Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 10

Sponsored Links

๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA!*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆโšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ
*BOOK 2*

*PAGE 10*

Shi kam a Yanzun gani yake bashi da kalmar da zaiyi amfani wajen nuna godiyar shi ga Meenal,
Domin dai duk da kasancewar ta yarinya k’arama da ya tabbatar da cewa a haife zai iya haifan ta sai gashi ta sanadin ta ne yau ya kasance cikin nutsuwar daya rasa tsayin wasu shekaru a yanzun Allah da ikon sa zai kwanta yayi bacci lafiyar Allah kuma ya tashi ba tareda yayi wani mugun mafarki ba sab’anin lokutan baya da baya samun isshen bacci, rashin baccin nashi kuma bazai sa yace ya tashi ya gabatar da nafila koda raka’a biyu bane, domin a lokacin nema yake jin wata irin muguwar kasala haka zai b’ata dare a banza shi baiyi bacci mai dad’i ba shi kuma bai raya daren ba, sai gashi yanzun Allah da ikon sa a cikin k’asa da wata d’aya komai ya canza ciki kuwa harda ibadan shi dan ya k’ara kusanta kanshi ga mahaliccin shi sosai ga kuma azkar da yakeyi akoda yaushe, yasan kuma yawan farin cikin da yakeji a zuciyar shi duk suna da na saba ne da hakan,

Yasan ya aikata kura kurai da dama a baya, domin dai adah can baya tunawa da damuwar kowa sai na matar shi kad’ai baik’i yab’ata da kowa ba indai har ita zatayi farin ciki to bazai tab’a damuwa ba wanda dalilin hakan ya b’ata mu’amalan shi da mutane da yawa bayaga abokan shi da sukayi kokarin ganin sun dawo dashi kan hanya ciki harda wasu daga cikin yan uwan shi wad’anda ya shatawa layi duk akan matar shi sai yanzun ne kuma yake jin bak’in cikin hakan ya kuma d’aura aniyar gyara kuskuren shi da yardar Allah,

Adah can baya yakan manta cewa akwai hak’k’in uwa da uba ya’ya da kuma k’anne ciki harda hak’kin ita kanta matar da iyaye suka aura mishi da take zaune cikin gidan shi a matsayin matar shi,
ya nisan ta da kowa babu mu’amala mai kyau balle akai batun shak’uwa dan harta yaran daya haifa duk da a Yanzun sunyi girman da zuwa gaba kad’an yasan maganar auren su za’a fara amma suma bai samu damar da zai zauna ya jasu a jikin shiba balle har yasan damuwar su da kuma abunda suke buk’ata na yau da kullum dan a lokacin uwar yaran ita kad’ai ce a gaban shi ta yanda baya iya tuna kowa sai ita, ita kad’ai dai itace a lokacin yake gani kamar duk wani farin cikin shi yana tare ne da ita,
Sai gashi Yanzun Alhamdulillah dan ba iya nutsuwar zuciya yake jin cewa yasamu ba harma da nutsuwa ta cikin gangar jiki domin a Yanzun mazan takar shi ta dawo ta yanda akoda yaushe yake jin kanshi a matsayin cikakken namiji kamar wani saurayin da yake cikin lokacin kuruciyar shi sab’anin shekarun baya da inba yana tare da Teemah bane bayama tuna cewa shi din namiji ne,

Abun mamaki ashe abundai daya raina itace warakar shi zai fito a sanadin ta, dan hakan yasa yake ganin me nene ma wanda Meenal zata nema a wajen shi har ya kasa cika mata shi?
Dan a Yanzun ta wuce neman abu a gunshi shi dai da yake matsayin Babban yayan ta shine zaiyi tsayin daka wajen ganin cewa bata rasa komai na buk’atar rayuwa ba,
Duk da ko a Yanzun bawai matsayin daya bata ya canza bane,
Ah ah sai dai yana d’aukar al’amarin ta da girma ne sosai ya kumayi imanin cewa ita d’in tun farko dama ba matar tashi bace shi yasa yake mata fatan Allah ya had’ata da wanda zai kaunaceta kamar fitar numfashin shi,

Ya d’ade zaune yana cigaba da kallon hotunan Moon tunawa da paper din da Meenal ta rubuta mishi sunan yarinyar ne yasa shi mik’ewa dan tun a ranar yana dawowa ya cire shi a cikin aljihu ya saka shi a cikin wallet din shi gudun kar ya salwanta,

Inda wallet din yake ajiye akan side drawer ya nufa yana budewa ko ya zaro shi a inda ya soke shi,
Babu b’ata lokaci ya bud’e ya karanto, a bayyane ya furta,

“Maimoon, Lagos, ah lallai zuwa Lagos ya kamani,”

Address dinta da Meenal din ta tura mishi ya k’ara dubawa, kafin ya d’auko wayar shi yayi saving number din dake rubuce a jikin takardar da sunan “Moon”
Sai da yayi kamar ya danna ma number d’in kira sai kuma ya fasa, domin kafin komai ya fara shiga tsakanin su zai so ya Santa da kyau ta yanda zai san ta inda zai fara dan ganin ya kamo zuciyar ta cikin kwanciyar hankali, kuma ma gani yake ai yanzun yayi wuri ace ya kirata.

Komawa kan kujerar daya taso yayi ya zauna yana k’are mata kallo,

“Wannan yarinyar da wuya itama inba irin halin kawarta take da ba, daga ganin bakin nan nata sai tayi yawan surutu, wai zata ma so tsoho kamata kuwa?, Allah ka dafamin in samu shawo kanta cikin sauki”

Ya fad’a a bayyane, can kuma kamar wanda aka tsungula sai ya fita daga wajen hotunan ya koma wajen ajiyar lambobi,
Number din da yayi saving da suna Joseph ya aikama kira,
Number din bata dade da shiga ba aka d’auki wayar da harshen turanci suka gaisa,
Da harshen kuma sukaci gaba da magana inda shi Sarki yake tambayar Joseph din cewa yana gari kuwa? Shi kuma Joseph din ya amsa da cewa eh yana nan,
“Zan turo maka pic din wata yarinya da address a kanta ina son sanin komai a kanta, idan nace komai ina nufin komai”, ya jaddada mishi,

“Babu damuwa sir duk abunda kake buk’ata zaka sani akanta cikin kwana biyu”

“Ok zan tura maka pic da address din yanzun”

Bayan Joseph ya amsa ne kuma Sarki ya yanke wayar sannan ya tura mishi,

“Ina ganin lokaci yayi da zan waiwayi Lagos”

Ya furta a bayyane domin tun kafin faruwar komai dama ya dad’e baije garin ba, ga shi kuma yanzun Zaria bata zuwuwa gaskiya dan ido da kunya wallahi,
Bai san da wani idon zai kalli baban shi da Malam ba idan yaje dan ta uwar gida mai sauki ne domin tuni suka dai daita tsakanin su, ba iya ita kad’aiba ma harda yan uwan shi yanzun shida kanshi yake kok’arin kiran su,
Shima kuma baban nashi suna waya dan shine ma ya shaida mishi komai daya wakana bayan ya gama mishi wankan tass a randa shi Sarkin ya kira shi, ya kuma ce mishi ya kira Malam ya bashi hak’uri,

Ranar daya kira Malam d’in sai Allah ya rufa mishi asiri wayar bataje ba dan wayar Malam din yana rufe,
Ranar daya k’ara kira kuma ya samu malam d’in yayi zaton zaiyi mishi fad’a ne ko ya nuna b’acin ranshi kamar yanda Baban shi yayi,
Sai malam ya bashi mamaki dan nasiha Kawai yayi mishi sosai mai shiga jiki ya kuma tunasar dashi akan rik’e ibada daga k’arshe kuma ya kora mishi warning akan ko kusa ko alama koda wasa shi Malam din yaji cewa Sarki ya saki Teemah tofa babu shi bashi,
Dan bayan mutuwar auren da maganar ta fita su dangi duka kowa tsinuwar shi akan Teemah ya k’are a zaton su ko itace silar da auren ya mutu shi yasa duk suke ganin laifin ta, yasan kuma tunda uwar gida tasa ya saki Meenal tana iya cewa ita ma Teemah sai ya saketa, dan haka Malam ya fad’a mishi cewa yayi na farko yayi na k’arshe idan ya samu matsala da matar shi inyaga cewa abin yafi k’arfin shi to yakai maganar gaban mahaifin ta tunda Allah yasa har yanzun yana raye,

Sannan ko dan darajar ubanta yaci a d’aga mata k’afa ga kuma yara har 4 Allah ya basu a matsayin zuri’a dan haka shi Sarki yayi hakuri daduk abunda ya faru a baya sai kuma a kori gaba,

Wannan abu sosai ya k’arama Malam kima a idon Sarki, domin dai a wannan lokacin da muke ciki bako wani uba bane za’a cutar da yarshi ya kauda kai balle kuma har ya rok’ama wacce ta cutar da yar nashi arzikin cigaba da zama da mijin data raba da yarshi alhalin yasa yana da ikon rabata da nata mijin itama,

To dai shima Sarki har yanzun fa bawai ya dena son matar nashi bane, domin dai ita d’in ita ce mace ta farko da zuciyar shi ta fara mata wankakkiyar kaunar da babu algus a cikin ta har yanzun kuma baya dena son nata bane,
Sai dai muce kaunar ta sauka daga kaso d’ari zuwa kashi 45,
Ya yanke hukuncin hukunta ta shi yasa ma har yanzun bai gwada neman ta ko a waya ba, tunda ya binciki mai gadin gidanta ya shaida mishi cewa bata gidan yasan tana gidan su dan haka bai damuba dan shima yana buk’atar suba juna space kowa ya sarara, dan yasan idan ya tunkareta a yanzun ana iya haihuwar uwar da bata da ido,
To gashi kuma yanzun uzurin zuwa Lagos ya kamashi dan yau d’ai daga ganin hoton yarinyar nan yaji ya zak’u yakai gareta dan ya ganta a fili dan yasan zatafi kyan kallo a zahiri, kwana biyun da Joseph yace mishi zaiyi dai dai da sanda shima zai koma KD dan haka yana komawa Lagos zai wuce,

Bai tashi daga wannan sak’ar zucin ba har sai da kirar Sa’eed ya riske shi inda yake ce mishi ya dawo mishi da zab’in gidan da yake ganin yafi dacewa,
Babu b’ata lokaci ko ya k’ara jawo laptop d’in ya kunna, a wannan daren dai bai kwanta ba sai da ya kira wanda batun gidan ke hannun shi ya kuma tura mishi Number din Sa’eed akan ya kirashi a gobe suje dashi yaga gidan sai suyi ciniki duk yanda akayi sai su fad’a mishi, ya kuma turama Sa’eed din number din mutumin shima.

Bayan kwana biyu,
Ya samu damar kammala aikin daya kaishi Calaba lafiya lau cikida tarin nasarori, dan haka ya tattara zuwa Kaduna, baiyi yunkurin zuwa Zaria ba yadai kira Sa’eed din shida Salman akan suzo su same shi,
Dan haka a randa ya iso suma suka isa kadunar sun samu wancan mutumin ma da za’a siya gidan a hannun shi har ya rigasu zuwa ma, koda suka isa su d’in ya aika bank suka ciro kud’in gidan millions of Naira, abunda ya Sa’eed matuk’ar mamaki shine ganin takardun gidan d’auke da sunan Aminatu b’aro b’aro, hakan yasa bayan wucewar wanda aka siya gidan a hannun shi Sa’eed ya kasa shiru sai da yayi magana da cewa.

“Sarki kunyi mantuwa fa wajen suna a takardun”

“Bamuyi mantuwa ba Sa’eed sunan da ka gani akan takardar na mamallakiyar gidan ne a yanzun”

“Meenal?”
Sa’eed ya anbata da alamar tambaya.

“Kwarai ita d’in dai domin ta cancan ta shi yasa na siya mata, itama kuma kyauta zatayi dashi ko zaka cemin baka san buri kanta bane?”

Cike da mamakin dabai saki Sa’eed din ba ya amsa da cewa,

“Burin ta uku,
Zama likita
Hawa babbar motar da zata kasance mallakinta
Na ukun kuma shine idan tayi kud’i ta ginama Baba Malam k’aton gida ya koma can shi kad’ai yabar family house”

“Madallah ashe baka manta burukan kanwar taka ba, to cikon na ukun ne na cika mata, sai dai ina rokon alfarmar maganar ta tsaya a tsakanin ni da kai sai ita Meenal din shi yasa kaga na aiki Salman ban bashi daman dazai san komai akan maganar ba dan bana son matsala dan ina gudun kar hassada ya shiga tsakanin ta da yan uwana na yarda da kai shi yasa na damk’a komai a hannun ka, idan ka kai mata ita zata gabatar ma Baba Malam dashi a matsayin daga wajen ta ya fito,
Ban san yaushe zatayi hakan ba amma ina fatan zaka tayani rufe maganar nan?”

“Insha Allah Ya’ya kamar yanda ka yarda dani bazakaga sab’anin abunda kake zato daga wajena ba, mungode ubangiji Allah ya k’ara arziki dan ba Meenal ce kad’ai zatayi godiya ba harda ni nima dan ba ita kad’ai ce take da burin canza ma Malam muhallin zama ba harda mu muna sai dai duk bamuyi yunkurin yin hakan bane saboda munsan bazai amince ba amma idan abun ya fito daga wajen ta tabbas bazai k’i amsa ba dan shima yasan ta rayu da burin gina mishi gidan dama tun tana k’aramar ta,
Mungode kwarai ubangiji Allah ya cigaba da bud’e maka kofofi na alkhairi yasa ka gama da iyaye lafiya, Allah ya raya iyali ya kuma kareka daga sharrin Makiya”
Ya k’arasa fad’a yana dukewa zuwa kasa,

“Kai miye haka tashi mana so kake Salman ya shigo ya fara tambayar ba’asi, dan Allah tashi ko ka manta nima yaron Malam ne tun kafin a haifo ku?”

Bayan dawowar Salman daya aika kasuwa yin siyayyar abubuwan da yasan za’a buk’ata a gidan ne kuma ya had’a musu da tsarabar daya taho dashi daga Calaba, sai da ya ware na gidan su dana gidan Malam sannan suma d’in ya jik’asu da nera sukayi Sallama da juna suka kamo hanya dan jirgin yamma zaibi zuwa Lagos dan haka yana buk’atar hutu sosai kafin yamma.

 

*UMMIEE ZARIA*โœ๐Ÿผ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button