Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 41

Sponsored Links

41

Tunda suka tafi hankalinsa naga titi,tuqinsa kawai a hankali cike da nutsuwa har suka kawo gidan amaren,jama’ar daya debo suka fita,saidai mubina ta kasa koda motsawa,saboda yadda kan mata ciwo ainun,ya kuma qaru ke ciwon saboda saraki,wanda baisan meke faruwa ba,don suna zuwa bayan ya kashe motar ya fice daga ciki shima.

Baisan tana ciki ba sai sanda zasu koma,da yake wadanda ya debo din ba komawa zasuyi ba,amiru ya bude gaban da niyyar shiga ya ganta,ya shaidata don haka ya tambaya,da qyar ta iya amsa mishi

“Please saraki ka daure mu ajeta koda pharmacy ne ta amshi magani,daga nan ta kira wani ko daga gida ne ya maidata gida” yace da samir sanda yake tada motar,shuru ya masa bai amsa masa ba,ya fara tuqinsa abinsa.

A bakin wani madaidaicin private hospital ya tsaida motar,yayi horn sau biyu mai gadi ya taso ya bude masa ya saka motar ciki

“Ho samir” amiru ya fada a ranshi,bai tsammaci ma yana da niyyar yin abinda ya sakashi ba,duk da yasanshi sarai,yana da matuqar tausayi da kulawa,mutum ne kuma shi mai tausayin mace qwarai.

Nurse ce ta fito ta kamata zuwa ciki saboda yadda take tafiya da qyar saboda ciwon da kan nata yake mata.

Mintina qalilan ta gama ganin likita,amiru na zaune yana waya yaga shigowarta,ba jimawa samir din ya shigo shima ya tada motar suka wuce.

Bakin wani pharmacy ya tsaya,ya wurgawa amiru dake zaune a baya takardar hannunsa ba tare da yace masa komai ba,ya dauka ya duba saiya saki qaramar dariya,ya fuskanci kamar bisa dole yake duk wannan hidimar,kuma yasan dama baiso zuwa kai amaryar ba,shi ya tattagoshi,don haka baice komai ba shima ya fita,ba jimawa ya shigo da ledar magungunan,samir din ya kuma tada motar suka wuce.

“A wacce unguwa zamu saukeki,zamu wuce gia dare na dada yi” lallausar muryarsa ta sauka a kunnenta ta sake haifar mata da kasala,saita lumshe idanu,murya can qasa ta gaya mishi sunan unguwar,tana kallonshi ta gefan ido.

Nutsuwarsa da jan ajinsa sunyi yawa,komai nashi bisa salo me qayatarwa,abinda ya fara fusgarta akanshi kenan tun karon farko.

Dai dai sanda zasu wuce ta wani waje taji amiru ya sako masa hira kan wajen,wanda dukka maganar tasu kan kasuwanci ne,sai tayi fakare tana sauraren yadda muryarsa ke fita da haruffa a jere masu cike da nutsuwa da kamun kai,hakan ya sake dulmiyata cikin wata duniya,har batasan sun shigo unguwar tasu ba,tadai ji amiru na tambayar number gidansunta gaya masa.

“Na gode sosai,Allah ya saka da alkhairi,na gode” ta fada cikin raunanniyar murya,tana wassafa yadda zata samu number dinsa cikin sauqi.

Sai a sannan ya kalleta,ya gyada kai kawai yana kauda fuskarsa,tadan leqa baya kadan tana yiwa Aamiru godiya sannan tayi hanyar gida.

Shigowar kira wayarsa ya sanyashi waiwayawa ya dubi Aamiru

“Pls karbi driving din nan” sai ya fito suna qoqarin musayar sit,yana shiga wani yaro ya fito da hanzari daga cikin gidan,dai dai sanda amiru ke fitowa shima don shiga gidan driver,yana amsa wayar,baiji abinda yaron ke cewa ba,har sai daya gama wayar,dai dai sanda suka dauki hanyar barin unguwar

“Ta aiko a bata phone number din ka zata maka godiya idan ta samu sauqi”

“Kai kuma saika dauka ka bata kenan?” Samir ya tambayi amiru ba tare daya waiwayo ya dubeshi ba,yana qunshe dariya ya amsa masa

“Tunin ma,mukasan inda rana zata fadi,tunda kaine a kasuwa ai gwara a bata,mu mun riga da mun sayar” harara ya balla masa

“Idan ban girgide maka auren ba kace bani bane”

“Tuba nake the giant saraki” ya fada yana daga hannayensa sama alamar surrender,saiyayi qwafa kawai,bai sake ce masa komai ba.

***********Gefanta ta ajiye wayar kana ta miqe tsaye,goye da hannayenta a baya ta soma kai kawo da alamun zuzzurfan tunani.

Wayar landline dake dakinta ta daga kai ta kalla,kana ta isa wajen da hanzari ta zauna daga gefan gadon,ta fara kiran sashen masu aiki.

Bugu biyu aka daga

“Turomin saratu” ta bada umarni sannan ta kife wayar,taci gaba da xama a bakin wayar,har zuwa sanda taji ana knocking qofar bedroom din nata.

Zamanta ta gyara sannan ta bada izinin shigowar,cikin daqiqu kadan matar ta bayyana,kakkaura ce baqa,bata da tsaho sosai,saidai da alamu shekaru sun fara zuwar mata,duk da ba wani masu yawa bane amma tayi qaura daga gurbin quruciya zuwa na manyance.

“Zauna saratu” mummy ta bata umarni tana bin saratun da kallo,saidai abinda ta kirata dominshi har a sannan bataji nutsuwar hakan cikin zuciyarta ba.

Bata saba saka kowa cikin sabgar ba tsahon shekarun data dauka tana gudanar da al’amuranta a sirrance,to a yanzun ma batason ta soma sanya kowa gudun cabewar lamura,duk da cewa saratu amintacciyarta ce,saidai bata sakar mata ragamar komai ba,ta barta ne tasan iyakar abunda taso ita saratun ta sani

Dan tsakin da batasan ya fito ba ta saki,saita dubi saratun

“Jeki abinki” har ta isa qofa tunaninta yakai mata ga yarinyar

“Ki kiramin wannan baquwar me aikin”

“Kaltume?”kai ta gyada

“Eh ita”

“To hajiya” ta amsa mata tana ficewa daga dakin.

Karamar ajiyar zuciya ta saki,bata kaisu shekaru ko wayewa ba,bare aje ga batun wayo ko gogewa da sanin rayuwa ba,hakanan tafiya da itan zai sake zama mata tamkar wani tsani izuwa wani bigire. Kanta ta sake gyadawa tana sake tabbatarwa da kanta hakan yayi.

Daga karatu kaltum din ta shiga bawa jawahir labarin qauyensu,bada labarin a wajen kaltume dai dai yake shawagin ruhinta cikin qauyen,tana jin nishadi har tsakiyar zuciyarta duk sanda zata bawa jawahir labarin,kamar yadda jawahir din labarin ke burgeta,tana jin kalar wata rayuwa ta daban da batasan da wanxuwarta ba.

Dai dai nan saratu ta shiga dakin,ta kuma shaidawa kaltum kiran mummy,gabanta ya fadi,suka hada ido da jawahir,sai jawahir din ta miqe

“Muje na rakaki” kanta ta girgiza

“A’ah….tunda batace kizo ba tabbas ni kadai takeson nazo din,ki zauna kada mummy tayi fushi,yanzu zan dawo” jawahir din batace komai ba har suka fice daga dakin zuwa katafaren sassan mummy,bisa jagorancin saratu.

Tun daga yanayin dakin kaltum ta tabbatar da cewa lallai akwai qatoton bambanci,akwai kuma izza da jin isa bisa ga komai na lamarin hajiya jiddan.

Binta take da kallo tare da qoqarin sake karantarta sanda take tunkaro inda take,duk wani motsi nata da yanayin dabi’unta ta gama karanceshi,tun a farkon xuwanta ta gama gane cewa,bata da rawar kai,yawan surutu ko kuma shishshigi

“Kaltume” mummy ta kirata sanda ta zauna a cure waje daya

“Na’am momi” ta amsa mata a nutse

“Inaso zaki rakani anguwa gobe,ki shirya kamar gobe na safe,banason ki wuce haka,hakanan banason ki gayawa kowa batun zuwa unguwar,ni mutum ce mai son sirri,banason mutum mara sirri kin fahimta ai” kai ta gyada mata,sannan ta bata umarnin tafiya.

Har takai bakin qofa ta kirayi sunanta

“Hatta jawahir banason taji,don ba inda zanje da ita” kai ta gyada tare da ce mata

“To”

*********Goma na safiyar washegari har da mintuna goma sha biyar ne,daya daga cikin motocin dake farfajiyar gidan,wadda take mallakin hajiya jidda aketa zubawa kaya a booth tari guda.

Hamshaqiyar mota ce wadda ta lashi kudade masu yawa kafin ta mallaketa,amma duk wanda zai kalleta koda baisa kudin abun hawa ba yasan motar taci kudinta.

Cikin shiga ta qasaita dake nuna ainihin zallar alfarma da cikar arziqi da dukiyar mutumin da take aura ta fito,tana taku ɗai ɗai tare da qarewa farfajiyar kallo sanda ta tsaya tana jira a bude mata mazauninta.

Daga can wata shiyya dake mahada da sassanshi na gidan shima yake takowa,cikin shigar suit na alfarma ,hannunsa riqe da wani file dake cike da takardu yana budawa daya bayan daya,yana takowa ne cike da sassarfa,gefansa umar ne yake masa wasu bayanai,wanda da alama sun shafi takardun hannunta.

Ita ta fara hangoshi,saita dan gyara tsaiwarta,sam idan zatayi irin wannan tafiyar bata qaunar su hadu kafin fitarta daga gidan,duk kuwa da cewa yawa yawan siyayyar da take fita daga gidan zuwa wancan wajen tana fitowa ne daga aljihunsa.

Rufe file din yayi ya miqawa umar kana ya masa magana kadan,sai umar din ya juya zuwa mota,shi kuma ya qaraso inda take tsaye

“Barka da safiya” kamar ko yaushe,cikin kallon dake nuna qauna da kulawa tace

“Barka kadai my son….za’a fita kenan”

“In sha Allah” ya amsa mata yana kallon kayan da ake zubawa a booth din motar,kayane masu yawan gaske na amfanin yau da kullum,tun kafin ya gama mallakar hankalinsa take zuba irin wadan nan kayan take fita dasu zuwa duba gidan marayu,wannan tshohuwar dabi’arta ce da kaf gidan sunsan da ita.

Yana tsaye harta shiga motar,shi da kansa ya rufe mata murfin motar,yana jin kyautatawarta data shaida masa zata fita ne da kaltume,hakan yana shaida masa cewa ta soma sakewa dasu cikin gidan kamar yadda yakeso.

Duka duka tafiyar bata wuce ta minti arba’in ba suka isa wata unguwa,akwai gine gine wanda suke a tsare,saida akwai qarancin zirga zirgar jama’a qwarai da gaske.

Qofar wata babbar katanga mai tsaho motar tasu ta tsaya,sai a sannan kaltume dake zaune gaban motar ta daga kanta tana bin katangar da kallo,tun shigarta motar bata motsa ba,saboda tsoro rashin sabo da kuma hada muhalli da mommyn karo na farko,duk da cewa tunda suka shiga motar mummyn ke waya,wadda ko abu guda daya kaltumen bata fahimta ba cikin hirar da takeyi din.

Babu wanda ya tanka ko ya motsa,har zuwa sanda mummyn ta daga wayar,ta kuma shaida isowarta,ba’a rufa mintuna biyu ba wani kakkauran mutum dogo baqi ya fito ta qaramar qofar gate din,fuskarta dauke da madaukakiyar fara’a ya qaraso dab da motar,sannan ya fara bawa dirvern mummyn wucewa zuwa qofar da zuwa yanzu aka wangale mata ita.

A hankali ta zuro qofafunta da suka fara rawa.

,kallon farko ta yiwa asibitin ta tabbatar asibitin masu rangwamen hankaline,duba da yadda suke ko ina bajaja a farfajiyar asibitin,kowa yana sharafin gabansa.

Tunda take bata taba tsintar kanta a muhalli makamancin wannan ba,hasalima ita din mugun tsoron mahaukaci gareta,jakar mummy dake hannunta da qyar take ruquwa,ji take kamar ta kama mummyn ta ruqunqumeta amma tasan batayi wannan isar ba,ta dubu drivern mummyn da matashin da suka taho tare,wanda sai da aka jirayi zuwansa daga wani waje da batasan ina bane sannan suka taho,saita fuskanci hankalinsu kwance yake,babu wani tsoro ko fargaba irin nata tattare dasu.

Cikin mintuna qalilan wasu mutane maza biyu mace daya suka iskosu,sunfi kama da likitoci dake kula da marasa lafiyan saboda yanayin suturar jikinsu,cikin wani irin girmamawa suka tarbi mummyn.

Sakin ajiyar zuciya kaltume tayi sanda taga sun durfafi wata qofa da babu yawan jama’a sosai,tsoron dake cike fal a zuciyarta ya ragu,don tayi tsammanin zasu kewaye marasa lafiyan ne kamar yadda tasan anayi idan mutum yakaiwa marasa lafiya ziyara.

Babban office ne me kyau ba laifi,su suka jawa mummy kujera daya don ta zauna,saita girgiza kanta

“Ai banga ta zama ba,muje na ganta tukunna,inga in akwai matsala sai a san matakin dauka tunda wuri”

“To ba laifi,amma yau da wannan zaku shiga?” Ma’aikacin daya tarosu ya fada yana nuna kaltume dake tsaye riqe da jakar mummyn da hannu,sai a sannan ta waiwayo ta dubu kaltume,batasan tana biye da ita ba da alama

“Ki koma can wajensu alasan ki zauna” ta bata umarni,saita gyada kai tana hade yawun tsoro,ta juya zuwa wajen motar tasu tana addu’ar ta isa lpy.

Qofar motar ta bude ta shiga saboda tsoro,tana bin harabar asibitin da kallo cikin nazari,wato ta karanci wani abu a rayuwa,shi mai lafiya duk inda yake dan gata ne,duk wanda Allah ya bawa kyautar lafiya ya gode masa,babu wata ni’ima data kai ta lpy dadi,gasu dai wadan nan bayin Allah,Allah ya amshe ni’imar hankali daga garesu qila badon sun masa wani laifi ba,sai don haka nan yaga damar ganinsu……

Tunaninta ya yanke da sautin qarar wayar mummy data bari cikin motar,kafin tayi wani motsi alasan ya zuro da kansa yana duban wayar

“Ko zaki dauki wayar ki miqawa hajiya?, professor ne yake kira,kuma fada take a irin haka idan ya kira ba’a kai mata ba,shima kuma bayaso ya kira ba’a dauka din ba” tabbas tsoro takeji sosai,amma babu yadda ta iya tunda ya buqaci hakan,saita ajjiye jakar hannunta,tasa hannu biyu ya dauka wayar tana kallon irin kyan da wayar ke dashi,duk da hankalinta ba’a nan yake ba,ta buda murfin motar ta zura qafafunta ta fito.

Tana tafe tana waige hara ta dawo office din,saidai wayam babu kowa,sai wani mutum guda dake tsaye yana rubuce rubuce cikin wani file.

Muryarta nadan rawa alamun tsoro da rashin sabo take tambayarsa mommyn.

“Tare kuke?” Ya tambayeta bayan ya kafeta da idanu,kai ta gyada,kamar bazaiyi magana ba,sai kuma ya nuna mata wata siriryar qofa hanya

“Ki shiga ta nan,daki na can qarshe hannun hagunki” kai ta gyada masa sannan ta nufi qofar.

Tsoro ne sosai ya kamata saboda yanayin duhun wajen daya bambanta dana waje,duk da haka bata fasa saka kai ba,saboda yadda wayar dake hannunta kiran yaketa shigowa yana yankewa,a haka harta isa dakin daya ce mata,saidai kuma qofar kamar a kulle take,sai qaramar taga dake bude,ta yanke shawarar ta leqa ta nan ko wani ta bawa ya miqawa mommyn wayar…….

*_KO KUNSAN DA YAWANMU LAIFUKAN DA MUKA YIWA ‘YAN UWANMU KE HANKADAMU WUTAR JAHANNAMA?_*

*_ZAGIN MUSULMI,CIN ZARAFIN MUSULMI,WULAQANTA MUSU,CIN HAQQIN MUSULMI,TOZARTA MUSULMI,YI DA MUTUM,RASHIN BASHI HAQQINSA NA KARE HAQQINSA DAKE KANKA,WATO KARE MUTUNCINSA DA ADDININSA,DA YAWA ABINDA MUKE RAINAWA MUKE GANIN BAIKAI YA KAWO BA,YA KUMA ZAMA JININ JIKINMU SHIKE KAIMU WUTA,Allah ka bamu dacewa_* 👏🏽👏🏽👏🏽👏🏽

*_WAIWAYE……ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau’in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI…..yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI’AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR…ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button