Sponsored Links
Captain Shayeedah Hausa NovelHausa Novels

Captain Shayeedah Hausa Novel

Sponsored Links

[10/03 12:55 pm] salmah💍💍: *_👮🏻‍♀CAPTAIN SHAYEEDA👮🏻‍♀_*-2
By
_MARYAM YARMAMA_
*DEDICATED TO*
SALMA ALI WADA
precious pretty slim

an shirya,kayan tafiya yaki,haka hau jirgin ruwa,hannatuce ta kalli captain shayeeda tana dariyar mugunta tace captain ancefa mutannen sun iya gudu kamar barewa,gaskiya komawa gida zanyi.

 

Daka mata tsawa shayeeda tayi tace ke!dole kokin ki kokinso muje mukamosu,lalle kin dauki aikin soja wasa,ko kin manta sai mushafe twenty four hours muna gudu,balle wasu kananin kwari

 

General ya kalli hannatu ya mata ido tayi shiru zasuyi maganinta,takamarta babanta senetor ne,intasan wani batasan waniba

 

 

::::;::;;;;;;;;;:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

*NIGERIA*
LANTANE CE tashigo kitchen,tana kwalawa saude kira saude saude

Saude ta juyo tace haba lantana irin kwala kirannan da kikemin sai kace hajiya?Allah yasa dai alkhairine

Lantana tace inafa kiran alkhairi anan,kinaganin wannan miskilar takusa ta dawo gida awannan satinma

Dafe kirji saude tayi tace badai shayeeda yar gwal ba munshiga uku

 

Lantana tace ko kuma ninashiga uku,ai gwandake girkine naki nikuma aikn gidane,ai saitafi tsautamin

Saude tace ai tafi ungulu rashin mutunci,tana burgenu yarinyar nan ba ruwanta gason simah wasa da jama,a da faran faran
Lantana tace bake kadaiba,wai najima simah saida dady ya kusan korarta akan yar gwal

Zaro ido saude tayi tace ai kam dady zasu iys kashe mutum in yaciwa yar gwal mutunci don haka tun wuri mukama kanmu kafin ayi waje damu,yarinyar da bata dariya saidai tawa iyayenta murmushi

Kyalkyalewa lantana tayi dariya tace ai naji ana cewa batta da ra,ayin soyayya,randa ta fada zata chanja

Saude tace Allah yashige mana gaba irinsune masu kuka akan so

 

*ENGLAND OCEAN*

tafiya suke acikin jirgin ruwa,shayeeda ta fita wajen jirgin da cameran hango nesa

Hannatuce ta biyo ta baya da nufin jefa shayeeda cikin ruwa

Wani irin juyi shayeeda tayi ta juyo wajen hannatu suka fara kallon kallo

Shayeeda ta nuna hannatu da bindiga tace au kina tunanun bansan abinda kuke shirrin yiminba

Ai ina sane daku,duk nasanku ,baku isa kuyimin abinda Allah baiyiminba,nayi gaba nabar yan baya ,

 

Surrender hannatu tayi tana kuka tace am sorry ma,wallahi general ne yace mukasheki a gudun tsira

 

Tafi shayeeda tayi tace good ashe kinsan halina tun ba,aje ko inaba kun fara tauna kanku,ni bazan kashekuba,bazan baku hakuri ku fasa kasheni ba,but a gudun tsira zakuyi mamaki,saikunyi kuka da idanunku,ni inada hangen nesa saikun nemi taimakona

Fakan idon shayeeda hannatu tayi ta galla mata harara

Murtuke fuska shayeeda tayi tace hmmmm hannatu budurwar general kiyimin duk abinda kikaga dama,na tabbata a gudun tsira zakisan general ba kaunarki yakeba,saboda jikinki yakesonki,

Yatsine fuska hannatu tayi tace ma general yana kaunata sosai har alkawarin aure yamin

Daka mata tsawa shayeeda tayi taceshut up ina magana kina magana

Tafiya hannatu tayi tana sorry ma

 

Sojoji mata da maza sunyi shirrin shiga ruwa,captain shayeeda ita zata wakil cesu

Jirginsu yana gap dana makiyansu,harbe harbe suka farayi wa juns

 

*to jama,a ku biyoni kuji maizai faru a gudun tsira,kodai anacin galaba akan shayeeda*
By
Maryam yarmama
[10/03 12:57 pm] salmah💍💍: *👮🏻‍♀CAPTAIN SHAYEEDA👮🏻‍♀*3-10
By
Maryam yarmama
Dedicated to
SALMA ALI WADA
PRETTY SLIMZY

 

CIKIN zafin nama shayeeda kekai harbin hartayi nassarar kashe wani acikinsu

Kayan shiga ruwa shayeeda sukasa,kowanne ya shife ruwa ,suna iyo
Shayeeda taji an janyota cikin ruwan,dada nitsewa tayi
General tayi arba dashi,kallon kallo suks fara,bawanda ya damu da daukewar numfashi,saboda a hancinsu suna sanye da oxygen

Kafa yawa shayeeda abaki,cikin jarumta shayeeda ta maidamai da mafi munnin martani,a baki tamai kafa,ta shako wuyarsa
General yaji azaba tayi yawa ido baro baro ya fara neman gafarar shayeeda

Kota kanshi shayeeda batabiba tayi waje tana harbi,har tsyi nasarar. Kashe mutane. Biyu

Barayin suka sauka daga jirgi ruwan suka nausa cikin duhun dajin mai. Dauke da dogayen bishiya mai kama da. Lema

Gudu. Shayeeda take,karo sukaci da wani barawon zata harbesa bullet dinta ya kare

Dariya barawon ya fashe dashi,ya nunatada bindiga

Surrender shayeeda tayi yayinda ta fakaici idonsa ta naushi. Idonsa, ta yi. Hanzarin kwace bindigar

Ta harbesa a kafa,

Sa masa ankwatayi. Ta nausa. Cikin daji,ihunsu. General da hannatu. Taji. Acikin. Dokar dajin

Buya tayi. Abayan. Bishiya,barayin. Tagani,sun zagaye su general,da hannatu ansa musu. Bindiga a kunne

Ogansune. Ya kalli. General yace. Akashe. Budurwarka. Kokuma akasheka

 

General. Yace. Ina akashe. Hannatun. Dan. Ubanta ba budurwata bace ni ba auranta zanyiba

Hannatu tana kukatace. Dama general dama ba sona. Kakeba,wayyo shayeeda kizo ki taimakeni

*masoya ayi hakuri da wannan,wlh ina karatune*

By
Maryam yarmama
[10/03 12:59 pm] salmah💍💍: *👮🏻‍♀CAPTAIN SHAYEEDA👮🏻‍♀*
11-20
By
Maryam yarmama
Dedicated to
SALMA ALI WADa
PRETTY SLIMZY

 

Shayeeda tasaita bindigarta ta harbi ogan,ya fadi take yamutu

Yaransa sukasa gudu,shayeeda ta bisu a guje,

Zagayeta sukayi su wajen ishirin,surrender shayeeda tayi ,ta aje bindigarta a kasa,tana kallonsu sunata nunata suna ta shekewa da dariya

Wani acikinsu yace wai mace ce zata kamamu wayyo dan mun fado

Ran shayeeda ya bace,sai fidda hucci take,basu ankaraba shayeeda ta dauki bindigarta ta kama daya daga cikinsu ta damkeshi kyam,ta nunasu tace duk wanda ya biyoni wlh saina kashesa

Bindiga suka dinga harbawa junansu,shayeeda ta samu nasarar kashe mutane goma

Ana cikin hakane, wani ya kusa ya harbi shayeeda aciki cikin zafin nama tayi saurin sunkuyawa bulley din yabi iska,
Itama ta maidamai martani

Shayeeda ta kashe su tsaf

Ta galabaita domin sunji mata rauni sosai,hannatu ce tazo wurin ta tallafa mata ta riketa tana mata sannu

Ritse ido shayeeda tayi tace hannatu ina general

Hannatu tace general sun tafi kwaso arzikin da barayin suka dauka a jirginsu

 

Shayeeda cikin sanyin murya tace good aikinku yana kyau

Hannatu tace gaskiya. Na jinjina miki ma kinyi matukar kokari

Shayida bata tanka mataba ta shige jirginsu,ihu sojoji suka fara suna daga shayeeda sama,matane suketa daga shayeeda sama suna hip hip hurray,we are the winner

Shayida ta basu umarnin su sauketa ta gaji zataje ta kwanta

Sauketa sukayi,yayinda sukaci gaba da rawa da kidin godiya ga Allah daya basu nasara

Shayeeda yashiga wani daki tana kewar gida,tana kewar mom and dad dole gobe su koma gida,tunda sunci nassara akan abinda ya kawosu

Kanol ne yashigo ya daga shayeeda sama ya bata kiss a kumatunta,yace congrat my love

Tsawa shayeeda ta dakamai ranta yayi mugun bacewa ta kanol kabir wannan wani irin iskancine,sai kace matarka zakazo ka dagani,kasani komin son da kakemon saidai ka hakura donni bazan auri mijin wataba

Jikin kanol yayi sanyi ya aje shayeeda yace kinsan yanda nake sonki kuwa shayeeda kimin uzuri in bakeba bazan iya rayuwa a duniyar nan ba,ki tallafamin

Shayeeda ranta ya kara bacewa ta nuna mai hanyar waje cikin gadara tace kanol ka fita kabar dakinnan ina bukatar hutu

A sanyaye kanol ya tashi yayi waje kamar yayi kuka,

Mutanen kasar england sunyi party bakadan ba,shugaban kasa ya bawa shayeeda kyautar estate guda uku,ya bawa general guda daya ,hannatu guda daya kanol guda biyu akasar england,sannan ya basu miliyoyin kudi,aka bawa shayeeda karin girma

Washe gari suka hau jirgi suka taho gida nigeria

A gidansu shayeeda masu aiki zuciyarsu sai harbawa yake,kowa ka gani jikinsa a mace yake
Momyce,take ta bawa masu dafa abinci umarni a kitchen suyi da kyau yar lele zata dawo

Fati ce tsaye a upstair tana kallon abinda yake wakana,duk tausayin masu aikin gidan ya kamata,hartaji kwalla na kokarin zubo mata ta share,dady ne ya shigo gidan yana ihu wai ina musa driver ne yaje ya dakko shalele bata juran tsayuwa

Tabe baki fati tayi,abin yana bata takaici,da yaya kamal yana nan shi yake saitawa shayeeda zama,amma yana kasar waje yana aiki

Momy ce tafito daga kitchen tace a a alhaji jirginsu ya isone? Dady yace tun yaushe to ai musa driver ya gudu garinsu
Dady yace what to mutafi muje mu dakko ta,yau ba wanda zai min excort cikin bodyguard,banson shalele ranta ya bace

 

Da sauri momy ta shirya ta riko hannun little hussy ta ce fati zomu tafi muje mu dakmo sister dinki,tabe baki fati tayi ta dakko mayafinta ta yafa ranta baki kirin

 

Dady sai sharara gudu yake akan titi,kamar zai tashi sama,suna zuwa jirginsu yana sauka
Sojojine suka fara fitowa kowa da kayansa soja a jikinsa

Shayeeda ce sanye da kakin soja,ga tasa hulan sojoji facing cap,tayi matukar kyau

Dady yana ganinta ya
Nufi wurin da gudu ya rungumeta,
Murmushi gwanda babu shayeeda tasaki,dayake bata dariya murmushinma da kyar takeyi tace daddy i miss you so much,shima yace me too my lovely daughter

Sakin dady shayeeda tayi ta nufi wajen momy da gudu ta rungume momy tace oh my beautiful mom how far,cikin farin ciki momy tace fine my sweet daughter ga kannenki su fati da little hussy

Sakin momy shayeeda tayi ta mikawa fati hannu suka gaisa kamar ba yan uwaba,fati ta kakalo murmushi tace sis you are highly welcome i congratulate you

Shayeeda cikin makoshinta tace thank you dear,ta kalli little hussy ta dauketa ta mata kiss a kumatu,dariya little hussy tayi cikin gwaurancinta tace yal lele tanda duwa
Make bakinta shayeeda tayi ta aje ta daka mata tsawa dont call me yar lele again call me aunty

Ihu little hussy ta farata buya a bayan momy tace mommy dodo bata dariya

Dariya mommy suka kyalkyale dashi,yayinda shayeeda ta daka mata duka tace nice dodonki

Kuka little hussy tasa yayinda fati ta dauksta ranta a bace tana lallashin little suka shiga mota sai hanyar gida

Horn suka dingayi,amma baba habu sao sharar barcinsa yake

Shayeeda abin ya bata haushi,bude motar tayi,ta bude katon kofar gidansu su dady suka rufa mata baya,tana zuwa ta saita fuskar baba habu ta shekamai mari,tace kai dan ubanka baccine ya kawoka
Fatima kukan zuci take tana Allah wadai da halin yar uwarta

Baba habu ya dinga bswa shayeeda hakuri,shayeeda ta kalli dady ranta abace tace dady wani irin arzikone baka taraba,ai wannan tsohon yayi girma a gadi;yakamata a samu samarai masu jini ajiki wanda sukayi diploma,kabawa habu miliyan daya yaje ya nemi jari yayi

By
Maryam yarmama
[10/03 12:59 pm] salmah💍💍: *👮🏻‍♀CAPTAIN SHAYEEDA👮🏻‍♀*
21-30
By
Maryam yarmama
Dedicated to
SALMA ALI WADA
PRETTY SLIMZY

 

Dady yace angama my daughter daga bisani ya kalli baba maigadi yace kazo anjima ka karbi miliyan daya ka koma kauyenku

Baba maigadi yace angode sosai alhaji Allah ya kara arziki

Dady yace ameen yayinda shayeeda tayi cikin gida,dady ne yazo ya danna mata intercom kofa ya bude tashiga katon falon

Murtuke fuska tahi ta nufi dakinta ta na shiga wani kamshin air fresher data tsana ya danno kai,yar kala ta saki ta fito falo da gudu ranta amatukar bace dady dasuke dinning suna jiranta

Yace lfy my daughter,dafe kirji momy tayi tace nashiga uku waya bata ran yar lele ne

Shayeeda tace wace yar iskace ta garamin daki,iyeh tasamin air fresher da bana so iyeh

Momy tace au yar lele shine ya bata miki rai saboda nasan bakyason masu aiki su gyara miki daki shine nasa kanwarki fati ta garamiki am so sorry baza,a karaba

 

Tsawa shayeeda ta dakawa momy tace ya isa,ta isa ga fati ta tsinketa da mari

Fati ta rike kunci ta kalli dady ko zai tsawatarwa shayeeda sai tagama dady ya daka mata tsawa yace ke faty ki bata hakuri meyasa zakisa mata room fresher da bataso banason a dinga bata ran yar lele in bahaka ran kowa zai bace

Kuka fati tasa tayi sama dagudu dady yabata shayeeda ya shagwabata bata ganin girman na gaba da ita wannan wacce irin rayuwace

 

Shayeeda tayi wanka tazo ta zauna a dinning momy ta bude fried rice dinda chicken wani kamshi ya maye wurin

Tsabar rainin hankali shayeeda ta toshe hanci tace mom waya dafa abincinnan?

Murmushi momy tayi tace saude ce da lantana suka dafa

What? Shayeeda ta furta da karfi ta yamutse fuska tace haba daddy dama har yanzu baku kori wayannan kazaman yan kauyennan ba ,ashe dama har yanzu baku daina cin abinci da diseases a cikiba,

Momy tace yar lele ko kin manta sunyu diploma a catering

Tsawa shayeeda ta dakawa momy,momy ta garkame bakinta tayi shiru,shayeeda ta tashi ta buga teburin cin abincin na glass ,duka abinda yake kai saida suka motsa har kula daya ya fadi tace dady!bazai yuba duk kudinka ace sai yan nigeria zakasa amasu dafa abinci indai bazaka dakko indi,ans ba to wlh bazan zauna a gidannanba,ku nemi wata yar badai niba

Dady ya shars gumunsa yace yar lele karki damu,komai kikace daidaine

Shayeeda ta zauna ta kwallawa saude kira saude!saude!

Da guje saude tazo jikinta na karkarwa ta durkusa har kasa tace you are welcome ma,

Shayeeda tace kafin kiyi welcoming dina kiyi welcoming din uwarki

Saude ta jinjiga kai tace thank you ma

Wani wawan mari shayida ta sakarwa saude dayasa tayi katantanwa ta zube awajen ba alamar numfashi

Momy rike baki tayi cikin tsoro ta fara saduda da lamarin shayeeda

Shayeeda ta dauki faro water ta sheka duka ajikin saude ajiyar zuciya saude tayi ta fashe da kuka ai girma zata girmi shayeeda ,shayeedar nawa take ai wlh karamar yarinyace yar 22 years amma take wulakanta manya

Shayeeda ta ku tattara kayanku dukanku za a sake zubi donbanason kazanta da sata don haka daddy ka salmesu gobe kayi waya akawo yan indi,a

 

Daddy yace yar lele indai haka zai faranta miki rai kamar anyi angama,kisha kuruminki

 

Tsaki shayeeda tayi ta kalli saude dake faman rusa uban kuka tace kije ki gayawa yan uwanki kazamai irinki,kice musu kowa tazo ta karbi kudin sallamarta

Saude tace dan Allah hajiya kiyihakuri da kudin aikinmu muke ciyar da iyayenmu don Allah karki koremu wallahi mahaifiyata bata gani makauniyace

Momy taji hawaye ya malalo mata tayi saurin gogewa tana dana sanin shagwaba shayeeda wai yau yar data haifa take tsoro .

Shayeeda ta tara yan aikin gidan harda masu bawa,fulawowi ruwa,tasa dady ya basu miliyan daddaya,tace gobe su tattara kayansu subar gidan.

Fati tunda akayi abinnnan tana ta dakinta tana ta kuka da dana sanin zaman gidan

 

Washegari aka zuba kyawawan indiyawa,masu jini ajiki,akwai masu dafa abinci,da masu gyaran gida,bawa fulawa ruwa,sai masu gadi samari matasa masuji da kansu

 

Momy ta tsotata da kallon da dady yakewa dayar yan indi,an mai suna najri yana lashe baki

Momy ta fusata ta ce ke tashi kibar nan,daddy yace a a ya zaki koreta bayan aiki aka kawota

Najri ta tashi tana wani tafiya mai dauke hankalin,nan daddy ya shagala da kallonta,ran momy ya bace tace oh ni yasu yar lele taja an kawo snatcher kwanannan kuwa za,amin kishiya, a zuciyarta ta fadi haka sannan daga bisan ta kalli dady tace haba alhaji wannan ba girmanka bane wannan fa yar cikinkace fa

Dady yace haba inkilme yakike zargina akan abin da bazan taba yiba

 

Momy ta mike tsaye tace tayaya bazan fadama gaskiyaba wallahi nayi dana sanin tarbiyar damuka dora shayeeda akai wallahi ba yanzu zamu ganeba sai, nan gaba

Shayeeda ce ta sanya kakin sojoji tana sanye da kakin sojoji tayi masifar kyau tace mom whats going on here am bathing i hear ur voice shouting and yelling to my dad

Momy ta amsa mata nothing my daugher i wanna said to urdad to change my car

 

Shayeeda tace to nizan fita aiki,sabida yau an kama wasu barayi zanje in musu hukunci

 

Dady ya saki murmushi yace my daughter yanzu bazakici komaiba?

 

Shagwane fuska shayeeda tayi tace no saina dawo,

 

Fita tayi suna mata adu,ar Allah ya bada sa,a,

Shayeeda taga motocin sojoji masu kareta bodyguard kkwaya biyar ,bude mata kofa sukayi ta shiga hadadden motarta,suna cikin tafiya duk inda sukabi sai anbasu hanya,kawai wani saurayi yana kan akwalar mashin ya gogi motar shayeeda,da gudu ya wullar da mashin din ya fanna a guje,itama shayeeda ta fusata ta fita a motar ta bishi aguje,

Gudu suketa fantamawa tayi nasarar kamasa ta wankesa da mari ta gwabji bakinsa tace harni zaka tserewa dakasan gudun da mukesha da bakiyi gigin guduwaba muke kai twenty four hour muna tafka gudu bamu gajiya sai kai karamin alhaki to mu tafi office zakayi bayani

Hakuri saurayin ya fara badawa amma shayeeda ta jefasa a mota

 

Mutanen da suke wajen suna mamaki ashe what man can do woman can do it even more better. It is true

 

 

Shayeeda ta shiga office dinsu dake abuja ta zauna akaton office dinta tana rubuce rubuce ta danna inta com tace hello ku shigomin da wannan dan iskan gagararren yaronnan abdallah

 

 

Ba,afi minti ukuba,aka shigo da wani hadadden guy,choculate colour ya hadu matuka gashi da idonsa sexy eye,kai masha Allah ya hadu ko ta ina,gashi dogo mai faffadan kirji ga bakinsa pink,yayi matukar haduwa

Yana zuwa yayi murmushi ya zauna a kujerar dake fuskanta shayeeda

Dago da dara daran idonta shayeeda tayi tace did i permit you to take asit who hell did you think you are

 

Cikin taushin muryarsa mai dadi ya bata amsa a gajarce yace am no body ,kuma ai bake zaki nunamin sit ba

Ran shayeeda ya bace bata taba musanyar yawu da waniba,kowa tsoranta yake amma wani dan talakawa yazo yana son ya raina mata hankali dole ta dau mataki akansa

 

Abdallah yace to malama in bazaki gayamin abin kirkiba zan koma sell dina,in kuma baki gaji da kallon kyakyawar fuskataba saiki gayamin

Shayeeda ta tunzura tana ta huci,abdallah ya tashi ya juya da niyyar fita,.muryar shayeeda ya tsinka tana cewa hey u stupid come back

 

Juyowar da zaiyi ta tashi ta nufo gabansa ta wanke fuskar sa da mari

Shima abdallah ya murde mata hannun data maresa shima ya wanketa da mari kwarara guda biyu,yar kara shayeeda tayi

Abdallah ya kyalleta yace ke harkin isa ki taba lafiyar fuskata ke wacece

 

Hawaye ya fara kwaranya a fuskar shayeeda tace kasan ni yar wace ka mareni?

 

Abdallah yace ni bansaniba kuma bana bukatar sani,ihu shayeeda tasa tana kiran sojoji sai gasu sun bayyana ta umarcesu tace kukama dan iskannan ku sashi a cell ku bashi azaba kumai hukunci mai tsauri kumai jini da majina

 

Kama abdallah sukayi suka rikesa,abdallah yace ashe ke ba jaruma bace meyasa bazakiyimun hukunci da kankiba saikinsa wasu,banza kazama kawai,kuchaka.

Shayeeda ta dakawa sojojin tsawa tace ku tafi dashi , nace

 

Shayeeda suna fita,ta cire hulanta ta wullar a kasa;ta barbaza gashinta ta dora kanta akan table din files din ta fashe da kuka tunda take a rayuwarta ba wanda yasa taba sata kuka,amma yau wani ya mareta ya sata kuka yaci mutuncinta,dady must here this,kuka ta fashe dashi

 

 

By
Maryam yarmama
[10/03 1:03 pm] salmah💍💍: *👮🏻‍♀CAPTAIN SHAYEEDA👮🏻‍♀*
31-40
By
Maryam yarmama
In dedication to
*SALMA ALI WADA*
&
*PRETTY SLIMZY*

*_WANNAN. SHAFIN NAKINE HAUWA ABUBAKAR (MAMEE)KE KAWACE TA GARI ,ALLAH YA BARKI DA MIJINKI ABIN SONKI ,YA KAWO YAYA MASU ALBARKA_*

 

 

Shamsu ne yace kunga mom irin abin da nake gayamuku ko gashi ai zata kashe dad Allah ma ya taimaka a kafa tamai,kun biyewa yarinyar kuka bata chance na zama soja ,kun sangartata kun biyewa ra,ayinta ,kunsa ta raina mutane

Dady da kafarsa ke azabar zugi da zubar jini yace,shamsudeen kiramin doctoci azo ayi treating dina a gida banason yan adawa suji labarin nan.

 

Lallata waya shamsudeen yayi ya kira doctocinsu na family,ba,afi mintinaba doctoci biyar suka zo suka shigar da dady,private room suka masa aiki,dady yasha wuya matuka,a duniya yaji ya tsani shayeeda bayason ganinta,surutai ya dinga ,likitocin sukamai aluran bacci,yasamu ya dan ritsa

Fitowa sukayi sukace,wa su momy anjima zasu dawo akaramai jini,zasuje su dakko kayan aikinsu.

Godiya su shamsi sukayi ,fatima na rike da little hussy cikin damuwa tace mudai anty ta jawo mana bala,i,ai nasan sai anyi haka tun icce yana danye ake tankwarawa,shiru momy tayi,yayinda shamsudeen ya umarci abokinsa ya zauna,fati taje ta kawo drinks

Shayeeda ce ta farfado ta dora hannu aka tana nashiga uku ni shayeeda ina zansa kaina na kashe dady

Harara momy ta dankara mata tace to ta Allah ba takiba ja,irar yarinya kawai,bake kince duk wanda yake gaya miki gaskiya shi kike kiba?

Shamsudeen yace rabu da ita sainaci ubanta da duka,ke captain ko to zaki dawo general ma da hujja,kuma aikin sojanma daya yau kin daina

Shayeeda tace yaya shamsi nikake fada?ni yar lele

Shamsudeen yace ko nima zaki kasheni ne,ai wanda ya shagwabaki yana kwance balle ya taka mana burki saimunci ubanki yau a giddannan dama haushinki nakeji

Fatima tace wlh saina ramawa momy abinda dady yamata ranar nan akanki

Shayeeda tace momy,kina kallo ana cimin fuska bazakiyi maganaba,momy anya ke kika haifeni kuwa?

Momy tace rufemin baki,kamar yanda kika fada yanzu tabbas bani na haifekiba,mahaifiyarki tun kina sakkowa duniya ta mutu,dady ne yafara rainanki watanki uku iyayensa suka auramaini ni yar cameroon ce

 

Dafe kirji shayeeda tayi tana jinjina kai,gaskiya tayi wauta ,ashe ita marainiyace,ashe batta da uwa a duniya,dady ya fifitata tasa yake tsawatarwa uwar goyanta,fashewa da kuka shayeeda tayi,tace nashiga uku ashe ni marainiyace,wayyo ya zanyi da rayuwata

 

Shamsudeen yace sai kiyi hakuri domin mu biyu muka rasa uwarmu,nayi nesa dakene sabida,banson inkara sangartaki ina tausayin maraicinki,saigashi Allah ya bamu momy ta rainemu uwa yayan cikinta

 

Jikin shayeeda yayi sanyi,ji tayi dady yanata kwallah kira shamsy!shamsudeen ina kake?

 

Da gudu shayeeda ta nufi hanyar dakin dady tana kuka,shigarta keda wuya ta fada bisa gwiwowinta,tace dady dady ashe ni marainiyace

Zuciyar dady ya karaya amma bai nunawa shayeeda komaiba ya daka mata tsawa tashi kibar nan ,daga yau ki cireni a rayuwarki karki kara cewa ni na haifeki zan bada sadakanki ga duk wanda naga dama,ki cireni a zuciyarki shayeeda nayi nadamar saninki arayuwata

 

Kuka shayeeda ta fashe dashi tace no no dady pls dont do that tome,dady pls karka auramin talaka,na tsani zaman talauci

 

Ran shamsudeen ya bace,au har yanzu baki sadudaba kenan,baki chanja halinki ba kenan lalle yarinyar nan

Murmushi mai ciwo dad yayi yace, hmmmm rabu da ita duk mai shayeeda tamin ba laifinta bane laifinane,amma yanzu komai ya zo karshe donyau zan daura mata aure ga wani mutum mai bala,in kaunarta,tunta karama namai alkawarin auranta

 

Shayeeda tace dady banason kowa banaso dady zanmutu ka taimaka

 

Likitocine suka shigo,suka gwada dady,aka gwada jininsu kamal dasu momy amma jininsu baizo daidaiba,na shayeedane yazo daidai

 

Dady ya tubure yace saidai ya mutu baza,a karamai jinin makiyarsa ba,shayeeda tanajin kalaman dady ta rusa ihu tace wayyo 🙉🙉Allah na dady ma ya tsaneni yanzu nashiga uku

 

Dady yace tashi ki fice kallonki ma innnayikara haddasamin ciwon kuma ki aje aranki nanda sati daya zan aura miki,wanda nayi niyya

Ihu shayeeda ta kara sawa tana dady banason talaka amsorry karkamin haka

Dady ya daka mata tsawa yace tashi ki ficemin ai bakin alkalami yabushe

*to masoya ayi hakuri acigaba da bibiyarmu aga,wani hali shayeeda xata shiga,tana cinye jarabawar da alhaji zai dorata akai ,ku biyoni kuji*

 

By
Maryam yarmama
[10/03 1:03 pm] salmah💍💍: *👮🏻‍♀CAPTAIN SHAYEEDA👮🏻‍♀*
51-60
By
Maryam yarmama
*DEDICATED TO*
SALMA ALI WADA

*PLS MASOYA AYI HAKURI ,NAYI MISSING DIN PAGE NA MAIMAITA 30-40 SAI BIYU,PLS DUK MAI CAPTAIN SHAYEEDA DAGA FARKO YA TUROMIN*

Kuka mai tsuma zuciya shayeeda take ,tana waiwayen dady ta fita da gudu daga dakin,ta hau upstair ta haye saman gado tana ta sheka kuka,tana tunawa yanda ta wulakanta mutane da dama taci mutuncin tsofaffi ,

 

Kuka ta rushe dashi,tace nashiga uku ya zanyi aiko bakin abdallah saiya kamani,yanda na sa akamai jini da majina,na zagesa nasa aka tsaresa;har naje kasar waje nayi watanni uku a kulle,oh Allah ya zanyi da rayuwata,ina zanga abdallah in nemi yafiyarsa.

 

 

*WAIWAYE ADON TAFIYA*

*CAPTAIN SHAYEEDA YACE GA ALHAJI RIDWAN .A. ABBAS WANDA YA KASANCE,DAN MAIDUGIRI SHUWA ARAB ,YA AURO MAHAIFIYARTA A ADAMMAWA,FULANI USIL KYAKYAWA,TUN YANA KARAMI YAKE DA BURIN ZAMA DAN SIYASA,SU UKU IYAYENSU SUKA HAIFA DAGA YAYARSA SAKINATU DAKE AURE A NIGER,SAI SHI,RIDWAN,SAI AUTANSU BALA,IYAYENSU SUN MUTU,SUN TASO CIKIN SODA KAUNA,SUNYU KARATU,SAKINATUCE TA DAU NAUYUN KARATUNSU INDA YA KARANCY POLITIES,AHAKA YA AURI MAHAIFIYAR CAPTAIN SHAYEEDA ,AMINA YAR FULANI WANDA TA KASANCE YAR MALLAM MAI TALLAN NONO,SUNJE WANI CAMPAIN NE YAGANTA TA KWANTAMAI ARAI,HAR YA TURO MAGABATA AKAYI AURE,AMINA TANA DA KUNYA DA SON JAMA,A FARKON HAIFUWARTA TA HAIFI KAMALUDEEN,SAI DATA SHAFE SHEKARA BIYAR SANNAN TA KARA SAMUN CIKIN SHAYEEDA,NAN NE ALHAJI RIDWAN YACI SENETOR YA TARE A ABUJA, NAN NAKUDA YAKAMA AMINA,SHAYEEDA TANA ZUWA DUNIYA ALLAH YAWA AMINA RASUWA,ALHAJI YAYI KUKA HARYA GAJI,YAN UWAN AMINA SUKAYI DASHI YABASU YAR YAKI ,HAKA SUKS HAKURA TANAR SUNA YA XAGAYO AKA SAWA YAR SUNA SHAYEEDA AKE KIRANTA DA YAR LELEN BABA,ALHAJI KO INA ZAIJE SHAYEEDA TANA HANNUNSA,SHAYEEDA TANA DA WATA TAKWAS ADUNIYA YA AURI MOMI SALMAH YAR CAMEROON,ITA TA RAINI SHAYEEDA, SHAYEEDA TANA DA SHEKARA BIYU ,MOMI TA HAIFI FATIMA KAMILLAR YARINYA,AKASASU AMAKARANTA,TUN SHAYEDA NA KARAMA TAKE DA RAINI DA GADARA DA KUDIN BABANTA,HATTA MALAMINSU TA MARA,DUK WANDA YACE YANASONTA SAITA GAYAWA. DADY TASAANWA MUTUM RAGA RAGA,ATARE AKA SHIRYA MUSU TAFIYA KASAR WAJE KARATU SUDA FATIMA,FATIMA TAKITACE ITA YAR MASS COMM TAKESON ZAMA,HAKASHAYEEDA TAJE TA KARANCI. SOLDIER. TAYI NDE DINTA,TANA. DA SHEKARA ISHIRUN DAYA BIYU AKA BATA CAPTAIN,YAN BAYANTA SUNSHA WUYA DA TRYING,BATA WASA DA AIKINTA,GA NUNA MULKI DA IKKO,DADY. YA GOYA MATA BAYA HAR DUKAN MOMY YAYI AKANTA,MOMY TA TAFI CAMEROON,KAMALUDEEN SHIMA YA KARANCI ENGINEERING;SANNAN YA KOMA LONDON KARO. FINAL SEMESTER DINSU,SHAYEEDA SUN HADU DA ABDULLAH NE. A WAJEN CIN ABINCI,DAMA IN SHAYEEDA. ZATACI ABINCI BATASON TAGA KOWA AWAJEN,ABDULLAH YANA. ZUWA;YA ZAUNA KUSA DA ITA YACE SANNUNKI YAN MATA,SHAYEEDA TA KALLI BODYGUARD DINTA TACE ME KUKE JIRA DA FITSARAR RANNAN KU KAMASA KU SASA AMOTA KU,SASA A CELL,*
ABDULLAH YA CIKA DA MAMAKI HAKA YA BADA HANNUNSA,SUKA SAMAI ANKWA YANA DAUKAR. ALWASHIN DAUKAR FANSA,DOLE YA AURI SHAYEEDA YA KAITA NIGER GIDANSA YA BAUTAR DA ITA,YASA TA ZAMA ABAR TAUSAYI ABIN KWATANCE GA WASU,HAR SHAYEEDA TAJE LONDON TA DAWO ABDULLAH WATAN SHI BIYU A TSARE A CELL,SHINE HAR SUKAYI. SA,INSA DASHI,
WANNAN SHINE TAKAITACCEN LABARIN SHAYEEDA WANDA MUTANE DA DAMA SUKESON DAUKAR FANSA AKANTA

 

_kwana biyu zazzabi mai zafi ya rufe shayeeda ko iya fita batayi,abin yan aikine suke kawo mata,kowa nagidan yayi banza da ita,dady ma baya zancenta shidai yananan yana samun lafiyar kafarsa,fatima ce tashigo dakin,tace aini shayeeda yanzu kikafara gani,inkin gama shirmen karyar rashin lafiyarki saikije ku zanta da mijin da zaki aura,_

_zaro ido shayeeda tayi tace what dama dady ba wasa yakeba da gaske aure zaimin. Pls yar uwata ki taimakeni kar ayi. Aurennan_

_dariya fatima tayi tace au yau nazama yar uwarki,ahayye sabon salo,kishirya nanda kwana biyu dady a badake ga wanda yaso,ki shirya wannan bikin kar yayan manya irinki kuma kawayenki su rainaki kima godewa Allah mijinki yana da kyau,yana da kudi,shi yazo ya tambayi aurenki harda kwallansa,_

Shayeeda tace it cant happen,ni shayeeda za,a wa auran dole,da gudu,shayeeda ta fita daga dakin ta sauka daga hostel ta nufi kitchen ta dauki sabon wuka, haduwa sukayi da momy ,momy ta dafe kirji shayeeda mai zakiyi da wuka

Shayeeda tans muzurai tace momy inbaki matsakin ban hanyaba saina kasheki,karki yarda darajarki ta zube a idona

 

Fatima dake sama tace mom ki matsa zata aikata,da hanzari momy ta matsa,shayeeda daga short nikker sai vest din sojoji a jikinta,duk da ba kwalya tayiba amma tayi kyau,gata da diri,shayeeda ta shiga falon bakin kamashin turaren sane ya doki hancinta,shayeeda ta toshe hanci wai wari😂(anata fassarar but anawa fassarar kamshi naji mai dady kamar in suri mutumin)

Mutumin danima bansansaba,ya juyawa shayeeda baya,shayeeda dake rike da wuka tace kai foolish wawa dolo,juyo ka kalleni,nan munafiki,wlh yau sai nazamo ajalinka

 

Murmushi dauke akan fuskarsa ya juyo da muryarsa mai taush yace to general shayeeda zaki iya kasheni yanzu,

A tsorace shayeeda ta ja baya,tun datake bata tabajin tsoran wani ba sai yau,a hankali tace abdullah fuskarta dauke da mamaki

 

Abdallah yace sunane ko kina tantama bani bane,to nine,dukan da kikasa akamin baiyi sillar mutuwataba ina nan araye nazo in aureki ne in rama abinda kikamin nikkin baninkin in miki tabin da bazaki manta daniba,in maidaki. Abin kwatance,in nakasaki,insa ki zama abin gudu ga kowa,in zama dakekaramar bazawara,ni abdallah na wuce haka yarinya kin kawo ruwan dafa kanki,ni abdallah zuciyata uwa garwashi take,ni damisane,ni jan gwarzone,wanda na yi farautar zaki,na kwana a dajin falgori,ni ne maganin irinku,kisani zan aurekine bawai don ina sonkiba,a a zan aurekine domin in muzguna miki,

 

Shayeeda ta kwallah kara ta zube awajen sumammiyya

Lalle kam akwai ryuwar danasani game da shayeeda,kucigaba da bibiyata

 

By
Maryam yarmama
[10/03 1:03 pm] salmah💍💍: *👮🏻‍♀CAPTAIN SHAYEEDA👮🏻‍♀*
61-70
By
_maryam yarmama_
_dedicated to_
_my salmati_

 

_wannan shafin nakune masoya,masu kirana awaya,masuyimin text masuyin chatting dani suna min fatan alkhairi ina godiya,na chanja number yanzu kuyi hakuri masoyana,_

 

_*sakon ban hakuri,pls masoya kuyi hakuri innaga littafin shayeeda zan cigaba da littafin *mahaukaci ko boyayyen masoyi*nasan mutane da dama bazakuji dadiba,kuyi hakuri,wlh innayi typing mai yawa sai yayi clearing ina mai kara baku hakuri_

♥dan Allah duk mai captain shayeeda da farko ya turomin dan Allah

 

Dady ne suka shigo da momy ta rikesa, dady yace aini nazata yar iskar yarinyar nan ta kashemin kai?

Abdallah kunya ya kamasa yace no dad tana ganina ma tasuma na rasa menene dalili?

Dady ya kalli fatima yace fatyna jeki wajen liman,kice ina gayyatarsa shida jama,arsa auran sirri dazanwa yata shayeeda yanzu,banson ta farka nafiso a daura aurennan;saboda in shayeeda ta farka zata iya kashe kowa za,a samu matsala,kaikuma abdallah inaso ka horata kacire mata mummunar akidar da take dashi,inaso shayeeda ta zama saliha;in cika burin margayiya amina

Fatima ta tafi gayawa liman,yayinda abdallah yace insha Allah zakuzo kuyi mamakin shayeeda,sai tazama abin kwatance ga kowa,

Dady yafashe da kuka yana thank you my son,nasan zaka iya kai jarumine,inason ko daya karka nunamata dukiya,inaso kuyi rayuwar kunci da ita,inason kuyi rayuwar talauci tasan menene duniya,inkamin haka kagamamin komai,tayi wanki da kanta dafa abinci da kanta komai da kanta.

 

Abdallah yace in Allah yayarda dady zaka sameni da bin umarninka

 

*BAYAN WASU MINTUNAI*

mutane talatin sun shaida auran shayeeda ridwan abbas da abdallah alhussain bash akan sadaki dubu talatin,inda shamsy (kamal) yazama waliyyin shayeeda,dady kuma waliyun abdallah,aka rabawa kowa dake wajen dubu ishirin

Yar india najri tafi kowa farin ciki,zata samu damar dady,in shayeeda ta tafi,zata juya gidan yanda taso,ta kwashi dukiyoyi alhaji ya zama nata ita kadai

Faty ta harhada kayan shayeeda wajen akwati goma,dady yace arage akwati abar mata uku;haka akasa abayan motar da dady ya bawa abdallah sabuwa dal,

Abdallah dakyar ya ansa,dady ya kara bashi a t.m din shayeeda dake dauke da miliyoyin kudi,da takardun ta na estate din da yake kasar england yace ya rike kar ya taba bata,sau ranar da tayi hankali zatama mutuniyar kwarai

Abdallah ya jinjina kai,dady yace to abdallah maikuke jira ka dauki abarka ka sata amotan kar shagwababbiyarka ta tashi aiki ya koma baya🙈🙈

 

Abdallah kunya ya kamasa amma ba dama ya musa dady,yashiga dakin da shayeeda take akwance,gashinta yayi buzu buzu ys rufe mata fuska;abdallah ya gyara mata ya tsaya ya kura mata idonsa

 

Ji yayi andafosa,firgigit ya tashi daga tsugunon da yayi,a hankali idonsa ya sauka akan shamsy dake ta faman tsiyayar da hawaye ,shamsy yace dan uwa na pls ka kullarmin da kanwata kaga sabuwar rayuwa zata shiga kuma marainiyace,ita kadai ce kanwata wanda uwa daya ta tsunguna ta haifemu,zan gayama maka abinda zakayi shayeeda ta soka,na daya shayeeda tanason mai kishin kasarmu nigeria,na biyu tanason dolly ,na uku tanason chocolate,na hudu tanason maison film din fada mai yabon sojoji,na biyar tanason maisona da dady,wannan zaka iya siye zuciyarta kuma yar lele batason amata tsawa,kuma tanada nemonia,intayi wanka da ruwan sanyi wuni take tana rashin lfy ,nagode Allah ya kiyaye hanya

Abdallah yayi murmushi ya dauki shayeeda cak yace amin y fita da ita yasata amota,yasata abayan mota, shi ya zauna a gaba,momu da dady suna dogo musu hannu har motarsu ta daga zuwa niger,faty ta dinga kuka koba komai tayi missing din fadarsu da shayeeda.

 

Haka abdallah ya dinga tafiya har dare ya gifta,suna shiga saharah,hadari ya hadu yayi baki kirrin,adaidai lokacin shayeeda ta farka kuka tasa tace karde mafarkina ya zama gaskiya,abdallah ina zaka kaini ka kaini wurin dadyna

Ran abdallah ya bace ya tsayar da motar ya fito,ya zaga gidan baya,ya bude ya finciko shayeeda har singlet din dake sanye a jikinta yadan yage,ya wurgota waje,

Tsoro ya kama shayeeda,dataga a wani kasa suke,ga iska da sanyi da kukan tsuntsaye,ga kasa mai dauke da iska sai barbade mata jiki yake,ga hadari yayi bakikirin,kuka shayeeda tasa tsabar girman kai taki tabawa abdallah hakuri,.

Tace nashiga uku ruwa yau zaimin duka,wayyo ciwona,kafin ta karasa an tsuge da ruwa tamkar bakin kwarya

Allah sarki shayeeda

By
Maryam yarmama
[10/03 1:03 pm] salmah💍💍: *👮🏻‍♀CAPTAIN SHAYEEDA👮🏻‍♀*
71-80
By
Maryam yarmama
Dedicated to my salmaty

 

Tausayinta ya kama abdallah,ga ruwan harda kankara yake zuwa,tuni ya suri shayeeda da take rawar sanyi yasata amota,nan zazzabi. Mai zafi ya rufeta

Tafiya abdallah yake amma hankalinsa yana kan shayeeda da tafita a hayyacinta nemonia dinta ys tashi,haka yaji kamar ya mata kuka,

Haka ya iso wani katon tafkeken gate ,gate din ya bude da kansa,

Abdallah ya faka motoci a gefen wasu hadaddun motoci,

Sakin baki shayeeda tayi da taga kogidansu baikai kwatan kyan gidansu abdallah ba,wai shin wanene abdallah iyeh?

Abdallah ne ya fito daga motar yace malama inzaki fito kifito nagaji da daukar katuwar captain

 

 

Shayeeda a hankali ta fito muryarta a dashe tace pls abd allah ka kaini asibiti,

Abdallah ya daka mata tsawa ke waye sa;anki dallah ki wuce mushiga ciki kibani hakkina,

 

Shayeeda ta rushe da kuka tace dan Allah abdallah kayi hakuri wlh banda lfy

Tabe fuska abdallah yayi yace mema zanyida abinki ,nasan maza nawa kika basu iyeh don irinku masu rawar kai akwai son maza

 

Tsugunawa shayeeda tayi ta rushe da kuka tana abdallah karka kasheni,da wannan kalamanka,wallahi bantaba sanin wani namijiba a rayuwata,

 

Abdallah ya dakamata tsawa harta firgita yace tashi cry cry mushiga ciki

Danna intercom yayi suka shiga cikin gidan,wani hadadden falo ya bayyana;har shayeeda zata zauna akan kujera,abdallah yace matsamin chan da kazamin jikinki zaki zauna akan kujera,zaman kasa yafiye miki
Jiki a sanyaye shayeeda ta zauna a kasa,shayeeda wanda nasanta da gadara da rashin kunya,tsiwa,da girman kai ta zama so silent,tana mugun tsoron abdallah yanzu(kaji mazan kwarai).

 

Abdallah ya buga waya yace kuka ka dafa tuwo da miyar kuka ka kawomin yanzu yanzu

 

Shayeeda a ranta tayi dariya tace lalle wannan dan kauyene,tuwo kuma tab

 

Abdallah sai waya yake ,shayeeda sai satan kallonsa take,suna hada ido abdallah ya daka mata harara yayi tsaki

Ba, jimaba sai ga kuku ya shigo da flas biyu,dawani dogon hula,yace yallabai angama,

Abdallah ya kashe wayar yace ka bawa wancan almajirar gata a zaune.

Kukun ya nufi waje yana ai yallabai wannan batayi kama da almajiraba,ya ajiye abincin ys fitaa guje

Shayeeda hawaye yana zuba a idonta tace abdallah ban iyaciba, abdallah kasa a dafamin indomie

Abdallah ya daka mata tsawa yace,ai yau dole kici tuwannan,kokuma inzo inmiki dura,
Kuka shayeeda tasa,ta bude kwanon tuwon dawane da miyar kuka.

 

 

Shayeeda taji amai ya taso mata,ta dinga shekawa,saukar belt taji a kyakyawan jikinta,abdallah ne tsaye a kanta,cikinbaccin rai yace wallahi indai baki ci tuwannan ba sai namiki jini da majina idiot

 

Kuka shayeeda ta karasawa tace kayi hakuri bazan iyaba

By
Maryam yarmama
[10/03 1:03 pm] salmah💍💍: *👮🏻‍♀CAPTAIN SHAYEEDA👮🏻‍♀*
81-90
By
Maryam yarmama
*in dedication to my salmaty*

 

*masoya littafin mahaukacin masoyi kuyi hakuri,ina tare daku karku damu zancigaba,so nake inyi muku typing mai yawa sai inyi posting*

 

 

Kuka shayeeda take ta cusa hannunta a tuwon dawar ta sanya abakinta,amaine ya taso mata ta dinga shekawa a cinyar abdallah,saida tayi mai isarta,ta tsorata ainun dataga a cinyar abdallah tayi aman,fuskar abdallah taga ya murtuke fuska,

 

Tashi abdallah yayi ya daddage iya karfinta ya zura mata belt din ,ihu tasaki tana dan Allah abdallah kayi hakuri

Abdallah yace yimin shiru banza kazamiya ai saiki taso kije kimin wanka,kuma in kinsan kinada gaskiya yau zan karbi hakkina

 

Zaro ido shayeeda tayi,ta tashi hajijiya ya kwasheta, fadawa luuuuuuu sai jikin abdallah ,abdallah yaji wani shock ajikinsa ,daya fuskanta komai zai iya faruwa a wajen ya hankadata gefe,ta gwara kai da *shower glass* jinine ya taru fara malala a goshin shayeeda,kara ta kwallah ta zube a wajen sumammiya

 

Tarota abdallah yayi,ya dauketa cak yasata a kafada,toilet ya kaita,ya dafa ruwan zafi,ya dakko first aid box,ya mata wanka ya gasa mata jikinta yasa mata bandage,nannade ta yayi,da towel ya ,kaita gado ya kwantar da ita,yana tausayama mata

 

Fita yayi yaje ya dakko,akwatunan shayeeda,ya zakulo mata singlet maikyau yasaka mata,ya mata alluran bacci,

 

Abdallah yace oh shayeeda kwana daya na fara saita mata hankali,harta dan rame tadan f’ada ciki

 

Washe gari ,shayeeda ta tashi yunwa takeji matuka,toilet dinta tashiga tayi wanka,tasa jallabiya fari kal na mata;tazo yin kwalya ta duba goshinta ya sha bandage,kuka ta sanya,tana wallahi abdallah mugune na asali Allah ya isa,ta sheka kwalya tayi kyau,amma hawaye sai gangara yake a idanunta

 

Abdallah dake tsaye yace baby kin gama zagina

Cikin shayeeda ya duru ruwa amma ta dake tace ehdin an zagadin an cema azzalumi

 

Abdallah,ya nufo wajen ya daddage iya karfinsa ya make bakin yace ni ba,amin tsiwa yarinya

 

Fashewa da kuka shayeeda tayi,ta tashi da niyyar fita waje cikinta ya fara kukan yunwa,cize lebe tayi,abdallah ya lura da ita ya dinga mata dariyar keta yana *wakar kushi khushi hota hai*

 

Harara ta dankaramai,suna hada ido ta wayance,

Fita falo tayi,ta nemi dinning ta rasa,ta rasa yanda zatayi ta tunkari abdalllah

 

Abdalllah ya nufo wajen yace yar kauye kingama dube dubenki

Ran shayeeda ya bace tace a a

Abdallah yace au bakinki bai mutuba ko,kamo hannunta yayi ya murda,kara tasaki tana wayyo dadyna

Kwas kwas din takalmi taji,wata hadaddiyar budurwa ce tashigo tasha kwalya kananun kaya,ta sanya glass farace kal,ta daura attachment,ta dan yafa sirrin gyalle,doguwar rigane a jikinta

Abdallah yana ganinta yace sumy mai kikazoyi a gidannan?

 

Sumy ta nufo abdallah da nufin rungumesa,abdallah ya kauce yayinda ya juya ya rungume shayeeda yana mata hot kiss,shayeeda itama saita biyemai don ta gusawa sumy haushi harda darling pls wacece wannan

Abdallah yayi murmushi yace budurwatace ada tare mukayi karatu awaje

Shayeeda ta tafa hannu tace good !

Sumy ta tunzura ta nufi,shayeeda ta rike kwalar rigarta ta daga hannu da niyyar marin shayeeda,taji an rike hannunta,abdallah ne ya kalleta yace ke?karki saki ki dukamin sweet heart dina ,karkimin asarar kyakyar fuskar my beloved wife

Sumy ta yarfar da hannunsa tace ai dama dole abdallah ka fadi haka,kaci moriyar ganga ka jefar,sannan ta kalli shayeeda tace kekuma kisani ni abdallah ya fara sani a diya mace,abdallah tantirin dan iskane

 

Shayeeda ta kalleta ta murmushin kishi da yake tace nasani kuma haka Allah yaso,kuma haka nakeson kayana,aike kika bashi kanki ya lalata dake,don blame him blame urself

 

Ran abdallah ya bace ya shako sumy yayi ball da ita yace ni zakiwa kazafi,ni zakiwa sharri,ko hannunki na taba rikewa.

Sumy dake kukan munafurci da kissa tace kadaina dukana karka zubar da cikin babyn mu

 

Kara shayeeda tasaki ciki! Hasbinallahu,ta fadi kasa tana abdallah ka cuceni ka maidani wajen dadina bana sonka bana kaunarka

 

Hawayene ya zubowa abdallah yace shayeeda ki yarda dani wlh karya takemin,kinji na rantse miki da Allah ni badan iskabane,bantaba sanin wata ya mace arayuwataba

 

Shayeeda ta ruga aguje zuwa dakinta ta kulle tana kuka,meyasa saida ta kamu da son abdallah sannan zai cusa mata bakinciki

 

By
Maryam yarmama
[10/03 1:03 pm] salmah💍💍: *👮🏻‍♀CAPTAIN SHAYEEDA👮🏻‍♀*
91-100

By
Maryam yarmama
In dedicated to
My besty
*SALMATI ALI WADAH*
_Thank you for ur love and support_

 

_thus page is dedicated to *sa,id bebeji(baban islam😝)*thank you for caring about my sweet brother,i love who care of my beloved brother_

 

 

Sumy ta dakamai harara tace aini abdallah kadan ka gani ,tunda kaki aurena,saina kori matarka ni inzo in zama matarka

 

Abdallah yace in Allah ya yarda ba abinda zai faru dani da masoyiyata,sumy kije nabarki da Allah ,insha Allah zakiga sakayya

Sumy ta kyalkyale da dariya tace hmmm abdallah ni dama ka taimaka ka kwanta dani,ko na danji dadi,kabani gudunmuwa ka kwana dani pls wallahi na kasa jurewa

Abdallah yace a,uzibillahi saidai in gayawata zaki dauka kije ki aikata abin da kikeso,amma kisani kuma ke shedace ba abinda abdallah ya tsana a duniya kamar zinah,Allah ya kareni daga aikata zina,kisani sharrin dayake cikin zinah inkikaji saikinyi dana sani,misali a yanzu ace,kina cikin aikata sabon Allah kika mutu baki tubaba,tun a duniya zaki fara gani,ga azabar kabari,ga tambayoyi daga mala,iku, ga haduwa da Allah ,ranar hissabi,ga azabar wuta wanda aka busamai azaba iri iri,inkin tuna lokacin da kike shayi a hostel dinki da kika kone da wuta yakikaji,balle wutar jahannama

 

Jikin sumy yayi sanyi tafara tsiyayar da hawaye,gashin idon dake manne akan idonta ta cire,ta cire ribon din attachment din tayi tana kuka da istigifari ,tace abdallah nagode da tunatar sani da kayi,kayi hskuri ka yafemin,ka kiramin matarka in nemi yafiyarta,

Abdallah yace ai matata bata rike mutum azuciya,nidai na yafe miki ,kije Allah yabaki mijin aure nagari,donni mijin mace gudane

Sumy ta fashe da kuka,ta tashi da niyyar tafiya ji tayi ankira sunanta a hankali sumy…..

Shayeedace tsaye tana mata murmurshi cikin murya ta kammala tace zo sumy zo

 

A hankali sumy tazo wajen,shayeeda ta kalli abdallah tana zubar da hawaye sannan ta kallin sumy tace sumy dagaske kinason abdallah na?

Sumy ta daburbuce,shayeeda tayi murmushi tace pls sister feel free to tell me,lokacin da kukayi karatu a turai kunyi soyayya?

Sumy tace tabbas,munyi soyayya da abdallah kamar zamu hadiye juna!

Shayeeda ta kalli abdallah ta tsuguna a gabansa;tace abdallah inkanawa Allah da annabi ka auri sumy ni na yarda,zan zauna da ita

Abdallah yace karki damu shayeeda zan yi abinda kikeso,murmushi shayeeda tayi ta fada jikinsa tana hawayen farinciki

Sumy ma farin ciki take,yayinda tace musu sai anjima,shayeeda tace a a tun yanzu?

Sumy tace zance gidan granny ne?

Bankwana sukayi,yayinda abdallah ya matse,shayeeda kam a kirjinsa ,shayeeda kirjinta ya fara dukar uku uku,faduwar gabanta ya tsawaita,amma takasa karban kanta,

Idon abdallah ya canja launi cikin murya kasa kasa yace my captain ki shirya tabar mijinki yau kafin wata tashigo,

Shayeeda tayi murmushi takara shigewa jikinsa tana angama yallabai

Wayar abdallah ne yafara kara,numban sumy yagani baro baro,

Dagawa yayi muryar yayan sumy yaji,yana kaine abdallah?

Abdallah yace eh nine lfy

Yayan sumy yace dama sumy ce tayi hatsari tana son magana dakai,gata kwance rai a hannun Allah

Salati abdallah yayi,
Aka kafawa sumy wayar a kunnenta,magana dakyar take tana abdalllah nagode da kasa na gane hanyar gaskiya,ka rike shayeeda amana,inama bankwana Abdallah nidai yau zan tafi,ka bawa shayeeda wayar

Shayeeda dake zunar da hawaye tace s….umy….. da yardar Allah baxaki tafiba muna tare dake

Sumy ta kayya bakiji yanda nakeji a jikinabane shayeeda,nidai ki rike abdallah domin mutum ne nagari nidai nawa yacika yau,kunsani a hanya madaidaiciya Allah yasadamu da alkhairinsa

 

Kuka shayeeda tasa ta na no bazaki mutuba;shiru taji shayeeda tana sumy sumy,kukan mutane taji a wayar

Kara shayeeda tasa tana ihun sumy sumy karki tafi mun riga munsaba,kin shiga raina sumy!na shiga uku sumy sumy

 

Abdallah ma hawaye ya fara kwaranya a idonsa oh duniya yanzu zaku gama hira da mutum yanzu zai mutu,ringing din waya yaji,yaya shamsy ne arubuce baro baro,shamsy ne yace yaya abdallah kunufo abuja yanzu ba lfyba,karka gayawa shayeeda kuzo kawai pls ko jirgi ku biyo kuzo abuja yanzu yanzunnan

 

Abdallah ya kashe wayar ya kalli shayeeda da take kuka tanamai kallon tuhuma

Abdallah yace shayeeda ki hada kayanki a karamin akwati,mu nufi abuja yanzu yanzu

Gaban shayeeda ya fadi tace ,me kuma yafaru a abujah,jikina yana bani wani abu yafaru

Abdallah yace cool down gobene auran faty fa

Shayeeda tace karyane wallahi bakason ku gayamin gaskiya wai meke shirrin faruwa damune,wayyo nidai dadyna da momyna

 

 

By
Maryam yarmama
[10/03 1:03 pm] salmah💍💍: *👮🏻‍♀CAPTAIN SHAYEEDA👮🏻‍♀*
101-110
By
Maryam yarmama
*dedicated to my salmaty*

 

*wannan shafin nakune masoyana,gaskiya nagode da karamin karfin gwiwa*

 

_WANE NE ABDALLAH_

 

Abdallah dane ga ambassador na niger alhussain,b,bash, dan sudanne ,ya auri yayarsu baban shayeeda sakinatu inda suke da yara hudu, sunusi ,sai abdallah,sai haleema da khadeeja,abdallah kyakyawane kamar yanda na baku labari a farkon littafin,yayi karatunsa a turai,abdallah bashida neman mata,da girman kai,fara faran da jama,a,duk yawan yan matan da sukeson abdallah haka baisa ya kulasuba,shidai tunaninsa yana wajen wata yarinya captain shayeeda da ake yawan posting dinta a news da facebbook da instagram,

Sai dayaje hutu gida yake nunawa hajiyarsa hotan shayeeda,anan ya fuskanci sunada alaka da ita,

Nan yakara kamuwa da sonta,abdallah yana yawan zuwa gidansu shayeeda shida yan uwansa saidai in batanan,shine suka hada plan da mom da dad na gyara shayeeda,abdallah shiyawa dady aiki a kafa,lokacin da shayeeda ta harbesa a kafa 😝😝 likitan tiyatane surgery

Wannan shine takaitaccen labarin gwarzon shayeedalle

 

 

Airport sukaje suka yanki tiket,jirgi mai saukar ungulu suka hau,shayeeda tasha hijjabi iya gwiwa

Awa biyu sun sauka a airport din abujah,karo shayeeda tayi da general,yace a a shayeeda akace kinyi aure kin aje aikin soja

Murmushi shayeeda tayi tace wlh kuwa,ai ina matar aure

Haka general sukayi musaba da abdallah,escort suka sarawa shayeeda,murmushi shayeeda tayi tace ku bari banaso

 

Bude musu gate akayi,mutanene makil a gidannan,

Shayeeda zuciyarta ya fara farbawa,da taga anata girke girke

Tabude kofa da niyyar fita,abdallah yace inazaki,ai tare zamu fita,kina ganin yanda aka zubawa motarnan ido ,ga yan mata chan birjik

 

Shayeeda ta ce kaga nifa ba wannan ne damuwataba sonake inga dad dina

 

Abdallah yace zaki ganshi mana

Abdallah ya fito daga motar,yazagaya ta baya ya budewa shayeeda mota,nan ido ya dawo kansu,shayeeda tasa kanta a kafadarsa ,ya rike hannunta suna tafiya,yan mata sai cewa suke dama nice,shayeeda anyi hankali duk inda taga wanda tasani har durkusawa take tana kwasar gaisuwa,har suka shiga parlour daya dinke da yan uwan momy da yan uwan baba

Shayeeda ta durkusa ta dinga gaisuwa,kowa yayi mamaki,abdallah ya hango mominsa suna hira da wata mata,tana ganinsa ta saki murmushi tace son zonan mana,kuzo kuda yar lele.

Shayeeda ta nufi wajen ta durkusa ta gaishe da momin abdallah

Cikin farin ciki momin abdallah ta amsa tace hnmmmm sirkata ykk

 

Murmushin jin kunya shayeeda tayi tace dama momy abdallah dankine?

 

Zaro ido momin abdallah tayi tace abdallah danane wanda na haifa,kinga kunada dankantaka sosai saiku rike juna amana,mai yasameki naga bandage a goshinki

Murmushin yake shayeeda tayi tace faduwa ,shine yaya ya garamin amma fa momy da zafi

Cikin tausaya tace ayyyah tashi kuje ku gaisa da dadynki yau ake auransa da najri yar india dinnan

Zaro ido shayeeda tayi tace nashiga uku yanzu ina momy,

Momin abdallah ta bata amsa ai momy ta daki tana hada kayanta zata tafi cameroon,mun bata hakuri taki sai kuka take.

 

Da gudu shayeeda ta haye sama,tana kukan itace sanadi,tana shiga taga fatima suda shamsy sun tsuguna suna bawa momy baki,shayeeda ta fashe da kuka ta nufi wajen momy

Momy ta daka mata hannu tace,karki cekomai,duk ke kikaja mana wannan abin,kawai ki tafi kuje kuyi rayuwarku da mijinki,tunda baki daukeni uwaba

 

Kuka shayeeda tasa tace momy bansan kowaba saioe kekika raineni ke kika min komai,don haka yau zan sakamiki,zakisan yarki shayeeda tsce kinfi karfin kishiya;momy trust me.

 

Shayeeda ta fita da gudu,ta nufi shasheb dady,abdallah ne a dutkushe yana gaisuwa ga dady,dady yasha farar shadda anmai aiki da bakin zare,ga abokansa sun cika dakin tam,sai washe baki yake

 

Shayeeda tace dady,fitgigit ya juyo yana sakarwa shayeeda murmushi yace a a my daughter ashe kinzo taho mana

Shayeeda ta hade rai tace dady yanzu haka zaka sakawa momy,dady yakamata ayi text koda zakayi aurennan domin lafiyarka

 

Dady cikin lallashi yace yar lele ki fahimta najri lafiyarta kalau kuma tana sona

 

Shayeeda ta dady bazaka ganeba yakamata ayi test

 

Dakyar dady ya yarda aka kirawo likitoci,dady ya bugawa najri dake dayan part din shayeeda waya yace hello dear ki sakko parlour abokaina suna son ganinki

 

An cika parlour makil,momy sai kuka take

 

Abdallah ya zauna,ya na kallon shayeeda dake zaune akasa yanda ta hade rai uwa ita za,awa kishiyar,dariya yayi,suka fada ido da shayeeda,shayeeda tadan kashemai ido daya,shima ramawa yayi

 

Can saiga najri ta fito tasha damammen wando,da riga wanda ya kusa kaiwa cinya amma singlet.

 

Shayeeda tashi tayi tace sannu munafuka saiki zo ki zauna a gwadaki,

Najri tace gwaji kuma?cikin harshen turanci

 

Shayeeda tace indai kin yarda da kanki kizo amiki gwaji

 

Najri ta juya tana wallahi baki isa ki tozartaniba,shayeeda ta janyota ta fara kirbarta,tana dan ubanki fadi gaskiya ko inkasheki anan

 

Dady ne ya dakawa shayeeda tsawa yace shayeeda mene haka ?

Shayeeda ta naushi bakin najri,najri da taji azaba ya isheta tace zan fada zan fada,wallahi ina dauke da h.i.v

 

Nan daki aka dau salati

Najri tacigaba,tace ankawomu nigeria ne donmu saci kudi,mu tafi dashi kasarmu,mu shafawa mutane da dama ciwonnan

 

Nan aka kara daukar salallami da salati,yayinda shamsy ya dakko belt suka dinga nadar najri

 

Baban abdallah yace ai yakamata a kirawo sojoji a tafi da shegiya

 

Abdallah ne yaja shayeeda da taketq huci,dady ya fashe da kuka yana rokan momy ta yafemai

Itama momy kuka ta fashr dashi tace itafa ba komai ta yafemai

 

Nan sojojine suka zo suka tafi da najri da magoya bayanta

 

 

By
Maryam yarmama
[10/03 1:03 pm] salmah💍💍: *👮🏻‍♀CAPTAIN SHAYEEDA👮🏻‍♀*
121-130

By
Maryam yarmama
*dedicated to my salmaty*

*wannan shafin nakune yan group dinmu mai albarka,online hausa writters,Allah ya kara mana hadin kai,da salama a group dinmu*

 

 

Abdallah ya kwantar da shayeeda akan gado,zazzabine mai zafi ya rufeta,tausayinta ya kama abdallah,

Fita yayi yasa aka kawo magani ya bata,har yanzu bata dena zubda hawayeba tace ka kaini gida yayana

Abdallah yace haba dear ki bari zazzabinnan ya sauka,sai in mukayi sallah ma tafi gida kinji ko?

Gyadakai tayi tana murmushi

Abdallah cikin zolaya yace ko indan karane dear?

Yar karar shagwaba tayi tace banaso ,wallahi da zafi

Sallah suka gabatar,gari ya waye,sukaci kwalya,sukayi tahowarsu gida

Shayeeda ta kalli abdallah dake tukkin mota yanabin wakar p-square oyiye yeyeye oyi yeyeye no one like you
Shayeeda tace yayana tayaya zamushiga gida wallahi kunya nakeji

Abdallah yayi kamar baijitaba yacigaba da wakarsa

A bakin gate sukayi horn maigadi ya bude musu,motar abdallah ya danno kai,abdallah yace ki make kamar bakida lafiya banson sumama su miki surutu nafiso,amin nikadai

Shayeeda tace a a gwanda amin nikadai,nafi sonka

Murmushi abdallah yayi,yace ainafi sonki

Murmushi suka sakarwa juna,abdallah yace kinga yanda aka taru kamar taron tururuwa ashe yau za,ayi dinner yar gata yar lele mai farin jini

Shayeeda tace kaga yanda ake ta yayyanka shanaye aketa sauke buhuhunar abinci ashe dinnern saraki za,ayi autan maza,dan gata;yarima,gwarzo barawon daya sace zuciyar shayeeda

Dariya suka saki atare,yayinda suna fitowa daga mota kallo ya dawo kansu

 

Suna shiga babban parlour mutanene burjik,anata tsokanan shayeeda amarya amarya ina kikaje da sassafen nan?

Nan abdallah ya dinga gaisuwa ya wuce wajen su dady,yabar shayeeda anata yarfa mata,fullawa da lalle,yar sudan aka dakko

 

Abdallah yana shiga su dady ne da momy da mominsa da dadinsa sunata hira,kallo ya dawo kansa,kunyace ta kamasa,dady yace sannunku da dawowa fitsararrun yara zaku ja mana zagi,to gobe ku shirya ku tafi gidanka dake malaysia,kuje ku karata abinku achan

Abdallah yace dan Allah dady karkuwa shayeeda fada battada lafiya

Momy tace aikai mugune kai yakamata awa fada

Shamsy ne yashigo yace a a romeo iyayen soyayya ashe kun dawo ina ka baro julliet

Duka fallon suka fashe da dariya;abdallah ya tashi yace nidai saina rama,

Shamsy yace a yahukuri romeo

 

Da daddare akaje akayi dinner get together ,dinner ya hadu,sojoji sunyi matching,an haska su shayeeda a gidan t.v,manyan mutane aka tara a haddaden dinner wanda shayeeda tasa wani material,blue da pink dan ubansu an mata wani dauri,sunyi masifar kyau,abdallah yasha suit dark blue,neck tie pink,rigan cikin fari wow perfect match

Sun taka rawa awajen nera tayi kuka,fati niger ta wakesu,umar m shariff ma ya wakesu sosai

Haka akaci akasha aka watse

Kowa ya koma gidansa aka bada kyaututuka masu ban mamaki,kowa dake wurin yasamu dubu hamsin hamsin,da hanset mai hotan su abdallah akai,da agogo ,sarkin kano ya bawa abdallah kyautar motoci biyu shayeeda motoci biyu,su saude da lantana sun hallaci bikin,

Kowacce da goyanta sunyi aure,

Minister yabasu kyautar estate dinsa dake kasar saudi arabi,a
Sun samu kyauta sosai,aka bude musu asibiti da sunansu , *sha,ab teaching and health hospital*

 

Shayeeda suka bada gudunmuwa abawa marayu da gajiyayyu suka bude makarantun boko da arabic domin gajiyayyu da marayu

 

Jirginsu ya daga zuwa makkah

 

By
Maryam yarmama
[10/03 1:03 pm] salmah💍💍: *👮🏻‍♀CAPTAIN SHAYEEDA👮🏻‍♀*
131-140
By
Maryam yarmama

*DEDICATED TO*
MY SALMATY

*THIS PAGE GOES TO YOU ZULAIHAT,AMINA PRETTY,BINTA KUMBOTSO,MINAL YAR BABA,SHAMSIYYA ALI, J.BOY, BLESSING ALI,AMINA BB ,YOU ARE SO MANY, THANKS FOR CALLING ME AND MESSAGING ME,YOU ARE IN MY HEART*.

 

_the end of this book_

 

Abdallah da shayeeda sun ,goge sunyi kyau,tunda shayeeda ta fuskanci tanada ciki,sabuwar shagwaba ta taso,suna rayuwarsu a malaysia,tayi kawaye da yan nigeria,da yan malaysia,

Shayeeda laulayi take,abdallah ya rikice sai tarairayanta ykk,sunyi bala,in kudi,

Sunyi kyau sun goge
Suna zaune shayeeda ta dora kafarta akan cinyar abdallah yana mata matsa tace honey wallahi ina tsoran haihuwa da zafi fa akace
Abdallah yace bawani zafi,kawai daike matsoraciyace,banki ko wani satiba ki dinga haifomin yan biyu biyu

Shayeeda tace anki wayon aikai baka taba haihuwa ba dole ka fadi haka,

Shayeeda ta tashi nakuda tasha wuya;batayi wani dogon nakudaba ta haifo yarta santalelliya,mai kama da mahaifiyarta kyakyawa

Yan nigeria sunzo,faty dadan cikinta ranar suna yarinyar taci sunan momin abdallah sakeenat(anace mata ninat)

Bayan wasu shekaru ta haifi tagwaye duka maza sukaci sunan dady ridwan da alhussain

Haka sukayi rayuwarsu mai dadi
Shayeeda ta zama hamshakiya,mai hakuri juriya,kyauta,taimako,bin iyaye,bin miji sauda kafa

Shayeeda zaune taje xikin yaranta,ninat tace momy yaushe zamu gida nigeria wai?

Shayeeda tace,nidai bansaniba in dadinka yazo ka tambayesa

Ihu sukaji ga uncle ga uncle,yaya shamsy ne da matarsa da yarsa guda daya

Shayeeda ta tarbi latifa da hannun dama,aka zauna ana hira
Abdallah ya shigo gidan dauke da jaka a hannunsa,yaransa suka,je suka rungumesa,shayeedama taje ta karbi jakarsa
Abdallah ya kalli shamsy yace alhamdudillah

Shayeeda ma tace alhamdudillah yau na dawo hanya madaidaiciya mijina nagode sosai Allah ya barmu tare,

Nima maryam yarmama nace
*ALHAMDULLILAH*

ananna dasa aya,a littafinnan,kurakuren danayi ubangiji Allah ya yafemin
Muje ga cigaban *MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI*
; DA
*SHARRIN YAN MATAN YAU*

_NAMIJIN GASKE_
*GODIYA TA MUSSAMMAN*
(1)MY SALMA ALI WADAH
(2)SUMY BASH
(3)DIJAH WAZIRI(YAR GARINMU)
(4)hauwa mamee
(5)aneelurv
(6)yan mata da mazan o.h.w
Da sauran da ban iya lissafosuba

*MIKA SAKON GAISUWATA GA*
→YARMAMA AND HAJARA HEART NOVEL
→SALMA NOVEL GROUP
→H❤H HEART NOVEL
→ONLINE HAUSA NOVEL GROUP
ALLAH YA BAR ZUMUNCI NA GODE DA KAUNAR DA KUKA NUNAWA NOVEL DINA
MASOYA INA DUMBIN GODIYA

BY
MARYAM YARMAMA
0801173457
07030772637
WHATSAPP ME ALL

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button