Sponsored Links
Hausa NovelsJarababben Namiji Hausa Novel

Jarababben Namiji 3

Sponsored Links

*3*

Julayb tunda ya sauka a Lagos yagane nanne kamar small depot na ƙananun karuwan abroad,wato ko wacce kalar ƴar Afrika burinta ta flexing a Lagos tabi maza ta tara kuɗi

Anan ya fahimci Lagos garin tara kuɗine da kuma kashewa

Saidai sam bai damesa ba,don shi yaba mace 500k a haɗuwar farko ba matsalar sa bace.
Shi dai yajisa yina nitso kawai🙃

Tangameman gida yikedashi a victoria island
Saidai tunda umma raudha tazo ta tare
Kullum dama dama take dashi don im bai kuskure mata ba dabtake da tace zatana binsa duk inda Zaije

A cewar ta Lagos akwai over crowding dole zai yi rashin tsaro

Don haka baza ta barsa yinafita anyhow ba,aje a sace Mata shi
Don ta lura bata taɓa zuwa lalataciyyar ƙasa kamar Nigeria ba komai yinsa ake yi unorganized

Bakamar ƙasar su da sauran advance countery ba da ƙarfe tsakar dare zaka fita comfortable
Nan ko ina

Sai abinda yafi damunta zafi don ita a duniya batason zafi su kuma garin tane a cewar ta

Lura da hakan da yayine tun kafin suzo yasa aka lallata duk a.cn da ke cikin gidan.

Ba solar sai generato me ƙaran tsiya wanda daya fara ihu barci yayi mata ƙaura kenan

Tuni ta soma yi masa ƙorafin su koma,shi kuwa yanzu yaga ta zama musamman yanda ya haɗu da tsalatsalan ƴan matan Afrika masu gurin morewa😔

Share ta yayi da ƙorafinta yamasoma hadahadan buɗe componies bayan tangama tangaman plaza mai ɗauke da boutiques da ake lodo zallan kayan larabawa da tantsatstsatsun gwala-gwalai tun daga ƙirar Dubai da nasu Saudi wanda za ana molding ƴan yayi ,inkin isa ki maƙala😂

Yanzu haka unguwa guda ya siya ya saka signboard aka sa ma wajen suna Arab garden

Aiko tuni ya fara fidda gini bayan ya kwaso ƙwararrun enginiers turawa sun fidda tsarin zanen companin da plazas ɗin
Abunka da baƙar fata tuni wajen ya samu farin jini da karɓuwa a wajen jama’a.

Don haka shi ƙorafinta ma daɗi yake masa amma kannewa yake yinanuna jimaminsa akan abin

Bayan kabbaro mata da maigidanta yayi kan lallai ta dawo shi bai san zaman ta a ƙasar
Wanda duk julayb ya kitsa masa

****
Yauma abinda ya faru kenan
Cikin sauri sauri ya fito in readeness ya tafi wajen sababbin babes ɗin da yayi jiya
sanye yike cikin wata yadi filtex milk colour mai sharara anmasa ɗinkin yayi, fitted cas jikinsa da adon coffee brown daga wuya . yasama cover shoe coffee brown yasaka harta tabarau ɗin fuskarsa iri ɗaya da agogon hannunsa

A gurguje ya fito cikin tabbataccen ƙamshin sa na dindindin
Wanda musamman yasa aka haɗa masa a wani kamfanin turare a jiddah.

Umma raudha na kishingiɗe a falo hannunta da wani faskeken mafici irin na sarakunan larabawa tana firfita , hannunta riƙe da remote tana kamo tashoshin larabawa…

Tana ganinsa ta miƙe zaune har ya ƙaraso inda take .har ƙasa ta duƙa yina gaisheta
Matsowa tayi ta kamosa ta rungume
Tsantsan taƙi sakinsa ahaka a gama gaisawa sannan tasasaauta riƙonsa tana kallon sa cikin yarensu take tambayarsa
“Manil hazal siyab ya habiby?”(wato wainnan kayanfa)

Murmushi yayi kafin yace “ummy uridu an ashbaha li umuratahum jami’an…li annahum tuhibbu arkanu siyabihim hadha…hakadha aidhan satakuna sababul ladhi tuhibbuniy jiddan li annani garibun alaihim”(wato ummy sunason irin wannan shigar da nayi ne, kinga in ina wannan shigar saikiga na samu karɓuwa a wajen su sosai, saboda kinga fa Ni baƙone a gare su)

” Ɗayyib…Na’am hadha jayd yaibny…this is perfectly right i like your smartness”(wannan abu yayi kyau,inason ƙwazonka)

“zomu zauna muyi magana akwai damuwa araina sosai” ta jawo hannunsa tana cigaba da yimasa magana da Larabci

sam ransa baisoba, saboda yasan ƴan matansa sunyi masa alƙawarin kawo masa ziyara yau gashi umma takasata tsare…

Ɓata fuska yayi kaɗan “momy ina baƙi da suke jira na”

Washe baki tayi kafin tace “yarona meyasa bakace suzo nan ba?”

“To ai basu san waje bane,don ƴan school ɗinmune mata suka zo ma wata coarse mate ɗinmu bikin aure ,and basu san gari ba”

Interrupting ɗinsa tayi”kai kuma kasan garin ko?”

“Lah bahakaba kinga inada driver zaikai Ni airport kuma nima zani mata bikin”

“Shikenan dama Ni yau nikeso zan bi Flight ɗin yamma in wuce Saudi ,abbeynku ya matsa in dawo …but before then nasaka wannan igbo driver ɗinka yasamo dattijuwa da zatana kula dakai,ka kuma saka a ƙara janma mai gadinka kunne dondai Ni ban iya yarensa wai ko Hausa ko hillotu infact i cant recall his language and his ethnic group in synopsize” take masa bayani da ingausan larabci da turanci

Dariya yayi “oh momy Fulani ba hillotu ba🤪…”
“What ever dai” ta faɗa tana caɓe baki

Ɗan ɗaure fuska yayi kamar gaske “ummy kar ki tafi ki barni Ni ɗaya…bansaba ba ko’ina muna zo tare,you’re lyk my bossom friend”

Rakwakwa tayi da fuska kamar zatayi kuka “ya gulam la takhaf ,la kin uizuka bi taƙwil laha azza wa jal”
(Karka damu yarona , kawai ina maka wa’azi dakaji tsoron Allah…zan rinƙa paying maka visit akai akai)

“Shikenan mom zan tafi “yafaɗa cikin ƙosawa karmata samu canjin ra’ayi

“Ka kula da matan nan karsu ɓata mun kai Please,be smart as you’re”

Da haka ya fita yina murna , lallai daga yanzu ne zan fara ƙara’in

“`CIGABA DAGA FARKON LABARIN“`

 

 

*INA JIN DAƊIN COMMENTS ƊINKU LALLAI JARABABBEN NAMIJI YA SAMU KARƁUWA…INAYINKU SOSAI MASOYANA💓*

 

 

✍️………..⛹️‍♀️🤸‍♀️
*Oum Aphanan ɗinku ce🌸*
[3/14, 06:40] Bamalli✌️: *Typing…✍️*

 

*JARABABBEN NAMIJI*

 

*Na…Oum Aphnan🌸*

________________________________

*ALHERI WRITERS ASSO.🖊️*

*A .W. A*

https://www.facebook.com/Alheri-writers-association-100452175039849/

________________________________

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button