Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 37

Sponsored Links

βšœοΈπŸ”±πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ”±βšœοΈ
*BOOK 2*

*PAGE 37*

Abun dai sai gashi kamar wasa amma kuma sai ya juye ya zama gaske domin dai tundaga ranar da AK yafice gidan a gaban ta bai k’ara yarda tayi tozali dashi ba domin gidan ya bari gaba d’aya yayi komawar shi Kaduna abinshi,
Ya zab’i yayi nesa da itane dan dukan su su sarara basai yana kusa da ita bane idan tayi wani abun zai gani har ranshi ya baci? To ya tafi ai sai taci Karen ta babu babbaka yanace itace a lokacin baya take tashin hankalin ta akan yan matan dake nuna cewa suna ra’ayin shi, wato ita harma ta samu damar kula wasu samarin harda basu damar zuwa har cikin gida su sameta alhalin shi ko ya nuna yana buk’atar keb’ewa da ita ta fito suyi hira a waje bata yarda shine zata zauna da wasu gardawa daga ita sai su a cikin falo wai sunan sunzo hira wajen ta, gaskiya dai yaji kishi matuk’a.
Dan haka tunda har ta b’ata mishi rai yayi rantsuwar bazai kulata ba har sai tayi biko dan yaji mai zafi ya daka domin ai ba mata kad’ai keyin yaji ba zai gani kwana nawa zai d’auketa ta sauke shegen girman kanta ta neme shi.

Bai k’ara kiran wayarta ba haka kuma ya soke aika mata sakon nin soyayyar daya saba tura mata sau uku a rana ma’ana safe rana dare,
Ku gane horon iyafa iya ita yake son horawa dan kuwa shidai yana da Sultana a gefe ita ke sanar dashi duk wani halin da Meenal din take ciki tun daga ranar daya d’auke mata wuta, idan yaso jin muryarta zai kira wayar Sultana idan kuma yana son ganin ta zai kira Sultana video call ita kuma sai tayi amfani da back camera ta hasko mishi sahibar nashi,

Ita ko Meenal Allah kad’ai yasan halin da take ciki domin dai duk yanda takai ga dannewa tana ta boyewa saida abin ya nuna a jikinta karsashin ta da walwalanta duk sai ya ragu laifin kanta kawai take gani da ace bata basu daman zuwa gidan ba da bazai gansu ba balle yayi fushi, gashi a banza ta b’ata mishi rai ta dalilin su alhalin shi kullum burin shi shine yaga ya faranta mata saboda dai kar tayi fushi, a d’an lokacin nan ba k’aramin sanya shi tayi a cikin ranta ba matsayi mafi kololuwa ta kaishi ta yanda batajin zata iya had’ashi da kowa gashi tun tafiya batayi nisa ba ita ta fara b’ata mishi rai dan haka duk sai tabi ta tsanagwami kanta,
So take ta kira shi taji yana ina wani hali yake ciki? Yana lafiya ko a’ah duk bata sani ba ashe ji da ganin shi da takeyi a kusa da itama rahma ne?
Yanzun da yayi nesa sai takejin kamar bata da lafiya duk ta rasa kuzari da kwanciyar hankalin ta,
To wai shi me yasa ma zaiyi fushi har haka ne?, inhar da gaske ya saurari hirar ta da ya Hashim kamar yanda yace ai ya kamata ya fahimci cewa su d’in dukan su basa gaban ta shi dai shi ta zab’a, wato shine yama tattara yabar mata gidan to ai shi kenan tunda haka ya zab’a yama dad’e bai tafi ba yafi ruwa gudu in yaso badai dan yaga
tana son shine yasa yake son ya jata a k’asa ba? To soyayyar taci uwata kuma kewa ai bata kisa dan haka can da yawar shi,
A wannan halin da take ciki haka ta dunga daurewa tana cigaba da nuna bata damuba suka cigaba da gudanar da sha’anin bikin su a unguwar malamai take uni saboda gyaran jikin da suma sukeyi dan yanzun basa zuwa yawo,su kuma su Maryam ganin shirun ta yayi yawa ne kuma basa ganin tana yawan amsa kira daga wajen AK kamar yanda suka saba sai ranar maryam ta gaji take tambayar ta ko sun samu matsala ne ita da mutumin nata?
Bata boye musu komai ba kaf abunda ya faru ta kwashe ta fad’a musu,

Ajiyar zuciya Maryam ta sauke bayan ta gama jin jawabin Meenal din,

“Bebs me yasa to baki kirashi kin bashi hak’uri tun ranar ba? Kema dai kinsan cewa ko waye dole zaiji babu dad’i”

“To me zance mishi idan na kira shi?” Ta tambaya da karyayyar murya dan Wallahi a dame take kwarai,

“In ma kina jin shakkun karki bashi hakuri ajin ki ya zube ne to ki kirashi idan ya d’auka sai ki basar kawai kice kin kirane kiji ya yake”
Meelat ce tayi magana wannan karan dan tasan tsabar jin kaine ya hana Meenal d’in kiran shi tun tuni,

“Sister don’t call him just send him a short text message,”cewar Sultana,

“Me yasa bazata kira shiba bayan kuma tsakani da Allah ita ce bata kyauta mishi ba ai kamata yayi ta kira ta bashi hak’uri tun sanda Abinda ya faru shine zakice ta tura mishi sak’o” Maryam ta fad’a tana jiran jin dalilin da yasa ita Sultanan tace kar Meenal ta kira shi,

“Will You please let me explain my self ko in barku da iyawar ku?” Sultanan ta fad’a tana wani shan kamshi, irin ita a dole tana nemar musu mafita,

“Ok muna jinki”suka fad’a a tare harda Moon wacce tunda suka fara hirar bata sa baki ba saboda ita damuwar da take ciki yaci uwar na Meenal ya shanye domin ita meenal ai tasan matsayin ta a wajen nata masoyin ko yau taso gabatar dashi a gaban iyayen ta kuma tasan da gudu zasu amince amma ita fa???

Gaba d’aya tun zuwanta komai yake shirin zama tarihi a tsakanin ta da Sarki, alaqar da taso ya yanke a tsakanin su tun tuni shine bai yanke ba sai yanzun da yasan cewa ya riga ya mata dashen son shi a cikin nata zuciyar!
Me yasa wai maza basa da adalci ne? Wannan abun shita gudarma kanta tun farko shine kuma yasa tun farko tak’i sakin jiki dashi tayi ta d’ariΒ² tana kakkaucewa dan dai ya rabu da ita amma yak’iya,
Bai barta ta huta ba har saida ya riga ya gama siye zuciyar ta, bikin Meelat yau saura kwana biyu sannan ita kuma kwana 7 din da Baba Usman ya bata tuni ta cinye shi, jiya da dare kuma shida kanshi ya d’auki waya ya kirata yana k’arayi mata tuni akan maganar su cewa karta manta dai ta fad’ama duk wanda ta tsayar cewa ya shirya turo iyayen shi cikin satin nan suzo su gabatar da kansu,
Ta tabbatar da cewa duk wani bak’on da zaizo ma Hajiya biki tabbas jibi idan Allah ya kaimu kowa zai halarto nan Zaria to wani amsa zata ba iyayen ta a sa’ilin da suka zaunar da ita danjin wata tsayar a matsayin mijin auren ta?
Wallahi tana son Sarki bata tabbatar da cewa ta kamu da mugun son shiba sai bayan zuwan ta garin nan da shi kuma yayi dif ya d’auke mata wuta ba kira ba sak’o,
To wanda ya wofantar da ita irin haka taya zata gabatar dashi ma iyayen ta? Idan suka kirashi shi kuma yanuna musu cewa baya ra’ayin ta ya zatayi kenan,
Me yasa rayuwarta ya juye upside down cikin kankanin lokaci haka?,
Tayi shiru tana sauraron shawarar su Sultana zuwa ga Meenal ne dan tasan ba iya Meenal dince kad’ai zata amfanu ba itama tana buk’atar shawarar sai dai kuma ta yanda zata bud’e baki ta shaida ma Aminan nata halin da take cikina ta gagara yin hakan duk da cewa ita Meenal din bata boye mata komai na alaqar ta da AK ba ta kuma tayata murna domin duk wanda yaga masoyan biyu yasan sun dace da juna kwarai, sai dai ita kuma ga abin yana matukar damunta a cikin zuciya amma ta kasa sharing din shi ma kowa a cikin su, to mema zatace musu bayan shi dayace yana son nata yanzun kuma ya juya mata baya,

***
Daurawa Sultana tayi da cewa,
“Tsaya kiji sister kin san dai ba kece budurwa ta farko da ta fara muna mishi soyayya ba, dan haka na tabbata yasha jin kalaman ban hakuri a wajen yan mata daban daban tunda ya saba kullum suke neman shi dan haka komai yayi gani zaiyi akan dai dai yayi shi,
Idan kika sake kema kika shiga sahun su kika ce a duk sanda kuka samu sab’ani haka kema zaki dunga jera mishi kira dan ki shawo kanshi tofa gani zaiyi baki da banbanci dasu,
Ki saurareni da kyau, bawai ina nufin cewa koda ace kece kikayi laifi kiyi mursisi ba, ah ah in kinyi laifi dole ki bayar da hakuri amma bada rawar jiki ba, ke macece kina da naki darajar dole kuma ki rik’e darajar ki, dan haka dole salon ban hakurin ki ya banbanta, akwai banbanci wajen ban hakuri tsakanin saurayi da budurwa da kuma mata da miji, ke yanzun bakuyi aure ba dan haka salon saurayi da budurwa zamu d’auka, kamar yanda nace d’azun sak’on text zaki tura yanzun ki d’auki wayar ki, ba rubutu mai tsayi zakiyi ba ki rubuta mishi cewa (kana lafiya) sai ki tura mishi,
Idan ya maido amsa hakan yana nufin cewa fushin nashi bamai nisan zango bane, idan kuma mukaji shiru sai muje mataki na gaba ina fatan kun ganeπŸ€·πŸ»β€β™€οΈ”
Ta k’arasa fad’a tana kai gorar fanta bakin ta ta kurb’a,
A yayinda Meenal ta d’auki wayar ta tana rubutu itama Moon nata wayar ta d’auka ta rubuta same abinda Sultana tace ta tura ma Sarki itama kamar yanda Meenal ta tura ma AK,

Ita ko Meelat tasowa tayi tsam ta zauna a inda Sultana take zaune tana jiran Meenal ta cika umarni ta k’ara d’aura mata wani karatun,
Dafa kad’unta Meelat tayi “Sultana a ina duk kika san wad’an nan abubuwan? Abubuwan da kikeyi suna bani mamaki da kuma d’aure min kai manyan cen ki yayi yawa”

Hannun Meelat din sultana ta kama ta sauke shi daga kan kafad’arta, tana yatsina fuska tace “ku dai da kuke son mai da kanku baya sai kuyi ta zama waye yace muku iya ilimin boko da islamiya kad’ai mace take buk’ata dan ta rayu cikin salama ne?
Baku san dole mutum yana bukatar ilimin zama da mutane ba, to ilimin zama da mutane ne wannan domin yana da kyau kasan dawa kake zaune ko dawa zaka zauna dan kaci maganin zama dashi,
AK bai tab’a soyayyar gaskiya da gaskiya ba sai a yanzun Meenal itace first love d’in shi amma sai wasa takeyi da damarta ta kasa gane cewa abubuwan da takeyi shi Sabon abune a wajen shi domin dai tsayin rayuwar shi ya saba mata ke kod’ashi suna kware mishi,
Sai gashi yanzun da take da damar d’aurashi akan nata tarbiyar ya kuma biyu mata yanda take so shegen wauta yasa tun tafiyar batayi nisa ba tana ta faman kwafsawa, wallahi ina jiye miki kar abubuwan da kike mishi susa yayi dana sanin fad’awa soyayyar ki…. ”

Katseta Meenal din tayi cikin fushi da cewa,

“To ni uban me nayi mishi kedai dama tuntuni na gane kinfi son shi dani” wayarta da yayi k’arar shigowar message ne ya katseta itama har rige rige sukeyi wajen d’aukar wayar su duba ko sakon shine ya shigo,
Maryam ce tayi nasarar d’aukar wayar,

“Wallahi shine” ta fad’a har hannun ta yana rawa a yayin bud’e sakon,

“Did you miss me?”

Shine abunda ya tura, dan haka a fili Maryam ta karanta dukan su suna sauraren ta,

“Kinyi kewar shi? ” itama Sultana ta maimata da k’aramar dariya a muryar ta,
“Wallahi AK yana sonki sosai Meenal karki yarda kiyi sakacin da zaki rasa shi kinga nifa tsayin lokacin nan tsumayin kira ko sak’on ki kawai yakeyi gashi dai kin gani sakon ki na isa gareki ya dawo miki da martani alamun da ke nuna shima yana cikin kewar ki”

Rufe fuska Meenal tayi da tafukan hannayen ta tana dariyar jin dad’i, koba komai tunda har ya dawo mata da amsa tasan cewa yana lafiya dama damuwarta tasan ya yake,
Daga gefen Moon itama nata amsan Sarki ya dawo mata dashi ga abunda nashi sakon ya kunsa shi kuma,

“I miss you soo much My Moon please allow me to come and see you, can i call to hear your voice now please”
Yalwataccen murmushi ne ya bayyana a fuskarta itama, sai dai bata bashi amsa ba tana jiran jin tabakin sultana tukun na,
D’aurawa Sultanan tayi da cewa yanzun dai tunda mun tabbatar yayi kewa shima to ki gyale shi karki maida mishi ko wani amsa mu bashi mintoci mu gani ko zai k’ara turo wani sak’on”

“Kuma😳 to idan kuma ya k’arayin fushi fa?” Meenal din ta fad’a tana kallon Sultana a marairaice,

“Bazaiyi fushi ba ina mai tabbatar miki da cewa kodai ya kiraki ko kuma ya turo wani sak’on”

Kamar yanda Meenal ta natsu tana jiran tsammani haka ita ma Moon dukan su tsammanin suke jira, maryam ce ta yanke shirun da cewa “Sultana kina gani har hanji ne?”

Dariya sosai Sultanan ta fashe dashi, “ni kuna bani mamaki wallahi”

“Ah ah kedai kike bamu mamaki abin mamaki kuma wai a hakan baki da tsayayyen saurayi to me kike jira” Moon ta tambaya,

“I am waiting for Mr right, nima mijina nike son in aura kamar ku dai wanda bazaiji nauyin ko kunyar nuna kaunar da yake min a ko ina ba kun gane ai dan nidai bana son ustazu wayayyen namiji nike so shi yasa har yanzun ban gama tantancewa ba, kunsan kwanaki wani abokin Ya Sheikh ne yaxo wai shi nan ala dole ni yake so” fashewa tayi da dariya tana dukan cinya tace “wai wai wai wayaga Sultana matar ustazu ninja kenan Allah dai ya raba bawa da wahala” dariyar suma suka tayata,

Moon ce ta amsa da cewa “kai gaskiya sultana kuna fama da wancan yayan naku, wai Sheikh fa in fad’a muku tunda na sauka a gidan nan wallahi ko sau d’aya bai yarda mun tab’a had’a ido ba, ke ko a hanya muka had’ufa duk’ar da kanshi yake shekaran jiyama wai harda Fauxieyerh yayi wai me yasa ni bana sa hijjab idan zan fita kuma wallahi yanzun ya dena zuwa sashen mommy Hauwa wai saboda ni bak’uwa ce, gaskiya dai yayan nan naku sufofin yan aljannah sak gareshi Allah dai ya bashi mata dai dai shi”
Hirar Sheikh din suka d’auko sukaci gaba da caccakan shi sultana tana basu labarin abokin shi da idan zaizo hira wajen ta saiya kwaso littafan addini wai da hirar banzan da zasuyi gara ya d’aura mata karatu abudai kamar a zamanin annabawa,
Suna cikin hirar ne wayar Meenal ya k’arayin k’ara sak’on AK ne ya k’ara shigowa wannan karon ma,

“Tun ba’ayi auren ba har kin fara yaji daga tudun wada zuwa unguwar malamai, to karki kiyi dare da yawa yau ki dawo da wuri I love you too” ya rubuta daga k’arshe,

“Hohoho dan Allah kuzo kuga yanda ake gudanar da wata sassanyar soyayya anan to wallahi yau nikam gidan Hajiya nika kwana yo ina dalili zan tare anan ga inda ake shan madarar love jama’a karfe nawa yanzun?”cewar Sultana

Shiko Sarki cewa yayi,

“ki shirya tarbata ayau idan na iso zan kiraki see you soon”
Hohoho dad’i kamar ya sumar da Moon haka ta dunga ji murmushin fuskarta kwata kwata yak’i d’aukewa,

“Kai ku tsaya! Waiku dan Allah baku lura da Moon ba wallahi akwai abunda take boye mana bata so mu sani tunda tazo na lura da hakan yanzun kuma ku kalli yanda take murmushi barrister me kike b’oyewa ne ko kema kin rufta cikin kogin ne?”
Maryam ta tambaya tana kada kai da nuna Moon din da yatsa,

“Yarsa ido kawai ke dai kika sani ni babu wani abunda yake damuna”

Meenal ce ta amsa da cewa “dan allah kyaleta ai kallonta kawai nake ki barta idan tayi wari ai zamuji yarinya in ma fargaban aure kike gara ki bari dan tunda Hajiya ta matsa kema kin san ba fashi gara ma ki zayyano mana naki samarin mu bajesu a teburin shawara mu tayaki zab’e atoh in kuma babu ni zan miki mijin”

Ita dai Moon shiru ta musu bata kulasu ba lallai yau idan Allah yasa Sarki ya iso lafiya ga da ga zasuyi shida ita tagaji da boye boye matsayin ta kawai take son sani a yau basai gobe ba,

Anayin Sallan Magrib Sultana da Meenal suka wuce tudun wada, ita kuma Moon cigaba da zama a gidan su Meelat tayi saboda idan ta koma gidan Malam bata san yanda zatayi ta fito su had’u da Sarki ba dan ko babu komai itama bazata yarda wani yagan su tare ba, ta kuma tura mishi sak’on Allah ya kawo shi lafiya,

A gidan Hajiya ko su Meenal suna isa Sultana tayi mata jagora suka shiga kitchen shinkafa suka samu an girka a gidan dan haka sai ta d’aura mishi tuwo raba hannu sukayi sultana ta dafa tuwon na masara ita kuma ta mishi miyar kub’ewa d’anye bayan sun kammala komai sama suka haura ita dai Hajiya kallon su kawai takeyi bata tambayesu dalilin shigar su kitchen ba balle suce ta fiye gulma gyara zaman ta dai tayi da kyau a falon ta dan tasan dai in ma bak’o zasuyi dole gidan zaizo dan tunda taga Meenal ta dawo gidan da wuri tasan ba’a banza ba,

Kwalliya na musamman yau Sultana tasa Meenal tayi itace kuma ta zab’ar mata kayan da zata sanya atamfa d’inkin riga da siketa ta kuma gyara mata fuska da kwalliya duk da kwalliyar bamai yawa bane daga hoda mascara sai jan baki Sultana tayi tayi ta sanya kwalli ita kuma tace a’ah wai bata son ta zaqe da yawa ya raina ta, k’in Saukowa k’asan sukayi sukaci gaba da zaman su a d’aki Sultana tana k’ara ba Meenal d’in shawarwari,

Karfe 9 saura sak’o daga AK ya shigo wayarta,

“Ki fito ki sameni nan da minti biyu a haraba”
Sultana ta mik’ama wayar bayan ta gama karantawa jiki na rawa ta tashi ta isa gaban mirror soson shafa hoda ta d’auka tad’an k’ara gyarawa ta d’auki turaren ta shima ta kara feffesawa ta zura takalmi, jiki na rawa ta fice daga cikin d’akin dan gani takeyi kamar idan ta tsaya b’ata lokaci minti biyun suka cika komawa zaiyi batareda ta ganshi ba, dariya sosai Sultana take mata, wai ba saban ba an fad’a soyayya.

Da gudu ta sauko ta fice daga falon ko Hajiya dake tambayar ta lafiya ta sauko da gudu gidan uban wa zataje da daren nan take shirin ficewa bata saurari Hajiyar ba ta fice dan itama tasan tana tsayawa lokaci kawai zata b’ata mata,

A harabar gidan taci burki tana gyara zaman rigarta ta kuma yafa gyalen nata a gefen kafad’un ta ta rife k’irjin ta, tana waige waige taga ta inda zai bullo,

Shiko dama tunda ya iso gidan shida kanshi ya karkashe wutan tsakar gidan ya kuma ce kar wanda ya sake ya kunna, ita ta fito daga cikin haske ne shi yasa koda ta fito duhun wajen yasa bata ganshi ba yayin da shi kuma yake can gefe yana k’are mata kallo daga cikin d’an kankanin hasken daya rage a tsakar gidan a hankali ya dunga takowa harya k’araso inda take yayinda ita kuma ta hango kawai sai kunyar kanta ya kamata dan tasan da zarar yaga kwalliyarta yasan cewa dan shi tayi dan haka sai ta juya baya taja gyalenta ta rufe fuskarta tana murmushin da bata san dalilin yin shi a wannan lokacin ba, shin najin dadin ganin shi ne ko koh dai,
Shiko yana isowa babu b’ata lokaci ya tsaya a bayan ta hannayen shi ya d’aura akan kunkumin ta ya rik’ota ya matso da ita zuwa jikin shi sai dai bai bari bayan ta ya tabi jikin shiba ya kwantar da kanshi a kad’arta daidai kunnen ta ya rad’a mata cewa,
“Likita did you missed me?” Ya tambaya da wata irin murya kwantacciya kamar baya son yin maganar,
Yummm haka ta dunga jin jinin jikin ta yana gudu daga wannan jijiyar zuwa wata,
Wallahi ji tayi kamar ta juyo ta rungume shi tace mishi nayi kewar ka AK, sai dai kuma ita d’in kunya ce ta haifeta dan haka bazata iya aikata hakan gareshi ba,

“Ki amsa min mana kewar nawa ne yasa kika gaza hakuri sai da kika nemo ni?”

Da sauri ta amsa mishi da cewa “ah ah kamannin fuskar kane dai ya fara bacemin shi yasa nace bari in tab’oka gashi kuma yanzun kazo naga fuskar naka”

“Da alama soyayyata ta rikita miki tunani shi yasa kika kira inzo ki ganni ko zaki dawo hayyacin ki kenan”
Juyo da ita yayi suna kallon juna ido cikin ido bayan ta d’an sauke gyalenta da tayi amfani dashi ta rufe fuska saiya zamana iya idanuwan ta yake gani, da kad’anΒ² ya dunga matsar da fuskar shi har ya zamana goshin su ya had’e dogon hancin shi ya goga akan nata hancin yana cigaba da kallon tsakaiyar idanun ta,
K’asa ya k’arayi da uryar shi, “toya yanzun kin d’auki hoton fuskar nawa dan so nike ki adana shi da kyau a cikin memoryn ki ta yanda bazaki k’ara mantawa ba”
Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana kankame jikin ta dan Wallahi ba k’aramin jarumta take gwadawa wajen hana kanta bashi kyakyawan runguma ba, wani iri take ji sosai a jikin ta natsuwar data rasa ne takejin yana dawo mata har bata san ya zata kwatanta yanda takeji ba,

Baya ya matsa yana mata dariya kafin yace “to likita na gane wato bazaki iya rikewa ba koh? Nima daurewa nikeyi muje daga ciki kafin a sab’a lamba” ya k’arasa fad’a yana kashe idon shi d’aya da d’age mata giraren shi,

Kai jama’a wallahi AK bayaji, dan ba karamin kunya ya bata ba har sai da taji kamar ta nutse a wajen.

 

*Ummiee Zaria*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button