Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 37

Sponsored Links

*KARKU MANTA A DADE ANAYI SAI GASKIYA,KUMA SAI AN GWADA AKAN SAN NA QWARAI*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke sanda ya tsaida motar a harabar wajen bayan ya gama dai daitata,ya dinga bin wajen dake cike da ‘yan jagaliya da kallo,dukkaninsu matasa ne masu jini a jika,wanda ya kamata a ce a dai dai wannan lokacin tunaninsu fresh yake,yana kuma gudana ne kan yadda zasu gina rayuwarsu data al’ummarsu dama qasarsu gaba days,sai gasu sun qare a wani waje zaune zube a wulaqance,mutum sama da ashirin na jiran mutum guda da sunan yi masa hidima ko bashi kariya,wanda basu da wani alfanu da zasu samu wanda ya wuce rugujewar rayuwarsu,da dan kudin dako cikakken abincin wuni guda babu lallai ya samar musu.

Idonsa ya lumshe yana jin ciwon hakan cikin ransa,yana daya daga cikin abinda yasa har kwanan gobe,ko sau daya siyasa bata taba burgeshi ba,yana ganin duk yadda kakai ga son tsaftace kanka ko zamewa hakan ba zai yiwu ba,wata qurar saita taddaka,inama ace mahaifinsa zai fuskanceshi yadda shi yakeso?.

A yadda ahalan ya gaya masa,mintuna biyar kenan suka rage su fito daga hall din,saboda haka saiya fito daga motar baya ya kasheta,ya tsaya a jikinta ya jingina yana ci gaba da nazarin wajen,har zuwa sanda aka fara fitowar,hakan yasa ya janyo hular kansa ya rufe fiye da rabin fuskarsa,don baisan yin magana da kowa,mahaifin nasa kawai yazo dauka.

Sannu a hankali ya tunkareshi sanda yake fitowa shida jama’arsa

“Barka da fitowa daddy” ya fada cikin girmamawa,saiya maida hankalinsa gareshi,yana masa wani duba na sama da qasa,gaisawar da suka fara yi da jama’ar dake tare dashi ta hana maganar da yaso yi din,saidai duk motsin da samir din zaiyi sai yaga idanunsa a kanshi,har zuwa sanda ya take masa baya zuwa bakin motarsa ya bude masa ya shiga,shima ya shiga mazaunin driver ya tayar da motar suka fara tafiya.

“Idan har kazo wajen nan ne don ka burgeni,babu abinda kayi illa ma bata min rai da kayi,ka duba tarin jama’a masu girma da mutunci a wajen nan,ka rasa dame zakazo min sai da qananun kaya?”professor ya fada cikin nuna zallar bacin rai,kafin samir yace wani abu ya sake magana

“Sai yau kaga damar dawowa kenan?,me yasa a kullum kai maqiyin burina ne da muradina?” Sosai furucin ya daki samir har zuciyarsa,ko yaushe yana aiki don ganin ya dai doita komai,amma idan komai yayi kamar zai gyaru saiya sake tabarbarewa da zarar ya danyi nesa da mahaifin nasa na wani lokaci

“Nakanji a raina wani lokaci inama ace kaine najwa….najwa ce kai,da nasan hakan ba zata faru ba” hannunsa ya dora kawai saman kansa yana shafan kan nashi tare da son hadiye abinda ya riqe masa wuya,ire iren wadan nan lokutan yafi qyamata cikin rayuwarsa,shi yasa koda zuciyarsa ta bashi shawarar kusantar mahaifin nasa,sai wata zuciyar ta haneshi,ya gwammace nesanta dashi saboda kubuta daga kalamansa masu ciwo irin wannan.

“Kayi haquri daddy” itace kalma guda daya daya iya furta masa,ya kuma maimaita masa ita kusan sau biyar kafin isarsu gida,wanda yana saukeshi ya wuce sashensa kai tsaye.

Kasa zama yayi ya dinga kai kawo a tsakiyar dakin yanason lissafa abubuwan da yawa da suke zuwa kanshi,kaushin daddyn agareshi kullum abune da bashi da sauqi ko rangwame,bayaga sabanin ra’ayoyi da zabe zabe na rayuwa babu wani mai muni tsakaninsu,amma a yadda yake mu’amalantarsa saika fassara abun da wani lamari mai girma wanda bashi da kyau.

Ya tafi da baya saboda samawa kansa mazaynu gefan gadonsa ki zuciyarsa zata samu nutsuwa,qafarsa ta daki locker gefan gadonsa,yakai kallonsa ga wajen,saiya fasa zama gefan gadon ya zamo ya zauna gabanta,ya zura hannunsa wani saqo dake jikinta ya fiddo muqulli ya zura ya budeta,ya sanya hannu ya fara fitar da abubuwan dake ciki yana binsu da kallo daya bayan daya.

Tarin hotuna ne mabanbanta,duk da cewa kowanne hoto mutanen jiki daya ne,amma yanayin sutura da kuma wajen da aka daukesu ya banbanta,a hankali wani abu ya fara taso masa mai kama da bege kewa da kuma qauna,saidai tashi daya wani abu mai qarfi ya taso ya dannesu,wanda hakan har yasashi miqewa daga tsugunnon da yayi,har zai bar wajen a haka ya tuna akwai Aamir a dakin,dalilin daya sanyashi dawowa ya tattara komai ya mayar muhallinsa kenan,saidai wannan feelings din daya taso masa yana jinsa yana motsawa a qasan zuciyarsa yana ci gaba da kaiwa sassan zuciyar nasa.

*********Zaune yake a gabansa da sanyin safiyar,zaman daya kusa kaiwa na mintuna talatin bayannya gama masa dukkan bayanin daya jima yana tsarawa zai gaya masan dangane da zaman kaltume a gidan,zai iya cewa tunda yayi hankali,kusan wannan shine kari na farko daya taba gaya ma daddyn abinda ba haka yake ba ma’ana qarya,komai tsanani ko kuma rintsi baya boye masa gaskiyar abu,kome gaskiyar kuwa zata haifar masa,har sai daya gama jiransa ya qarashe kallon labaransa,sannan ya maida kansa gareshi da wani irin duba,sanda mommy ke ajjiye masa zazzafan ruwan baqin shayi don ya dumama jikinsa da hanjinsa kafin lokacin cin abincin safensa yayi

“Kafin ka sanarmin komai…..mommynka ta riga data shaidamin” ya fada muryarsa a nutse,a hankali samir din ya daga kai suka hada idanu da mommyn,don basuyi haka ba,ya shaida mata da kansa zai gaya masa,to amma kamar yadda zuciyarsa ta gaya masa tayi hakanne don bashi kariya kamar yadda ta saba,hakan ce ta faru,don alamun kada ya damu tayi masa da idanu,dai dai sannan kunnuwansa sukaci gaba da dauko masa maganganun daddyn

“Abun mamaki,koda yaushe jidda qoqarin baiwa samir kariya kikeyi akan duk abinda yakeso,kina sanya qafa kina fatali da nawa muradin,basan me yasa kike daure masa qarqashin yin duk abinda ya tsarama kansa ba” cikin salo da kwantar da murya tace

“Banda abinka daddy,meye ne da son yakeyi wanda ba dai dai bane ba?,shi daya fa Allah ya bamu,yanzu idan ban bashi qwarin gwiwa da kariya ba?,waye zan bawa?”

“Ok,hakan shi ya baki qarfin gwiwar tayashi ya dinga karya min tsaruka da dokokina ko?” Da sauri ta girgiza kai

“Ba haka bane…..daddy yaran yanzu bada qarfi ake binsu ba,ba’a son a dinga tilastasu saboda gudun abinda zaije yazo” shuru ya ratsa falon,wani abu ya sauka zuciyar samir,hakanan yaji kamar wannan amsar batayi masa ba,shi ba yana yin komai sabida bijirewa ba,ba yanayin komai saboda yana tunanin shine dai dai ba,a’ah,yana yin komai ne saboda yana da tabbacin haka komai din ya kamata ya kasance,maganar momy ta gaba ta tsaida tunaninsa

“koda raheena bata a nan,ina kallonshi a matsayin amanar…..”

“Dakata….kada ki sake min magana makamanciyar wannan” daddy prof ya katseta yana dubanta,saita kafeshi itama da nata idanun tana karantarsa,akwai wani abu data jima tana qoqarin karantarsa tattare dashi,wanda har yanzu hangen ta da tsinkayenta ya kasi canko mata ainihin meye shi,saidai ta karanci akwai fushi daya cakuda da wani abu,abunda shi dinne takeson ganowa.

Sauke idanunsa samir yayi daga yake rarrabawa a tsakaninsu,ambatar sunan kadai ya daki zuciyarsa,baikai ga rarrabe tunaninsa ba muryar daddy ta sake ratsa kunnensa

“Bana daukan masu aiki underage,ka sani dokata ce,don hakan kamar kashe musu rayuwa ne,kuma koda zan dauka mutual person sai nasan daga ina mutum yake…..saboda haka ka dauka yarinyar mutane ka maidata inda ka daukota tun muna shaidar juna dani da kai” sosai gaban samir din ya fadi,in har daddyn ya kafe akan haka ba shakka akwai matsala,saboda ba yanxu ya shirya fuskantar wannan damuwar ba,ya bada lokacine zuwa sanda qura zata lafa

“Daddy…..amma da zaka saurareni da ka fahi……”

“Samir……na gama magana,gobe idan Allah ya kaimu akwai tafiyar dake gaba na,kada na dawo na sameta a gidan nan,bijirewa hakan xai iya zama ggarumar matsala tsakanina da kai” daga hakan ya dauki cup din dake gabansa ya fara shan tea dinsa,sai kawai samir din ya miqe,yana jin sanda mummy ke qoqarin sanya baki a cikin matsalar amma daddyn ya dakatar da ita.

Tunda tayi alwala da taimakon biba ta bada faralin salla take xaune a inda ta idar da sallar,har zuwa lokacin da biba zuwaira ta turo qofar a karo na biyu tun bayan fitarta

“Har yanzu kina zaune?,inaga ya kamata kiyi wanka ko?,tunda na nuna miki yadda zaki kunna shayar” dan gyara zamanta kadan kaltume tayi,tana qoqarin sake fuskarta,ganin yadda duk abinda biban zatayi,tana yi mata shine fuskarta cikin fara’a

“Da cewa nayi sai zuwa anjima”ta bata amsa tana wasa da qasan hijabinta daya dan bule.

Kai biba ta girgiza

“A’ah fa,gidan nan dabam yake,kamar yadda mutanen ciki suke na daban,kiyi wanka,saiki fita ku gaisa,sannan ki samu abu kici karki zauna da yunwa irin ta jiya” kai ta daga mata a sanyaye tana duban agogon dake maqale a bango,duk da bata gane qarfe nawa yake bayarwa,amma a jikinta tasan safiya ce sosai yanzu,wanda bazai wuce tara na safe ba,duk da ko a gida bata kaiwa rana sosai ba tare tayi wanka ba,irin na ‘yammatan garinsu da suke kaiwa yamma lis,sai an dawo daga tallah,la’asar sakaliya,sannan ayi wanka,a hade harda kwalliyar zuwa dandali.

Kalle kallen data tsaya yi a bandakin ya sanya ta bata lokaci sosai,ta tsaya gaban babban madubin dake bandakin tana kallon fuskarta,kallo na sosai a karon farko.

Koda ake cewa tafi habi duhu bata taba zata duhun nata yakai haka ba,a gurguje ta cuccuda abinda ya samu sanda taji muryar biba ta sake dawowa,ta maida kayan jikinta ta fito.

Dubanta biban take cikin mamaki

“Bakizo da wasu kayan bane?” Sai data kalleta kafin ta bata amsa,tun sanda wancan da batasan sunansa ba ya kirata take kula da damuwa da al’amarinta,tana ganin hakan muraran cikin idanunta

“Nazo dasu”

“Yauwa,dauko ki canza wasu,ki ajjiye wadan nan” qarasawa tayi inda ta sakaya qullin kayan nata,ta bude ta soma dubawa,biba na tsaye tana bin kayan da kallo

“Sune kayan naki wai?”ta sake tambayarta,dauke idanu kaltum tayi daga kan kayan ta mayar ga biban,tana mamakin yadda ta tambayeta

“Eh” ta amsa mata a gajarce

“Shikenan ba laifi,dauki daya a ciki ki saka” ta qarashe maganar tana ajjiye mopper da abin shara don kintsa dakin.

Da hanzari kaltume din ta karba

“Ki barshi zan share” da tace ta barshi,don batasan matsayinta cikin gidan ba,kada ta aikata ba dai dai ba ta jawa kanta wani abun na daban,ganin ta dage sai ta sake mata,ta koma bandaki ita ta fara gyarashi.

Tana tsaka da sharar tana cike da mamakin yadda wajen yake sharuwa subul subul,babu qasa,babu qura,ga sauqin shara.

A dan zabure ta dago jin an turo qofar dakin,har jawahir data shigo cikin shirinta tsaf na tafiya makaranta ta ankara da hakan,saita sake mata murmushi

“Yi haquri,na tsorataki ko?,sauri nake,ina biba zuwaira?” Qofar bandaki dake budewa ta kalla,dai dai sanda biba ke fitowa

“Diyata an fito?”
“Eh wallahi….don Allah biba zoki zubamin…..zan makara Allah,ya saraki na samu zai saukeni” da kallon mamaki kaltume ki binta,da alamu tana da kirki sosai a fuska,saidai kuma yadda take magana a shagwabe ya bata mamaki,ita bata taba ganin inda babba kamarta ke shagwaba ba,wanda inda a karkararsu ne tana da yara uku ma.

Nauyi taji ya kamata sanda suka hada idanu da jawahir,ta kamata tana kallonta,ga mamakin kaltume saita sakar mata murmushi

“Baquwa ya sunanki ne?”
“Kaltume ce” biba ta amsawa jawahir sanda jawahir din tayi gaba,biban na biye da ita a baya suna surutu.

Tana hakimce saman dining din tana breakfast cikin salon da zai nuna izza mulki da kuma iko da take dashi,falon baby daya cikin yaran gidan,sai masu aiki daketa kai komo suna gudanar da hidimar gidan ta yau da kullum wadda ta zame musu jiki.

A irin haka kaltume suka fito tana biye da biba,a mugun darare tana raba idanu tana kallon yadda Allah ya zuba ruwan kyau cikin falon da batasan wanne suna zata bashi ba.

Sai data kusan gama cin dankalin gabanta sanda suke duqe suna gaidata sannan ta ture farantin

“Lafiya lau….ita zaman me takeyi da baki shiga da ita cikin ma’aikata an bata aikin daya dace da ita ba?” Mommyn ta jefawa biba tambayar,kasancewar itace shugabar duka ma’aikata mata na gidan,saboda dadewar da tayi cikin gidan

“Ai dama bansan wanne aiki ya kamata a bata bane,nace ne bari na fara tambayarki tukunna” shuru ne ya biyo baya tana nazari,akwai abinda takeson aiwatarwa,saidai batason wanzar dashi da kanta lallai saita hannun professor,duk da tana hangen lokaci xai mata tsaho kafin komai ya mata yadda takeso,amma zatabi lokaci bisa takatsatsan da rashin gaggawa kamar yadda ta saba

“Kije ki bata duk aikin daya kamaceta…..amma tayi qazanta da yawa,banason a bata aikin daya dangancin abincinmu” ta fada fana dan qarewa kaltume kallo

“To hajiya” biba ta fada tana miqewa.

A hankali kaltume dake duqe itama ta miqe kanta a qasa,ita sam bata gane abubuwan da suke faruwa da ita,tun daga sanda aka daura mata aure zuwa yanzu,ita ba haka tasan ana zaman aure ba,shi wanda yake a sunan mijinta har yanzu jikinta da zuciyarta sunq amsar kalmar,a kallon ma datayi masa a jiya gaba daya sai taga wani irin bahagon dacewa tsakaninta dashi,tunda ya kawota gidan ya ajjiye bata ganshi sau biyu ba,na biyu an kawota wajen wannan matar dake tsareta da wani irin kallo dake sanyata fargaba da tsoro,kuma taji ana maganar a bata aiki,har tana qyamarta,bayan ko kafin ta fito ma sai da tayi wanka,to meye abun qyama a jikinta,to ko su a tasu duniyar haka ake zaman aure?,ta kasa warware wannan zaren,amma dai….koma meye zata zuba ido taga iya gudun nasu ruwan.

Babban kitchen ne,wanda duk girmansa an yishi bisa tsari na zamani,tsari me qawatarwa,kowa dake cikin kitchen din aikinsa yake gabatarwa,sai biba ta dinga bi da ita gurin kowa tana nunata suna gaisawa,kana daga bisani ta nuna mata waje tace ta zauna.

Bata musa ba ta zauna din,tsahon lokaci idanuwanta suna biye dasu,duk da rabi da rabin hankalinta naga gidan wajen ummanta,tare da tunanin a wanne hali take ciki,amma ta cika da mamakin yadda za’a ce wai wannan qawataccen wajen wurin an tanadeshi ne kawai saboda dafa abinci,tabdi,lallai wani aikin sai binni,ashe duk labarin maraya da sukeyi basusan ma komai game da ita ba,tunda hasashensu bai taba hasko musu irin hakan ba,to waishi mijin nata wayeshi ne,kuma me suke a wannan gidan?,a nan zasu dawwama ko zasu tafi?.

Ganin zaman ya soma tsaho ba tare da biba ta waiwayeta ba saitace da ita ta bata aikin da zatayin

“Ki zauna abunki,babu wani aiki me yawa yau,sai gobe idan Allah ya kaimu,idan kin gaji zaki iya komawa dakinki ki zauna” zata iya gane hanyan komawar amma bata da sha’awar ta koma din,don haka taci gaba da zama a wajen,har zuwa lokacin da najwa ta fito yin breakfast,ta kuma aiko cewa biba takai mata kayan karinta dakinta.

Kaltume ta baiwa wasu qananun kofunan qarau masu kyau da wani plate tace ta tayata dashi,tana biye da ita,suka wuce wani qayataccen falon kafin su dangana da dakin najwa din.

Tana zaune saman sofa ta miqe qafafunta da alama wayarta dake saman cinyarta take amsawa,kanta babu dankwali,tana sanye da wasu kayan bacci masu kauri da zasu iya tare mata dan sanyin da aka fara busawa,sai gashinta da bai wuce tsayin dan yatsa ba,saidai kuma a kwance yake yasha gyara.

Suna shigowa ta katse wayar,fuskarta a murtuke ta sauke qafafunta qasa tana bin kaltume da kallo sanda ta qaraso tana dire kofunan kamar yadda taga biba tayi

“Move dalla malama,matsa nace!” Ta fada cikin tsawa kamar zata sanya qafa ta buge kaltume,tsoratar datayi yasa taja baya da sauri,saura kadan kofunan da bata gama ajjiyewa ba su daki qasa su fashe

“Zuwaira meye haka din?,zaki kwaso min yarinya tana wari ki shigomin da ita?,tana tabawa mutane kayan abinci?” Kan biba a qasa tace

“Kiyi haquri”
“Fita ki bani waje,kin tsaya kina dumamawa mutane waje….idan ta fita ki dauka freshner ki fesa min”.

Da sauri kaltume taja da baya sannan ta juya tana hada hanya saboda sauri ta nufi qofa,tana jiyo sanda biba ke fasa freshener din,saita lumshe ido tana sakin ajiyar zuciya,tana jin yadda bugun zuciyarta ke qaruwa saboda tsoratar da tayi,su wadanne irin mutane ne wadan nan?,wacce iriyar rayuwa suke?.

“Kiyi haquri kinji?,haka take bata da kirki,nan muma kowa haquri yakeyi da halayenta” biba ta gaya mata bayan fitowarta daga dakin,kai ta kada,ta motsa labbanta a hankali

“Ba komai” saidai tana ji a zuciyarta,tunda har ya tabbata haka halayyarta take,ya zame mata dole ta nisanceta,duk da cewa ta girmemata,haka nan yanayin sukuni da muwalati na rayuwa sun bayyana banbancin dake tsakaninsu,to amma fa zuciyar nan tata har yanzu itace a qirjinta,ba zata juri cin mutunci da wulaqanci ba,bayan ba wani abu ta aikata mata naba dai dai ba.

*********Cikin takun dake qara nuna qasaitarsa,hannyensu biyu duka soke a aljihun Blazer din dake jikinsa ya isa bakin babban gilashin daya mamaye bangon yamma na office dinsa,wanda hakan yake bashi damar hangen ilahirin makekiyar harabar kamfanin dama wasu sassanni na unguwar,hannu yasa ya yaye dan wani abu da aka zuba daga gaban glass din me madadin labule yana furzar da iskar bakinsa,idanunsa ya sauka parking lot dake cike da motocin ma’aikata,can ya hangi fawwaza gaban tata motar,ta sanya muqulli tana bude motar,duk da ka gane yanayin fuskarta sosai,to amma daga nam yana iya karantar yanayinta.

Daga bakin office dinsa take,ya tabbatar ranta a bace yake,saboda hanawa da yayi a barta ta shigo wajensa,gaba daya yau ita da ire irenta babu wanda ya bari ya shigar masa office,shi yasa ya zaunar da umar daga waje,saboda yana da tabbacin shi din zai iya yadda yace masan.

Bai bar wajen ba har sanda ta shiga tabtada motar ta fice daga kamfanin,ya sani cewa ba lokacin tashi bane,kuma fitar tata tamkar ta karya dokar kamfani ne,saidai yana sane da komai,zai kuma yi maganin matsalarta.

Sauke labulen yayi,ya juyo a hankali yana duban saman table dinsa dake cike da files wadanda dukkansu shi suje jira,ga alamun gajiya da kasala sun bayyana qarara cikin kyawawan qwayar idanunsa.

Gaban teburinsa ya qarasa,ya dauki wayar landline yayi magana ta sakanni da basu wuce takwas ba sannan ya sauke wayar,ya koma ga files din yana buda wasu daga ciki,har zuwa sanda qofarsa tayi ‘yar qara alamun ana neman izinin shigawa,sau daya ya danna wani abu dake gefansa,qofar ta bude aka shigo

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button