Sponsored Links
Hausa NovelsSoldiers Family

Soldiers Family 13-14

Sponsored Links

Page 13&14

__”ko da suka K’arasa acan suka Sami gimbiya halila bayan tayi musu duk abunda yadace kana tayi musu sallama ta tafi…bawan Allah bai tashi ba saida yashafe awa biyar 5hr Yana baccin wahala kamun ya farka, mama na gefenshi ta zabga uban tagumi tana kallanshi ganin yabud’e idonshi Yana k’ok’arin tashi zaune yasa mama temaka mishi ya tashi tare da d’aukomai ruwa tabashi tana fad’ar sannu Abba gashi kawanke bakinka sekaci abunci…shidai da Ido kawai yake binta Kuma beyi abunda tace ba ganin hakan yasa mama zuba ruwan ahannunta takuskure bakinta tare da janyo hannunshi shima ta zuba mishi, ba musu ko yayi yadda tayi sai da ya wanke bakinshi sosai kana tabashi abinci aiko kamar jira yakeyi yakarb’e dasauri yafaraci…Ido mama tazuba masa sai da ya cinye tass kana tabashi ruwa yasha abun mamaki sai kawai taga yana Mata murmushi itamayi yimasa tayi kana tafita gunsu biba…tin daga wannan ranar mama ke kula da Dan tsohonnan Kuma betab’a yunk’urin gudu ba ko cutadda ita Kuma duk zamanda suke shibetab’a ganin su mero ba ko gimbiya halila dake kawo musu ziyara Shi mama kawai yake gani itace cinshi da shanshi har sallah ma yanzu sukeyi tare abun gwanin Sha,awa tad’aukeshi kamar mahaifinta..!

Dubai

Fitowarshi kenan daga wanka Yana goge jikinshi yajiyo sallamar Suhaif daga perlon jallabiya ya janyo ya saka tare da boxes d’inshi kana yace ya shigo shiko ya zauna gefen gado Yana shafa manshi…shigowa Suhaif yayi ya tsaya Yana kallonshi jin anshigo anyi tsaye kuma ba,ayi magana ba ya sakashi d’agowa yana duban k’ofar Ido yak’ara bud’ewa sosai Yana kallonshi ganin idonshi cike tab da k’wallah…Baki yabud’e zaiyi magana sai kawai Suhaif ya fad’a jikinshi tare da ƙanƙameshi yana sakin marayen kuka..hankali tashe Alyasat ya shiga shafa bayanshi yana me karanta duk addu,ar da tazo bakinshi domin yasan tabbas ba lafiya ba?…bai hanashi ba kuma bece komai ba sai da yayi me isarsa kana ya d’ago yana kallonshi cikin muryarshi data disashe saboda kuka yace, “Yaya Sat ammy Yaya sat Miyake faruwa damune da iyayenmu abbe ya Bata ammy takwanta ciwo yanzu kuma abun sekara tsananta yakeyi” kasa ƙarisawa yayi saboda d’agowar da Alyasat yayi masa da ƙarfi Yana fad’ar, “me yasami ammy? Wani abunne yafaru? kuka Suhaif yakoma sakawa kamun ya bashi labarin yadda suka sami ammy a yau cikin tashin hankali Alyasat ke maimaita kalmar, “innalillahi wa innailaihhiraji un” yanayi yanajin abunda ya tokare masa zuciya na faɗawa sunɗau tsawon lokaci ahakan kamun Alyasat ya zaunarda shi, ya buɗe baki zaiyi magana kenan Alhassan da Alhusain suka shigo suma ga dukkan alamu kukan sukayi cikin sauri suka ƙarisa wurinshi tare da rungumarshi atare suna faɗar, “I miss you my lovely bro I miss you so much please karka tafi kabarmu ammy batada lpy abbe” shiru yayi saboda hannu da Alyasat ya ɗora mashi abaki Yana girgizamai kai tare da share mai hawayenshi, sunɗau tsawon lokaci ahakan kamun suji voice d’inshi yana faɗar, “kuyi haƙuri ku dena kuka ku kasance masu ta wakkali ga Allah Subhanahu Wata’alah, aduk abunda ya sameku ku tuna cewa duk wani tsanani yana tare da sauƙi muɗauka wannan abun dake faruwa ga iyayenmu jarabawace Allah ke mana” shiru yayi yana ɗan cizar laɓɓanshi (lips) ɗinshi kamun yaci gaba da faɗar, “wannan abun ƙaddarar rayuwar suce bamu isa mu canzata ba muzama masu d’aukar k’addara me kyau ko akasin haka kunji ko? kurinƙa yi musu addu,a itace abunda suke buƙata agaremu adaidai wannan lokacin, Allah ya warware Mana koma miye Dan Alfarma Sayyidina Rasulillah”…

“Ameen ya Allah suka amsa atare” kana yatattarasu duka suka nufi bedroom d’in ammy yadda ya barta hakan suka sameta addu,a sosai suka yiwa mahaifiyar tasu kana suka Kira d’aya daga cikin masu kula da ita domin surik’a kwana tare suko suka fito wannensu zuciyarshi acinkushe.

Fita Alyasat yayi izuwa part d’in habibbty Koda yaje bakowa a perlon hakan yasa yanufi bedroom d’inta nan ma batanan wucewa yayi tabaya domin yaduba kotana lambu sai kawai ya hangi Najeeb zai shiga bedroom d’inshi wata budurwa na biye dashi domin shiko anan yake da d’aki part ɗin habibbty mamaki sosai ya kama Alyasat na mi wannan budurwar ta zoyi d’akin Najeeb ba dai cikin ƙannensu bane to wacece? Wata zuciyar tace masa to Kuma wacece miye ruwanka tinda bakasan abunda ya kawota ba kawai sai ya wucewarsa inda yasamu habibbty acan lambun kuwa..zama yayi akusanta tareda Dora kanshi gefen kafad’arta sai dai bai sakarmata nauyin shiba..shafa kashi tayi kamun tace Alyasat..”uhm ya,amsa atak’aice…shiru tayi nad’an wani lokacin kamun tace ka cigaba da hak’uri kaji Kuma ka kulada kannenka nasan izuwa yanzu kasan abunda ke faruwa da mahaifiyarku ni kai na abun na kwancemun lissafi amma duk tsanani yana tare da sauk’i kaji mijina..kai kawai yad’aga mata domin baiji zai iya magana ba…. murmushi tayi ganin hakan kamun tace, “sai magana ta biyu kana jina kuwa?”

Idonshi yad’an bud’e alamar Yana jinta kamun yakoma lumshesu..”hummm me hali baya fasawa ta fad’a aranta afili Kuma sai tace sai zancen aure kasani ya dace kayi aure Alyasat tinda Kaine babba kodan a samu mace agida waddda zata tayaku kula da mahaif

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button