Sponsored Links
Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 92

Sponsored Links

Page 92

Kasa ci gaba tayi da lissafa kudin,idan tayi gaba sai ta dawo baya,dole ta zube kudin tana jin kamar ana sukar zuciyarta da mashi,ta miqe tana gyara daurin zaninta da dan qaramin cikinta wanda ya fara fitowa kadan,duk da duka duka bai wuce wata uku ba,amma saboda tana da tumbi har ya fara bayyana kansa.

Tana doso su tana qare musu kallo,dukkansu daga shi har ita sun canza,kamar wadanda ke rayuwa a wajen nigeria ba

“Hafsatu kina me?,kina me kika zauna kina gadin gida?,kina meye kika zauna?” Zuciyarta ta fara raya mata,take taji ranta yayi mugun baci,kamar ma kada ta isa inda suke,tunda tun tsaiwarsu babu wanda ya fahimci wanzuwarta a wajen.

“Sannu da zuwa” ta fada ciki ciki,qamshin turaren widad wadda ta tsaya daura da ita na cika mata hanci yana kuma qara iza wutar kishinta a zuciyarta.

Waiwayawa yayi ya dubeta,har ya daga hannu zaiyi welcoming nata kamar yadda suka saba da widad,sai kuma ya tuna yanzun zata ce yara,ko ta canzawa abun akala,yayi qoqarin sakin qaramin murmushi yana kallon yadda ta canza,cikin tun baiyi nisa ba ya fara birkitata

“Sannu mom mimi,ya gida ya jikin?” Ya tambayeta,duk da kullum sai ya kira yaji jikin nata

“Alhmdlh” ta furta tana qoqarin saisaita kanta,saboda wani mugun muzanta da taji tayi tsaiwar da tayi kusa da widad din,ta glass din motar da suke tsayen take satar kallon mugun tazarar banbancin dake tsakaninsu da ita,saita zama kamar wata mai aikin gidan,don haka ta janye jikinta a dabarance zuwa gefe sanda widad din ke gaidata,gaisuwar data qona mata rai,don duka hankalinta nakan mimi tana janta da wass,ta amsa mata ciki ciki.

Motar ya rufe yana ci gaba da riqon nawwara a hannunsa,ya juya zuwa sassansa yana yiwa naawara waqar da ya saba yi mata hafsat din tabi bayansa da sauri

“Uncle” widad tayi kiransa da narkakkiyar muryarta,ba abbas da aka kira sunan shi ba,hatta da hafsat sai da ta tsaya cak,yaji kiran har jikinsa duk kuwa da ya saba,amma yau sai yaji kamar muryarta ta qara zaqi

“Kayana please uncle,nagaji part dina zan shiga na huta”

“Hutu” hafsat ta fada a ranta

“Bai kamata acena qyale ta har tana samun damar hutawa cikin gidan nan ba”hafsat din ta fada a ranta,batasan ya akayi ta barta harta ajjiye dukka wani aiki da take mata ba

“Munyi haka ne dake?” Ya fada yana narke mata shima da salon da ita ta koya masa,sai hafsat din ta daga kai da sauri ta kalleshi cike da mamaki,abbas din ke abu kamar wani qaramin yaro?.

Baisan me akeyi ba,don idanunsa na ga widad

“Alqawari ne zan cika Allah uncle” ta fada tana maqale kafada

“Alright” ya amsa mata yana miqawa hafsat nawwara da nufin ta riqeta

“Ajjiyeta mana” ta fadi cikin zafin zuciya, ganin yadda ita yakewa maganar,amma duka hankalinsa na kan widad din,baice komai ba ya juya da nawwara a kafadarsa ya daukar mata luggage din yana biye da ita a baya har zuwa sassanta.

Da idanu ta rakasu,wai me yake faruwa ne?, yaranta ma farinciki suke da zuwan yarinyar ne?,ga wani abu me girma data lura yana gilmawa cikin idanuwansu shi da ita.

Ko kafin ya dawo tuni ta tsufa cikin falonsa,tunani yayi mata katutu,koda ya shigo falon ta daga kai ta dubeshi sai taji gaba daya ta raina kanta,ga laulayi daya sanyata ta kwantsame ta fita hayyacinta,gefe guda rashin gyaran da bata daukeshi a bakin komai ba shima ya taka rawa wajen lalacewar tata.

Kusan yinin ranar cikin qunci ta yishi,tana aikace aikacen da ba kasafai ta fiya yinsu ba sai abbas din yazo tana fama da qunci,itakam widad koda ta isa sashenta zagewa tayi ta gyarash fes,yaran na biye da ita har ta gama,ta kama yaran bisa radin kanta tayi musu wanka,tana jin dadin yadda yaran ke qaunarta,a nan falonta ta barsu bayan ta dora aninci mai sauqi,ta shiga itama ta sake wanka.

A gaban madubi ta tsaya daure da towel tana kallon kanta,ko ina na jikinta ya fara cika,abinda yaketa bata mamaki kenan,hasken data qara ya ninka nata nada,tasan bata canza mai ko sabulun wanka ba bare tace ko sune suka saka,don kanta ta gaji da kallon kan nata,bata kuma gano dalilin wannan canjin ba saita tabe baki kawai taja manta ta fara shafawa.

Hafsat din na gyaran sashen shi kuma yana gyaran closet dinsa,duk da yasan zaiyi wahala gobe widad din bata gyara ta ba,amma kuma yana tausayinta,yana ganin kamar aikin yana mata yawa,don sanitation irin wanda yakeso take a sassan nasa bayan hafsat ta gama jiqa jiqarta.

Baisan ma ta gama ta fice ba sai daya gama wanka yana neman wasu qananun kaya nashi,ya tuna suna cikin akwatin widad din,dole ya dora jallabiyya saman towel din dake daure a qugunsa ya wuce sassan nata don ya ciro kayan.

A falo ya tambayi su mimi antynsu,sukace tana ciki,ya wucesu bayan ya sake canza musu channel zuwa mbc 3.

Sanda ya buda qofar dakin nata ta zame towel dinta tana saka brassiere,tsaf ya qare mata kallo ta cikin mudubin yana jin numfashinsa yana sauyawa,don komai ya fito masa muraran,komai na widad din sake daukan hankalinsa yakeyi kowacce rana,sai yaji ya kwadaitu da son jin duminta cikin jikinsa,don haka ya taka a hankali har ya isa gareta,yayi caraf ya riqe towel din sannan ya fincikota a tausashe zuwa jikinsa.

Tare suka sauke ajiyar zuciya shi da ita,ya zaci zata nema qwacewa ko zame jikinta,sai yaji tayi luf cikin qirjinsa,qamshin sabulun wankansa yana mata dadi sosai har zuciyarta,wannan ya bashi damar aiwatar da abinda zuciyarsa ke kwadaita masa hankali kwance,har sai da taji yana niyyar zarmewa sannan ta zare jikinta tana tuna masa su mimi dake parlor.

Da jirkitattun idanunsa da suka sauya launi yake dubanta tare da tayata daura towel dinta da ya zame,daurin gaba yayi mata,ya cukuikuye towel din a tsakiyar qirjinta yana duban wajen,sai tasa hannunta guda daya ta rufe,daya hannun kuma ta jawo hijab dinta dake gefe ta soma yunqurin sakawa,ya saki siririyar dariya yana cewa

“Please mana,minti kadan fa zan dan kalla saiki rufe”. Ya soma kicin kicin qwacewa ita kuma tana nade kanta a ciki tana dariya,da wannan har ta sake komawa jikinsa.

Ganin aikin take kamar zai kasheta,ga laulayi gaba daya jikinta babu cikakken qwari,don haka ta tsame hannunta daga yankan salad da takeyi ta nufo sassan widad din.

Tun a hanya take kwatanta da yadda zata fuskanceta do kada ma taga sassauci a fuskarta ta nema kawo mata wargi.

Bin ko ina na falon ta dinga yi da kallo,ko ina fes kamar yadda abbas yakeso,ya koya mata kenan,tsinanniyar tsaftar nan tasa,taja mugun tsaki tana tambayar su mimi widad din

“Tana daki,yanzu abba ya shiga kiranta” wata mummunar faduwa gabanta yayi,abbas kuma?,me yakeyi a dakin?,bayan yau din kwananta ne?,ta gama masa wahala daga kaucewarta har ya baro sassan?,cikin mamaki zafin zuciya da kuma kishi ta doshi dakin,batayi wata wata ba ta murza handle din ta tura da qarfi ta shiga,shigar da batayi mata dadi ba sam,shigar da sai da taji kamar kanta zai tarwatse,abbas dinta widad din kwance a jikinsa suna qyalqyala dariya,duk sun yiwa shimfidar gadonta squeezing.

Tare suka daga kai suka dubeta,saita kasa jurar ganinsu ta soma girgiza kai,ga widad kuwa mo gezau batayi ba,tadai ci gaba da janye hijab dinta daga hannunsa tana cewa

“Laaa,mummyn mimi wallahi bamuji sallamarki ba,uncle ne,yana nan yana…….” Ido ta runtse da sauri taja baya,ta kuma buga qofar da kyau,gudu gudu sauri sauri ta fice daga sassan kuka yana kubce mata.

“Yana nan yana me uncle din?” Abbas ya fadi yana jefa mata hararar tsokana,can qasan ransa a bace na yadda ta kutso mata har bedroom dinta ba tare da sallama ko neman izini ba, dariya ta qyalqyale dashi,duk.da qasan ranta taji haushi,ta riga ta saba da dabi’ar yin sallama kafin ta shiga waje,amma ita hafsat din qatuwa da ita batasan tayi ba?

“Ba komai” ta amsa masa tana dariya,saiya tsaya kawai yana kallonta yanajin wani farinciki yana wanzuwa cikin rayuwarsa,tsahon seconds sannan ya miqe yayi kissing goshinta,ya qarasa akwatin ya dauki kayansa yana tsokanarta ya fito.

Yana dosar dakinsa ya jiyo sautin kukanta,ya girgiza kai kawai yanajin takaicin hafsat din,yana saka kansa cikin dakin ta daga kai tana dubansa,idanunta sharkaf da hawaye,tasan halinsa sarai,miskili ne na qin qarawa yaso,ganin yayi.kamar.bai ganta ba ya nufi dressing mirror dinsa saita buda baki a zafafe

“Na gode,na gode sosai da cin fuskar daka yimin,yau kacal amma harka fara satar kwana na kana kai mata?” Kamar bazai.amsata ba har ya gama fesa turarensa bayan ya fidda jallabiyyar jikinsa,sai a sannan taga towel kawai yake daure dashi, zuciyarta ta sake fusata qwarai,ya juyo ya dubeta

“Ina kwanan yake?,ina cewa rana ce yanzu?,da kika shiga kuma wani abun kikaga munayi?” Tambayoyin nasa sai taji gaba daya na rainin wayo ne

“Kayi laifi amma kana yin kamar bakayi komai.ba abban mimi?” Ta fadi tana nuna qirjinta da yatsanta,zare towel din ya qarasa yi yana sanya kayansa,sai da ya gama tsaf har sannan tana zaune tana dubansa,ya dawo gabanta ya tsugunna yana kallon qwayar idonta,ya sauke idanunsa zuwa ga hannuwanta da farcenta ya dan soma taruwa,ga ‘yan qananun datti nan sun fara shiga qasan farcen,sun nuna kansu ne saboda yadda hannun da farcen suka kode dalilin rashin digon lalle ko kadan a jikinsu,abinda yafi tsana kenan ya gani,shi yasa sanda yake bauchi da kansa yake daukarta ya kaita gidan qunshu ya ajiyeta ya kuma bar mata kudi masu dan yawa akan ayi mata,amma da wahala idan ya kaita sau goma ayi sau uku saita kawo uzuri tace layi yayi yawa bata samu ba,wani lokaci ma kafin yazo daukarta ta hayo motar haya ta dawo gida,yasan kuma tabbas kudinta kawai take karbewa daga wajen mai qunshin,a yanzun yanason kama hannun nata amma yanajin wani iri,tun daga ranar da widad ta fuskanci me son lalle ne bata sake zama hannunta haka ba,hasalima bata rabo da sargen da take sawa yatsunta idan bata samu lallen ba,abinka da farar fata,mugun kyau yakeyi mata,wani zubin har tukuici sai ya ajjiye mata.

Duk da haka ya kama yatsun hannun nata yadan ja kadan yadda zata fahimci zancan yace

“Dani dake waye yafi wani laifi?,Allah da kansa fa cikin qur’ani yake cewa ‘yaku wadanda kukayi imani,kada ku shiga gidajen da ba naku ba har sai kun nemi izini kunyi sallama akan ahalin gidan,wannan shine mafi alkhairi a gareku,idan ma baku samu kowa ba a cikinsu gidajen kada ku shiga har sai an muku izini,idan kuma akace ku koma ku koma’ kinga anan kin sabawa koyarwar qur’ani da sunnah” tunda ya fara maganar ta zuba masa ido tana hawaye,yau gidanta ake cewa ba zata shiga duk inda taso ba saita nema izini saboda ya ajjiye wata

“Yanzu abbas gidana kake kafamin wadan nan sharuddan a kansa?”

“Ya salam”ya fada yana lumshe ido takaici yana kamashi,wacce irin qwaqwalwa take da ita,yana gaya mata Allah da annabi tana gaya masa molanka da son zuciyarta, kafin ya buda idanun ta dora

“A jikinka fa na sameta,ranar kwana na,kaci amanata kanason juya laifin kaina,wallahi sai yanzu na gane dalilin da ya sanya yarinyar nan ta fara rainani,kana raba mana kwana,kana duk abinda kakeyi dani da ita,tana shirme kana biye mata shi yasa take kallon kowa a banza…..”. Tsam ys miqe

“Excuse me”ya fada a taqaice yana rabata ya wuce,don bazai iya ci gaba da daukar rainin hankalinta ba,kamar yadda ya fuskanci gaba daya ba zata taba gane abinda yake nufi ba.

Gaba daya ranar ta bata ta da kuka da takaici,taji a ranta ta riga ta gama yin sake,saidai har yanzu akwai sauran dama da zata nunawa yarinyar ita ba kanwar lasa bace.[3/21, 3:59 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button