Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 24

Sponsored Links

Jefa qafarta kawai take ba tare da tana kallon gabanta ba,wani zafi qirjinta yake mata,kamar yadda taji idanuwanta na suya,saboda radadin hawayen dake taruwa cikinsu,wanda sukeson zubda kansu amma ta hanasu sauka.

Tunda ta samu nasarar fitowa daga cikin gidansu saboda sanda mahaifinta ke zazzagar masifa,cikin tashin hankali,saboda batason kunnuwanta su sake ji.mata wasu kalaman na daban bayan wadanda taji,A hankali ta yiwa kanta hanya zuwa bakin rafi,cikin ikon Allah kuma bata hadu da kowa a hanya ba,bare ya tsareta da tambaya ko ya kawo mata cikas.

Dab da ruwan ta zauna,yayin data rungume gwiwoyinta dukka a qirjinta,ta kuma zubawa ruwan idanu,babu abinda ke yawo a kanta sai kalaman mahaifinta,tana jin yadda suke yawo a saman kanta,kamar ana mata tsawa cikin kunnuwa.

Wani rauni ne ya mamaye zuciyarta,wanda ya sanyata ballewa da kuka,kukan da ya taho da nauyi da kuma qarfinsa,saboda yawa da girman damuwar da take ciki,kuka take sosai,irin kuka daka rasa matallafi ko wanda zaka dora kanka a kafadarsa da zummar samun lallashi ko kuma qwarim gwiwa.

A hankali yake tattaki a kewayen gurin,yana sake nazarin filin,tako ina filin yayi,kuma zai dace da gidan gona qwarai da gaske,yana buqatar wasu shawarwari daha wajen wani mutum babba mai hankali,kamar dai mahaifinsa,saidai shi yasan bashi da wannan gurbin ko kuma damar,saboda ya riga daya sani,abune mawuyaci mahaifin nasa ya fahimceshi,baisan meyasa ba kasafai yake fahimtar dumuwarsa ba?,baisan me yasa bai auna damuwarsa da ra’ayinsa da kuma abinda yakeso akan mizanin ababen da yake buqatar a kula shi domin su?,wani aikin sai uwa…….wani sashe na zuciyarsa ya gaya masa,maganar data sanyashi lumshe idanu yanajin wata faduwar gaba da wani suka a qirjinsa

“La’ilaha illallah” ya furta a hankali,baikai kuma ga hade labbansa ba sautin kukan ya shiga kunnuwansa.

Da sauri ya bude idanuwan nasa,sannan ya fara waige waige a nutse yana neman daga inda kukan ke fitowa.

Taku ya soma yi zuwa gaba kadan ganin bai samu nasarar ganin mai kukan ba,sai sautin kukan dake ci gaba da tashi,takun nasa da bai haura goma ba ya hangeta.

A durqushe take kamar me neman gafara,saidai kuma kuka take haiqan mai cike da nuna rauni da kuma gazawa.

Idanu sosai ya zuba mata,yana iya hangenta tar daga inda yake tsayen,hannayensa soke a aljihun wandonsa
“Kuka?” Ya fada cikin zuciyarsa kama me tambayar kansa da kansa,a ganin da ya mata tun karon farko,zarrar da yake ganin tana da ita,baiyi tsammanin ganinta cikin hali na kuka irin haka ba,saiya soma takawa a hankali yana nufarta.

Saidai tun baiyi nisa ba yaja ya tsaya,gami da takawa kansa da kansa burki,sam ba halinshi bane,ba kuma dabi’arsa bace shiga shirgin daba nashi bane,yana ganin kuma bai kamata ace a yanzu ya fara ba,kan mutanen da yake hangen baqin dabi’u wanda jahilci rashin ilimi da rashin wayewa ya haifar musu da su.

“Kattume…..kattume” kiran sunanta ya mamaye wajen,shi da ita dukka suka maida idanuwansu ga inda kiran ke fitowa.

Lantana ce afujajan,tana tafe kamar zata tashi sama,sai kaltum din ta zuba mata idanu tana kallonta da dan sauran hawaye da suka fuskarta kwalliya.

Gab da kaltum ta zube,fuskarta kamar zata fasa kuka tace
“Wai me yake faruwa kaltume?,me yake faruwa a cikin gari?,yanxun nan wasila ta fito ita da qawayenta suna shewa…..wai an kawo kudin aurenta da nasuru gidansu yanzu yanzu…..har tana cewa da zafinsu suka iso,saboda fitowar kudin kenan daga gidanku?,me yake faruwa?,da gaske hakane?” Sai data lumshe idanunta tana jin yadda labarin ke barazanar danne fitar numfashinta,kafin tayi jarumtar baiwa kanta qwarim gwiwa,ta gyada ma lantana kai tana dubanta kai tsaye

“An karbi kudin auren nasuru daga gidanmu lantana haka ne,amma bani da masaniyar an kaiwa wasila,tunda ba’a fi awa da karbar kudin ba”.

Tsaiwarsa sosai samir dake tsaye daga can baya inda ba lallai su iya hangoshi ba ya gyara,yana sake cusa hannayensa cikin aljihun wandonsa,idan bai manta ba…..kamar wanda take maganar a kana saboda shine taqi saurarar abokinsa haladu….to amma how comes aka amsa kudin?” Ya samu kansa yana yiwa kansa wannan tambayar,saiya sake tsaiwa yana sauraren amsar da lantana take bawa kaltum
“Kai jama’a……haka wasila take?,wacce iriya annmimiya ce ita?,ta yada qarya da sharri gareki,ta rabaki da masoyinki,sannan kuma ita ta mallakeshi?…..”.

Lumshe idanu samir dake tsaye yayi,bayanan lantana da suka fito a jejjere ya daki zuciyarsa,qarya,ha’inci,cin amana,qazafi…..yara qananu da duka duka rayuwarsu a yanzun take tasawa,amma har su iya shirya irin wannan aiki?,banda ma rayuwa ce irin ta qauye,kafataninsu suna qarqashin kulawar karatu ne data iyaye,babu wadda a cikinsu yake ganin takai girma da zata dauki irin wadan nan abubuwan,saiya tuna qanwarsa kuma autarsu jawahir…..duk cikinsu babu sa’arta,amma har yanzu kallon qaramar yarinyar da bata gama mallakar hankalin kanta suke mata ba.

Baiji sauran tattaunawar da suka biyo baya ba,sai jin magana yayi cikin daga murya da fushi.

Matashin saurayine tsaye gaban kaltum din,tashin hankali sun bayyana qarara saman fuskarsa,yayin da kaltum ke fada cikin fushi

“Baka da sauran abinda zaka gayamin nasuru,kaje kawai yayi biyayya wa iyayenka”

“Don Allah ki saurareni kaltum,ki fahimceni mana,lantana ki ganar da ita,duk abubuwan da suka faru babu wanda nake da masaniya a ciki,wallahi Allah nima sai yanzu baaba take gayamin komai,koda naje gida nemanki umma tace batasan inda kikayi ba,itama nemanki take,bansan komai ba”.

Wani kallo ta watsa masa,muryarta na rawa tace mishi

“Nasuru” saiya amsa da sauri,yana fatan jin kalaman fahimta da kuma goyon baya daga gareta

“Kana tunanin inda nice ummanmu tayimin abinda baba tayi maka….zan bijire mata ne?,zan sake kallonka da sunan aure?” Saita girgiza kai

“Har abada na haqura,iyaye su na dabanne…..ka koma kabi zabinsu”.

Babu wanda maganarta bata burge ta kuma dakeshi ba a wajen,hatta samir dake tsaye da basusan da tsaiwarsa ba dariya nason subuce masa,shikam salon soyayyarsu dariya take bashi,wani lokaci abun kamar wasan ‘yar tsana,duk da cewa a wannan karon sai yaji yanayin da suke ciki ya dan tabashi,amma ta wani fannin idan ya kalla kaltum din,dukanta bata wuce ace rainonta ake ba,amma ake maganar soyayya da aure……saida kuma,maganarta da tayi a yanzun sosai ta tabashi,ta kuma sanyashi cikin wani yanayi daya jefa tunaninsa izuwa wani bigire mai nisan da baisan iya adadin lokacin da zaikai kafin ya kamoshi ba,ya tuna masa wani babban jigo na rayuwarsa,majinginarsa kuma wani gwaggwaban sashe dake da kaso mafi girma cikin rayuwarsa,sai jikinsa yayi sanyi shima kamar yadda jikin sauran yayi,su duka ukun hardashi dake a bayan fage,suka zuba mata idanu sanda take bin hanyar barin rafin zuwa gida.

Batayi cikakken taku goma ba sukayi kacibus da bilal

“Yaaya,ina kika shiga umma nata faman nemanki?”

“Muje bilalu” ta furta da sauri tana yin gaba,saboda batason nasir ya cimmata,tana fatan yanke alaqa ta har abada tsakaninta dashi,tana son zuciya ruhi da gangar jikinta ta manta dashi,ya kuma bace bat daga cikin rayuwarta gaba daya,bacewa ta har abada.

Daga inda yake tsaye yaga zuwan bilal da juyawarsu a tare,ci gaba yayi da kallonsu suna yiwa ganinsa nisa,bilal……ya ganeshi,a hard worker,yana mamakin qwazon yaron wajen aiki,baya fushi,baya gajiya,yakan hada aikinsa dana wasunsa duka yayi ba tare daya damu ko ganin ido ba,a tashi biyansu kuma a biyasu kai daya,kullum sh yake riga kowa zuwa,ya gama karantarsa….yana aikine da zuciya da kuma jikinsa gaba daya,babu alamun ha’inci ko gajiyawa cikin aikinsa,dalilin da yasa aka nemoshi bayan tafiyarsa da daina zuwansa aiki,dalili da yasa yaji cikin zuciyarsa yaron zai zama wani abu,yana da wasu nagartattun boyayyun halaye da yaji sha’awar sanyashi yayi karatu me zurfi,yakan dan dauki wasu mintuna lokaci bayan lokaci su danyi hira dashi,yana magana cikin nutsuwa da girmamawa.

Cikin zuciyarsa yake jin tabbas akwai wata rayuwa,akwai wata rayuwa cikin rayuwarsu,akwai wani abu,duk da ba kasafai yake damuwa da abinda ba’a sanyashi ciki ba,bai daukar al’amuran da basu shafeshi ko ba’a nemi jin ta tashi ba,matuqar ba cikin nemon taimako ko halin hau’ula’i kake ba,to amma,shima mutum ne kamar kowa,wani lokaci akwai ƊABI’AR ZUCIYA,nason jin wani abu da son sanin ainihin abinda ke faruwa.

Ajiyar zuciya ya sauke yana juyawa don barin wajen,zuciyarsa na qoqarin yakice masa wancan abun da yaji ya gani,tana tuna masa tarin nasa matsalolin,amma ba shakka,cikin maganganunta akwai abubuwa da yawa data fada,wanda suka tsame masa kamar wani tuntuntuni cikin rayuwarsa.

********kwanaki biyu kenan tana jin wani ciwo a ranta,duk sanda ta tuna wasila sai taji babu dadi har cikn ranta,duk da tasamu gudunmawar qarfafawar gwiwa da maganganu masu ma’ana daga mahaifiyarta,to amma totally gaba daya batajin dadin komai,tana jin gidan nasu kamar wata maqabarta,duk wani sauran walwala da suke qoqarin ganin cewa sun samar a gidan babu ita ta gudu,wani shafi na masifa bala’i mita da cin fuska mahaifinsu ya bude,babu wata rana da zata fito ta kuma fadi basu ji babu dadi ba dangane dashi.

Dukkansu sun fawwalawa Allah,suna qoqarin kai zuciyarsu nesa,dannewa da kuma dabi’antar da zuciyar tasu bisa doro da bigire na haquri.

A dan tsakanin rayuwa ta koya mata abubuwa masu tarin yawa,wani dimbin ilimi ta samu,ilimin daya tasamma sauya wasu daga cikin halayenta,ta koyi taushi da laushi,ta koyi cinye da danne matsi da qunci.

*********A nutse taja murfin langar data cikata da dambu,wanda sukayi da ragowar shinkafar data rage musu cikin gidan,daga ita kuma basu da wani sauran tartibin abunda zasuci sai abinda baban yaga dama ya basu.

Tun daxu aka gama dambun,ana kuma jiran shigowar bilal ya kaiwa habiba dambun,saidai har yanzun shuru babu shi babu dalilinsa,ummansu dake fitowa daga bayan gida ta dubi kaltum din

“Kinga kaltum,dauki mayafinki ki xagaya ki miqa mata kinji,dawowae bilalu ba yanzu ba,tunda aka kusa gama ginin nan yanzu ba kasafai yake shigowa da wuri ba” tunda abun ya faru batason fita ko ina,zata iya cewa bata qara fita koda babban tsakar gidansu ba bare waje,amma yanzun ba zata iya musu da umman ba,saidai gidan habiban ne ma batason zuwa,saboda ta layinsu wasila zata wuce,rashin son bi ta layinsu wasila kuma bai isa hujjar da zata wofantar da aiken umman ba,don haka ta amsa mata da to,ta miqe ta shiga daki.

Da hijabinta a hannu ta fito,sai taja ruwa ta zuba a buta,ta wanke qafafuwanta da fuskarta ta shafa mai,sannan ta saka hijabin ta dauki kwanon ta fito.

A farfajiyar gidan nasu taga inna laure da siya a tsaye,asiyan taci ubansu ado,sai tashin qamshi take,riqe da wata qaramar jaka da tafi kama data matafiya,idaunta ta dauke,sai su duka suka tabe baki,kafin asiya ta sheqe da dariya sannan tace

“Nidai inna zamu tafi,sai Allah ya dawo damu,kuyi amfani da wadan nan kudaden,banason naga kuna cikin garau garau”

Sosai inna lauren ta wage baki,kamar wadda aka danqarawa kyautar kujerar makka

“Yar halak,’yar arziqi irin albarka,yarinyar dana haifa da bismillah,kedai kin shigo duniya a sa’a,Allah ya tsaremin ke,ya qara nesanta tsakaninmu da talauci”

“Ameen baabata” ta fada cikin farinciki.

Tuni kaltum ta qara sauri ta fice abinta,bata bari kunnuwanta sun jiye mata sauran maganganunsu ba,bare ranta ya ida baci,zuciyarta cike fal da mamaki.

Mamakin nata yana da nasaba da asiya,da jiya ta shiga bayan gidansu tana wanka,taji asiyan na shaidawa babanta suna da tafiya a gobe,daga makaranta kuma aka shirya tafiyar,zasu cikin gari kwana daya zasuyi,su ‘yan babban aji.

 

D/Z
25

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button