Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 25

Sponsored Links

βšœοΈπŸ”±πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA!*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ”±βšœοΈ
*BOOK 2*

*Page 25*

 

Wani abu mai girma ne ya d’arsu a cikin zuciyar Malam a dai dai wannan lokacin,

domin dama tunda Sheikh d’in ya iso garin na Zaria Allah yasa shakuwa da fahimtar juna a tsakanin shi da Malam domin Allah ya wadata Sheikh Naseer d’in da tarin ilimin addini sosai har gobe kuma yana kan neman ilimin ne bawai ya dena ba,
dan haka da yazo sai ya sauke kanshi yake cigaba da d’aukar karatu a wajen Malam duk lokacin da Malam din yake gida,wani lokacin ma shine yake wakiltan Malam wajen karantar da dattawan dake d’aukar karatun bayan ishsha’i a wajen Malam d’in,

Idan kuma Malam ya fita zai zauna yayi ta nazarin tarin littafan da suke falon na Malam, wannan halin nashi da Malam ya lura dashi na jajircewa wajen neman ilimin addini ne kuma yasa ya k’ara kusanci sosai a tsakanin su,
Irin su Sheikh dole duk mutumin daya mu’amalance su yayi sha’awar had’a zuria dasu
Domin dai babu ta gefen da yake da tawaya a rayuwar shi, matashin saurayi ne mai jini a jika dan duka duka bazai wuce shekaru 34 zuwa da 6 ba dan gatan da tun tashin shi bai san wahalar komai ba sai na neman ilimin da yasa a gaba,
Wannan dalilin ne kuma yasa har yanzun ko tsayayyar budurwa baya da ita dan ko batun auren ma bai farayi ba tukun duk da cewa yanzun haka kannin shi maza biyu dake bi mishi duk sunyi aure sun barshi, iyayen shi kuma basu matsa mishi da zancen auren bane saboda sun san ko yayi auren tofa matar bazata samu kusancin dako wacce macce take samu tsakanin ta da mijin ta ba, saboda shi dai wani irin mutum ne mai matuk’ar son sirri a rayuwar shi kwata kwata baya son wani abu da zai had’ashi da jama’a balle kuma wani ya takura mishi,
Yafi gane ya keb’e kanshi waje d’aya yayi ta karance karancen shi,

Sai dai kuma shidin dan ka’idane dukan rayuwar shi yana gudanar da ita ne akan koyarwar addini d’an boko ne na gidi sai dai gaba d’aya baya mu’amalah irin tasu ko a sutura yafi ta’amali da kayan mu na hausawa in basu ba kuma to koda yaushe zaka same shine sanye cikin jallabiya inba a cikin d’akin shi ba bazaka tab’a samun shi cikin shiga ta k’ananun kaya ba,

hakan ne kuma yasa duk wanda zai zauna dashi dole saiya zama mai kiyaye iyakoki domin abu k’ank’ani zaka aikata yanzun nan ya zaunar da kai ya fara karanto maka Allah yace annabi yace,

Shifa tun tashin shi bai yarda yayi aboki ko d’aya ba, abokan shi sune kannin shi,
Yana da fasali da k’ira mai kyau ga kuma cikar halitta kyakyawan namiji ne sosai sai dai bashi da hasken fata,
Domin kaf yaran gidan su farare ne tass amma shi sai ya surka kalar tashi fatar batayi haske irin nasu ba amma kuma tashi sai tafi tasu d’aukar idon mai kallo shi ba bak’i bane ba kuma zamu sashi cikin sahun bak’ake ba ah ah yafi kama da bak’aken larabawa kamar yanda mutane da dama suke fasalta shi,
Ganin farko idan ka mishi zaka hango tsabar hutu da tsaftar dake tare dashi dan shi saboda tsabar sanin ciwon kai ko d’an guje guje ko d’aga karfen da matasan zamani keyi bayayin su baya da kiba ko kadan ba kuma zamu kirashi da siriri ba komai nashi dai dai shi Allah ya mishi,

Tun daga wannan ranar Malam yake ta neman hanyar da zai k’ir k’iri kusanci tsakanin Meenal da Sheikh domin shi dai yana ganin cewa Sheikh ne irin mijin da ya cancan ci auren Meenal dinshi, yasan idan har suka had’a kansu babu wanda bazaiyi farin ciki da hakan ba dan ya tabbatar da cewa idan Meenal ta auri Sheikh zataji dad’in zama dashi sosai ga soyayyar da zata samu daga dangin shi kuma domin ya tabbatar da cewa Momin Abuja zata kula da Meenal d’in kamar yanda zata kula da Sultana,
sai dai bazaiyi gaggawa ba saboda baya son yayi wani abun dazai k’ara kawo nakasu a cikin rayuwar Meenal d’in a karo nabiyu zaifi kowa farin ciki idan ya kasance cewa sune suka had’a kansu bawai auren had’i ba.

Dan haka sai ya zamana shima Sheikh din duk in suna tareda Malam sai malam yayi ta yabon kyawawan halayen Meenal d’in a gaban shi haka zaiyi ta bashi labaran daya shafi Meenal d’in harda irin yanda tayi nata yarintar da kalar rikicin da tayi tayi kafin auren ta, har rikicin da tayi lokacin auren ta da Sarki duk sai da ya bashi labari,
Wannan dalilin ne kuma yasa shima Sheikh d’in yake kokarin nuna kulawar shi aka Meenal din dan ya tabbatar da kaunar da Malam yake mata kamar yanda ya dad’e yana jin ana fad’a, abunda shi kuma bai sani ba shine wannan kusancin dake tsakanin shi da Malam shine abu na farko daya fara jawo mishi bak’in jini a wajena Meenal dan gaba d’aya zaman shi a sashen malam din yasa gaba d’aya kota shiga wajen ita kuma bata sakewa.

kullum idan Meenal taje wajen Malam sai yasan yanda yayi ya sako mata zancen Sheikh kullum Malam cikin yaba kyawawan halayen shi yakeyi a gaban ta, a kokarin shi na ganin ya cusa musu ra’ayin juna sai ya zamana duk wani abu daya shafi sheikh d’in Meenal yake sawa tun daga gyaran d’akin da Sheikh d’in yake kwana wanda yake anan cikin sashen na malam abincin da sheikh d’in zaici kai wani abun haushin ma ko aike malam zaiyi sai ya had’a meenal din da sheikh yace suje tare,
Ita kuma gaba d’aya abun nan ya kai mata ko ina bata dai da yanda zatayi ne kawai, dan sosai fa sheikh yake shiga mata hanci da kudundine ba dama yaga ta zauna tana kallon films dannar waya ko wani abun zai wani fara mata wa’azi cewa da zaman da takeyi da qur’ani ko wasu littafan ta d’auko ta karanta,
kai mutumin nan fa ya kai mata ko ina kamar akan shi aka saukar da ustazanci shi yak’i ya saki jikin shi yayi enjoying life din shi haka yake son duk wanda yake rayuwa a kusa dashi ya rayu kamar shi dai, haba dan jama’a a ina ake gudanar da rayuwa babu nishad’i naga dai ko abinci bashi ciyuwa sai an sarrafa shi da kayan d’and’ano.

Wai saboda tsabar sa ido irin na ustazun nan wata rana sun shirya tsaf zasu fita ita da Sultana Tudun jukun suke son zuwa ita dasu Maryam a wannan ranar, har sun sallami Mommy Hauwa suna shirin fita sai Ya Sa’eed ya shigo sashen nasu,
Bayan sun gaisa ne yake tambayar ta cewa,

“Meenal yaushe zaki koma Tudun wada dan akwai sakon ki a hannu na amma nafi so sai kin koma sai inzo muyi magana ko kin dawo nan d’in kenan gaba d’aya?”

“Ah ah wallahi nikam ban dauwa ma a gidan nan indai wancan sabon ustazun na cikin shi, komawa na kuma yana iya kamawa ako wani lokaci, duk Anbi an tara yan sa ido a cikin gidan ne zan zauna tab’
In maganar tana da mahimmanci ka bari idan na dawo zanzo sashen ku sai kuyi maganar acan”

“Ah ah sirri ne bana so kowa yaji shi yasa ki bari kawai idan kin koma can sai inzo,
Ina zakuje yanzun? ”

“Tudun jukun zamuje daga nan zamu wuce G R A gidan Sa’adatu mukai mata anko kasan mu yanzun kuma ba zama, yauwa Yayana nace tunda dai kamin allah sanya alkhairi na mota har yanzun baka bani kud’in sa mai a motar ba!”

“Oh yanzun kuma wajena za’a amshi kud’in man kenan?”

“Ah ah nifa ba wai na rok’a bane amma dai idan ka bani bazan k’i amsa ba kasan ai nidai bana maida hannun kyauta baya”

Hannu yasa a cikin aljihun shi ya zaro wallet din shi yan dubu dubu ya zaro bai k’irga ko nawa bane ya mik’a mata,

“Gashi in kuma bazai isa ba in kun fita sai ki biya wajen Farouq ki amsa ko kuma a wajen shi sabon ustazun shima”

“Ai da ina kusa bazaka b’ata kud’in nan bama, ke Meenal ina ce d’azun nan kika amshi kud’in mai a hannun Abban ku? Anya kina da tausayi kuwa? kin san bazaki iya cacar siya ma motar mai ba kika amshi kyautar ta nifa bana son wannan d’abiar naki na titsiye mutum kisa ya miki kyautar da baiyi niyya ba, ko kuma shi kenan tunda kin san suna baki komai kike so sai ki tun karesu kai tsaye, suma fa suna da nasu iyalan a k’ark’ashin su, ke baki da wani matsala sai dai a baki kud’i ki kashe”
Cewar mommy Hauwa

“To Mommy tsakani da Allah in ban amshi kud’i a hannun suba ai ko Allah ma sai ya tambayeni gani da yayye maza da yawa yarinya yar dangi to so ake inje in rok’a a wani wajen daban bayan gasu nan reras kin haifo musu ni,
Ai hak’uri kawai zasuyi su dage da nema Allah kuma yaci gaba da bud’e musu k’ofofi na alkhairi suyi ta bani ina Tarawa a nawa asusun Allah Mommy kud’i nike son tarawa masu yawa in Siyama Babana gida yaje can gefe ya huta da hayaniyar jikokin da suka cika mishi gida.

Da sauri Meenal din ta fice daga falon tana dariya,

Tsaye a wajen motar ta ta iske Sultana,

“Me kike jira kuma da baki tada motar ba?”
Ta tambaya tana shirin zagayawa gefen mai zaman banza dan in zasu fita Sultanar ce ke jan motar dama tunda suka dawo,

“Zonan kema!”

Tajiyo muryar Sheikh yana bata umarni daga bayan ta,

“Na’am nii ina kwana!” Ta fad’i nii d’in tana nuna kanta saboda ta tantance koda ita d’in yake yi,

“Lafiya lau eh kefa ina zaku? Ina lura da yanda kullum sai kun fita daga gidan nan bakwa kuma dawowa da wuri ina kuke zuwa? ”

“Gidan Sa’adatu zamuje”
Meenal ta bashi amsa,

“A hakan kuma kike shirin fita babu mayafin kirki a jikin ki?”

Shiru tayi tana binshi da ido kamar bata fahimta akan me yake magana ba,

“Eh nace baki da Hajibi ne ke?
tunda kika dawo ban k’ara ganin ki da Hijabi a jikin kiba kullum sai dai ki zura doguwar riga ki yane kanki da figaggen mayafi ki fita haka nan kina yawo a gari ko kunya bakyaji,
ko dama su hijjaban dana dunga ganin kina sawa a can gidan rasuwar na aro ne?”

Sim sim Sultana ta fara takawa sai da tayi d’an nisa dasu kad’an kafin ta tattaro rigarta ta kwasa da gudu ta koma sashen Mommy Hauwa dan tasan yana gamawa da Meenal din wallahi kanta zai dawo,
Ita kanta Al’amarin na yayan su yana matuk’ar d’aure mata kai, tsananin shi yana neman yayi yawa wallahi shi fa ko a can Abuja kannin shi ba wani son zaman shi a kasar sukeyi ba domin dai daya dawo tofa dole kowa ya aro ustazanci ya yafa shima,
shifa komai sanyi ko tsananin zafi bai kaunar yaga kannin shi mata da jiki a bud’e, ah ah in shiga zakiyi sai dai ki kin kima k’aton hijabi sannan kibi da safa hannu da k’afa ga kuma uban niqabi kamar wata ninja,
Shi yasa tunda yazo gidan suke matuk’ar shiri da Fauxieyerh kanwar Meenal saboda ita dai haka nan Allah ya halicce ta duk wuya duk rintsi bazaka rasata da hijjab a jikin taba tana nan kullum jiki a kudundune uwa wata konanniyaπŸ˜’,

Sab’anin Meenal da tun tasowar ta ita daman kowa yasan mafi yawar suturun ta dogayen rigunan abaya ne sai kuma ta lulllub’e jikin ta da mayafan su, koda tayi aure kuma bawai ta canza shiga bane,
Yanzun kuma data samu cigaba sai ya zamana shigar nata ya canza mai makon dogayen rigunan da take ta’amali dasu a lokacin baya yanzun takan sirka dasu riga da zani ko riga da siket English were tafi amfani dasu ne ranar da take gida shima kuma tafi ta’amali da riga da Sket a gidan Hajiya ne kad’ai take sakewa tayi kalar shigar da tayi ra’ayi tunda can din babu tarin maza kamar nan gidan su,

Mai da kallon ta tayi zuwa ga kayan jikin ta,
Doguwar rigar abaya nefa navy blue a jikin ta sabuwa dal dan yau ta fara sakata yana cikin tsarabar da Momin Abuja ta kawo mata,
kuma ko kad’an babu ta inda rigar ya kamata dan a sake sosai rigar take, kuma gyalen datayi rolling dashi ma yana da girma dan ya sauko sosai ya rufe mata har kasan k’irjin ta,

“Ki koma ciki ki sanya hijjab in fitar ta zama dole!”

“Iyye 😳”
tace tana zaro idanuwa cike da mamaki,
Jama’a yau nike ganin mulkin mallaka, to inba haka ba ina ma ruwan shi da itane da zai nemi matsa mata,
Zaman shekaru 6 tayi da Sarki amma ko sau d’aya bai tab’a ce mata ta koma ta canza kaya wai dan zata fita ba, kafin auren ta ma ai tayi zama a gidan nan amma ko Malam bai tab’ayin mata magana akan shigar da takeyi ba, kuma ita a iya hasashen ta bataga ta inda shigar ta ya gaza ba, babu inda ta bari a bud’e komai a lullub’e yake daga kafarta tafin hannu sai fuskarta ne kad’ai fa a waje,

“In kin gama nazarin kina iya komawa daga ciki, baki fita gidan nan har sai kin sa Hijjab na fad’a miki, dokar daya kamata ace kece kike kafama kannen ki sai gashi kema yi kikeyi kamar wata *Yarinyar goye* ”

Innalillahi jama’a wai ita Uwar malam ne ustazun nan ke cema tanayin abu kamar wata yarinyar goye,
Aiko yasin ya shirya ganin aikin yara indai ita ne badai ya samu waje yazo gidan su ya zauna har shine yake ganin cewa yana da damar kafa mata wasu sharad’od’i ba.

“Ni bani da Hijjab kuma wannan shigar ita na sabayi tun ban kai haka girma ba, kuma babu wanda ya tab’a cewa dole insa Hijjab dan zan fita dan babu ta inda suturar jikina ta kasa”

“Sune basu ga inda ta kasa d’in ba amma aini gashi na gani, ki koma ciki ki tsaya a gaban mirror ki kalli kanki da kyau”

“To ai dai nace maka bani da Hijjabai anan gidan kayana suna gidan Hajiya sai naje can zan kwaso tunda na aron da nike sawa na baro ma maisu kayanta”

Tsalle daya yayi ya haye saman booth d’in motar dake kusa dashi ya d’auki kiran daya shigo wayar shi ya shareta,

Haushi bak’in ciki da takaici sune suka nemi sata ta jawo kafar shi ya fad’o daga saman motar da yake zaunen,

Kuma wallahi wallahi bai isa ya hanata fita daga gidan nan da shigar nan ba,
Toma waye shi dazai wani ce zai kafa mata dokar da dole tabi, allah ma yasa ba iya wannan ne kofar fita daga gidan ba, dan haka fuuuu ta juya ta koma sashen nasu, tana shirin shiga Sultana ta sawo kai zata fito sanye da zumbulelen hijjabin ta har k’asa mai ruwan kwaiduwar kwai,

“Ya koro ki kizo ki canza shiga kenan? ”
Sultanar ta tambaya tana dariya,

“Wannan yayan naku sam bashi da halin kwarai wallahi to wai ma ni kad’aice mace a gidan nan dazai wani samin ido har haka?
Ina ruwan shi da shigar jikina tunda dai bashine yake siyan min sutura ba,
Kuma wallahi bazan canza kayan ko insa Hijjab dinba kuma sai na fita d’in sai dai idan na dawo ya dafani ya cinye”

“Ke Sister karki wani b’ata ranki, akan abunda yace indai Ya Sheikh ne haka yake indai yana waje duk sai ya takura ma rayuwar mutane yake jin dadi”

“Key din motar fa?”
Meenal ta tambaya.

“Gashi nan a cikin jaka ta”

“Ok to jeki kawai zan same ki a kofar gidan su Meelat ko kuma mu had’e a kasar layi kawai dan ta k’ofar baya zan fita, idan ya tambayeki ni kice mishi nayi fushi na fasa fitan kinji”

“Wai da gaske bazaki sa hijjab d’in mu tafi ba? Koni da kikaga nasa ai dan dai kawai a zauna lafiya ne amma muna fita zan cire shi sai zamu dawo zan mayar dashi a jikina”

“Wallahi bazan saba in kuma ya tab’a siyamin kyalle da sunan sutura ne sai ki fad’amin, ke karfa kiga wai dan yana matsayin yayanki kiyi zaton zan d’aga mishi k’afane idan naga zai takura min tam”

Tana gama fad’in hakan tabi ta baya ta fice daga gidan shiko Sheikh yana can yana zaman gadi koda Sultana tazo ta shiga motar harta mishi sallama cewa sai ta dawo bai tambayeta ina Meenal ba domin daga yanda tabar wajen yasan fushi tayi.

Moon kwance take akan gadon d’akin ta misalin karfe 10 na dare, wayane a hannun ta tana chat dasu Meelat da suka bud’e group wanda suke tattaunawa akan bikin Meelat d’in,
Sai dai lokaci lokaci takan fita da group d’in ta amsa sakon da Sarki yake turo mata,

“Mai kikeyi har yanzun bakiyi bacci ba?”

“Nothing important kawai muna hirane nida su Meelat kasan next week ne bikin ta so shirye shiryen bikin mukeyi muna tattaunawa ne”

” oh kuna da biki shine ma babu gayyata?”

Saida ta tura mishi da emoji mai murmushi kafin ta bashi amsa da cewa,
“😊 wannan kuma tsakanin ka da k’anwar Meenal ne”

“Oh kenan ke bazaki iya gayyata na a mai makon taba kenan? ,
to in haka ne ki shirya sai mu wuce tare gaba d’aya dan nima dama wani abune ya tsayar dani a garin ku da yasa nakai har yanzun ban koma ba kinga sai mu wuce kawai tare inba damuwa”

“Ok to kana ganin har zaka gama naka uzurin kafin lokacin?”

“insha Allah ina sa ran hakan addu’a dai nike tayi har yanzun da kuma neman zab’in Allah,
Kin san me?”

“Ah ah sai ka fad’a”

“Aure nike so in k’ara Moon, kin san wanda ya d’and’ana zama da mata biyu da wahala ya iya rayuwa da mace guda 1 kuma sai in lalura ne ya gifta”

Tun d’azun da suke hirar a kwance take,
Amma tana gama karantar wadannan kalmomin ta mik’e zaune dangal gal gabanta na tsanan ta bugawa,

Innalillahi wa’innah ilairir ta shiga karantowa kasa k’asa a yayinda take jin wani kalar tashin hankali yana yunk’uro mata,

To kenan dama duk kusan ta kanshi da yakeyi da ita bawai dan yana sonta bane?
To in har dama yana da wacce yake so a gefe mai yasa rana d’aya kwatsam ya dawo cikin rayuwarta har yasa zuciyar ta ta samu kusanci dashi,
K’arar kiran daya shigo cikin wayarta ne ya katse mata dogon tunanin da takeyi,
Number din shi da tayi saving da *King* ne ya fito b’aro b’aro a fuskar wayarta,
Bata iya d’aukar wayar ba harta k’ara ci ringing d’in ta yanke,

Sako ya k’ara tura mata ta WhatsApp din yanzun ma inda yake cewa,

“Na kira baki d’auka ba! Koda yikema ba damuwa muyi hirar anan kawai”

“Hummm” shine amsar data tura mishi,
Bai damu ba ya k’ara tura mata da wani sak’on kamar haka,
“Na samu macen da nike ganin zatayi dai dai da tsarina, saboda itane ma nabaro aikina na taho, sai dai har yanzun shakka da tsoron yanda zata amshe ni hakan yasa na kasa fitar mata da abunda yake cikin zuciyata, tsoro nikeji kar sai na tunkare ta ita kuma tace min na mata tsufa, I really don’t know how to tell her I’m in love with her, ko zaki iya taimaka min?”

Amsa ita kuma ta tura mishi da cewa,

“Just let her know that you love her, tell her karka b’ata lokacin da wani zai so ya maka shigar sauri, kuma da kake maganar cewa ka mata tsufa indai tana sonka ai bazata tab’a ganin tsufan naka ba, kai dai kabar rai da abunda yake so kawai”

Wani sak’on ya k’ara turo mata kamar haka,

” You are right ok let me practice once on you first,
*I LOVE YOU MAIMOON*”

“I love you too,
You can now go ka fad’amata gaskiyar abinda kake ji a kanta! Zan kashe wayana sai da safe, idan mun had’u zanji yanda kukayi da ita”
Itama ta tura mishi

“Wait please don’t go, saboda na riga na fad’amata har ma ta bani reply ko”
Ya aiko mata,

“Wow na tayaka murna”

“Bari in turo miki amsar da ta bani”
Saman chat d’in su ya koma yayi tagging d’in amsar data tura mishi d’azun inda tace “I love you too”
Sai ya rubuta mata “kinga amsar data bani”

😳 zaro idanuwan ta tayi waje cike da mamaki da sauri hannun ta ya typing ta tura mishi cewa,

“Amma wannan ai chat d’in da mukeyi da kaine!”

“Eh ai saboda kece yarinyar da nike so d’in shi yasa, Nagode kwarai da amsa tayin soyayya ta a gareki, a yau kinsa nima ina jin kaina kamar sabon saurayin da bai tab’a aure ba balle har ya haifi yara 4 insha Allah kuma zanyi k’ok’ari zuwa gobe in kawo ma Baba Usman gaisuwa da rok’on iri dan gaskiya ina buk’atar ki a kusa dani kwarai da gaske, ki kwanta kiyi bacci yanzun sai da safe,
*I LOVE YOU TOO SWEATHEART*”

Yana tura mata ya kashe data dan yasan dole zata nemi k’ara jin ta bakin shi.

*Ummiee ce*✍🏼

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button