Sponsored Links
Duk Karfin Izzata Book 1Hausa NovelsHausa Novels and Love Stories

Duk karfin Izzata Book 1 Paga 4

Sponsored Links

Episode 4*

YOLA

Almost 11 na dare hiyana na waje tana neman diyana amma shiru shiru ba diyana ba lbrn’ta hiyana tayi kuka har ta godewa Allah kamar zatayi hauka, ta juyo ta dawo gida jiki a sake ba kwari, yanzu tama daina jin yinwar da takeji burin ta kawai taga ƴar uwar’ta
tana shiga gida ɗakin su tanufa kwanche tasamu lamrat da amrat manne da juna sunyi barchi, ga hawaye nan abushe a fuskar su da’alama sunyi kukan yinwa har sun gajine barchi ya dauke su
zama tayi akasa kusa dasu su,ta zuba musu blue eyes nata, wasu siraran hawayen takai’ci nabin kunchinta duniyar tunanin inda diyana take tafaɗa, kamar daga sama taji an bude kofar zanan ɗakin nasu an shigo, zubur tamike tana kallan sa ɗauke yake da wani abu a’kafadarsa kamar mutun hasken fitilar baya haska su sosai shiyasa bata gane me yake ɗauke dashi ba, murya na rawa “tace yaya bello kaine, kasa kasa bello yafa magana “eh nine kana ya raɓa ta gefen su lamrat ya kwantar da diyana, a ruɗe hiyana tace “yaya bello me yasame’ta’? aina kagan’ta? Ta mutune’? Naga bata numfashi
“hiyana kinitsu mana bata mutu ba suma tayi, kinga yanzu dare yayi zanje gida da safe in kunzo ɗeban ruwa saimuyi magana,in bahaka ba kinsan idan inna ta ganni to nashiga uku, dan haka kiyi shiru karma taji wani motsi, yana gama faɗin haka yajuya ya fiche daga ɗakin
itakuwa hiyana ta gyara zaman ta, tana kallan fuskar diyana tana kuka, haka ta kwana kamar yadda taga rana haka taga dare

washe gari tun asuba inna ta shigo ɗakin nasu hannu ta riƙe da tulu mai ɗauke da ruwa da karfi ta zubawa diyana nan take diyana ta farfaɗo tana ihu, inna bata bi ta kanta ba ta juya ta zubawa amrat da lamrat a razane suma suka farka, juyawa inna tayi ta zuba sauran ruwan a awajen Kwan chiyar hiyana a tunanin ta hiyana na ɗakin,Amma sai taga akasin haka ba hiyana a wajen a fusache ta juyo gun su diyana zatayi magana taji diyana na sambatu, tana faɗin “dan girman allah buba ka kyale ni kayi kahuri, wayyo allah hiyana ta ina kike kizo ki chech..bata karisa maganar ba taji saukar duka ta ko ina ajikin ta, ihu diyana ta fasa wayyo Allah na shiga uku hiyana kizo ki tai makeni buba zai kashe ni, wani bugu inna ta kai mata a baki sai da bakin nata ya fashe, ihu a zaba diyana ta saki, shake mata wuya inna tayi tana faɗin “me buba na yamiki da za kiche ya kyale ki, ko kinga buba a nan ne eh, kodai wani mugun abun kuke shirya masa, jin maganar inna yasa diyana ta dawo chikin hayyachin ta, da kyar ta iya faɗin “inna kiyi hakuri zan mutu dan Allah ki sake min wuya, naushi inna ta sake kai mata a baki tana faɗin “ki mutu mana ina ruwana daman uban me kuke tsinanamin a gd ba gara ku mutu kowa ya huta ba, kara shake diyana inna tayi sosai sai dataga blue eyes nata sun fir fito waje sosai tana kokarin mutuwa da gaske,da sauri ta sake ta tana mai da numfashi, juyawa tayi tana kallon amrat da lamrat in da suka takure waje guda suna hawaye chikin tsawa tace “ke lamrat kitashi kije ki ɗoramin girki idan kin gama kizo kitafi talla, ke kuma amrat ki wuche kije kimin wankin kayana kiyi shara da wanke wanke, itakuma wan nan shai ɗaniyar ni zata sa na zubar da ruwa a kasa koh to wlh gaba ɗaya ruwan gidan nan sai na zubar dashi ku ɗebo wani, ke diyana ki tashi ki ɗauki kofin ki nemo wan nan shai ɗaniyar kufara ɗebomin ruwa kuma wlh daga nan zuwa karfe 10 ku chika komai na gd nan, dan dole yau ku jemin tallah ba zanyi asara ba, tana gama faɗin hakan,
ta juya tayi nufi hanyar fita har ta kai bakin kofa sai kuma tace wlh idan kuka bari na kai tsakar gd baku fito ba na lahira sai yafi ku jin daɗi, jiki ba kwari lamrat da amrat suka mike suka fice suka bar diyana kwanche baki na jini sai kuka mara sauti dake

Inna na fitowa tayi karo da hiyana a tsakar gida hannun ta rike da cup guda biyu da alama ruwa take ɗebowa “ke ni zakiwa iskanchi to wlh barikiji duk ruwan dake gidan nan saina zubar dashi a kasa kun ɗebo wani, san nan kuma ke kafin kifara zubawa a randu nan nan, sai kinyi sahu 10 kina ɗebowa kina zubar wa a kasa har sau 10 tukun nan, kifara zubawa a tulu, ni zakisa nayi a sara ruwa ba nashiga ɗaki zan tashe ki ashe ba kinan ki kasani na zubar da ruwa a kasa koh, ke gaki mai wayau tun asuba kintafi ɗebo ruwa, kuma barikiji duk yadda zakuyi kuyi nan da karfe 10 dole kuchika ko ina na gidan, nan san nan ku jemin talla dan yau bazanyi asaraba, tana kaiwa nan ta wuche tanufi kichen, tafara zubar da ruwan dake chikin randu nan da kuma tulu nan,sai da ta tabbatar babu wani tulun daya yage da ruwa a chikin sa san nan tafito tawuche ɗakin ta ta haye gado, babusallar asuba
Dur kushewa kasa hiyana tayi ta rushe da matsanan chin kuka, mai tsuma zuchiyar mai sauraro, kuka take kamar ranta zai fita sai datayi kukan, mai isar ta san nan ta ɗago kai tana kallan su amra dake tsaye a bakin kofar dakin su, alama ta musu da hannu aka sutafi sufara aikin su kar inna tafito ta gansu, ganin babu diyana a wajen ne na yasa ta mike da kyar tanufi ɗaki dan tadubo ta

Kwanche ta samu diyana sai kuka take “ita chikin muryan kuma tace diyana kitashi mutafi mu fara aikin mu tafaɗi hakan chikin shasshakar kuka “wlh hiyana bazan iya tashiba jinake kamar zan mutu chikina murdamin yake saboda yinwa “to diyana ya zamuyi kinsan dai in kika zauna inna ta dazo ta sameki duka zata kara Miki, kitashi muje saiki zauna a gonar yaya bello ni kuma na ɗebo ruwan “to zoki rikeni natashi, matsowa hiyana tayi ta kama kafaɗarata, ta tai maka mata tamike har tangal tangal take kamar zata faɗi da kyar ta tsaya a kan kafafunta aruɗe hiyana tace “diyana yanaga jini a jikin zanin ki wai ma ina ki kaje jiya
“a tsorache diyana tafara magana hiyana bansan ya akayi naga jininba nima, daga gabana ya fito
shiru hiyana ta ɗanyi kafin tace to chanza kaya muje, zamuyi magana a hanya dan in muka tsaya magana a nan inna zatazo ta same mu, da sauri ta ɗauko wa diyana wani tsunmar zanin atampa yasha ruwa duk ya koɗe ta ɗaura mata, tariko hannun ta
da kyar diyana ke ɗaga kafa da kyar take ɗin gisa kafar tana tafiya suka fito tsakar gida, suka samu su amrat kowache takama aikin ta, amma kallo ɗaya zaka musu kasan suna chikin tashin hankali ga yinwa duk sun galabaita, girgiza kai kawai hiyana tayi, ta duƙa ta ɗauki cups ɗin data ajiye suka nufi waje

Suna futa hiyana tafara tambayar diyana “ina kikaje jiya diyana “jiya na kwantane awajen da kika barni sai barchi ya ɗauke ni ina chikin barchi kawai sainaji a’na kokarin chiremin zani, nabuɗe idona a razane sainaga bubane, da nayi kokarin guduwa shine yakamani ya wanka min mari, kuma yasa kafa ya takamin wuya ya chiremin zani, inata rokansa da ya kyaleni amma yaki da kyar na samu na laluɓi wani karfe nabuga masa a kafa, shine yachire kafarsa a wuyata yafaɗi kasa ni kuma natashi da kyar zan gudu kawai naji ya bugamin wani abu a kai daga nan kuma ban sake sanin komai ba saida inna ta zuba mana ruwa ɗazun ta kare maganar chikin shesshekar kuka “to ae na ki kasamu jinin jikin kin nan kuma “nifa hiyana nache miki ban’saniba kawai ganinsa nayi ” jinjina kai hiyana tayi tana faɗin yazama wajibi muneman wa kammu mafita wlh ” to yanzu ya zamuyi ke nan tayi maganar dai dai lokachin dasuka isa bakin rafin”hiyana tace ki bari inmun samu lokachi iri idan inna bata nan sai muje muyi magana da bappa, yanzu dai ki ɗebo ruwa ki wanke jinin jikin ki nan, san nan muyi al’wala kinsan jiyama bamuyi sallar azhar laasar mangariba da kuma issha ba, gashi yan zu kuma ana sallar asuba sai muhaɗa dukka,muje kasar itachen chan mubiya bashin sallolin kafin mufara ɗiban ruwa “to kawai diyana tace san nan tanufi bakin rafin ta ɗebo ruwa ta koma gefe ta wanke jikinta tas san nan sukayi al’wala suka nufi kar’kashi bishiyar mangoron suka shinfiɗa ɗan kwalin su suka ta da sallah,
sai da suka biyan bashin sallar da akebin su, najiya san nan sukayi sallah asuba

addua hiyana tai sosai” ya allah kayafewasu amra ba laifin su bane innache kehanasu yin sallah Allah mun’tuba haɗa sallah da muke Allah kayafe mana
diyana kuwa adduar Allah yakawo musu mafita take hakadai suka gama adduar san nan su kamike ” hiyana tanufi bakin rafi tana faɗin diyana kishiga gonar yaya bello ki zauna ki huta, ruwa ta ɗeba a cups ɗin ta kama hanyar gd, ta kuma diyana tashiga chikin gonar yaya bello ta zauna da yake gonar a bakin rafin yake daga chikin gonar kana iya kallan chikin rafin

har karfe 8 na safe diyana na zaune a chikin gonar bello, hiyana kuwa saifaman jidan ruwa take ammafa da cups yan zuma taɗebo ruwan takama hanyar gida tanajan kafarta da kyar da kyar har takai kusa da gida zata shiga ke nan, buba ya tare mata gaba ɗaure fuska hiyana tayi sosai” babu kabani hanya
hannu buba yasa ya buge cups ɗin dake hannunta yafaɗi kasa ruwan yazube, hiyana kamar zatayi kuka ta duka kasa ta ɗauki cups din har kwallah yafara zuba a idan ta batachewa buba ko kalaba takama hanya tajuya tanufi hanyar komawa rafin, tana tafiya wasu siraran hawayene masu dumin gaske ke zuba mata a’kan kunchin ta.

haka takoma rafin tasake debo ruwan tajuyo ta zata tafi ke nan taga diyana a tsaya a bayan ta “hiyana kawo in karɓa miki kekuma kije ki huta tunda tun asuba kike deban ruwan nan “aa diyana kingafa ke baki da lfy dan haka kije ki zauna kibari zanyi “diyana tace aa to kawo nayi ko sahu 10 ne sai ki karba ” sahu 10 yayi yawa diyana ki daiyi 3 “to bani cups din, mikama ta cups ɗin hiyana tayi, tawuche tanufi chikin gonar yaya bello
diyana kuma tanufi hanyar gida kodataje itama zata shiga gida buba tagani tsaye a bakin kofar gidan su batache masa ko sannuba tazo taraba gefen’sa zata wuche, buba ba tsoran Allah yasa hannun sa yasake buge cups din ruwan da diyana take da shi suka faɗi kasa ruwan ya zuɓe “a fusache diyana ta ɗago zatayi magana kome ta tuna kuma sai tafasa ta duƙa ta ɗauki cups din tajuya takama hanyar komawa rafin, buba kuwa yana ganin ta tafi yayi murmushi mugun ta cheke da izza da iya shege yafara magana,”ai kunshiga uku dani wlh bazan taba bari ku zauna lfy ba, narinka kuntata muku san nan kuma in na Auri hiyana in maida ta baiwar kowa na kauyen nan,dariya yayi sosai san nan ya chigaba da chewa kai amma goggo habiba ma yar aljanna che wlh ta iya horaku ɗeban ruwa da kofi ai shine maganin ku, a hakanma nikuma ba barin ku zanyiba, narinƙa addaban rayuwar ku kenan ina kifar da ruwan, yau sai kafarku ta daina takawa yasake kwashe wa da dariya kamar mahaukachi

diyana kuwa juyawa tai komawa rafin ta taɗebo wani ruwan tanufo gida, ko datazo kofar gida ba’tasami buba’ba ba’karamin daɗi tajiba alhllh ta furta san nan tanufi gidan zata shiga, kamar daga sama taji an buge cups ɗin hannunta sun faɗi kasa ruwan yazube
a fusache ta ɗago ganin bubane a gabanta hakan yasa tarufe ido ta zabga masa mari a kumatu
diyana daman bata da hakurin jure wulakanchi

buba kuwa bai’yi wata wata ba ya kwashe kafafunta tafaɗi kasa kanta ya bugu da jikin wani dutse dake bakin kofar gidan, wani ihu azaba ta sake, buba kuwa bai tau saya mata ba ya hau bugunta kamar ai aikoshi
diyana sai ihu take ganin zai mata illa babu wanda yakawo mata agaji yasa tamike da kyar tana kokarin guduwa
damkoh hijabinta yayi tabaya ya shake mata wuya ya bugata da kasa wani azaba taji gashi yaki sakin hijabin nata ga wuyan’ta a shake da gyar take numfashi ,tagama sad’dakkarwa mutuwa zatayi sae kuma taji buba yayi ihu kuma ya saketa “da kyar ta iya buɗe ido ta sauke su a kan yaya bello dake tsaye rike da sandar kiwo,sai huchi yake kamar wani zaki, ga buba kuma sume a kasa
hannu yaya bello yasa ya ɗauke ta chak ya saɓata a kafaɗarsa yanufi hanyar rafin da ita, nan sukabar buba kwanche, bello irin mazan nanne masu karfi gashi dogo sosai kakkarfa

kai tsaye gonarsa yanufa da ita hiyana na zaune taga yaya bello ɗauke da diyana a kafadarsa
da sauri tamike tanufi’sa tana faɗin hande miboni yaya bello me kuma yasame’ta bello bai yi magana ba sai da ya isa wajen dayake zama inyazo gonar, wajen shinfiɗe yake da katifar chiyawa, akai ya kwantar da diyana da sauri hiyana ta karisa wajen ta zauna a kusa da diyana, tana fadin “diyana me yasame’ki waya bugeki waya pasa maki baki “hiyana kiyi shiru mana ki kyale’ta ta ɗan huta tun da kika gammu tare ai koma me yafaru zakiji chewar bello” hiyana dai hankalin ta bai kwantaba mikewa bello yayi yana faɗin ina zuwa san nan yakama hanyar fita daga gonar

hiyana na ganin yaya bello ya tafi, ta matso kusa da diyana ta rike hannun’ta murya na rawa tafara magana “diyana meyasame’ki, chikin sarƙewar murya diyana tache “buba ne ya bugeni, dafe kai hiyana tayi tana faɗin “diyana banache duk abun da buba zai miki kirinka hakuriba, ae’nafaɗa miki koma me kika masa a kan mu abun zai sake dawowa tun da mudai bamu da gata, bamu da mai tare mana fada ki dubafa kigani gaba ɗaya kauyen nan gudun’mu suke saboda kalar idon’mu, kinsa ni wasuma har mayu suke chemana, wai idon’mu ba irin na mutane bane irin na mayune bawanda yake kusantar mu kowa wai tsoro muke bashi, duk kauyen nan yaya bello ne kawai mai tausaya mana sai bappa, su biyu suka rage mana amma duk da kinsan da haka sai kije kirinka biyewa buba kina jawa kanki wata masifar koh
hiyana zata sake magana kenan idanta ya sauka a kan jinin dake jikin zanin diyana,a ɗan razane tace “diyana wai wan nan jinin kam na menene haka, chikin dashe war murya diyana tache “nima wlh ban saniba tunfa dana tashi yau da safe naketa ganin jinin yana fitowa yaki dai nawa, girgiza kai hiyana tayi tana faɗin “kuma kin duba bakiji chiwo’ba “ni banji wani chiwo’ba, shiru hiyana tayi tana tunanin a dai iya karatun da bappa ya koyamu’su tabbas yataɓa faɗa musu idan mace tafara girma to zata fara jinin haila, to ke nan wan nan shine, to idan koh hakane ae no yakamata nafara jinin ba diyana ba, tun da ni che babba amma yau zanje na tambayi bappa gaskiya dan muji wan nan jinin na lfy tayi nisa chikin tu naninta
sae’ taji muryan yaya bello yana faɗin tashi kuchi abinchi, dawo da kallanta kan’sa hiyana tai yana rike da samira rufe da pai pai, a dayan hannun’sa kuwa kwaryar nono ne, ajiye musu yayi yana faɗin “kutashi kuchi dawuri “yaya bello bazan’mu iya chin abinchin nan,mu barsu amrat ba, basu chi komai bafa tun jiya da safe hiyana tayi maganar kamar zatayi kuka,yaya bello yace “hiyana karki damu kuchi kinji zanje in sayo muku rogo a dan dali sae’ ku ɓoye ku kai musu yana gama faɗin hakan ya ɗau fatan yar’sa yanufi wajen da yake shuki, hiyana ta miƙe,ta kama hannun diyana ta tai maka mata ta miƙe zaune, san nan ta jawo musu samiran Abinchin gaban su ta buɗeq, ɗumamen duwon dawane mai kyau da miyar kuɓewa yaji man shanu gashi sai tiriri, yake kuma da yawa dan yakusa chika samiran nan fa sukafara chi, hannu baka hannu kwarya, saida suka chinye tas san nan suka jawo kwaryar nonon ma suka shanye, hiyana tamike ta ɗauki samiran da kwaryar nono ta nufi rafin ta wanke’su san nan ta debi ruwa a chikin kwaryar tash takuma kawowa diyana

wai shin wanene bello?

Bello dai dashi da buba babansu daya mamane daban daban baban su buba kuwa yaya inna habibache inna habiba kishiyar mamansu diyana bello yana da mata yayi aure kuma a chikin gidansu yake zaune da matar tasa shiyasa duk taimakon da zaiyiwa su diyana yakeyi a boye dan indai yabari inna habiba tasani to wlh sharri zata masa tache yana nemansune ta haddasa masa masifa tsakaninsa da matarsa shikuma yana matikar tau saya musune shiyasa yake tallafa musu wan nan takai checchen wanene bello ke nan

hiyana ta kawowa diyana ruwan ansa diyana tayi tasha san nan hiyana ta dubi diyana tache to barinaje na chigaba da ɗeban ruwan “aa mutafi tare dai dan yanzukam nasamu karfi ae “to muje jerawa sukayi har inda bello ke noma sukaje, suka masa godiya tare da sallama, to bello yace san nan yaɗora da chewa “an jima zan kawo muku rogon bari na gama noma naje dan dali ya sawo muku koh sai kubawa su amrat ɗin “to yaya bello mun gode sosai hiyana tafaɗa tana kamo hannun diyana har sun juya zasu tafi hiyana takuma juyo tache yaya bello wai dan allah me buba yayiwa diyana jiyane naga jikin’ta sai jini yake

Shiru bello ya ɗanyi kamar mai tunanin wani abu, a nitse yafara magana babu abun da yama’ta dayaso yama’ta fyaɗe’ne sai kuma Allah ya tsare najiyo ihun’ta shine naje na kwache’ta, amma lokachin dana shiga ɗakin buban, dai dai lokachin yabuga mata sandar’sa a kai shiyasa kikaga tasuma, batun jini kuma ina ganin girmane yazo mata amma kuje gida zansan abunyi a kai hiyana tace “yaya bello menene kuma fyaɗe “shikenan ku daije gida ba sai anmiki dalla dalla ba, chewar bello
Jiki ba kwari suka’nufi rafin suka ɗebi ruwa a kofu nan suka wuche gida da sallama suka shiga gida inna na tsakar gida tana ƙirgawa lamrat robobin nonon dazata tafi talla dasu a tsiyache innar ta ɗago tana kallan’su ” kuzo ku ajiye kofin, ku ɗauki tallar nan kuje ku sayarmin idan kun dawo ko da dad darene kwa karasa ɗiban ruwan “da sauri sukaje suka ajiye cups ɗin a kichin, suka fito suka dawo gaban ta suka tsugun na

Kirga musu nonon inna tayi tana gamawa ta fara musu kashe di, “wlh ko kwana zakuyi a chan ku kwana amma karku dawo baku sayar da nonon nanba
to kawai suka che mata san nan suka ɗauki tallar kowa da nata kwaryar suka nufi hanyar fita daga gidan suna masu tau’sayawa amrat dan kuwa yanzu duk aikin gidan nan ita kaɗai zatayi innalillahi wa inna ilaihir rajiun suna fita “diyana ta dubi hiyana tafara Magana wai yanzu yazamuyi ne kinfasan mu ba’a sayan faran’mu, dan chemana suke mayu ajiyar zuchiya hiyana ta sauƙe kafin tace “Allah na tare damu ai, muje kekam muyi addua,
kai tsaye dandali suka nufa dukkan’su uku diyana hiyana lamrat sukabar amrat a gida daman ita amrat ba’a ɗora mata talla sai dai aikin gida kawai inna ke kasheta dashi
suna zuwa kowa ta ajiye kwaryar nonon ta nan take mutanen wajen suka fara matsawa nesa dasu, sudai ko ajikin su dan in da sabo sun saba zaman’su sukayi shiru bawanda yache dawani kala a chikin’su
wani

Wani katon mutunne mummuna baki yazo wajen dasu diyana ke zaune ko sallama bai yiba ya dubi diyana yace ke ki dama min fura da nono na naira 100 ki kawo min masauki na, ya karisa maganar yana nuna mata hanya da masaukin nashi yake “nifa bansan wajen masaukin naka ba diyana tabashi amsa “dakin fita daga dan dalin nan kika ɗan yi kwanar hagu zakiga wata bukka to nanne wajen nawa “to zan kawo ma chewar diyana, juyawa yayi yabar tafi,
Hiyana ta dubi diyana dake kokarin dama nono a kwarya dan ta damawa mutumin tache “aa diyana wlh bazaki kai masaba’ nifa tunda nake zuwa dan dalin nan ban taɓaganin mutumin nan ba kai ni ko sau ɗaya ma ba a dan dalin kawaiba koma aina ban taba ganin’saba
Girgiza kai diyana tayi tana faɗin aa hiyana kibari nakai masa in bahakaba Kinsan dai bamai sayan fura da nono mu ko “to shike nan diyana kije,ki kai masa amma kiyi addua dan wlh in tsoran, karya sacheki kinga ba sanin sa mukayiba a diyana ta amsa da “to tafara dama furan

bajimawa tagama dama furan ta ɗauka tanufi inda mutumin ya nuna mata, a bakin kofar bukkan nasa ta tsaya ta masa sallama, yana daga chikin dakin ya amsa sallamar tare da faɗin “ki shigo mana, diyana ba musu ta shiga a zaune ta’sameshi a tsakiyar ɗakin, gabansa taje ta ɗuka ta ajiye masa damammi yar furan a gaban sa, tana faɗin a ban kuɗin murmushi yayi ya ɗago jajayen idon’sa yana kallan ta “yarinya mai kyau kinasan kuɗi koh, diyana zatayi magana sai taji ya riko hannun’ta yachi gaba da faɗin “ni zan baki kuɗi dayawa in kinaso ya kai karshen maganar, yana kokarin rungumar’ta
Da karfi diyana ta ture’sa tamike da gudu ta nufi waje, tana waige waige ko mutumin yana binta, a dai dai bakin kofar ta waje tayi karo da bello, baya tayi zata faɗi da sauri bello ya riko kafaɗar ta yana kallon chikin idon tana yana faɗin lfy diyana ita kuwa sai waige waige take, murya na rawa tache “yaya bello wlh shine ya kamamin hannu wai zai bani kuɗi
A’fusache bello yache “ae daman bayan’ki nabiyo, yanzu zuwa’na dan dali na tambayi hiyana ina kike shine fadamin kinzo kawo wa wani nono, yanzu dai ki koma dan dali ina zuwa yayi maganar tare da sakin kafaɗar ta
Da gudu diyana tawuche tanufi dandali, shi kuma bello yanufi chikin ɗakin mutumin zaune ya samesa yana shan furan da diyana ta kawo wani kallan banza bello ya bishi dashi daga sama har kasa kafin yache malam wanene kai ” mutumin yaɗago kai daniyar yayiwa bello rashin mutunchi sai kuma yaga bello chikakken namiji’ne mai ji da karfi dan ko faɗa zasuyi bello zai masa dukan mutu, dan haka sae yanitsu chikin girmama’wa yace “ni bakoh ne rai a ɓache bello yafara magana “eh ae nasan kai bako ne tun da ban taɓa ganinka a nan ba chewa nai daga ina kake, kuma meyakawo ka garin nan shiru ya ɗanyi kafin yache “daga kauyen tongo nake kuma hanyache tabi dani tanan na tsayane dan na hutane, idan na huta sai nachigaba da tafiya “shine zaka lalata mana yara bello yayi tambayar chikin tsawa, shiru mutumin yayi
Yaya Bello ya chigaba da chewa aradun Allah idan kasake yiwa ɗaya daga chikin kannena magana wlh sae dai a ɗau gawarka murya na rawa mutumin yace “kayi hakuri bazan sakeba, bello bai sake magana ba yasa kai yafeche daga dakin a fusache,

wajen su diyana yanufa,suna zaune suna yar hirar’su bello yazo kusa dasu kamar mai sayan nono kasa kasa yafara magana “duk wanda ba zai sayi nono a nan ba sai dai abari, karku kuskura ku sake kai ma wani sai dai ya hakura san nan kuma ki damamin fura da nono na 100, da sauri hiyana ta bude kwaryar nono ta ɗauko roba biyu ta juyesu a chikin wani dan karamin kwarya tasa fura biyu ta dau ludayi tafa damawa, tagama ta juye masa a leda ta mika masa,hannu yasa ya ansa, yasa ɗayan hannun sa a aljihun ya chiro kuɗi naira 500 ya juya gabas da yamma dan yaga akoi mai kallan sane ko babu, dan bai san inna tasani, mikawa hiyana kuɗin yayi, Kin ansa tayi, tana girgiza masa kai alamar ya bar kuɗin kawai, kan pai pan dasuka rufe kwaryan nono ya ajiye musu kuɗin kasa kasa yache kichere 100 na nono kibawa inna, sauran 400 kisaya muku rogon 100 ki ajiye 300 kuma zai muku am fani gobe, bai jira amsar suba yajuya da sauri, dan ya lura hankalin mutane yafara dawowa kansu kar wata matsalar tazo tafaru

wuni zumbur su hiyana sukayi awajen ban da bello daya saya nonon bawan da yasake saya, shima mutumin da diyana ta kai wa nono bai basu kuɗin ba, haka sukayita zama da nono har karfe 6 na yamma, san nan hiyana ta miƙe tana faɗin kutashi mutafi gida, mikewa diyana da lamrat sukayi suka ɗauki kwaryar nono suka ɗora akansu suka kama hanyar gida
Suna tafiya ne diyana tache “wai lamrat waya saye furan ki na jiyane lamrat tace “ae dayake kinga jiya kasuwane akoi baki,ni kuma kinga ai idona ba irin naku bane ba wanda yake chemin mayya shiyasa bakin suka rinka sayan nonon
Hiyana ta girgiza kai tana faɗin “ae kema da idon ki yayi irin namu babu wan da zai saya koda bakin nema, suma chewa zasuyi ke mayya che
Diyana tache “yanzu ya zamuyi da inna, ɗaure fuska hiyana tayi tana faɗin “ya zamuyi kuwa dukane dai kamar yadda muka saba shi zamusha “Allah kakawo mana mafita chewar diyana, dukkan su suka amsa da ameen

Da sallama suka shiga gidan sai faman rakuɓe rakuɓe suke, muryan inna che ta daki dodon kunnen su daga ɗaki, tana faɗin “ae shiyasa nakesan hiyana ta Auri buban kinga ita hanyar mutuwar ta mai sauki ne, sukuma sauran zamusan yadda zamuyi dasu
amma bazamuyi kisa a chikin gidan nan ba dan kinsan al adar kauyen nan, amma na chi al’washin duk dabbobin nan nine zan gajesu wlh dukkan’su nizan zama sanadiyar mutuwar su , wata murya mara daɗin ji sukajiyo daga chikin ɗakin inna tana faɗin “ae wahalar da kike ba suma habiba am zata iya zama ajalin su, Wani dariya inna tayi san nan tace ae yanzu ma kara nin’ka musu wahalar zanyi, kuma sati nan mai zuwa za’a ɗaura Auren buba da shigiyar nan .

Baya baya sukayi suka fita daga gidan suna fita suka rushe da kuka,suna kuka suna tafiya har suka isa kasan itachen mangoro dake ɗan bayan gidan su zama sukayi awajen,suka sauke kwaryan nono dake kansu suka chi gaba da kukan su, sai da sukayi kukan mai isarsu san nan sukayi shiru dan kan su, dan duk chikin su ba mai rarrashin dan uwansa

Suna zaune awajen har aka kira sallar mangariba, tukun nan suka mike, suka ɗauki kwaryar nono jiki ba kwari suka nufi gida ko da suka shiga, a tsakar gidan suka samu inna jiki a sanyaye suka karasa chiki gaban ta sukaje suka tsugun na, suka sauke kwaryar,sukayi jugum jugum gwanin ban tausayi suna jiran hukunchi, inna naganin haka tagane basu sayar ba miƙewa tayi tanufi ɗaki ta dauko wani katan bulala tafito, tafara bugun su dashi
Diyana da hiyana suka hadu suka rufe lamrat bulala na sauka ajikin su, bugun su inna take baji ba gani abun tun suna iya kuka ma har kukan nasu ya daina fita duk sai da tamusu ruɗu ruɗu da jiki, ta kyale su ta kuma fiche daga gidan tana ta mai da numfashi, Amrat na ganin inna ta fita, itama tafito daga ɗakin bappa tayo wajen su da gudu tana kuka haka suka haɗu a tsakar gida suka rungumi juna sunata kuka, sai da sukayi kuka mai isar su
San nan su kamike jikin dukkan su jikin su sai karman yinwa da wahala yake, suka nufi dakin bappa da sallama suka shiga amma bai amsa musu ba, akusa dashi suka zauna yana kwanche idon sa Abuɗe yana kallan sama
chikin shesshekar kuka hiyana tace “bappa ina wuni shiru bai amsa ba ” bappa bakada lfy ne diyana ta tambaya a ruɗe, nan ma shiru bai amsa ba Hiyana tasa hannu ta taɓa shi ko motsi bai yiba a firgiche tafara jijjigasa tana ihu tana kiran sunansa Amma shiru
Chikin kiɗima hiyana tafito daga ɗakin tayi waje tana ihu

 

London United Kingdom

Tsaye yake a tsakiyar babban palon su hannun’sa ɗaya na rike da trolley ɗayan hannun kuma yana rike da wayarsa yana latsawa, sanye yake chikin black jeans da blue t-shirt ya rage tsawon gashin kansa, yanzu gashin bata wuche zuwa iya wuyar’sa ba, yana sanye da booth black colour a kafarsa dakuma p-cap shima baki hannun sa na ɗaure da wani haɗadɗen agogon daimon mai kyau da tsada fiskar nan kuwa babu alamar annuri akanta a taure take tam kamar an aiko masa da sakon mutuwa amma yayi kyau sosai laɓɓansan nan kuwa kamar yasa jan baki jaa sosai ga sajen sa a kwanche yasha gyara bakaramin kyau yayiba, faffaɗar kirjin san nan kuwa a tsaye dam dam kamar zai fashe ga damtsen hannun sa a chike kamar zasu yaga hannun rikar, almost 10mnt yana tsaye

A hankali Aryan ke sauko daga saman stair ɗin shima shigarsa iri ɗaya dana DON abun mamaki shima ya yanke gashin kansa ya rage mata tsawo, rike da trolley shima yana ja sauko wa yayi yazo dai dai inda DON ke tsaye, da wan nan sexy voice nashin ya furta sorry bro,DON bai tanka saba yaja trolley sa yanufi kofar fita, da sauri Aryan yabi bayan sa sukayi waje tare, da gudu rundunar jibga jibgan sojojin masu ji da lfy da karfi sunsha trenin suka nufosu, da sauri abdol ya karɓi trolley hannun DON, Shahram kuma ya karɓi trolley hannun Aryan, suka samu su a chikin haɗaɗɗun motachin, da akajera musu dan tafiyar

Aryan yadubi DON yace “muje a mota ɗaya koh,DON batare daya amsa ba yace “wai ina Aiman da Ahmad ne “ae tunjiya suka wuche naija Aryan yabashi amsa yana kallan fuskar sa kama hanya kawai DON yayi batare daya sake magana ba yanufi motar, da sauri abdol yabuɗe masa kofar motar, slowly ya shiga ya zauna, ɗaga hannu Abdol yayi ya sara masa san nan ya rufe kofar motar, zagayowa ta ɗayan kofar motan Aryan yayi, da sauri Shahram ya buɗe masa kofar a nitse ya shiga ya zauna Shahram ya sara masa san nan yarufe kofar motar
Da gudu sojojin suka hau nasu motochin su suka tadasu, da matsakai chin gudu suka nufi gate ɗin tun basu kariso ba security suka wangale masu gate ɗin, da gudu suka danna hanchin motochin waje,motar sojoji 2 a gaba sai motar su DON a tsakiya sai motochi 2 na sojoji a baya gudu suke shararawa a kan mikakkiyar titin

Aryan ya dubi DON yace sai dai fa mutafi da jet ɗinka dan kuwa nawa yana naija dashi su Ahmad suka tafi “Ok kawai DON yache, chikin kankanin lokachi suka isa Airport Already angama shirya komai su kawai a ke jira, batare da ɓata lokachi ba suka fito daga chikin moton su suka nufi kyakkyawa kuma haɗaɗɗen privet jet ɗin DON mai ɗauke da tambarin sunan’sa PRINCE SAFRAS suna shiga batare da ɓata lokachi ba jirgin yaɗaga sai malam Aminu Kano international Airport Kano Nigeria

 

More comments and share pls

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button