Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 12

Sponsored Links

 

Sanye yake da jallabiyya fara qal mai sulbi,wadda ta saukar masa har daidai idanun sahunsa,bata qarasa masa har qasa ba saboda yanayin tsahonsa,tattausan farin slippers ne a qafarsa,idanunsa saye da farin glasses,sai jarida dake riqe a hannunsa wadda suke buga bayanan kasuwanci da kamfanunuwa,tattausan qamshin turaren tuscany ne ke fita a jikinsa,kamar yadda sumarsa ke sheqi,duk kuwa da cewa dare ne.

Yana tsaka da dubawa ne kiran prof ya shigo wayarsa,don haka ya miqe ya tattara dukkan abinda yake ya fito don amsa kiran nasa.

Qasa qasa yayi sallama cikin falon nasu,wanda yake shuru sai qarar na’urar sanyaya daki hade da qamshin turaren daki.

Mutum uku ne xaune a falon,wanda kusan koda yaushe haka zaka samesu,kowa yana abinda yafi qwarewa akai.

Jawahir wadda ke kwance rub da ciki tana game a tab,sai najwa sata tasa litattafai a gaba masu tulin yawa tana dubawa,yayin da humaida ke gyaran faratanta,a yadda suke zaunen saika dauka kowa a cikinsu baisan da zaman dan uwansa ba.

Sallama yayi muryarsa can qasa,idanunsa saman tvn wadda babu wanda yake ta kanta a cikinsu,hasalima volume dinta can qasa yake,kuma suna wani program ne mai muhimmacin daba lallai su ya burgesu ba,saboda basu san muhimmancinsa ba.

Dukkaninsu kowacce cikinsu tadan gyara yanayin yadda take saboda nuna sunsan da shigowarsa,jawahir ta miqe zaune daga rub da cikin data yi,najwa ta gyara glass din fuskarta bayan ta kalleshi,humaida ta lanqwashe qafafunta,duk da bata gama yankan farcen ba.

Kusan kamar a tare humaida da jawahir suka gaidashi,ya amsa cikim yanayin kulawa yana dubansu,sannan idanunsa suia sauka kan najwa,saita sake sanya hannunta ta gyara glass din fuskarta sannan cikin wani yanayi kai kama da jin isa isa tace dashi
“Barka da dare”
“Barka”ya amsa a taqaice yana duban hanya,inda hajiya jidda ke fitowa,kamar kullum kamar kuma kowanne lokaci daya kasance prof yana gida ta fito cikin shiga ta alfarma,wani dandatsetsen lace ne da duwatsun jikinsa keta bada qyalli da walqiya,isan ka ganta a sannan zakayi tsammanin zata wata dinner ce,bawai kwalliyar me gida a cikin gida ba.

Fuskarta dauke da madaukakin murmushi take dubansa,cike da kulawa da tsantsar qauna data bayyana cikin qwayar idanunta
“Son….kada dai ace ka gaji da jiran abincinka ka biyo sahu?,yau ba favourite dinka akayi ba,sai nasa hasana ta sake girka maka wani abun,don banson ka fita waje neman wani abun,ko ka kwana da yunwa” dan murmushi ya saki,wanda yafi kama da washewar fuska,koda yaushe kulawa take bashi ta musamman,a kullum soyayyar da take nuna masa tafi ta kowanne mutum dake cikin gidan,idan ua debe mahaifinsa kawai,koda yaushe kuma kowanne lokaci komai nasa yakan kasance na daban kuma na musamman a wajenta,saidai kuma…..baisan dalilin da yasa zuciyarsa ta zama wata irin zuciya mai tarin butulci da saka alkhairi da sharri ba,ko sau daya ta kasa jin farinciki da wadan nan shekaru data kwashe tana bashi dukkan kulawa goyon baya da qauna,ta kasa jin nutsuwa akan kanta na dinga alkhairi da hidima da takeyi dashi,idanunsa sun kasa manta ta,itace dai a wannan matsayin daya santa,itace dai wannan din daya sani,ta kasa gogewa daga yanayinta na baya,duk da tarun shekaru da kuma sauyawar rayuwa da kuma yanayi,wanda dukkan dan adam yake samun kansa a ciki.

“Yau din ban shigo da yunwa ba mommy,da kin qyaleta,abba nazo gani,yace min yana son ganina,ina tsoro kada naje bacci ya debeni ban samu zama dashi ba,kada ya tsammaci ina gudu ne kamar ko yaushe”murmushi tayi
“My son….dan abbansa,nikam naga sanda wannan dramer taku kaida abbanka zata qare,shi har yau ya gaza fuskantarka,ya sallama…,kai kuma kana kam bakanka…..ka gaza sakar masa….”
“Wacce gulmar tawa akeyi?”suka tsintsi muryar prof daga bayansu,yana fitowa daga qofar data sada wannan sashen da nasa sashen,cikin doguwar rigar jallabiyya,shi dinma kamar dai samir din,sai jini yayi aikinsa,daka kalli samir ta yanayin qirar jiki….sak prof din,saidai kuma kamanni a fuska bashi bane,kana iya daukan wanna ka baiwa jawahir dake zaune,itace Prof din zammm,don najwa ma mommynta ta biyo.

Dukkansu suka waiwaya suna dubansa sanda yake fitowar,jawahir da mommy murmushi sukeyi,yayin da najwa ta dake kamar bata a wajen,duk sanda irin haka zata faru takan yi dif kamar bata wajen,tana matuqar kishin samir,sau da dama tana jin inama ace itace shi,inama ace itace babbar diya namiji kuma ga professor din ba samir ba.

Inda suke tsayen ya qaraso,fuskarsa kadaram kadaham,cikin girmamawa kowa ke gaidashi,sannan daga bisani ya waiwayo yana duban samir din
“Ba don nayi kiranka ba da ba zaka nemi ni ba kenan?”ya fada da wata murya mai nauyi,idanuwansa saman fuskar samir din,wadda take fayau,bata dauke da kowanne irin emotion,a ladabce yace
“Afwan daddy…..”yayi maganar ne yana dan ranqwafawa alamun girmamawa,shuru yayi bai sake cewa komai ba,saiya juya yana neman wajan zama nan cikin falon,duk da cewa ba dabi’arsa bace yin hakan,da wuya ka sameshi zaune a nan,indai ba abinci zasu ci su dukka gaba dayansu ba,ganin haka ya sanya humaida miqewa,don ba kasafai take zama cikinsu ba idan tagansu dukka tare waje daya kamar haka,kuma tasan ba wani kira ko zama daddyn ya umarxi kowa da kowa ba.

Qasan carfet din samir ya samu ya zauna sosai daura da daddyn,don taqin dake tsakaninsu kadanne,a sannan jawahir tuni harta miqe,ta shiga kitchen ta hado musu abunsha mai sanyi,irin sanyin nan baina baina mai saukar da nutsuwa,wanda bazai cutar da haqora ko bakinka ba,ta hadashi ne da kanta,saboda sanin da tayi,daga daddyn har samir din suna son natural juice.

Sai data zubawa kowa cikin cup sannan ta turashi gabansu,ta miqe tabar falon,saiya zamana daga mommy najwa sai samir din da daddyn.

Lemon daddyn ya soma kurba mai dan yawa sannan ya ajjiye yana harde qafarsa daya cikin daya,idanunsa saman fuskar samir din
“Kamar dai kowanne lokaci,duk da cewa dukkan alamu sunata nuna kansu akan cewa ban isa da kai ba……” Da sauri kalmar daddy ta sanya samir daga kanshi cikin yanayi na rashin jin dadi ya dubi daddyn sannan ya sunkui da kai,baisan me yasa har kwanan gobe daddyn ya gaza fahimtarsa ba ballantana yayi masa uzuri,koda yaushe tunanin daddyn a kansa daban yake,sai yayi kama zai fahimceshi sai kuma komai ya sake damalmalewa”akwai wani taro na musamman da xamu gabatar,wanda ya danganci dukkan wani babban mutum mai fada aji cikin jam’iyya…..shima dai zan miqa goron gayyatata zuwa gareka,bazan fasa ba bazan gaji ba,saboda bani da magajin daya wuceka,inason in sake nuna fuskarka a wajen,kamar yadda kullum kowa ke qoqarin jan nasa,yana sake nunashi,da qulla kyakkyawar alaqa tsakaninsa da manyan mutane”shuru yayi sanda yakai aya yana duban samir,wanda qwaqwalwarsa ta tafi tunani,zayaso ace addyn nasa ya gane,ya kuma fahimci tsantsar rashin sha’warsa kan dukkan wata harka data shafi siyasa,zayaso ace ya fahimci abun babushi sam a jininsa,amma yanzu dukkan wata magana da zaiyi daddyn zai fassarata ne ta wata fuska daban,ma duk da haka bai fasa ba,saboda yasani cewa abinda zaiyin gaba yake da abinda daddy yakeso yayi,don haka cikin kwantar da murya dake cike da zallar girmamawa yace
“In sha Allah zan halarta daddy…..saidai kuma a jibi nakeson zuwa wani qauye zan gabatar da wani aiki,zanyi qoqari na katse wani abun na halarci inda kakeso din”ya fada ba don wai har cikin zuciyarsa yana jin farinciki da abinda ya fada din ba.

Da sauri najwa ta daga kai ta dubi samir don bata tsammaci jin haka daga bakinsa ba,wannan wata babbar dama ce da take dako,wadda zata fara gwada sa’arta,sai kuma gashi samir din ya wargaza mata budget
“Shikenan……babu damuwa,nidai fatana kaje din”
“In sha Allah daddy”ya amsa masa a ladabce
“Allah yasa….”ya amsa yana kuma dorawa da fadin
“Fawwaz ya kawo qararka” daga kai ya sakeyi a take,kai tsaye yana duban daddyn,maganar saita dakeshi ta kuma bashi mamaki,qararsa tame?,me yayi masa?,idan da akwai mutumin daya kamata ace an kawo qararsa din fawwaz dinne,saidai kafin ya furta komai mommy ta rigashi magantuwa ta hanyar fadin
“Qarar son?,me yarona kuma yayi?ta yaya za’a kawo qararsa?”tayi maganar ne cike da tarin mamaki,fuskarta kuma babu alamun fara’a ko kadan,waiwaya prof ya soma yi ya dubeta,kana ya bata amsa
“Shi yaron naki kenan har abada baya laifi,baya kuma aikata ba dai dai ba?……”kai ya girgiza ranta a hade
“Bance haka ba daddy,amma.ina da tabbaci ko meye samir zai aikata yana da dalilinsa,ka soma jin ta bakinsa kafin yanke kowanne irin hukunci” duake idanuna prof yayi daga kanta ya tattara kan samir sannan ya fara magana
“Fawwaz ya gaya min hanyar da kakebi wajen sarrafa duk wata riba da alkhairin da kamfani ya samu,har zuwa yau dun nan da kayi qarin albashi kanka tsaye,ba tare daka tsaya kayi la’akari da irin abubuwan da shi ya hango maka su ba,wansa ni duk cikin lissafinsa ina ganin maganarsa da ra’ayinsa suna tafiya kan dai dai,kuma bisa mizanin da ya kamata,sannan a wajena hasashensa yafi zama dai dai fiye da.naka kai hasashen da tunanin”.sosai abinda fawwaz din yayi ya daurema samir kai,tun ba yau ba yake lura da tarin abubuwa masu yawa tattare da fawwaz din,baisan me yasa ya sanya idanu da hankalinsa kacokam kan rayuwarsa da yadda yake gudanar da ita ba
“Kai nake sauraro” prof ya fada har yanzu yana kallon samir,kamar yadda mommy ma idanunta suke a kanshi.

Zama yayi sosai ya tanqwashw qafafunsa,sannan shima ya aza idanunsa kan fuskar mahaifin nasa
“Daddy,dukkan abinda nake aiwatarwa bai saba doka tsari ko yarjejemiyar da muka dora tsarin kamfanin akanshi ba,duk wani aiki da nake aiwatarwa ina yinsa ne bisa tsarin daya dace,daddy….yau koda ace ba bisa tsari nake komai ba,kudin da nake fiddawa ina gabatar da wadan nan abubuwan dani dakai dukka munfi qarfinsu…..wani tallafi da nuna tausayi ne tsagwaronsa zuwa ga wasu gungun mutane da suke neman ayi musu wani abu guda daya biyu zuwa uku cin rayuwarsu,ruwan sha ilimi da wajen ibadarsu” sosai mommy ta ritsashi da idanu tana nazarin wani abu,yana da fasahar harshe da iya magana,wadanda akullum sune abubuwa guda biyun da take jinsu saman wani mizani mai girma,saita sauke ajiyar zuciya mai nauyi,kafin wani daga cikinsu yace komai ta fara magana
“Ni nasan yarona bazai.aikata wani abu da bai dace har irin haka ba,hasashe ne da tunani mara tushe kawai fawwaz din yakeyi,maimakon yayi qoqarin kula da kwaikwayo da ayyukansa…..bari fawwaz din yazo,saina bata masa ransa wallahi”ta fada tana qara tim kicin kicin matuqa da fuskarta.

Hannu prof ya daga mata kawai sannan ya magantu
“Ni bance ba,ban aiki kowa ba,kome fawwaz yakeyi yana yine saboda qaqarin ganin daidaituwar lamuran dan uwanshin nan mara tartibiyar alqibla”ya qarashe maganar yana tsagaitawa kamar me buqatar hutu,kafin daga bisani ya dora
“Shikenan,wannan naji bayaninka….amma wanne irin zuwa qauyenw haka wannan,babu ji babu gani,da wannan tafiye tafiyen naka,har yaushe ka maida hankalinka kan aikinka yadda ya dace?” Tamkar ita prof din yakewa wannan ‘yar titsiyen haka ta marairaice fuska
“Daddyy….don Allah ka barshi haka nan,ya zuwa yanzu fa samir.ba qaramin yaro bane,kai da kanka ka fada fa….”
“Kada ayi masa fada kenan?”ya furta yana duban doguwar fuskarta,wadda duk yadda tsufa yakai ga son haike mata taqi bari hakan ta faru,cikin ranshi yana sake jinjina mata da yaba qoqarinta,zallar qauna da kulawa da take nuna ma samir din tana bashi mamaki kullum kwanan duniya,zata yarda kowa a gidan yayi kuskure ko laifi ciki harda autarta amma banda samir,koda yaushe ita daidansa take gani,dai dansa take nuna masa,duk da tarin tulin wannan sabanin da suke yawan samu,kan banbance na tsari da ra’ayin rayuwa da suke samu
“Ba haka bane…..ba kuma haka nake nufi ba…..”ta soma fadi a tausashe,saidai kuma qarar wayar samir din ta katse dukkan abinda zata fada,ya fara qoqarin cirota ya maidata silent,baisan yaya akayi ayau din ya manta bai sata silent din ba,kamar yadda yakeyi duk sanda zashi gaban daddy prof din.

Mummy jidda ce ta katse masa yunqurin nasa ta hanyar fadin
“Jeka amsa wayarka…..zan turo maka da sauran abinda kake buqata” Tsam ya miqe,don dama abinda yake nema da buqatar ji kenan tun dazu daga mahaifin nasa amma ya qiyi masa,yaqi jinin ranaku irin wadan nan,da daddyn nasa zai zaunar dashi yana sake tuna masa qadamin da suke kai dukka su biyun.

Gefanta ta ajiye littafinta tana cire gilashin fuskarta shima ta dorashi saman littafin,fuskarta ta yamutse sosai tun kafin ma ta furta komai
“Daddyyy” ta kirayeshi,wanda kiran yaja hankalinsu dukka su biyun shida hajiya jidda,saidai ita mommy kanta ta dauke tana sake tsiyayawa prof lemon da tuni ya shanye cup din farko
“Daddy…..wai me yasa ba zaka haqura hakanan da ya samir ba,gani daddy,na dauki damarar share maka hawayen daya kasa share maka,duk don saboda kai daddy nake wannan karatun fa,saboda kai na zabi wannan course din da nakeyi don na faranta maka,beside ni ma ga jawahir….duk da na fita sha’awa da qarfin zuciyar son zama maka hasken idaniya….daddy what man can do woman can do even better mafa daddy….ka barshi kawai ya rayu yadda yaso,mu biyun nan mun isheka makwafinsa”. Wata hadaddiyar tsawa mommy ta dakawa najwan tana dubanta,fuskarta murtuke tsaf,wanda babu mamaki da najwa din tana kusa da ita babu abinda zai hanata zazzabga mata mari,amma tunda ta danyi nisa da muhallin da take zaune saita fara zuba fada kamar xata ari baki
“Ashe ke din baki da hankali najwa?,kin manta waye samir ne a wajenku?,yayan naki kike fadin wannan maganar a kansa?,mahaukaciyar ina ce ke?,tashi maza ki bani waje kafin na taso nabi ta kanki keda tarin litattafanki,shashashar banza kawai mara azanci”ta fada tana huci.

Cikin mamaki najwa ta janye idanunta daga fuskar mahaifiyar tata,saita soma debe litattafan nata bayan ta miqe tsaye
“Xo nan najwa” Daddy ya fada a hankali,wanda hakan yasa ta dakata da abinda takeyi,ta qataso inda yake ta zauna daga gefansa
“Kullum kuma koda yaushe ina alfahari da ku,musamman ke din nan,koda baki fada ba na sani kuma ina hankalce,kuma ina yabawa da qwarin zuciya da kike dashi akan kaina,da son cika min burina da kuma mafarkina,amma abu daya nakeso ki dinga tunawa,samir inda ace shi din wani ne shi yafi cancanta yahau bigiren da kika fara hawa,saboda wataran ya zame muku babban bango majingina kuma garkuwa a gareku,koda bayan babu raina,inaso kici gaba da kallon sakir a matsayin babban wa uba a gareku kinji,hakan bazai hana rayuwarki ci gaba da tafiya kamar yadda take ba a yanzu,kiyi koyi da jawahir ta wannan bangaren,bani da burin daya wuce koda yaushe na ganku tamkae tsintsiya madauri guda,wannan ne kada zai hana maqiya da mahassada suci galaba akanku…..kin fahimta?”ya fada yana dubanta,kanta kawai ta daga a sanyaye,amma a zahirin gasiiya babu wani abu da kalamansa suka qara mata illa dafi da guba a cikin zuciyarta,sai take gamin a fakaice kamar yana gaya mata cewa……mace fa ba kamar namiji take ba,mace ba zata taba zama kamar namiji ba
“Allan yayi muku albarka,ya albarkaci rayuwarku…..”
“Amin” ta amsa ciki ciki tana miqewa,dukkansu suka bita da kallo,shi da mommy din,tana jiyo sanda daddyn yake cewa
“ke kuma hajjaju banason fada irin wannan……najwa jaruma ce,zuciyarta kuma a dake take,karki kassaramin qwarin gwiwar diyata,nasan ta fada ne kawai saboda tana hangen dan uwanta zai bawa mahaifinta kunya kamar yadda ya saba,ita kuma kunyar ce bata son naji ta,ke kuma matsalarki anytime when it come to samir baki ji baki gani,kowa ma baida gaskiya saishi” wannan kalaman su suka janye kas mafi rinjaye daga abinda najwa taji da farko ya tokare mata qirji,yayin da hajiya jidda ta saki wata ajiyar zuciya,wani yanki na farinciki ya ratsa zuciyarta,wanda batasan na meye ba,daga kuma ina yake,saidai duk da hakan bata fasa amsa masa ba
“Am sorry Prof,amma samir yayansu ne,dole su bishi,haka kuma bazan gaji da nuna musu su girmamashi ba”..…….

Wayar na riqe a hannunsa yana qoqarin maida kiran da aka masa ganin cewa umar ne me kiran,wanda tuni kiran umar din ya riga daya zama miscal.

Bugu biyu umar din ya daga,saiya tsaida tafiyarsa,ya jingina da qarafunan barander da yake tsaye akai,sannan ya goya hannunsa guda daya a qirjinsa,daya kuma yana riqe da wayar yana amsa wayar.

Cikin nutsuwa irin tashi yayi sallama,cike da matuqar girmamawa umar ya amsa,sannan ya gaidashi,ya dora da bayanin dalilin kiran
“Na bincika yallabai,kuma dukkan abinda kaji suna tattaunawa gaskiya ne,yanzu haka ma a gobe yake tunanin maida musu kudin qurensu,hakanan gobe ne rana ta qarshe ta biyan kudin registration din kamar yadda kaji ya fada” Sauke hannun nasa dake harde a qirjinsa yayi bayan yaji bayanan umar na qarshe,kansa a qasa yana ci gana da sauraren sauran bayanan da Umar din yake masa,yasa qafarsa guda daya yana tona fararen duwatsun da aka yiwa qasan harabar varender ado dashi,yana jin zuciyarsa na masa wani nauyi kadan kadan.

Har saida umar din ya kammala bayanansa tsaf sannan ya sauke ajiyae zuciya,cikin sanyi yace
“Ka duba account dinka,zan turo maka da saqo,ayi dukkan abinda ya dace,inason ka gama da matsalarsa a gobe…..”
“In sha Allahu sir”
“Yauwa”ya fada sannan ya sauke wayar daga kunnensa.

Muryar jawahir da yaji daga bayansa ya sanyashi tsaiwa daga latsa wayar da yakeyi,ya waiwaya ya dubeta,tana takowa inda yake tsayen,hannunta dauke da wani kyakkyawan kwando,daya daga cikin abinda yake iya hangowa a ciki flask na tea,wanda yake da yaqinin favourite tea dinsa ne a ciki.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button