Sponsored Links
Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 15

Sponsored Links

Page 15

Qwayar idanunsa ya daga kan takardun yana dubanta sanda take shigowa dauke da kwanukan,ya sauke boyayyar ajiyar zuciya yana qarewa dressing dinta kallo,baisan sai Yaushe hafsat zata canza ba,baisan me zaiyi da zai canza ta ba,duka wani burinsa a kanta ya dade da tarwatsewa,wani lokaci sai ya dinga gani kamar ba hafsat dinsa ba.

A gabansa ta ajjiye abincin sannan ta koma gefansa ta zauna tana maida idanunta ga takardun da yake dubawar shima

“Ga abincin” ya daga takarda daya yana juya bayanta ba tare da ya kalleta ba

“Shi zai zubamin kansa da kansa?” Jim ta danyi sannan ta tabe baki,wani lokaci ya fiya jin kai da izza,hutsu ne na gaske,sai yayi kamar ya sauko ko ya canza sai kuma ya sake hargitse mata,ita kanta tana sarawa kanta yanda take haqurin zama dashi,sai ta sauka tana zuba masa ta ajiiye gabansa tana komawa mazauninta.

Sai daya qara minti kusan biyar sannan ya ajjiye takardun ya sauko,tana ta satar kallonsa,tana son masa maganar motarta data fara bata matsala tana shakka,dazun sun rabu ba ta dadi ba,yanzun kuma taga yana hada kaya,ta tabbatar kayan tafiya KD ne,wala’alla ya haqura ne ya janye qudurinsa?,idan hakanne ita tafi mata nono fari,saidai tafi kowa sani,shurunsa bashi da sauqi,mataki ne zai dauka daga baya ta ruwan sanyi,koma dai yaya ne idan har ya janye din shikenan its buqatarta ta biya,a hakan ta daure dai tayi gyaran murya kadan.

Ya jita sarai yayi kamar baiji ba,sai data gaji da gyaran muryarta sannan ta magantu

“Wai kayan tafiyar kake hadawa?”

“sune” ya bata amsa a taqaice

“Allah yasa a koma a sa’a,mudin ko weekend ma dinga zuwar maka,kaga bazai shafi karatun mimi ba” ta fada har qasan ranta tana jin ta fada ne kawai don ta wanke kanta,bawai don zata iya wannan jigilar ba

“Yayi” ya amsa mata a taqaice kawai,don baison doguwar magana.

Shuru ya sake ratsa tsakani,tana ta tauna yadda zata gaya masa zancan motar,don so take kafin bikin qawarta din nan ya sauya mata,taje a hajiyar ta da sabuwar mota,ba wannan qaramar motar da kowa ya sanya da ita ba

“Nace ba” ta fada a darare

“Uhmmm,kikace me?”

“don Allah ba…..abban mimi motata…wallahi matsala take ta bani,sannan ma tayi tsufa da yawa,kada kunya na dinga shigarta bayan mutane sunsan matsayinka” shuru kamar bazai amsata ba,yaci gaba da cin abincinsa,yayin data kasa ta tsare ta kafeshi da idanu tana jiran ta cewarsa,har sai data gaji da jiran amsa ta sake magantuwa

“Bakace komai ba abban mimi” plate din hannunsa ya ajjiye,ya waiwayo ya dubeta

“Bani da kudi a yanzu” fuska ta dan bata

“Abban mimi baka da kudi fa kake fada?,ko allowance dinka ya isa ka canza min babbar mota bama qarama bafa”

“Kudina a yanzun bana canza mota bane,ina da abu me muhimmanci da ya fishi” daga haka ya miqe yaci gaba da aikinsa hankali kwance,cikin bacin rai taci gaba da zama wajen,tana ta baqin rai ita kadai,zantukan yayarta take tunawa

“Kada fa kiga mijina ya canzamin mota ki dauka kema wannan mijin naki me ra’ayin riqau zai canza miki mota ta sauqi,mafi kyau ki haqura da maganar zancan mota yanzun,nasan halinsa sarai ba canza mikin zaiyi ba” a sannan baki ta tabe tana dan kada qafarta

“Kiyi haquri umman walida,amma banjin yadda abbas ke kashemin kudi da yadda yakeji dani kina samun haka wajen baban walida…..”

“Ke kinga dakata,karki gayamin baqa mana” ta dakatar da ita,duk da cikin wasa suke maganar

“Kowa ya san abbas yana jiqaki,amma kuma duk cikinmu babu wadda juya miji ke mata wahala irinki koba haka bane?” Ta fada tana duban sauran sisters dinta dake wajen,dariya suka danyi suna gasgata maganar maman walida din da suke kira da anty balaraba,wannan ya hasalata,ta kuma ci musu alwashin kawo sabuwar mota don ta nuna musu ta isa da mijinta kamar kowacce mace.

Har yaci qarfin aikinsa tana zaune a wajen bata sake tofa tata ba,ta tattara fushin duniya ta azama ranta,me yasa koda yaushe abbas din sai ya kunyatata yakejin dadi?,kafin ya kammala aikin ta tattare tabar masa wajen,sai kawai tayi komawarta sashenta,tayi kwanciyarta acan.

Shima daya gama komai kwanciyarsa yayi,bai wani tsaya bi ta kanta ba,bayason rainin wayo da kuma rashin hankali,ta kuma fi kowa sani abinda baya tolerating kenan.

Washegari haka tayita kumbure kumburenta,sai ya nuna baisan ma abinda takeyi ba,ayi masa laifi kuma a fishi fushi?,yayita hidimarsa da yaransa,yana kuma yin breakfast ya shirya zai fita,mimi ta maqale masa sai ta bishi,ya kaita gidan hajiya,hafsat din nata danqara masa mata harara amma yarinyar batasan tana yi ba,ya shiga dakinsu ya shiryata da kyau cikin sabbin kayanta dake danqare a cupboard ba’a sanya musu,baisan uban me takeyi da kayan ba,yasan dai wani lokaci takan diba ta rabar,duk cikin fariya da alfaharin shi din wuyansa ya isa yankan da yake danqaro musu suttura ya ajjiye.

Yana fita ta bishi da tsaki ta kuma miqe abinta saman doguwar kujera tana gunaguni,duk yadda take sonshi yana sanyawa yana fita a ranta gaba daya,bata isa ta sashi yayi abu ba sai abinda yayi niyya ya kuma tsarama kansa,kallo ta kunna abinta tana daga kwance,nawwara da yau suka samu albarkar wanka tun safe tana ta kaikawo tana wasanta qasan carfet,har bacci ya dauketa ta bingire a nan.

Har biyu ta buga tana kwance tana kallo bata da niyyar tashi ta kintsa gidan,sai da taji sallama daga qofar falo sannan ta miqe tana sauke qafafunta qasa.

“Anty ummee,ni banma dauki murya ba wallahi”

“Ina zaki dauka kin tasa tv a gaba” ta fadi tana duqawa ta dauke nawwara daga qasa ta maidata saman kujera sannan ta zauna daga gefanta tana cewa

“Yanzun da banzo ba a qasa zaki barta har tayi barcinta ta tashi” baki ta tabe,bacin ranta da ya dan lafa yana motsa mata

“Hmmm,a qufule nake anty ummee,ubanta yaja mata,shi ya qunsan takaici”

“Ke kam damuwarki da abbas bata qarewa,gashi dai baki rasa komai ba amma ko yaushe cikin complain?”

“Na rasa ya zanyi dashi anty ummee,dan bada umarnin nan da mata kewa miji ni bansanshi ba” baki ta tabe tana jingina sosai da kujera

“Ke kikaso hafsa” bata motsa daga wajen ba ta zayyanewa anty ummee din komai,itace wadda take bi a dakinsu,uwarsu daya ubansu daya,sai data gama tas sannan ta dubeta

“A cikin banza ma ke banza ce wallahi hafsat,ke ko asiri kike fa saikin hada da kissa da kisisina yake ci maka yadda kakeso,ke dan makircin nan na mata ma ace baki iya ba?,ko da yake ko an doraki ma sauka kike” ta qarashe maganar tana yaada kanta gefe cike da takaicin ‘yar uwartata.

Matsowa tayi sosai kusa da ita

“Zanyi wallahi anty ummeee” sai data qare mata kallo sannan ta zauna sosai tace da ita

“Ki tattara kayanki ki bishi kaduna kamar yadda yakeso,yaran idan ta kama ko gida ko hannun hajiyarsa basai ki barsu ba?,bama mimi bace ita kadai?,idan kuka tafi can daga ke saishi,ba ‘yan uwansa akusa ba ‘yan sanya idanu,Allah ne kadai yasan nawa zaki tatsa daga jikinsa,masu aikin damarar nan fa ba qaramin iya soyayya sukayi ba,amma ke gaba daya komai naki a rikice?ki bishi ki kwantar da kai,dadin yadda kika faranta masa ma wallahi baisan sanda zai sauya miki motar ba babu wanda yaji ba wanda ya gani” Fuska ta bata,don ta dauka wata mafitar zata bata ba wannan ba,sai itama anty ummee din ta zuba mata idanu tana dubanta

“Ba zakije ba kenan?” Cikin tsuke fuska tace

“Ni anty ummee,kaduna fa wa na sani wa ya sanni?”

“To ai shikenan saikiyita zama bauchi ki tsanana uwar da zaki tsinana” ta fada tana buga cinya. Shuru tayi na wasu sakanni tana nazari,yayin da anty ummee ke qarewa qawataccen falon nata kallo yadda ta barshi komai a zaune da duwawunsa,babu tsari bare kintsi

“Shikenan anty ummee,an gwada aiki da shawarar taki,zanje”

“Yadaifi miki” ta bata amsa sannan ta maido dubanta kanta

“Yanzu kika tashi a barci ne wai?” Kai ta girgiza tana dubanta

“A’ah,me kike gani?”

“Bakiji bashi bashin da jikinki yakeyi ba?,sannan wannan uwar bolar da kika barwa falonki ta mece?” Shinshina jikinta ta soma yi,sannan ta bata fuska,don ita bataji komai ba

“Ni ba abinda jikina yakeyi,hancinki ne dai,falo kuma wallahi yara ne suka bata su da ubansu kafin su fita,don jiya da daddare fes na shareshi kafin na kwanta,yanzu kuma ina shirin tashi na sake gyarawa kika shigo”

“Allah ya sawwaqe” kawai tace da ita,tasan halinta ba yau ba ba jiya ba,koda ta tsaya gaya mata qarancin tsaftarta ma uzurin yara zata yita kawo mata,kamar ita tafi kowa haihuwa a duniya.

Suna taba hira tana gyara falon har ta gama,ta shiga kitchen tana tunanin me zata dafa harda abbas din,don ba zata iya girki biyu ba,tayi yanzu tazo tayi musu na dare?,sai kawai ta dora.taliya da miya,suka wuce uwar dakan hafsat din anty ummee na sake jaddada mata muhimmancin binsa kadunan,tare da dabaru na kissa na yadda zata samu yadda takeso.

Ita ta tayata suka hada kayanta dana yara,don tasan iya wannan sai ya zame mata aikin gabas,cikin kayan nata taga wasu night gown,tasan kudinsu saboda ta gansu wajen wata qawarta kwanaki da tayo order dinsu

“Kai….wadannan nighty din fa?”

“Sunyi kyau ne?” Ta amsata tana zuge qaramar jakar data zuba undies dinsu

“Sosaima,ke bakisan kudinsu ba?” Baki ta tabe

“Bana ce ba gaskiya,shi ya siyomin su kwanaki,ni kuma Allah ya gani bazan iya sanyasu ba,kamar waga kafira,shi yayita wani aiki kamar dan iska dan iska,ko kunyar yaranshi biyu baya ji” galala anty ummee ke kallon hafsat din,idan tayi wani abun kamar batayi karatu ba,ita yanzun just shekara ashirin da takwas zuwa da tara har tayi tsufan da bazatayi gyara ba?, Amma da yake itama kayan takeso sai bata bata shawarar komai ba,ta ninke abinta ta sanya a jaka,ita tasan darajarsu.

Da ta tashi tafiya ta sake tambayar wasu designers turare da ya siyo mata,guda uku ne,guda biyu dubu ashirin da bibbiyu ya siyosu,guda daya dubu talatin,hakanan yake,mayen qamshi ne,shi yasa baya siyan banzan turare,ko su mimi zai siyawa turare baya siya musu na qaramin kudi,bata damu da su ba shi yasa.batasan daraja ko tsadarsu ba,tace ta dauka wanda takeso,ta kuwa dauke dan dubu talatin dana ashirin da biyun guda daya tayi tafiyarta,dama yawa yawan zuwanta gidan abinda ke kawota kenan,don ta qaru da ‘yar uwarta,duk da tana bata shawarwari na gaskiya a wasu lokuttan,rashin daukan shawara ke damun hafsat din,data fara saita tattara ta zubar,tafi ganewa yawan qorafi da kai k’ara.

*_RIGIJI GABJI!_*πŸ”₯πŸ”₯

*_WANI KAYA SAI AMALE_*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

*FITATTUN ZAFAFAN DA BABU NA BIYUNSU*πŸ”₯πŸ”₯

*JERIN GWANON LITATTAFAI ABOKAN TAFIYAR JUNA MASU MABANBANTAN LABARAI DA FASAHA*

*_’YAN BIYAR DIN NAN NE FA_*

*_SARAKAN LABARUN_*

*NISHADI*
*CAKWAKIYA*
*GWAGWARMAYA*
*BARKWANCI*
*TSANTSAR DARASIN RAYUWA*

*TARE DA*

*ZAZZAFAN SALO NA SOYAYYA MAI RIKITA TUNANI DA TSUNDUMA MAI KARATU CIKIN TAFKIN SHAUQI*

*SUN SAKE SHIRYAWA TSAF,DAUKE DA WANI TARAGO MAI CIKE DA LABARAI MASU ZAZZAFAN ZAFI!!!*

*KIN SHIRYA MADAM?*

*MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA*

*DAUD’AR GORA* Billynabdul

*KI KULANI* Missxoxo

*IDON NERA* Mamuhghee

*RUMBUN K’AYA* hafsat rano

*A RUBUCE TAKE* Huguma

*ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN*

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number

09033181070

*MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU*

09166221261

*Yan NIJER πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺzaku tuntubi wannan number*

+227 90 16 59 91

*Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*πŸ™πŸΎπŸ™πŸΎ

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks: huguma*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button