Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 15

Sponsored Links

โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ
*BOOK 2*

*PAGE 15*

Tunda suka shiga cikin falon yake ware ido yaga ta inda zai gano Meenal ko Hajiya sai dai dukan su babu wacce ta fito falon ya daiyi ma mutanen falon gaisuwa Mommy Hauwa ma dake d’aya d’akin da Hajiya take ta fito sun gaisa itama ya mata gaisuwa Raheenat d’in ma ta fito sun gaisa,
Bayan sun fito daga sashen na Raheenat gefe suka koma k’arkashin canopy d’in dake harabar gidan suna ci gaba da hira dan tunda aka idar da ishsha’i yan zaman gaisuwan suka watse sai ya zamana saura yan gidan kawai,
D’aya bayan d’aya matan su Ya Sa’eed suka dunga fitowa sunayin sallama da mazajen su, sai yayi yunk’uri kamar yace su taimaka su kira mishi Meenal sai kuma ya k’asa suna zaune a harabar gidan har karfe 10 na dare ya gota su Ya Sa’eed suka fara haramar komawa masaukin su, dan haka tare suka fito daga cikin gidan dasu Ya Sa’eed d’in sai dai su suna fitowa sukayi Sallama dashi suka shiga motocin su suka wuce masaukin su duk da ya musu tayin zuwa can gidan shi amma suka nuna mishi a’ah karya damu,
Bayan wucewar su shima cikin motar shi ya koma ya kwantar da kujerar motar ya kunna ac sannan ya sanya karatun qur’ani a radio din motar yana bi da sauti mara amo,
Lokaci bayan lokaci yake duba wayar shi a zaton shi wai ko hajiya zata tab’o shi suyi haramar wucewa suma tunda dare ya farayi sai dai kuma shiru,
Sai ya d’auki wayar da niyyar ya kirata kuma sai ya fasa,
Can dai daya kasa sukuni ganin ana neman k’arfe 11 sai kawai ya maze ya lalubo number d’in nata ya doka mata kira,
D’in din din wayar taci gaba da k’ara sai dai kuma harta yanke ba’a d’aga kiran ba, bai gajiya ba haka yaci gaba da danna mata kira ba k’ak’kautawa amma sai da ya mata kira 6 babu wanda ta d’auka,
Ajiyar zuciya ya sauke mai zafi,
To me ya samu Hajiya haka kardai ace hartayi bacci ne ta barshi a kofar gidan mutane ya dakon fitowar su,

Yau rana ta farko da yayi abunda bai tab’ayi ba,
Number d’in Meenal wacce ya dad’e da adanata a cikin wayar shi ya lalubo, ya dad’e yana k’arewa number d’in kallo wacce yayi saving dinta da emoji mai shape d’in ๐Ÿ’ž heart,
Ya dad’e yana jayayya tsakanin shi da zuciyar shi, wannan tana fad’i mishi cewa ya kirata kawai dan wannan shine damar da yake dashi na samun kusanci a tsakanin su, yayin da wata zuciyar kuma take ce mishi yayi hak’uri kawai ya wuce ya tafi tunda dare dai ya riga yayi in yaso ai gobe ma rana ce, sai yasan yanda duk zaiyi goben dan yaga sun koma can gidan nashi da kwana,
Sai dai kuma a kokarin shi na fita daga kan number d’in nata kuma kawai sai yayi dialing number din ba tareda ya luraba har saida kara d’in d’in d’in da wayar take alamun cewa kiran yaje kan nata wayar ne ya ankarar dashi,
Da azama har wayar na neman kub’ucewa daga hannun shi yayi saurin yanke wayar yana sauke ajiyar zuciya kamar wani wanda ya had’u da abun tsoro, bai gama dai daita kanshi ba wayar nashi ta fara k’ara, k’ur yama wayar domin kuwa Meenal d’ince ta biyo bayan nashi kiran,

Kamar bazaiyi picking kiran ba sai kuma can dai kiran na gabda katsewa ya runtse idanuwan shi ya amsa kiran nata ba tareda yakai wayar kan kunnen shiba sai kawai ya sata a speaker,

“Assalamu Alaikum”
Tayi sallama daga gefen ta bayan ya d’auki wayar,

“Ameen Alaikum Salam, baku gama bane wai dare yana yifa kice ma Hajiya ku nike jira ina waje a inda mukayi parking d’azun”

Yana gama fada mata hakan yayi saurin yanke kiran ba tareda ya tsaya sauraren amsar da zata bashi ba, dan Allah ya sani bazaiso yaji cewar bazasu bishi zuwa nashi gidan daga bakin taba,

Ita ko ata gefen ta bayan ta idar da Sallah Maryam da Meelat ta kira a waya ta had’asu da Raheenat sukayi mata gaisuwa,

Ta dad’e zaune tare da Raheenat d’in a cikin d’akin dan ko lokacin dasu AK d’in suka shigo sashen tana jin shigowar su bata daiji fita zuwa falon bane shi yasa kawai tayi zaman ta bayan fitan su kuma cika d’akin da suken yayi da yayyin su mata nan kuma sabon hira ya b’arke akan mutuwar auren ta, da yike yawancin su tun bayan mutuwar auren nata basu had’u ba,
Kun san mu mata ba gidan mutuwa ba yasin ko cikin mak’abarta ne sai dai in hirar bata zoba amma sai anyi,
To hirar mutuwar auren Meenal d’in shi ya rage jimamin mutuwar da suke ciki aka cigaba da tattauna batun ko wacce a cikin su na tofa albarkacin bakinta daga masu ganin laifin Sarki sai masu ganin laifin Teemah,
Itafa gaba d’aya ma wallahi ta manta da batun cewa wai zasuje gidan AK dan tunda suka iso ita da Hajiyan kowa nashi sabgar kawai yakeyi,
Bata tashi tunawa ba sai da ta kira, koda ya kirata tana cikin yan uwanta suna hira ita kuma dama bata tab’a saving number din shiba shi yasa koda ya kirata bata san shi bane ganin dai cewa kiran ya katse shi yasa ta biyo bayan kiran dan taji ko waye kuma duk hirar da sukeyi ita bata san dare yayi sosai har haka ba,

Koda ya gama rattafa mata abunda zai fad’a ya yanke wayar, bata wani damu ba sukaci gaba da hirar su ita da yan uwanta, dan rabon da su had’u a waje d’aya irin hakan gaskiya an dad’e tunda ko biki sukeyi a gida duk wacce tazo d’akin uwarta take sauka sai dai a had’u a tsakar gida amma yau gasu kusan su duka dan ma wasu basu samu isowa ba sai gobe wad’anda suke kusan ne dai yau suka samu isowa,

Ita ko Hajiya a gefen ta tun bayan data idar da Sallah ta fito daga d’akin suka k’ara sabon gaisuwa da mutanen dake sashen har zuwa sanda Mommy Hauwa da Innar yara suka mata jagora suka shiga sashen sauran matan gidan suma suka musu gaisuwa bayan sun dawo kuma cikin d’akin da aka sauke tan ta koma aka gabatar mata da abinci taci,
Duk abunda akeyi tana ta lura dan ta kirga d’akunan dake cikin sashen d’akuna ukune a kalla kuma mutanen dake cikin sashen mata wad’anda tasan kwana zasuyi kun kusa ashirin ko fin hakan ma banda yaran su, to idan dare yayi wani irin kwanciya za’ayi har aji dad’in bacci shi take ta lissafi,

Sai dai bazatayi saurin bada kaiba tunda ita ba yarinya bace ta gane cewa shima daya gayyace sun zuwa gidan shi yana da nashi dalilin dan haka shiru zatayi tukun, duk zaman da takeyi lokaci lokaci take kallon agogo taga ko zai kirata, kuma itama koda ya biyo ayari suka shigo falon tsaf taji shigowar nashi kuma bayan Jidda ta shiga wajen tama ta k’ara jaddada mata cewa AK ya shigo ya musu gaisuwa dan ita Jiddan ma bata san cewa shine ya kawo suba tayi zaton ko da motar Meenal sukazo har sai da Hajiyar ta sheda mata cewa ai shine ya kawo su tukun,
Ganin cewa Meenal bata neme ta shi yasa ta share batun duk da dai ta yanke cewa idan 11 tayi taga bai kiraba kuma Meenal bata tada maganar ba ita zata kira shi dan gaskiya tasan in tace ta kwana a gidan bazata sake ba, in yaso ita sai ta bishi Meenal din ta zauna tunda ita zata sake a cikin yan uwan ta,
Sai gashi tun sha d’ayan bata buga ba da yaji shiru shi ya kirata, kuma duk kiran da yake mata tana kallo tsaf sai dai kuma itama sai ta wana shi kafin,

Haka yaci gaba da zama a cikin motar yana duba lokaci daga kan minti d’aya sai gashi anci kusan mintuna 15 ba Hajiya ba Meenal,
kamar ya tada motar yayi tafiyar shi dan yasan da gangan yarinyar nan ta shanya shi sai kuma dai ya daure ya k’ara ba zuciyar shi hak’uri ya danna ma number din nata kira a karo na biyu,

Wayar bata dad’e tana k’ara ba ta d’auka,

“Bakiga Hajiyan bane wai ko ya akayi ne kun shanyani a waje sai jira nikeyi duk mutane sun gama watsewa ko baku san dare yayi bane?”

“Umm nifa bazan bika ba anan zan kwana sai dai ko ita Hajiyar ne zata bika,”

“Oh kenan ma d’an iska kika maida ni tun dazun dana kiraki ma baki fad’ama Hajiyan sakon ba,”

Mtwss yaja tsaki mai tsayi bayan ya yanke wayar dan ranshi fa ya fara baci yanzun kam,
A bayyana ya furta,

“Kunga abinda nike ta gudu tun tuni kenan koh, Soyayya da kana nan yara, to ita wannan ma tun ban furta mata cewa ina son ta d’in ba tasan ta shanya ni a waje kamar wani dan iska anya yarinyar nan duk ranar data gane ina sonta ba sai ta mai dani sakarai ba kuwa?, ina ma amfanin haka gaskiya soyayya bata min adalci ba miye haka mutum duk yabi ya susuce,”
Hannu shi ya d’aura a saman kai ya yamutsa gashin kan nashi yana fesar da huci mai zafi,

“Wai yarinyar nan nufin ta duk zaman da nayi a wajen nan zai tashi a banza ne? Lallai ma naki wasa ne Wallahi baki isa ba, Allah yasa nima ina da gata a cikin gidan bari ma ki gani”
Ya fad’a yana d’aukar wayar shi ya lalubo number din Mommy Hauwa,
Babu b’ata lokaci ko ta dauki wayar da sallama,

“Aunty nace dan Allah kiyi ma su Hajiya magana su fito haka nan mu wuce dare yayi, na kira number din Hajiyar bata d’auka ba ban sani ba ko tabar wayar nata a cikin jaka ne kin san halinta kilama ta manta dani ne”

Ya d’aura da cewa bayan ya amsa Sallamar na Mommy Hauwa,

“Ayya kayi hakuri bayi in mata magana zasu fito yanzun babu mamaki kam in akace maka Hajiya manta tayi”

Ta fad’i hakan tana kallon Hajiyar,
Shi kuma daga can gefen yanke wayar shi yayi hankali kwance dan yana da tabbacin cewa wannan aikin kuma ya kammala ba Hajiya ba har ita d’ayar mara kunyar saita fito, dan haka sai yama kawai ya tada kujerun motar daya kwantar ya gyara parking din motar zuwa dai dai bakin gate din gidan ta yanda suna fitowa shiga kawai zasuyi,

Maida kallon ta wajen Hajiya Mommy Hauwa tayi bayan ta gama magana dashi,
“Hajiya ina kika ajiye wayar ki hala?”

“Me ya faru kike tambayar wayata?”
Hajiya ma ta tambaya kamar bata san akan me zatayi magana ba bayan taji komai na kiran da AK din yama Jiddan,

“Mai Jama’a ne ya kirani yanzun ashe tun tuni yana kofar gida yana jiran fitowar ku, ai dai ya kyauta wallahi da bai wuce ba, dan dama ina ta tunanin yanda za’ayi bacci a sashen nan yau, gashi har daren ma yayi, yace ya kiraki ba’a d’auka ba shine ya kirani ai gara kuje can d’in zakifi sakewa ma, ai dama kayan ku yana cikin motar koh naga baku shigo nan dashi ba?”

“Ke barshi kawai ai dare kuma ya riga yayi kirashi kice nace yaje kawai saida safe zamuyi kwanan mu anan, ai dama ba munzo jin dadi bane”

“Ah ah Hajiya dan Allah kuje kawai tunda har Allah yasa bai tafi ba koni ai dan dai kar aga mun kwasa duka mun tafine da nima binku zanyi can din, bari in kira Meenal itama tunda ta iso suna can sun kule d’aki sai hira suke kamar ba’a gidan mutuwa suke ba, ”

Jidda bata fito a d’akin ba sai da ta taso Hajiya a gaba suka fito a d’akin a falon suka had’u da Meenal wacce sai yanzun ne ta fito da niyyar zuwa ta isarma Hajiya sakon AK din,

“Yauwa gara da kika fitoma muje Kunbar min d’a acan waje yana jiran ku ga dare yayi”
Cewar Mommy Hauwa,

“Mommy nifa anan zan kwana ai na fad’a mishi sai dai Hajiya ta bishi”

“Ke dallah can ban son maganar banza, ita Hajiyar ce zata tafi can din ita d’aya ina ce tare kukazo dukan ku, wuce ki d’auko Jakar ki ki fito ku wuce dare na k’arayi”

Badan Meenal taso ba haka ta koma d’akin ta d’auko jakarta ranta a b’ace, lek’awa d’akin itama Hajiya tayi dan yin Sallama da mutanen cikin,
Sai da suka rakasu Hajiyar har bakin motar AK din dake kofar gidan, gidan baya Hajiya ta zauna kamar lokacin da sukazo, Meenal ma gidan bayan ta bud’e zata shiga Mommy Hauwa ce ta hanata da cewa,
“Shi din driver din gidan ku ne da kema zaki koma baya ki kame ku barshi da tuk’aku? Dallah koma baya keda baki san abun arziki ba”
Simi simi ta wuce ta bud’e gaban motan ta shiga ran nan nata a bace, sallama suka musu suka juya cikin gidan shi kuma yaja motar suka bar kofar gidan ranshi fess duk da yana ganin yanda Meenal d’in ke ta faman b’ata rai baibi ta kanta ba tuk’i kawai yaci gaba d’ayi,

Kamar yanda yayi alqawari sai da ya koma ta chawai ya siya musu chips din da Meenal tace tana so da kazar sannan sukaci gaba da tafiya, shida zai d’auke hanya zuwa malali kawai sai ya mik’e zuwa unguwan Sarki koda ya isa inda suke siyar da ice cream din bai tayama Meenal shiga wajen ba fakawa yayi yaje ya siyo musu ya dawo motar ya k’ara bata wuta suka koma daga baya zuwa Malalin,

Sai da yayi ta yawo dasu akan tituna kafin ya d’auke hanyar gidan shi, daga Hajiya har Meenal dai babu wacce ta tanka mishi a cikin su dan ita Hajiya dama tunda ta shigo wayar take amsa wayar Baba Usman dan haka bata damu da sanin ina yake kaisu ba sai dai in taga ya tsaya ta d’ago taga inda suke taci gaba da wayarta,
Ita ko Meenal duk da cewa a cikin zuciyar ta taji dadin yanda ya cika mata alkawarin daya dauka taji dadi amma sai ta fuske abunta taci gaba da hura hanci duk da dai daurewa kawai take amma wallahi ta matsu su isa gidan nashi kafin ta bada kanta sakamakon kanshin chips dana kazar da suka mamaye cikin motar basar wa kawai takeyi amma da lafiya lau ne tabbas da tun a cikin motar zata fara aikasu zuwa masaukin su,

“Bieeee” din daya danna ne ya dawo da hankalin ta kan kofar gidan da yake tsaye saboda tunda suka shigo cikin layin take faman bin gidajen layin da suka shigo din da kallo, gidaje a tsare lafiyayyu wanda kai bawa ko baka tambaya idanuwan ka ne zasu shaida maka cewa unguwan bana yaku bayi bane, dan gidajen sun jeru ne wannan yana wane wannan dan kyau,

Waigawa tayi dan ganin ko Hajiya ta lura da abunda ita take kallo sai taga Hajiya ko a jikin ta hirar ta kawai takeyi,
Sulalawa da motar yayi zuwa cikin gidan bayan an bud’e mishi gate d’in,

Tun kafin ya faka take faman k’arewa gidan kallo,

Hajiya dake bayan motar ita ta fara fita ba tareda ta jira ya bud’e mata kofa ba wannan karan,
Mutuniyar ko sai da ta kwamuso ledar kaji dana chips din ta kafin ta fito daga cikin motar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button