Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 39

Sponsored Links

⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️
*BOOK 2*

*PAGE 39*

D’aure fuska AK yayi dan karma Hajiya taga fuskar shi sakwa² ta d’auki maganar su shiririta dan yasan halinta tsaf tana iya daga shi har Sarkin ta musu fatattakar kare, amsa mata yayi da cewa,

“Eh shi d’in ne dai wanda kika hasaso kuma babu wani wanda ya wuce shine dai, tareda Moon d’in suka zo nan koma menene tsakanin su ai zakiji daga bakin shi tunda dai gashi yazo,”

“Kai d’an nan kar kayi fushi kaji, karkaji nace mai ya kawo ka nan kayi zaton ko da wani nufi na fad’i hakan, ah ah wallahi kai kam ai ka zama d’an gida zuwan daren nedai ya bani mamaki, dan nasan ba sabon ka bane, to Barka da zuwa fa ya wajen iyalin naka da ita uwar gidan kuna dai lafiya koh? ance ma kayi sabon gida dan haka, ka dawo nan Kaduna gaba d’aya kaida iyalin taka to Allah ya sanya alkhairi yasa anyiwa wayan raine, allah kuma ya k’ara arziki a kuma cigaba da kiyaye addu’a sai kaga kofofin arziki suna ta budewa wallahi”

“Ameen ya rabbi Nagode kwarai Hajiya kowa lafiya lafiya Allah kuma ya k’ara miki lafiya kema” Sarki ya amsa dashi kanshi a k’asa,

“To ameen dai madallah ina fatan dai lafiya dan nayi mamakin ganin ka?”

Hannun shi yakai bayan k’eya yana gyara zaman hular dake kanshi kafin ya d’an k’ara sassauta murya duk da muryar tashi bata rik’uwa yace,
“dama Hajiya nazo gaisheki ne”

“Kai madallah aiko ka kyauta nagode da gaisuwa Allah dai yayi albarka kaji,
Gashi kuma kayi min zuwan dare amma dai nagode wanda ya biyoka har gida ya gaisheka ko bai kawo maka komai ba ai ya kula da kai, toni zan shige daga ciki ka gaisheda gida”
Ta yunk’ura da niyyar tashi AK ya tsaida ita inda yake cewa,

“Hajiya zuwan nan da yayi fa wajen ki yazo dan iri ya gani a gidan ki ya biyo, kuma ni a matsayina na yaron gidan babba munyi magana dashi harma na bashi sa Albarkan ki dai muke nema yanzun Hajjaju”
Komawa tayi ta zauna tana maida kallonta kan AK dake magana,
“Kasan nifa idan mutum zaiyi magana dani nafi gane ya fito kai tsaye ya fayyace min komai bana gane nuku² da kananun munafunci, yo fadama gareni a cikin gidan balle ace ina noman rani da za’azo neman iri a wajena?… ”
Katseta ya k’arayi da cewa “amma Hajiya aikema kince Sultana ta fad’a miki cewa saurayin Moon ne yazo koh”

“Kai dakata min dan Allah,ina ce koda na fito ku biyu na cimma zaune anan d’in shifa wannan d’in da kakeji da gani shine dai tsohon mijin Aminatu ko baka ganeshi da kyau bane ko kuma dai kallon tsoro ka mishi?
Ina had’in tsohon mijin Aminatu kuma da Moon wacce ke can kudu?ina ga dai a hanya suka had’u shi kuma ya rage mata hanya zuwa nan gidan kasan kuma ita Sultanan ba sanin shi tayi ba shi yasa tace haka inba hakaba Wannan ma ai ba zancen da kai zai d’auka bane abu dai kamar muna garin da ba’a sallah”

K’ara d’aure fuska AK yayi jin Hajiya tana neman jagwalgwala maganar, da hausa fa yayi magana da ita bada wani yaren ba balle tace bata gane me yake cewa ba, shi kuma Sarki sai wani k’ara nok’e kai yake,

“Hajiya koma dai garin suwa muke shi dai d’in da kike gani yau yazo gidan nan ne dan ya gaishe da kakar budurwar da yake nema ya kuma gabatar miki da kanshi a matsayin mai neman auren jikar ki,
Kai kuma ka wani zauna kayi shiru ni kad’ai zan maka yak’in neman auren ne?”

Dif ruwan kan Hajiya ya d’auke dan Wallahi ita dai a cikin kalaman da AK yayi babu guda d’aya wanda zata iya cewa ta fahimci abunda yake nufi,
Kuji wani hauka fa wai cewa yake shi Sarkin ne wai saurayin moon to wannan batu ai sai dai a garin mahaukata wallahi,

“Tuf tuf tuf” ta tofar da miyau daga bakin ta,

“Kai dai kana da bak’ar d’abia wallahi Abdul, wacce magana ce kake fad’a haka irin ta masu shaye shaye?,
Shi Sarkin shine yace maka son Moon yake ko koh ah ah kaine da iya tsara zance ka tsara jawaban ka dan kawai ka mai dani wata abokiyar wasar ka, to wallahi ka fita idona tun wuri in rufe, ya mutum zaizo har gida dan ya gaishe ni da girman ka da komai sai kawai ka wani tak’ark’are ka dunga sheqa mishi k’arya,
Kai kuma wallahi ka daiji kunya dirkeken soja dakai ka zauna kana jin yana sheko k’arya akan ka baka zage kwanji ka wauwanke mishi fuska da mari ba aikin banza kawai”

Gyara zama Sarki yayi duk da yanda yaga Hajiya tana kumfar baki hakan bai sare mishi gwuiwa ba, domin dai tunda har ya iya kawo kanshi ba wani can da ban bane ya kawo mata zancen to gara ayi wacce za’ayi kawai, dan haka sai ya zamo daga kan kujerar da yake zaune bayan ya zame hular kanshi ya ajiyeta a gefe, bai yarda ya kalli fuskar hajiya ba ya fara magana,

“Hajiya kiyi hakuri ban sani ba ko har yanzun a mai laifin daya aurar miki jika ya saka kike kallona, bazanga laifin kiba in kin kalleni a matsayin mai lefin sai dai ina mai k’ara baki hakuri abunda ya faru tsakanina da Meenal ya riga ya faru ya wuce, aure ne Allah ya kaddara a tsakanin mu a cikin zaman mu kuma sai Allah yasanya hijabi a tsakanin mu, tun kafin in san zan auri Meenal nakejin soyayyar yar uwarta a cikin zuciya ta, ban bayyana bane a wancan lokacin saboda nayi duba da k’aracin shekarun su ko secondary school basu gama ba, Allah ya sani ban tab’a kallon Meenal da fuskar soyayya ba a tsayin zamana da ita, rashin sonta kuma bai sa na cutar da ita ba, nasan zaki fassara abin ta fuskar cewa kusancin yayi yawa na auri Meenal yanzun kuma ince ina son Moon saboda dangar takar iyayen su da suke uwa d’aya uba d’aya amma Hajiya a addinan ce hakan ba haramun bane…..”

Hannu Hajiya ta d’aga mishi alamun dakatar wa,
“Eh kawai haka mutane ke cewa ba haramun bane amma mu hausawa cewa mukayi ana barin halas kodan kunya kuma wata kusar tafi wata, dab haka in ma dai wannan shirmen ne yasa ka kwaso jiki da tsakar daren nan uwa mafatauci ka duro min gida tattara maza maza ka koma inda ka fito, idan a dangin ku kun saba kwamacala ni anan gidan baza’ayi min ba, yo ita Moon din hauka takeyi ma da zata yarda harta kulaka kana matsayin tsohon mijin yar uwarta sune fa sukayi ma Meenal din yan matanci a matsayin kawayen amarya, yo wannan abi idan ya tabbata kuma ai sai a buga mu a jarida wallahi ace ka auri yar mace ka saki ka koma kan yar namiji,”

K’ara gyara zama yayi ko gezau bai nuna alamun mikewa ba balle tasa ran zai bar mata falon,

Sultana wacce tun d’azun take zaune akan dinning domin bayan ta kira Hajiyar data sauko kitchen ta shiga ta zubo abinci ta zauna tanaci, biyu ta raba hankalinta d’aya akan abincin da take ci d’aya kuma tana k’arewa Sarki kallo tana kuma sauraren hirar dake gudana a falon,
Ko ita fa maganar yayi mata wani iri, taya ma zaka auri k’awa ka saki sannan kuma kace zaka auri aminiyar ta wannan abun baiyi ba sam koda ko ace babu dangan taka na jini a tsakanin su balle kuma tsakanin Moon da Meenal kai gaskiya kusancin yayi yawa ko ita bazata goyi baya ba dan hakan yana iya shafar zumunci, tututura abincin tayi ta maida plate din kitchen ta wuto da niyyar haurawa sama ne Hajiya ta tsaida ta,

“Ke Sultana haura maza kiyi min kiran Moon ta sauko yanzun ina son magana da ita dan bazasu mai dani wata sakarya ba ita Moon din har idonta yayi budewar da zata zagaye taje tana soyayya da tsohon mijin yar uwarta”

“Hajiya me yasa kike so dole dai sai kin tadama kanki hankali ne wai?
Miye na damuwa a cikin maganar nan naga dai AUREN nan ba wai ya haramta bane, amma sai tada jijiyoyin wuya kikeyi idan ita yarinyar tana son shi zaki hanata abunda take so ne?”

“Kwarai zan hanata dan ko ban isa da itaba na isa da ubanta” ta amsa dashi tana huci,

“Hajiya dan Allah kiyi hakuri wallahi ba yanda kike tsammani bane, da zuciya d’aya nike son Maimoon kuma nayi alkawarin zan kula da ita zan riketa amana idan kuka bani auren ta dan ina sonta”

“Ita waccan da aka aura maka da farko meya hanaka kulawa da ita ka riketa amanan? Ita data kasance maka zab’in uwama kayi fatali da ita ka kai gida ka jirgeta uwa majigi shine zaka k’ara sad’ad’owa ido babu kunya kace wata jikar nawa kake so, wato ni gani Hajiyar mahaukata ni kuma sai in goya maka baya to baka isa ba har yanzun rass nike lissafina bai goceba,”

Su ukun suka sauko Maimoon Meenal sai Sultana a bayan su, kuka mara sauti moon takeyi Meenal ke bata hakuri da cewa tabar kukan tana kuma share mata hawaye har suka sauko k’asan,
Tun kafin su nemi waje zama hajiya ta kaida tambayoyin ta kan Moon d’in,

“Ke bar kukan munafuncin naki dan bazai fishsheki ba kizo ki fad’amin uban meye tsakanin ki da tsohon mijin yar uwar ki,
Maimoon ashe har zaki iya zagayewa dan cin amana kije kina soyayya da mijin daya maida miki yar uwa k’aramar bazawara sai yau da tsakar daren nan saboda tsabar kun shahara wato kun riga kun gama kulla tuggun ku shine ya wani kwaso min ke kukazo min gida zai wani ce wai yazo gaisheni da kuma rok’on iri, to ba iri ba yabanya ma taci buhun ubanta, ido ba kunya kika kwaso shi kuka yimin saukar dare alhalin ko sanda yana auren yar uwarki gata nan nidai ba zuwa min gida yakeyi ba,
Ke kuma da kika wani kwakumeta a jikin ki wani irin rashin sanin ciwon kaine wannan amanar ki taci fa ta koma tana tarayya da tsohon mijin ki duk bamu da labari… ”

“Hajiya dan Allah kiyi hakuri ki dena fad’ar nan haka dare nefa, amma sai faman fad’a kikeyi kuma ai ban ce miki bani da masaniya akan abunda yake faruwa ba, nasan kuma kuma nice ma na bashi number waya da adireshin gidan su moon d’in acan Lagos yaje ya sameta”

“La’ilaha illallahu muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam³” hajiya ta dunga maimaita tana tafa hannuwa cike da jimami da mamaki duka a lokaci d’aya,

“Yanzun nan ke yar gidan Jidda Ashe rashin sanin ciwon kan naki har yakai can, ace miji ya sake ki wai kuma harya dawo ya miki dadin bakin cewa yar uwarki yake so ke kuma saboda rashin sanin ciwon kai kika d’auki number da adireshin ta kika bashi,
To ke Moon dama can son nashi kema kikeyi koh shi yasa koda yaje kika amshe shi hannu bibbiyu?”

“Ah ah Hajiya wallahi gashi nan koshi zai fad’a miki gaskiya tun sanda yazo wajena ni ban bashi fuska ba shine dai ya nace kuma koda na fad’ama Umma itama cewa tayi in rabu dashi bata bani goyon baya ba, shi yasama koda yace zai tura ni kuma na hanashi turawa saboda ban san da wani idon zan kalli mutane ba wallahi Allah Hajiya ko yanzun ban san cewa nan gidan zai kawo muba da bazan biye mishi muzo tare ba dan Allah kiyi hakuri Hajiya”ta k’arasa fad’a a yayinda ta durkushe a wajen tana kuka,

“Maimoon” AK ya kira sunan ta a dake,

Bata iya amsawa ba saboda tsoron daya rufeta dan tasan kila shima kallon yar cin amana zaiyi mata,

“Waiba sunan ki na kira bane da bazaki iya amsawa ba, taso ki dawo nan kusa dani tambayar ki zanyi” ya fad’a a tsawace,

Da rarrafe ta k’ara inda yake hawaye dama² a fuskarta,

“Kina son Sarki?”

Dan dago kanta tayi kad’an ta saci kallon hajiya wacce ba ita kad’ai ba dukan su Moon d’in suke kallo sai dai ita kuma mai makon ta bashi amsa ah ah sai kawai ta maida kanta k’asa ta fashe da kuka mai k’aramin sauti irin mai fitowa daga cikin zuciyar nan,
Ita taya zata iya amsa cewa eh tana son shi bayan ga Hajiya nan ta kafa ta tsare akan bata yarda da zancen auren ba,
Batajin ta Meenal domin a zaman da sukayi ita da Meenal a cikin d’akin zancen da suka tattauna kenan dan Meenal din ta fito ta fad’a mata gaskiyar cewa itace taba Sarki number da Address din ta kuma inhar Moon din tana son Sarki har yanzun ita zata tsaya ta jajirce wajen fahimtar da iyayen su bayan ita kuma suna da goyon bayan AK dan haka shawo kan Hajiya bazai zama aiki ba, amma yanda taga Hajiya na tada jijiyoyin wuya ne ya karya mata kwarin gwuiwa dan Wallahi idan har Hajiya tace ah ah to ah ah din ne zai tabbata ita da Sarki sai gani sai hange.

“Moon karkiji tsoron kowa anan ki fad’amin in har kina son Sarki ni kuma na miki alkawari wallahi zan tsaya miki har sai na tabbatar da d’aurin auren ki, kin san dai koni ina da ikon aurar dake koh amma bazan ce mishi na bashi ya turo ba har sai naji ta bakin shi dan haka ki bud’e baki ki amsa min karkiji tsoron kowa kina dani ninan zan tsaya miki, kina son Sarki zaki aure shi”

Gyad’a kanta tayi alamun eh,

Shi kuma sai yace “ah ah bana son maganar kurame da baki na tambayeki dan haka bud’e murya ki bani amsa kina son shi”

“Ina son shi amma Hajiya ai tace bata yarda ba”

“Fad’i ki k’ara ban fa yarda ba shima da yake neman d’aure miki gindin naga uban shima a karkashin ikona yake bare kuma shi, shida bai aurar da kanshi bane yake batun aurar dake,”

“Hajiya yarinyar nan dai gashi a gaban ki tace tana son shi dan haka dan Allah kiyi hakuri kisa albarka ki barsu suyi auren su dan baki san abunda Allah subhanallah wata alah ya b’oye a cikin tarayyar suba idan akwai rabon aure da haihuwa a tsakanin su ina mai tabbatar miki da cewa idan fa har kika d’age akan cewa baza’ayi auren ba Allah yana iya nuna ikon shi akan ki, sai ya d’auke ki daga duniyar gaba daya bayan kin gushe su kuma suyi auren har su hayayyafa…. ”

“Kaine zaka mutu Abdul Khareemu badai niba dan uban ka, harni zaka fad’ama cewa idan na d’age zan mutu, to insha Allah zanci gaba da zama cikin koshin lafiya har zuwa sanda zan gama aurar da jikokina tass dan hasken fuskar annabi, wato so kakeyi kace ni bani da taqawa bani da tawalu’u to ni bazan ja da ikon Allah ba tunda shi ya had’asu ita kuma tace taji ta gani sai shi to ai sai suje suyi ta fama dama ni surutun mutane ne bana so ato yanzun duniya abin surutu sam bashi da kad’an wacece nima dazan zakalkale inyi ta tada jijiyoyin wuya bayan ita Meenal din ma naga ta nuna ko a jikinta,
Kai kuma kaji da kyau karkaga na saduda kayi zaton ko zansanya maka idone bayan auren sai yanda kayi min da rayuwar jika ah ah gara in fad’a maka ka shirya wannan karan koni ko kai in kuma kasan cewa har yanzun baka isa da gidan kaba to kar In k’ara ganin kafar ka a wajen jikata, idan kuma ka isa da gidan ka ka kai namiji gobe iyayen ta maza zasu iso dan haka kayi hanzarin turo naka iyayen garesu dan a gabatar da neman aure ba kuma lokaci mai tsayi za’aja ba dan sabon gida kayi gara itama ta tare a cikin shi tun yana da sabun tan shi”

“Nagode Hajiya Allah ya k’ara girma dama kuma tun a can Lagos din na tura manya sunyi magana dashi Baban namu shine ma yace ayi hakuri a jira har Abban saudia ya iso k’asar sai a gabatar da komai idan sun iso nan, na dai yanke hukuncin zuwa in gabatar miki da kaina ne shi yasa nazo yau kiyi hakuri dan Allah”

“Ikon Allah kace min sai da kuka riga kuka shirya komai kaida iyayen ta kafin ka iso nan, to ai yayi, ai koba komai da ta fad’a wani hannun gara kai d’in koba komai na gida ne kuma kowa ya maka shaidar arziki inaga dama can Moon itace allah ya kaddara zata zama matar ka shi yasa auren ka da yar uwarta yazo a yanda yazo to Allah ya sanya alkhairi ya kuma kad’e fitina karkaji komai kaji tunda shi wannan uban nata ya yanke cewa ya baka nasan koda ace iyayen su basu sani ba shi zaiyi bakin gwagwadon shawo kansu balle kuma ashe suma suna sane toni awa ince zanyi jayayya da ikon ubangiji”

AK ne ya fara tashi ya shige d’akin daya zuba kayan shi wanda yake nan k’asan sanadiyar kirar wayar shi da akayi,

“Ku tashi ku bamu waje zanyi magana dashi,” cewar Hajiya tana kallon su Moon,

Mikewa sukayi dukan su suka haura saman sai da ta tabbatar sun shige ta kuma kalli k’ofar d’akin AK taga a rufe yake sannan tayi k’asa da murya ta fara cewa,

“Tashi ka koma kan kujera” sai da ya koma kan kujerar sannan ta daura da cewa,

“Sannu fa da kokari d’annan wallahi nidai tunda uwata ta haifoni duniyar nan ban tab’a ganin mijin da bayan ya rabu da mace yake binta da alkhairi ba irinka, sannu kaji Allah dai ya k’ara arziki amma kam kayi hidima ga mota ga kud’ad’e ga kuma kyautar gida sukutun, nace to kardai kace kaji shiru ita Meenal din bata kira tayi maka godiya ba wallahi ba laifin ta bane laifina ne domin nice har yanzun ban gabatar mata da gidan a matsayin kyauta daga gareka ba,
Kasan halin Meenal sarai yar tutsuce tana sanin cewa daga wajen Kane kyautar gidan tana iya murje ido tace bata buk’ata shi yasa kawai na yanke hukuncin cewa zan bata ne a matsayin cewa kayan d’akin ta dana siyar ne na had’a da kudin daka bata nayi mata ciko na siya mata gidan nasan zatafi yin farin ciki da haka,
Daga baya idan ta gabatar ma da uban nata idan komai ya lafa sai in bud’e mata gaskiyar zancen, Sa’eed kuma ya fad’amin cewa baka son asan cewa kaine ka siya gidan da sunan ta dan haka ka kwantar da hankalin ka wannan sirrin babu maijin shi daga nan wajena kuma shima nasan bazai tona ba,
Sai batun Moon kuma nidai na baka goyon baya dari bisa dari sai dai bazan gaji dayi maka tuni ba nasan dai zuwa yanzun kasan kalar matar da kake aure atoh dan haka a daure a cigaba da kiyaye azkar sadaqa da kyauta a kuma dunga shan tsarin jiki duk da allah ke tsarewa amma kula da kaya dai yafi ban cigiya, ban kuma ce wai dan zaka auri jikata ita na gidan ka wulakanta taba koba komai ka dunga duba matsayin ta na uwar yaranta idan tayi ba dai daiba ka tsawatar mata kaine sama da ita, ita kuma Allah ya shirye ta tabar duk wasu abubuwan da basu dace ba Allah kuma ya baka ikon yin adalci a tsakanin ku,
Na fad’a maka dai da wuri nike son ayi komai dan had’awa nike so ayi dana shi wannan yayan nasu daya gama zazzageni a gaban ka, dan shike neman auren Kanwarka Aminatu shin ko wajen ka zamuzo neman auren nema kai Babban yaya?”

Hajiya ta tambaya da dariya a muryar ta,

“Ai hajiya indai shine na bashi Meenal ko gobe ya shirya yazo da goro kawai ni kuma zan d’aura musu aure,”

“Oh kace kaima gaban kanka zakayi kamar yanda shima ya daki k’irji wai shi mai k’anwa zai aura mata wanda take so, to ai shi nashi maganar bata shiga gida ba tukun amma da iyayen shi sun iso zasu kai zancen can gidan su, ai ka gane ita waccen da suka haura sama tare dasu Meenal din ko?”

“Ah ah ban ganeta ba gaskiya”

“Ash sha to kanwar kace itama d’iyar mamarku ta Abuja ce tunda sukazo da rasuwar mijin Raheenat ita bata koma ba ta tare a wajen takwarar ta Aminatu, idan kaje gidan Malam ma zakaga d’an uwan ta yana nan wani ustazu suna ce mishi Sheikh Naseer yaro mai hankali dashi ni burgeni yake da farko har nayi sha’awar had’ashi da Moon fa ashe ba rabon shi bace”

Dan murmushi Sarki “eh nasan shi Sheikh d’in ita ce dai ban wayeta ba,

Hirar ne sosai ya b’arke tsakanin Hajiya da Sarki suna zaune a falon har karfe 11 na dare ya gota, sai da Ak ya fito daga d’aki yake ce mishi,
“Sarki idan ka biyema Hajiya fa zaku kwana kuna hira ne idan kuma ka shirya kwanan gidan sirikai ga d’akina nan idan kun gama hirar sai ka shigo mu kwana tare,”

Agoge Sarki ya kalla yana mik’ewa tsaye, “kasan kwata kwata banyi zaton lokaci yaja haka ba ashe dare ya farayi ban sani ba kuma ko gida ban shiba, Hajiya bari in wuce nagode kwarai Allah ya k’ara girma da jinkiri mai albarkha”

“Ameen ta amsa dashi tana mai cewa ka gaishe min da uwar gida kwana biyu bamu had’u ba,
Ficewa sukayi shida AK daga falon sai da AK ya raka shi har wajen motar shi sukayi sallama ya tada motar ya fice daga gidan duk da cewa AK yace mishi ko ya kira mishi Moon suyi sallama ne shi kuma Sarkin yace ah ah ya barta kawai tagama hutun kukan son shi da tayi d’azun,

Falon ya koma bayan wucewar Sarki sai da ya kulle kofa kafin shima ya shige ciki kamar ya haura sama ga k’ara gano Meenal sai kuma ya hana kanshi ya wuce nashi d’akin shima ya rufe k’ofa.

 

*Ummiee ce*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button