Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 25

Sponsored Links

Lantanar tana sake jin tausayin kaltum cikin ranta,saboda gaba daya ta rame,ta kuma sauya,ba kamar yadda fa santa ba

“Dauki ruwa kisha kattume” lantana ta fada a tausashe,bata musa mata ba,saboda tuni maqogoronta ya bushe,saboda tsoro da firgici tare da tunanin kalar amsar tambayar da tayi daga bakin lantana,saita dauka din,ta kurba sau uku ta ajjiye,dai dai sanda lantana ke tambayarta

“Amma dai lafiya kattume?” Kai kaltum ta girgiza,sannan ta fara magana cikin sanyi da rauni

“Wai lafiya lantana?,me yake faruwa dani?”

“Me kika gani?”, Lantana ta maida mata tambayar tana kallonta

Kai kaltum ta juya sannan tace

“Duk inda nabi ko nayi…..sai naga kaso mafi yawa na mutane suna bina da kallo” shury lantana tayi,wanda hakan ya qara yawan fargabar kaltum,ta kuma kasa sake tambayar lantanar,har sai data magantu da kanta

“Da kaina dama na yanke inje har gida na sameki koda baki zo ba…..kaltume,lallai mutum abun tsoro ne,bayan abinda wasila tayi miki bai isheta ba,tana ci gaba da yadaki,tana gayawa mutane cikin shege kikayo shi yasa aka gasa aurenki,nasuru wai da kansa ya buqaci aurenta saboda ya rama cin amanar da kika yi masa,wannan shine babban dalilin da yasa kikaga mutane na miki irin wannan kallon”.

Batasan hawaye take ba sai da taji duminsu saman fuskarta,wai dama haka mutum yake?,kodai tasu jama’ar ne haka?. Tunaninta ya yanke sanda lantana take cewa

“Wasila ta bawa mutane masu irin tunanina mamaki,ta barki mana da tabon data yi miki?,yanzu ta ina zaka fara wanke kanka daga wannan batancin?”

Sak irin tambayar data zo kan kaltum kenan,ta yaya zata sauya tunanin mutane daga kanta,duk da cewa ba’a bari a kwashe duka,duk da cewa koda ta wanke kan nata ba kowa bane zai yarda?,amma a qalla ta rage wani abun.

Zumbur ta miqe tana goge damshin lemar hawayen fuskarta

“Idan zaki dandali anjima,ki biyomin” ta qarashe maganar tana yin gaba,sai lantana ta bita da kallon mamaki,tare da tambayar kanta me xata je yi a dandali,matar da duk randa aka ganta a dandali lallai ba qaramar sa’a aka ci ba,saidai kafin ta tambayeta harta fice daga gidan ta quracewa ganinta,ta barta da tambayar kanta tambayar da bata da amsarta.

*8:00 pm*

Sanye yake da wata qawatacciyar tattausar riga hoodie zip mai hade da hula,tana da dogon hannu,hakanan tana da dan kauri ba laifi,kalarta ruwan hanta ce mai asalin kyan,trousern jikinsa ya dace sosai da kayan daya sanya din,sai wata hula daya sanya a saman kansa,wadda take shige data sanyi,sakamakon sauyin yanayi na busawar iska da aka samu,sakamakon sanyi dake sallamawa mutane.

Har ya janyo takalman daya saba sanyawa duk yayin da yayi irin wannan shigar,sai kuma ya fasa,sakamakon tunawa da yayi cewa,yazo garin ne a sunan lebura kamar kowa,saiya watsar dasu,ya miqe zuwa qofar dakin,yana fidda zazzafar iska daga bakinsa,zafin da zuciyarsa tayi tun dazu har yanzu batayi sanyi ba,dalili kenan daya daga waya ya kira hannafi,yacewa umar ya shirya suje dandali ya rage dare.

Duk da cewa akwai abubuwa masu tarin yawa cikin qauyen da yake kallonsu cike da kusakurai,to amma yanayin yadda wajen ke cike da masu neman na kai,da kuma qoqarin nishadantar da kansu da sukeyi yana burgeshi.

Sama da qasa umar ya kalleshi sanda ya fito,ganin har yau dai wata shiga yake a hargitse,kamar ba sarakin daya sani ba,wanda baya saka kaya sai designers,wadanda suka amsa sunansu kaya

“Muje ko?” Saraki ya fada yana tsare umar da ido,saboda yadda yaga yana kallonsa,saiya dan sosa kansa kana yabi sarakin a baya.

Su biyu suke tafe zuwa dandalin,lantana da kuma kaltum,wadda tunda suka taho take riqe da kara a hannunta tana dan kadashi,zuciyarta cike fal da tunani,lantana dake gefanta itama tana nata nazarin,ganin har yanzu kaltum batace ga abinda zataje dandali yi ba
“Amma dai kaltume ba fada zakije kuyi dasu wasila ba ko?” Wani busashen murmushi ta saki,ba tare data kalli lantana ba tace
“Fada?,Allah ya kiyaye,zanje ne kawai na isarwa da jama’ar qauyen saqon daya kamata ace sunsani,tunda sun kasa tunkarata,wanda ya yarda ya kyautatawa kansa,wanda kuma ya riqi akasin hakan shi yaga zai iya” kai kawai lantana ke gyadawa,tasha jin ana fadin kaltumen gwanar iya magana ce da tsari,duk cikinsu babu wanda ya kamota,bata tana sake gasgatawa ba irin yau,haka shuru yaci gaba da wanzuwa a tsakaninsu,har zuwa sanda suka qarasa dandalin.

Abun tamkar wani afi,dandalin yau ya cika sosai da jama’a,har hakan yaso basu mamaki gaba dayansu daga ita har kaltum,saboda ba kasafai aka fiya samun irin wannan cikar ba,saidai hakan bai hanasu kutsawa zuwa muhallin da suke tsaiwa ba,kutsowar tasu dataja hankalin mutane,suka fara kawo idanuwansu kansu.

“Alqur’an gata can,gata ca yauma tazo,gaskiya nazo wajen nan a sa’a” cewar haladu yana washe baki,kamar wanda aka yiwa bushara.

Maganar data sanya samir dake zaune saman wani dan teburi,da alama wata sana’a akeyi a kanta yau mai teburin bai samu zarafin yinta ba.

,tunda yazo ya samu su haladun a wajen,suna ganinsa suka sake masa,kamar sun jima da sanin juna,tun yana biyewa hirar da suke masa har ya qosa,kasancewar bai saba ba ya koma yaqe,daga bisani da yaga abun bana qare bane,sai yace musu ciwon kai yake,abinda yasa suka janyo masa tebur din kenan ya zauna

“Amma haladu baka da hankali…..wai kana nufin har yanzu son yarinyar nan kakeyi?” Abokinsa da samir ya sansu tare tun a ganin farko ya fada yana duban haladu cike da mamaki fal sama fuskarsa.

Tsaki haladu yaja yana daidaita tsaiwarsa,ta yadda zata bashi damar ganin kaltum da kyau

“Tome za’a fasa?,mutuwa ko hisabi?,ni ai fasawar wancan gajan gaba ta kaini,wai gobarar titi a jos”

“Amma haladu bansan baka da hankalo ba sai yau…..yarinyar da tayi cikin shege…..,qawarta ta shaida haka,matar qanin babanta ma ta bada shaidat faruwar abun,wanda xai aureta ya karbi kudinsa…..shine kai zata sanya kanka a cikin irin wannan hadarin?”. Lafuxxan bakin labaran su suka dauki hankalin samir,ya cira kansa a hankali dake duqe a dazu yakai shi zuwa sashen da kaltum ke tsaye ita da lantana,tazarar dake tsakaninsu da ita ba wata mai nisa bace can,hakan ya bashi damar kallon fuskarta sosai.

Very young girl,wadda baiga komai tattare da itaba face qananun shekarunta,siririn jiki da kuma baqar fuskarta da babu koma a samanta sai karan hanci,ko cikakken qirji bai hango ba bare su zame mata ado,har a yaushe tasan wani abu da zata bata rayuwarta irin haka?,bama wannan ba,shi wanda suka aikata abun tare,indai har hakanne….indai har da gaske ne,meye abunda yaja ra’ayinsa a kanta?,baya bata da duk wani abu da zaija ra’ayin namiji akanta?,bata mallaki komai ba face baqar fata,mai duhun da bashi da kyan gani.

Idanunsa suka sauka kan qafafunta dake saye cikin takalmin roba da yaji ana kira da BURIN ALMAJIRAI,sai ua sauke idanun nasa,yana jin qirjinsa yana nauyi,ba shakka tafiya mabudin ilimi ce,yaga abubuwa masu tarin yawa da suka sha bamban da abubuwan dake faruwa a duniyarsa.

Kallon banxa haladu yayi masa,yana sake jan tsaki

“To saime?,ita soyayya bata duba wadan nan,bakasan yadda nake sonta bane da ba zaka ce haka ba” kai abokin nasa ya kada,da alama maganganun haladu sun kaÉ—ashi

“Amma dai kasan duk yadda kakai ga sonta su gamandi ba zasu barka ka aureta ba ko?,tunda babu wanda baiji labarin abinda ta aikata ba” a fusace haladu ya fuska ci labaran

“Wai tsaya labaran,kai da kaketa wannan hanqilon,a gabanka akayi ne?,ko zaka iya rantsuwa sa alqur’ani izifi sittin cewa lallai ne ta aikata abinda ake zargin?,zargine fa…”

“Eh zarginne,amma bisa qwaqwwarar shaida da hujja daga makusantanta……..” Sauran maganar da labaran yayi niyyar fada ta maqale,saboda yadda sukaji filin ya gaba daya ya dauki wani irin shuru,sai dukka suka maida hankalinsu ga filin,don ganin abinda yake faruwa,ciki harda samir,kamar wadanda akaja hankalinsu zuwa can

Kaltum ce take takowa zuwa tsakiyar filin,sanye da fingilalliyar rigar atamfa wadda taci duniya dai dai gwargwado,zanin jikinta yasha bamban da rigar jikinta,sai maqalallen hijabinta daya zama kamar na gado.

Kowa idanu ya zuba mata yana kallonta,saboda sun manta rabon dasu ganta cikin fili irin haka,baka filin ba,dandalin ma zuwansa ya zame mata wani tsohom tarihin da sai sanda taso waiwayarsa take zuwa,koda tazo ta watsar da waqenta mai dan karen dadi da takeyi,duk kuwa da nacin da ake mata,dama can kuma ba rawa take ba,yana waqen ne hade da rausayar da har yau ‘yammatan suka kasa kwaikwayar irinta.

Abu na biyu kuma kusan labari yaje kunnen kowa na cewa wai tayi ciki,ga tunaninsu tabar fita koda nan da qofar gida,wala’alla ma a gaba kadan ta tattara tabar qauyen,saboda matan da irin hakan ta faru dasu cikin qauyen basa qara wasu kwanaki masu yawa suke barin qauyen,saboda gudun kada abunda suka aikata ya bullo kowa ya gani xahiri,da wadanda suka yarda dama masu shakka.

Kamar saukar ruwan sama saman kwano a lokacin da ba’a shirya ba muryar kaltum ta fara fita,cikin wani irin amo da sauti daya ja hankalin na kusa dama na nesa.

A hankali take rausayawa,cikin wata irin tarin nutsuwa data tafi hade da sautin amon waqarta,wani irin karin waqa dake sanya zuciya ta rusuna,ya kuma ja hankalin mutum daga farko yaji abinda ke faruwa a tsakiya da kuma qarshen waqar,shurun da wajen kawai yayi ya isa ya shaida maka cewa waqar na daukar hankalin jama’a tana kuma ratsasu yadda ya kamata.

Tsahon minti uku waqar ta dauka kafin takai qarshenta,wanda zuwa sannanZukatan mutane da dama sun shiga shakka da kuma kokwanto,aka shiga cece kuce da qananun maganganu a wajen,kowa da abinda yake zantawa da ‘yan uwansa,kawunan mutane ya rarrabu,mafi rinjaye daga cikinsu sun yarda da abinda ta fadi din,musamman wadanda sukasan yanayin rayuwar gidansu,da yadda ta rayu,take kan rayuwar ma,yayin da wasu kuma suka ce sam,kawai tabarmar kunya takeson nadewa da hauka cikin waqe,daga cikinsu akwai wasila da jama’arta,wasilan ta cika tayi fam saboda irin magangnun da kaltum din ta yaba mata a habaice,ta kirata da sunan wadda bata ramin kanta,saidai ayi mata ta shige,ta kirata da matar cushe wadda bata daraja,maicin amanar masu amana,itakam kaltum ta gama da ita.

Fit aka nemeta a waien aka rasa,ciki harda lantanar da suka xo tare,ji tayi bata da wani sauran dalili da xai zaunar da ita a wajen,uwa uba batason babansu ya dawo gida bai cimmata ba,batasan me zai afku ba.

Tafiya take a hankali,tana jin yadda jikinta yake a sanyaye,duk da cewa ta furxar da abinda yake cikin zuciyarta,aqalla ta samu wani relief ko yaya yake,saida qafafunta a sanyaye suke,gabanta na yawaita faduwa,tana jin kamar akwai sauran qura a gaba,qurar data sani ta fiddo mijin aure,dama wadda bata sani ba wadda ubangiji kadai ya barwa kansa sani.

Ta gama lalubenta kaf bata san wanda xata tsayar din a matsayin miji nan da wata guda ba,indai kuwa hakan ta faru,bata da wani xabi illa ta saurari haladu,duk kuwa da yadda ranta da zuciyarta basu kwanta dashi ba.

Yana daya daga cikin mutanen da waqenta ya jefa nazari cikin zuciyarsu,daga nan inda yake zaune yana jin yadda tabar baya da qura,yadda jama’a keta cecekuce akan maganganun data fada,masu fashin baqi nayi,masu qarawa abun gishiri suna yi,kowa da inda yasa gaba.

Tsaki yaja yana watsa matsalar gefe guda,baiga amfanin shima ya tsaya yabi sahunsu ba,ta hanyar baiwa kansa aikin tantance abinda kalamanta ke nuni akai,shima fa yana da abubuwan daya kamata yaui concentrating akansu.

Har ya buda baki zaiwa umar magana akan ya taho su tafi saiya fasa,ya saki wani qaramin murmushi sanda ya hangeshi ya tsaida wata budurwa yana tsarata,ko hankalinsa baya kaiwa bayansa.

Ya sani kawai salon abun nan ne da hausawa ke cewa rage dare,saboda already umar din akwai wadda ya tsayar jalila,har momy yasa taje ta gaisar,ba tare daya nuna ya ganshi ba ya juya ya kama hanya shi kadai,bai nemi umar ba bare hannafi.

Ci gaba take da tafiya hankalinta naga tunanin da tayi zurfi a kai,kamar daga sama taji mutum yif ya cake a gabanta,razana tayi sosai,ihu taso qwalawa Allah ya taimaketa bakinta ya furta
“A’uzubillahi minashshaidanir rajim!” Da qarfi tana fidda idanunta sosai,tana son bambance waye ta hasken farin watan da ya haske sararin samaniya…

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button