Dabi’ar Zuciya 11
11
A mararrabar hanya suka rabu da nasirun,shi yabi hanyar da zata sadashi da gonakinsu,ita kuma tabi hanyar da zata kaita gidan matar da zata kaiwa kudin kabewa.
Tun daga nesa ta hangi sashen da tsohuwar makarantarsu take da al’umma a tsaitsaye,wasu manyan lafiyayyun kyawawan motoci guda uku fake a gefe,saita dauke kanta ta wuce zuwa gidan mari mai Saida kayan miya,ta shiga suka gama magana ta bata kudin ta fito.
Idanunta sake sauka yayi ta gefan makarantar,har yanzun mutane ne a tsaye a wajen suna zagaya makarantar,zuwa yanzu jama’ar dake cika wajen sun dadu,don an samu dadin ‘yan kallo,wadanda kallon motocin dake wajen da kuma aikin da taga kamar ana danyi ya kawo,cikin masu kallon kuwa harda manya.
Baki ta tabe tana dannjan tsaki,mutane suna bata mamaki,komai qanqantar abu abun kallo ne a wajensu
“yaya”taji kamar muryar bilal tana qwalla mata kira,saita dakata da tafiyar sannan ya waiwaya.
Bilal dinne kuwa,ta zuba masa idanu tana jiran qarasowarshi,kamar ko yaushe fututu dashi,da wahala kaga bila din tsatsaf dashi,idan ba ranaku irin na juma’a ba ko kuma ranakun idi, saboda koda yaushe cikin aikin wahala da neman kudi yake.
“kai kuma me kakeyi a nan?,Allah dai yasa ba fada ake ba”dariya ya danyi
“ni bana tsokana ai yaya saidai a tsokaneni….ba fada ake ba,wasu ne wai suka turo a sake ginin makarantar me tafasa,sannan a gina mata masallaci babba nayin sallah,shine na maqale a wajen ko Alla zaisa a sakani cikin masu aikin ginin”tsaiwa tayi tana kallonsa sosai,kamar kowanne lokaci shi.bilal din tunaninsa daban,ba kasafai yake hango wani abu ba,saidai shi a hango masa
“kai wato samun aiki ne ya dameka,bama ka tunanin shiga sahun daliban da za’a dauka ida an gama gyaran makarantar ko?”dariya ya danyi
“karatu fa yaya?….tabdi ba yanzu ba”
“au bazakayi ba kenan”sai yayi murmushi
“zanyi amma ba yanzu ba”
“Allah ya shiryeka”ta fada tana yin gaba,ya biyota a baya yana ci gaba da bata labarin irin mutanen da sukazo wajen,’yan birni sosai ‘yan gayu,kowa sai kallonsu yake,harda cewa
“yaya motarsu kamar madubi,idan ka tsaya a gabanta Allah har kanka kana iya gani,da guduwa fa aka dinga yi,kowa yana tsoron kada ya bace”murmushi ta saki kawai
“naji,kaidai ka kula,ba ruwanka da kowa,ka kiyaye”
“ni dama yaya meye nawa?,kawai aiki nake nema”shiya rakata har gida suna hira,sannan ya zauna yaci abinci ya sake ficewa.
Da yammacin ranar aka kama habiba,kuma shima abun ya qayatar kamar dai jiyan,komai a tsare akayi lafiya aka gama lafiya,saidai rashin ganin mutum biyu ya baiwa kaltum mamaki qwarai da gaske inna da kuma suwaiba,babu su babau labarinsu har akayi aka gama.
Washegari akayi wuni da daurin aure,wata washegaein kuma aka dauki habiba zuwa gidanta,ranar sun sha kuka dukkaninsu,sai kaltum ta dinga jin kadaici sosai,ta dinga jinta wani iri tun a ranar,ta tabbatar wani sabon zaman ke sake fuskantota,wanda batasan da wacce fuska zaizo mata ba,ta dawo gida jiki a sanyaye bayan sun baro habiba da tsohuwar da zata zauna mata kafin gobe suje ayi mata budar kai.
Washegari da safe suna tsakar gida suna karyawa saiga sallamar inna,abinda ya bawa dukkaninsu mamaki, tare da tambayar kansu dalilin zuwan innar,tunda dai har akaci aka cinye innar bata koda rabo dangar gidan ba,hakanan sisinta da sunan gudunmawa ga bikin jikarta bai ratsa hannun umman ba,sai yau a rana ta qarshe da za’a gama komai kuma sai innar tazo?.
Daga umma altine,yakumbo indo kowa fuskarsa cike da mamaki take,hakanan babu watq cikakkiyar fara’a jin dadi ko walwala suka tarbeta,saimw umman ce daya yunqura cikinnzallae farinciki ta shimfida mata sabuwar tabarma wadda ta habiban ce da aka manta ba’a tafi da ita ba,yau za’a tafi da ita,jikin umma na rawa tasa aka zuba mata kunu da qosai da sukayi aka aje ma innar,sannan ta tsugunna gefanta tana gaidata,bayan umma altine da yakumbo indo sun gaidata,sai kaltum wadda ke zaune gefe,ta zubawa sarautar Allah idanu,ta kasa ta tsare taqi tashi,don itama tana son taji dame innar taxo.
Badai tace komai ba har aka gama gaisawar,hakanan bataqi jan kwanon kunu da qosai ba ta fara kaiwa baka,har zuwa lokacin da masu tafiya suka fara da taruwa.
Tsaf kaltum itama ta shirya cikin daya daga cikin atamfofin da nasuru ya siya mata,wadda ta saka shekaran jiya,yau din sai tayi maimaice,zata shiha dakinsu ta debo ragowar kayan sawar habiba taji innar na cewa
“Wannan saqar tabarmar tayi kyau….irinta naketa nema zan siya ba’a samomin ba”tasan halin innar sarai,don haka saota fasa shiga dakin,ta waiwayo tana cewa
“Kuma gata na ko ina a kasuwar darimi,idan kina so ajjiye kudinki jibi naje da kaina na siyo miki” harara ta balla mata
“Naqi na bayar din,wannan din da kika dawo dominta ita zan dauke dan uwaki,shegiya manna’il lil khairi”baki kaltum ta tabe,sannan tayi gaba,dama tasan abinda innar keso kenan,ita akuwa bataga dalioin da zaia bata kawo komai ba sannan ta dauki wani abu sabo na amarya ta tafi dashi ba,Allah ba zata bar mata ba,saida duk yadda za’ayi ayi.
Tana tsaye bakin window tana fakon innar,har Allah yasa ta tashi zata shiga bayi,da sauri kaltum ta fito,taja tabarmar ta nade tsaf tayi dakinsu da ita,ta daga shimfidarta ta fara shimfida tabarmar daga qasa,sannan ta maida kayan kai,ta yadda babu yadda zaka gani kace tabarmar tana qasan,sannan ta fito tsakar gidan,tana ci gaba da hada abinda take da buqata.
Tana jin sanda innar ta fito tana neman shimfidar tata,neman duniya anata juyayi amma kaltum tayi fir da ita,umma ta kirata taja mata kunnen indai ita ta dauka ta fito da ita amma tace batasan zance ba,daga qarshe ma da innar ta soma zarginta tana antayo mata zagi saita dauka mayafinta ta fice
“Shegiya mai baqin hali,gadon tsiya da talauci,shi yasa gashinan ubanku har yau jiya iyau”haka ta dinga gayaqa kaltum din,darajar ummansu kawai taci ta fita bata tanka mata ba.
Bata dawo cikin gidan ba sai data daidaici lokacin tafiya yayi,ta dawo kuwa a dai dai,don an gama haduwa,an fito da sauran kayan da za’a tafin dasu.
Dai dai sanda ta shigo ta ji inna na fadin
“To zuwaira…..ina kayan garar ne?”muryar umman a tausashe tace
“Babu inna,ba’a samu yi mata ba” haba innar ta kama
“La’ilaha illallahu,yanzu zuwaira garar ma saita gagari yarinya?,haba wannan wanne irin abun kunya ne?,ace kun kasa yiwa yarinya gara fisabilillahi?,yo ko bashi bakwaci kuyi mata ita ba ku fidda ita kunya?,wallahi ba don na riga nazo ba,kuma banason surutu kada ace banzo ba da babu inda zani,haba” tsit wajen yayi,aka koma kallon kallo na mamaki,yayin da umma ta samu waje ta zauna jin yadda mahaifiyarta ke shirin kwance mata zani a kasuwa,yakumbo indo ce ta karba
“Haba inna wannan aikinki ne ai dama a matsayinki na kakar yarinya,ke ya kamata kiyi,basu da suka gama hidimar biki qarfinsu ya qare ba” shalele ce tayi magana,shi yasa innar yin shuru bata sake cewa komai ba baya ga
“To naji uwar iyawa”da haka aka tattaru aka dunguma gidan amarya habiba.
Ba shakka habiban tayi sa’a,don kwana daya tal a gidan yusufa amma sun sameta tare da tarin alkhairansu,ita kanta ‘yar tayin zaman yabonsu take,anan akayi budar kai cikin karamci,aka sake tattarawa kuma biki ya qare akabar amarya ita da angonta,daga nan kowa ya wuce gida,na nesa ma suka je suka kintsa kayansu suka yiwa umma sallama suka wuce,umman nata godiya a garesu saboda tarin karamci zumunci da kuma karar da suka nuna mata.
*_MABUDIN RAYUWA_*
Tun bayan tafiyar habiban sai gidan gaba daya ya rage yi mata dadi,sauqin abun ma dama can ita da umman abokan hira ne,bata mata irin alkunyar nan da akewa dan fari,suna hita sosai,hakanan suna shawara sosai da ita,saidai wani lokacin ba komai zata yi magana da umman a kansa ba,dole akwai buqatar abokin shawara,ada suwaba ce,amma a yanzun suwaiban gaba daya ta yada ita,ta kuma janye jikinta,sosai da kaltum din,kai kace basu taba wata mu’amala ba,tun kaltum din na bibiyarta har itama ta gajibta qyaleta,sai bilal,wanda shi ba mace bane bare,asalima bilal din ba mazauni bane,bama kamar yanzu daya samu aka sanyashi cikin masu aikin ginin sabuwar makarantar da akewa qauyen,sam baya wuni a gida,daya karya da safe ya fice wani lokaci sai dare,ko abincin rana baya waiwaya,kullum ya zauna hirar da yakewa ummansu shine,zasu samu kudi sosai idan suka gama aikin,idan aka bashi kudin umman tashi za siyawa kayan sawa,ya gyara sashen nasu,sannan ya bata jari,itama yaya kaltume zai siya mata kaya ya bata jari,sam babu sunan babansu cikin lissafinsa,koda umma tace babanku fa bilalu?,ka manta dashine?,budar bakinsa sai yace
“Banda shi umma,ba yanzu ba tukunna, Shima idan ya samu baya tunawa damu”kai umman ta kada,har cikin ranta tana jin takaicin wannan abu,Allah ya sani iyakar iyawarta tayi domin ganin sun qaunaci mahaifinsu yadda ya kamata,amma shida hannunsa yake rushe duk wani gini da tayi,saboda a gabansu yake iya cin zarafinta,a gabansu yakeniya barinsu da yunwa,su kansu basu tsira ba,don basa samun dukkan wata kulawa da sauke haqqi irin na uba daga gareshi
“Nima kuwa bazan karbi komai ba kenan bilalu”ta fada umman tana tsareshi da idanu,idon nashi ya zaro
“Saboda me umma?,na miki laifi ne?”saita daga kanta alamun eh sannan tace
“Bilalu indai ba zaka yiwa mahaifinka abu ba nima ba zaka min ba watarana,mahaifinka mahaifinka ne,kome yayi maka,kome ya zama kuwa,don shine silar samuwarka,baka da abinda zaka saka masa dashi,kome zaka bashi,kyautata masa kuwa wajibinka ne bilalu,bakai ba dukkaninku”ta fada tana dubansa shida kaltum,wadda tunda suka fara zancan bata ce komai ba,tana ta cinn tuwonta,wanda dawar ma bilal dinne ya kawota,don ita a wajenta hukuncin bilal yayi mata dai dai,bataga laifin yaron ba ko qanqani,kai kawai ta gyadawa umman tasu tana miqewa da kwanon hannunta,ta isa gaban tukunyar tuwon da aka jiqa da ruwa,wadda ita kadai ce tayi saura ba’a wanke ba,saboda umman bata bari su kwana da wanke wanke,tana jin sanda bilal din yake cewa
“Kiyi haquri umma,indai na bashi zaki karba to zan bashi” zuciyarta cike fal da tausayin bilal din tace
“Allah yayi muku albarka gaba dayanku,ya rabaku da sharrin zamani” ya amsa da amin.
Daga saman dan wani dutse da suke zama suyi wanke wanke kaltum ta zauna kawai tana qarewa umman tasu kallo ita da bilal,wai abu me nauyi yana reto a zuciyarta,tana jin yadda hawaye ke kwaranya daga can cikin zuciyarta,tana qaunarsu,tana sonsu,saidai batasan yadda zata inganta rayuwarsu da tata rayuwar ba,tana fatan idan tayi aure nasuru ya cika mata burinta,wanda dashi take fatan ya zama mabudin yayewar dukkan wata damuwa tata a rayuwa.
Ta jima zaune a wajen tana kallosu yadda suke hira,bilal yana kwasar umman kamar kakarsa,da yake ya saba haka yake mata,har sai da umman ta dubi sashen da take,ta yafitota da hannu tana cewa
“Taso ummukulsum daga nan wajen,magangara ce,kuma dare ne”ta fada cikin nuna qauna da kulawa,saita miqe a hankali tana dawowa inda suke din ta nemi waje ta zauna.
Dubanta bilal yayi
“Yaaya….tun dazu nakeson baki wani albishir amma saina mata”ya fada cikin excitement yana miqewa tare da kakkabe rigarsa daya kwashi qasa,harara kaltum ta watsa masa
“Allah yasa da gaske kake kake wani cika baki ba albishir din shirme bane” baki ya bude yana kallonta,sannan yace
“To wallahi yaya qatoton albishir ne,kuma kin yarda indai hakanne idan na baki zaki bani goron albishir din?”
“Na yadda”ta fada tana qaramar dariya,saiya wuce zuwa dakinsa da sauri yana fadin
“Zan baki mamaki kuwa”.
Bai jima ba ya dawo hannunsa dauke da maka makan takardu guda uku masu tsaho da fadi,ruler da abun rubutu,sai marker da colour da drowing ya zube a gabanta.
Ido ta fitar tana duban kayan sannan ta dubeshi kusan lokaci daya ita da umma
“Bilalu,ina ka samo wadan nan?”sai daya zauna sannan ya amsa mata
“Wadan nan takardun na jikin bangon ajujuwan da aka rushe ne,aka ce mu dauka idan muna so,su kuma saura kudin abincin aikina ne,na raka bashir kasuwar lahadi na gansu acan na siya miki”.
Fuskarta ta cika da murmushi da wani irin qaunar dan uwanta,farinciki sosai ya kamata na abinda yayi matan
“Kai….kai bilalun umma,da gaske kake kuwa?”
“Gasu gabanki yaya?”
“Ashe dama kana sona haka?”ta fada tana dariya idanunta a kanshi,sai yayi murmushi kawai ba tare daya amsa mata ba
“Umma…..kinga abinda Bilal ya siyomin dan Allah”
“An gode maka Allah ya qara zumunci ya hadamin kanku”
“Amin umma wallahi” ta amsa tana jujjuya takardun tare da sake qare musu kallo,tana tunanin abinda zata zana a cikinsu.
Sai data gama murnar sannan kuma ta dubi bilal din
“To a ina kake cin abinci?,kai daba gida kake dawowa kaci ba?,kuma gashi ka tattara kudin haka kawai ka siyomin kayan zane?”
“Ana kawo mana abinci lokaci lokaci,ko a kira masu talla a siya mana,ko mantawa suke sun bamu kudin?” Kai ta jinjina,taga qoqarinsa,shi da bai iya tara kudi,daya samu aci cikin ciki kawai,idanunta ta dauke daga saman kayan ta mayar kan fuskarsa
“Amma dai zanfi so ace ka tara kudadenka bilal,idan aka gama ginin nan,koda ni ban samu shiga ba….kai ka shiga bilal,kayi karatu don Allah”
“Tare dake fa muke zuwa makaranta duk bayan sallar asuba yaya kin manta?”kaita kada tana ci gaba da kallonsa
“Na sani,karatun zamani bilalu,karatun boko.kamar kowa,ni ina sha’awarsa sosai,amma tunda bani da wani isashen lokaci babu kuma dama zanso ace kai kayi,ko don ka taimaki kanka,ka kuma taimaki ummanmu” shuru yayi na wasu sakanni,sannan daga bisani ya amsa
“Me zai hana yaya ke na tara miki kudin ki shiga?”kanta dai ta kuma kadawa
“Kai yafi cancanta kayi bilal,kainw namiji,ni dana fara za’a fara batun aurena,azo a cireni kaga anyi asarar kudin da aka kashe”
“Zanyi yaya”ya bata amsa yadda ya saba bata,da alamun baison zancen ma gaba daya.
Murmushi ummansu tayi,ta jima da fahimtar bilalun baya son makaranta sam,musamman karatun boko,shi yasa duk yadda kaltumen tayi dashi yake zillewa,itama kaltum din dole tayi shuru ganin ya miqe,saiya qarasa ya dauki wata tsohuwar hularsa daya wanke ya sanya a kansa yana cewa
“Umma zani dandali……yaya gaba daya kin rabu da zuwa”
“Hmmmm”kawai tace,don ita kanta tana son zuwan,amma hakanan zuwan ya fita a kanta,tun wancan ranar da babansu ya fadi mummunar kalma a kanta
“Zanje,sai wani lokacin saimu tafi tare” kansa ya gyada ya fice abinsa ta bishi da.kallo.
Bilal kenan,shi sam a rayuwarsa bashi da tension,duk da tarin qalubale iri iri dake bibiyar rayuwarsa,amma kamar baisan dasu ba,duk da cewa akwai quruciya a sha’aninsa,tunda har yanxu shekara sha hudu yake,sai tsahon qafa da zai sanya mutum yayi tunanin yakai shekara sha bakwai.