Dabi’ar Zuciya 61
61
Cikin kwanakin da suka biyo baya gaba daya gidan ya canza ya koma wani iri,tamkar gidan da ake zaman makoki,duk da wani ɓarayi na farinciki da ya samu cikin zukatansu,to amma mummy ta bar musu babban tabo a rayuwarsu.
Mummy tana kwance a asibiti,ta samu mummuna yanka wanda ta illata qodarta,najwa na hannun ‘yan sanda,saboda asibiti da suka qi amsar mummy lokacin da aka kaita,suka dage kai da fata sai an nemo ‘yan sanda,drivern gidan professor da yaga zai shiga ciki bayan bashi yayi aika aika ba yayi musu bayanin komai,take suka garzaya,suka kuma damqe najwa sukayi ram da ita,baiwar Allah jawahir na azare tana ta tambayar kanta abinda ya faru amma bataji komai ba hakanan bata ga komai ba,don haka sai tadan kwantar da hankalinta,sukaci gaba da zama da tsohuwa yadikko tana kula da ita da ciwon suger dinta daya tashi,ta ta’allaqa zuwan nata ma da ciwon nata da ya motsa.
Ta gefen dadday gaba daya tunda al’amarin ya faru yana dakinsa ya kulle kansa,babu wanda yake bari ya shiga kamar yadda shima baya fitowa,yayi kuka yayi kuka har baisan adadinsa,yayi nadamar da yace baiga amfaninta ba,yaji gaba daua siyasa ta fice masa fit a ka,ya tabbatar abinda ya sake kawo wannan matsalolin da gidansa ya fuskanta shine rashin samun wadataccen lokacin zama da iyalinsa da ya fara samu sanadin siyasa,ya tuna yadda rayuwar gidansa take a baya,ya tuna irin soyayya qauna da kulawa da yake samu daga raihana,yayi kukan da tunda mahaifiyarsa ta haifeshi bai taba irinsa ba,har sai da idanunsa suka soma rauni.
yayin da saraki ya duqufa wajen ganin an duba lafiyar mommansa an tabbatar da ingancinta.
Cikin hikima da isa irin ta ubangiji treatment kadam take da buqata,sai kuma idanunta da ya samu raunin gani saboda zama a duhu data jima tana yi,so ko yaya ta shiga haske sai yayita damunta,wannan dalilin ya sanya aka yi mata glass da zata dinga amfaji dashi sanda zafa fita ga haske har zuwa sanda ganinta zai dai daita.
Sai da yaga yadda jikinta ya fara kyau,ta fara dawowa cikin hayyacinta sannan ya karkata zuwa ga gyaran dukkan abubuwan da suka wakana.
Da farko bai sanya an kama bala ba,saboda bisa dukkan binciken da yayi ya tabbatar masa da cewa tursasashi akayi ya aikata abinda yayi din,saidai kuma ta yaya zaka yarda kaci amanar mutumin daka jima kana aiki qarqashinsa yana hidimta maka?,wannan shike nuna babu aminta ko kadan tattare dashi,wannan dalilin yasa ya sallami bala daga bakin aiki,abunda ya sanyashi cikin tashin hankali da baqinciki me yawa,haka nan ya kori fawwwaz shima,sa’an nan yana jiran samun lafiyar mummy ya hada ita da hajiya shuwa ya shigar da qara akansu,saboda lallai ba shakka akwai abinda yasa hajiya shuwa yin wannab tonon sililin,ya tabbatar ba banza ba,da ita kuma da mummy shi a wajensa dukka masu laifi ne,laifinsu daya.
Abu na gaba ya sanya an tattarewa mummy dukka wasu kaya da suka shafeta an kai Warehouse na kamfaninsa an jibge,bayan ya samu Tex daga daddyn kan ya aiwatar da hakan,saidai abu daya ya kasa tabawa ya kuma kasa magana akai shine najwa,sosai jikinsa ke sanyi idan ya tuna waye mahaifinta?,meta aikata?,don jawahir ko sama da qasa zasu hadu baya jin zai bari sunanta ko rayuwarta su baci,kuma bayajin zai bari ta kufce daga hannunsa ko a cire mata sunan ‘yar uwa kuma autarsu,saidai kuma ta yaya zai binne abun?,bayan idan ta dawo zata tambayi mahaifiyarta da ‘yaruwarta?,ba shakka yaqi ne babba a gabansu.
Baiyi qasa a gwiwa ba wajen sawa a cafko dukka ma’aikatan da mummy tayi amfani dasu wajen tsarewa da cutar da momma,daga nan aka miqa su kotu aka kuma fara shari’a dasu,bayan ya dora umar kan case din,cikin qaramin lokaci saiga batun ya yadu,cikin manyan shafukan jarida,labarai na gidan radio da television,kafofin sada zumunta,ko ina ka leqa zancan ake tattaunawa
“MATAR BABBAN SIYASA KUMA DAN KASUWA PROFESSOR RASHID AZARE TA BAYYANA A GIDAN MASU TABIN HANKALI,BAYAN DA ABOKIYAR ZAMANTA KUMA ‘YAR AIKINTA DATA AURE MATA MIJI TAYI MATA QULUMBOTO TA BADDA ITA TSAHON SHEKARU ASHIRIN DA DORIYA SABODA KISHI KAWAI” topic ne daya dauki hankula matuqa da gaske,aka dinga tattaunashi ana yamadidi dashi.
Koda batun yakai kunnen samir sai yaji dadi da ya karbi wayar jawahir babbar ya hadata da keypad kan zai sauya mata wata,gidan yadikko kuwa ba wani kallo ta cikayi ba,yasan ba lallai labarin yakai kunneta ba,idan ba takanas wani zaiyi ya gaya mata ba.
Cikin qanqanin lokaci al’umma da dangi makusanta suka fara tururuwar zuwa yiwa momma barka da fitowa da kuma jajen abinda ya faru,abinda ya sanya samir ya bada umarnin duk wanda yazo ace momma din bata gidan,badon komai ba,sai don yana buqatar ta samu hutun daya dace,ta sake komawa hayyacinta,don har a sannan tana samun kulawar lafiya daga wajen qwararren likita da samir din yayo haya takanas aka ware daki guda ya zuba duk abinda ya kamata kamar dakin asibiti yake kula da ita.
Cikon sati na uku momma ta fara komawa nutsuwarta,da taimakon bibi da kuma kaltum da take qoqari wajen girka dukka kalar abincin da tasan zai maida ma momman lafiyarta cikin sauri,takan dafa mata dawa kamar shinkafa,tasa mata manja da gishiri,kuma momm din bata qi,tana amsa taci,hakan tasa qashinta ya fara samun qwari nan da nan,kuzarinta ya dawo,abinda zai baka mamaki,tamkar ba itace ta rayu tsahon wannan lokacin tana azabtuwa a rufe ba,saidai idan kayi duba da kasancewarta mace mai tsananun ruqo da ibada tun da can ba abun mamaki bane,to sai kuma zamanta a wancan wajen ya sake sawa ta kusanta kanta da Allah sosai,yawan ambaton Allahnta yafi na baya kafin wannan musibar ta sameta,lalllai ba shakka ambaton Allah kat ne!,dashi kadai kuma zukata suke samun nutsuwa.
Amiru shine ya ankarar da samir rashin fitowar daddy kwata kwata,sanda yaje gareshi ba yadda baiyi ya fito din ba amma daddyn yace yayi tafiyarsa,ya shiga damuwa samir,saboda yasan abinda daddyn ke dubawa da abinda ke damunsa,saidai yadda ya roqeshin ya tafin hakanan ya tafin kamar yadda ya buqata.
Wata sabuwa……sanda yake gayawa momma matakin da daddyn ya daukarwa kansa saita kauda kai
“Ka rabu dashi,qila wannan shine abinda yafi dacewa da shi,saidai a gobe inason ka hadani dashi,ina buqatar takardar sakina,don inason nan da rana ita yau na wuce gaban dangina,wadanda basu da labarin fitowa ta” kai samir ya daga,fuskarsa cike fal da damuwa gami da tarin fargaba,da gaske momma take tafiya zata sakeyi a karo na biyu ta barsu?,idan ta tafin to ya zasuyi su rayu?,waye zai zauna dasu?,wacce rayuwa daddyn zai fuskanta a nan gaba?.
“Momma….idan kika tafi kuma?…..” Hannu ta daga masa
“Bance kace komai ba” sai yayi shuru yana sadda kansa,kafin ya miqe a hankali,yana jin maqogoransa a bushe,don haka yayi hanyar kitchen don ya samu ruwan da xai sanya masa ko xai dawo dai dai.
Tarin ganyayyaki ne gefe guda a kitchen din,wanda dukka tayi amfani dasu,wasu cikin girkin da a yanzu takewa momma din,wasu kuma ta zuba cikun kunun ganye data kammala ta sauke,tana ta kiciniyar bude flask don xubawa a ciki kada ya huce.
Daga bakin qofar kitchen din ya dakata,duk kuwa da tarin qishirwar daya kwaso,ya zuba mata idanu yadda taketa bata fuska da yarfa hannu saboda yadda murfin flask din yayi mata tauri yaqi buduwa,sake gwadawa tayi still yaqi,sai ta sake yamutsa fuska taja ta zauna kan kujerar plastic din dake kitchen din tana tura baki,kamar wani ne yayi mata laifin.
Idanunsa ya lumshe a hankali,murmushin da baiyi zato ba ya kufce masa,yana jin wata qauna da soyayyarta mai qarfi tana zarmewa gami da kwarara cikin zuciyarsa,tana hawa kuma wani mataki da matsayi mafi qololuwar daraja cikin ransa,matsayin da mahaifiyarsa kadai yakejin ta wuce nan.
Bai taba zato ku tunanin yarinyar tana da dakiyar da zata aikata abinda ta aikata din ba,bai taba kawowa tsayayyar zuciyarta takai haka ba,abu mafi burgewa tattare da ita tausayi da imani irin nata,da son tsage gaskiya komai dacinta…..wanda dama wannan halayyarta ce tun dadewa.
Sake dubanta yayi,ta dan fada ita kanta,tunda momma ta shigo gidan bata huta ba itama,bayan ta gama dawainiya da lalurar daddy,shikam a duniya me zaiyi mata ya saka mata?,bayan tsaftatacciyar soyayyarsa da yakejin kaf duniya babu matar data cancanci ta mallaketa irin ita?,UMMANTA ta fado masa a rai,dukka jiki da zuciyarsa sun masa amannar cewa za’a samar da mace kuma uwa ta gari a wajen,haqiqa ta canci dukkan wata soyayya da qauna gami da kulawa.
Hannayensa ya sauke ya saka kai zuwa cikin kitchen din ahankali,idanunsa na akanta,cinyoyinta sun fito sosai ta cikin wandon rigar baccin jikinta,hakan ya bawa hips dinta damae fitowa sosai,sai ya maida hankalinsa ga qirjinta,wajen da akoda yaushe yake tsole masa ido .
Sun fita sosai sun kuma tsaya car a jikinta,hakan ya sake baiwa structure na jikinta fita,yabi santala santala hannayenta da a baya suka cika sirantaka,wanda a yanzu sun cika sosai.
Gab da zai isa gareta ta miqe,ta dan qara gaba kadan zuwa gaban famfo ta tara,ta kunna ta tara saman flask din,wai ko saukar ruwan zai sa flask din ya saki ta samu damar budeshi.
Ba zato taji an kama dukka qugunta an riqe,amma sai qamshin turarensa ya bata amsar waye,take jikinta ya amsa gaba daya sanda yake sake matso da ita cikin jikinsa,rungumeta yayi sosai sannan ya miqa dogayen hannuwansa ya gefe da gefanta ya jawo flask din yaa bude mata shi,ya daurayeshi sosai sannan ya ajjiye a gabanta
“Gashi nan,me aka dafa mana ne?,saboda rowa gaba daya mu ba’a taba yi mana tayi ba ko?”
“Subhanallah” ta fada cikin zuciyarta tana qanqame jikinta waje daya,saboda yayi maganar cikin kunneta,hucin numfashinsa da na bakinsa wanda ke bada qamshin mint ya shige kunnenta,ya tada duk wata tsiga ta jikinta,yayin da shi kuma yaci gaba da sansanar wuyanta,sassanyan qamshin turaren data shafa daren jiya na shiga hancinsa,yana aikawa da wani rikitaccen saqo zuwa qwaqwalwarsa,a nutse ya shinfide tafukan hannayensa saman mararta,idanunsa a rufe yana ci gaba da sansanar wuyanta zuwa gashinta dake qamshin man kitson da tayi oiling dashi.
Idanunta ta mayar ta lumshe itama,saboda yadda gaba daya kowacce gaba ta jikinta lakarta ke mutuwa,ta dora hannuwanta saman nashi hannun tana son zamesu daga mararta,saboda yadda ya tsayar qara gudun zuciyarta
“Karki cire……baki qara wani period din ba?” Ya tambayeta muryarsa qasan maqoshi,kamar wanda ke mata rada,fitar furucin ya qara rudata,saita girgixa masa kai da sauri alamun a’ah
“But….me yasa baki gaya min ba sanda ya dawo?,ko baki shirya karbata a matsayin mijinki ba?” Gaba daya ya sake rudata dajin abinda ya fada din,miji?,ita a yanzu har isarta takai yayi matar aure da ita?,kamar yasan me take tunani,saiya saketa,yaja baya kadan,sannan ya juyo da ita tana fuskantarshi,ya zuba mata idanu da birkitattun idanuwansa da suka sauya launu,tun tun tuntuni……baisan wane baiwa ne da ita haka ba,da yakan samu kansa cikin burkicewa duk sanda jikkunansu xasu hadu waje guda,ko don bai saba hakan ba sai a kanta?.
Dukka tafukan hannayensa biyu ya saka a kuncinta na dama dana hagu,ya dago fuskarta sosai ta yadda zai iya kallon qwayar idanunta
“Bansan ke alheri bace a rayuwata sai a yanzu,ban kuma sani ba…..ko zai iya karbar wannan samir din a matsayin mijinki?” Idanunta ta runtse,tambayar tayi mata tsauri sosai,yana kasheta ne da wannan tsaiwar tasa cikin jikinta ba tare daya sani ba,muryarsa kadai matuqar dab da ita take hautsina mata tunani take,tasa ta manta abinda takeyi
“Bansan wanne irin tukuici kike da buqata daga wajena ba”
“Ka kaini gida,inason naga ummata” ta samu kanta da fada,hawaye kuma ya biyo bayan maganar tata.
Kai ya fara girgizawa
“No….no, stop it please” ya fada yana sanya yatsansa yana dauke mata hawayen saman fuskar tata,ido ya tsura mata sosai yana kallon zanen fuskarta,komai yana zaune bisa muhallinsa bisa tsari da halitta me kyau,wannan shine kallo mafi kurkusa daya taba yiwa kaltum din,dan madaidaicin bakinta idanunsa yakai kai,ya zarto da hannunsa wajen zuwa daidai hancinta,ya dora yatsansa guda biyu ya soma zagaye tattausan lips dinta.
Da hanzari ta qwace fuskarta ta hanyar ja da baya saboda jin wani shock da tayi kamar an jata,tun daga yatsun qafarta har zuwa qwaqwalwarta,sai ya harde hannayensa yana fidda murmushi yadda ta juya baya ta kasa hada ido dashi,idanunta na nuna zallar kunyarsa data kamata.
Qarasawa yayi inda flask din yake ya dauko ya biyota dashi,ya ajiye kusa da ita yana cewa
“Zan dauki lokaci me tsaho ina koya miki yadda zaki rayu dani,babu abinda kika sani dangane dani illa kamannin fuskata……a yau na shiryawa shaidawa dukkan wanda ya kamata cewa KE MATATA CE” Haka kawai taji gabanta yayi mugun bugawa,tsoro ya kamata,saita daga fararen idaunta ta kalleshi kafin ta janyesu,ta koma qoqarin sauke tukunyar kunu.
Duk sanda ta kalleshi da fararen idanun nan nata yakanji wani abu ya tsarga masa,ba tun yau ba,ba tun wannan lokacin ba….yakejin hakan,kusan tun ganin farko da yayi mata,ya manta rabon da yaga mace mai fararen idanu kar haka irin nata,sai ya dauka wannan banbancin ne.
“Bakya sona ne?,ko ban miki ba?” Ya fada yana ware hannayensa gaba daya bayan ya zagayo gabanta ya tsaya,a sace ta kalleshi ta dauke kai,cikin ranta tana fadin,komai kyau isa mulki dukiya ko nasabar mace,bata isa ta kalli samir yace baiyi mata ba…..indai ba irin mazan aljanna takeso a kawo mata duniya ba
“Kalleni sosai…..” Ya fada yana sake matsota,sai tayi saurin ja da baya,sannan ta take ta fice daga kitchen din da gaggawa,don tabbas ta bari yaci gaba da hada jikinsa da nata…..batasan iya yadda adadin sonsa zaikai cikin zuciyarta ba.
******Qarfe bakwai na dare ne,cikin shigar laffaya mai azabar kyau butter colour ta nannade jikinta,kamar yadda take kusan rabin shigarta kenan a shekarun baya tun duniya tana kwance.
Samir ne ya sake knocking qofar,wanda cikim jagulewar rai da zuciya dama yayo rakiyar,don kawai bazai iya saba umarnin momman tasa ba.
Karo na kusan biyar ya sake bugawa kafin ya iya jiyo maganar daddyn can qasa
“Waye?”
“Samir ne….momma keson magana da kai” daga nan inda yake tsaye,yana iya jiyo qarar saukowarsa da qarfi,da alama amsar da samir din ya bashi tayi masa ba zata,ba’a kuma cika minti daya ba qofar ta bude,karo na farko tun bayan satittikan da suka shude daya rufe da kansa.
Kallo daya samir yayi masa tausayinsa ya sauko masa,gaba daya ya hada wata qasumba a fuskarsa da kansa,wadda ta cika da furfura,ramar da yayi ta bayyana har saman fuskarsa,wasu qashi dukka sun bayyanar masa.
Idanunsa nakan momma din a sanda ya bude qofar,sannan ya matsa yana basu damar shigowa.
Samir yana iya ganin yadda ya saka wani qyalle yana kadewa momma kujerar tare da gaya mata ta zauna,saidai a maimakon hakan saita koma can wani waje nesa kadan ta jingina,fuskarta kuma babu alamun annuri ko fara’a ta fara magana
“Na riga dana hada kayana,inason komawa qasata cikin dangina,nazo ne domin karbar shaidar sakina…..saboda al’adarmu saikin nuna ta koda wani auren naki na gaba zai taso,ina fatan ba zamu tsawaita magana ko bata lokaci ba” sosai tashin hankali ya bayyana kan daddyn,sai samir ya kauda kansa,saboda tausayin daddyn nasa,ya dade da yi.masa uzuri,saboda yasan dukkan abinda ya faru MAKIRCI DA KISSA ne sukayi aikinsu,mummunar kissa abar qyamata.
Muryar daddyn a dakushe ya fara magana
“Raihana….kiyimin rai don Allah……karki ce zaki tafi ki barni,kunyar ki da kunyar yadda zan tunkareki ya sanya na kulle kaina tsahon wadan nan kwanakin,saboda bani da wani abu da zan gaya miki wanda zan wanke kaina,nasan cewa na rusa dukkan wata yarda da aminci dake tsakaninmu”
“Kayi haquri na roqeka nima,komai da ka yimin na yafe maka albarkacin danka,amma a yanzu ina buqatar shaida ta,saboda inason na koma qasata cikin ahalina na qarasa rayuwata”
“Har yanzu da aurena a kanki raihana……saboda bayan na rubuta saki guda daya……munyi rigima sosai da hafsa a sannan duk da ba’a ganki ba bakya nan,ganin yadda ran hafsa ya baci sai nace na maidaki,kuma daga ranar har kawo yau a yanzun ban janye ba……saidai in sake jadda miki cewa ke matata ce,hafsa itace shaidata”
Wani nannauyan numfashi samir ya sauke,yanajin wani sanyi yana ratsa zuciyarsa,saidai cikin lokaci kadan momma ta kafe kan batasan wannan ba,don haka samir ya zare jikinsa daga dakin,bai kuma tsaya ako ina ba sai dakin hajiya qarama.
Baiyi qasa a gwiwa ba ya gaya mata abinda ke faruwa a sashen daddyn,daquwa ta watsa masa
“Don qaniyarka me yasa zaka rakatan?,me yasa baka zo ka sameni ba tukunna” kanshi ya shafa,yadda yaga hajiya qaraman ta miqe cikin gaggawa yasan komai zai dai daita,mayafinta taja kuwa ta fice,shi kuma ya koma ya zauna cikin kujerun dake dakin yana sauraron dawowarta.
Kusa awa guda hajiya qaraman ta sake dawowa,da alama ansha fama ansha gwagwarmaya,saidai yanayin fuskarta kawai ya tabbatar masa komai ya dai daita
“Kaje yaya yanason ganinka” tsam ya miqe yabi bayanta har zuwa sashen daddyn.
Kallo daya yayi musu dariya taso kubce masa,fuskar daddyn wasai ,saidai momma da har yanzu a cunkushe take,fuskarta na nuna fushi,amma kuma idan kayi mata kallon tsanaki zakasan cewa fushi ne akeyi irin na masoya.
Gaban daddyn ya qarasa ya duqa
“Gani daddy” gyara zamansa yayi sosai yana kallonsa
“Samir….inason in sake neman afuwarku ne gaba daya kan dukkan wani abu da ya faru”
“Daddy…..kasa a ranka nidai a wajena…..kamar komai bai faru ba……saidai…..inason dukkaninku kuyimin afuwa,saboda na aikata wani babban kuskure watanni masu yawa da suka shude,kuma na kasa gayawa kowa a cikinku” dif sukayi,kowa yana dubansa,kowa kuma da abinda zucuyarsa take ayyana masa,aka rasa me magana,sai daddy
“Na yadda dakai samir,kome zaka aikata ina da kyakkyawan fatan da zaton bazai zama mai munin da zai cutar da al’umma addini ko mutuncinka ba,kada kaji komai,sanar dani” zama yayi sosai,cikin nutsuwa ya shiga shaida musu dukkan abinda ya faru,tun daga lokacin da ya fara sanin bilal,rayuwar kaltum har zuwa yadda auren ya dauru.
“Alhamdulillah” hajiya qarama ta furta tare da wata ajiyar zuciya mai qarfi
“Mun godewa Allah da ya sanya iya haka ce ta faru…..hankalina har ya kwanta” to ga momma da daddy ma kusan abinda ya faru kenan,saboda ya sanya kowa a cikin taraddadi,saidai amsar daddy ta sake kwantar masa da hankali
“koda kaltum bata zauna damu ba….koda ita ke da buqatar ta aureka tabbas zamu aura mata kai…..barema tun zuwanta…..babu wanda bai yaba da dabi’u da halayenta ba”
“Banajin a duniya akwai yarinyar da zanso banda kai bayan ita” amsar da ta fito daga bakin momma kenan,sai ya runtse idanu yana tasbihi ga ubangijinsa,lallai duk wanda ya nufaci ubangiji wajen aikata wani aiki…..to babu makawa zai shige masa gaba,zai share masa hawayensa,hakanan duk wanda yaji tsoron Allah xai samar masa mafita……zai kuma azurtashi ta inda baya zato.
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*_DA ZAFINSU_*
*_A TSARE SUKE_*
*_SUN TANADESU_*
*_CIKIN SALO NA HIKIMA DA BAN SHA’AWA_*
*_ƘAWATATTU kuma ZAFAFAN DOCUMENTS HAR GUDA 25 na ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR da aka tanadar muku dasu_*
*_tun daga batch 01 har batch 05,duka bisa farashin rangwame_*
*_MAZA TUNTUBESU TA WADANNAN LAMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA_*
_WADANDA SUKESON TURAWA TA ACCOUNT SU YIWA WANNAN NUMBER WAYAR MAGANA_
08184017082
_MASU TURA KATIN WAYA KO VTU KUMA_
09134848107
*_TARON GAMAYYAR ZAFAFAN MARUBUTA…..MASU ZAFAFAN ALQALUMMA_*