Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 56

Sponsored Links

56

Sake maida kallonta tayi ga qofar dakin bayan ta dauke idanunta daga doguwar hanyar da har yau wanda ke tafiyar baikai ga bayyana zuwa inda take ba,ga mamakinta sai taga qofar na bude,sabanin daxu da ta ganta kamar a rufe,kafin ta kammala tunanin da zatayi taga anja qofar an bude mata,saita sauka da sauri ta sanya kai cikin dakin.

Hannunta taji an fincika,data duba sai taga matar ce,kafin ta gama tantance komai ta isa da ita bakin dan duqurqushin gadonta ta dage mata,ta gane me take nufi,don haka ta shige,ta sauke xanin gadon da ya sauka ya lullube har qasan gadon,tana iya hangenta ta tsakanin labulen ta koma ta zauna kamar yadda take daxun,wanda da zamanta da qarasowar wanda taji takun nasa duka bai wuce second biyar ba.

Yana mita ya shigo,kamar wanda yake magana da mutum me hankali
“Lalle sabi’u yana wasa da aikin nan,baisan girman aikin dana bashi ba,baisan kuma wace hajiya jidda ba,banda guntun iskanci ya za’ayi ya barwa mutane daki a bude?,salon ki fita ya jawo mana jidali?,dole nayi masa jan kunne me qarfi,idan bazai iya ba ya ajiye a bawa wani”.

Abinci taga ya ajjiye mata,ya dan tsaya kadan a kanta na wasu daqiqu,ba jimawa wayarsa tayi qara,yayi hanzarin dagawa ya soma amsawa,saiya juya yana ficewa daga dakina da alama wayar da yakeyi ta shagaltar dashi bai rufe dakin ba yadda suka saba ya fice da sauri.

Kaltum dake qasan gadon gaba daya jikinta ya jiqa da gumi,gaba kura baya sayaki,gata a cikin dakin me lalurar tabin hankali,wanda har sarqa aka tanada cikin dakin,da alama ana sanyata lokaci bayan lokaci idan buqatar hakan ta taso,na biyu ta ratso ta shigo wani shinge da aka jima ana mata gargadi kan furta koda kalma daya a kanshi,yau sai gashi,bama zancan muhallin ba,ta keta duk wani gurbi ta dangana da tsakiyar shingen tsundum

“Fito,ba zasu dawo ba sai tsakiyar dare ko kuma gobe…..” Taji ta furta da muryarta a sarqe kamar daxun bayan ta yaye xanin gadon.

Mamaki ya sanya kaltum ta xuba mata idanu,ta yaya take magana sak irin ta masu hankali,muryarta ras a kuma nutse?,banda yanayinta babu abinda zai sanyaka kayi tunanin ba lafiyayya bace,kamar tasan tunani da mamakin da takeyi sai ta sake jin muryarta

“Cikin hayyacina nake,kar kiji tsoron komai,fito….ina jin kece addu’ata dana jima inayi” wadannan kalaman nata su suka bata qwarin gwiwar fitowar kamar yadda ta buqata.

Zama tayi dandaryar qasa kamar yadda take daxun,saita yiwa kaltum nuni da wajen xama da hannunta,ta qaraso a hankali har yanzu da ragowar fargaba cikin ranta,saidai kuma ta samu qwarin gwiwa,ta zauna tana fuskantar kaltum din,a hankali ta buda baki

“Duk da bandan wacece ke ba,aiken jidda ce ke ko kuma ubangiji ne ya jeho min ke ki xame min haske kamar yadda na dauki tsayin shekaru ina roqa…….inason insan wacece ke” qas kaltum tayi da kanta,taga abubuwa masu tarin yawa suna kai kawo

“Ni ba kowa bace,face wata mara gata da galihu da samir ya dauko daga qauyensu,ya dawo da ita cikin gidansu,ya bata gata da galihu da kuma dukkanin kulawa”

“Samir dina?,ya zama mai tausayi da taimako kenan kamar yadda nake roqon ubangijina?” Ta fada muryarta na rawa,da alama zuciyarta fa tsinke,kuka na dab da zuwa mata kowanne lokaci.

Kai kaltum ta gyada mata tana dubanta

“Amma ya akayi kika sake dawo kanki cikin wannan hatsarin?,bayan na tabbatar zuwanki na farko qaddara tasa jidda zuwa dake?,kuma ina da yaqinin kin samu kyakkyawan jan kunne daga gareta?kinsan wacece ni ne?” Shuru tayi zuciyarta na raunana,batasan amsar da zata bata ba.

“Zuciyata ce ta kasa nutsuwa,tana ta gayamin na dawo gareki,bayaga tarin mafarkan da suka cika barcina” kai ta gyada tana kallonta,cike da yabawa da jarumtar yarinyar,tunda har tasan jidda,amma ta yadda ta fuskanci kowanne qalubale ta dawo gareta,ba tare da tasan ainihin wacece ita ba.

“Nice mahaifiyar samir…..samir dana ne” maganar data sanya kaltum ta kusa shidewa bayan ta dago da kanta,tabbas ta jima tana qiyasta haka,ta dade tana jin kamar hakane,ashe hakanne da gaske?.

Dauke idanunsa yayi daga kanta sanda take bacew ganinsa,ya sauke wata boyayyar ajiyar zuciya,idanunsa suka sauka kan amiru,sam baisan ya xuba masa ido yana kallonsa bane sai yanzu,wani qaramin murmushi amirun yayi ya dauke kansa,shima sai ya janye idanunsa,ya maida ga jauhar daketa fama da chart,amma rabin hankalinta na ga samir da takeja da hira,saiya miqe a hankali,a sannan ta daga idanunta daga kan waya tana dubansa

“Bakaci ko spoon daya bafa” kai ya girgiza yana zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa,a daqiqun da suka dan shude lokaci kadan yana jin kamar akwai wani dan waje da zai iya koda loma biyar ne,to amma bayan barin kaltum wajen…..sai yaji kamar ta tafi da dukkan wani sauran waje daya rage da zai iya zuba abincin

“Am coming”ya fada yana takawa a nutse yana barin wajen,gaba daya hankalinsa yaji ya dauku xuwa wajen daddy,mintunan da likitocin suka bashi zasu duba daddyn yana da tabbacin kafin qarasawarsa dakin sun cika.

A nutse yake takawa zuwa cikin dakin,bayan likitoci sun kammala aikinsu,sun kuma gama masa dukkanin bayanai kan cewa akwai ci gaba a ciwon nasa,su qara haqurin fitar dashi a basu kwana uku,idan hakan yaci tura saisu daukeshin.

Duk duniya baya jin akwai wanda yakejin abinda yakeji a qirjinsa,yana jin wata muguwar kewa tare da fargaba tana shigarsa,idan ya rasa daddyn ya tabbata bashi da kowa kenan,tunda har yau baisan duniyar da MAHAIFIYAR DATA GUDU TA BARSHI TAKE BA,abinda ya kasa goguwa cikin idanunsa,yana iya tuna sanda ta fice daga gidan ta gaban idanunsa,yana kuka yana daga mata hannu,amma ko sau daya bata waiwayo ta kalleshi ba.

Runtse idanunsa yayi,a hankali ya taka zuwa gaban gadon,ya sake janyo kujerarsa da kusan kowanne lokaci take ajjiye a wajen ya zauna gaban daddyn yana ci gaba da kallonsa.

Ya jima yana karanta addu’o’i yana tofa masa saman kansa,kafin ya sanya hannunsa cikin tafin hannun daddyn ya runtse a nasa,sannan a hankali ya saukar da kansa yana kallon hannuwan nasu dake sarqafe da juna.

Motsawa kadan yaga sunyi,abinda yasashi sake qura musu idanu ba qaqqautawa,still ya sake ji da ganin sun motsa din,sai kuma ya damqe hannun nasa gaba daya,abinda ya saka samir daga kansa da hanzari kenan zuwa fuskar daddyn.

Kamar numfashinsa zai dauke saboda farinciki sanda sukayi ido hudu da daddy yana kallonsa,bakinsa ya sarqafe,ya kasa furta kowacce kalma

“Allah yayi maka albarka” yaji kalmar ta fita daga bakin daddyn,saiya sake qura masa ido yana mamakin furucin daga bakinsa,sake maimaitawa daddyn yayi,bakin samir yana rawa yace

“Am….een…..ameen daddy,sannu”saiya gyada masa kai

“Dagani na zauna” ya fada a hankali muryarsa na sarqewa

“Bari a yiwa likita magana” ya fada da sauri yana miqewa

“Fara daga nin tukunna,ba abinda zai faru da izinin Allah,akwai maganar da nakeson gaya maka kafin shigowar kowa” cikin hikima ya dagashin ya jinginar dashi,yana fatan basuyi kuskuren aikata hakan ba,saidai yana zama yadan fara haki

“Daddy….ka bari a kirasun” qaramin murmushi ya saki yana dafa kafadar samir din,cikin hakin ya sake cewa

“Nayita roqon Allah……ya bani aron……rai da lokacin da zanta ce maka……Allah…..yayi maka albarka…..na….godewa Allah da…. .ya aramin din…..,abu na biyu……banason kace komai akan ciwona…..koda kuwa akwai wani abu da kake zato……ina bala?”

Cikin mamakin kalaman daddyn yace

“Yana dakin da aka kwantar dashi,amma da gobe zasu sallameshi” sai daddyn ya gyada kai,yana son cewa wani abun amma hakin ya qara yawa,abinda ya tilastawa samir din fita da hanzari kenan,saidai wani sashe na zuciyarsa ya cika da farincikin da zai iya cewa tunda yake rayuwa a duniya bai taba jin irinsa ba.

“Ni din mahaifiya ce ga samir,yaro daya tilo nawa dake raye a duniya….haifaffiyar qasar sudan ce,birnin Khartoum,munyi auren saurayi da budurwa da rashid a lokacin da yake University of Khartoum wato U of K,bayan ya kammala karatunsa muka tattaro muka dawo qasar nan da zama bisa amincewar dangina da kuma yarda da nagartar halaye da dabi’unsa.

Muna zaune cikin lumana da rufin asiri,da amintattun masu aikina guda biyar,saidai biyu daga cikinsu sunfi shiga raina,kuma minfi shaquwa dasu,zuwaira da kuma harira.

Muna zaune da kowa lafiya a dangin rashid,saidai bani da ‘yar uwa qawa kuma aminiyar da nake jinta a raina kamar hafsat,ta daukeni kamar ciki daya muka fito da ita,kamar yadda nima na dauketa hakan.

Mun samu zama na fahimtar juna da qauna,har zuwa lokacin da rashid ya shiga siyasa bayan na haifi samir da wasu ‘yan watanni,siyasar data dauke hankalinsa matuqa fiye da yadda yake a da,duk da cewa dukkan wani haqqinmu babu abinda ya sauke ko ya fasa bamu,saidai mun rage samun lokacinsa kamar da,saboda harkokinsa na siyasar da kuma kasuwancinsa da Allah ya sawa albarka yaketa habaka.

Kowacce rana a rayuwar dan adam tafe take da qaddararta,muna cikin wannan xaman namu na aminci,kwatsam jidda ta shigo rayuwarmu,shigar data sauya qaddarata izuwa bigiren da muke kai a yanzu.

A wata rana bayan mun fito daga asibiti,nakai samir dake fama da zazzabi,nida zuwaira,zuwaira na gaban mota ita da driver ni ina baya muna hira kadan kadan sanda driver zai fito daga cikin asibitin,daga gefe a rakube na hangi wata yarinya,wadda a qalla zan bata shekara uku ko hudu,kuka take sosai tana kakkarwa,har zamu gota tausayinta ya tsargamin saboda irun kukan da take,na saka driver yayi parking,na fita na sameta.

Ta dan tsorata da farko da ganina,amma daga baya saita saki jiki,na tambayeta ta gayamin labarinta kan cewa,su ba ‘yan garin nan bane,bata da kowa a duniya,saida kakarta ta rage mata,ita ke riqonta,to itama kakar tata sai Allah yayi mata rasuwa,sai wata mata dake siyan quli da daddawa wajen matar ta dauki riqonta,ashe matar magajiyar karuwai,data kaita gidanta tayi tayi da ita kan ta shiga harkar neman maza amma taqi,dalilin da yasa ta dinga gana mata azaba kenan,data gaji shine ra gudo.

Sanda na dauketa zuwa gidana banji komai a raina ba,hakanan ban kawo komai ba,kawai na saka a raina cewa,duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimakeshi.

Amma tunda muka zo gidan muka tattauna da xuwaira naga rashin gamsuwarta da lamarin,abun ya dan bani mamaki,saboda nasan cewa ba halayyar zuwaira bace,tana da kirki tana da tausayi,abinda yasa muka jitu kenan tamu tazo daya,saidai duk da na karanci hakan ga fuskarta,bata fito fili ta gayamin ba,har sai dana tuntubeta da cewa

“Naga kamar xaman hauwa dana yanke tare da mu baiyi miki ba ko?” Murmushi kawai tayi sannan tace

“Ba haka bane,rayuwa ce yanxu ta canza,duniya ta zama abar tsoro,taimako ya zama shima abun tsoro,kawai dai inaga ya kamata kisan ainihin wacece ita kafin ki xauna da ita” a lokacin murmushi nayi

“Banda abinki zuwaira…..ta yaya zansan wacece ita?,bayan bata da kowa?” Kai zuwaira ta kada

“Bazaiyu mutum ace kaf danginsa babu mutum ko daya ba,ba’a rasa saura,idanma babun,can inda ta zauna ita da kakarta kafin rasuwarta ya kamata ki tambayi halayyarsu kiji” a lokacin gani nake kawai hasashe ne irin na zuwaira,amma kamannin jidda basuyimin kama dana wata mai mummunar dabi’a ko halayya ba,don haka nabi zuwaira da cewa zan bincika na share zancan kawai,jidda taci gaba da rayuwa damu.

Abun kamar hadin baki haka hafsa tace min,da yake tana da zafi ma har sabani mukaso samu da ita,tace nikam bani da wayo ne ko bansan ciwon kaina ba,da zan dauka mutum rana tsaka na kawoshi rayuwata ban bincika ainihin wayeshi ba,nace mata babu komai,Allah na nufa,kuma ina fatan ya sanyawa nufina albarka,tun tana mita da qananun maganganu har ta haqura ta zuba idanu,saidai a yadda take kallon jidda da yadda take mu’amala da ita zakasan kwata kwata bata kwanta mata a rai ba,don ba haka take mu’amala da sauran masu aikin gidan ba.

Ta bangaren rashid ban samu matsala ba,saboda a sannan din jiddan da girmanta,budurwa ce,ta haura shekara ashirin ma,saboda haka ta haura shekarun da baya daukar masu aiki a cikinsu,yace dai kawai idan ina ganin dai daine shikenan,ta zauna din tare damu.

Maganganun zuwaira da hafsa suka sanya naqi sakin jiki lokaci daya da jidda,na dinga karantarta a nutse,amma banga wani aibu ko mummunan hali tattare da ita ba,sai hidima da soyayya da take nunawa samir,fiye d wadda ni uwarsa nake nuna masa,hakanan fiye da wadda su zuwaira ke nuna masa,idan tana gidan samir baya kuka,babu me tabashi,babu me masa fada,baya neman abu ya rasa,kai hasalima idan kaga samir a wajena tun a lokacin nono kawai zai sha ya koma wajenta,ko yaye dana tashi ita ta karbeshi ta yayeshi,a lokacin hafsa ta tada ballin bala’i kan ita tace zata yayeshi ai,zata hadashi da yaronta amiru,wanda suke sa’anni,tsiran kwana biyu ne haihuwarsu,jidda na kuka tana bata haquri ra tattara samir ta kai mata,don ko sau daya bata taba nuna ta gane hafsa bata qaunarta ba,hakanan bata taba nuna damuwa kan rashin qaunar dake idanun hafsa ba,kullum girmamata take da nuna mata qauna.

Kowa sai daya tausaya mata sanda samir ya tafi yaye wajen hafsa,ta koma sukuku babu wani walwala,har rashid ya gane,a sanna magana ta soma hadasu,ya tsokaneta da maman samir,yace kuma zai lallaba hafsan ta dawo mata dashi.

Wannan shine silar fara magana tsakaninsu,saboda mahaukacin son da rashid yake nunawa samir,kamar an gaya masa cewa shi kadaine abinda zai haifa a duniya.

Na riqe jidda cikin martabawa da girmamawa,na bata suttura irin wadda nake sawa,na bata irin abincin da muke ci,na bata makwanci tamkar na matar gida,na kula da buqatunta fiye dana kowa,saboda a lokacin ina ganin tafi sauran ma’aikatana quruciya,inaso ta tsare kanta da mutuncinta har tayi aure.

Cikin hakan na duba certificate na secondary dinta,banyi qasa a gwiwa ba na samar mata gurbin karatu cikin jami’ar da nake koyarwa,ba matsala ko wahala ta samu saboda muqamin da nake dashi a sannan, course me kyau na samar mata,saboda dukka ina duba gobenta.

Tafi tafi jiddan ta soma sakewa damu,ba jimawa ta koma kamar ‘yar gida,a hankali sai duk wata sabga ta gidan ta fara komawa wuyanta,bayan tsantsar kulawa da samir,wanda wani lokaci tare suke zuwa lactures su dawo,har wasu ma na tsammatar danta ne,wanda sukasan bata da aure kuma sun dauka qanwata ce,dukka ina ce musu eh,saboda nima inajin dadin zama da hauwa,tana da matuqar ladabi da biyayya,hakanan tana yabawa sosai da dukka hidimar da nake mata,saboda babu abinda zan siya ban siya mata ba,don a lokacin dan dai Allah ya hadani da mutane masu tsarkakakkiyar zuciya ne,daba shakka a sannan babu abinda zai hana hassada da qyashi shiga zukatan su zuwaira akan jidda,amma Allah baisa sun nuna komai ko sun damu ba.

Cikin qanqanin lokaci ban farga ba na fara ganin wasa da dariya sun fara shiga tsanin rashid da jidda,na danju kishi kadan,amma abun ban wani bari yayi tasiri sosai a raina ba,saboda naga dukka akan samir ne,fiye da rabin hirar tasu ma duk kan samir ne da abinda zasuyi yaji dadi,rayuwarsa ta inganta,don haka sai na saki raina,da zuciyata daya naci gaba da sabgata.

Kwatsam ban ankara ba sai sabo da shaquwa ya fara gittawa a tsakaninsu,hira raha da wasa da dariya,tun ban damuwa har na fara jin kishi sosai a raina,amma na rasa ta yadda zan yiwa rashid qorafi,saboda yadda jidda ke bani girma tana kuma sake bada himma wajen kula da samir da nuna masa soyayya da kulawa.

Wasa wasa abu yaci tura,har takai ta kawo rashid zai dauki jidda da samir su fita shopping ni ina zaune,koda abu ne wani lokacin idan bana kusa saidai ya bawa jidda ta riqemin kota ajjiyemin,idan nayi magana sai yace,ai yaga na aminta da jiddan ne,kuma yarinyar nan tana da hazaqa da qoqari,komai.naki dana yaron nan ita ke muku shi,haushi ya cikani,na tsuke fuska nace

“Ai ba gazawa taga nayi ba ko bare ka gayamin haka” dariya ya fashe da ita

“Kai raihana,ban sanki da wannan ba,kishine kawai yake damunki hala,amma jidda ai hutu ce a wajenki,kaf masu aikin gidan nan babu wanda yake aikatuwa irinta” gaskiya ne abinda ya fada,amma abinda na gani shine,babu wata sabga data zama wajibina dana gaza,komai na kula da mijina ban fasa ba,aikina bai sanya na rageshi da komai ba,kuma shi dinma harkokinsa sun sanya ba mazaunin gida bane.

Abu daya ne da ban ankara dashi ba sai sannan,jiddan tana da azarbabi,wasu abubuwan na rashid ko na samir duk sanda na tashi xanyi saina tarar tayi wuf tayishi,koda baqi nayi kafin nace ayi musu kaza tayi,duk wanda yazo gidan saiya tafi da kirkin jidda a bakinsa,duk sanda muka hadu ya dinga tambayar ina jidda?,yarinya me kirki,musamman dangin rashid,cewa suke nayi dace da yarinya me kirki,ranar da family na daga sudan sukazo kuwa,zaka ce wajenta suka zo,duk wata hidima tasu a wuyanta take har suka tafi,da na dan motsa zatace aa na zauna miyi hira da baqina.

Randa na hada undies din rashid xan wanke a toilet dina,nayi baqi na fito muna gaisawa bayan ta saukesu a wannan lokacin na fara taka mata burki kan ta daina shiga hurumin daba nata ba,tana hawaye ta bani haquri,idan raina ga baci nayi haquri,ita batayi don wani abu ba,tayi ne saboda taga jiya iwar haka ina kwance bani da lpy ina fama da zazzabi,yadda naga tanata kuka tana bani haquri sai naji babu dadi,naga kamar ban kyauta mata ba,tunda kulawa ce tasa haka,amma komai kulawa bai kamata ta taba kayan da suke sirrin mijina ne,nace mata ya wuce amma ta kula.

Kwana biyu haka ta dinga rayuwa sukuku a gidan,har samir sai daya koka saboda yadda ta koma ba kuzari,rashid ma ya fuskanci haka,ya kuma sameni da maganar.

Fada sosai na dinga yi,ta inda nake shiga ba ta nan nake fita ba,saboda raina haka kawai naji yana quna,bugu da qari kima yaron cikin dake jikina,wanda ya qaramin zafi,baice komai ba harna gama,sannan ne ya amsa min da

“Kada dai kije kishi ya rufe miki ido ki batawa wanda yake qoqarin kyautata miki” lafazin da ya sanya jikina yayi sanyi kenan,na rage daurewar dana fara yi mata.

Yan kwanaki tsakani laulayi ya sakani a gaba,sai komai ya sake komawa hannun jidda,ni kaina a sannan na yaba mata,yadda take hidima damu kan jiki kan qarfi,bata xama ta huta kona minti daya,ga makaranta tata data samir wanda ya fara zuwa ba jimawa,ban samu kaina ba har sai da nayi barin cikin,taci gaba da hidima da ni har na warke na koma kan harkokina.

Ban jima ba na sake samun wani,shima dai itace komai.namu,wannan ya qara kusanci me qarfi tsakaninta da samir dama rashid,shima dai cikin sai da ya fita na samu sauqi,bayan na warke saina sake ganin canji sosai tsakanin rashid da jidda,idan nayi magana yahau fada,yace duk kyautatawar da takemin bana gani?,sai shi don ya kyautata mata?.

A wannan lokacinne rigima kusan taso barkewa tsakanin hafsat dashi,ta shiga maganar,ya hadamu duka yace bamu da kirki kuma bamu da halacci,kamar yadda na gaya miki,hafsat tana da zafi,saita qyaleshi kamar anbar maganar,tafiya tana kamashi tazo ta sanya jidda tattara kayanta tace lallai sai tabar gidan.

Yadda jidda ke kuka tana roqon tayi haquri ya karyarmin da xuciya,ina qoqarin cewa ta barta,amma hafsa ta hada harda ni,haka nan tasa jidda ta tattara tabar gidan,ta gama kin bambamin fadan na zauna lusaranci,idan baiyi wasa ba zafa qwace rashid a hannuna,tayi ta gama ta fita.

Tunda jidda ta fita duka sai tausayinta ya kamani,na kasa nutsuwa,musamman idan na tuna cewa bata da kowa,to ina zataje?,itace tambayar data dinga damuna,na tsaya gaban madubi na dubi kaina,sai naji bana ji sam bana tsoron zama da jidda,banjin zata iya qwacemin rashid,duba da irin halaccin da na yiwa rayuwarta,halaccin da nakejin ya isa yasa jidda taji kunya da nauyin aikata min ba dai dai ba,uwa uba bata ko kama qafata wajen kyau da diri ba?,to meye zanji tsoro?,wannan tunanin ya sanyani fita neman inda jiddan tayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button