Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 60

Sponsored Links

60

A hankali bibi ta sulale a wajen saboda kasa qarasawa da tayi zuwa wajen momma raihanan,duk da burin hakan da takeyi,amma sam qafafunta sun kasa daukarta,ganin abun take kamar almara,kamar cikin irin mafarkan data saba yi,idanunta suna iya hango mata sanda samir da momman suma suka durqushe zuwa qasa,sai giftawa kaltum da amiru suna qoqarin dagata.

*******. *****. *****. *****

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke bayan dawowa da yayi daga dogon tunani,yau babu kowa a parlor din nasa,samir da amiru sun fita sun shaida masa zasu wani waje,jawahir dinsa ta shiga makaranta,mommy ta tafi asibiti a duba mata bayanta dake ciwo,najwa kuwa dama sau daya tal take shigowa dubashi……sau dayan da idan zai yiwu da ya hanata shigowa ma,saboda wasu tarin dalilai,da kuma rashin alfanun zuwa dubiyar tasa ma gaba daya.

Ko sau daya yaga gilmawarta kota mahaifiyarta sai yaji wani abu yana motsa ranshi,abun da har yanzu yake masa zafi da ciwo a qirji,kullum addu’a yake dare da rana,tun daga wancan lokaci kam rabbus samawati ya warware dukkan wani qulli dake cikin rayuwarsa.

Wannan zaman da yake a yanzu yana yinsa ne badon bai warke ba,a’ah,yana yinsa ne saboda jinyar zuciyarsa,a duk sanda ya tuna irin musgunawa da miyagun kalaman da yake jifan samir dasu a baya sai yaji zuciyarsa ta quntata,babban abun tambayar shine……a koda yaushe jidda bata hanashi jifan samir din da miyagun kalamai,saidai kawai fa nuna a fuskarta,bata taba tursasa samir dai dai da rana daya yayi abinda yakeso ba,koda kuwa shi baya so,inda raihana ce zata bar haka ta faru?……

Gabansa yayi wani muguj faduwa da tuna raihanan da yayi,a hankali tunaninsa ya koma baya,zuciyarsa ta shiga tuna masa wace raihana?,tun daga haduwarsu har zuwa rayuwarsu…….

“Daddy……kayi baquwa” muryar najwa ta katse masa dogon tunanin da ya fada,ya daga kai yana duban yarinyar,duba me kama dana qurilla,sai ya buda bakinsa a hankali

“Wacece?”
“Hajiya shuwa,…..maman fawwaz,tace saqo tazo kawo maka” mamaki sosai ya kamashi,a iya tsahon saninsa da hajiya shuwan aminiyar matarsa ce,tun suna da jajayen sawayensu kawo yanzu,babu kuma abinda yake hadasu da ita illa gaisuwar mutunci,to amma,baisan wanne irin saqo bane wannan

“Ki rakota ta shigo” ya fada yana gyara zamansa saman kujera,sai ta juya da saurinta ta fice,tana addu’ar Allah yasa maganar nemawa fawwaz aurenta ne,saboda tasan indai hakan ta faru tofa burinta ya cika,daddynta bashi da matsala,yana qaunarta,hakanan yafi mummyn sauqin kai.

Daga kai yayi yana amsa sallamarsu ita da fawwaz sannan yayi musu izinin zama,suka gaisa sukayi masa sannu da jiki,sannan najwa ta juya tana cewa

“Hajiya bari na kawo muku abun motsa baki” daga haka tayi gaba tana jin dadi cikin ranta,shuru ya ratsa wajen na wasu sakanni sannan hajiya shuwa ta fara magana

“Nasan zakayi mamakin jin cewa gurinka nazo…..nazo kawo maka saqo ko?” Kai ya gyada yana dubanta

“Qwarai kuwa” saita motsa jakar hannunta me dan fadi da yalwa

“To ba abun mamaki bane,duba da cewa…..jidda ta buqaci duk wani abu nata dake hannunmu na dawo mata dashi…..to…..kasan mu da riqon amana da kuma cika alqawari,nazo na taras bata nan,to banason baiwa diyarta kayanta tunda da alama diyar halin mahaifinta tayo…..kayi haquri,bakai nake nufi ba,domin kai din ba mahaifinta ba,kai ubanta ne,uba kuma irin na riqo,wanda ya dauki nauyin dukkan wasu nauye nauyen na diyoyin daba nashi ba har zuwa sanda suka zama mutane……” Takai qarshen maganar tana ciro wasu takardu daga jakarta,sannan ta dora idanunta ga daddy wanda ya zuba mata ido sosai,yana son gaya alamun hauka ko tabin hankali tattare da haj shuwa da take furta wadan nan kalaman

“Nasan ka shiga mamaki ko?,to ina tafe da hujjata ta gaya maka haka,ungo wadan na takardun guda biyu” ta fada tana miqawa fawwaz su,shi kuma ya miqawa daddyn sannan ta dora

“Takardar farko takarda ce ta asibitin daka taba kwanciya jinya sanda ka samu hadari shakaru talatin baya,a lokacin da danka samir bai wuce shekara uku a duniya ba,baya nine na cewa wata jijiya cikin jikinka da zata iya bayuwa ga samun cikin matarka ta tabu,saidai daga shekara uku zuwa hudu zata iya komawa kan aikinta,matarka zata iya daukan ciki harma ta haihu…..,a wannan lokacin raihana cikin gidanka bata da wani amfani,saboda siddabaru da kissa da jidda tayi amfani dasu ta shiga tsakaninku…..don haka jidda ita ta karba takardar.

Da ganin bayanan jiki hankalinta yayi matuqar tashi,tayimin bayanin cewa indai haka ta kasance shikenan bata da wani riba a aurenka,saboda raihana nada da namiji,ita kuwa bata da qwai ko guda daya,yaushe zata yita zama har sai ka warke?,warkewar da babu tabbas?ita data shigo da burin tayita haifa maka yara,dalilin da ya sanya duk cikin da raihana ta dinga samu bayan samir ta dinga lalata mata shi kenan ba tare da saninku ba gaba dayanku….” Daga kai daddy yayi da sauri ya dubeta,kai ta gyada masa alamun tabbatarwa sannan kuma taci gaba

Da wannan dalilin jidda ta boye wannan takardar bata bari kowa ya gani ba,qarshe ma saboda gudun bacin rana ta bani ajiyarsu,tun daga ranar jidda ta shiga neman hanyar da zata samu ciki,dalilin da yasa ta komawa ainihin saurayinta daya fara yi mata ciki har sau biyu a duniya.

DAGE cikakken dan sara suka,kuma tantiri,wanda ya taso a gidan da babu cin yau babu na gobe,bangar siyasa da daba sata da shaye shaye shine aikinsa,ba wani jimawa kuwa ta samu cikin NAJWA dashi,ta kuma haife maka,ka amsheta a matsayin ‘yarka…….,bayan wannan tasan yadda ta hada masa TARKON da ya kashe mutum aka kaishi gidan kurkuku,daurin rai da rai,yanzu haka yana can.

“La’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin” daddy ya furta kansa a qasa,hawaye na qoqarin saukowa daga idanunsa

“Bayan ta haifa najwa tun kafin takai dage gidan kurkuku dama tace ba zata koma masa ba,da alama yara mata iya baiwa mahaifar mace,don duk cikinta na baya guda biyu data zubda mata ne,saita koma kan lecturer dinta data qyalla idanu ta gani,ta kuma samu labarin ‘ya’ya maza gareshu guda hudu rigis,burinta bai cika akanshi ba,sai satoshi tasa akayi,ta kuma bashi abun gusar da hankali yayi mata yadda takeso,tsahon wata biyu yana aje a wajenta tana yadda takeso dashi ba dare ba rana,bata sakeshi ba sai data tabbatar ta samu abinda take da buri,wanda bayan komai ya kammala ya shiga baqinciki da takaici,abinda kusan yayi ajalinsa kenan,ya hadu da hawan jini,wannan shine mahaifin jawahir”

Kamar ta buga masa guduma aka da qahon zuciya haka yaji,saboda bai taba tsammatar hakan akan jawahir ba,yarinyar da tayi matuqar shiga ransa,yarinya mai hankali da nutsuwa….tausayi da kuma sanin ya kamata,har gwara najwa….tun daga ranar da yaji bala na waya da ita….tana bashi umarnin ya watsar da daddyn bisa titi bayan an tsinke musu burki yasha jinin jikinsa,jikinsa yake bashi tabbas ba diyarsa bace ta halak,saboda abune mai matuqar wuya ɗa na tsantsar halaliya,dan da aka auri mahaifiyarsa bisa tafarkin shari’a,aka haifeshi bisa tafarkin shari’a ya iya kashe mahaifansa

“Sanda raihana ta sake samun ciki abun yayi matuqar daga hankalin jidda,kuma ya tabbatar mata da cewa lallai ka samu sauqi,tana tsoron kada raihana ta sake haihuwa ta samu da namiji ita tana zaune,abinda yasa ta yanke shawarar kau da ita,ta kuma yita qoqarin ta samu haihuwa da kai koda sau daya ne…..saidai inaa,bata samu wannan rabon ba har yau……..

“Wadan nan takardun na qasa sune zasu baka tabbacin maganganuna na yanzu……raihana kuwa……” Gabansa yaji yayi wani mummunar faduwa data kira sunansa

“Ya Allahu” ya furta a sarari,hakan baisa haj shuwa ta tsaya ba,don burinta kawai ta gama kwancewa mummyn zani a kasuwa

“Bayan ta gaza kau da ita daga duniya…..Gidan mahaukata jidda ta kaita…..har yau kuma tana raye……saidai ni kaina bansan wanne gida bane,kuma a ina yake……ga wadan nan,duka takardun kadarorin raihana ne data sace ta rabawa yaranta,wadan nan kuma kudaden kamfanin saraki da ‘yarka tasa dana ya debo mata,ta hanyar amfani da siddabarun na’ura……..

Tunda ta fita daga gidan takejin gabanta yana faduwa,abinda ya hanata dogon tsaiwa kenan cikin asibitin,ta kasa tsaiwa ma taga likitan ta juyo gida.

“Sannu da zuwa hajiya” saude mai aiki ta fada ga jidda,saidai bata amsa mata ba ta jefa mata tambayar dake cin ranta tunda ta shigo,saboda taga motar hajiya shuwa a farfajiyar gidan,batayi mamakin zuwanta ba,saboda a jiya sunyi waya,tayi mata cin mutuncin da dukka yazo bakinta,gami da kakkausan gargadin ta jawa fawwaz kunne ya maido komai dake.hannunsu,ta daukoshi zuwa daular gidanta ne saboda ya amfana shi da uwarsa darajar amintar dake tsakaninsu,hajiya shuwan batace mata ta tafas ba,wanda mummy ta dauka shakka ce tasa haka,har sai data gama sannan tace

“Ki kwantar da hankalinki,gobe zan dawo miki da komai da kaina ba saqo ba” tayi zaton zata sameta a falo a zaune,sai kuma taga falon wayam

“Su waye sukazo?”
“Hajiya shuwa ce da fawwaz,amma suna wajen alhaji” saude ta amsa mata,gabanta yayi mummunar faduwa,me ya kaita wajen daddy kuma?,me taje yi?,a iya tsahon zamansu bata taba haka ba,amma sai zuciyarta ke qoqarin gamsar da ita cewa dubashi suka shiga yi,don haka ta sauya akalarta zuwa parlor din daddyn a sukwane tun kafin hajiya shuwan ta mata wata barnar,tasan halinta sarai,bata barin kota kwana,hakanan koda zatayi asarar wani abu nata muddin zata dauki fansa zata iya aikata komai.

Najwa dauke da babban faranti data cika da fruit tabi bayan mummy,wadda batasan tana biye da ita ba,itama bata kirata ba saboda mugun haushinta takeji,saboda tana son kawowa soyayyarta dama plans dinta tarnaqi,don haka taci gaba da bin bayanta har suka shiga falon.

Kallo daya ta yiwa daddy kamar yadda shima yayi mata ta fuskanci lallai akwai gagarumar matsala,hakanan kuma komai ya qare

Dukka wanda yake cikin motar kuka yake riris,amiru ke driving kaltum na zaune daga gefansa gidan gaba,daga baya kuwa bibi ce riqe da hannun momma,sai samir daga daya side din ruqunqume da ita,zaka zaci cewa zata sake bace masa,kanta na boye cikin qirjinsa saboda haske da ya yiwa idanunta yawa,sakamakon dadewa da tayi bataga hasken rana ba.

Hadiyar wani abu kawai yake daga maqoshinsa zuwa cikinsa,idaunsa tamkar garwashin wuta,zuciyarsa na ayyana masa wanne irin hukunci ya kamata ya dauka akan duk wanda keda hannu wajen qarara da rayuwar mahajfiyarsa cikin wannan wajen?,wajen da duk wanda ka ganshi a ciki to dole ce ta kaishi bawai son rai ba?,ya dauko mahaifiyarsa ne cak ya fito da ita daga wajen,ba tare daya tsaya yabi ta ba’asin komai ba,don a yanzu ta tata yake tukunna kafin zuwan komai.

Wayarsa daya manta da ita gaba daya cikin motar ta dauki tsuwwa,tafi kusa da amiru saboda tana kusa gear

“Sabi’u yana kiranka” baiyi niyyar amsawa ba,amma jin sunan me kiran nasa yasa ya karba wayar ya kara a kunnensa.

“Najwa?,najwa kuma?” Shine abinda ya maimaita,bayan sabi’un ya bashi bayanan cewa itace waya ta qarshe da bala yayi da ita bayan ta sanya an tsinke birkinsa dana mahaifinsa,bisa taimakawar fawwaz.

“Wuce gida damu” samir ya gayawa amiru a tsawace,kamar wanda ya fara fita a hayyacinsa,yana jin cewa tabbas akwai babban tashin hankali kenan,abinda da farko ba haka ya tsara ba,ya tsara ya wuce da momma din daya daga cikin gidajensa.

Dadi ya saukarwa bibi,don dama haka takeso,tanaso taga yadda qaryar jidda zata qare,tana son taga tadda zata kalli momma raihana……

A rikice ta maida dubata ga hajiya shuwa,wadda take binta da kallo tare da murmushin mugunta a fakaice,ganin mummyn ta gaza cewa komai sai kallo da take rarrabawa a tsakaninsu tace

“Yauwa…..gwara da Allah yasa ma muka hadu,ga saqonki nan dukka na damqa hannun mijinki” take qafafun mummy jidda suka dauki rawa,wato an samu sabani kenan?.

Ta aika yara bayan fitarta su qaddamarwa hajiya shuwa su dauko mata dukkan wasu takardu nata da suka shafeta na sirrinta da take bata ta adana mata,sannan su karbo dukkan wasu kudi da takaddar kadara ta najwa dake hannun fawwaz,ashe ita nan ta nufo kenan?,ko kuma sun sameta tsallakewa tayi?,kamar tasan abinda take tunani sai tace

“Ai yaran da kika tura ya karbo miki saqon munyi sabani dasu ne,muna fita daga layin suna shiga……”

“DAGE da gaske shine mahaifin najwa?,lecturer mahaifin jawahir?” Daddy ya jefi mummy jidda da tambayar don tabbatarwa da kansa abinda hajiya shuwa ta fada.

Yadda tayi wani mugun shock daya sanyata yin taga taga zata fadi saboda girma da nauyin tambayar ya sanya duk wanda ke wajen fahimtar gaskiyar maganar,ciki kuwa harda jawahir da maganar ta sanyata kurumta na wucin gadi,basu kuma fahimci tana wajen ba sai da plate din hannunta ya fadi ya tarwatse da dukkan abinda yake ciki

“Qar…..qarya take min,so take taga bayana……qarya take” mummyn ta fada jikinta yana rawa

“Da dukka wadan nan shaidun dake hannuna?…..duk da hakan qarya take?!” Daddyn ya qarashe tambayar cikin daka tsawa mai kada hantar mutum,ya wani jirkice zuwa mayunwacin zaki dake farautar dukkan dabbar data gifta ta gabansa.

Ja da baya mummyn ta fara yi a tsorace sanda daddyn ya miqe yana tsuma yana nufota,idanunsa a birkice,tunda take bata taba ganinsa cikin siffa irin wannan mai ban tsoro ba,gaba daya ya sauya daga rashid din zuwa wani mutum da zuciyarsa da kuma fuskarsa ke cike taf da bala’i.

Cak taga ya tsaya ya tsurawa bayanta idanu ,abinda ya sakata waiwaya itama da hanzari.

Tashin hankalin da tayi arangama dashi sai taji yafi wanda ta shigo ta taras cikin dakin,tayi wata muguwar girgixa da razana kamar zuciyarta zata yanko daga qirjinta ta fado qasa.

,sai data gwammace dama bata waiwaya ba,ina ma suman qarya tayi kafin idanunta suga wannan babban bala’in da tashin hanakalin,yau din wacce irin baqar rana ce a gareta?,wanne abu ne yake shirin samunta haka?.

Tuni daddy ya miqe tsaye,labbansa suna haduwa suna rabuwa,jikinsa ko ina rawa yake,idanunsa qyam saman fuskar momma,yana son magana amma kowanne furuci ya kasa fita daga labbansa.

“Raihana…..ya akayi kika fito?” Kalaman da suka subuce kenan daga bakinta sanda momma raihana ta kafeta da idanu,a zatonta tana zanta hakanne a zuciyarta,batasan cewa maganar ya fito fili ba sai sanda taji bibi na maida mata amsa

“Ubangijin da baya barci bare gyangyadi shi yayi ikonsa ya fiddata daga kurkukun da kika jefata ba tare data aikata laifin komai ba”……

Kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai sai jin qarar mummy sukayi,dafe da gefan cikinta jini yana bin qafafunta,kafin hankali yakai ga abinda ga sameta cikin qiftawa da bismillah muryar najwa cikin wani mahaukacin sauti ta mamaye wajen

“Gwara na kasheki na kuma kashe kaina,gwara na dawwama a gidan prison,da ace wani riqaqqen dan daba talaka shine mahaifina,Allah ya isa tsakanina dake……Allah ya isa,bazan taba yafe miki ba,kin cuceni daya zama ba daddy ne ubana,gwara na kasheki…..” Ta fada tana daga wuqar hannunta,wadda ta daukota ne cikin fruits din data kawowa su hajiya shuwa.

Babu wanda ya motsa saboda cetar mummy,sai zagaye da suka fara yi a parlor din,duk da jinin dake diban mummyn amma najwa yunqurin binta ta qara mata takeyi.

Hajiya qarama ce wadda basusan sanda ta iso ba ta hankade najwan ta fadi gefe

“Meye hakan?,kinyi hauka ne?ku dukanku kuna kallonta tana yunqurin kash……”maqalewa maganar tayi a maqoshinta sanda idanunta suka sauka fuskar momma,fuskar data jiqe da hawaye tana bin hafsanta da kallo.

“W…..waw…..wa nake gani kamar raihana ta?” Kusan tafi momma kuxari,saboda haka kafin ta qaraso ita ta rigata,suka rungume juna kana suka fashe da wani nannauyan kuka mai ratsa zuciya.

Hayaniyar da ta barke cikin falon yasa suka saki juna,najwa ce ta isa ga hajiya shuwa taci kwalarta da kyau,fawwaz na tsaye daga bayanta yana qoqarin rabata da wuyan mahaifiyarsa qarfi da yaji

“Munafuka algunguma,ki gaya musu gaskiya,ki gaya musu gaskiya,dama ba qaunata kuke ba?,zuwa kikayi ki rabani da ubana ki manna min wani uban?” Murmushi hajiya shuwa ta saki

“Sakeni ‘yar nan,yanzu kuwa zan maimaita a gaban kowa saboda su xama shaida”

Hankali kwance hajiya shuwa ta maimaita dukkan maganar data gayawa daddy,sulalewa hajiya qarama tayi qas kamar yadda momma ta sulale itama,yayin da samir ya dafe bango jiri na shirin kada shi,kaf cikin zancan ba wanda yake hangowa…..tausayinta keson wasa da numfashinsa irin jawahir, innocent girl……son zuciya yasa mahaifiyarta ta bata mata rayuwa…..ta jirkita mata asali,ya Allah…..yanzu jawahir ba jininsa bace?,ba daddy bane ya haifeta?.

Amiru da idanunsa suka kada jazur ya dubi sashen da hajiya jidda take,jini take zubdawa sosai,kuma ci gaba da zamanta a haka dai dai yake da rasa ranta,sai ya hango fuskar jawahir…..mutuwar mummy da mummunan labarin professor rashid ba shine ainihin mahaifinta ba abun zaiyi mata yawa,abinda yasa yayi tattaki kenan ya fita ya kira driver ya taimaka suka kamata zuwa mota

“Ko kwana daya baxan iya qarawa da igiyar aurena a kanki ba…..na sakeki saki daya,na sakeki saki biyu,na sakeki saki uku jidda…..daga can idan kin rayu kada ki dawomin gidana,ki jirayi kuma sammaci daga kotu” wadan nan kalaman sune suka yiwa mummy jidda rakiya sanda su amiru suke fita da ita,abinda yasa numfashinta ya qarasa tsaiwa cak daga qirjinta……

Kansa samir ya girgiza,ya zaro wayarsa ya kira jawahir,bayan yayi qoqarin dai daita muryarsa

“Kina ina?”
“Ya saraki….ina makaranta”
“Idan kin fito ki wuce gidan hajiya qarama,gobe da safe da wuri xan turo driver ya kaiki azare wajen yadikko”

“Azare kuma yaayaa?” Ta fada a shagwabe cikin mamaki

“Eh azare, just say yes”

“Yes yaya” ta fada tana dariya,saiya maza ya katse wayar,karon farko hawaye na sulmiyo masa,yasa yatsansa ya dauke,wannan wanne irin son zuciya ne da zaiyi nasarar cusa baqinciki a rayuwar wanda baiji ba bai gani ba?.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button