Sponsored Links
Duk Karfin Izzata Book 1Hausa Novels

Duk karfin Izzata Book 1 Page 22

Sponsored Links

Episode 22*

 

Sosai Aryan ke kallan chikin idon ta, kasa tayi da kai dan bazata iya chigaba da haɗa ido da shi ba, sake matsowa kusa da ita sosai yayi, ya matse ta da jikin,bangon “murya na rawa tace dan Allah yaya Aryan kayi hakuri, maganar da tayin nan yasa yaji tamkar an chan ka masa mashi a zuchiya,da kyar ya iya buɗe baki kamar mai raɗa yake faɗin “wae banace karki sake magana ba, hannu tasa ta toshe bakin ta, a hankali ya haɗe fuskar su waje ɗaya,hanchin su na gogan na juna rutse ido tayi dan baza ta iya kallan chikin idon saba,calmly yafara magana “daga yau karki sake kwalliya da daddare,kuma idan wani yasake yima ki magana kika amsa shi sai na ɓab’ɓallaki, yau kuma ina ɗan kwalin ki, a tsorache ta buɗe baki har kerma lips nata keyi tana faɗin kayi hakuri…bai bari ta karisa ba da sauri ya ɗora ya’tsansa a saman lips nata, yana girgiza mata kai yana faɗin “ae banche kiyi magana bako, kiyi shiru ki saurare ni, kawai, shiru ya ɗanyi yana kallan yan da lips na ta ke kerma dan tsoro jiyayi tamkar yayi kissing nata, amma ba zai iya hakan ba itakuwa kara runtse ido tayi dan sai kerma gaba ɗaya jikin ta yake, almost 10mnt suna saye a haka, da kyar ya iya buɗe baki dan yadda yake ji, ya chigaba dace wa “me yasa bakya jin magana tane eh? ko dan kinga ina damuwa da kirinƙa sa ɗan kwalin shiyasa kike kin sawa, to shike nan zan fara hukun taki,a kan hakan,yanzu dai zo nan kifara tsallen kwaɗo yana kai karshen maganar a zafafe ya sake ta da sauri ya juya ya koma saman sofa ya zauna sai lumshe ido yake

ahankali ta duka yafara frog jump tana kewaye palon tana hawaye,tun tana kuka a hankali har tafara da ɗan sauti, yana zaune yana jin ta sai faman runtse ido yake,yana chiza laɓɓan SA, dan har chikin ransa yake jin kukan nata, amma yazama dole yarin ƙa hukun tata, kodan tarin ƙa jin maganar sa, frog jump take sosai ga high heel a kafarta kamar an hanata chirewa, sai kuka take,kaɗan kaɗan tafara jin chiwon chiki,amma tana tsoran faɗawa faɗa masa, azaba yayi azaba,sae faman nishi take numfashin ta na fita da sauri sauri jinyadda take numfashine yasa Aryan ɗagowa, ya kalle’ta,Subhanallah, da sauri yamiƙe yanufeta yana faɗin lfy kike kuwa sis,bai kai ga karisawa wajen taba yaga ta sulale kasa kamar bata numfashi,da sauri ya karisa wajen ya duka, a ruɗe yasa hannu ya tallabo kanta yana faɗin Ke,ke,lfy kike kuwa,ɗayan hannun’sa yasa,a saitin kofar hanchin ta dan yaji shin tana numfashi, jin bata numfashi alamar ta sume,ne yasa ya miƙe da sauri ya ɗauke’ta chak yaɗora ta saman sofa, yanufi freij ya ɗauko robar ruwan Faro mai sanyi yadawo ya zauna a gefen ta, buɗe robar ruwan yayi ya tarbo a hannun’sa ya shafa mata a fuska,dogon numfashi taja, a hankali ya furta “ke kina lfy kuwa slowly ta buɗe idon ta a kan face nashi,da sauri ta sake runtse idon tana matsar kwalla, shiru yayi yana kallan’ta wasa wasa tafara juyi tana kara sautin kukan,”ke wae meke damun ki’ne,ya tambaya a ɗan ruɗe dan a’yanayin dayake kallanta kamar period nata ne ke san zuwa chikin kuka take faɗin “chiki yaya Aryan chiki’na wayyo Allah,hiyana ta kizo zan mutu, da sauri yasa hannu ya chire hannu’ta daga rikon datawa chikin nata,ya dora hannun sa awajen,a sukwane kuma yachire hannun nasa dan wani irin shock da yaji, kallan face nata yake dan ya tabbatar da abun dayake zargi shin period ko dai nomal chiwon chikine, ita kuwa sae kuka take, bazai iya jure kukan nata ba, a zafafe ya miƙe ya koma chikin betroom ɗin sa, jim kaɗan sae gashi ya fito riƙe da sirinjin allura,idon ta a lumshe sae kuka take tana juyi a saman sofan, a gefen ta ya zauna ya kama hannun ta a hankali,dan yasan in ta buɗe ido bazata tsaya ya mata allura ba,gashi tana bukatar alluran kodan period ɗin yazo mata da sauki,chikin dabara ya ɗaure hannun nata ya fara ne man jijiya,itakam sae kuka take dan ba tama san yana kusa da ita ba, gyara zaman’sa yayi da kyau, chikin dabara ya tsira mata alluran da sauri ya mata ya zare,sirinjin, a’sukwane ta buɗe ido tana ko’karin ihu,hannu yasa ya rufe bakin nata yana girgiza mata kae,”tashi kije ɗaki ki kwanta yayi maganar yana zame hannun sa daga bakin’ta, chikin dashe war murya take faɗin “yaya Aryan wlh bazan iya tafiya ba,ta karisa maganar tana sakin wani,kuka mara sauti,dafe kae yayi yana faɗin”wae banace kukan nan ya isaba kiyi shiru haka nan,yana gama faɗin hakan yamiƙe,ya ɗauke ta chak ya saɓa’ta a kafaɗar’sa yayi waje da ita,da sauri sauri yake tafi kai tsaye ɓangaren Ammi,yanufa da ita,da sallama ya’shigo palon babu kowa,a hankali yafara takawa izuwa ɗakin su kamar bai san taka kasan, kodaya shiga sae daya sauke wani nauyayyar ajiyar zuchiya,dan ganin su Zahra sunyi barchi, saman sofa ya kwantar da ita, ta buɗe baki zata masa godiya da sauri ya juya ya bar ɗakin,har yana tun tuɓe, chire takalman kafar ta tayi ta kwanta,ta dafe chikin ta ba jimawa barchi yayi awan gaba da ita

Aban garen Aryan yana fita ɓangaren Ammi ɗakin sa ya koma,a gurguje ya shiga, toilet wanka yayi ya shirya chikin kayan barchi,riga zuwa goiwa mai igiya, gaban rigan a buɗe take faffaɗar kirjin nan nasa awaje rigar fari ne tas,mai laushi sae kamshi yake zubawa fitowa palo yayi ya ɗauki coffee ɗin da diyana ta kawo masa,ya koma betroom,kaɗan yasha saboda coffee ɗin yayi sanyi, ajiyewa yayi kan table ɗin tsakiyar ɗakin,ya haye saman katafaren gadan’sa ba jimawa barchi yayi awon gama dashi

Washe gari tun asuba su Ammi suka shirya, Ammi Aunty farida hiyana diyana Zahra yusuf Khalid Aryan da kuma DON, lamrat da amrat kuma Anbar su wajen Aunty mardiya “wasu dan ƙara dan karan, motochi masu numfashi guda 5 suka ɗauƙesu zuwa Airport, ajere motochin suka jera har Airport, Ammi da Aunty farida mota ɗaya suka shiga,DON da Aryan motar’su ɗaya,hiyana diyana da kuma Zahra motar ɗaya Khalid da Yusuf ma motar’su ɗaya,ɗayan motan kuma sojoji ne a chiki,diyana sae murna take yau zataga yaya bello da innar yaya bello, Zahra ma sae murna take yau zataje kauye dan inba makaranta ba bata taba zuwa ko inaba,shiyasa ta dage sae tabisu, idan muka koma ɓangaren DON kuwa kamar zai mutu dan bakin chiki sae wani ɓata fuska yake kamar anche masa kwasan kashi zaije,Aryan Khalid Yusuf kam ko ajikin su basu damuba,

“da private jet na yaya Aryan suka tafi,tun jirgin’su bai sauƙa ba motochi 6 daga gidan sarkin yola ke jiran’su a Airport karfe 10 na safe jirgin’su ya sauƙa, basu wani ɓata lokachi chikin jirgin ba suka fito,DON yafara fitowa fiskar nan tamkar wani mayin wachin zaki taku yake irin na jaruman maza,daka kansa kaga wadda akai wa zuwa dole,Aryan na biye dashi a baya,sai Khalid da Yusuf,Aunty farida rike da hannun diyana suma suka sau’ko Ammi na biye dasu Abaya,sai Zahra da hiyana,Shahram da Abdol ne karshen fitowa,kae tsaye wajen motochin suka nufa, da sauri Shahram da Abdol suka fara buɗe musu kofar motochin, Aunty farida da Ammi mota ɗaya suka shiga,DON da Aryan motar su ɗaya, Khalid da Yusuf suma motar su ɗaya,hiyana diyana Zahra matar su suma ɗaya,sai Abdul da Shahram suka shiga ɗayan motar suma,kamar dai yadda sukazo,a jere motochin suka bar Airport ɗin da ma tsakai chin gudu,

kai tsaye kauyen jambutu suka nufa, wato kauyen su hiyana haka suka rinƙa keta dajin nan har kofar gidan su hiyana sukayi parking,na motochin, da yake yau kasuwar garine, shiru garin yayi ba jama’a duk sun tafi kasuwa,da sauri Shahram da Abdol suka fito daga nasu motar, Shahram yazo ya buɗewa Aryan, Abdol kuma ya buɗewa DON,kafa DON ya zuro waje batare daya fitoba yana zaune chikin motar,yana latsa waya yana wani kwaɓe fuska, Aryan kuwa,fitowa yayi yana kallan yanayin garin,Ammi da Aunty farida suka fito suka jera zuwa chikin gd “Ammi nikam bari naje dubo yaya bello tukun nan chewar diyana tafaɗi hakan tana murnushi,”bazakije ba wuche ki koma chikin moto Aryan yafaɗi hakan chikin tsawa,”Ammi dake tsaye a dai dai bakin kofar shiga gidan su hiyana, tace “a’a ina ruwan ka da ita, kasan halak chin da bello yamusu ne jeki abun ki diyana muma muna zuwa ai,bari mu gama da nan tukun nan, Tun Ammi bata kae karshen maganar ba diyana ta kwasa Aguje ta tanufi hanyar gidan su yaya bello, kwafa Aryan yayi a zuchiyar sa yana faɗin zamu haɗune, hiyana da Zahra ma fitowa sukayi su kabi bayan su Ammi, “to ni dai tun da Allah ya kawomu kauye yau barinaje naga gari chewar Khalid da sauri Yusuf yace “a’a jirani muje tare jerawa sukayi tare sukanufi chikin gonaki, wani dogon tsaki DON yaja yana faɗin “ni gaskiya an chucheni wlh da akasani dole nazo garin nan, Aryan dake tsaye kusa dashi bai san sanda dariya ta kub’che masa ba dan yadda DON yayi maganar, wani mugun kallo DON ya watsa masa yana faɗin me kakewa dariya to “kai nakewa dariya mana yanzu dan Allah prince menene laifin garin nan, ae kodan albarkachin a nan aka haifi Ammi ka girmama garin koh, tsaki kawai DON yaja batare daya sake chewa komai ba

Diyana kuwa da gudu ta faɗa gidan su bello ko sallama babu tun a kofar gida take faɗin “yaya bello ina kake yaya bello ina kake, bello da buba suna zaune a kan tabar ma a tsakar gida innar bello na girki, inna buba bata nan, hasana matar bello tana Shara,a tsakar gd, da sauri bello ya miƙe jin muryan diyana,dan kuwa ko mutuwa zaiyi ya dawo bazai manta voice na diyana ba, da gudu diyana ta kariso chikin gida kai tsaye wajen yaya bello tanufa zata rungume’sa kome ta tuna sai kuma taja birki, tana kallan sa shima ita yake kallo chike da farinchi yace “diyana kece? diyana baki yaki rufuwa sai dariya take tace “yaya bello ina….bata kai karshen maganar ba ta sake wani ihu sakamakon san dar da bubu ya buga mata a goshin’ta, kan kache me jini ya wanke mata fuska ihu take sosai shi kuwa buba kamar mahaukachin ya sake ɗaga sandar ya buga mata a kafa, nan take ta faɗi kasa tana ihu, a zafafe bello ya ɗamki sandar yana kokarin kwache wa buba kuwa yaki saki nan take suka kaure da faɗa, da gudu innar buba tafito daga kichin tana salati, hasana kuwa jefar da tsintsinyar hannun ta tayi tanufi ɗaki da gudu dan tsoro, ganin buba da bello sun kaure da faɗane yasa diyana ta miƙe da kyar, tanufi hanyar fita daga gidan,asukwane buba ya sakarwa bello sandar yabi bayan diyana da gudu yana faɗin yau sai na kashe’ki shegiya, diyana kuwa ganin buba na zuwane yasa ta tattara iya sauran karfin ta ta watsa da gudu tayi waje tana ihu

Jin ihun diyana yasa Aryan ɗagowa a’sukwane, ganin diyana na gudu ga jikinta duk jini yasa Aryan ya nufe ta da sauri, da gudu su Ammi ma sukayo waje jin ana ihu,

Diyana na kokarin faɗuwa Aryan ya karisa a zafafe batare da ya damu da jinin dake jikin taba ya rungumeta a kirjin’sa yana faɗin “lfy me yasa me ki eh.. bai kai ga rufe baki ba sai ga buba ya fito da gudu yana faɗin “sai na kashe ki ni zanyi ajalin ki a zuchiye Aryan ya saki diyana tana tangal tangal zata faɗi bai ma luraba idon sa ya rufe gadan gadan ya nufi buba,da gudu Aunty farida ta kariso wajen ta riƙe diyana dake kokarin faɗuwa,ta rungumeta suka koma chikin gidan su hiyana na, bello daya biyo bayan buba dan ya dakatar dashi kar ya bugi diyana ganin dasu Ammi tazo yasa ya koma gefe ya harɗe hannu a kirji yana kallonsu, DON kuwa yana zaune ko kallan inda su diyana suke bai yiba bare ma ya tanka sai latsa wayarsa yake, dayaji hayaniyar jama’a na damun sa sai ya ɗauko bluetooth yasa a kunnen sa ya kunna kira’an Al qur’ani mai girma na minshawi ya kure volume ya jingina da kujerar motar ya lunshe ido

Buba ganin Aryan ya tin’karosa gadan gadan ga fiskar nan tasa kamar wani,mayinwachin zaki, a’sukwane buba ya juya zai koma chikin gd, sai dai ina taku biyu Aryan yayi ya dam ki wuyar’sa ta baya ɗagashi sama Aryan yayi, yayi wurgi dashi gefe wani ihun azaba buba ya saki, gadan gadan Aryan ya nufeshi dam kar wuyar sa yayi ya kai masa wani naushi a fiska nan take wajen ta kunbura, ihu buba yake kamar makoshin sa zata fashe, baji ba gani Aryan ke kai masa bugu ta ko ina, jin yadda buba ke ihu da kyar muryar sa ke fita ne yasa Ammi ta nufesu da sauri dan kar Aryan yayi kisan kai, daga ɗan baya Ammi ta tsaya,a tsorache tace “Aryan ka kyalesa haka ya isa, Aryan bai ma san tana yi ba dan baya ji baya gani bugu kawai yake kai wa buba duk ya fashe masa jiki ga fuskar sa ta kun bura sun tum,

Ammi ta ruɗe sosai dan Aryan baya chikin hayyachin’sa kotayi magana bazai jiba gashi Aunty farida tayi chikin gd da diyana, bare ma tayiwa Aryan magana, da sauri ta juya tanufi wajen DON zaune yake a chikin motar idon sa a lunshe hankalinsa kwanche, dan yada Bluetooth bai ma san meke faruwa ba”kai katashi kaje ka dakatar da Aryan daga bugun ɗan mutane Ammi tafaɗa tana kallo face nash, shiru DON bai amsa ba kuma bai buɗe ido ba, ganin hakan yasa Ammi tayi tunanin kodai barchi yake, da sauri tasa hannu tana ɗan bubbuga Shi, slowly ya ware green eyes nashi a kan face ɗin Ammi, da sauri ya chire bluetooth dake kunnensa yana faɗin Ammi lfy, “ina fa lfy ga Aryan chan yana kokarin kisan kai, katashi kaje ka dakatar da shi daga dukan ɗan mutane, ɗaure fuska DON yayi yana faɗin “to ni Ammi ina ruwana basu suka ja ya bugesu ba daman ai mutanen garin nan da dabbobi suke..wani birki ya jaaa da maganar asukwa’ne ya daɗa waro manya manyan green eyes nashi yana kallon Ammi, data ɗaga yatsu biyar zata zabga masa mari sai kuma itama ta dakata tana kallonsa, chikin fushi Ammi tafara magana “to a nan aka haifi uwar idan mutanen garin nan dabbobi’ne to fa kasa har dani ina daga chikin dabbobi nima ko naso ko baka so nan shine tushen ka ta ɓangarena kuma ina alfahari da hakan,idan kaga dama katashi ka dakatar da ɗan uwan ka idan kuma bakaga dama ka barshi yayi kisan kai tana kai karshen maganar ta juya a fusache ta koma chikin gida,

dafe kai DON yayi yana faɗin “dan Allah Ammi kiyi hakuri na tuba, why why zan ɓatawa mahaifiya’ta rai sosai haka, har take kokarin yin abun da bata taba kotan tawaba mari Ammi, kuma ni NO yau gaskiya na kure ta, sosai dole naje na nemi yafiyarta ya karisa maganar yana miƙewa kai tsaye wajen su Aryan yanufa,yana taku irin na jaruman maza,
yana zuwa yasa hannu ya damki damtsen hannun Aryan ya jashi baya, a fusache Aryan yasake nufar buba gadan gadan, rikesa DON yayi yana faɗin “wai wan nan dukan na menene haka ya isa baka ganin ya suma ne wai ma me ya haɗaku kune, shiru Aryan yayi yakasa magana sai huchi kawai yake ga wani iska mai zafi dayake furzarwa daga bakinsa, hannunsa DON yaja har wajen mota, ɗauko robar ruwa DON yayi a chikin motar ya buɗe bakin robar ya miƙawa Aryan, ansan ruwan Aryan yayi ya kafa robar a bakinsa ya farasha, ganin yakusa shanyewa’ne yasa DON ya ɗauko masa wani yabuɗe yana jiran ya karisa shan’yewa, tas Aryan ya shanye ruwan, yayi jifa da robar, yasa hannu ya anshi wanda DON ke riƙe dashi ya duƙa ya zuba ruwan gaba ɗaya a tsakiyar kansa,shiru yayi Almost 7mnt sai faman furzar da wani iska mai zafi daga bakin’sa yake, ganin Aryan bai da niyar miƙewa yasa DON kamo hannunsa ya mikar dashi ya zaunar dashi chikin mota yana kallon face nashi “are U okey bro DON ya tambaya yana nazarin face ɗin shi, jinjina masa kai kawai Aryan yayi batare dayayi magana ba “me ya haɗaka da mutanen kauyen nan,har ka masa irin wan nan duka, a zafafe Aryan ya ɗago kamar wadda akawa allura yasake miƙewa yana kokarin nufar buba, da sauri DON yasake kamo hannunsa, yana faɗin “it’s ok zo kayi zaman ka ya isa haka kodai so kake ka ɗau doka a hannun kane ya isa pls, da kyar DON ya shawo kan Aryan ya hakura ya kyale buba, shiru sukayi Aryan na zaune chikin mota DON na tsaye a kusa dashi yana kallansa, almost 15mnt san nan Aryan ya ɗago yana faɗin “ina su Ammi, wani dogon numfashi DON yaja tare da sauke ajiyar zuchiya kana yace, thank God daka dawo chikin hayyachin ka, tsaki Aryan yaja kafin yace “ni bansan wulakanchi da che maka akayi bana chikin hayyachi nane pls ka faɗamin ina su Ammi “suna chikin gidan chan mana yayi maganar yana nuna gidansu hiyana da hannu, shiru Aryan yayi kamar mai tunani jingina kansa yayi da jikin kujerar motar ya lumshe ido, zuba mi shi wan nan manya manya green eyes nashi nan DON yayi yana ta kallonsa kamar mai son gano wani abu a tattare dashi.

A ɓangaren buba kuwa, a sume yake ga jiki duk jini, bello ya ɗauke sa Chak ya saɓasa a kafadar’sa yayi chikin gida dashi, saman ta burman dake shinfiɗe a tsakar gidan bello ya kwantar dashi san nan yakira hasana, yace ta kawo masa ruwa, da sauri hasana ta kawo ruwan a kwano bello ya ansa ya ɗiba a hannun’sa ya shafawa buba a fuska, shiru bai farfaɗo ba, sake ɗibar ruwan bello yayi yasha fa masa nan ma shiru, bai farfaɗo ba zuba masa ruwa mai ɗan yawa bello yayi shiru buba ko motsi baiyi ba, dukar da kai bello yayi sai tin kirjin buba yasa kunnensa dan yaji shin mutuwa yayi ne, tabbas zuchiyar buba na har bawa to amma an zuba ruwa an zuba bai farfaɗo ba, shiru bello yayi yana tunani a wan nan yanayi innar bello tafito daga bayi ta same’su chikin ruɗu da kiɗima ta nufe’su tana tana faɗin “bello me ka masa badai dukan’sa kayi ba “a’a inna bani na dake sa ba yan uwan’su diyana ne suka masa hukunchi “to yanzu bello ya zamuyi kasan, san dai bala’e mahaifiyarsa yanzu ko zamu tsallake inuwar mu bazata taɓa yarda ba kai ka bugesa ba, shiru bello yayi bai sake chewa komai ba ya zubawa buba ido .

A bangaren su Ammi kuwa zaune suke a tsakar gd diyana na kwanche a kan chinyar Aunty Farida tayi barchin wahala duk da an wanke mata goshin nata jinin bai daina zuba ba, miƙewa hiyana tayi tana faɗin “Aunty Zahra kizo muje ɗakin bappa,”to Zahra tace san nan ta miƙe suka nufi ɗakin bappa, kamar yadda suka bar ɗakin haka yake ba’a taɓa komai ba sai uban kura da datti da ɗakin yayi, nan fa hiyana ta shiga kakkaɓe kurar ta fito ta ɗauki tsintaiya a waje ta koma chikin ɗakin ta hau gyaran ɗakin

Gyara zama Ammi tayi tana fuskantar Inna tafara Magana “habiba kinsan kafin Ahmadu ya rasu babu Aure a tsakanin ku Koh, to yanzu mu ba wan nan che ta kawo muba, yanzu dai wan nan gida da kike chiki kirike mun barmi’ki, ki chigaba da zaman’ki a chiki da sauri Aunty Farida tace “Ammi ya zakiche kin bata gidan kuma ina che ae ba zai yiwu kiyi kyauta da dukiyan marayu, batare da izinin suba, murmushi Ammi tayi nasu irin na manya kafin tace “feeda wan nan dukiyar dakike gani bana su hiyana su kaɗai bane har da nawa a chiki nima ina da kaso, dabbobi 60 baban mu ya rasu ya bari ga filaye da gonaki, ba yadda za’ayi nayi kyau ta da abun da ba na waba Aunty farida zatayi magana hiyana tafito daga ɗakin bappa da gudu tana faɗin Ammi ki..

 

*💫STAR LADY💫*

 

*DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star Lady*

*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button