Sponsored Links
Hausa NovelsJarababben Namiji Hausa Novel

Jarababben Namiji 71-72

Sponsored Links

*71 – 72*

Waigowa tayi ta kalleta kafin ta watsa hannunta akan kambin motan.

“Danginkine sukazo ?”
“Eh inajin hakan…”
“Ooops tafiya ta sha ruwa ,saidai wata jiƙon,but for now ban numbernki”
“Ai banda waya ,wayan ogane a hannuna kuma bana ma amfani dashi”
“Oga?!!”
Ta maimaita sufrisingly “Hmmm any way zan saita alamarin komai,now muje kiban wayan in ɗauki numbern”

Fitowa sukayi a motar tana ɗingisawa ,yayinda matan suka futo yuuu daga motar suka biyo bayan drivern takalmi maƙale a hammata tun daga haraban gidan gani suke kamar sun shigo wani dausayi na musamman ,a wajen ƴan ganin ƙwaƙwam kenan ,sauran kam a motar suka ƙame don sunce basu fitowa a zuƙe jinin su,don mai gidan nan bai rasa dodo me basa kuɗi.

Mairone bayan tsayawar da sukayi da anty jidda wai don su taryesu, saidai mene? Kwata ² basu ma kallesu ba ,gadai dukkan alamu basu gane mairon bace.

 

Jinjina kai sukayi kafin jiddan ta riƙeta su koma ciki.
A falo kam zaman dirshan sukayi masa a ƙasan tayils kamar masu roƙon gafara,a haka suka gaisa dashi,don haka a dole shima ya sakko ƙasan da bayi yuwuwa ace surukansa na ƙasa shi yina sama

 

Sallama mairo tayi tareda jiddan,kafin taje ta sulmiya ta gaishesu
“A’aha mairamuuu keshe bamu ankare dake ba? Tabarkalli,tavarkalli…tabarkalli abun aro”suna tafa hannu tareda washe baki.

Murmushi tayi ta sunkuyar da kai

Tsam julayb ya miƙe zuwa ɗakinsa ,kafin yayi waya a kawo masu abinci as he orderd.

Aikuwa sun bararraje sun shana saidai kewayen gidane sukace ala bada lada,waje ko ta ina glasai inasu da shiga ya rufe dasu…waya sani ma su kurda kansu inda in ya rufe dasu harma anyi fawansu a gama ba wanda ya ji.

Mairo kam tasha gulma ,kamar mene ,mun dai san halin ƴan ƙauye da gulma.bare an ganta tana ɗingisawa kowa huuuu wannan ido babu ruwa ,daga shiga bako jira ,bare alkunya dama itama ɗin a riƙe take
Wata tsohuwace ta karɓe”allah sarki ƴayan zamani ,mu lokacinmu sai mace ta shekare a ɗakin miji ,suna wasan ƴar ɓuya”
Gabaɗaya yaran matan ne suka hayayyaƙo mata.
“Kaji yakumbo to wacce tayi haka a wannan zamanin saidai taji anyi bata,don saidai taji ayyururi guɗa amarya…lolz

Jidda kam janta ciki tayi ta karɓa wayarta ta saka numbobinta tayi dialing yashiga tayi saving itama tayi mata saving nata a wayarta.
Daga nan sukayi sallama akan sai sunyi waya.

Gida kam ya kacame ya hargutse,a dole ya ɗebo ma’aikatansa mata uku da zasu kula dasu har su tafi.
Kaf bq sukayi don sunce basu kwana anan ,akwatu kuwa haka sukasa aka sakko dasu kaf suka gani a ka kwashe aka maida
Don ko tunanin ƙirga turame ba maiyi a cikinsu.

Yo wani turame da lesuka bayan daidaida akwatuna gaddama aka soma yi wannan tana cewa itafa kallai talatin da biyar ne ,wannan nacewa “Ra’ayul aini naga saba’in a ƙididdige”
Watane ta turo baki ,tayi tsalle ta dawo tsakiya.
“Kajimun rabo,keda shanaye goma baki iya ƙidiyasu batare da kuskure ba ,wane ke da iya ƙirga kayan alatu haka,ai kwarjinin su ma sai su la’anta maki ido”
Dariya suka ɗauka “Hahaha lantai badai iya tsina da zagiba”

*****
Washegari da sassafe kowa tayi wanka a garden ɗin gidan ,wasuma ko wankan basuyiba haka suka ɗuru a mota ko karyawa sun ƙiyi ,sai sutu sutun beredi da kowa ya lalloda.

Bandir² ɗin abayu ya bada yace a raba masu da kuɗi 500k ,yara kuma riguna ƴan kanti masu kyaun gaske.

Sunyi godiya sosai,kafin sukayiwa mairo fatan alkhairi suka ɗebi hanya,ƴan gulma baki fal tsegumi,sunga bariki ,bariki ta gansu

******

Jidda daga gidan su mairo wani genune cataring and makeup school ta je ta nemo a cikin garin…tasa aka nuna mata shugaban wajen wacce ta kasance bayarbiyace amma babanta bahaushene,so tanajin hausa ba laifi…
Zama sukayi na musamman akan yanda zata koyawa mairo girki da make up cikin sati biyu…harka na naira…tako amince zatana zuwa kullum har gidan mairon tana koyadda ita…tayi billing take anan ta biya.

*****
Gidakam yasha gyara sosai kafin ya dawo normal ,sannan ya ɗauki ƙamshi.

Saida sukayi mata girkin dare kafin suka fita gidan

Suna fita saiga jidda ,da mai koyarda girki,sai wasu mata biyu ,da dattijuwa da ƴar yarinya…dattijuwa zatana mata hidimar girkin gida da share share…itakuma yarinyar ɗan aike dasu wanke²

Julayb yaji daɗin jiddah ,sai yanzu ya gane masoyinka masoyinkane yau gasu ahmad da ya aminta dasu sun kware masa baya.
Itakuwa da ya tozarta ita take lelen matarsa

Caterer bata fita gidanba ,saida ta tura mata nau’ikan duk girkin da zasu koya da drinks a waya ,kai harda kwalliya da ɗaurin ɗankwali…yanda da tazo sai dai sufara practicing bayan uta kuma ta kalla

 

 

✍️
[3/14, 07:07] Bamalli✌️: *Typing…✍️*

 

*JARABABBEN NAMIJI*

 

*Na…Oum Aphnan🌸*

________________________________

*ALHERI WRITERS ASSO.🖊️*

*A .W. A*

https://www.facebook.com/Alheri-writers-association-100452175039849/

________________________________

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button