Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 38

Sponsored Links

โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ
*BOOK 2*

*PAGE 38*

A daidai k’ofar falon Hajiyan yaja ya coge hab’ar shi ya dafe kamar mai tunani kafin yana wani fusgewa cike da basarwa yace,
“Ni anyama zan shiga nifa da nace sai nayi sati ban shiga falon nan ba kuma adadin kwanakin satin basu cika ba har yanzun dan haka kije kawai saida safe, damuwar ki ai dama na rashin ganina ne koh to gani kin ganni hankali ya kwanta”
Juyawa yayi da niyar barin wajen ita kuma da azama ta tari gaban shi, boyayyar murmushin da bata bayyana a fuskar shiba yayi dan dama yayi hakan ne dan yaga shin zata hana shi tafiya ko zata tsaida shin? Da gaske dai itama ta kamu ashe? Yake tambayar zuciyar shi, a fili kuma sai ya fuske yake tambayar ta da cewa,

“Yane akwai wani abun ne kuma?” duk’ar da kanta tayi tana wasa da yan yatsunta batareda ta d’ago sun had’a idoba tace,
“To bakai bane kawai daga zuwan ka ko zama bamuyi ba zaka wani ce zaka tafi, kuma fa ku lafiyata baka tambaya ba bayan kayi kusan sati ban ganka ba Allah kuwa har ciwo saida na kusayi”
Subhanallah ta furta tana rufe baki dan Wallahi subutar bakine ba abunda taso cewa kenan ba, wai miye haka yake faruwa da ita ne duk tabi ta wani rikice a gaban shi kamar wata sabon shigar soyayya salon duk ya gama raina ta,
Daure fuska tayi ta kauda kai gefe dan karma ya raina ta ehe,
Takowa yayi zuwa inda take ya rik’o hannayen ta duk da yanda take k’okarin kwace wa ya hanata,
“Fad’amin meya sameki da baki ganni ba? Baki da lafiya shine bazaki kirani ba? Meke miki ciwo yanzun ko kin warke? Idan baki da lafiya ki dunga kirana kina fad’amin kinji ni kuma komai nikeyi zan barshine in dawo inzo in dubaki lafiyar ki tafiye min komai karki k’ara yarda kiyimin wasa da lafiyar ki” hannun shi d’aya yakai kan wuyanta wai shi nan a dole so yake yaji ko jikin ta akwai zafi,

Baya ta matsa kad’an shi mai yasa ya kasa gane cewa ita bata son yana garajen kai hannun shi jikin ta ne? Duk sanda ya tab’a ta jikinta sanyi kalau yakeyi kamar an cirota daga cikin k’ankara,

“Nifa na warke kuma nace ka dena tab’ani bana son,”

“Kin warke?”ya tambaya yana binta da kallo bayan ya cire hannun shi a wuyan nata,

“Na warke fa,”

“To sannu Allah ya k’ara sauk’i yanzun kije ki kwanta saida safe”

Ita da take cewa bata son yana tab’ata sai gashi ta rik’o hannun shi a shagwabe, “to zaka wuce kuma baka shiga cikin ba, nayi maka girki fa ko bazakaci abincin dana b’ata lokaci na girka maka ba?” ta tambaya a marairaice,

Da mamaki yake kallon ta kafin yace “ni kikayi ma girki wai?”

Shiru tayi ba amsa,

“Me kika girka min koda yike koma menene ci zanyi tunda ke kikayi, ashe dai ana sona har haka amma da sharad’i bazan shiga inciba har sai kinyi alqawarin cewa zaki bani abincin a baki in kuma ba haka ba ink’i shiga wallahi” ya karasa fad’a yana d’aure fuska,

“Kai dan Allah” ta fad’a tana bubbuga kafa a kasa,
Shi kuma saiya kauda kanshi gefe kamar bai ganiba,
“Nidai dan Allah muje gaskiya in bakaci ba zanji babu dad’i kuma zanyi fushi, indai zakaci naji zan baka a bakin”

“Kinyi alqawari? Kuma kar ganin idon Hajiya yasa kice bazaki bani ba idan mun shiga” ya fad’a yana kamo hannun ta suka shiga falon da sallama a tare,

Gilashin dake taimaka ma Hajiya wajen ganin kananun rubutun dake cikin littafin addu’oin dake hannun ta tana dubawa tasa yar tsarta ta sauke zuwa kan hancin ta, ta saman gilashin taci gaba da kallon su bayan ta amsa sallamar da sukayi girgiza kai tayi tana tab’e baki kafin ta gyara zaman gilashin taci gaba da karatun ta,
AK bai saki hannun Meenal ba har suka k’araso inda Hajiya take kafin ita Meenal din ta zame hannun ta a cikin nashi ta wuce kitchen ta fara kwaso abincin data shirya mishi ta barshi suna gaisawa da Hajiya, fira suke a tsakanin su akan isowar su Abba Ahmad da su Baba Usman dama sauran ahalin gidan da zasu iso gobe,
Sai da ta gama shirya abincin akan dinning kafin ta dawo yake, “na gama shirya maka abincin fa”

“Ikon Allah wato yan magana dai duk abunda zasu fad’a akan dai dai yake, cewa fa sukayi inda ranka kasha kallo, yau ko nice na tabbatar da haka yanzun nan dama ke takara hana kanki sukunin da kikayi daga dawowar ki d’azun kika shige cikin kitchen kika fara girke girke dan munafunci shi kike dafama abinci? Ina fa zaune a falon nan kika kammala amma ko tayi bakiyi min ba alhalin naga dai kayan abincin ba ubanki malam bane ya aiko min dashi, aini tunda naga kin dawo gidan nan da wuri yau dama nasan a rina wai an saci zanin mahaukaciya ashe d’an gudun hijira ne yake tafe, to duk dai ku gama munafuncin ku insha Allah gobe iyayen ku suna isowa zan iza keyar ku gara su tafi can su amso auren ko tarewa ne ayi daga baya dan nidai bazaku jawomin sabon zance da karkata kaiba ina zaman zamana ku maisheni tsohuwar kawai wallahi,
Kai kuma ina fad’amaka su kud’ad’en nan da kake ta faman boyon su a cikin asusun bankin ka gara ka fiddasu kayi k’okarin kammala ginin can da kaketa shiririta har yanzun ka kasa kammala shi in kuma wancan gidan hayan zamu kai maka matar duk salmakal, nidai bazan iya gani ba bazaku jamin makantar da ban shirya ma zuwan ta ba, kuma nima ki dibo min tuwon ki kawo min shi zanci”

Sim sim Meenal ta wuce ta d’ibo ma Hajiya tuwon ta kawo mata,

“Kin daiji kunya meenal nan inda nice nace ina son kimin tuwon nan na tabbata k’ememe zakiyi amma shi kin iya zagewa kika shiga kitchen kika girka mishi”

Ita dai Meenal bata kulata ba ta juya ta koma kan dinning d’in surutun Hajiyar ne yasa Sultana saukowa,

“Hajiya keda waye kike fad’a da daren nan?”
“Nida wa kuwa banda wadan nan su biyun, koda yike kema ai duk jirgi guda ya kwaso ku kwashi kafafuwan ki kiyi gaba ki bani waje”

“Allah ya baki hakuri Hajiyar mu, barka da zuwa yayan mu ya kwana biyu”

“Lafiya lau sultana ya kike ya shirye shiryen bikin?”
“Alhamdulillah ya naku kuma?”

“Mun gode Allah zo in aikeki d’akina please”
Karasawa kusa dashi tayi shi kuma ya cire key din d’akin ya bata,
“Sorry akwai kaya a falo kiyi ma cikin su Kabir magana wani ya tayaki kwaso kayan ku shigo dasu”

Amsar key d’in tayi ta fice shi kuma ya gyara zama ya fuskanci Meenal “Bismillah na shirya”ya fad’a yana bude bakin shi alamun ita yake jira,
Sai da ta saci kallon Hajiya ta tabbatar da cewa hankalin ta baya kansu kafin ta dawo da hankalin ta kanshi ta fara bashi tuwon a baki,

Yana cikin cin abincin Sultana ta dawo ita da Isah ne suka kwaso kayan dan Kabir baya gidan,

“Ku ajiye kayan anan” ya fad’a daga inda yake,

Bayan ya gama cin abincin falon ya koma ita kuma Meenal ta kwashe kayan takai kitchen ta gyara wajen, ware kayan yayi ya tura ma Hajiya nata gabanta “Hajiya ga naki kayan cin biki ne kuma ga naku nan”

“Ah dad’ina dakai wani lokacin akwai iya kamantawa Allah dai yasa ba’a nuna min banbanci ba, da dai ni kad’ai kake ma abu amma yanzun tunda ta kwara ta dawo gidan nan muke zaman kishiyoyi sai ka mata abu sai goma da kudin ka ni banci nera biyar taka ba,
Ke sultana matso min da kayan nan kusa dan idan na duba naga naku yafi nawa tsada canzawa zanyi atoh”

Bude kayan sukayi kayane tun daga kan atamfa leshi shadda ga kuma takalma da jakunkuna a cikin kayan su Meenal ko harda su d’an kune da sauran kayan kwalliya na mata godiya duka sukayi Hajiya kuma na addu’ar allah ya kara arziki nata kayan ta fara kwashewa tayi ciki dasu kafin Sultana itama ta kwashi nasu ta haye sama ta ba masoyan waje dan su samu damar tattaunawa da kyau,

Suna cikin hirar ne kuma wayarta tayi k’ara wanda bata yi tsammanin kiran shi a dai dai wannan lokacin bane ya kirata, ba kowa bane kuma face Sarki,

Tayi kamar bazata d’auka ba kasancewar AK dake wajen sai kuma ta hasaso rashin d’aukar wayar kuma yana iya sawa ya zargi wani abun dan haka sai kawai ta dake ta d’auki wayar bayan tama AK “Ya’ya bari in amsa wannan kiran”

“Ki gama wayar ki fad’amin dalilin da yasa har yanzun kike kirana da suna Ya’ya bayan ga sunaye nan masu dad’i da masoya ke kiran junan su amma ni sai dai ki wani ce Ya’ya ko dad’in ji babu”

“Assalamu Alaikum” ta fad’a a yayinda ta d’auki wayar gaisuwa suka fara gabatar wa, kafin sarki yace,

“Nayi laifi shi yasa kike fushi dani koh?”

Da sauri ta amsa da cewa “ah ah wallahi Ya’ya ba haka bane abubuwa ne dai suka d’an shamin kai shi yasa ban kira ba amma dama ina da niyyar kira inyi maka fatan alkhairi na tarewa a sabon gida”

“Kina gida ne?” Ya tambaya yana katseta,

“Eh ina gida” ta fad’a tana Satan kallon AK wanda shima jin tace tana gidane yasa ya kalleta,

“Ok to zamu iso gidan anjima kad’an nida kyautar da kikaimin Allah yasa dai Hajiya batayi bacci ba dan ina son mu gaisa”

“Da gaske kakeyi Ya’ya? Kai amma ko wallahi naji dad’i sosai ba damuwa sai kun iso ai Hajiya ko tayi bacci ma ina iya taso maka ita balle kuma idonta biyu ma yanzun haka”

Yanke wayar sukayi duka su biyun ita ko dad’i kawai takeji,
Kenan hakan yana nufin Sarki ya amshi Moon a matsayin yana son ta,

“Keda waye a waya?”
“Nida Ya Sarki ne” ta fad’a kanta tsaye,

Daure fuskar shi yayi shi kuma, “wani Sarkin?”
Kallon shi tayi da mamaki wani irin tambaya ne wannan kuma, shine zaice mata wani Sarki, aiko ita ta fishi zama yarta kife dan haka cikin idon shi ta kalla ta kuma bashi amsa da cewa,

“Ya Sarki dai daka sani tsohon mijina shine zaizo” ta fuske abinta,

“Me zai kawo shi gidan nan da daren nan ne naga sai wani rawar kai kikeyi?”
“Matar dana zab’a mishi ya aura zai kawo min mu gaisa kuma daga nan zai nemi iri a wajen Hajiya bakaji yace yana son su gaisa ba? ”

“Ni ban gane me kike nufi ba”

“Ok ok to bari in maka gwari gwari, kana Jina?”

“Eh ina jinki”

“Yauwa kagani ko tun shekarun baya can kafin ma insan cewa za’a had’ani aure da shi a cikin k’awayena akwai wacce ta nuna tana son shi dan yana burgeta tun a lokacin, da farko nayi zaton wasa takeyi amma yau da gobe yanda take yawan tambayar shi da kuma sako min labarin shi idan muna hira da ita a waya duk da cewa ba gari d’aya muke ba a hankali saina fahimci cewa ta kamu da son shi amma azatona bata gane hakan ba ko kuma dai tana boye min, kai daga karshe dai na gane da gaske son shi takeyi duk da cewa tasan yana da mata harda yara amma bata damuba tace zata zauna dashi a hakan sai gashi kwatsam rana d’aya mafarkin ta ya ruguje daga sanda aurena dashi ya tabbata,
Kasan me?”

“Me zan sani kuwa kici gaba da bani labari kawai”

“A lokacin na tausaya mata duk da cewa nima din abin tausayin ce lokacin, kaga dai tanaji tana gani ta rasa masoyin da take so tun bata riga ta gabatar da kanta a wajen shiba, ni kuma sai aka k’ak’aba min shi duk da nasan kawata na son shi amma babu yanda na iya, kasan har hakuri saida ta bani akan cewa da tasan cewa shine zai zama mijina da bazata tab’a yarda ta furta tana son shiba, kuma lokacin da nike gidan shi bata tab’a zuwa gidan sai baya nan saboda bata son su had’u shi yasa ni kuma da muka rabu ya rok’eni in fad’a mishi abunda nike so sai na bashi hoton ta da address dinta harma da number ta akan cewa idan yaji yana sonta ya neme ta to kaga ashe ya nemeta har sun sasanta kansu shine zai kawo ta in warware mata dan nasan dole ko ba komai zataji wani iri kar ace tana soyayya da mijin daya rabu da kawarta”

“Amma dake da ita duk yarinta ke damun ku” AK ya fad’a yana tab’e baki,

“Kai ya’ya yarinta kuma? Halacci dai nayi mata dan bashi da mugun halin da za’akishi”

“Wacece ita hala?”

Kauda kanta gefe tayi, “ai idan na fad’a maka fad’a zakayi tunda gashi yanzun ma kace wai yarinta ke damun mu”

“Waye yace miki zanyi fad’a nid’in? Ai nima nasan zafin soyayya yanzun dan haka bazanga laifin kuba dukan ku, ke abunda kikayi kin kyauta shi kuma Allah yasa yasota da gaskiya har cikin zuciyar shi kar yayi mata kallon macen da aka cusa mishi kamar dai yanda ya miki”

“Ah ah bazaiyi haka ba insha Allah,”

“Wacece nace ko bazaki fad’amin nima in goya muku baya ba?”

“Moon”

“Kina nufin Maimoon dai na Baba Usman?”

“Eh” girgiza kai yayi kafin yace “allah ya shirye ku yaran nan ashe kun dad’e da k’onewa an kara ne kawai babu wanda yayi a cikin mu”

“Kai dan Allah waima konewa, nidai dan Allah kasa baki a maganar nan nasan idan Hajiya ta amince dole kowa ya yarda kaji?”

“Ke wai mutumin da ba’a tabbatar da lafiyan shi bane zaki had’ashi aure da yar uwar ki?”

“Lafiyan shi kalau mana waye yace maka bashi da lafiya ne?”

“Oh lafiyar ce kenen yasa yayi ta kallon ki uwa hoto….. “Katse maganar yayi bai k’arasa ba itama kuma sai kawai ta basar,

Sukaci gaba da hira tana mishi magiya akan dan Allah yasa baki Hajiya ta amince,

*** A unguwar malamai ko Sarki yana isowa Zaria ya kira Moon a waya cewa ya shigo tana ina ne?
Yanke wayar tayi sai ta tura mishi text cewa tana gidan su Meelat amma yanzun zata ajiye Maryam a gida dan motar meenal wanda shi Sarkin ya bata tana hannun Moon d’in da ita suketa zirga zirga ita da Sultana, idan ta ajiye Maryam zata kira shi sai ya fad’a mata inda zata same shi dan gaskiya a tsorace take bata son wani ya gansu a tare,

Bayan ta sauke maryam a gida ta juyo a k’ofar gidan shi ta sameshi shima a cikin nashi motar kamar yanda yace mata zai jirata a wajen, bata fito daga motar ba ya kunna nashi motar yayi gaba ita kuma ta dunga binshi a baya har suka fita daga cikin unguwar suka kama hanyar tudun wada, horn ta dunga danna mishi tana son ya tsaya dan tana son taji ina zai kaita badai gidan Hajiya ba amma ya shareta ta kira shi a waya yana d’auka sai cewa yayi ta kwantar da hankalin ta tabiyo shi suje kawai,
Ita dai a babu yanda zatayi ne ta dunga binshi kila ya lura da tana cikin furgici shi yasa ya canza hanya ba wanda ita ta sani yabi ba kafin ta ankara dai kawai tagan su a bakin gate d’in gidan Hajiya ne bai tsaya a waje ba horn yayi aka bude mishi gate ganin motar Meenal a bayan nashi ne kuma yasa su Isah basu tambaye shi wajen wa yazo ba tunda tare yake da yar gida,
A harabar gidan dukan su suka nemi waje suka faka shine ya fara kashe tashi motar ya fito ya koma motar da Moon ke ciki dan ta kasa kashe motar balle ta fito,
Sak’eยฒ kawai takeyi, me Sarki yakeyi haka da zai jawota suzo gidan nan bayan yasan Meenal tana nan, gefen mai zaman banza ya bud’e ya shiga ya zauna,

“Hajiyata idonki kenan, to barka da dare ya gajiyar hidin dimu ai da nace to Sarki kuma laifin me yayi tunda gimbiyar shi ta baro kudu zuwa arewa babu kira ba sak’o? Ashe dai ina da sauran gata ba’a manta dani ba,
Karki damu kanki cewa zakiyi wani dogon tunani akan dalilin zuwan mu nan, dafarko dai nazo gaisheda Hajiya ne ina kuma son gabatar da kaina a gaban ta kafin Allah yayi ma su Baba Usman isowa gobe, na biyu kuma nazo ganin kanwata ce ina son kuma tasa baki ko zaki yarda da batun neman aurena a wajen ki ki yarda cewa ba yaudaran ki zanyi ba nasan duk wannan nukuยฒn da kikeyi saboda Meenal kikeyi abunda baki sani ba shine da yardar Meenal na kawo kaina gaban ki, sai da na fara rokon alfarma a wajen ta akan tamin hanyar yanda zan sameki tunda nidai ina sonki kuma addini bai haramta aure a tsakanin muba ita tabani number address dama sauran bayanai a kanki dan haka kima dena damun kanki da zaton ko kinci amana ko wani abun makamancin haka nine nan na ganki ina so ba cusa min ke akayi ba”

(Ku gane Sarki ya boye mata gaskiya ne saboda kartaji ba dad’i, bawai da wani nufin daban ya juya labarin ba)

“Ina fatan cewa yanzun da kikaji gaskiyar komai bazaki k’ara hanani gabatar da kaina ko kuma kici gaba da boye soyayyar muba?”

D’ago kanta tayi ta kalle shi, “dama Meenal tasan komai?”

“Eh ta sani”

“To amma bata nuna min tasani ba”

“Saboda bata son kiji babu dad’i shi yasa”

“To ya akayi kasan su Baba zasu iso gobe?”

“Saboda na riga na gabatar da kaina tun a Lagos yanzun haka Abban ku na Saudia ake jira yana isowa komai zai kammala ina fatan kinyi farin ciki dajin hakan?”

Kafafuwan ta ta cusa a tsakanin cinyoyin ta tana boyewa murmushi kwance a fuskarta,

“Oh kunyana kike ji yanzun kuma, to bari kiji nidai gaskiya bazan yarda aja lokaci mai tsayi ba dan ina bukatar matata, sannan kuma zakiyi hak’uri dan idan Allah ya nufa an d’aura auren bazaki zauna a Lagos ba Kaduna zaki zauna tare da uwar gidan ki da yaranta bazan hanaki aiki ba sai dai ina fatan aikin ki bazai sa ki gaza samun lokacin da zaki bani kulawar daya dace ba?”
Shiru tayi bata amsa mishi ba,

Wayar shi ya ciro ya kara kiran Meenal ya shaida mata cewa suna harabar gidan,

“Ya’ya sun iso” take fad’ama AK,

“Ai naji isowar su tun d’azun kuma nace miki ki dena kirana ya’ya koh”

“To da wani sunan zan kiraka?”

“Jeki shigo dashi zamu zab’i sunan daga baya”

“To muje tare”

Tare suka fita tunda suka fito kuma AK ya kama hannun Meenal din ya runtse cikin nashi tayi tayi ya sake mata hannu yak’i,

“Oh ke bakya son shima ya gane cewa kema kin samu mijin aure ne?”

Koda suka isa hannu AK da Sarki suka ba juna sukayi musabaha ko wannen su fuska kadaran kadahan babu fushi kuma babu sakewa, a can gefe Moon ta lab’e dan daga AK har Meenal din kunyar su takeji wallahi,
AK ne ya musu jagora har falon na Hajiya suna shiga kuma Moon ta gudu sama Meenal kuma ta take mata baya tana tsokanarta da cewa ai dama ta fad’a mata cewa koma miye take boyewa idan tayi wari zasuji,

“Da gaske dai ashe kaine sirikin nawa?” AK ya fad’a bayan sun zauna,
Karamin dariya shima Sarki yayi kafin ya maida mishi martani da cewa,
“Kamar yanda kaima gashi da gaske naga alaman kana shirin zama sirikina, ko ka manta ita Meenal din kanwata ce, kaga kenan komai yazo da sauk’i sai muyi bani mandaqo in baka Manda kai anan kaine zaka jagoranci zamowana siriki a gidan ni kuma sai in maka jagoranci nima a gidan mu kaga komai ya tafi dai dai kenan”

Dariya AK yayi kafin yace “ina fatan dai ka shirya fuskantar Hajiya gaba da gaba koh? Dan kasan itace boss gaka kuma jami’in tsaro balle ince ka bata cin hanci dan ina fad’a maka matar nan yar rashawa ce”

Dariya Sarki “karkaji komai na riga na shirya fuskantar kowa dama qalubalen daga kanwar kace itama nasan yanzun kam na gama da gefen ta,”

“To ai ba laifi indai ka shirya to nidai na baka dan koni ina iya aurar maka da ita”‘cewar AK,

“Allah ko mutumina? To in haka ne nima na baka uwar Malam a matsayina na Babban yayan ta ka fito kawai idan ka shirya” Sarki ya fad’a yana bashi hannu suka kashe,

Sultana ce ta sauko kasan ita nan a dole wai kitchen zataje alhalin kuma tsabar gulma ne ya fiddo ta Sarki take son gani dan labarin shi kawai takeji yau kuma gashi yazo har gida ina zata yarda wannan damar ta wuce ta bata sauko sun gaisa ba,

“Yauwa Sultana koma saman nan dan Allah kice ma Hajiya tayi bak’o”

“To” ta amsa dashi kafin ta mik’ama Sarki gaisuwa bayan ta k’are mishi kallo, juyawa tayi zuwa d’akin na Hajiya da Sallama ta bud’e k’ofar ta shiga,

“Me kuma ya faru na dawo d’akin ma bazaku barni in huta ba sai kun biyoni”

“Allah dai ya baki hakuri Hajiya dama Mai Jama’a ne yace in kiraki kinyi bak’o yana falo yana jiran ki, kamar dai saurayin Moon ne yazo gaishe ki dan tare da ita suke” tana gama fad’a mata ta fice daga d’akin,

Ita kuma Hajiya jin cewa saurayin Moon shi yasa bata b’ata lokaci ba ta ziro hijabi ta fito ita dai Allah ya sani tana matukar so taga ta aurar da jikokin nan nata, shi wannan din da yazo in dagaske ne ai dama kawai zata bashi ya turo iyayen shi ayi a wuce wajen dan dama ita Batama Moon din sha’awar auren Lagos,

Batayi saurin gane ko waye a falon ba har saida ta sauko ta nemi wajen zama ta zauna shi kuma sarki tana zama sai ya zamo daga kan kujerar shi ya fara gaishe ta,
Lafiya lau suka gaisa sai da ya koma ya zauna ta kare mishi kallo da kyau kafin ta maida kallonta kan AK ” kai Abdul nace wannan kamar d’an gidan uwar gida ko? Ina nufin tsohon mijin Meenal koba shi bane? To me kuma ya kawo shi nan? Nidai Sultana cemin tayi Saurayin Maimunatu ne yazo gaishe ni koshi wancan d’in ya wuce ne?.

 

*Ummiee ce*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button