tayi itama ta amsa da “Ameen Hajja tamu”.
Sweerie zama tayi tana gaishe da Hajja, sai Hajja ta haɗe fiska taƙi amsawa, sweerie dai abun dariya ya bata sai ta gaishe da sweedy da Indianci tana tambaya Afreen, Hajja ce ta ce “yara gaba da baya kun rungume harcen Hindu kunqi na ubanku, ko wa ya faɗa muku haka akeyi oho muku ku kuka jiyo ai, inbaku koya ba ma ku ta mastewa, ke kuma wato na ɓata rai ban amsaba shi ne ba za ki tambayi laifinki ba kika gaisheda yayarki kika bawa banza ajiyana, to a kunnen Mustapha tunda baccin asara da mutuwan rai kuke yi har kun ja Fatu na ta makara, aka taɓa ta akanki zan rama mata”.
Sweerie murmushi tayi ta ce “Allah huci zuciyan Hajja tamu ta malam muhammadu, Allah baki haquri”.
Hararanta tayi ta ce “in Allah ya bani haqurin sai ki ƙwace, dan tsabar lalacewan zamani ace da asuban farko ki kama qiran sunan bawan Allah yana kwance makwancinsa cikin rahamar Ubangiji nasan yanzu haka kin kora sallahn asuba da ya kai masa ziyara ja’ira”.
Duk dariya suka sanya, sai ga Afreen ta fito tana faɗin “a wani islamiyyan aka faɗa miki haka Hajja?
“A islamiyyan uwaki Maryam da ubanki Nura tunda ke saboda balagan rashin jinki sai yanzu kike fitowa kuma ba gaisuwa kike stomo baki cikin zance na da jikokina”.
Afreen taɓe baki tayi ta zauna sweerie ta gaisheta sannan ta haɗa shayinta tana korawa, buɗe kulolin tayi ganin abinda yake ciki ta ɓata fiska ta ce “ɗumamen tuwo sai kace muna cikin daji gaskiya yau zan koma abun ya isheni”.
Hajja guntun tsaki taja ta ce “Nura ma da ɗumame ya ci ya girma har ya auro Maryam ta haiho ki, ki koma dama ba wanda ya gayyato ki ke kika kawo kanki neman wajan zama, ‘yar kalen dangin stiya”.
Afreen bata kuma cewa komai ba ta cigaba da lasta wayanta, sweedy ma shirun tayi dan kaman ma hankalinta baya wajan sai sweerie da ke aikin dariyan surutun Hajja.
Hajja miqewa tayi bayan ta wanke hannu ta wuce ta zauna a kujerun palourn tana faɗin ” ‘yan banzan sai yaushe za su sakawa mutane vidiyon masu karairaye jiki kaman ba qashi ne da su ba (kung-fu China Film🤣).

Innai suna isowa da Rabe Allah ya taimaketa ana assembly tukun ba’a fara tare latti ba, hamdala tayi ta shige makarantan cike da ɗaukin son ganin Afrah, dan kaman fushi take da ita rabuwansu na qarshe.
Layin ‘yan ajinsu ss1 taje ta staya tana ta kan leqe-leqen ta ina zata hango Afrah dan bata kalleta ba, wata Malama ce ta masta alama da ta nustu daga wajan stayuwan malamai, sai na daina leqe-leqen tana Allah-Allah a kammala taga Afrahnta.
Har aka gama assembly, aka yi inspection bata ga Afrah ba, itama Allah ne ya taimaketa da an doke ta dan anbada style ranan bata zo ba bata da lafiya, aka gama aka sallami ɗalibai kowa ya kama hanyan ajinsu, sai lokacin ta tabbatar Afrah bata iso ba dan leqawa ta dinga yi ba ita har suka isa aji kowa ya samu wajan zamansa ya zauna, ba jimawa Malam ba wasa ya shigo.

Afrah tun daga mota take aikin yarfe hannu da ta tambayi driver ya faɗa mata time dan ta tabbatar yau ta kaɗe har hanjinta, sweetie sai surutunta take yi ita kaɗai Afrah tunaninta na kan lattin da tayi, suna isowa kuwa lokacin angama wastewa a assembly kowa ya tafi aji, tun daga bakin gate take hango ‘yan latti, kaman za ta zura a guje haka take ji, driver ya sauqesu ta kama hannun sweetie suka shige, fiska tayi suka yi hanyan class amma discipline Master ya daka mata stawa ya stayar da su, Afrah jikinta na ɓari suka dawo wajan suka bi layin tare lattin, sweetie ce tayi magana qasa-qasa “Aunty masoyiya mukam ba’a dukanmu latti a Canada ki ce Darling ya maidake school namu na Canada”.
Afrah kaman za ta yi kuka itama qasa-qasa ta ce “mintin zuciya kibar magana za mu ƙara laifi”.
Sweetie shiru tayi tana dariya qasa-qasa.

Jay ne ya fito da shirin sa staff na tafiya office, qananun kayan da suka yi mugun karɓansa ya fito sanye da su, dinning ya wuce yana kan duba agogon da ke maqale a hannunsa, mummy da Daddy ya samu a dinning ɗin, ɗan rusunawa yayi ya gaishe da Daddy ya amsa ya kuma gaishe da mummy itama amsawan tayi ta tashi ta sanya masa abun karyawan, Daddy ne yayi gyaran murya ya ce “Jabeer kai da ɗan uwanka ku dage kuje Maiduguri ku stayar da mata dan kun fara isanmu, iyayenku mata su kula da mu su kula da ku, yanzu dubifa a maimakon kai ko matarka wani yayi saving namu shi ne mamanka ce take saving naka ba kunya ka amsa ka ci, to ko kuje ku duba da kanku ko muyi magana da Mustapha a zaɓa muku kawai a ɗaura”.
Jay kansa a qasa bai cewa Daddy uffan ba yana jefa chip’s nasa a baki da wuri-wuri yana bi da tea da mummy ta gama haɗa masa yanzu.
Mummy ce tayi magana itama “maganan ɗaukomin yarinyana ka tabbatar ka dawo da wuri kaje ka ɗaukota”, kaman zai yi kuka jin surutun iyayen nasa ga shi yayi latti sauri yake yi ya ce “Habibty dude zai je dubo su sweetie inyaso sai ya ɗauko ta”.
“Eh dole tunda ni ban isa da kai ba ka ce son zai ɗauko ta, to kai nakeso kaje ka ɗauko ta banson rashin kunya”.
Jay ba yanda ya iya ya ce “to habibty zan ɗauko ta Allah huci zuciyanki”.
Qwafa Daddy yayi ya ce “yara duk kunbi kun rena mutane, wato dan an sake muku shi ne zai zama abin yinku, ba laifinku bane nine na qyaleku tun kuna yara kuke qiramun mata Habibty, to ya isheku kowa yaje ya nemo tasa habibtyn kubarmin tawa in ba za ku ƙirata mummy ba sai ku ƙirata Maryam mu tabbatar kun girma”.
Jay ganin yau iyayen nasa da shi suka tashi a wuya sai ya ɗaga cup na tea ɗin ya shanye tass ya miqe ya musu bankwana bi jira sun ce komai ba ya fice abinsa yana faɗin “yau ko wa ya taɓo ku kuke sauqewa a kaina oho! To Nima na tafi kuma daga asibitin zan wuce Ashaka tare da ita za mu dawo inyaso ayi mana faɗan tare ba ni kaɗai ba” ya shige motansa ya nufi FMC Gombe.

Kwance yake a haɗaɗɗen gadon sa yana mustu-mustu alaman yana son farkawa, qarar da wayansa yayi ne ya sanya shi qarisa buɗe ido ya miqa hannu ya ɗau wayan, ganin sabon number sai bai ɗauka ba ya miqe ya zauna, can sai ya tashi ya shige toilet yayo wanka ya fito ɗaure da towel iya guiwansa, wayan ne ya qara ringing ya ɗauka ya ga Numbern ɗazu ne sai yaja staki ya wuce gaban mirrow ya gama shafe-shafensa ya gyara gashin kansa da gemunsa sannan ya wuce ya sanya kayansa, wayan ya ɗauka yana ƙoƙarin fita sai ga qira Managern sa na Jigawa, fasa ficewan yayi ya koma bakin bed ɗin ya zauna yana picking call ɗin Managern ya gaishe sa ya kuma qara jajanta masa sannan ya ce “Sir inba mastala akwai buqatan zuwanka Companyn kana da baqi”.
Dafe kai DMD yayi dan shi a wannan yanayin bayajin yana da nistuwan da zai iya haɗuwa da wasu, cikin yanayin rashin son magana ya ce “su waye ne baqin?
“Sir wasu turawa ne sai Alhaji Abdullahi Naira, sunce suna buqatan ganinka na faɗa musu akwai bussyn da kakeyi amma sun dage a haɗa su da kai shi ne nace sai na faɗa maka sai a sanya lokacin meeting”.
Iska mai zafi ya busar a bakinsa sannan ya ce “gobe Thursday by 2pm su tabbatar ba su yi latti ba dan ina da abun yi”.
“Okay Sir”.
Kitt DMD ya kashe wayansa cikin gajiya dan yasan gobe ranan yin ciwon kansa kenan, in akwai abinda ya stana meeting barinma da turawa dan su basusan darajan lafiyan jikinsu ba surutu kaman dan shi kaɗai aka tsaga musu baki, saqo ne ya shigo wayan ta Gmail nasa ya shiga ya duba ganin wani abun sai ya kuma dafe goshi yana faɗin “na fara gajiya da ayyukan nan mutum ba zai yi lokacin kansa ya huta ba, am not going to Canada without Ammi duk abinda zai samu Companyn ya same sa mtsww!”
Miqewa yayi ya fice a ɗakin ya sauqo palourn qasa ya tarar Daddy na shirin fita, gaishesa yayi ya amsa yana faɗin “son zan fita ko akwai wani magana?
DMD kaman baison buɗe baki ya ce “Daddy ba komai dama inaso ne a maida kuɗin reward na wanda ya kawo Ammi ya koma 10millions ne”.
Daddy murmushi kawai yayi ya ce “karka damu son, in duk duniya abinda muka mallaka za mu bayar Maimuna ta dawo to za mu bada, amma bana tunanin issuen kuɗi ne ya sa haryanzun ba labari kai dai mu dage da addu’a, in na dawo za muyi magana ko”.
“Okay Daddy a dawo lafiya”.
Daddy ficewa yayi yana tausayin yaran, Darling dinning ya wuce ya haɗa tea da kansa ya sha ɗan dai-dai sannan ya miqe ya nufi ɗakin mummy, a hanya suka haɗu itama tana nufo palourn, gaisheta yayi ta amsa sannan ya juya zai fita, mummy da kallo ta bisa tana faɗin “yau ko shayin ba za’a sha bane balaraben Ammi?
Yana murmushinsa mai stada ya juyo ya ce “habibty na sha har da chip’s na taɓa sai na dawo” ya faɗa yana ficewa a palourn shi ma.
Mummy dai ta yarda ya ci dan tunda yasan anyi chip’s to yaje dinning dan haka sai ta qira mai aiki ta tattare wajan ita kuma ta zauna tana kallo.
Yana ficewa ya hau motansa haɗaɗɗe ya nufi FMC Gombe, yana isa yayi parking ya shige hanyan office na Jay, turawa yayi ya shiga bai ko yi knocking ba Allah yaso ba kowa sai Jay da ke faman rubuce-rubuce a files, jin an shigo ba sallama ya ɗago da tunanin ko DMD ne ai kuwa shi ɗin ne, girgiza kai yayi yana faɗin “nasan ba mai shigomin office haka sai kai dude, wallahi ka bi a hankali dan watarana kunyataka zan yi domin ni kasan ba kunya gareni ba kana shigowa kawai ka ganni saman babe muna sharholiya”.
DMD zama yayi a kujeran dake gefe can da Jay yana faɗin “aikinka kenan, ga shi ka zama likita sai iskancin ya ƙaru, ni na rasa dalilina na son biyoka ma tunda samun ciwon kai kake”.
Dariya Jay ya kwashe da shi ya ce “to daganan za ka fahimci in tarkona ya kama mace to fa ta shiga uku ba sukuni sai ta ga jabirunta ta faɗin Hajja wai jabiru, kai da kake namiji ma kana ta bina balle mace ah kace nikan ba ruwana da suratul Yusuf ko Maryam normal ne”.
DMD miqewa yayi ya shige room ɗin cikin office ɗin ba tare da ya tanka masa ba, zama yayi a kan 3seater da ke ɗakin hankalinsa gaba-ɗaya na kan wayan hannunsa, qoqari yake ya ji da issuen Companies na Canada ba sai ya koma ba.
Jay ya tashi zai bi DMD ciki sai patient suka shigo, sai da ya gama da su sannan ya biyo DMD yana faɗin “dude ya batun zuwa Ashaka?
DMD da hankalinsa ke kan aikin da yake yi ya ce “yaushe muka yi da kai zan je Ashaka?
“Dude banson irin maganannan ba kai kace za kaje dubo su sweetie ran Wednesday ba, ko ka manta ne?
“Ohh god! Wallahi gaba ɗaya Jay na mance, yanzu ga tafiya Jigawa gobe ya kamani ga zuwa Ashaka bari na wuce yanzu dan na dawo da wuri” faɗin DMD yana ƙoƙarin miqewa.
Jay ya ce “dude please ka dawo da Afreen wallahi Habibty ta damu a ɗauko mata yarinyarta kuma ga shi ni anjima ma ina da operation”.
“Amma dai jabeer Habibty ta ce ba Mufaddal ba ko dan haka ba wacce zan ɗauko a mota ta”.
Jay yasan dama za’a rina dan haka ba yanda ya iya sai ya ce “to ka jira ni sharp-sharp nayi operation sai mu wuce, dama Habibty ta ce ni ta aika ba kai ba ni zan ɗauko mata yarinyarta”.
DMD komawa yayi ya zauna bai ce wa Jay komai ba sai ma hankalinsa da ya qara maidawa kan abinda yake yi a wayan.
Jay ficewa yayi, can ba jimawa ya dawo ya sanya labcort ya fice, eye glasses nasa ya sanya sannan ya sanya safan hannu da facemask ya fice a office ɗin, direct theater room ya wuce inda ya tarar duka nurses ɗin suna jiransa sun kammala komai wa patient ɗin theatern kawai zai yi.
Sai da suka kwashe a wanni biyu a theater room ɗin sannan ya cire safan hannun ya jefa a bowl na nurse’s ɗin ya fice, yana shiga office nasa ya zare facemask yana faɗin “Allah ka basa lafiya kasa munyi a sa’a” ya shige room da DMD yake ya cire labcort ɗin ya shige toilet sai can ya fito ya gyara jikinsa yana faɗin dude ka sanya wani bawan Allah a addu’a sai kaga yanda cutan ulcer ta masa kaca-kaca da hanji, kai jama’a Allah raba ɗan adam da wahala, ai cuta masifa ce yau duk qiyayyarka ga mutum ba zai sanya maka ciwo ba ai ba qinka yake yi ba, wallahi ulcer babbar cuta ce gwanda ka dage da ci dude inka staya rigima ta kama ka za ka faɗawa ‘yan Canada billahillzi”.
DMD ba tare da ya ɗago ba ya ce “Allah ya basa lafiya, mu wuce yanzu”.
Jay hararan wasa ya aikawa DMD ya ce “amma ba ka da mutunci balle imani, na staga bawan Allah nayi tafiyata ai ma jira anjima kaɗan mu tabbatar komai normal sannan ko hutawa ban yi ba, gaskiya ba ka da kirki dude ko zuciyan musulunci ma ba ka da”.
DMD murmushi yayi kawai da gefen baki hankalinsa na kan wayansa bai ce masa uffan ba, Jay ya tashi ya koma office nasa.
Sai da aka jima sannan Jay yaje da kansa ɗakin da aka dawo da patient ɗin ya tabbatar komai lafiya sai jiran farkawansa sannan ya ce da Nurses su kula da shi zai je aikan mummynsa zuwa dare zai dawo ya duba jikin patient ɗin, ya koma yayiwa DMD magana sannan ya miqe ya fito suka shiga motan DMD Jay yabar nasa a asibitin dan in sun dawo sai ya biyo asibitin kamun ya koma gida, suka kama hanyan Ashaka Jay na surutun sa DMD sai jifa-jifa yake amsa wani maganan.

Malam ba wasa tun da ya shigo yake satan kallon Innai dan gani yayi ta rame amma ta ƙara kyau, magana yayi a zuciyansa shi kaɗai “wannan yarinya akwai kyau kaman aljana, ba dan rashin girman ta ba me zai hana nabi ta shawaran Jay”.
Innai dai yau ko ta kan malam ba wasa bata bi ba hankalinta gaba-ɗaya na kan qofa zuba ido take taga ta inda Afrah za ta ɓullo, shiru-shiru ga shi windonsu ko ka leqa baya facing na gate balle ka kalli ‘yan latti dan bata cire tsammanin Afrah latti ta yi.
Malam ba wasa sai da ya ɗan yi wasu abubuwa sannan ya fara qiran sunan rigister, yana tsaka da qira sai ga discipline master ya yi sallama a bakin qofan ajin, barin qiran sunan Malam ba wasa yayi ya ce “Malam ka shigo”.
Discipline master shigowa yayi suka gaisa da Malam ba wasa ɗaliban ma suka miqe suka gaishe sa sannan ya ce “Malam Farooq ‘yar a cikin ‘yan ajinka waɗanda suka yi latti ana dukansu ɗaya a cikinsu ta faɗi ta suma”.
Malam ba wasa cikin ko inkula dan haushi students masu latti suke basa ya ce “ku wasta mata ruwa in ta farfaɗo ku qara mata ta kuma suma ku wasta mata ruwa haka-haka har ku gama dukan naku ai ita tajawa kanta tunda yara basa ji, kuzo makaranta akan lokaci ya zama aiki mu malamai ma sai mu rigasu zuwa dan tsaban sun renamu kuma a hakan iyayen suna stawatar musu da ba’a stawar musu wa yasan lokacin da zasu dinga zuwa”.
Discipline master ya ce “malam Farooq wallahi an watsa mata ruwa amma ko mosti bata yi, ga shi tazo da wata yarinya wacce da alama ba’a makarantan nan take ba, yarinyar ma sai indianci take yi wai su a Canada ba’a dukan su latti ga shi an daki auntynta an kashe ta sai ta kullemu”.
Malam ba wasa cikin haushi ya ce “dama har da ‘yar rakiya ta taho? Me sunanta?
“Students naka sun ce sunanta FATIMA NURA MUHAMMAD”.
Discipline master na kammala faɗin sunan Afrah ba ɓata lokaci Innai kaman wacce aka stikara kaman aljana kamun malam ba wasa ya ce wani abu har ta fice a class ɗin da gudu tayi wajan ‘yan latti tana qiran Afrah dan har ta fara hawaye, Afrah ta taɓa faɗa mata ita in aka daketa ciwo take yi storon duka take yi”.
Malam ba wasa da mamaki ya juya suka fice da discipline sai kuma ya dawo ya jawa ‘yan ajin kunne sannan suka wuce, ya iske Innai ta rungumi Afrah sai kuka take kaman ance mata ta mutu, ga sweetie kuma a gefe sai sharɓan nata kukan take itama tana masifa da indianci, malam ba wasa kallonsu yayi tare da yin qwafa ganin irin ihun da yarinyar da aka zo da ita take yi tana qoqarin tara musu jama’a dan har malamai sun fara nufo su ga ɗalibai sai leqowa ake wasu ma fitowa suka yi daga ajujuwansu suna ganin gulma.
Stawa ya dakawa Innai yana magana da turanci “ki ajiyeta ki koma class kamun na yi ball da ke, za ku tara mana mutane mutuwa ta yi ko kasheta aka yi”.
Innai duk da kuwa stawan ya storita ta amma ko mosti bata yi ba, malaman da suka iso ne suka fara tambayan akasi, shi malam ba wasa haɗe fiska yayi sai discipline master ke bawa Kowa amsan abinda ya faru a taqaice in suka tambaya.
Duk malaman sun taru anrasa ya za’a yi, har sai da principal yazo da kansa sannan ya stawatar musu sun saka yara gaba ba zasu yi wani motsin ba in yarinya ta mutu fa? Duk haquri suka bada saura suka bar wajan aka qira Malama mace tazo ta ɗauki Afrah suka kai ta masallaci, aka shashshafa mata ruwa amma ko mosti bata yi ba ganin haka aka qira malam ba wasa akan ko za’a kai yarinya gidansu, malam ba wasa ya ce eh yasan gidan nasu, sai principal ya ce a ɗau school boss a kai su.
Innai duk abinda ake yi tana maqale da Afrah tana kan shararo hawayenta, ita kuma sweetie surutu take kan yi, malam ba wasa sai yanzu ya kula da ita ya ce “sweetie” kallonsa tayi kaman ta ganesa shi ne wanda suka je gida da big bro aikam ta ce “uncle sun kashe Aunty Afrah akan latti kuma ba kyau dukan yara ɗalibai” ta faɗa da turanci, murmushi malam ba wasa ya yi a ransa yana faɗin “wannan dokan ku ne a ƙasashen waje mukam a Nigeria ba ruwansu a ta jibgan yara kaman jakkai Shiyasa wasu yaran ma basa fahimtan karatun”.

MASU SHARHI UWAR BATOORL TAKU TA GODE🤝 DAN SHARHIN KU SHINE QWARIN GUIWANA
MASU GODIYA BANSON THANKS NAKU KUMIN SHARHI KAWAI SHI NAKE BUQATA.

 

INA KUKE MASU SANA’A, SANA’A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana’ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇’𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺

 

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

LAFAZI WRITER’S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member’s ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR’S ANNIVERSARY

FAN’S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔’𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.

💋💋 امى بتولة💋

 

 

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 51_52

Malama mace aka sa ta ɗauki Afrah ta sata a school boss ɗin sannan malam ba wasa da sweetie suka shiga, Innai tana kuka ta zo zata shige amma malamai suka nuna ba inda za ta je, malam ba wasa yana ganinsu ya kau da kai,har driver ya tayar da mota sannan ganin Innai yanda har fiskanta yayi ja sai ta basa tausayi ya sa driver ya staya ya ce wa malaman Innai ‘yar uwan Afrah ce sannan suka barta ta shigo driver ya ja suka tafi, gefen Afrah taje ta rungumeta sai sannan Malam ba wasa aya dube ta ya ce “share hawayenki da ranta”.
Innai share hawayen tayi kaman yanda ya umurce ta, sweetie dai sai kallon Innai take dan ta mata kyau ita a rayuwanta tana son mutum mai kyau kuma mara jiki shiyasa take jin haushi in an qirata ‘yar lukuta.
Malam ba wasa ne ya dingá directing na driver har suka isa gidan sannan yayi parking su Innai suka fito shi kuma ya ɗauki Afrah sannan ya sallami drivern akan zai koma school ɗin da kansa, driver ya juya su kuma suka shige gidan malam ba wasa na mamakin rashin nauyin Afrah duk da yarinya ce amma ko kaɗan kaman an ɗaga papper.
Da sallama suka shiga palourn sweetie da ta riga su taba faɗin “Hajja ki fito ba kin takurawa Aunty masoyiya taje school ba bayan ta ce miki tayi latti ga shi sun dake ta sun sa ta daina mosti” sai kawai ta fashe da kuka tana gana maganan.
Afreen da fitowanta kenan daga ɗaki tana waya da mummy tana faɗin “habibty har yanzu fa 12 ya kusa ana neman azahar bai zo ba, nikam zan taho da kai na kawai”.
Ganin sweetie na kuka sai tawa mummy sallama ta kashe wayan tana tambayan sweetie lafiya? Bata ida rufe baki ba malam ba wasa ya shigo da Afrah a hannunsa, ai wajansa tayi da sauri tana tambayan me ya samu Afrah?
Malam ba wasa ajiyeta yayi akan 3seater bai ce uffan ba ya mai da kallonsa kan sweetie ya ce “qiramun Hajja”.
Hajja da ke fitowa a ɗaki ta ce “ganinan me aka kawo mun ɗan nan, ke kuma sakalatun kukan me kike wa ya dawo dake daga makarantar?” Qarisa shigowa palourn Hajja ta yi bata ma lura da Afrah da aka kwantar ba balle Innai da ke raɓe-raɓe ba wanda yasan da ita a palourn sai malam ba wasa dan ko sweetie ta manta akan sun taho da wata ƙawar Afrah.
Malam ba wasa gaishe da Hajja yayi yana faɗin “ayi haquri Hajja wallahi ba’a san da tana da wata laluran ba shiyasa aka dake ta”.
Hajja da sai yanzu ta kula da Afrah ai miqewa tayi sai ganinta aka yi gaban Afrah tana faɗin “Ni Fatu na shiga uku wai dukan lattin aka miki da gaske, yau na ga ta kaina na ɗauka wasa kike ba kiyi latti ba, dan Allah takwara ta tashi kinji” Hajja ta faɗa har da guntun ƙwallanta.
Malam ba wasa dai ya rasa yanda zai yi dan shi kunyan Hajja ma yaji an daka mata jikarta, Hajja kuwa masifa ta dinga yi kaman zata ari baki, har su sweerie suka fito a ɗaki suma, ita sweedy har da ƙwallanta, sweerie kuwa faɗi take, “ai wallahi da a Canada muke da tuni yanzu ankai malamin da ya bugi Afrahty children’s right association an bi mata haqqinta, mastalana da mutanen Nigeria kenan ba abinda suka iya sai dukan yara, mu ko yaro laifi yayi baka isa ka hukuntasa mugun duka har ya suma ba tuni ma’aikata suka zo suka tafi da kai ko kai ne mamansa ko babansa ba ruwansu, shiyasa AL’ADAN su ke burge ni ba kaman Nigeria ba sun san yanda ake bi da yara su dinga jin magana ba tare da duka ba.”
Shi dai malam ba wasa rasa yanda zai yi yayi, cikin qarfin hali ya ce, “Hajja ko akwai abinda ake mata in haka ta faru?”
Hajja ta ce, “ɗan nan ba wani abu face a kaita asibiti tayi jinyan kusan mako guda, kai Allah mun tuba Allah ka yaye mana masifan da ƴan adam ke jawomana.”
Jin abinda Hajja ta faɗa sai ya ciro wayansa ya qira Jay suka yi magana ya faɗa masa suna hanya kar su kai ta asibiti zai taho da duk abinda ya kamata, bayan sun yi sallama kenan ya faɗawa Hajja sai ta ce, “yanzu kai ma da nake yabon haka halinka yake? Biyewa jabiru za kayi kamun ya iso yarinya numfashi ya qarisa guduwa ko, to ban isa ba asibiti zamu kai ta”.
Sai da ƙyar malam ba wasa ya lallaɓa Hajja suka zauna jiran zuwan su jay shima bai koma school ɗin ba ya zauna, zuwa yanzu malam ba-wasa ya manta da Innai kuma ga shi tana staye a rakuɓe duk abinda ake yi bata zauna ba dan ganin yanayin gidan nasu sai storo ya kamata ga shi tanajin masifan da Hajja ke yi duk da ta saba da ba Baabaa Mero amma sai taji storon kakan Afrah, malam ba wasa shiru ya zauna idonsa na kan TV sai su sweetie da suka zagaye Afrah suna mata fifita sun cire mata hijab ma zuwa yanzu.
Malam ba wasa juyawa yayi da niyan kallon direction na Afrah, ai sai idanunsa carab akan qirjinta da yake sun cire mata hijabi kuma Afrah dama tana da breast kawai ba manya har can bane ƴan dai-dai ne, saurin kawar da kai malam ba-wasa yayi yana maida idanuwansa kan TV.
Hajja dai sai azalzala mita take yi kaman ta jawo Jay.

DMD da ke driving ne ya ɗan kalli gefen da Jay ke zaune ya ce, “what’s wrong with Afrah?”
Jay dafe kai yayi ya ce, “dude ai Afrah bansan ko wacce irin yarinya Habibty ta haifa ba, yarinya sai storon bulala ga rashin ji, ace ana taɓaki da bulala kaman ansa wuqa anyanka ki shikkenan kawai sai ki sandare, ai ina jiyawa me auren Afrah wataqila ma ko sharholiya zai yi sai ta sume masa”.
DMD jin maganan Jay ya koma shirme sai ya ja guntun staki, “mtsww! Ɗan iska qanwar bayanka ma sai kayi maganan banza a kanta” yana gama faɗa ya qara gudun mota dan su isa da wuri.
Suna shigowa Ashaka suka staya Jay ya sayi wasu abubuwa a pharmacy sannan suka wuce gidan Hajja, sai da yayi parking mai kyau sannan suka fito da sallama suka tura qofan palourn suka shige, Jay da ke gaba yana kallon hanya direct kujeran da Afrah ta ke kwance a kai ya wuce yana cewa, “Autan habibty Allah yaye miki ragwanta da storo”.
DMD da ya fidda waya yana dannawa shi ma ya shigo palourn ba tare da ya ɗaga kansa ba yana tafiya sai ji kawai yayi ya buga karo da mutum, rai ɓace ya ɗago zai ga wacece a cikin yaran sai yaga wata kyakkyawan yarinya amma baƙuwa, ƙwafa yayi har zai wuce ya dawo yana kallonta jikinta na rawa ya ce “ke ƴar qauyen ina ce da ba za ki matsawa mutane a hanya ba, idiottttt!”
Duk da a hankali DMD yayi maganan amma maganan ne ya janyo hankalin duka yan palourn dan kallon shi da wa kuma ga shi ya staya a gabanta ya tare ta, malam ba wasa da sweetie sai yanzu suka tuna da Innai, ai da sauri malam ba-wasa ya ce, “afuwan DMD baƙuwace ƙawar Afrah ce.”
Jay jin ance ƙawar Afrah da sauri ya leqa dan yaganta amma kuma DMD ya tare ta basa kallonta duka, sweetie ce taje tayi hugging nasa tana basa haquri sannan ya masta, Hajja dai ƙwafa tayi ganin yanawa yarinya qarama magana kuma ba dama a masa faɗa ya ɓata rai.
Innai hawaye take yi jikinta na rawa ga shi kuma ta gaji da tsayuwa dama qafanta da maciji ya sareta ciwo yake mata, Hajja tausayi yarinyar ta bata sai ta mata alama da taxo tana faɗin “qyale mugu wanda bai san qanne ba, zo abunki kyakkyawa kaman jikokina”.
Maganan Hajja duk dariya ya basu wai kyakkyawa kaman jikokinta, Jay kam ai kuwa yana ɗaura ido akan Innai ya tabbatar ba ko kokonta ita Afrah ke nufi sai ya ji yarinyar ta burgesa, Afreen haka kawai taji kyawun Innai ya bata haushi sai ta banka mata harara tana faɗin “dukanki aka yi kike kuka da wa ya kawoki?
Hajja sheqeqe ta sheqawa Afreen kallon rashin mutunci ta ce, “tabbas ba ki da mutunci yarinyar nan, kinaga ta rako ƙawarta ba lafiya kina qara mata masifa bayan wanda shugaban masu baqin hali ya mata to wallahi ki fita harkana ko na saɓa miki, zo nan abinki ƙawar fatuna” cewar Hajja tana miqawa Innai hannu kaman wata ƴar goye.
Ita dai Innai duk storonsu ya bi ya cika ta, dan storon Hajjanma take yi jin irin masifanta kaman ya fi na Baabaa Mero, Sweedy dai duk bata ce komai ba tana zaune gefen Afrah, ita a duniya sai abu ya shafe ta take sanya baki halinta sak na DMD, sai dai itama Innai ta burgeta, sweerie kuwa ganin Innai kusan sa’arta ai taji itama ta samu ƙawa, kusa da ita ta masta ta kama hannunta tana faɗin “habibtynmu kibar kuka Afrahty za ta warke” ta ja hannunta har wajan Hajja sannan ta zaunar da ita gefen Hajja, ruwa taje ta kawo mata amma ta kasa sha har yanzu jikinta rawa yake tana hawaye, haushi da tsoron wanda ya mata faɗa ya cika ta ji take kaman ta tashi ta gudu, ganin yanayin Innai sai malam ba-wasa yaji ba daɗi DMD bai kyauta ba, Jay da ke qoqarin yiwa Afrah allura ne ya juyo suka haɗa ido da malam ba-wasa ya kyafta masa ido ɗaya suka yi magana da ido, sai duk suka danne dariyansu dan su kaɗai suka san me suka faɗa.
DMD guntun tsaki ya ja shi kaɗansa, Hajja kallonsa tayi tana faɗin “Allah ya yayemaka cutan da ke damunka, dan ko staka ma cuta ce staki garesa balle ɗan adam ɗan mutum”.
DMD ɗaga Afrah yayi ya kai ta ɗakinta ya mata allura ya sanya mata ruwa, sai lokacin ta fara sauqe ajiyan zuciya a jere a jere kaman wacce tayi gudu ko ta sha kuka, sai da ya gama komai sannan ya rage mata qarfin ac ya ja qofan ya fita, ganin har azahar yayi sai su Jay suka fice dukansu uku suka tafi masallacin anguwan bayan sun yi alwala, Afreen harara ta wurgawa Innai da batasan tanayi ba ta wuce ɗaki ta banko ƙofa, sweedy dai zama tayi bata tashi ba dan tana fashin sallah, sweerie ce ta ja hannun Innai suka shiga ɗakinsu ta nuna mata toilet akan tayi alwala amma sai Innai ta kasa sai da sweerie ta gwada mata yanda ake amfani da komai sannan tayi alwalan ta tayar da sallahn azahar nata a zaune dan zuwa lokacin stayuwan da tayi har qafafuwanta sun fara kumbura bayan ciwo da suke mata, tana idarwa tayi addu’a sai ta zuba tagumi a wajan idanuwanta na kan Afrah, tuno stawan da DMD da ta raɗawa suna da mugu ya mata shi ya sanyata qara yin hawaye tana tunanin gida da Baabaanta, ko Baabaa Mero tsakanin su mitan da take mata amma ba’a mata stawa irin haka, sai kawai ta fashe da kuka, sweetie da ta shigo ɗakin zuwa tayi tana cewa, “ƙawar Aunty masoyiya me aka miki? Kiyi haquri da Darling nasan laifinsa ne yana tafiya yana danna waya amma ya miki faɗa kiyi haquri muma haka muke fama, amma inkuka saba za ki daina jin haushinsa dan yana da daɗin zama, yanzu kizo inji Hajja” ta faɗa tana kamo hannun Innai da ta miqe da qyar sakamakon qafafuwanta da suke mata mugun ciwo, da qyar take takawa har suka iso palourn kanta a qasa dan ita ko fiskan sa bata gani ba Lokacin da ya mata stawan, har wajan Hajja sweetie taja hannunta ta zauna tana ciccije baki ji take a gaban baabaanta take ta saki kuka dan ciwon da qafafuwan ke mata.
Daga malam ba wasa har Jay duk sun kula da yanayin tafiyanta, amma Hajja sai ta riga su magana ta ce, “ƙawar fatu na menene sunanki?”
A hankali Innai ta ce, “Innai”.
Daga Jay har malam ba-wasa zaro ido suka yi jin wai sunanta Innai, DMD a zahirance hankalinsa na kan wayan amma jin ta ce Innai sai ya yastina fiska a ransa yana faɗin “village girl”.
Hajja murmushi tayi ta ce, “suna mai daɗi, amma asalin sunanki fa?”.
Nanma a yanayinta na sanyi ta furta “Maryama”.
“Ah Masha Allah! Shiyasa fatu ta ishemu da zancenki ashe sunan uwatta gareki, yayi kyau! Ke Munawwara je ki kawo mata abinci ta ci”.
Sweerie dinning ta wuce ta ɗibo mata rice and stew da yaji namomin zabbi dan abinda Hajja takeso kenan, kawowa Innai tayi Hajja ta karɓa ta ce, “Maryam sauqa qasa ki ci abinci ya shiga cikinki ko, kibar damuwan nan haka anjima kaɗan za kiga ta farfaɗo storo ne da ƙawar ta ki”.
Innai da yunwa ke cinta amma girgiza kai tayi a hankali ta ce, “na qoshi kaka”.
Hajja jin Innai ta qirata kaka sai ta ɓata fiska ta ce, “a lallai zamu ɓata inkika qara cemun kaka, yaushe nayi stufan da za’a qirani kaka, qirani Hajja yanda kowa ke cewa kamun mu ɓata, ke kuma Munawwara kai mata abincin ɗakinku ta ci acan naga kaman kunyanmu yake ji fulakon su na fulanin za tayi”.
Sweerie abincin ta ɗauka ta kai mata ɗakinsu, Hajja ta ce, “tashi kije ki ci”.
Innai a hankali ta miqe dan burinta tabar palourn kuma gidama take son tafiya duk da tafiso sai Afrah ta farka, a hankali take takawa qafan nata na rawa kaman za ta faɗi, Jay ne ya kasa haquri ya ce “Qanwata qafafuwan ciwo suke miki ne?” Bai ida haɗa leɓensa na qasa da na sama ba qafafuwan Innai suka kasa ɗaukan ta tayi ƙasa za ta faɗi, amma kamun ta qarisa Jay da malam ba wasa har rige-rigen tarota suke yi, aka ci sa’a ta faɗa jikkn Jay wanda ya ji kaman ta tabbata a jikinsa a haka, dukda zubinta na mutan qauye ne kuma gata Fulani wanda ba’a rabasu da qarnin nonon shanu, amma qamshi take yi, ɗaga ta yayi itama yayi hanyan ɗakin su Afrah da ita Hajja na mata sannu tana sawa Jay albarka, Malam ba-wasa dai fiskansa ba yabo ba fallasa shi kuma gogan naku duk da kansa na qasa amma tsaki ya ja yana furta “idiottttt”.
Hajja haɓa kawai ta kama tana ganin ikon Allah wajan DMD sai ta ce, “kai Mufaddalu dama ba ka da tausayi ba ka da imani? Kaji kunya Wallahi mai halin kafuran da kawai”.
Bai ko kalli Hajja ba ya miqe ya fice a palourn, ita kuwa Afreen kaman za tayi kuka haka ta tura baki tana hararan Hajja wai ta mata baqin-ciki tana ganin fiskan masoyinta, Hajja da ta kalli kallon da Afreen ke mata taɓe baki tayi ta dankwaleta ta ce, “tashi maza ki bisa, ai shi qanin ubanki ne dole dan na masa faɗa ki hararen, kuma yanzunnan ba anjima ba ki haɗo naki ya naki kibarmin gida ja’ira kawai”.
Afreen tashuwa tayi tana qunquni ta shige ɗakinsu, sweedy dai in matacce na magana to tayi, duk abinda ake wanda za ta iya gani ta gani wanda ba zata iya gani ba idonta na kan wayanta.
Jay a gefen Afrah itama ya kwantar da ita, yana qarewa fuskanta kallo ji yake wani abu na fisgansa game da ita amma sai ya share ya ce “me ya samu qafanki Qanwata?
Ai Innai kaman me jiran ƙiris sai ta fara kuka har da sheshsheqa, sai rararshin dole ya kama Jay da qyar ta stagaita kukan ta faɗa masa tunda maciji ya sareta qafan ke ciwo ga shi ta tsaya sosai, ruwa ya bata ta sha sannan ya ce ta lallaɓa ta sauqo ta ci abinci zai kawo mata magani ya fice a ɗakin ita kuma ta sauqo, bai wuce cokali huɗu ta ci ba ta sha ruwa ta zuba taguminta.
Hira ya samu Hajja da malam ba-wasa suna yi, nan ya faɗa musu damuwanta ya ce zai je sayo wani allura ya mata, Hajja ta basa amsa da “a dawo lafiya” malam ba-wasa ya miqe suka fice tare.
Qiran DMD ne ya shigo wayan sweedy dan dama sun sayo MTN line da Afreen, ɗauka tayi tana sallama, jin abinda ya faɗa sai ta ce, “to Darling”. ya kashe wayan a ɗaya ɓangaren ita kuma ta miqe ta fice a palourn ta nufi sashin yayyunsu mazan, da sallama ta shiga ta samesa zaune yana danna wayansa as usual.
Gaishesa tayi ya amsa sannan ya ce “ku qara haquri da addu’a Allah dawo da Ammi lafiya, gobe zan wuce Jigawa akwai abinda kuke buqata?”
“Bakomai Darling, Allah dawo da kai lafiya Allah ya bada sa’a Allah ya bayyana Ammi lafiya, amma please ka tafi da sweetie dan wallahi ko yau ita ta taimaka wajan yin lattin Afrah wai sam sai ta bita ita kuma ba yanda ta iya suka tafi ga shi taja andaketa”.
“Okay kice ta shirya anjuma zamu koma Gombe tare sai mu wuce gobe, ran Saturday zamu dawo”.
Sweedy na hamdala za’a rage mata aiki ta amsa sannan ta tashi ta fice ta barsa yana wayansa, da sallama ta shiga palourn ta iske sweetie na kan kasa fitina sai ta ce, “inji Darling ki shirya za ku tafi anguwa”, sweetie mayyar yawo har da stallen murna ta shige ɗaki wai tun yanzu za ta shirya, Hajja da harara ta bita tana faɗin “ko shan-shani ya ganki ya sara miki da son yawo, gashi kinja an zane baiwar Allah, itama dai ta ja wa kanta da kini-bibin stiya”.
Jay motan DMD suka shiga, suna tafiya suna hira da malam ba-wasa.
“Freind yarinyar nan ta haɗu iya haɗuwa ashe gaskiyan Afrah kawai fedding bottle ne mastalan” cewar Jay yana driving.
Dariya Malam ba-wasa yake yi har da na mugunta ya ce, “shegen kaya ashe qarewa ɗalibata kallo kake yi banda labari, kuma dan kai shahararren ɗan iska ne wato har da suna kasawa ‘yan biyun mata wai feeding bottle hhhh! To headquartern kuma me ka sa masa?”
Jay murmushi yayi ya ce, “wannan kuma ka jira sai na bi hanyar garin za’a sanya masa suna, iya yawan haukatani da za’a yi iya cancantan sunan da za’a sa masa”.
Dariya suka dinga yi har suka je pharmacyn suka sayo alluran suka dawo, Jay ya mata sannan har la’asar tayi, ganin haka Malam ba-wasa ya buqaci ta fito su tafi kar azo ɗaukanta bata nan, Innai kaman za tayi kuka haka ta fito tana ɗan ɗingishi dan zuwa lokacin qafan ya mata dama-dama, tanason tafiya gida amma haushi take har zata tafi Afrah bata tashi a bacci ba gashi ko da ta farka bata yi magana ba ta cigaba da bacci.
Jay ya sa Afreen ta fito su tafi, sweetie ma ta fito a shirye za ta bisu duk ɗaukanta anguwa ne kaman yanda sweedy ta faɗa mata, Hajja har compound na gidan ta rako Innai tana mata godiya sannan ta koma ciki, DMD da ke zaune mazaunin driver kallo ɗaya ya musu ya kau da kai, Jay taɓe baki yayi yana faɗin “Afreen, sweetie da habibtyn Afrah ku shiga baya, freind mu yi squatting a gaba before ku sauqa”.
Da wani mugun sauri DMD ya juyo yana wa Jay kallon bakasan me kake faɗa ba, “Mtsww! Ka faɗi abinda zai yiwu dan ba ɗuruwamin a mota za’a yi kaman cow’s ba, you better know’s the fuck you’re saying, in kuma ba za ku tafi ba nayi gaba”.
Innai storo da haushi da kuma stanan sa ne suka qara samun gurbi a zuciyarta ji take kaman ta shaqesa kowa ya huta, maimaita abinda ya faɗa take a zuciyanta “Fuck you’re saying”, qwafa ta yi a hankali tana jin kaman ta fice ta nemi abun hawa ta wuce makarantar.
Jay shima haushin DMD ya ji dan yasan maganan nasa da Innai yake yi, shi dai DMD taɓe baki yayi sai kuma a hankali kaman bai son magana ya ce, “You’re waisting my time”.
Malam ba wasa ne wannan karon yayi magana, “freind ku ɗauki Maryam ku ajiyeta a school ni zan biyo bayanku banason azo ɗaukanta a samu bata nan kar mu ja mata faɗa kaga ƙawarta ta biyo”.
Jay guntun tsaki ya ja, kamun ya ce da Afreen da sweetie su shiga motan, Innai ya duba ya ce, “habibtyn Afrah get in”.
Innai lumshe idonta tayi ta tattaro duk iya jarumtar ta da kafiyanta da taurin kanta ta kawo gaban goshi ta buɗe idon sannan cikin sanyin murya ta ce, “hamma bb(big bro) ku tafi kawai ni zan hau mashine”.
DMD jin abinda ta faɗa da sunan da ta qira Jay sai ya ja staki, shi kuwa Jay sunan daɗi ya masa har sanda ya murmusa sannan ya ce “a’a Qanwata, sai dai ku tafi da freind kar ki ɓata ba kisan hanya ba” ya faɗa yana nuni da Malam ba-wasa dan ta gane, wani ɗan iskan horn da DMD ya danna sai da hantan cikin Innai suka kaɗa idanuwanta suka kawo ƙwalla a take, malam ba-wasa cikin hanzari ya riqe hannunta suka yi gaba yana mai jin haushin abinda DMD ya musu, shi kuwa Jay rai a ɓace ya shiga motan DMD ya ja su, sunzo dai-dai su Innai ya ce, “Qanwata sai mun sake haɗuwa, kai kuma malami banson shishshigility” ya faɗa yana kallon Malam ba-wasa wanda ya fahimci me yake nufi na ya saki hannun Innai, sai kawai ya sake suka fice, motan su Jay na tafiya cikin ikon Allah su ma suka samu abin hawa, suna isa makaranta suka tarar har ɗalibai sun waste, Innai kaman za tayi kuka haka tayi rau-rau da ido, Allah ya taimaketa ta hango Rabe a can gefen wata bishiya, har wajan Rabe malam ba-wasa ya rakata ta hau ta masa sallama ya amsa yana murmushi ya ce, “Allah kai ku lafiya Maryam, kema Allah baki lafiya”.
Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yastunta ta amsa, Rabe ya ja mashine suka kama hanyan gida.

Jay tunda suka baro gidan Hajja ya ke aikin cin rai ya ɓata fiska ya qi ya cewa DMD komai, shi ma DMD ganin haka ya taɓe baki tare da ɗaga kafaɗa alaman ko a jikinsa ya cigaba da driving da mugun gudu, sweetie dai bacci ne ya ɗauketa ita kuwa Afreen aikin satan kallon DMD take yi har suka isa Gombe, Jay cikin dakewan murya ya ce “malam a asibiti za ka ajiyeni”.
Bai ce masa uffan ba ya ja su har cikin asibitin, sai da Jay ya sauqa sannan yayi reverse suka kamo hanyan gida tare da sweetie da Afreen.
Jay yana shiga ya samu har lokacin patient ɗin bai farka ba, sai ya wuce office nasa y taɓa ayyuka zuwa magrib ya kama hanyan gida.
DMD suna isa yayi parking ya sauqa, Afreen da ke baya yake jira ta fito ya kulle mota amma ya ji tana qoqarin tayar da sweetie, guntun tsaki ya ja yana faɗin “excuse me”, mastawa Afreen ta yi shi kuma ya ɗauki sweetie a kafaɗansa ya kulle motan suka yi cikin gida, ba su tarar da kowa a palourn ba sai ya wuce ɗakinsa da sweetie in ta farka ta koma wajan mummy da kanta kamun gobe su tafi.

Har bakin ƙofan gidan Baabaa Mero Rabe ya ajiyeta kaman kullum ya mata sallama sai gobe ya ja mashine ya tafi, gidan ta shige bakinta ɗauke da sallama amma shiru Baabaa Mero bata amsa ba, hanyar banɗaki ta bi da ido nan taga zanin Baabaa Mero a rataye alaman wasta ruwa take yi, ɗakin ta wuce ta cire uniform nata ta ɗau madaran shanu da ta gani mai ɗimi ta shanye tass sannan ta sanya kayan islamiyya ta fito ta tafi dan dama tayi sallah a gidan Hajja.
Baabaa Mero iyayen jimawa a banɗaki ta fito ta leqa sama ƙasa ba taga Innai ba sai uniform nata kawai, taɓe baki ta yi ta ɗauko kayan makarantan ta wanke mata ta ɗaura alwala ta shige ɗaki tana faɗin “ko kin dage da zuwa bokoko a wuta da islamiyyan wa billahillzi sai na miki aure ba ruwana kije can gidan ɗan iskan sa zai aureki ba nunu ku fama ni ya ishe, kayan makarantan ma sai ni zan wanke miki “.

Innai sai da Magrib aka tashe su, bata dawo gidan Baabaa Mero ba ta wuce gidansu tare da Hassu, suna tafiya suna hira Hassu ta ce “Adda Innai kinga nono na suna kumbura sai zafi suke mun bansan wani ciwo ne ya sameni a qirji ba, zan je na nunawa Baabaa ko Inna a shafamun magani”.
Innai murmushi ta yi ta ce, “ah lallai Hassu tamu ta fara irga dangi, kice Baffai ya fara tarun aurar da ke, karki gayawa Inna ko Baabaa za su dinga stokanarki ki bari girma za kiyi kinji” faɗin Innai tana murmushi.
“Adda Innai ai kin girmeni amma ke naki bai yi ba sai nawa kuma kice girma ne, caɓ ɗin nikam ban yarda ba ciwo ne sai na faɗawa Inna”.
Innai taɓe baki tayi ba ta ce komai ba har suka shige gidan nasu, kowa buta ya ɗauka suka yi sallah, suna idarwa Hassu ta kawo musu tuwo amma Innai taqi ci wai cikinta a ƙoshe, Hassu bata masta mata ba ta ci tuwonta ita ɗaya, tana mai da kwana kitchen ta ji Sallaman Baffai, oyoyo ta masa ya tambayeta addanta ta faɗa masa tana ɗaki sannan ya ce su yi sallahn isha’i su zo, dawowa tayi ta faɗawa innai sai suka miqe da alwalansu suka gabatar da sallahn isha’i sannan suka fito amsa qiran Baffai.
“Sannu da dawowa Baffai na” cewar Innai tana murmushi ta zauna gefen sa, Hassu ma ta zauna gefensa, amsa mata yayi da fara’a ya tambaye su ya karatu suka basa amsa lafiya sannan ya ce, “ku karanto haddanku naji”, Innai ce ta fara rera nata ya kammala sannan Hassu ta yi, duka sun iya sai ya musu ƙari, sannan ya laluɓo ƴar wayansa da ke kukan neman agaji ya kara a kunne yana faɗin, “Magaji ka isa lafiya? Ya garin? Ya hanya? To a mayar da hankali, Allah ya taimaka”, duk amsa masa Magaji yayi sannan Baffai ya bawa Innai wayan suka gaisa, magaji na ƙara ja mata kunne akan makaranta, Hassu ta miqawa wayan ita ma suka gaisa sannan ta miqe ta kai wa Inna A’i suka gaisa ta kai wa Mama Lami ita ma suka gaisa sai ta dawo wa Baffai da wayansa, Baffai amsa yayi yana murmushi ya kara a kunne ya ce, “To Magaji a mayar da hankali ko, sai gobe zan haɗa ka da Baabaa, yanzuma haka karatun nake dubawa qannenka, to Allah muku albarka sai da safe”.
Baffai ya ce, “dada Baffai mako noi ɓandu?”
“Alhamdulillahi Baffai, qafana yayi sauqi”.
“To Allah qara sauqi, yau naje rugan tudu matar nan ta ce na gaisheki yau she za kije za ta koma zuwa juma’a in aka kunce maganin ƙafan nata ta fara takawa”.
Innai tura baki tayi, dan bata mance a hanyan ne ta haɗu da stautsayin maciji ba, a hankali ta ce, “Baffai min kam mi yahai(ni ba zanje ba)”.
Murmushi Baffai ya kuma yi jin abinda ta faɗa sannan ya ce “shikkenan ni zan faɗa mata hakan kince ba za kije gaisheta ba”.
Innai langwaɓe kai tayi ta ce, “Baffai ni faɗa bance haka ba”.
Hira ya dinga yi da yaran nasa da Hassu da Innai har ganin dare yayi sannan ya sanya musu albarka ya ce duk suje su kwanta, Innai a bakin qofan Inna ta tsaya bata shiga ciki ba ta mata sai da safe, haka mama Lami ma, Hassu za ta rakata amma ta hanata ta ma Baffai sallama ta fice da gudu ba birki har sai da ta shiga gidan Baabaa Mero tana faɗin “wayyo sun biyo ni”.
Baabaa Mero da ke qoqarin shumfiɗa tabarmanta jin abinda Innai ta faɗa da kuma gudun da tayi sai ita ma ta rufa mata baya ta shige ɗakin ta banko ƙofa tana zare ido, a hankali ta ce, “Ta tabbata ni Meramu na shiga ɗaki na kasa fita, yanzu ke takwara wani sallau sallamammen ne ya biyo ki haka kaman ana gudun fanfalaƙi, dubeni fa ragaja-ragaja har da ‘yar lalitan dukiya ta na jefar dan storo, kai amma da na Kama wanda ya biyoki sai na sassake masa goshi ko bai da shi dan mai anguwan qauyensu, dan tsaban jaraba stoston bente da ya biyoki me zai miki?” Cewar baabaa da ke zaro ido tana haƙi.
Innai faɗawa kan gadon Baabaa mai rumfa tayi tana dariya har da hawaye jin surutun Baabaa wai kaman gudun fanfalaƙi, hhh!.
Baabaa Mero a harzuƙe ta ce, “takwara ina magana kina dariya dan rashin imani kina ga har da doka ɗan gangariyan qugu na nayi da ruɓaɓɓen ƙofan qyauren nan, kar dai kice mun tijaranki ne ya mosta kika sa ni gudu kaman ana yaqin biyafara na biyu dan uwaki Indo”.
Innai dariya ta cigaba da yi tana kama cikinta dan har ya fara murɗanta saboda dariyan, Baabaa Mero ai kaman za ta fashe haka ta cika ta iyo kan Innai tana faɗin “babu ko shakka kin mai da ni mai stintar leda a bola, amma ni ko zan kirɓaki kaman tuwan takwara(sakwara) a turmi in baki faɗan gaskiya ba”.

09161720046
Uwar batoorl taku 🤝❤️😁

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button