Sponsored Links
Hausa NovelsKyalKyalin Kauna Hausa Novel

KyalKyalin Kauna 86

Sponsored Links

[8/15, 8:01 PM] SAFIYYA: Ammi tasan sarai Baba zai biyota bazai taba bari ta tafi ba, hakan yasa tasa keken yasha kwana yabita wata hanya dazaisa subi anguwanni, tunda ta auri Baba bata tabajin yabata mata rai kalan na yau ba at this point bawai faking nashi takeba jitake auren ma yakare tahuta she is tired, tagaji da Baba, she tired of him, he’s always trying to blame her a anything, maisa yake tunanin approach nashi is right?
Yasmeen batai karyaba he is really wrong, tasan yaron nan yamusu laifi amman duk Baba ne yaja, yanzu Allah yadaurama Yasmeen sonshi, is only right as a caring father ya tsaya ya saurari diyar tashi, ya saurari yaron ma but no duka baiyiba, look at all abubuwan dayake yi beating the boy, attacking him, saikace yana fada da tsaran wasanshi, har Yasmeen bai bari ba, dukanta yake, hawaye ta goge she’s so bittered ahaka har sukakai anguwan su ga mamakinta motan Baba tagani yayi parking akofar gidansu yafito ya tsaya yana zare idanu yana kai koma, kana ganinshi kasan bakaramin tashin hankali yake ciki ba, hade rai tayi har sukakai kofar gida keken yayi parking, duba daya tazaro tabama mai keke ta sauko zata shige gida batare data kalli Baba ba karaf yarike mata hannu azuciye Ammi ta juyo tana kallonshi tace “wh bazance muna kofar gida ba zan kwasamaka mari idan baka saken mini hannu na ba”
wani kalan kallo Baba yake mata gabanshi nafaduwa sosai baitaba ganin
irin fushin nan akan fuskan Ammi ba, fizge hannunta Ammi tayi tawuce tashiga cikin gidansu inda taga Mahaifinta zaune atsakar gida kan tabarma dattijo ne ya tsufa sosai ga mahaifiyarta duk suna kallonta da alamu Baba yariga yashigo yamusu magana har ga Allah bataso tazo tatafama tsofaffin nan hankali ba but duk Baba ne yaja, ahankali tabude baki zatai magana hannu Babanta ya nuna mata babban dakinshi dake chan dayan bangaren yace “wuce kishiga ciki ki zauna mijinki yazo yayi magana dake banson kicemini wani abu, wuce kije badan taso ba ta juya ta shige dakin tabude tashiga ko minti biyu batayi da zama ciki ba Baba yabude kofan dakin yashigo tamaida kofan yarufe yajuyo
yakalli Ammi dake zaune ko dagakai batayi ta kalleshi ba dasauri yazo gabanta kneeling yayi jikinshi ko’ina rawa yake yana kallonta cikin tsantsan hankali yace “dan girman Allah Maman Nana kirufamin asiri kizo mutafi gida kiyakuri” batare da Ammi tadagakai ta kalleshi ba tace “na tsani ganin ka
Baban Nana, I hate halayyan ka, and I don’t think zan iyacigaba da zama dakai dan dabi’unka sunsan na tsaneka gabaki daya, na bar maka yaranka duka da gidanka ka hada duka ka cinye” hannunta Baba yarike dasauri yana girgiza mata kai yace “wh wh na rantse miki kome nakeda shi aduniyan nan idan har babu ke bazan tabajin dadinshi ba, nasan inason yarana Maman Nana but idan baki tareda ni bazan ma taba samin natsuwan sonsu ba, nasan namiki laifi amman dan Allah kiyakuri” anatse Ammi tace “saikuma kayi kanka akeji idan kana tunanin hakurinka zaisa nabika kayi kuskure one thing dana sani shine bazan sake auren stubborn man arayuwana ba” dawani irin sauri Baba da gabanshi ke faduwa yace “me kike nufi da maganan nan dakikeyi, wani aure kike magana”?
Cikin tsantsan rashin mutunci dan
Ammi sotake ta gumamai tace “idan zan sake aure mana tunani kake narabu dakai zama zanyi? Har yanzu da kuruciyata da kyauna wani auren zan sakey……….’
” Dawani irin sauri Baba
yadaura hannunshi kan bakinta.Yanda Baba yadaura hannunshi kan bakinta zaka dauka zai nane bakinta ne, idanunshi sunyi jazur kaganshi saiya baka tausayi, duk yanda Ammi keji kaman ta cije hannun nashi kasawa tayi tasauke kanta ta daina kallonshi sabida kada yaga yanda yabata tausayi, gently Baba yazare hannunshi dagakan bakinta ahankali yadaura kanshi kan cinyanta kaman dan yaro, ahankali cikin lallashi sosai yace “nasan ban kyauta miki ba amman kiyakuri dan Allah I promise you zan chanza daga yanzu I will be listening to you tare zamu dinga making decision, please ki fahimce ni and look at things daga view dina, maisa babu wanda ke fahimta ta bana cikin hayyacina yaron nan yazo ya cutar damu gabaki daya jibi yanda ya maida Yasmeen, Yaya zanyi da raina ina zansa raina naji dadi”? Shiru Ammi tayi tana kallonshi saikuma chan tasauke ijiyan zuciya tace “Ibrahim” dago kanshi Baba yayi yakalli Ammi anatse Ammi tace “inaso kasani cewa ba’a zafafa tsana aduniyan nan, nasan yaron nan yamana laifi but yanzu kai laifin naka na neman ture nashi u are too harsh, you’re being inconsiderate, kowa da kaddaran shi arayuwa kaje islamiyya kasan wannan, auren yaron nan da Yasmeen ka daukeshi amatsayin kaddara, ka zauna ka saurari diyarka let Yasmeen talk to you, Yasmeen ba yarinya bace, she’s a woman, tasan metakeyi, she might not be brilliant amman Allah yamata nata baiwan, she’s smart, soyayya is real dan haka kadena karyata nata, nima bagani ba Allah yajarabeni da son fitinannen mutum irinka dudda gaka ga halinkan nan” hannun Ammi Baba yarike gam kaman dan yaronta dake neman gafara murya chan kasa Baba yace “na tsani yaron nan ne yabata rayuwan Yasmeen, shekaru ashirin muna kiwon kamilan diyarmu rana daya yaron nan yazo ya rusa tarbiyan ya maida mana da diya bazawara, taya zan taba daina tsanan yaron nan eh”?
Sosai Ammi ke kallon Baba dan from what she’s seeing Allah ne ya aiko
Maheer rayuwan Baba to teach him a lesson dan daga Baba har Maheer din sunada hali dayawa in common, ijiyan zuciya tasauke tace “tashi ka koma gida zan zauna anan for now nadan huta kafin nadawo gidanka” ga mamakinta hawaye tagani ya sauko daga idanun Baba yakankame hannunta arude yace “dan Allah dan Allah karkimin haka, wh wh wih kini na rantse har sau uku namiki alkawari bazan kara abinda nayibadan Allah dan Allah kirufamin asiri kizo mutafi tare pleaseeee kinji Maman Nana I am sorry” rufe idanu Ammi tayi tajuyar da kanta Baba ya bala’in bata tausayi, tashi Baba yayi dasauri yajawota ahankali zuwa jikinshi
yadaura kanta asaman cikinshi yana bubbuga bayanta cikeda so yace “| know I’ve been hurting you kiyakuri kiyafemini yar aljanna I promise bazan karaba kinji, sorry my best” duk yanda Ammi taso kasawa tayi babu yanda tayi dole tahakura koda tazauna anan tunanin Yasmeen kadai bazai barta haka ta hakura tare suka fito
Baba yakara musu wa’azi sannan sukai sallama suka tafi, wani super market Baba yakai Ammi yace kome takeso tadauka murmushi kawai tayi ta kwashi all abubuwan datakeso su atamapa da laces da turaruka yabiya kudi tsaf suka fito yasaya mata gasassun kaji suka yakoma mota yajuyo yakalleta yace
“saikuma me kikeso”? Sosai Ammi ke kallonshi kafin anatse tace “inaso ka saurari everything
Yasmeen has to say to you? Sit and talk to her idan Munje gida, can you do that kodako maganan mijin nata zata maka?” Gyadama Ammi kai Baba yayi yace “eh” koda sukakai gida dasauri Baba yafito yabudema Ammi kofa, fitowa tayi ahankali tawuce ciki direct dakin da Yasmeen take tayi kwance taga
Yasmeen din akasa da alamu ma bacci bai dade da kwasheta ba danga ragowan hawaye afuskanta bala in tausayi Yasmeen take bata she just wish zata iya cirema yarinyar damuwanta, hannunta takai ahankali tadaura saman goshin Yasmeen din jikinta zafi dukan da Baba yamata ne, sallaman Baba yasa tadago kanta takalleshi hada idanu suka ahankali cikeda nadama yace “jikinta da zafi”?
Sauke kanta Ammi tayi tareda girgixa mata kai, zuwa yayi yazauna kusada Ammi tareda dafa Ammi ahankali yace
“I promise bazan kara daga hannuna natabata ba kinji” gyadamai kai Ammi tayi, anatse Baba yace “je daki bari ni natadata na kwantar da ita akan gado, jeki wanka kafin nazo” Ammi batai musu ba ta gyadamai kai tamike tafice daga dakin juyowa Baba yayi yakalli Yasmeen Allah ne kadai yasan yanda yakeson yaranshi barinma Yasmeen, ahankali yakai yatsanshi yashare hawayen dake kan fuskanta yayi shiru maisa Yasmeen bazata so mahaifinta kaman yanda shi yake sonta ba and support him? Me criminal boy din nan yamata? Maisa take sonshi? Why?
Mesa takasa sadaukar da soyayyan yaron nan sabida farin cikin mahaifinta?
Maisa kikeda taurin kai Yasmeen?
Mamana bahaka takeba” Baba yay maganan ahankali yanasa hannu yadagota bude idanunta Yasmeen tayi ahankali ganin Baba saida tadan firgice tasake bude idanunta tarrr gabanta nafaduwa, ahankali Baba yawani kalan rungumeta tsamtsam baki yabude
zaice sorry yakasa magana hawaye sun taru a idanunshi, murya chan kasa Yasmeen tace “Baba kayakuri kayafemini abinda namaka dazu, wh Baba ina sonka sosai, banda mahaifi irinka aduniya” dagota yayi daga jikinshi, ahankali yadagata suka mike tsaye da kyar ta tsaya da kyau kar Baba yagane sai yanzu taji kafanta namata nauyi duk yayi tsami, hannunta Baba yakama yazaunar da ita abakin gado yayi shiru yana mata wani kallon kallo ba wai kallon fushi ba irin kallon nan da lyaye kema yaransu dakesaka su feeling so guilty dayasa kawai Yasmeen taji she’s feeling extremely guilty, iyayefa iyaye ne kuma sune sukasan kan yaransu. Anatse Baba ya nuna kanshi yana kallon kwayan idanunta calmly yace
“Fateema kin zabi yaron nan sama da mahaifinki ko”? Dasauri Yasmeen ta girgizamai kai tabude baki zatai magana Baba yace “kul bafada nazo miki ba nazo nabaki hakuri ne”
yadan sauke ijiyan zuciya, yakalleta yace “Fateema nayi Babban kuskure yau har ina dukanki duka abubuwan nan ina neman gafara agareki, kinsan d’a dan halas wanda ka haifa ka haifu shine kakeda iko dashi, shine wanda zaka iya daga hannu ka hukunta kacemai yayi yayi yabari yabari, yara nagari sune wayanda sukasan cewa fushin Allah nadaga fushin iyaye sannan yardan Allah nadaga cikin yardan iyaye,
Fateema cikin yarana ku uku na fifita ki kan all of them amman yau kin bude baki agaban kowa kincema ni mahaifinki I am wrong!”
Dasauri Yasmeen tabude baki zatai magana Baba ya girgiza mata kai yayi dan murmushi yace “baki kuskure ba l mahaifinki am wrong Yasmeen, ke Yasmeen y’ata you are right” yayi
murmushi tareda kai hannunshi yashare hawayen dake zubowa daga idanun Yasmeen yayi murmushi yace “| promise bazan kara saki kuka ba dan haka wipe your tears Fateema, matsalan shine I expected so much from you Dan nadauka ke diya ce wacce zata cire iyayenta daga kunya tarufa mana
asiri but I was so wrong Yasmeen bazaki taba fifitani mahaifinki ba, daki fifitani gwara kin fifita wani” dasauri Yasmeen tace “Baba wih bah…….
Tareta Baba yayi yace “bawai nace kinyi kuskuren hakan bane, you we
have every right Fateema ki zabi criminal wai mijin nan naki akaina ni mahaifinki dan haka babu matsala bakomi
rayuwane watarana kema zaki haifa yaranki zu zabi wani chan awaje sama da ke zaki gane ne hakan ke nufi”dawani kalan sauri Yasmeen tasauko daga gadon tai kneeling gaban Baba tana
kuka sosai mara sauti jin kaman Baba baki yamata tace “wlh wih Baba bazan taba zaban wani sama da mahaifina ba” dan murmushi Baba yayi yace “ai bacewa nayi laifi kikayi dan kinyi hakan ba Fateema taso ki zauna”
yay maganan yanakai hannu zai dagota
Yasmeen takasa tashi sabida kuka hakan yasa Baba yabarta, yayi murmushi tareda cije lebe ahankali yace “Yasmeen yama sunanshi uhmm Uhmm Pablo ko Maheer ne ma shinedai kika zaba ko kikeso wanda
Baban ki is wrong about” Baba yasake murmushi anatse yace “gobe ki shirya
tsaf zaki iya komawa wajenshi ko gidanshi dazama duk wanda kikaga yamiki” wani irin kallon Baba Yasmeen takeyi da bala’in mamaki anatse Baba yace “I am wrong Yasmeen na yarda nai accepting dan haka ki tattara kitafi zaki iya zama agidanshi har sai lokacin kasheshi yayi agidan yari ko duk yanda kikeso kiyi Wallahi Wallahi bazanyi fushi ba amman inaso nagaya miki cewa har abada Yasmeen na yafeki cikin yarana!”
Yanda gaban Yasmeen yafadi saida guiwowinta
datai kneeling dasu suka karkace takalli Baba, Baba yayi murmushi yace “kuma wih bawai narikeki azuciya bane Allah ma yaga zuciyata amman dai na yafeki sabida aganina babu amfanin
zaban yaron dabai zabeka ba, kinyi girma kin nuna mini kene kikasan what
is best for you nida namiki abubuwan that were best for you for 20yrs is nothing yanzu, dan haka I accept kinason mijin naki sama da ni mahaifinki,
kumani mahaifinki nadaga miki kafa duk yanda kikeso kiyi da rayuwanki kiyi babu ruwana dagayau amma dai niba mahaifinki bane Fateema, idan za’a tareni ace yarana nawa zance biyu!
Farida da Nana, you are not my daughter yanzu Fateema! Ke diyar kanki ce, kinada iko da kanki kiyi yanda kikaga dama da kanki I wish you all the best. best,
Allah yamiki albarka kinji, bari naje na kwanta saida safe”
Toooh tafaru takare. Dakyau Baba!!!
Yanda Yasmeen ke kuka har abargon zuciyan shi Baba keji wato haka akema yaro mai taurin kai,
, tunda abin nan yafaru yaune yaga ya damke Yasmeen a hannu chak yay crushing ego nata da confidence sannan yayi resetting brain nata da mind,
sai yanzu ya shiga da ita cikin senses dinta,
tashi yayi yajuya zai wuce chak yaji tarike kafanshi dasauri, tana wani irin kuka mai taba zuciya tace “Baba zan iya jure komi aduniyan nan amman bazan taba iya jure mahaifina yace yayafeni ba,
Baba ina zansa kaina wanake dashi banda kai Baba why will you disown me”?
Ahankali batare da Baba yajuyo ba yace “ke kika fara disowning dina Fateema, kuma nace miki bakomi ban rikeki araina ba, nabarki kiyi yanda zakiyi, sabida baki sharemin hawayena ba doesn’t mean Farida da Nana bazasu sharemin ba,
Alhamdulillah amfanin yara da yawa kenan, saken in tafi Mamanki na jirana”
sakin kafan Baba Yasmeen tayi tazagayo tagabanshi dasauri tana kuka at this point babu abinda ke ranta sai yanda Baba yanuna zai manta da ita daga cikin yaranshi bazatama iya kwatanta yanda taji abin aranta ba,
tana wani irin kuka tace “wallahi Baba Kaika haifeni kuma nahaifu, banda wani mahaifi sama dakai aduniyan nan and I will always be your daughter,
ka isa dani, Baba ka isa dan…..
” kafin
tagama maganan Baba yace “idan na isa dake akan mene kokuma akan wani daliline zaisa ki kasayin abinda nace kiyi? Akan mene bazaki iya hakura da yaron nan ba? Eh akanme? Kin fison anamin dariya ana nunani akan titi ana cewa ina kama criminals ina
15:50
turasu gidan yari gashi yanzu diyata ta auri daya kuma nakasa rabata dashi is that what u want? U want to put me your father in shame? You don’t care about me? U don’t care yanda nadawo laughing stock aduniya? You don’t care akan yanda ake zagina mahaifinki? You don’t care to protect my name or image? Tayaya nima zan cigaba da zama mahaifinki butulun yarinya dake mai ba iyayenta akunya!”?
15:50
Zuciyan Yasmeen har wani kayau kayau din daci yake mata bata tabajin batajin dadin komi ba kaman yanda taji batajin dadin daren nan ba, tadade tana kallon fuskan Baba tana kara nanata kalman butulun yarinya azuciyanta tama kasa motsi, ganin tai shiru sai kallon Baba datakeyi yasa Baba ya fizge kafanshi yabita gefenta zai fice dasauri
Yasmeen tarike kafanshi tace “Baba!”
Chak Baba ya tsaya yajuyo yakalle azafafe yace “mekuma yanzu!”?
15:50
liyan zuciya Yasmeen tasauke ahankali tace “Baba ni ba butulun yarinya bace, Baba ka rainane and install good values on me, I can give my whole entire life for you Baba sabida kamini abinda yafi
15:51
haka koda yau nabaka duka rayuwana ban gama biyanka ba Baba infact I can never repay you”
15:51
tadanyi shiru tareda sauke ijiyan zuciya kana ganinta kasan abinda takeso tace yana mata nauyi da ciwo arai ahankali tana kallon Baba tace “Maheer ko!”
15:51
Tadan lankwasar da kanta gwanin ban tausayi, fuzar da iska mai zafi Yasmeen tayi daga bakinta kafin ahankali tana kallon fuskan Baba tace “Baba na yarda na rabu da Maheer har ab……. abada!”
15:51
Wani hawaye mai zafi suka zubo mata, tadan runtse idanunta dasauri kafin tabudesu sunyi jazur muryanta nadan rawa yana shakewa sosai tace “Baba narabu dashi har abada na yarda da duka hukuncin daka yanke akaina dakuma au……auren”saikuma nabiyu ana raba Auren muka dawo zaki har garin nan gabaki daya!”
15:52
Yay maganan yana kallon Yasmeen dake kallonshi gwanin ban tausayi yace
“zan kaiki gidan wani aminin Baban mu dake Yola chan zakije kiyi idda kina gamawa kicigaba da school zakiga nan da 1year kin manta da yaron gabaki daya kaman ba’a halitto dhi ba aduniya kin yarda”? Gyadamai kai Yasmeen tayi tana hadiye kukan ta tace “na yarda” wani kalan murmushi Baba yayi yaduko yadagata ya rungumeta yace “good girl ko kefa wannan shine halayyan yara nagari yaran da suke rufawa iyayensu asiri basa tonama iyayensu asiri aduniya
zamanin mu ko menene iyayenmu keso shi muke yi koda bamaso kuma duk yaron dayama iyayenshi biyayya baya ganin badaidaba arayuwanshi, yaron
dakema iyayenshi biyayya cigaba yake arayuwa bazaki gane how happy kika sani da daddaren nan ba dan haka zan miki addu’a Fateema”

gyadamai kai Yasmeen tayi tana ganin yanda Baba kewani kalan farin ciki wanda rabonta dataga yayi irinshi tun kafin tai aure
kama fuskanta Baba yayi ya manna mata kiss agoshi yace “Allah ubangiji yamiki albarka Fateema, yanda kika fifitani kan kowa yau dinnan kema Allah ya fiffitaki ranan gobe kiyama, Allah ya haskaka rayuwanki, Allah yabaki farin ciki everlasting one, Allah yabaki miji nagari wanda yafi yaron nan, yaro
kamili mumini mai daraja da kima mai addini da gaskiya dakuma girmama magabatan sa, Allah ya miki albarka Fateema na” ahankali Yasmeen tace
“Ameen Baba”
murmushi sosai Baba yayi yasake manna mata peck agoshi yace “kwanta to kiyi baccin ki” gyadamai kai tayi ya kwantar da ita tareda sa bargo yarufeta ya Tofa mata addu’a yace “saida safe ko” gyadamai kai tayi yajuya ya kashe wuta yafice tareda jawo mata kofa yana murmushi sosai, wani kalan kai hannuwa baki Yasmeen tayi tafashe da kuka sosai Mai bala’in tsumarai wayan da Maheer yabata dake cikin bra dinta ne yahau vibrating dasauri tasa hannunta yaciro number daya gani yasa tagane Maheer ne kaman wanda yaji ajikinshi kukane yakara zuwan mata ta tura wayan karkashin filo tana kuka tace “Maheer kayakuri, I tried, I tried, I fought for this relationship, I fought for this Marraige, but I guess banda karfi da will like you, I can stand anything but not mahaifina yayi disowning dina yace ni ba diyarshi bane, bazan iya rayuwa ba iyayena ba babu yan uwana ba, Maheer I really love you I really do but I guess haka Allah yakaddara aurenmu zai kasance, maybe both me and you are destined to be sad arayuwan nan, nasan bazan taba so wani aduniya sama dakai ba, u will always be wanda nakeso Maheer I am sorry, Yasmeen is sorry” tana maganan taciro wayan daga karkashin filo dake vibrating har lokacin ta ijiye kasa ta taketa wayan ta tarwatse tadauke sim din takai bakinta ta tattaune tana wani kalan kuka sannan taciro ta yarda akasa ta tsugunna ahankali jin jiri take gani gawani amai dayataso mata dudda yanda taso tafita taje waje anan daki tai aman sabida babu abinci acikinta ma ruwa ne kawai aman very yellowish da kyar taja tsumma ta goge aman sannan ta lallaba tahau gado jin tana ganin jiri ahaka wani wahalallen bacci ya kwasheta.
[

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button