Sponsored Links
Bakar Ayah Hausa NovelHausa Novels

Bakar Ayah Book 1 Complete

Sponsored Links

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_____________
____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

*Assalamu alaikum*

Godiya ga Allah maɗaukakin sarki daya kawomu wannan rana na fara sabon littafi.
Dama an ce rana bata ƙaryah saidai uwar ɗiya taji kunyah. Barkanmu da wannan rana mai albarka,dafatan An wayi gari cikin ƙoshin lafiya.

*GARGAƊI*

Ban yadda wani ko wata ya kwafamin littafi ba ta kowacce siga,sannan akwai halayya da ɗabi’u a cikin wannan littafin wanda basu dace ba,dafatan za’a ɗaukesu a matsayin darasi mai isarda saƙo.
Sannan abu na ƙarshe ayimin afuwa idan wani yaci karo da abinda yayi daidai dashi,banyi niyyar yin hakan ba sam.
Nagode sosai ayi karatu lafiya……

Page 🖤01🖤

……….”zaki iya ki daure kinji,ki daure zaki iya,kin kusa saura kaɗan ,daure daure ga nan kan ina hangoshi”
Nurse ɗin take fada,wacce ta haɗa gumi sharkaf saboda firgici.
“Nafara gajiya nurse,karfina duk ya ƙare!”
Share gumin tayi a karo na ba adadi kafin ta kalli wata wacce take gefenta,da alama tafi waccar ɗin matsayi,dan kayansu ma ba iri ɗaya bane.
“”Ke maza hanzarta ki ƙira doctor yanzunnan,kice ana neman sa da gaggawa a labor room 24”
“Toh ranki ya daɗe”
Ta faɗa tareda zubawa dagudu. Bayan barinta wajen sake maida hankalinta tayi kan hafsa,wadda take ta nishi amma babu alama haihuwar tana kusa,gashi kuma jininta ya hau sosai babu dama suyi mata cs.
Girgiza kanta tayi cikeda tausayawa,dan duk wanda yakalleta a wannan halin yasan ba ƙaramar wahala take sha ba sosai.
“Sannu kinji,bari yazo ya duba koda akwai matsala,dan ni gaskiya bamu taba ganin irin wannan ba tunda muke anan asibitin,komai ƙalau amma kan yaron yaƙi motsi tunda yafara fitowa?”
“Nurse to ki sake yimin allurar naƙudar mana,inaga yanxun a dace wataƙil”
“Ahah kiyi hakuri,a iya daga jiya da daddare zuwa yanzu mun yi miki allura kusan biyar,bazayyi ki sake ɗaukanta ba yanxu,tana da haɗari sosai.
Baridai doctor yaxo muji mai zaice,inshaaallah zaki haihu lafiyah,kada ki damu,Allah yana tareda ke”
Karfafa mata gwiwa ta cigaba dayi akan lamarin,duk ita kanta ta sare da irin wannan case ɗin.
Waje ta leƙa suka haɗa ido da HAJIYAH ZEENAH,wanda tun ɗazu take zirga zirga a wajen.
“Ya ake ciki nurse,ta haihu ne?”
Jijjiaga sister suwaiba tayi,shekararta ashirin kenan tana karbar haihuwa,amma wannan kam yacaza mata kai matuƙa,.
“Har yanzu dai hajiya lamarin jiya i yau,ni har na fara tsorita ma da abin,gashi tana naƙuda amma kuma babu haihuwa babu alamunta”
“Kai innalillah,ni banma san mai zanyi ba,ga IYAH SAYYADA ma,saida akayi da gaske kafin ta hakura da zuwa asibitinnan,nasan tana can ta ɗagawa kowa hankalinsa,sannan gata itama yarinyar tana shan wuyah sosai……to maizai hana ayimata cs,shi mijin baya ƙasar,amma kuma ƙaninsa yana nan ai sai ya saka hannun”
“Shima hakan bazayyi yiyu ba Hajiya,domin jininta yana at risk,a kowanne irin lokaci zai iya zama matsala”
Suna cikin maganar ne likitan ya iso wajen da coat a jikinsa,da alama zuwansa kenan.
“Ya akayi sister suwaiba,naji ance kina nemana a ɗakin haihuwa,wane abune haka daya gagareki?”
“Uhm sir babbar matsalace sosai,yarinyar kwana uku kenan tana naƙuda,gashi tana last stage,amma kuma jinjirin ya gagara fitowa,idan muka saka hannu kuma saiya koma da baya,sannan da alama kaman yaron bashida rai”
“Oh to a shirya shiga operation mana,bazayyi yu a barshi a cikinta har yanzu ba ai”
“Uhm uhm sir jinin yana over tension fah,operation bazayyiyu ba shima”
“So do you like us to watch her die(so kike mu zuba mata ido ta mutu) dolene muyi wani abun,maza muje na ganta yanzunnan.
Naji kince mrs.JABEER .A.JAAN ce koh”
“Eh hakane doctor,yana shirin tahowa yanzunnan”
Juyawa yayi yana duba file ɗin ta suka haɗa ido ta hajiya Zeena,waccce gabaɗaya damuwa a tattara akan fuskarta.
“Barka dai ranki ya daɗe”
“Yawwa barka doctor,ya kamata kuyi wani abun,idan ta kama fita da ita ne ma sai a shirya yanzunnan ta private jet”
Karki damu hajiya,zamu yi iyah koƙarimmu akan matsalar.
Daga haka suka shige site ɗin da Hafsan take kwance.
Wayar tace tayi ƙara,hakan yasa ta koma inda su LAYLAH matar ƙanin mijinta (facalah)suke a zaune.
“Hello ina jinka ABDULMALEEK ya ake ciki?”
“Hmmm ummah ina hanyar zuwa asibitin,kuma tare mukeda Iyah Sayyada,tace wai dole saitazo taga jikinta,na kawota ko muyita wani wajen?”
Jan ajiyar zuciya Hajiya zeenah tayi kafin tace.
“Shikenan babu komai ka kawotan,idan ka kaita wani wajen ma,kasan bazata haƙura ba”
Sauƙe wayar tayi tana kallon Lylah wacce take danne danne a wayah.
“Lylah Iyah Sayyada tana zuwa,yakamata ki ɗora alamar tausayi akan fuskarki,inba so kike kuyi ba”
Tabe baki Lylah tayi tareda cewa.
“Nina gaji da zaman wajennan wlh,kawai akan wata zata haihu a ce saikazo ka zauna,da muka zauna ɗin uwar me muka tsinana a wajennan ne,in matsalar wanine a sakoka,idan taka ce kuwa kai kake magance abinka”
“Toh yanxun wannan habaicin dani kike kokuma da mijinki dayace kizo? Bar ganin ina cikin jimami ki sami dama akaina,kinfi kowa sanin halina banida daɗi,batun zama kuma babu wanda ya riƙeki ki tashi ki bar wajen,daɗin ta ma kema naki ahalin ba ƙalau suke zaune ba,shanyayyen ɗanki ma ya isheki”
“Ehhh naki shanyayyene,amma dai surukata ai bata kashe kishiyoyinta koh,matsala kan ai tana gindinki,surukarki tazame miki alaƙaƙai,kowa shaidane ita ta kashe kishiyarta,wannan ma kar ace komai,dan biri yayi kama da mutum”…………..”
“Lahhhh ha ila ni Sayyada Tatin,yanzu mai zan gani,maizan gani haka,ƴar jikartawa tana ciki rai a hannun Allah,ku kuma kuna nan kuna saida hali…….ke Zeenatu,wato surukarki batada lafiya ma amma bazaki daina ɗiban rashin arziƙi ba koh……”
“Amma iyah Sayyada itah fah ta fara,kuma…….”
“Dallah rufemin baki ni,saina kunyi abu nayi magana kununamin ku ƴan zamanin nasara ne,kalleku tula tula daku,ƴaƴanku na ƙasar masu jan kunne suna holewa,nikuma ƴar jikata ƙwaya ɗaya ta ni kaɗai take da,an kasa yimata gatan magani,sai paracetamal ake bunka mata dan rashin imani”
Dukkan su jugum sukayi suna jinta,ta riƙe ƴar ƙafar data ke mata ciwo tana ta zuba kaman ƴaƴan kanya,idonnnan sai fici fici nashi takeyi,kaman na ƙwarƙwata.
“Habba Sayyada kiyi shuru mana,wai bakya ganin yanda kika tara mutane sai kallonki suke ne,ni wlh dana sani dana barki kin cigaba da kukannaki ban kawoki ba”
“ABDULMALEEK ya faɗa yana zuya fuska”
Duka ta kai masa a gadon baya tareda cewa.
“Gyauton uwarka data ke tsayennan Audulolo,a gidan ubanwa nayi kukan,ko sharri zakamin dan ka rainani?”
Daga haka bai sake cewa komai ba ya koma gefe yana kallonsu,ta kama uwarsa ta matar baffansa sai tsefesu take a dandazon mutane.
“Mai me Kakah ma yagani ma a wannan matar ya aura har ta haifi ubanka oho,mtsww ba dama ka fita da ita saita zubarmaka da ajikinka a gaban abokanka”
Gyaran muryah likitin yayi hannunsa duk jini,ga gumi akan fuskarsa.
Sakin baki sayyada-tatin tayi tana kallon jinin dayake hannunsa,
“Kai…..ɗan saurayi,yanzu wannan jinin danake gani a hannunta na hafsatuna neh,mai kayi mata kaji mata ciwo haka?”
Saurin cire safar hannunnasa yayi tareda ɗorata akan tiren da nurse ɗin take binsa dashi
“Ahh iyah ba haka bane,jinin haihuwa ne kawai”
Ɗora idonsa yayi akan Hajiya zeena,tareda yimata Alamar yanason magana da itah.
“Am Iya bari muyi magana da Hajiya yanzu nan”
“Mai zaka faɗamata,faɗaminnan ni kakarta,duk nan wajen nafi kowa ƙaunar ta da son ta rayu”
“To Iyah a halin yanxu gaskiya,bamu sam mai zamuyi ba,dan wani abin mamaki ma,ta daina magana saidai bin mutane da ido,sannan gabobin jikinta munaji suna karyewa kass kass a duk sanda ta ɗan motsa,da alama kuma bata cikin hayyacinta…..”
“Yimin shuru haka baƙin jakada,ya isheka haka,wayyooo hafsatuna shikenan,sun haɗu sun cinyemin ita,saida nace bazan bashi ita ba matarsa mayyace,amma suka ƙeƙasa ƙasa su a dole wai yana sonta,kuma tana da hankali.
Gashi nan sun kaita wannan la’ananniyar matar tasa tacinyemin itah,bazan taba yafemuku ba wayoo ni Tateen ƴar mai Gaskiya”
Share hawayenta take da gefen gyalenta,tana kuka amma bakinta ya gagara yin shuru.
Buge likitan tayi tareda cewa.
“Dallah matsa na wuce naje na ganta,marasa imani kawai”
Turus tayi a bakin gadon,ganin yanda jikinta ya koma kaman babu gabobi,ta kwance take da tulelen ciki kaman gawa,dan yanxu kamma babu damar nishin da tayi ɗaxun.
Faɗuwa Sayyada-tateen tayi tana burburwa a kasan tile ɗin ɗakin,kaman sabuwar ƴar bori.
Sai ƙiran sunan LUBAN take da su hajiya zeena da Lylah tana tsine musu.
Abdulmaleek neh ya shigo ɗakin tareda dafa kafaɗunta,suma su Hajiya zeenah shigowa sukayi suna kallon yanda kamannin hafsan suka sanja daga yanda suke.
Madeenah ce da Maleekah ƴayan hajiya Zeena mata(ƙannen Jabeer babban yayansu,sai kuma Abdulmaleek &Abdulkareem su ƴan biyune,sun gama karatunsu wannan shekarar,ABDULMALEEK engneer ne,Abdulkareem kuma doctor ne na ƙwaƙwalwa,yana housemanship a india.
Sai mai binsu Madeenah,tana 300 level a University of abuja,ita kuma Maleeka a 100 level,suna zuwa su dawo).
“Allah sarki zainabuna ma(Mahaifiyar Hafsa,kuma kanwar baban su ABDULMALEEK),haka ta mutu a haihuwa,aka haifamin ita,sai gashi itama suna so ta tafi ta barni a lokacin haihuwar”
Likitanne yashigo da sauri shida nurse din suka fara shiryata zuwa ɗakin tiyata,
“Kiyi haƙuri hajiya,zamu shiga da ita tiyata,saboda mun gano abin cikinta bai mutu ba har yanzu,saidai amma kiyi haƙuri,dan iya ba lallai takai labari ba,amma duk da haka muna buƙatar addu’arku”
Dagata sukayi tareda ɗorata akan wani sabon gadon kaman gawa,suka nufi ɗakin tiyatar,suna barin wajen Sayyada-tateen ta ƙara gudun kukanta,kaman wata ƙaramar yarinya.
“Shima jabeerun sai naci bantan ubansa,dan tsabar ran yarinyar nan bai dameshi ba,shine ya ɗaga kafa daga dawowarsa shekaran jiya har ya koma yau da sassafe koh hmmmm,bamai zugashi ai sai wannan mayyar kuɗin,a son kuɗi zakiyi komai”
Ta faɗa tana nuna Hajiya zeena,wacce ta ɗauke kanta tana tabe baki,dan inda sabo sun saba ma……..

Kwana uku baya……….

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤02🖤

Ƙwana uku baya…………

________________”Ina jinka ZULUNGUM ya kake ganin za’ayi toh yanxun,nidai duk yanda zakayi kayi,kawai so nake ayi mata kisan wulaƙanci,saita ƙwammaci bata shigo rayuwar mijina ba.
Duk wata mace data rabeshi banda maƙiyiya sai ita,zan iya komai kuma domin rabashi da ita.
JABEER JAAN(JJ) nawane ni kaɗai a faɗin duniyar nan,ƙaddarar sa ce ya zauna dani ni kaɗai,duk da kuwa bana haihuwa,yanda bazanga ƙwaina ba a duniya,shima bazai taba ganin nasa ba har ya bar duniyar nan, saidai idan nina haifa shine zai gani,amma idan baniba babu wata ƴa kuma.wannan alƙawarina ne ni LUBNAH ƴar URWATU”
“Shikenan yanda kika ce aikin bazai gagara ba,saidai kafinnan zaki ajiye nairah Miliyan ɗaya da rabi kafin a fara aikin,dan zubar da cikin a yanzu zayyi wuyah,saidai a bari idan yakai matakin haihuwa sai a hanashi fitowa,koya kika ce toh”
“Hmmm idan hakan zaifi ayi hakan,amma ni da son samuna ne kafin na koma gida na sameta anyi filla filla da naman jikinta,babu wani abu dazai nuna itace,vazaka gane bane boka,natsani na buɗi idona na ganta a cikin gidannan,da wannan tsinannan cikin tana turashi,nafiso a kasheta irinnna waccar matar,kafin ma takai ga wani samun ciki”
“Kai……!! Tsiyata dake lubna gaggawa,inkika bi a sannu,kuma kina bawa Aljanu jinin da suke buƙata,babu abinda bazaki samu ba,har matakin zaman ki na CEO ma duk zai cika nan da zuwa gaba.
Idan aka kawar da itama rufe idonsa za’a yi daga kan duk wata ƴa mace da take doron duniyar nan,ke ɗai zai dunga kallo a duk inda idonsa ya sauƙa”
“Shikenan nidai duk yanda zakayi ma kayi”
“Amma fah akwai ƙa’idoji da dole saikin kiyayesu,na farko;dolene kijata a jiki,ta yanda zata yarda dake har ki dunga sanin ya take ciki,na biyu kuma akwai wata ƴar tsana da zan baki,ki tabbatar kin saka jininta a jiki,lokacin da tazo haihuwa ki dunga karya jikin tsanar,zai zamo tamkar jikinta kike karyawa,daga lokacin da kika karyata tayi laushi,ita kuma sannan zata fuskanci tata mutuwar tareda abin cikinta”
“Naji wannan bayani naka,za’ayi yanda kace ba matsala,lokacin dazata dunga ihu sannan zuciyata zata wanke da zama min da tayi a cikin gidana.
Nagode gaskiya yau da gagarumin abinda ka bani,zan tafi,dan yau zai dawo daga taron daya tafi England”
Tashi lubna tayi daga ƙasan da take zaune tareda kaɗe zaninta tana murmushin samun nasara.
Hanyar fita daga wajen ta nufah mai matuƙar bada tsoro,amma hakan ko a jikinta,dan akan kishin mijinta babu abinda take ganin zai iya saka mata zani yarabata dashi.
Saida ta ɗanyi tafiya mai nisa kafin tazo wajen inda ta ajiye motarta,Wai hausawa suna cewa SA KAI YAFI BAUTA CIWO.
Saida tayi tafiya mai nisa kafin ta shigo garin abuja,direct JAAN ESTATE ta wuce da baƙar motar ta.
Nufar babban get ɗin tayi cikeda ƙasaita da izzah,wanda hakan a jininta yake.
Titin dazai kaita apartment ɗinsu tabi,wanda take ɗan ciki kaɗan da bakin babban get ɗin.
Saida ta wuce nasu Hajiya Zeena kafin ta iso nasu part,shima da get ɗinsa mai zaman kansa,yana ɗauke da part biyu,amma a haɗe suke ta tsakiyah,inda side ɗin Jabeer yake.
Ba hanyar nata part ɗin ta nufah ba,da alama wajen Hafsa zataje.
Fuskarta a murtuƙe take saboda tsanar baiwar Allahn,amma haka ta danne saboda zancen boka ta saki fuskarta kaɗan.
Da sallama ta shiga tangamemen falon,mai adon Green da purple,yayinda nata kuma yake fari da ja.
Haushi ne yakamata ganin kayan Alatun da mijinnata yasaka mata,tafison komai yazama ita kaɗai take dashi bada wata matar ba.
“Assalam ƙanwata kina cikine””
Hafsace ta fito daga ɗaki da doguwar riga a jikinta marar nauyi tana tura zungureren cikinnata.
Kallon Lubna take da mamaki,dam yanda taga murmushi akan fuskarta abune da bata taba gani ba a faɗin rayuwarta,a ranta addu’oi take jerowa duk wacce tazo bakinta.
“Lafiya ƙalau Anty lubna,sannu da dawowa ya hanya”
“Hanya ƙalau,har zan shige nace bari nazo naga ko lafiya kike,nasan babu kowa a gidan saike kaɗai,ga Honey ma bayanan,an barki ke kaɗai ga ciki”
Ƴar dariyah Hafsa tayi,har sannan bata share tantamar inaga antynnata ba lafiyar ta ƙalau ba,dan in ana neman rashin imanin matar to a tambayeta”
“Ayyah ba komai anty,akwai Alawiyyah ai ƙanwata,tana taimaka min da abubuwa,Hajiya ma kuma tana shigowa akai akai”
Mintsine bakin lubna tayi tareda cewa “munafukar tsohuwa” a ranta.
“Ohh kinga shaɗaf na manta da hakan,dama saidai ta hakan ai,akwai abincine ki bani,yanzu na fawo gashi banci komai ba”
“Ah….ehhh barina duba kitchen ɗin,ki zauna akan kujera naje na dawo”
Murmushin yaƙe Hafsan take dan kwata kwata abin bayyi mata a gaske yake faruwa ba.
Bayan tabar wajen tashi lubna tayi tana kalle kallle a cikin falon,yaune zuwanta na farkon wajen da niyyar arziƙi,saidai tazo tayi tijara ko kuma kashedi,dan haka har tazo ta tafi bata gane mai yake wakana a wajen sai yanzu.
Tana cikin kalle kallenne Hafsa ta dawo ɗauke ta plate a hannunta,ta rufe da wani a sama.
Karba lubna tayi tana murmushi tareda cewa.
“Yawwa nagode ƙwanta sosai,amma zan iya tafiya dashi saina kawomiki plate ɗin?”
Ɗaga mata kai Hafsa tayi cikin ladabi.
“Lahhh ki tafi dashi Anty babu komai”
Daga haka lubna tajuya ta fita da plate ɗin abincin a hannunta.
Tana shiga part ɗinta ta buɗe kwandon shara ta zubashi a ciki,tareda jefa plate a ɗin a wajen wanke wanke tana kaɗe hannu kaman ta dauki kashi.
Ɗaya daga cikin masu aikinta ta ƙwalawa ƙira.
“Bishirahhhhh!!!!!”
“Naaama ranki ya daɗe”
Ta karisa magana tana zurowa da gudu.
“Gyaran gidannan bayyimin ba kwata kwata,ku tabbar kun sake gyarawa kafin magriba”
Bayan ta wuce wacce aka ƙira da bishira ta samu waje ta zauna,tareda sakin wata ajiyar zuciya,banda neman na halali mai zai sakasu aiki a wajen wannan dujal ɗin.
Bayan ta fito daga wankane taji ƙarar motoci suna shigowa cikin apartment ɗinnasu.
Shafe shafe tafarayi,dan tasan mai gidanne yadawo daga taron shekara da sukeyi da sauran companies..
Har lubna ta gama shiryawa ana ta ƙiran Sallah amma bata ga Jabeer ya shigo ba,abinne yafara bata haushi,dan tasan yanzu haka yana sashen Hafsa,saboda ita tana da ciki ita kuma batada shi.
A bangaren J.J kuwa yana fitowa daga motar muhimmin ƙira ya shigo wayarsa,ana nemansa da gaggawa,dan haka a take ya ɗau ƙaramar motarsa personal ya koma.
Bashi ya dawo gidanba sai bayan isha.
Sallama yafara a bakin falon lubnan,amma shuru bata kulashi ba har ya shigo cikin ɗakinta.
A zaune take akan kujerar dressing mirror tana danna waya,tacika tayi famm kaman zata fashe.
Mamaki abin yabaww J.J,dan yasan babu abinda yayi mata kafin tafiyarsa,hasalima sanda ya fita daga gidan bata nan ta tafi gidan ƙawarta batareda yasani ba,shine ma yakamata yayi fushi,amma kuma wai itace dayin fushin.
“Lubna inata Yin sallama kinaji kaman ba musulma ba?”
“Hmmm banyi niyyar amsawa bane,dan tsabar rashin adalci wato,tun ɗazu kashigo gidan amma kana wajenta,ita gamai haihuwa koh,sai nayi magana tsofi suce banida haƙuri”
“Ke suwaye tsofin,iyayena koh? Yayi miki kyau,wai yaushe zaki sanja haline kam,dawowa ta fah kenan,yanxune ma nashigo gida,hmmm ALLAH ya shiryeki,banida lokacinki tunda lafiyarki kalau fine,na sauƙe miki haƙƙinki,saida safe”
Yana gama faɗin haka ya bar sashennasa cikin bacin rai,tasashi kuwa sarai,idan yayi zuciya da ita ta ƙwammaci ya mareta daya tura mata aniyarta,dan sai yayi sati bai kalli inda take ba.
Tsuka taja duk da taji tsoron fushinnasa,dan Allah ne kaɗai yasan irin yanda take so tajishi a tareda ita,dan ita kanta shida ce shiɗin jarumin namijine a ta kowacce fuska,badai mace ta rainashi ba,saidai ma ta gaza.
Dama ƙarin haushinnata kenan,ba a sashenta yake ba,shiyasa take wannan kumbure kumburen.
Hafsa tana kan sallayah ya isa ɗakin cikin fushi.
Sallama tayi tareda sake masa murmushi lokacin da suka haɗa ido.
Shima murmushin yayi mata,duk wani bacin rai da lubna tayi masa sai yaji yana sauƙa.
“Ka dawo lafiya ya hanya?”
“Alhamdulillah,ya zaman gidan da lafiyarku”
“Muna lafiya kalau,barina kawo maka abinci”
“Ahah ki barshi,barina yi wanka tukunna”
Tashi yayi ya rage kayan jikinsa tareda shiga banɗaki.
Kafin ya fito ta fitar masa ƙananna kaya marasa nauyi.
Da safe suna cikin yin break fast lubna ta shigo sashen riƙeda plate ɗin jiya a hannunta.
Tasha wani matsatstsen lace kalar zinare da baƙi riga da skirt,ba laifi tanada yar ƙiba,amma kuma bayada kunkumi sosai mai cika ido,sannan ba fara bace,saidai sanadiyyar mayuka na zamani,tayi fari tass kaman fatalwa.
Wani shu’umin murmushi tasake mai,dauke da ma’anoni kala kala.
Hafsa ce ta gaishe da ita tareda yi mata bismillar abinci,Jabeer kam ko kallon ta bayyi ba,sauri yake yagama cin abinci yafita wajen aiki.
“Ayya wai break fast,naga kam kuna cikin nishadi sosai,plate ɗin jiya na dawo miki dashi”
Ta faɗa tamkar mutuniyar kirki. Jan kujera tayi babu kunya a kusada Jabeer ta zauna tareda yimasa kallo ƙasa ƙasa.
Hafsa tana kallonsu amma ta kawar da kanta tareda zubawa Lubna itama abincin.
Bayan kamar minti biyune Jabeer ya ɗago ya zabgawa lubna harara,saboda yanda take ɗaga ƙafar wandonsa da kafarta ta ƙarƙashin tebur ɗin.
Har ya buɗe baki zayyi magana ganin bata daina ba ya fasa,saboda yanda Hafsa ta ajiye cokalin hannunta tana rike cikinta.
Tun kafin Jabeer ya taimaka mata,lubna ta riƙeta tareda yimasa magana ya ɗakko key ɗin motarsa.
Cikin sauri suka nufi asibitin da itah da gaggawa,sai bayan sun isa an shiga da ita ɗakine tukunna suka samu damar ƙiran Hajiyah zeenah,wanda cikin ƙankanin lokaci ta tashi hankalinta,sai gata itada Laylah,matar baffansu ABDULLAHI. Sayyada-tateen kam ba’a sanar mata ba,saboda kowa yasan halinta da surutu da ɗaga hankali.
Safa da marwa suka fara a bakin labor room ɗin,itadai luban kallonsu kawai take,duk sanda suka nuna damuwa ƙara bata haushi suke,musamman yanda jabeer yafasa tafiya ko ina,kowa addu’ar ta sauƙa lafiya yake,ita babu wanda ya kula da ita.
Ƙara wayarta tayi a cikin jaka,wanda hakan yasa ta nufi wani dan waje gefe da inda suke tsaye.
“Hello Hajiya na ɗebi miki jinin,yanzu zan fito daga ward ɗin,sai ki bini zuwa nurse section na baki”
“Okay babu matsala”
Tana kashe wayar tayi murmushin mugunta tareda kallon inda hafsan take kwance,fitowa nurse ɗin tayi kanta a sunkuye ɗauke da test tube na jini ta nufi sashen su,babu wanda ya kulada ita,domin kowa yayi zaton abu zata kai wani wajen.
Lubna tana ganin hakan ta bi bayan nurse din,saida sukaje inda babu kowa kafin ta tsayah,
“Yawwa gaskiya kinyi ƙoƙari sosai,ai dama yanda kika faɗa cewar kin bata maganin naƙuda tasha da safe,shiyasa na shiga sashen domin na biyosu asibitin.
Aikinki ya cika,na tura miki miliyan ɗaya acct ɗin yanda mukayi nagode ni barina na tafi”
Lubna ta faɗa bayan ta karbi jinin tasaka a jaka.
“Kwanan ki ya ƙare Hafsatuwa kema kaman ɗayar,nariga na faɗamuku,duk wacce ta rabeshi to kabarinta ta tona,koda kuwa wacece”…….!!!!!

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤03🖤

Saida taje daff da inda su Hajiya Zeena suke tsaye ta riƙe kanta tareda fara layin ƙaryah.
Lylah ce ta kulada ita tace.
“Lubna kema kuwa lafiya,naga sai layi kikeyi?”
“Uhm kaina ne nake jinsa kaman zai fashe,bana jin daɗinsa ko kaɗan”
“Toh ta tafi gida mana,dama waye ya riƙeta,ni nayi mamaki ma danaga tazo wajennan”
Hajiya Zeena ta faɗa tana binta da harara. Itama ta wata fuskar ramawa tayi,tareda yimusu sallama tabar wajen,shikuwa uban gayyar dama yayi fushi da ita jiya. Dan haka ko kallon ta bayyi ba.
Dariyah ƙasa ƙasa Hajiya Lylah tayi,da alama show ɗin yayi mata dadi sosai.
A daddafe tana nishi ta nufi motar ta,hadda tsayawa ta huta kana ta cigaba da tafiyah.
Saida tabar layin asibitin kafin ta saki shewa tareda ciro wayar ta a jaka.
“Kee Dallah ki tsaya nayi magana,nasamo mahaɗin yanzunnan,naji kincemin kinaso kiga yanda zan gama da ita,to ki hanzarta,dan ba’a son tafara naƙuda tukunna,idan ta haihu to aikin bazayyi yiyu ba”
Kashe wayar tayi tareda ƙarawa motar wutah tana waƙa.
Bata ja wani lokaci ba ta isa gida,kasancewar basuda nisa da asibitin.
A bakin ƙofar gidan ta samu motar Yaseerah ƙawarta tana jiranta,bodyguard sun hanata shiga,ta bar ID parmission dinta a gida saboda sauri.
Horn Lubna tayi musu tareda nuna musu motar Yaseerah lokacin da tazo shiga.
Tafiya take tana binta a baya har suka isa apartment ɗinsu.
Direct sashen Lubanan suka wuce cikwda raha da kuma shewa,tamakar tarkon su yakama Toron giwa.
“Wai dagaske kike luby,nifah har yanzu ban yarda ba irin wannanan asirin yana duniyah,kina daganan saiki kasheta hankalinki kwance?”
“Ƙawarai ma kuwa,ki zuba iso kawai kigani,lokacin dana taho bata haihu ba dan haka mu hanzarta”
“Idan ta haihu shikenan bazai aiki ba?”
“Ahah ba aikine bazai yi ba,kawai so nake na haɗa itada abin cikin na kashe,kingane dai koh,tunda kema ƴar garice ai”
Ba’a falo suka zauna ba,saboda tsaro sai suka shige ɗaki.
“Wai lubby har yanzu tsoron Kucakan gidannan kike yi,i think no need,tunda kece kike aikatawa,kuma ma hakan yafi,ta hakanne kaɗai zasu ƙarajin tsoronki su daina aura masa mata,habaa mutum baza a barshi ya wataya da mijinsa ba ya more”
“Hmmm barsu mana,nafisu iya shege ai,kome suke ina daidai dasu, ko nace ma nafisu”
Tana maganar ne tana fitowa da ƴar tsanar daga cikin jakarta,sannan ta ɗauko jinin Hafsa ma a cikin kwalba,zubawa tayi akan ƴar tsanar gefen bakinta yana motsawa tareda bada wani shu’umin murmushi ganin alamun samun nasara a aikinnata.
“Kinga Seerah inaga aikin yayi,saboda jinin ya tsotse a cikin dollyn,yanzu zan fara ƙiran sunanta sau uku sannan saina fara kakkaryah ta”
Tana rufe baki kuwa ta fara aiwatar abinda ta faɗa a aikace.
“Hafsa….hafsaaa…….hafsaaaaa,kwananki ya ƙare ganinan kema gareki!!!!!”
Ƙaƙasss tafara kakkaryah jikin ƴar tsanar,wanda duk sanda tayi hakan sai wata ƙara tafita daga jikin abin,amma hakan ko tsoro bai bata ba bare tausayi,saima wani ƙara ƙwarin gwiwa daya bata tareda nishaɗin matsalarta tana shirin kauwa daga gabanta.
Ta ɗauki kusan minti talatin tana aikin,domin idan ta karyah saita jira kafin tacigaba dayi,badan komai ba sai dan tasake bawa kanta lokacin hakan.
Saida ta gama kafin ta jefar da ƴar tsanar a ƙasa tana maida numfashi,hannunta da kuma jikin tsanar dukka jinin hafsa ya bata.
“Nagama da ita itama seerah,itama ta tafi kaman yanda ɗayar ta tafi,babu wanda zan ƙyale,hakan alƙawari na ne danayi”
Ajiyar zuciya ta saki tareda komawa ta zauna a kusada seerah,kaman wacce tayi aikin daidai.
“Huh ya kike gani seerah,kina ganin ta mutu kaman yanda nake buri”
“Indai har da gaske kin yadda da aikin zulumgum,kuma kin tabbatar kinyi yadda yace,ni ina ga babu wani abin damun kai a lamarin,kinyi yadda ya dace,to yanzu yaya? Zaki kira kiji ko ta mutune ko kuma shuru zakiyi kar ace kece kaman koyaushe”
“Hmm ko nace nice ko kar nace nice dukkansu kowa yasan nice na aikata,abinda yasa kika ga banbar gidannan ba,saboda bahaka nabar mijina ba,duk aikin yasoni tamkar uwargijiyarsa bayyi aikiba,amma namasa aikin da bazai taba sakina ba,har mutuwarsa,saidai idan nice naga damar tafiyar.
Sukuwa bazasu so mutuwar ɗansu dan nabar gidan ba,dan haka a zauna a haka,su cigaba da kawo ƴaƴansu cikin gonata ina murƙushesu kaman ƴaƴan kaji”
“Heee gaskiya bakida dama lubeee,shiyasa fah a Club ɗinmu ke ta dabance,to ni kinga barina tafi,Old lady tana ta ƙirana zanje na ɗora abinci,saikinjini ko sai na jiki”
Daga haka seerah ta ɗau jakarta tayi gaba.

•••••••BACK••••••••

“Innalillahi innalillahi innalillahi……….”.
“To sai salati kike kamawa amma bakya ƙarisawa,nasan yanda kuka shaƙu da hafsa Madeena,amma addu’a zaki mata ita take buƙata a yanzu”
Abdulmaleek ne yafaɗa cikin tausayawa,dan kowa yasan Madeenah batada wata ƙawa bayan Hafsan,kasancewar tare suka tashi,kuma kansu ɗaya.
“Yah Abdul kana gani fah,kalli yanda take shan wahala,jikinta duk ya lanƙwashe,shikenan fah bazata tashi ba”
“Am sorry sis ki dunga yi mata addu’a kinji,ikon Allah sai kiga ta tashi da ƙafafunta,komai nufine na Allah”
Ɗaga kai tayi Alamar taji abinda yace,bayan suɗin babu wanda yake magana a wajen,sai Lylah abu kaɗan taja tsuka ta turo baki,ita a dole an sakata zaman wajen babu yanda zatayi.
Hajiya zeenah ce ta juya ta rafka mata harara,har zatayi magana ko mai ta tuna sai kuma tayi shuru tareda minding nata business din.
Ƙarar ƙofar dakin tiyatar ne ta ankarar da dukkansu,inda kowa ya juya yana kallon waye zai fito daga ɗakin.
Doctor Basheer ɗinne ya fito ɗauke da hankerchip a hannunsa yana share ruwan gaban goshinsa.
Kallon su yayi da alamar bayason faɗamusu abinda yake kan fatar bakinsa.
“Am sorry munyi iya ƙoƙarinmu amma……….”
Abdulmaleek ne ya katseshi tareda cewa.
“Uhm doctor duk wajennan nine namiji,shin ko zamu iyah yin magana dakai a office tukunna,kafin saina faɗamusu,bai kamata ka dunga faɗan magana a waje ba irin wannan ,musamman da iyah a wajen”
Kowa na’am yayi da maganar abdulmaleek din,inda doctor yashige office shima ya bishi.
Ya ɗau kusan miniti talatin kafin ya dawo inda su hajiya zeenah suke,duk da yanda yake ƙoƙarin saita Yanayin fuskarsa,amma kana gani kasan ba ƙaramar magana bace a bakinnasa.
“Am sorry to said,she’s gone,Allah daya fimu sonta ya karbeta Iyah,please dan Allah karki saka damuwa a ranki sosai kinji,ki ɗauka cewar Hakan shine abinda yafi mata Alkhairi akan rayuwar da take ciki.”
Ɗan ja da baya Sayyada tatin tayi ta zauna a akan kujerar da take bayanta,saida ta saita ta kwantar da hankalinnata da taimakon Abdulmaleek kafin ta ɗaga kai ta kalleshi.
“Toh…toh ina yaron naji ance yana da rai kafin ayi mata tiyatar koh?”
“Ahah iyah,an fitar dashi da rai,amma kuma yabi bayanta bayan mintuna da yazo duniyah,saboda shima abin ya shafeshi sosai,bai daɗe ba ya koma ga mahaliccinta”
“Naaaa shiga uku shikenan jinin zainabuna ya ƙare a duniya,wacce nake ganin zata maye min gurbinta itama ta bi bayanta,hadda ɗan dazan riƙe naji daɗi shima ya tafi,yanxu wannan tantiriyar mayya mai yasa zata min haka mai yasa zata lagarta min rayuwar iyali…….yanzu……..”
“Dan yarasulullahi Iyah sayyada ki taimakemu kiyi shuru,Hafsa Addu’a take nema a halin yanxu,naƙira baban su Abdul da kuma Abba ƙarami,dukkan su suna hanyar zuwa inshaaallah”
Hajiya zeena ce tayi maganar tana share ƙwallar da take idonnata,ita ba komai ne yasake girgizata da mutuwar ba sai yanda taga ci taga rashi,burin wannan ɗa yazo duniyah amma sai gashi wata ta kasheshi tun kafin ta ganshi.
Wani tirurine da kuma bakin ciki tareda muradin ɗaukar fansar jikanta suka turnuƙe a cikin ƙirjinta.
Babu abinda take ambata sai sunan Lubnah a zuciyarta.
Suna cikin tsaye xugum zugum Alhaji Abdullahi ne yashigo shida Jabeer,wanda kana ganinsa kasan abun ba ƙaramin dukan ƙirjinsa yayi ba sosai.
Bai taba zaton zai rasa hafsan ba inaga kuma Ɗannasa dayake jinsa tamkar tsoka ɗaya a cikin miya.
Tunda yazo wajen bayyi magana ba,banda rawa babu abinda jikinsa yakeyi,duk yadda Mutanen wajen suka kai ga jin haushinsa saida ya basu tausayi,duk da shi mutum ne mai sanyin rai,amma kuma da wuyah mutum yaga Lagwonsa ya karye kamar haka.
Ɗakin da hafsan take ciki ya nufah jiki a salu’be.
A kwance take akan gadon tiyatar an rufeta da farin kyalle,gefe kuma jinjirinne shima an naɗeshi da farin kyallen.
Kallo ɗaya yayiwa inda jinjirin yake ya ɗauke kansa,dan baya fatan ma ya buɗe yaga menene a ciki,saboda yasan hoton bazai taba barin zuciyarsa da tunaninsa ba,ya dunga farautarsa kenan har ƙarshen rayuwarsa.
Hannunsa yasaka na dama yafara yaye farin kyallen dayake kan hafsan,duk da yanda hannun nasa yake rawa amma yana iya koƙarinsa wajen ganin yayi mata kallon karshe,macen da duk namiji zayyi mafarkin samu a rayuwarsa,hankali,tunani,tausayi,uwa uba sanyi rai da sanin yakamata.
Ko mutum bai taba zama da itaba yasameta yasan sai ya ratsa duniyah kan ya samo irinsu,to inaga shikuma da dama yana cikin duhun rashin sa’ar samun mata,kwatsam lokaci ɗaya hasken yazo masa yafara haska duniyarsa….kashh sai kuma gashi ya ɗauke ya barshi a duhunsa wanda yafi ma na baya,saboda a da bai ɗanɗana hasken yaji ba,yanzu kuwa daya ɗanɗana yaji saiya ke ji tamkar duniyah sun taru sun juya masa baya.
Jajayen fatar bakin sa da suke rawa saboda tashin hankali ya fara motsawa tareda son furta wata kalmar.
“Meyasa meyasa………lokacin da ban shirya ba……”
Ƙwallah ce ta ɗigo daga idonsa zuwa kan goshin matacciyar da take gabansa a kwance.
“Ki jirani nima ina nan zuwa wajenki kinji,banga laifinki ba da kika tafi,domin babu komai a duniyar sai rashin daɗi,kece kika fara nunamin ba yanda na ɗauketa take ba,saidai kuma yanzu dakika tafi nasan babu wanda zai sake nuna min yanda kika nunamin……ALLAH YA JIƘANKI HAFSA”
Yana gama fadin hakan yasaki mayafin yamayar mata kaman yanda ya ganshi,daga nan yafice daga ɗakin yana share hawayen daya taru a idonnasa.
A zaune take tasaka riga rabin ciki,da wando matsatstse,head phone akan ta,da kuma cocumber akan idonta tana jijjiga kai.
Da alama yanayin yanayi mata daɗi sosai.
Bishira ce tashigo falon jikinta har rawa yake domin da isar da saƙon da take ɗauke dashi.
“Hajiya hajiyah hajiya….”
Saida tayi ƙira sunfi biyar kafin Lubnah ta cire cocumber dake kan idonta ta kalleta.
“Menene kuma yanxu kike buƙata kika zo kika durkusamin kaman mai neman gafara,mayu kawai.”
“Uhm hajiya dama …..wani labari naji wai Hajiya hafsa ta rasu a asibiti dazu”
“Oh an faɗi ta mutun,yaya hadda ɗan cikin suka rasu ko ya?”
Abin yaɗan bawa bishira mamaki amma ta danne,dan dama ko karen gidan ma aka tambaya ai yasan itace ta kasheta,to amma wazayyi magana,duk yanda gidan suke ji da taƙama da kuɗi,amma bazasu iya shari’a da lubna ba,saboda baban ta shine Chief private lawyer da abuja take ji dashi,kuma lubna ita kaɗaice ƴar sa mace,zai iya komai dominta.
Musamman daya zamo basuda hujjah bayananniya cewar an ganta ta kasheta,shiyasa take kashesu da boka take cin karenta babu babbaka.
“Eh hajiya naji ance wai harda yaron duk suka mutu,ana tahowa da su gida ma ayimusu sutura a binnesu”
“Huh naji daɗin wannan labarin naki”
Ta faɗa tana murmushi,gefenta ta juyah ta ɗauko dubu biyar ta miƙawa bishiran,dan dama dansu ta kawo mata labarin,duk da zagin data sha bai dameta ba tunda an bata kuɗin.
“Nagode nagode hajiya,zakuwa kijini da wani labarin idan nasamo”
Daga haka taja dabaya ta fita daga falon jikinta har rawa yake don son kuɗi.

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤04🖤

Ƙarar jiniyar motar asibiti ce tafara amsa kuwwa a gidan,wanda hakan ne ya shaida alamar shigowa da gawar Hafsa tareda jaririn yaronta cikin gidan.
Bayan motar asibitin ta shigo sai kuma motocin su Jabeer suma suka biyo bayanta.
Kowanne idan kaga fuskarsa kasan mutuwar ta shigeshi,yanda suke fitowa daga motar jiki a sanyaye.
Sashenta aka nufa da ita domin yi mata sallah a ɗakinta,duk abinda ake Lubna bata fito ba,bare tazo wajen yin suturar.
Sai bayan an tafi da ita kafin tafito da jumbulelen hijabi a jikinta fari tana rarraba ido.
Babu abinda kakeji a wajen sai kukan Sayyada-tateen,wacce babu yanda ba’ayi da ita ba,amma taƙiyin shuru sam,kowa tausayinta ne ya kamashi,saboda babu wanda baisan shaƙuwar da sukayi ba da hafsan.
Bayan dawowa Daga binnetan aka cigaba da karbar gaisuwa,Saidai duk wanda yazo yiwa Jabeer gaisuwa sai a ce bayanan.
Abinne ya ɗaurewa abokinsa kai Khaleel,wanda hakan yasashi shigowa cikin gidan nemansa.
Da madeena suka haɗu a hanyar shiga sashensu zata kaiwa ƴan uwan Hajiya zeenah Abinci.
“Am Madeena ina kuwa JJ( Jabeer Jaan) banganshi ba,gashi ana ta zuwa yimasa gaisuwa a waje”
Alamar mamakine yaɗan hau kan fuskarta,dan itama batasan inda yake ba,sannan babu wanda yaga shigowarsa,sashensu ma mutanene a wajen sosai.
“Ahah Banganshi ba,bansan inda yayi ba,kuma ina kyautata zaton baya Sashensu ma,dan wajen akwai mutane sosai. Amma ka ƙirashi mana kaji inda yake”
“Tun ɗazu nake ƙiran wayarsa switch off,tabbas mutuwar Hafsa ta girgizashi,amma bai taba yin haka ba ya kashe waya dukka,kuma a irin wannan yanayin da mutane zasu nemeshi sosai”
Dukkan shuru sukayi kowa yana tunanin shin a ina zasu ganshi,can bayan shurun nasu madeena tace.
“Uhm barina tambayi ummah kota san inda yake ”
Daga haka ta wuce tabar Khaleel a tsaye,yana jiran fitowarta.
Wasa wasa anyi sadakar uku amma babu Jabeer babu Alamarsa,kowa yayi ta mamakin ina yashiga,anyi zaton ma ko ya bar garin.
Sai washagarin kwana uku mutane sun fara raguwa sannan yashigo gidan da motarsa.
A hankali yafito daga motar yana jefa ƙafa kaman mai koyon tafiyah,idanuwansa sunyi luhu luhu sai lumshesu yake kaman wanda yayi maye,kallon mutanen da suka kewayeshi yayi,amma babu wanda yayi wa magana,har hajiya zeenah wacce ta kafeshi da ido,da alamar tambaya a kallonnata.
Hanyar sashensa yayi kansa a sunkuye,bai juyoba har ya shige ya turo ƙofar.
Bai cire takalman ƙafarsa kana bai fasa tafiya ba har ya shiga cikin ɗaki.
Kan luntsumammen gadonsa ya faɗa a haka yana jan gwauron numfashi,tareda fesar da iska mai zafi.
Runtse idanuwansa yayi na tsawon sakanni kafin yafara buɗesu yana sauƙesu akan farin POP ɗin ɗakin.
Hawayene sirara suke bin gefen idanuwansa suna zuba akan zanin gadon,bai damu daya share su ba,haka yabar su suka cigaba da zuba har na tsawon wani lokaci.
Wayarsa ya fitar daga cikin Aljihun wandonsa ya kunnata.
Kaman jira kuwa takeyi,tafara amayar da saƙon da aka zubo mata lokacin da take kashe.
Ƙuramusu ido yayi suna ta shigowa,saidai ko kaɗan bai nuna alamar ma zai buɗe ko ɗaya daga cikiba,shidai yana kallonsu kawai.
A jiyeta yayi a kan drawer gadon ya shiga banɗaki,har sannan wayar bata daina ƙarar shigar massage ba.
Ya daɗe a wankan kafin ya fito sanye da towel a ƙugunsa,ɗaya kuma akan sa yana tsane ruwan jikinsa.
Farine ba sosai ba,sannan yana ƙirar jiki,da alama ba haka aka bar jikin ba ana motsashi.
Yanada baƙin gashi sosai,amma daga ganin yanayinsa kasan bashida laushi a nature sa,ana amfani da manyan mayuka ne wajen bashi gyara na musamman.
Kallo ɗaya yayi kansa a madubin dage gabansa yayi saurin ɗauke kai.
Da alama bayason kallon ramar da take kwancene a kan fuskarsa,kana da kuma launin idanwansa wanda har yanzu basu dawo da haskensu ba.
Riga da wando yasaka marasa nauyi yafita daga ɗakin da sauri,jin alamun ana buga ƙofar falon da ya sakawa key shigowarsa.
Da Madeenah suka haɗa ido lokacin daya buɗe ƙofar itada Maleekah,ɗauke da kulolin abinci a hannunsu.
Ganin kallon tuhumar da sukewa idanuwansa ne yasashi saurin ɗauke ido tareda komawa cikin falon ya barsu a tsaye.
Suma basu damu daya ce musu su shigoba suka biyo bayansa,dan sunsan ko za’ayi shekara bazai faɗa ba ɗin ba.
A jiye kayan abincin sukayi a kan center table ɗin dake gabansu, Madeenah ce tayi ƙarfin halin faɗamasa saƙon da aka aikota dashi.
“Uhm ummah tace idan ka gama tana nemanka a sashen Abbah”
Bayyi magana ba duk da tasan yaji abinda tace,dan haka kowa ke fama da halinsa na rashin magana shida Maleekah.
Har takama handle ɗin ƙofar zata fita taji muryarsa ƙasa ƙasa,inda akwai surutu a wajen ba lallai taji mai yake faɗa ba.
“Lubna tana nan?”
Haushine ya turnuƙeta sosai,bayan kwana uku daya ɗauka bayanan,ana nemansa an damu dashi,amma yana dawowa bai tambayi kowa ba sai wata Lubna.
“Bansani ba”
Shine amsar da Madeenah ta bashi a daƙile,kafin tayi wuff tabar sashennasa,kar ya huce akanta.
Fitowa yayi daga sashen ya nufi hanyar na Lubna.
Ga hasashensa kuwa bata nan kaman yanda yayi zato,ina taje oho.
Tun halinta yana bashi mamaki yanzu abun har ya zame masa jiki,lokacin da ake wani abin daya girgiza kowa a gidan,ita sannan zata shirya tabar gidan,ko kunya ma da kuma bakin mutane bata ji.
Jawo ƙofar yayi ya nufi Apartment ɗin iyayennasa.
A zaune yake mahaifinnasa kaman kullum akan Wheelchair,shekararsa uku kenan akai tunda ya samu paralyse na Accident,a lokacinne Jabeer ya karbi kujerar CEO na Companyn.
Maganinsa Hajiya Zeenah ta balla ta miƙa masa,tareda kofin ruwa.
Sallama Jabeer yayi a hankali can ƙasa ƙasa yanda za’a jishi amma kuma bada sauti sosai ba.
Hajiya zeenah ce ta waigo ta kalleshi daga haka da maida kanta wajen mijinnata.
Gaisawa sukayi da mahaifinnasa kafin daga bisani ya tambayeshi jikinsa.
“Jiki Alhamdulillah Jabiru,Naji ummanka tace kwana uku baka gida sai yau ka dawo?”
“Eh Abba dama……dama….”
“Bakomai nasan yanda kakeji a ranka,rashin mata da kuma ɗa,musamman a yanayinka abune da yakamata ayi maka uzuri,sannan kuma a jajanta maka.
Allah yabaka ikon yin haƙuri da kuma tawakkali,sannan kuma ka dage da addu’a da miƙa lamarinka ga Allah,watarana zai wuce sai labari”
“Inshaaallah,nagode Abba”
“Tabbas ansan anyi maka mutuwa,amma bai kamata ka kashe wayarka sannan kuma tafi batareda ka sanar da inda kake ba,Abokan kasuwancinka jiya suka zo daga india yimaka gaisuwa,sai tafiya sukayi basu sameka ba……..”
Shuru Jabeer yayi yana jinta,yanda take faɗan baya nan,badan ta damu dashi ba sai dan ta damu da yanda aka zo ba’a sameshi ba,shikansa wani lokacin yana zama yayi ta tunanin shin Hajiya zeenah ce ta haifeshi,saidai ga sauran ƴaƴan ma haka takeyi,wanda yake nuna zai fiddata kunyah yayi kuɗi shine a gaban goshinta,gaba ɗaya batasan nuna soyayya ga ɗanta tsakani da Allah ba,saidan wani abun duniyar.
Haka ta horar dasu tun suna yara,burinta su zamo sunfi kowa,indai har wani ya fisu to anan zasuga bacin ranta a fili.
Shiyasa takeji da Jabeer saboda yana matakin farko a compayn nasu,abu ɗaya ne yake cimata tuwo a ƙwaryah,shine mata marar arziƙi da Allah ya haɗashi da ita,saikuma rashin haihuwa da bai samuba.
Lokacin daya auri hafsa ta samu ciki,tafi kowa farinciki,itama zata samu jika a daina yimata habaici,saidai kash Yanda taso bai yiyuba. Wannan dalilinne yasa ta ƙunshe vaƙin cikin Lubna a cikin zuciyarta.
“Haba Zeenatu wai meyasa kike hakane,yaronnan fah Matarsa ce ta rasu da kuma ɗansa,kuma kinfi kowa sanin yanda waƴannan mutane suke a wajensa,dan yatafi yabar gida,daga dawowarsa ki fara wai abokan kasuwancinsa sunzo bayanan basuji daɗi ba?”
Jumburo baki tayi tareda hararar Jabeer ɗin ta ƙasa ƙasa,
“Haba Alhj yanzu kai baka ga maganata akan gaskiya,yanzu daya tafi da wani muhimmin aiki ya taso fah,yakake ganin za’ayi,kuma dazakace haka duk waye ya jawo komai idan bashi ba,da bai auro waccar masifarba aida komai bai faruba. Hmmm ai bari ayi sadakar Arba’in,takardarta zai bata ya auri ƴar mutunci wacce zata haihu,ba ita ba juya”
“In kina so ma kice yasaketa yanzu,ai duk ɗaya ne tunda kin faɗi Abinda ke bakinki,ki dunga sararawa zuciyarki dai,kina yayyafa mata ruwan sanyi,dan yanzu girma yafara kamaki,inba so kike ciwon zamani ya kama ki ba”
Shuru sukayi dukkan su babu wanda yasake cewa komai,kana ganin Hajiya zeenah kasan da maganganu a ranta fal,ganin idon mijinnata ne yasata yin shuru badan ta haƙura ba.
Shikuwa dama Jabeer duk maganar da suke a iya zuciyarsa yake saƙasu,ko ɗago da kansa bayyi ba.
Alhj Aliyu ne yakalleshi cikin tausayawa tareda cewa.
“Tashi ka tafi Jabeer Allah yayi maka albarka,sannan yakamata ka ɗau hutun Aikin kaje wani waje nesa da gidan kaɗan huta na wani lokaci”
“Toh Abbah”

Alhaj Abdullahi ne ya fito daga mota ransa a bace ya nufi bangarensu.
Sauri yake zubawa kaman zai tashi sama,dan dama irin mutanennnan ne masu firitt jiki da kuma sauri.
Bai samu kowa a falon ba, dan haka Ɗakin lylah ya nufah.
A zaune take tana bawa Haneef Abinci a baki,wuyansa sai gilu gilu yake da ƙyar yake karban abincin.
Tsayawa yayi bakin ƙofa batareda yayi ƙyakykyawan motsi ba yana kallonsu.
Tunani yatafi yanda rayuwar su take kasancewa shida matar tasa,shekararsu sha shida kenan da aure,babban ɗansu haneef mai shekara Sha biyar,Allah ya jarabceshi a Lalura,ko kansa baya iya tsayarwa bare yayi wa kansa wani abun.
Saurna yaransu kuma huɗu dukka matane,shikaɗaine dansu namiji saidai dashi gwara babu a wajensu.
Yanada shekara ɗaya a duniyah yakoma haka,har yau babu wanda yasan meyasa ya koma haka,anyi na gargajiya anyi na asibiti amma abu yaci tura.
Haneef ɗinne ya juyo yakalli mahaifinnasa dake bayansu,aikuwa ya wangale bakinsa yawu yana zuba,alamar yana masa dariya.
Itama lylah juyowa tayi ta kalleshi tareda cewa.
“Ahh yaushe ka shigo,amma lafiya na ganka da wuri haka ka dawo,ɗazu fah kake cemin yau sai dare ka dawo”
“Hmmm kedai bari laylah,ni narasa yanda zanyi da wannan yaron,nine nafara sanin companynnan kafin yasani,amma dan tsabar babu wanda yake ganina da daraja a gidannan,wai aka ɗau kujera mafi matsayi aka damƙa masa.
Project ɗin danacemiki zan jagoranci aikinsa,saida suka zo yau da suka ga Jabeer baya nan wai bazasu yadda na jagoranci aikin ba,tunda hutu yatafi kuma ya kusa dawowa to zasu jirashi ya dawo”
“Kutt to miye dalilin daya saka bazasu baka ba,ba kaine Defuty CEO ba,duk wani aiki dayake ai kai yakamata kayi in bayanan.
Hmmm dama na daɗe da faɗamaka ai cewar duk gidannan ƴan baƙincikine,babu wanda yadamu da rayuwarmu a cikinsu,in ina faɗamaka kana ganin banason yan uwanka,yanzu ai gashi ka gani da idonka”
“Nagani kam,duk wani aiki danayi a companynnan banida daraja a cikinsa,yau inna faɗi na mutu babu abinda iyalina zasu tsira dashi,dolene na ɗau mataki akai”
“Hmm hakane kam,yanzu inka yarda a ɗau mataki to kabar komai a hannuna,nikuma zan saita komai yanda ya kamata,buɗar idonka kawai zakayi ka tsinci kanka a matakin CEO na JAAN company”
“Na baki dama kiyi komai ma yanzu,nima yanzu bazan saurara ba,dole na ƙwaci haƙƙina a ciki”
Wata dariyah gefen baki laylah tayi tareda kanne ido guda ɗaya.
“Ka zuba ido kaga aikin laylah masoyina,bazan baka kunya ba”

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤05🖤

“Ke Madeena zoki rakani gidan Hajiya ladi,na daɗe banje ba,kullum cikin samun abin tashin hankali muke”
“Kai ummah Binciken semina fah nakeyi,maleeka ta rakaki mana”
Haɗe girar ƙasa da sama tayi,tasani sarai babu wani bincike da takeyi,dan tana jin ƙarar game ɗin candy crush a wayar tata,Kawai dai dan kar tajene su haɗu da Al’ameen a gidan,Babban ɗan Hajiya ladi wanda suke son haɗata dashi,shi yana so,amma madeena kam kwata kwata bayyi mata ba.
“Banason shashanci dallah sanjo kayanki kizo mu tafi,yara ana nuna muku abinda zai taimakeku kuna wani abun daban”
Cikin zumbura baki babu yanda zatayi ta sanjo kayan harda guntun hawayenta.
Tasan badan komai mahaifiyarta take son haɗata dashi ba,saidan yanada kuɗi,ita kuma wanda takeso bashida kuɗi,tunda ummannata taji zancen a wajen Maleekah tayiwa tufkar hanci,a cewarta ƴaƴan ta bazasu auri talakawa ba.
Tafiya suke a motar Madeenah tacika tayi fam,babu abinda ma yafi bata haushi kaman yanda yadunga yi mata izzah,dan yasan mamuƙata ake a wajensa,kawai dan yasameta mai sanyi bata mayar masa magana.
Basuyi tafiya mai nisaba suka iso gidan Hajiya Ladin,shima gidane tankatsetse naji da faɗa,kana ganin tsarin gidan kaga jiji da kan yaran gidan,kasan sunayi ne da dalili.
Wanda hakanne yasa su Madeenah jin haushin ƴaƴan aminiyar uwartasu.
Suna fitowa daga mota ,wata mata tayi musu iso zuwa ainihin falon hajiya ladin,ba wanda take tarbar mutane haka ba.
A zaune take a falon suna taɗi da ƴar ta guda ɗaya mace JAWAHEER,wanda bazata wuce sa’ar Madeenah ba,dan set ɗin su ɗaya ma,saidai ita Business Admin take karanta,irin na Jabeer.
Dukkan ahalin guda biyu babu wanda baisan yanda ake muradin haɗa jabeer da Jawaheer aure ba,saidai kash lubna tayi musu cikass,tazame musu kaɗangaren bakin tulu,har kawo yanxu babu abinda basuyi ba,amma su kansu sun tabbatar Asirin lubna yafi nasu ƙarfi,babban tsoron su kar Jabeer ya aureta a yanxu itama ta kasheta.
Sakalci take zubawa son ranta,ita kuma hajiya Ladi tana shafa mata kai,wanda yake kan cinyarta,duk da shigowar su hajiya Zeenah ma hakan bai sa ta ɗago ta kallesu ba,saima ƙarawa abinda take ƙaimi.
Hajiya ladi ce ta kalli Jawaheer tareda cewa.
“Kai mana Baby waike ko kunya bakyaji yin fitina a gaban mutane,kuma hadda maman yayannaki koh,ki tashi ki gaishesu mana,sannan ki kawo musu ruwa”
“Toh amma ruwa kam su jenifer suna nan su kawo musu mana koh momy,kinji fa nace miki jiya jikina tsami yayi dana tashi a bacci”
Ƴar dariyah hajiya zeenah tayi,tareda cewa.
“Ohhh lallai Jawaheer ɗin mama,har yanzu dai kece da cinya koh,saiki sha magani ai ki huta”
Sakin baki Madeenah tayi tana jin abinda ummanta ta faɗa,tsamin jikine zai hana mutum kawowa baƙi ruwa,kuma ji abinda suke faɗa…..anya kuwa ba asiri hajiya Ladi tayiwa uwartasu ba,inba haka ba wannan ai ya wuce ɗaukar tunani.
Harara Madeenah ta gallawa Jawaheer,wanda itama ta rama a take,kaman ba itace take sakalcin ƴan shekara biyu ba,gaisuwar da akace tayin ma batayi ba ta tashi ta tafi. Half vest ce a jikinta sai bom short,su a dole suna kwaikwayon turawa,ko mahaukaci yagani yasan abin bayyi tsari ba,amma Hajiya zeenah idonta ya rufe akan mutunin nata (kuɗi) kwata kwata bata ga hakan ba.
Har taje bakin ƙofar fita daga falon ta juyo ta kalli Madeenah.
“Ahh Madeenah zamuje ciki mana na rakaki sashen Yah Ameen”
Kallon ta Madeenah tayi babu yanda ta iya tabi bayanta,saboda kallon da Hajiya zeenah tabita shi,na gargaɗin karta musa.
Itakuwa tasani sarai ba abin arziƙi bane yasaka Jawaheer ƙiranta,dan tafi kowa sanin wacece Jawaheer ɗin.
Kaman kuwa dama jira suke,Madeenah tabin bayan Jawaheer hajiya zeenah ta matso gefen Hajiya Ladi.
Labarin abinda ya faru tafara zayyane mata na mutuwar hafsa,kasancewar basu samu tattauna hakan ba ana abin mutuwar.
Wani murmushin ciki ciki hajiya ladi tayi,koba komai taji daɗin hakan,duk da taso lubna ce ta mutu,in suka tashi hafsa bazata yimusu wahalar kawar wa ba a cikin tsarin.
“Toh naji mai kikace Zeenatu,amma ya kike ganin zamuyi yanxu toh,wanann idan muka barta bamu san wani irin barazana zatayi ta kawowa ba,sannan gaskiya bazan yadda Jawaheer tazama surukarki ba wannan matar tana gidan”
“Nasan da haka,abin da yafi mu zauna a mukawo shawara kawai,ni burina shine ta fita daga rayuwar ɗana,yazamana cewar inada iko dashi yanda naga dama”
“Plan biyu zamuyi yanzu,na farko shine ki ƙirasu dagashi har matar tasa,kafinnan ki tabbatar yasha wannan maganin a abinci tukunna.
Komin asirin dayake jikinsa to a take zai daina aiki na minti talatin,a lokacin saiki umarceshi da yayi mata saki uku,kinga koya dawo asirin dai aikin gama ya gamu.
Idan kuma wannan bayyi aiki ba,to inaga wata matar zamu aura masa,mu nuna mata muna tareda da ita,ta dunga yin duk abinda muka ce,idan tayi nasara akan Lubnah itama saimu kawar da ita,idan kuma batayi nasara ba itama ta kasheta,shikenan kinga dai ba ƴar mu bace dai abin ya faɗa kanta ba”
“Wanann aiki yayi,kai ai ƙawance dake Hajiya ladi nasara ce,da duk ban tuno haka ba…….”
Suna barin falon sashen Jawaheer suka nufa.
Part ne mai zaman kansa dukka natane,komai taga dama shi takeyi a ciki,da ƴan aikinta da komai.
Zama tayi akan kujera tana kallon Madeenah wacce take tsaye batace komai ba.
“Ki zauna mana ko sai na zaunar dake,bar ganin ina kallon inda kike,wallahi albarkacin kin haɗa jini da masoyin xuciyata kike ci,idan ba haka ba ke kin isa kiga inuwa ta ma…..gayyar tsiya kawai,kin tsaya akaina babu wani nuna ladabi,kaman ba yayan ki zan aura na”
“Ai koh yayana zaki aura?…meyasa har yanzu baki aureshin ba toh,wannan zancen har ya gunduri masu jinsa,anaso ana tsoro,in sonsa kike da gaske ki aureshi mana yanzu ƙirr,ina baki jiki a kabarinki ba,ƙaramar ƴar iska kawai.
Batun na nuna miki girma kuma,ke inban da na jefa yayanki a gwandon shara na ƙi aurensa,ai da yanzu na daɗe da zama babbar yayarki,kuma…….”
Kafin Madeenah ta cigaba da magana Jawaheer ta wanketa da wani mari mai ƙara,wanda hakan yasata yin shuru da abinda take faɗa ta dafe kumatunnata,ɗaya hannu kuma ta wanke Jawaheer itama da mari.
Faɗa suka fara da doke doke,inda Madeenah ta buga Jawaheer a akan tiles ɗin falon,daidai shigowar su Hajiya ladi kenan,ƴar aiki ta shaida musu mai yake wakana.
Da sauri hajiya ladi ta ture Madeenah akan Jawaheer tana salallami.
“Yau mai zan gani,Madeenah karya min ƴa zakiyi ki fallasheni,ji wani bugawa da kika mata wanda tunda na haifeta bata yi ba”
Jawaheer najin haka ta fashe da kuka tana yarfe hannu,kaman ba itace tafara takalal faɗan ba.
Hannu hajiya ladi tasaka a fuskar Jawaheer tana shafa inda Madeenah ta mareta,wanda yayi jajur yaji fuskar ƴar hutu.
“Mari!!!…..?”
Shine abinda Hajiya ladi ta faɗa cikin bacin rai.
Dukkansu su ukun Madeenah suka tsaya suna kallo harda Hajiya zeenah,ganin hakan yasa itama tayi saurin cewa.
“Itace tafara marina,dan kawai nace idan tanason yaya Jabeer ƙirr ta aureshin mana,shiyasa nima na ram……”
Wani marin Hajiya zeenah tasake zabga mata a ɗaya kuncin,sanann cikin bacin rai ta haɗa da cewa.
“Dan tana son yayanki shine zaki dunga yimata haka,ai tafiki tunda ana saka ta yin abu tayi,da kika bugata a ƙasa idan kika karyata fah,dallah wuce mutafi gida,batun aurenki da Aminu kuma ba fashi,ina akan hakanne kike hucewa akan ta,mai baƙin hali kawai”
Masifa Hajiya zeenah ta dunga surfawa Madeenah,yayinda ita kuma Hajiya ladi ta rungume Jawaheer tana shafa bayanta,har sanann bata daina ihu ba kamar ƴar yaye.
Hawayene yake zuba akan fuskar Madeenah,badan zafin marin da aka mata ba,saidan zafin takaicin yanda har yanzu mahaifiyar tasu ta kasa gane mai yake faruwa,idonta ya rufe kirif akan muradanta,ko ƴaƴan ta bata iya buɗe ido ta gani,bare wani abun taban.
Sallama Hajiya zeenah tayiwa Hajiya ladi tareda bata haƙurin abinda ya faru,har sanann bata wani huce ba,ciki ciki take amsawa,ita a dole an taba mata rabin rayuwarta.
Takaici in yayi dubu to ya kama Madeenah har maƙoshinta.
Suna shigowa gida Madeenah ta shige ɗakinta tareda rufo ƙofah,har wajen magriba bata fitoba,Hajiya zeenah kuwa batabi ta kanta ba,dan ita ta manta ma da ita.
Tafiya take tana zuwa tana dawowa a falon,gabaɗaya abinda aminiyar tata hajiya Ladi ta faɗa mata take tunawa na jiya. Shin zayyi aiki ko bazayyi ba bata saniba,da aika a ƙiramata shi,har yanzu bai shigoba,so take ta ƙirashi cin abincin safe yau.
Maganar Iyani ce ta dawo da ita daga kogin tunanin data tafi. Amintacciyar mai aikinta,koh su Jabeer ma tashi sukayi suka ganta a cikin gidan,komai nagidan kaff tasani,saidai ba komai take saka baki a cikiba,mijinta kuma shine masinjan Alhj Aliyu,wanda bayan ya sauƙa a kujerar CEO ma,bai yasar dashi,sai yace suzo gidan su zauna.
Abinda Hajiya zeenah bata hana na da taji zancen,saboda tanajin daɗin aikin iyani sosai,komai tagani bazaka taba jinsa a wajen wani ba.
“Hajiya angama haɗa abincin yanda kika ce”
“Okay shikenan bari su ƙariso”
Tana nan tsaye a wajen Jabeer ya shigo shida Lubna,fuskarsu ɗauke da mamaki wai Hajiya zeenah taƙirasu karin kummallo a sashenta,abinda bai taba faruwa ba kenan,har lubna tace bazata zo ba,saidai kuma komai yakamata kaje kaga menene.
Kujera suka ja kowa ya zauna bayan sun gaisheda itah,iya Jabeer ta amsawa,luban kam ko kallonta batayi ba,itama data ga haka ta yatsina fuska.
Iyahni ce ta zuba musu abincin dukka kafin ta koma gefe.
Abincin suka fara ci,har sun kuka gamawa Hajiya zeenah ta miƙawa Jabeer kunun gyaɗa a cikin jug mai sheƙi.
“Ka kunun gyaɗa anyi,kaine mai sonsa sosai,nasan kuma yanzu baka samun arziƙin shansha tun mutuwar matarka”
Kallon lubna yayi ƙasa ƙasa kafin ya ɗauki jug ɗin ya tsiyanya a kofi.
Itakuwa lubna ko uhm batace ba,dan dama tasani sarai dan aci mata mutunci aka ƙirata wajen.
Bayan sun gama karawar ne wayar Jabeer tafara ƙara,yana dubawa yaga khalil ne.
Goge bakin sa yayi zai tashi,amma maganar Hajiya zeenah daya doki kunnensa ne yasashi komawa ya zauna.
“Koma ka zauna akwai abinda zaka min”
Tana gama faɗin hakan ta ciro paper da biro ta ajiye masa a gabansa.
Kallonta yake sanann kuma yana kallon paper da alamar tambaya akan fuskarsa.
“Ummah wanann kuma fah,wani saƙo zaki aika”
“Eh saƙo zan aikawa ta kusada kai,yanzu nnan basai anjima ba inaso ka rubutawa Matarka saki uku a jikin takardarnan ka miƙa mata”
Zaro ido Jabeer yayi yana kallon Hajiya zeenah,wacce ta turbune fuska kaman a soja a fagen ya ƙi.
“Ummah saki kuma,mai yayi zafi haka”
“Ba zafi ba har ƙonewa ma yayi,yanzu nan ka rubuta kana batamin lokaci,kuma umarni ba wai shawara ba……koka rubuta mata ka bata,ko kuma na tsine maka yanzunnan…….!
Wanne ka zaba??????”

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤06🖤

“Saki kuma ummah?”
“Eh saki haka nace,ko baka jiba kurmane kai nasake maimaita maka,ka rubuta sakinta ka bata tabar gidannan,bana sonta a cikin gidannan”
Yawu ya haɗiya mai nauyi kafin yakai hannunsa zuwa kan takardar,tambayoyine suka fara kwaranya a cikin ƙwaƙwalwarsa,meyasa sai shine,meyasa komai shikaɗai zai dunga faruwa dashi? Daga ya fita cikin wanann ifila’in sai kuma yasake shiga wani. Koyaushe shidai bazai daina fita daga chaƙwakiyar mata oho.
Biro ya ɗauka tareda takardar baya ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi.
Hannunsa yana rawa yakafa biron akan takardar,ko meyasa hannunsa da dukkan gabobin jikinsa suke bijirewa umarnin mahaifiyar tasa,zuciyarsa sai bugawa take a matakin daya fi na bugawar kowacce zuciya,ji yake kaman wata boyayyar igiya ta riƙe hannayensa ta hanashi aikata abinda aka umarceshi dayi.
Sautin amon dariyar Lubnah ne ya hanashi fara rubutun.
“Hahhaha Hajiya zeenah kenan,a tunaninki dan kawai kin ƙiramu kinyi wani ƙulunbotonki na lokaci kaɗan,saiki samu abinda kikeso daga gareshi?
Indai har duk lokacin dana ɗauka ina tsaye akan sa,wannan maganin naki zayyi aiki mai nayi kenan duk tsawon lokaci?
Hmm to bariki ji na faɗa miki,…..koda kinyi nasarar fitarda Jabeer daga cikin ikona,bai isa ya sakeni ba dakansa,kuma ya waye washagari da numfashinsa,saidai idan nice da kaina nace ya sakeni.
Anriga an gama maganin,an zuba a kogi ruwa ya tafi dashi,aikin da baya taba karyewa kenan,sai ankai ruwa rana.
Kinga kuwa kozai karye ba’a wajenki ba.
Zabi ya rage gareki Hajiya zeenah,zaki iya sakawa ya sakeni yanzu,amma shima zai mutu,saiki zaba shin zama dani ko kuma gawar ɗanki?”
Tana gama faɗin hakan ta tashi tabar falon ɗauke da murmushin mugunta akan fuskarta,inda ta bar Hajiya zeenah a zaune tana buɗe baki a sake.
Maida kallonta tayi ga Jabeer wanda ƙarfin maganin ya sakeshi,ya kwanta a wajen jiki a sake,da alama bacci yayi ma bai san mai sukeyi ba.
“Me….me nakeji haka ni zeenatu da kunne na?”
Tashi tayi daga dinning ɗin ta nufi ɗakinta,ko kallon Jabeer bata sake ba wanda bacci ta ɗaukeshi a wajen.
Bayan ta tafi iyani ce ta matso wajen tareda ɗebe kayan wajen,a ranta tana mamakin rayuwar masu kuɗi,ita kanta haushin Lubnah takeji,tana ga babu wanda yakaita jin haushinta,itace sanadiyyar mutuwar ɗanta.
Dan kawai ya karza mata mota ta saka akayi ta dukansa saida ya suma,bayan sati guda a asibiti yace ga garinku. Wannan abun yana ran iyani,wanda bata ganin zai gushe daga ranta,har randa ƙasa zata binne mata ido.
Ƙarar waya ce ta tashi Jabeer daga baccin da yayi akan dinnimg table ɗin,yana dubawa ya missed call ɗin Khaleel har wajen goma.
Mamaki abin ya bashi,musamman yanda ya kwanta bacci akan table ɗin cin abinci..
Lokacin wayarsa ya duba,kusan ƙarfe Goma,awa kusan guda kenan da rabi yana bacci. Motsa jikinsa yayi wanda yayi masa nauyi sosai. Tsayawa yayi cakk tunowa da yayi da abinda Hajiya zeenah ta umarceshi dayi.
To shida aka ce yayi saki mai yasa kuma yayi bacci,wata ajiyar zuciya yayi da godiya ga Allah da muryar lubna ta ceceshi dayin sakin,duk da baiji abinda take faɗa ba.
Lokacin dayake niyyar sakin baiji wanann tsoron dayake ji idan zai saketa ba,yanzu kuma tsoron yadawo cikin zuciyarsa sabo fill,bayason ma yaga takardar balle ya rubuta sakin a jiki.
Miƙewa yayi daga kujerar ya nufi ɗakin Hajiya zeenah,duk da cewar bayason abinda take buƙatar ya aikata,amma kuma yanajin babu daɗi ya tafi batareda yaji mai ya faru ba.
A zaune take akan Kujerar madubi tana kallon madubin.
Sallama yayi a hankali amma bata amsa ba,har zai ƙara wata sallamar a zatonsa bata ji mai yace ba,saikuma yaji maganarta.
“Sai yanzu ka tashi daga baccin?”
“Uhm mai ya farune na kwanta bacci nan take,sannan mai kuka tattauna da lubna”
“Babu komai,yayi kyau da baka san mai ya faruba,ka tafi aikinka kawai,nasan za’a nemeka,babu abinda ya faru,karka saka wani dakuwa a ranka”
Duk da cewar muryar mahaifiyar tasa ta faɗa masa sabanin abinda take faɗa,amma kuma tunda tace ba komai shikenan,shima sai yabarshi a akan.
Yana fita ya shiga motarsa driver yaja shi,har suka isa companyn yana tunani,amma yagagara samun ƙwaƙƙwaran wani abu guda ɗaya da tunanin ya bashi mai ma’ana.
A bagaren Lubnah kuwa tana fitowa daga sashen Hajiya zeenah ta cize fatar baki,dama tunda taji wai ƙiran zuwan karin kummalo tasan ba abinda arziƙi bane,saidai ta yanke shawarar taje taji damai surukarta ta tazo,ga zatonta kuwa wani abu suke kitsawa.
Basu sani ba dukkansu tafi ƙarfinsu,kallonsu kawai take daga iya gudun ruwansu,da tayi niyyar a asirce Jabeer karya kula kowacce mace a duniya sai ita,amma yanzu ta sanja shawara,hakan ya nuna tamkar tsoro take bata yadda da kanta ba kenan,dan haka zata bar koma wacece ta shigo cikin gidan,koba komai tasamu abinda zata dealing akan mijinta.
Murmushin mugunta tayi taresa ciro wayarta tana neman number bokan nata,da alamar shawarar data yanke tayi mata,zata ga wace marar tsoronce zatayi kishi da ita,babu wacce take kawowa a ranta sai Jawaheer,wacce dama tasan tana crush akan mijinta,saboda tana tsoronta ne shiyasa taja birki.
Ringing biyu wayar tasa tayi ya ɗaga tareda sakin wata dariyah.
“Madam Lubnah kin bani tazara,kuɗina sunyi kasa fah,gashi ke ba a ganinki sai kinzo muhimmin aiki,ke kaɗaice kike ƙirana na ɗauka nayi miki aiki batareda kinzo ba”
“Kaga zulumgum ba wanann ba,wannan aikin dazayi min akan Jabeer,kabarshi kawai na fasa,bashshi ya kawo duk wacce yakeso cikin gidan,sanann suma iyayensa su aura masa duk wacce suka ga dama.
Inaso ne kowacce tayi danasanin saninsa,bazan iya hakan ba sai kowacce tashigo cikin gonata,sanann zan ɗana tarko na kama akuyar data ke cimin Danga”
“Yanda kika ce madam,hakan ma yayi,ta nanne zaki dunga yin aikinki akansu kina horar dasu”
Sun ɗan daɗe suna maganar a wayar,dukka bai wuce na kisa ba da kuma na yanda zatayi nasara a rayuwa.
Iyani ce ta shiga ɗakin Hajiya zeenah ɗauke da lemo da kuma kofi a hannunta,dan dama ta saba takan kaimata lemo mai sanyi idan tayi irin wannan tunzurar,saidai na yau kaman yafi na ko yaushe,dan tunda ta shiga ɗakin da safe har azahar bata fito ba.
Hakanne yasaka iyani cikin tunanin ko ƙalau.
A zaune take a bakin madubin kaman ɗazu da Jabeer ya sameta.
A hankali iyani ta dan matsa kusada ita tareda yin magana a hankali.
“Hajiya yakamata ki dunga daurewa kina barin wani abun,girma yafara kamaki,karki jawa kanki wata matsala,tabbas babu dadi kam,amma wani abun a dunga bashshi shine yafi dacewa”
“Iyani iyani iyani na barshi ya wuce?…. Ke ganau ce ba jiyau ba akan abinda t tsinanniyar yarinyar tayimin,nifa na haifi yaron amma ta maidashi gabaɗaya ƙarƙashin ikonta,har faɗamin take tafi ƙarfin babu abinda na isa nayi..
Taya kike ganin wannan abin zai fita a raina na mantashi? Ji nake kaman nayi a hauka a halin yanzu,wannan la’ananniyar ta kaini bango fiyeda yanda kike zato,ta kashe wasu ta ƙuntatawa wasu,ta zalunci wasu,tunda tazo gidannan babu wanda ya taba jin daɗinta,ƙarin baƙincikin shegiya juya ce,bata komai saidai taci tayi kashi………”
“Eh to hajiya idan har abin ya dameki kuma kinaso kiɗau fansa har haka,mai zai hana nabaki wata hanya,saidai kafin nafaɗamiki zangaya miki gaskiya……..Ki gwada neman amincewar BOMBEE (BAƘAR AYAH)wataƙila ta yarda ta aureshi,idan ta baki wasu sharuɗɗan,tabbas zata magance miki duk abinda Lubnah take ji dashi,saidai fah……….”
“Saidai me inajinki wacece ita a ina take?”
“Uhm kawota cikin wanann ahalin naki tamkar kin ɗau wuƙa kin dabawa kanki ne,domin ko ke dakika kawota idan abinta yazo kanki bazata raga miki ba sam,ita din annoba ce da ba wanda ta bari,ko makiyinka bazaiso manna maka itaba ballantana kuma masoyinka hakan ma ke uwa ki aurawa ɗanki ita……ina gwanda miki fitinar Lubnah da nata fitinar”
“A wane waje take,ki sanar dani naje na sameta,sannan menene labarin ta”
“Uhm a garinmu take,saidai nima bantaba haɗuwa da ita ba,kasancewar ba a garin na girma ba,a wajen yan uwana nakejin labarinta,ƙarshen labarinta da naji ance wai Barikin sojoji sun koreta saboda fitinarta bazasu iya ba,ta koma jejin Garinmu da zama a can Gyembu”
“Soja kuma,soja ce ita?”
“Eh sojace tun tana da ƙananun shekaru da shiga,ban san mai yafaru ba dai kasancewar bandamu nasanta ba,amma naji dai ance ba kasafai yanxu ake ganinta ba,saidai in wani ya tabata tazo yimasa hukunci”
“Shekarar ta nawa,kinganin zata amince da abinda zan nema a wajenta,kincemin babu wanda yake sakata abu tayi sai taga dama,sannan kinsan fah lubna da asiri take kashe kishiyoyinta,bakya ganin itama zata kasheta? Koda yake in hakan yafaru ma babu abinda yadameni,indai zata min abinda nakeso shikenan”
“Hhhhh hmmmm hajiya kenan,ni kaina da labari kaɗan naji,nasan hakan bazai faru ba sam,amma dai tunda kinga zaki iya shikenan sai mu kama hanyar gobe inshaaallah,…..amma fah kiyi shawara kafin”
Iyani da faɗawa Hajiya da alamar ta farka da abinda take tunanin zatayi tun kafin lokaci ya ƙure mata.
Saidai Hajiya zeenah tayi nisa batajin ƙira,akan cikar muradinta na rusa Lubnah babu abinda bazatayi ba,inyaso koma mai zai faru ya faru daga baya.
Daga haka ranta yayi fari,ganin ta samu mafita akan abinda yake cimata tuwo a ƙwaryah.
Washagari da safe,da shirin tafiya Hajiya zeenah ta tashi,ina tayiwa Alhj aliyu daɗin bakin ta samowa Jabeer ne mata wacce zata aura masa,babu yanda bayyi ba akan karta kashe ƴar mutane a banza,amma kuma ta ƙeƙasa ƙasa,shiyasa ya ƙyaleta ya zuba mata ido. Wanda yace zai haɗiye gatari saika sammasa ƙota.
Itama iyani a daren tabawa mijinta labarin abinda yake faruwa,shi bai ce komai ba,dan dama hanyar dazai rama abinda Lubnah tayimasa yakeyi. Dan haka zanice ta tadda muje.
Bayan itada iyani sai mijinta,daga nan babu wanda yasan abinda zataje yi,shikansa Alhaji Aliyu bata sanar dashi wacece ba.
Da haka suka kama hanyar jihar taraba Hajiya zeenah iyani da kuma driver,sai tsarabar da sukayiwa iyayen iyanin.
Ita gaba takaita,koba komai zataje gida batareda ta kashe komai ba……….
Muje zuwa,yanxu labarin zai fara……….

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤07🖤

_________________________

GEMBU babban garine dayake Tsibirin MAMBILA a Sardauna local government dake jihar Taraba a nigeria.
Shine gari na karshe daga nan sai a shiga ƙasar camaroo,hakan nw yasa ya zamo gari mai tarin ƙabilu da kuma tarun yaruka,kama daga irin su Bummi wanda sune manyan ƙabilun garin,sanann kuma akwai Mbubo, Ngebu,Fulani. Wannan sune mafiya yawan mutane da ake samu a yankin,saikuma sauran mutane kaman su Igobo,Hausa,da yaruba,dama wasu daga cikin ƙasar camaroo,wanda mafiyansu kasuwanci ne ke kaisu wajen.
Gembu garine mai tarin ni’ima da kuma ban mamaki.wanda yana ɗaya daga cikin gari mai ƙasar noma ganyen shayi,ba iya ga nigeria ba har ma a africa.
Hakanne yasa wajen yazama mai albarka da kuma tarin hanyoyin samun kuɗi.
Saidai abu dayane yayi wa garin cikas,shine rashin hanyoyin shiga masu kyau,domin nan ma ba iya Nigeria ba,harga duniya baki ɗaya,hanyar garin gembu na ɗaya daga cikin hanya mafi hatsari wajen binta. Saboda manyan manyan tsaunukan da hanyar tabi ta kansu,wanda ake ƙiran su da “Gangirwal” wato a harshen Hausa yana nufin Dutsen mutuwa kenan. Tsaunukane masu matuƙar duhuwa da kuma halittun daji a ciki.
Wannan dalilinne yasa duk da kyawun garin,da kuma albarkarsa baya shiga ran mutane da dama,saboda hatsarin hanyar daza’abi wajen zuwan sa.

Kaɗan kenan daga labarin Gembu,wasu abubuwan zakuji idan muna cikin labari.

___________________

Tun sassafe suke tafiya har rana ta take,kafin suka isa garin Taraba,kasancewar basuda wanda suka sani,hakanne yasasu yanke shawarar kwana kafin gobe su haura mambila,wannan shawarar iyani ce,dan ta fisu sanin wajen.
A super market suka tsaya suka ci abinci,da kuma ɗan hutawa kafin su wuce hotel din da drivern yayi musu booking.
Hajiya zeenah ce takalli iyani wacce take cin abincinta hankali kwance,da alama dama ta saba da irin wannan tafiyar,ba kamar itaba wadda yawanci a jirgi takeyin tafiye tafiye,wannan ma dan tana so ya kasance sirrine shiyasa tayi ta a mota,amma babu laifi tanaji a jikinta kam sosai.
“Wai yanayin hanyoyin basu da dadi bi,gabaɗaya cikina ya hautsine,abicin ma na gagara cinsa da yawa”
“Uhm amma Hajiya inaga kici abinci sannan kuma ki huta sosai,da safema ki karya sosai,don abinda yake gaban mu babban aikine”
“Wane irin aiki kuma,duk wannan jololon drivern ne yaƙi gudu,da yanzu mun haura garin ai,ni na matsu na haɗu da yarinyar nan,naga ya take”
Hajiya zeenah tafaɗa tana yatsina fuska tareda zefah yankan wainar ƙwai a bakinta.
Itadai duk abinda take kallonta kawai take,kallon farko dan zakayiwa Hajiya zeenah kasan batasan wane irin abune yake gabansu ba,a zuwa cikar burinnata.
“Koda yayi gudu ma,bazai yiyu muyi kasadar haura mambila dare yayi mana a wajen ba,saboda hanyar tanada hatsari sosai,inshaaallah saidai gobe mu kama hanya da safe.
Daga haka Hajiya zeenah bata sake cewa komai ba,bayan kaman wasu mintuna ne wayarta tayi ƙara,tana dubawa taga sunan hajiya Ladi.
Kallon iyani tayi wanda itama tagani amma ta ɗauke kai,saboda abinda bai shafeka ba saika bishi da ido.
Da kaman bazata ɗauka ba,saikuma ta ɗauki ƙiran tareda ƙaƙalo murmushin dole tayafa a fuskarta,dan ita kanta tasan idan Hajiya ladi taji abinda yake faruwa,baƙaramin bacin rai zatayi ba,musamman daya zamo so take da tunda tsara komai idan ya danganci auren Jabeer ɗin.
“Hajiya ladi yakk ya kuma yaran?”
“Yara ƙalau,nace dan Allah batun business ɗina ne na dubai,ko zaki shirya ki rakani zuwa jibi,wlh wacce muke tafiya fa itane Yaronta ba lafiya”
“Ahah gaskiya nima bazan samu damar zuwa,dan yanxu haka ma bana gida na tafi ziyara gida,kuma zanyi a ƙallah sati kafin na dawo”
Ɗan jimm Hajiya ladi tayi,kafin kuma sukayi sallama ta ajiye wayar.
“Hmm bazan faɗamiki mai yake faruwa ba harsai na dawo,saboda karma kice baki yarda ba,abinda bazan iya jiba kenan,dan indan akan muradin tarwatsa lubna ne da ahalinta,banajin akwai mai yimin burki”
Duk maganar can ƙasa ƙasa takeyinsa,ita kanta iyani dake gabanta kaɗan kaɗan take jin abinda take faɗa.
Bayan sun isa masauƙinsu nan ma ba kwanciya sukayi ba,duk yanda iyani tayi da Hajiya zeenah ta huta ƙin amincewa tayi,dole saita bata labarin rayuwar garinnasu,wanda rabin tambayar duk akan Rayuwar Bombee ne,
Da safe ƙwanƙwasawar drivern ne ta tashesu,mai suna Iliyah,yaje kawo musu abi karyawa.
Nan ma bayan sunci sun shiryah kafin suka cigaba da tafi.
Kalle kalle suke ta windowa,ganin manya manyan duwatsu,ga kuma yanayin weather daya sanja nan take,yakoma liff liff har a jikin fata.
“Kai iyani amma garinku yana da kyau,wai dama haka yankin taraba yakene? Wanda bai zoba baiyi kallo ba”
“Kallo ma tukunna hajiya,nan bakiga komai ba”
“Koh ?”
“Uhm”
Suna cikin zancene aka ƙariso daidai inda hanya zata hau sama,tasha ce a wajen cike da mutane,drebobi kala kala,wasu suna saƙƙowa da motoci,wasu kuma suna hawa dasu.
Faka motarsu sukayi a gefe inda iyani tacewa Iliya ya tsayah,ita kuma tafita zuwa wajen direbobin.
Bata daɗeba sai gata tadawo wajen gefen hajiya zeenah.
“Hajiya munyi sa’a,munsamu drivern dazai haura damu,mungama ciniki dashi kuɗin zaki kawo a bashi.
Lokacin da Iyani ta faɗi kuɗin saida Hajiya zeenah ta zare ido tareda cewa.
“Ke wai wane irin driver kenan,inada driver ki hayomin wani yanzu nan kuma ki zugamin kuɗi,?”
“Hajiya wanann ai yayi kuɗin aikina na shekara,hauka ake?”
Iliya ya faɗa cikin ƙufula,ganin kuɗin da ake shirin bawa wani kawai ya haura dasu,bayan shi duk abinda yayi a shekara kenan.
“Haurawar banza,muja motar mu mana mu haura da kanmu,dole sai wani ya haura damu,shekara da shekaru muna tuƙi duk a haka zai tsayah”
“Toh koh daga haihuwarka kake tuƙi,babu ta inda zaka iyah haura hawan mambila batareda ka faɗa,abin ya wuce yanda kuke tunani…..,..Hajiya ki bashi kuɗin ya haura damu,idan ba haka ba wasu zasu hayeshi,saidai mu jira zuwa nan yamma kuma in wani ya saƙƙo”
Hajiya zeenah tanajin haka ta ciro kuɗin ta miƙawa iyani,bawai kuɗin ne batada shiba,kawai yanda ta bada kudinne a abunda bai cancanta ba take jin takaici.
Saidai kuma ya zatayi,iyani tariiga ta ga logonta,indai akan cikar burinta ne,ko ya ninka wannan ma zata bayar,yanzu ma jin zasu jira hardai yamma ne yasata miƙa mata kuɗin.
Shikuwa iliyah ganin dagaske kuɗin za’a bawa wani lokaci guda,yasashi jin takaici a ransa,har yafara yankewar cewa zai dawo wajen da aiki.
Bayan iyani ta tafi da bashi kuɗin,sai gashi sun dawo taredashi,kansa irin cibi cibi ɗinnan,baki baƙiƙƙirin,gashi irin mutanennan ne kaman iska zata huresu,cikin ƙaƙau kamar itace.
“Heee hajiya gaskiya fah kinyi sa’a mace kika turo akayi cinikin,bilahillazi da banni da tausayi akan mata koh ninkin wanann kuɗin bazan karba ba,dandai ina son kaiwa balance wajen ogah ne a yau,shiyasa ma na karba wallahi.
Yaya kun shirya ne mu haura,ko kuma zaku sake shiryawa”
Ya ƙarisa maganar yana cize baki”
Zaro ido Hajiya zeenah tayi tana kallon iyani,wacce bataji tsoro ba kaman itada drivern. Wai wannan ne zamu shiga cikin mota ɗaya dashi muyi tafiya?
Ganin sunyi shuru basuce komai bane yasashi buɗe gaban motar yana shirin zama akan iliyah.
Sauri yayi ya matsa,yayinda wani warin gardawa ya bugeshi,cikin ƙanƙanin lokaci ya kaure cikin motar.
Koƙarin toshe hanci Hajiya zeenah takeyi,saidai kuma tana tsoron su haɗa ido da sabon mutumin ta madubi,yagane danshi suke toshe hancin. Tunda ya takalleshi sau ɗaya wani mungun tsoronsa ya zartu cikin zuciyarta,batajin zatayi gigin tunzura zuciyarsa bare taga mazayyi.
A wajen iliyah ma hakan take,abinne yabashi mamaki ganin yanda yakusa zama akan cjnyarsa,amma ko kulada shi ma bayyi ba,hankalinsa yana kan motar daya shiga yanzu.
Abubuwan ta ya fara duddubawa yana wage baki,da alama yanayin motar yayi masa yanda yakeso.
“Heeeehuuuu kai kai,rabona dana tuƙa lafiyayyar motar zuwa gembu harna manta,kullum saita yan iskan direbobin hanyar nan,amma yau kam za’ayi ɗiba tafiyah bilahillazi,irin wannan mota haka mai girma?”
Ya faɗa bayan yagama kurma ihun,sanann kuma ya ƙara da dariyah irinta tantirannan.
To to bil’adama a ɗaura belt maza,zamu hau ga sansanin aljanu,yanzu zamu fara da sama ta ɗaya,har zuwa sama ta takwas,daganan kuma sai ayi gangara,wanda bayason yayi karoda abinda zai dunga farautar mafarkinsa,wato masu ƙananan kuruwa a cikinku su rufe ido,zamu fara aiki.
Duk maganar dayake kallonsa kawai suke,da duk cikinsu iya iyanice kawai tasan mai yake nufi,ita kuwa batasamu damar faɗa musu abinda yake nufi ba taji yafara jan motar. Dan haka iya faɗamusu tayi su suka belt,daganan kuma aka fara tafiyah.
Giya ya danna tareda takar motar ya ɗorata sama.
Ganin yanda yake shirin takar motar kaman yasameta a jari bola,yasa iliya koƙarin yimasa magana,saidai tun kafin yace komai yaji kaman an ɗaga motar a sama,saboda yanda suke ƙoƙarin hawa wani uban tsauni dayake gabansu.
“Hahhhah inason kallon wannan yamayin a fuskar abokan kasuwan ci,karku damu domin ƙiran sunana ku zageni,kuna cewa karka kashemu tsinannan Allah,banshiya mutuwa ba wayyo……to kuce min TORO sunan kenan,kunga zaku fi daɗin cewa ”Allah ya tsine maka toro” ihu shagali”
Yana gama faɗin hakan kuwa ya hango idon Hajiya zeenah,wacce tamanne a jikin kujerar bayan,idon ta sun firfito kaman an jijjiga bera a buta……
“Hajiya tundaga hawan farko har kin yi laushi,todai karki manta ki adana kuɗinki fah,don kowanne hawa akwai nasa ƴan fashin,in bakida kuɗi a miki dukan kuɗin.
Yawan hawanki da shiga duhuwar dajin gangirwal,yawan gamuwarki da rabonki………muje zuwa……

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤08🖤

Hasashen sa kuwa bai tafi a banza ba,dan Hajiya zeenah tanajin an fara gangara ta mulmulawa toro ashar.
“Kai kuwa wanne ɗan rashin arziƙine,kashe mu zakayi bayan ka karbi kudi,wannan wane irin wajene na kawo kaina ni zeenatu,akan wata biyan buƙata ta duniyah. Juya juya damu na fasa zuwa garin waje saikace hanyar aljanu”
Juyowa toro yayi yana dariyah,tareda ƙarewa mutanen cikin motar kallo kafin yace.
“Ai hajiya tunda har muka ɗau hanya tofa sai munkaita casss,kuma banda abinki hawa ɗaya fah muka hau,harkin sare da tafiyar. Hm aikinci sa’a ma da ba motar ogah kika hauba,Aradu ta inaga mutuwa zakiyi muss kafin a isa,maza ma kwakwalwarsu juyewa take idan suka hau motarta zuwa gembu bareke.
Ki gode Allah ta ɗau hutu bata nan hanya bata haɗaku ba”
Duk maganar dayake Hajiya zeenah kwatakwata bata gane mai yake nufi,dan zuwa yanzu ɗankwalin ta ma yabar ƙoƙon kanta,batun gyale kam tun a hawan farko sukayi sallama.
Wani tsaunin ya nufa da mungun gudu,take kuwa su iliya suka sake zare ido tareda salati mai cikeda ihu.
A haka sukayi ta gwabzawa har zuwa wasu daƙiƙu masu yawa.
A lokacin duk wanda yaga Hajiya zeenah bazaice itace wannan matar ba mai kwalisa da kuma izzah,jikinta duk yayi dama dama da aman abincin dataci da safe,idonta yayi zuru zuru kaman wanda tayi azumin shige.
Zuwa yanxu sunyi hawa mai nisa akan tsaunin,dan sun fara shiga waje mafi duhuwa a kan wajen.
Ƙara gudun motar sukaga toro yayi tareda zurawa hanyar ido yaga ta inda wani abu zai bullo.
Aikuwa hasashensa bai tafi a banza ba,dan wasu mazane suka fito sun shafe dukkan jikinsu da da baƙin shuni,gasu murtuƙa murtuƙa,fuskar nan babu alamar rahama.
Kashe motar Toro yayi tareda waigowa ya kalli iyani,dan duk cikin motar ita kaɗaice mai ɗan dama dama a ciki,duk itama haka take kaman gawa taƙi rami.
“Keee ki kama wannan matar ki gyara,wani plan zamu haɗa,idan kuma ba haka toba tara ba har ɗari ma kunshiga a wajen wanann arnan dajin. Ni babu abinda zasu min,amma kukam bazasu ragamuku ba”
“Meyasa bazasu ragamana ba toh”
Iyani da samu damar tambayar sa cikin ƙarfin hali.
Wata soyayyar dariyah yayi kafi yasake zubamata ido wanda yasha kwalli marau.
“Iyata kenan aini da kike ganina bazasu tabani ba,saboda ni yaron BB ne,babu wanda ya isa taban a cikinsu idan na nuna musu tambarina na ƙungiyarta”
Yafaɗa yana nuna musu wani tatoo ɗin baƙar macijiya a wuyansa,an rubuta BLACK BLOOD CLUB(BB) a gefenta.
“Menene BB yake nufi kuma”
Kungiyarmu kenan,wanda shugaba take jagoranta,idan kanaso kayi tukin mambila kuma ka dunga fita lafiyah,to ka shiga kungiyar BB,muna kaiwa kudin duk wata wajenta,itakuma tana yimana shamaki da duk mai kawomana cikas daga cikin aranan jejinnan.
Suma kuma tayi yarjejeniya dasu bazasu taba yaranta ba,ita kuma zata barsu suyi nasu aikin”
“To baka ganin zasu kamamu dukka hadda kai,musamman ma idan yazamo bata nan bare ta ceceka?”
Iliya ne wanann karon ya samu damar tambayr tasa,dan bayan shugowar su cikin jejin,bayan wannan majanuniyar hanya ya kuma samun wani abin mamakin.
A yanzun ma saida toro yayi dariyah kafin yace.
“Hhhh duk yanda zan faɗamaka bazaka ganeba,duk da cewar akwai kishi kishin labarin cewar bata cikin jejinnan a yanzu,tana can kan ainihin dutse,tana rainon ɗanta data haifa wata biyu da suka wuce……duk da haka babu wanda ya isa ya taba ko dabba idan nata ne a cikin jejinnan bare kuma ku yaranta,inda badan suna tsoronta ba,mu kanmu bazasu barmu da sana’rmuba.
Amma yanxu duk wanda ya matso kusana na nuna masa tambarina amma kuma yaƙi barni,kawai dannan signal ɗin jikina zanyi,daga nan ita kuma zata ga inda duk nake…….hmmm karkuyi hasashen ma wane hukunci zasu fuskanta,saidai su tashi daga jejin gabaki ɗaya kafin tazo farautarsu”
“Tambaya biyu zanyi maka malam toro.
_shin taya zata gane sune suka tabaka to?
_sannan shin bata hanaku bayarda wanann bayanai nata mai hatsari,iyah a mota muka haɗu dakai,amma kuma harka bada wannan labarin dangane da ita,baka ganin kaima zaka iya sakata cikin matsala da wannan labarin?”
Kallon iliyah toro yayi bayan yaji mai faɗa,da wani mai shugabanne daya shiga tunanin irin bayanan daya basu,amma toro ko a jikinsa,saima ƙara kwanciya dayayi a jikin kujerar matuƙin motar.
“Amsarka ta farko,signal datake jikinmu ba guda ɗaya bace,idan mai bincike ne yakamamu da wacce zamu aika,idan aranan jejine da wanda zamu danna,idan kuma namun dajine shima da wanda zamu danna,idan kuma hatsarine shima da wanda zamu danna,in mutuwa kuma mukayi akwai wacce zata kawo da kanta.
Tambayarka da biyu kuma,bata taba cemana karmu bada bayananta ba,hasalima neman abu take wanda zata lakato wani,amma kuma babu wanda yake kulada sha’aninta,sannnan a yanda na kejin labarin ta,bata son masu mulki da masu kuɗin ƙasar nan,Sannan duk da kasancewarta jami’ar atsaro a ,yanzu kuma ko sunan bata sha’awar jinsa……..
Lahh na manta abu ɗaya ma,wani naji kace bana tsoron kukai labarinta,dan yarusulu ku kai labarinta,intaga dama ko gawarka baza’a ganiba bare kakai labari,abun ai ba yanzu aka faraba………”
Shuru motar tayi kowa yana saka labarin toron a mahangar tunaninsa,indai abinda yafaɗa da gaskene,to kuwa wannan wacece haka ,mutumce kuwa?….
Shawarar da toro yabayar suka yarda da ita,duk da saida aka tsayah hajiya zeenah ta kintsa jikinta tukunna,fuskarta kaman tayi gudawa dan rama.
Shiryawa sukayi akan Hajiya zeenah ƴar uwar mahaifiyar ta ce,saikuma iliya da iyani yaranta ne.
Cikin ɗarɗar da addu’ar Allah yasa aikinsu yayi suka fara tafiyah zuwa cikin duhuwar jejin.
Wasu irin bishiyoyine a cikin dajin masu manyan manyan ganye,da alama suna samun ruwa yanda yakamata,duhuwar da suka bayarne yabawa arnan dajin samun damar kaiwa sumame batareda matsalaba.
Lura sukayi da yanda toro yafara tafiyar da motar ta siga daban,hakanne yaƙar hauhawar gudun da zuciyarsu takeyi zuwa wani mataki mai yawa.
Signa yayi Iliya dayake gefensa tareda yimasa alamar ya suna zuwa.
Aikuwa kaman kiftawa sukaga mutane sanye da baƙaƙen kaya sun dira a gabansu,hannunsu riƙe da bindiga wasu kuma da kwari da baka.
Hailala da salati hajiya Zeenah tafara tana zazzare ido,ƙiris take jira taji ta inda za’a kawomata farmaki.
Wani daga cikinsu ne ya matso inda motartasu take,da alama shine shugabansu,dan yana sanye da jan ƙyalle maimakon baƙi kaman na sauran.
Yare suka fara shida toro,wanda su Hajiya zeenah basa jin mai suke faɗa,da alama ɗaya daga cikin yaren yankinne,bayan kaman wani lokaci ne ya juyo ya kalle su,fuskarsa da alamar mutuntawa ba kaman ɗazu ba,babu tantama Toro yasanar dashi dangan tarkasu da ogar tasa kaman yanda ya tsara.
“Hajiya ina wuni fah ya gidah?”
Yafaɗawa Hajiya zeenah cikin hausarsa da daƙyar ake ganeta.
Gyaran murya Hajiya zeenah tayi tareds tattaro dukkan jarumatarta,ta amsa masa gaisuwar batareda da sake haɗa ido dashi ba.
“Hajiya ƴaƴan ki ba irin kayanki mai kyau jikinsu,ke wane irin uwane kam?”
Zuru tayi tana kallonsa,sai yanzu da kulada kayan jikin iliyan,wata maleliyar riga ce a jikinsa,da kuma wani wandon jeans koɗaɗɗe,gwanda ma ita iyani tasaka atamfa mai fasali.
Rufe ido tayi tareda cewa
‘Iliya wataran shi zayyi ajalina da wannan shegen shigar tasa,badama a bashi kaya ko a bashi kuɗi ya siya saiya sayar ya kashe kuɗin’
Maganar toro ce ta risketa tana tsaka ta maganar zucin.
“Ka ganene,hakan ra’ayinsane,sannan kuma batare suke da hajiyan gari ɗaya ba,tafiya ce ta haɗasu yau”
Kallon rashin yarda ogan yabi toro dashi tareda cewa.
“Toro kasake rena mana hankali ne fah? Dama kayi mana wasu kwanaki fah?”
Mazewa toro yayi ganin suna son ɗagoshi tareda yin magana yana haɗe rai.
“Kaga ogah wannan ba irin na wancan bane,ni yaushe zan hanaka karbar kuɗi a wajensu,kawai dai aikin shugabane ne shiyasa,inkuma kana ganin na barka ka tabasu,sai ku ƙaƙare da ita toh”
Nazari ya tafi,yana shakkar ya kamasu kuma toro da gaske yake,yabarsu kuma toro ƙarya yake masa fah,gashi rukuninsa tunda suka fito basu kama ko ɗaya ba sai yanzu.
Haka suka cigaba da magana,babu yanda ya iya yabarsu suka wuce,dan idan yakamasu kuma toro da gaske yake to kashinsa ya bushe a wajen shigabansu,don idan BB ta tashi saita ƙwaci kusan kuɗin dasuka yi shekara suna tarawa.
Da haka su Hajiya zeenah suka tsallake tujarar mutanen dajin da taimakon toro.
Tafiyah suka cigaba dayi cikin hawa da sauƙa,zuwa lokacin babu zancen ihu ko kuma firgici,sunyi shuru sun miƙa lamarinsu ga mai duka,suna jiran sanda zasu jisu sun faɗa ko kuma toro yace musu sun iso.
Bayan gwarwarmayar da suka shiga daga ƙarshe sun kai ga isa garin gyembu shazaran majaran.
Iyani ce mai ɗan karfin hali a cikinsu,ita tasamu damar yiwa toro godiya da taimakon da yayi musu,dan har gida ta roƙeshi ya kaisu,saboda a halinda iliyah yake ciki bazai iya tuƙa motar ba
Duk abinda ake Hajiya zeenah bata sani ba,gabaɗaya hankalinta baya jikinta a lokacin.

………Toh su Hajiya zeenah tundaga yanzu anyi laushi,burin zao cika a haka kuwa?……

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤09🖤

Buɗe ido tayi ta kalleta a wani ɗaki mai rufin zana,saidai yanayin zanar wata kalace daban mai ƙarfi da kuma adon rawaya rawaya.
Abinda ya farune yafara tariyowa cikin ranta.
Kama daga fitowarta daga gida neman wacce zatayi mata maganin lubna,harma da kuma shigowarta wata duniya sabuwa da tayi.
Zabura tayi ta miƙe tareda ya mutsa fuska,jikinta yayi tsamin kaman anyi mata dukan tsiyah.
Tambaya tafarayi a cikin ranta,akan nan ɗin inane,batakai ga samun amsar tambayar ta ba,kokuma son tunowa yaushe ta shigo wajen ba,ta kalli labulen ɗakin ya motsa,da alama wani ne ke son shigowa a cikin ɗakin.
Zurawa baƙin ƙofara ido tayi,yayinda bayan kowanne daƙiƙa zuciyarta ke hawar da bugunta zuwa matakin sama.
Sauƙe ajiyar zuciya tayi tareda runtse ido ganin ba kowa bace ta shigo face Iyani.
Tana sanye da wasu irin kaya da bata taba ganinta da irinsu ba,hannunta kuma ɗauke da akwashi guda uku akan akan faifayi.
Murmushi tayi tareda ajiye abin hannunnata kana tace.
“Ina kwana Hajiya sannu da tashi,ya jikin?”
Batareda ta amsa gaisuwar ba tafara jefowa iyani tambayoyin data kasa bawa kanta amsarsu.
“Menene ya faru bayan barin mu jejinnan,sannan nan inane?”
“Uhmm Hajiya suma kikayi lokacin da toro ya sauƙemu,bayan munshigo garine na roƙeshi ya kawomu har ƙofar gidanmu,kasancewar ni ban iya tuƙi ba,shima kuma iliya a lokacin bazai iya tuƙi ba”
“Yanzun wane lokacinne,tun yaushe nake kwance?”
“Eh tun jiya da yamma,yanzu kuma karfe 9:45am na safiyah.
Yakamata kici abinci kiyi wanka sannan ki rama sallolinki,kafin kuma muyi maganar abinda ya kawomu”
Tana gama bata amsar ta buɗe kwanukan da suke gabanta,ɗayah tuwon Doyane,ɗayan kuma miyace mai kala kalar ja da kuma baƙi,wanda Hajiya zeenah bata taba ganin irinsa ba”
“Wannan kuma mai nene?
“Uhm ɗayane daga cikin irin abincin nan yankin,muna dayawan doya sosai,shiyasa yawanci abincinmu muke sarrafata dashi,baƙin cikin miyar kuma kifine da kuma busashshen inibi,kici akwai daɗi sosai.”
Daga haka tabar ɗakin domin bata damar samun cin abincin.
Kaman mai tsoron kada taci ta mutu haka ta tsoma hannunta a cikin miyar takai bakinta domin ta ɗanɗana.
Uhm babu laifi fuskarta ya nuna abincin yayi daɗi,babu bata lokaci tafara yankar tuwon doyar tana ci,har saida taji cikinta ya ɗauka tukunna.
A ranar basu samu damar fita zuwa gidan su Bombi ba,saboda har yanzu jikinsu bai dawo normal ba daga tafiyar da suka niƙo.
Iyanice ta kalli mahaifiyar su wacce take zaune tana bushe tsinkayen da suke cikin ganyen shayinta,maganar da iyani tayi ne yasakata tsayawa da abinda take takalleta.
“Inna ina labarin Bambi kuwa,wacce da addah ke bani labarinta?”
“Oh ɗiyarnan,ke kuma mai zakiyi da labarin bombi har kike tambaya,na daɗe banga mai son yaji sunanta ba ma ,ballantana kuma labarinta”
“Ayyah inna inaso na haɗu da itane,akwai abinda nakeso muyi magana da ita akai,gidansu zakiyi min kwatance?”
“Handi mee Iyani,ki haɗu da Bombee?,akan wanne babban dalili haka?”
“Lahh bafah abune babba sosai ba,dama Hajiya ce takeson yin magana da ita”
“Hajiyannaki dan batasanta bane hala,tun wuri ina yimuku kashedi ku fita a harkar wannan yarinyar,dan ita ɗin tauraruwa ce mai wutsiya,ganinta bashida alheri ko kaɗan,maza ma basuja da sunanta bare kuma ku da baƙine,bakusan komai a gameda garinnan ba da kewayensa”
Shuru iyani tayi tana kallon mahaifiyar tata,da alama bazata samu amsar da takeso ba a gareta sam.
Tashi tayi ta nufi ɗakin da Hajiya zeenah take,tun kafin tace wani abu Hajiya zeenah ta dakatar da ita tareda cewa.
“Naji duk abinda innarki tace iyani,tabbas daga yanda nakejin labarinta a bakin mutane,ita yarinya ce mai hatsarin gaske,saidai nayi tafiya mai nisa nazo garin da take,bazan iya tafiya haka hannu rabbana ba batareda na ganta ba,idan itace taƙi amincewa buƙatata to shine zan haƙura”
‘Jinjina taurin kai da kuma Ra’ayi irinna hajiya zeenah tayi,a zatonta jin labarin inna zaisa tace ta fasa,amma kuma ashe abin ba haka bane’
“To shikenan Hajiya zamu je gidanna su a gobe inshaaallah,koma menene sai muji mai zatace”

___ ____ ___

A bakin wajen wani mai shayi iliya ya tsayah ta motar,tareda fitowa ya nufi wajen da samarin ke zaune a waje.
Sallam yafara yimusu suka amsa,kafin ya tambayesu abinda yake nema.
“Bayin Allah idan bazaku damu ba dan Allah gidan su Bombi muke nema?”
Kowa zaro ido yayi yana kallonsa ,wani kanma daya kurbi shayi da biredi,bai san lokacin daya furzar dashi ba yana kallon iliyan.
“Kai amma kai baƙone a garinnan koh,rabon danaji ance gidan su bombi shekaru da dama,ai kawai kace mana gidan su Innayee,waye ma yasan gidannan danasu bombi,ko mutanen gidan bazasuso ka haɗata da gidansu ba,amma jirani nagama shan shayi na rakaka gidan,maƙwantanmu ne katanga ɗaya”
Yana gama faɗin hakan ya cigaba da cusa biredinsa,iliya yana tsaye yana jiransa har yagama kafin yazo suka nufi wajen motar.
“Kai kuma daga cewa zaka tambayo gidansu saika yi tafiyarka, kaman an aiki bawa garinsu,wannan kuma wanene a tareda kai,a shegen surutunka har kayi aboki a garinda baka sani ba koh?”
“Ahah hajiya wannan ɗin ɗan anguwarsu su bombinne,na jirashi yagama shan shayine,akan zai rakamu gidan”
Kallon ta fahimta tayi musu kafin da ɗauke kanta.
Zagayowa yayi ta zauna a wajen zaman banza ba gefen drivern kafin suka fara tafiyah.
Tunda suke tafiyah babu wanda yace uhm a cikinsu,sai iya saurayin dayake nunawa iliya inda zaibi,da haka har suka ƙariso ƙofar gidan su bombin.
Sallama yayi musu tareda cewa.
“To ga gidan da kuke nema kun ƙariso,Allah ya baku sa’a sannan ya fitarku matsala,ni nayi nan”
Baƙin ƙofar gidan suka ƙarisa tareda yin sallama,da har sun sare akan babu wanda zai fito,sai kuma sukaga wani dattijo fari sol mai ɗan tsayi kaɗan ya fito daga gidan.
Gaisawa sukayi hannu da hannu da iliya kafin yayi musu iso zuwa cikin gidan.
“Lale maraba daku,daga ina haka kuka zo”
“Eh to tafiya da nisa malam,ko zamu iya shiga mu zauna”
“Eh to mai zai hana”
Tun daga bakin zauren gidan yake ƙwalawa matar tasa ƙira.
“Yawuro ina kike so munyi baƙi daga waje mai nisa”
Farar dattijuwa ce tafito daga ɗakin,fuskarta cikeda fara’ah,kana ganinta kaga wayayyiyar mata.
“Lale marabanku da zuwa,sannunku da zuwa”
Cikin annashuwa da sakin fuska ta tare su,duk da kasancewar bata sansu ba.
Ruwa aka kawo musu mai sanyi tareda kindirmo,domin kowa yakallesu dama yaga wayayyun fulani masu cikeda ilimi,domin duk yankinsu su dama fulanine a wajen.
“Innayee maza kizo ki gaisheda baƙi mana,sau nawa nake faɗamiki banason wannan halin na kunyah sosai”
“Lahh mace ai ana sonta da kunya,musamman a wannan lokacin”
Hajiya ta faɗa itama cikin fara’ah.
“Eh to hakane,musamman ma kinga mu fulani hakan a cikin jininmu yake”
Suna cikin maganar ne farar yarinyar tafito daga ɗakin kanta a sunkuye,a gaban su Hajiya zeenah ta tsugunna tareda gaishesu ƙaramar murya mai sanyi,kayan Makaranta a jikinta,da alama islamiyyah zataje.
“Ina kwana Hajiya ya hanya”
“Lafiya kalau,makaranta za’aje kenan,to Allah ya taimaka”
Motsin mutum sukaji yana shirin fitowa daga wani ɗaki take kallon na Yawuron.
Wata matace tafito daga cikin ɗakin tana shashima bangon da take bi.
Duk da kana kallon yanyinta zaka hango tana cikin yanyin laluri,amma kuma fatarta fari sol,ga idonta kuma dara dara,saidai da alama basa aikinsu da kowanne ido yakeyi.
“Innayi innarki daneji ta fito,rakata banɗaki dannan buta a hannunta,da alama bayi zata zaga”
Tun kafin ta rufe baki innayin ta tashi tareda ƙarisawa wajen wacce aka ƙira da Danejin.
Duk abinda yake faruwa su Hajiya zeenah suna kallo,har innayi takai matar banɗaki ta dawo da ita ɗakinnata.
Sallama tayiwa su Hajiya zeenah da kuma innar tata,kafin ta tafi makaranta.
Malam Ahmadu yashigo gidan tun bayan da yayiwa su Hajiya zeenah iso ya fita.
“To Hajiya muna jinki mai yake tafe dake,domin bamu wayeki ba,gashi kince mana wajen mu kika zo”
“Eh hakane malam wajenku nazo,idan baxaku damu ba dama wajen ƴar ku nazo da magana muhimmiya,shin kozan iya ganinta?”
Murmushi Yawuro tayi,da alama hasashenta yazama gaskiya,neman iri hajiyan tazo nema a wajen su.
“Ai Hajiya kin riga kin ganta,saidai ko kuma maganar manyan yanzu daza’ayi”
“Ahah baki fahimceni ba,bombi nake nufi,akwai abinda nakeson tattaunawa da itah”
Tsitt wajen yayi kaman an ɗauke ruwa,yayinda murmushi da kuma fara’ar dayake fuskar mutane biyun ya bace nan take,babu abinda ya maye gurbi zai mamaki da kuma baƙinciki.
Baki buɗe suka tsaya suna kallon Hajiya zeenah,kafin daga baya mlm Ahmdu yasamu ƙwarin gwiwar cewar.
“Uhm Hajiya inaga kinyi batan gidane,amma ni ƴata guda ɗayace Khadeejatu(innayi),bayan ita kuma banni da wata”
“Amma mlm an ce mana nan……….”
“Ya isa haka hajiya,tun inaganin girman ki,kina ganin nawa ki daina kawomin wanann zancen,idan kuma kin dage dole saikin samo mai sunan da kika ambata,to ki tafi jeji can inda yadace da mai sunan,amma banan ba gidan mutunci”
Yana gama faɗin hakan yatashi yayi waje.
Itama yawuro kallonsu tayi tareda cewa.
“Dan allah kozaku iya tashi,ina son naɗe tabarmata da kuke zaune akai”
Cikeda mamaki Hajiya zeenah suka tashi suna kallon Yawuron da lokaci ɗaya ta sauya daga matar da ta tarbesu.

Toh fah yaya takene?…….

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤10🖤

Har suka fito daga cikin gidan su bombin babu wanda yacewa wani komai,saboda ɗumbin abin mamakin da suka gani.
Magana suka ji a gefensu,suna waigawa suka ga ashe saurayin daya rakosu gidanne,yana jingine a bakin motar tasu.
“Sannunku da fitowa,na tabbatar masu samu amsar abinda kukaje nemaba”
“Taya kasan hakan,ko shiyasa ka tsaya kana jiran mufito,kenan kasan inda take?”
“Eh to nasani bankuma sani ba,kunsan ance ba’a aikin banza,zan nuna muku hanyar dazaku bi ku sameta dai.
Amma daman batun ku tsaya cikin gari kuna nemanta bazaku taba samunta ba,wanda suka sani ma bazaku kaiku ba,saboda gudun abinda ke iya zuwa ya dawo.”
Karisawa wajen motar sukayi inda saurayin yake tsaye,Hajiya ce ta kalleshi cikin maganar serious tace,
“To shikenan naji zan biyaka idan ka fadamin inda take,amma kafin sannan inason nasan ita wacece daga abinda ka sani,saboda daga yanda naga iyayenta fuskarsu sauyawa tayi lokaci guda,dan na ambaci sunanta,menene dalilin hakan.
Tunda kace maƙwantansu ne kai,to bashakka kasan wani abu dangane da rayuwarta”
“Zaro ido yayi kafin yayi murmushi,dan da alama bayyi zaton zata nemi sanin tarihin bombi ba,amma kuma koma wanene yaga abinda ya faru,dole zai zargi wani abun”
“Tabbas hakane nasan bombi ciki da bai,kuma inaga bayan mutanen gidansu babu wanda yasan ta kamanni,kasancewar ni ɗan ɗakin mahaifiyarta ne ina yaro,saidai amma saikin biyani,sannan kuma saikin min alƙawari babu wanda zai san na faɗamiki wanann labarin,saboda kar in kinji labarin ta ki fasa neman ganinta”
“Namaka alƙwarin babu wanda zaiji,sannan kuma zan biyaka kamar yadda ka buƙata,kawai burina shine ka faɗamin gaskiya”
“Inshaaallah zan faɗamiki gaskiya,amma kafin sanann mu shiga daga motarku,gudun mutane kar su ganmu,dan idon mikiya ne da ita,tana da mutane a wurare da dama a ko’ina.
Ina tsoron kar na samu matsala”
Amincewa sukayi da zancen saurayin,koba komai hakan yafi da tsayuwarsu a wajen.
Barin ƙofar gidan sukayi,tareda kama hanyar da yace su bi.
“Da farko kafin mu fara sunana Umar,ana ƙirana da MARUJE,labarin daya faru shekara ashirin da biyu baya,ya fara ne……………..

_______*****________

Ayyiriri ayyiriri,Malm Ahmadu ya iyo amaryah a hayin Fulanin yanki, masu ƙura,itace ta farkon mace wacce aka aura da Garesu.
To ikon Allah,shikuma mai takaishi auren ƴarsu,ana fa cewa iri irinsu mayune,shine yaje ya ɗakkowa kansa irinsu,ƙyan ɗan macijine fah dasu wayannan mutanen,lallai Inna laari taga takanta,saita san irin zaman dazatayi da ita. Su fah maza kana zaman zamanka sai su ɗakko maka alaƙa ƙai,daga kawai ta shekara uku babu rabo shine har ya manta soyayyar da sukayi dandali ya auro mata fulanin ƙaurah”
“Hmm kema dai kya faɗa,muma ina gashinan masu haihuwar ma anyi mana kishiyar daga shekara biyu da aure,maza ai sai a barsu”
“Larai ta faɗa tana nuna Innar muruje da baki,wacce take alwalar Azahar”
Duk abinda suke tana jinsu,amma ko ci kanku bata ce musu ba,saima shigewa ɗaki da tayi.
Dare yana kawo kai guɗa ta cike anguwar tasu da kuma raye rayen fulani sama sama,wai hakan ma ba’ayi wani bidiri da al’adu ba,kasancewar iyayen yarinyar basason auren.
Malm ahmadu ne yadage akan sai ya aureta,lokacin daya ganta takai nono gonarsu talle,dayake yana kuɗi a lokacin sosai,duk anguwar babu wanda yakaishi girman Gonar Ganyen shayi,gashi yanada hanya sosai a kamfanonukan da suke siye da siyarwa dasu.
Tun daga bakin ƙofar shigowar tasu LAARI ta fito da fara’arta ta tarbi Amaryartasu. Al’amarin daya bawa aminanta ma mamaki,ba iya su dangin amaryarba,dan kafin shigowarsu babu irin abinda su Larai da danginta basuce ba akan abokiyar zamannnata ba,amma tayi shuru tai biriss da abinda suke cewa,sai daga shigowar amaryar ta bawa kowa mamaki.
Duk da hakan ba abine dama da bazai iya faruwa ba,kasancewarta mace mai shuru shuru kuma marar hayaniya,sannan kuma ta yarda mijinta,tunda tasan badan yana ƙinta yayi mata kishiyar ba.
Har ƙofar ɗakinta ta rakata tareda buɗe mata kai.
“Sunan Laari,nice Abokiyar zaman ki dakika shigo gidannan kika tarass,ina fatan zaki ɗaukeni kema abokiyar zama,sannan kuma zaki bani hadin kai mu samar da zaman lafiyah,Allah yasaka albarka da zaman lafiya a zamantakewar mu”
“Ɗan murmushi Daneji(an samo sunan ne daga Alamar “fari” a harshen fillanci,Ainihin sunan ta shine Fatima,taci sunan mahaifiyar baffansu. To kasancewarta fara sosai ko a gidansu yasa ake ƙiranta da Daneji).
“Inshaaallah zaki sameni mai binki sauda ƙafa Addah laari,nagode da ƙaunarki gareni,bansan da wane kalmomi zan yaba miki ba”
“Bakomai ki nuna min a ta fuskar halayyarki ma ya isa”
Daga haka Inna laari takoma turakarta wajen mutanenta,tabar Daneji da Nata ƴan uwan a sabon gidannata.
Sai bayan kwana biyu da kawowa amarya kafin ƴan biki kowa ya watse,aka bar amarya daga ita sai halinta.
A zaune take ta tafi tunanin yanda rayuwarta a sabon wajen zai kasance,musamman da tasam cewa yan uwanta na daff ta yin ƙaura zuwa arewancin nijeria,dan dama su ba mazauna bane,abinda iyayenta suke tsoro kenan dama ita kanta,shine su barta a wajen da basuda tabbacin dawowa.
Saidai komai yayi rintsi maganin sa Allah,haka iyayennata suka koyar da ita,dogaro da Allah a kowanne lokaci,duk da kasancewarsu masu tashi basuyi boko ba,amma karatun addini kam ko na garin bazasu nuna musu ba.
Saurin share guntun hawayen daya gangaro mata tayi,jin motsin mutum ya shigo ɗakin.
Inna laari ce ɗauke da ƙwaryar abinci a hannunta.
Ƙarisawa tayi inda Daneji ke zaune a hankali tareda dafa hannunta.
“Nasan kuka kikeyi,saidai bazan hanaki ba, ko kuma naga laifinki,domin kowa yasan abin sai anjure tukunna a saba. Dan haka kema kiyi ƙoƙarin daurewar kuma ki saki jikinki,komai zai wuce kaman bai faruba inshaaallah.
Da haka cikin sigar lallashi da jan hira Laari tayi nasarar saka murmushi a fuskar danejin.
Har suka fito tsakar gidan suna aiki tare,yar hira suke kaɗan kaɗan,yawancinta kuma Laari ce keyi,sai ta tambayeta ne tace,uhm ko uhmuhm.
Haka zamannasu ya fara gudana,cikin zaman lafiya da kuma mutunta juna,abin ba ƙaramin faranta ran malm Ahamdu yayi ba,ganin matannsa sun rungumi junansu suna zaune lafiya.
Inna laari ce keyin Abinci,ita kuma Daneji tayi wanke wanke da kuma shara,sannan ta gyara mata kayan abinci.
Bayan sati da kawo Danejine su Larai suka shigo ganin amaryah.
Tundaga zaure ta rankwaɗa Sallam,dan dama itace a gaba sai kuma Shatu tana binta a baya,ta riƙe hannun ɗanta Muruje,wanda ko sati bayyi ba da yaye.
“Salamu alaikum masu gidannan,gamu munzo ganin baƙuwa ta ganmu mu ganta,ta kuma ganemu”
Inna laari ce ta amsa mata wacce take cikin ɗakin girki tana hura wuta.
“To sannunku da shigowa,sai yai kuka zo ganin amaryar?”
“Iyyi to ya zamuyi,munyi ƙoƙari ma,ita ina bata nememu ba,sai mune muka zo ganinta”
“Hayen wuri kukayi ai,dama tana shirin zuwa muku”
Duk zancen tsakanin larai da Inna laari akeyi,shatu kan da daneji basuce komai ba. Sai bayan an gama gaisawane suka shiga ɗakin Amaryar.
“Ahhh babu laifi kam ɗaki yayi kyau,zamuga shin za’a kawo kazantar ɗaki,ko kuma dai duk sammakal ne”
Larai ta faɗa tana fitstsina ido tareda dukan ɗan ƙaramin kunkuminta.
Shatu ce ta kallin Daneji itama ta kalleta,amma larai ko a jikinta,saima surutu da ta cigaba dayi,da kuma ganin ƙwakwaf.
Itada kanta da abin ya isheta tabar ɗakin,tareda nufar ɗakin Inna laari,a bakin ƙofa ta tsayah kafin tashige ta kalli shatu.
“To ni barina yi ɗakin yawuron gidan,ta inda muke muyi namu yakin,wanda ko an fadama mutum bazai ganeba,saura kuma a zunguri hancina idan anga na kauda ido”
Itadai shatu bata ce mata komai,saima maida kanta da tayi kan Daneji wacce take zaune a bakin gadonta.
“Hmm kiyi haƙuri fah amarya,yanayin zamanne sai haƙuri,bazaka iya sanja mutum ba,saidai dole kasha maganin zama dashi.
Sannan abinda zan faɗamiki kiyi taka tsantsan sosai,karki saki jiki ki bada yardarki dabaɗaya,za’ayi miki abinda bakya tsammani.
Murmushi Daneji tayi,da alama bata ɗau maganar shatun da gaske ba,saima kauda zancen da tayi ƙoƙarin yi.
“Ayyah Addah shatu babu komai dai,Inshaaallah babu wata matsalar……..kai ɗan saurayi ya sunanka?”
Ganin duk yadda take ƙoƙarin nusar da Daneji bata damuba,saima dauke zancen da take shirin yi,yasa itama Shatu tabar zancen tareda cewa.
“Ohh wannan sunan Umar,amma yara sun saka masa Muruje,kiji wani suna kaman na Warjayi”
Ƴar dariyah Daneji tayi,da alama sunan da kuma yaran sun bata dariya,haka ta zage tana ta tsokanarsa shikuma yana yi mata ƙiwuyah.
“Inasonsa ki bani shi innar muruje”
“Hhhhh baban sa zai dawo gidannan kenan,in kikayi haƙuri kema zaki haifi naki kaman yaune,saidai zai dunga zuwa miki yawon yamma”

Larai ce a zaune ta baje ƙafa kan kujerar Laari zance yayi zance,wanda yawancinsa duk na Adashen da suke ne a anguwa.
“Uhmm daikuma naga yarinya tasake abinta tayi mursul,ga kulawar miji ga kuma ta kishiya,abin har ya taru yayi mata yawa”
“Ke larai,banda abinki dama ai jajir take lokacin data zo ma”
“Ohh to inaga idona ne yagani badaidai ba,nikam da badan nasanki ba,sai nace yarinyyar can asirin tayi miki,dan inajin labarin duk abinda kike mata a wajen malm,insun zauna malam ahmadu na bashi labari. Yayi tayimin tujara kenan wai ni naƙi a zauna lafiya.”
“To kema ki riƙeta ku zauna lafiya mana larai,ni banga laifin shatu ba……”
“Ahah ahah nina gani inke baki ganiba,idan dole haka kawai banason ta saina ce inayi,gwanda tasan bani sonta,ta tsare tata rayuwar nima nayi tawa,innace zamuyi zaman da kuke da itama nayi ƙarya bazan iya ba”
“Kiji gulma irin ta maxa,wato mlm ne yake bashi labari?”
“Tabb yau kika sani,gulma ai ta daɗe da tarewa wajen maza,idan sun zauna a wannan majalisar,basa lazumi ko salati,sai aukin cin tsire da gulma,shiyasa kiga cikinsu tula tula kaman ƙore,kai sun barka da ɗumame da kuma cikon cefane”
Larai ta ƙarisa fada tana tashi tareda nufar ƙofa.
“To mu munyi nan,sai kun shigo,dan Allah kicewa magajiya zanyi ɗaukar wannan watan na adashen,auren ƴar yayata ya taso”
“To shikenan zan faɗa mata”
Daidai fitowarta daga ɗakin,itama shatu ta fito daga ɗakin Daneji,sallama sukayi musu suka fita.

…………”uhhhhhh uhhhhhh” ……….”laari Daneji fah amai take kwarawa tun daren jiyah,lafiya kuwa????………….

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤11🖤

Kwanaki sunzo sun tafi,a ƙallah Daneji ta samu shekara guda babu kaɗan gidan malam Ahmadu,kuma har yanzu babu wata matsala data fito tsakanin ta da mijinta,ko kuma kishiyarta. Tana binta ta sau da ƙafa,itama kuma tana kyautata mata a matsayinta na babba.
Tun bayan watanta uku a gidan Malam Ahmadu yafara zaton samun ɗa,amma ganin shuru shuru yasa shi dole ya bar zancen.
Daga lokacin yafara zaton wataƙila wata matsala ce daga gareshi.
Hakanne yasa ya nunka kulawar dayake basu fiyeda a lokacin baya,domin sasu manta lalurar tasa.
Daneji ce a cikin ɗakin madafah tana girki,tun jiya take jinta wani iri,amma haka ta daure,dayake ansan mace da dauriya da kuma murƙushe kanan nan ciwo da laulayi.
Doyar da take dafawa zatayi sakwara ta buɗe,saidai ƙamshinta yana bugunta taji amai ya taso mata.
Da sauri tayi waje tana ƙoƙodon amai.
Inna laari ce ta fito daga ɗakinta domin ganin mai yake faruwa.
Ruwa ta debo mata ta gyara bakinta tareda yimata sannu,suna cikin hakanne shima Malam Ahmadu ya shigo gidan ya dawo daga wajen ɗaurin auren daya fita da safe.
Inna laari yafara tambaya mai yake faruwa,saidai kafin ta bashi amsa Daneji tacigaba da aman da takeyi,saidai takai ga ta amayar da duk abinda taci da safe.
Kafin lokacin ƙalilan ta galabaita ta fita hayyacin ta,kamata inna laari tayi suka shiga rumfah ta zaunarta,inda shikuma malam Ahmadu ya fita ƙiran ƴar mai ganye,dake tsallaken gidansu,domin ta duba taga mai yake faruwa.
Basu daɗe ba suka shigo tare,takalmanta fantala fantala zani a tsangale,sai jijjiga kai take ƙanƙanin. Hannun danejin ta kama tayi shuru,kafin tafara wasu ƴan dube dubenta,can ta waigo ta kalli mlm Ahmadu tareda cewa.
“Iyyyeeee Alhandu alhandu,Yarinya ciki gareta,ƙaruwa ce ta samu sai kuyi murna ku godema Allah”
Tun kafin tagama maganar Mlm Ahmadu yafaɗi ƙasa yayi sujjada,tareda fashewa da kukan murna.
“Daneji ɗiyar arziƙi,allah shi miki albarka,haƙika kin sakani farinciki dana daɗe ban shiga ba a rayuwata,Allah ya saukeki lafiya. Inna ƴar mai ganye kinada kyauta ta musamman na wannan albishir ɗin,yanzu dame dame take buƙata kenan”
“Babu abinda take buƙata,illah tarage yawan aikace aikace amma ba wai kartayi ba,sannan a kulada abinci masu gidan jiki sosai,nagode nagode mlm Allah yayi albarka,ni bari na tafi toh Allah ya raba lafiya,zan aiko yaro da ruwan saiwoyi ya kawo mata ta dunga sha”
“Shikenan iyah mai ganye mun gode”
Duk abinda ake iya Iyah mai ganyece da kuma Malm Ahmadu,inna laari bata ce komai ba itada Daneji,wacce take ɗan sauƙar da numfashi a hankali.
“Sannu mai zakici toh,bari a nemo miki Kwankwason akuyah a dafa miki”
Ɗaga masa hannun Daneji tayi alamar yabari,amma mutumin ko kallonta baiyi ba,sai ma fita da yayi da sauri bajam bajam da babbar riga.
Binsa inna laari tayi da kallon kafin ta jijjiga kai tayi ɗan murmushi.
“Zaki iya isa ɗaki ko kuma na rakaki? Zan ƙarisa abinci”
“Ahah zan iya Adda laari nagode da kukawarki”
“Babu komai kisamu hutu sosai jikinki yayi laushi,bari yakawo naman saina dafa miki,Allah ya sawwaƙe ya raba lafiya”
Daga haka Daneji ta ƙoƙarta tashige ɗakinta,ita kuma inna Laari tacigaba da aikin abincin data bari.
Tundaga wannan rana Daneji ta gagara lafiya,kullum cikin laulayi take,yau da lafiya gobe kuma babu,abinci kuwa kusan kowanne kala bata iya cinsa.
Tun malm Ahmadu yana ɗokin magaji har zuwa yanxu abin yafara bashi tsoro da tausayi,inda yafara tambayar dama haka goyon cikin yake.
Inna laari ce take rawa take kidanta a tsakar gidan,ita kam daneji Ba sosai take fitowa tsakar gidan ba,in mutum ya ganta to zagawa zatayi makewayi ko kuma alwala.
Haka rayuwar tacigaba da tafiyah,da daɗi da kuma babu,har yazamto cikin daneji yayi girma sosai,ana saka ran ko yaushe zata iyah haihuwa. A lokacinne kuma aka dage dabata dan taimako,ita kanta inna laari ba’a barta a baya ba,takan samo mata ɗan taimako daga wajen mahaifinta,dayake shima malamine.
Ɗakin Danejin inna laari tashiga da ƙwaryar magani a hannunta,magana tayi mata kasancewar ta juya bayanta bata kallonta.
“Daneji tashi kisha maganinnan ya tsumu sosai,karkuma yazo ya sane”
Duk maganin da Inna laari take bata a dole take sha saboda rashin dadinsu,saidai saboda karta nuna mata kazawarta a ƙoƙarin datake da ita yasa ta yunkura ta tashi. Alkhairin da inna laarin tayi mata bazata iya ƙirgasu,ji take a yanzu bata da kowa na kusada ita kaman ta,musamman daya kasance batada kowa a garin,ƴan uwanta tunda suka tashi batasan a yanzu inda suke ba.
Karbar maganin tayi dayake cikin ƙwarya takaishi bakinta tana yatsine fuska.
Da kyar tayi kurba uku kafin ta miƙamata ƙwaryar ta koma ta kwanta.
Cikin dare malm Ahmadu ya zabura ya tashi,jin ana jan bayan rigarsa daga ƙasa,lalumar fitilah yafara yi domin ganin mai yake faruwa,don yasan bazai wuce Daneji ba,don yana shashimawa yaji bata wajen data ke kwance ɗazu.
Yanzu haka haihuwa ce,yafaɗa a ransa,don dama tun shigar watan haihuwar tata inna laari ta lamunce masa ya koma ɗakinta da zama,saboda kar haihuwa tazo mata cikin dare babu kowa a wajenta.
Baiƙi karbar tayinta ba,saima godiya dayayi mata,dan hakan baƙaramar dabara bace.
Haska fitilar yayi a wajen dayake jiyo motsin danejin,tana durƙushe ta kifa kanta da bakin gadon,ƙasanta duk ya jiƙe da ruwa yana ta malala mai haɗe da jini.
Salati malam Ahmadu yafara tareda buɗe ƙofar da sauri ya nufi ɗakin inna laari.
Tana bacci sai jin muryarsa tayi yana ƙiranta,cikin magagin bacci tafara tambayarsa.
“Lafiyah malam naganka a razane,ko haihuwarce kai tazo?”
“Ehh…..ehh itace ,maza kizo ki gani koda wani abu dazaki taimaka mata dashi”
Tashi inna laari tayi tabi bayan malm Ahmadu zuwa ɗakin danejin,wacce take kwance har yanzu a inda yatafi ya barta.
Ƙarisawa wajenta tayi tana kallon yanayin da take ciki,saidai da alama haihuwar takawo kai amma kuma dasaura,don babu alamar tahowar ɗan har yanzu.
“Inaga har yanzu fah da saura,amma barina kawo ruwa a goge mata jikinta,sanann kuma tacire wannan riga da zanin,suma bazata ji daɗinsu ba”
To kawai malam Ahmadu yace mata,domin aikinsa kallone kawai,bashida tacewa bayan hakan.
Yana nan zaune a gunta har inna laari ta dawo da ruwan dagama gyara mata jikin,sannan tabata fallen zani ta ɗaura.
Kaman jira kuwa take tafara nishi da yunkuri,har wajen fitowar asslatu suna kanta,tana nishi amma babu haihuwa,saidai yafi na ɗazu,tunda ana ganin kan yaron,aikinne dai har sannan da saura.
Yanda suka ga rana haka sukaga dare akan Danejin,wacce take fitar da nishi mai haɗe da ƴar ƙara na galabaita da gajiya.
A hanyar zuwa masallacine malam Ahmadu ya biya gidansu iya mai ganye,yake faɗamata abinda yake faruwa,aikuwa nan da nan ta shirya tanufi gidan,jiki yana bari taji daɗin kyautar da yayi mata wajen faɗar haihuwa.
Sai bayan rana ta fito gadan gadan haihuwar ta taho,inna laari tana gogemata goshi,ita kuma iyah mai ganye tana taimaka mata wajen fitoda jijirin.
Kaman jira shima yake kuwa ya canyare wajen da kuka,har makwantai ana jiyoshi.
Ɗago dashi iyah mai ganye tayi tana duddubawa,take kuwa tasaka guɗa.
“Ayayyyyyriririrrri malam Ahmadu yasamu ɗiya mace,barkanki dazuwa duniya ɗiyar Albarka”
Sai bayan tagama guɗar kafin ta kalli Daneji wacce take maida numfashin gajiya.
“Sannu sannu ƴar nan,sannunku keda abokiyar zamannnaki,dole kisha wuya kam,yarinya tafarkallah mashaallah,ga tanan kuwa jajir da ita kaman uwarta,ta amsa sunan ƴar Daneji.
Laari saiki taimaka mana da daro ruwan zafin da zasuyi wanka itada yarinyar.”
“Ruwan kan daman an ɗumama tun tazu,saidai ko na kaimuku banɗakin kiyi mata wankan,kafin ku fito itama jaririyar sai a gyarata”
“To shikenan hakan ma yayi sannunki da ƙoƙari”
Kaman yanda ta faɗa ruwan takai musu banɗaki,inda iya mai ganyen zatayiwa mai jego wanka,yayinda itama ta haɗa wani a baho zatayiwa jaririyar.
Shigo ɗakin tayi da ruwan wankan ta ajiye,kafin ta nufi inda jinjirar take kwance a tsumman mahaifiyar tata,ɗaukarta tayi a hannunta tareda yin murmushi,kana kuma tashare guntun hawayen dayake kan fuskarta.
“Allah sarki jinin Mlm Ahmadu ne a hannuna,ashe zanga jinin malm Ahmadu da raina,duk da cewa banice na haifa masa ba,amma nayi maka murna dakaga jininka”
Lokacin da su iyah mai ganye suak fito daga wankan inna laari na zaune a ɗakin tana tsane ruwan jikin yarinyar,wadda tayi shuru a cinyar inna laarin tana jin ɗumin dayake ratsata.
Iyah mai ganye ce tafara magana tareda cewa.
“Hoɗan kiji yarinya tayi shuru kaman ba haihuwar yau ba,kokukanta bamuji ba na wanka”
“Ko kishi kike kai kinganta da juriyah zata ƙwace miki kujera kai iyah”
Inna laari ta amsawa iyah mai ganye cikin sigar zolaya. Suna cikin hakanne kuma kaman an tsikareta ta canyare da kuka kaman ansaka a speaker.
Nannaɗeta tayi a zanin tareda miƙawa daneji ita akan ta gwada bata nono.
Itama iyan mai ganye ƙara ƙarfafa mata gwiwa tayi cewar tashayar da yarinyar,musamman da sukaga tana kauda kai akan yarinyar tana nuna halin fulani.

……………Shuɗiyar ƙwayah kuma(blue iris),kodai bata gani kai………daneji da faɗa a ranta.

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤12🖤

Hannu tasa ta karbi jaririyar tareda mannata a jikinta,wata irin tsagwaron ƙaunar yarinyar ne ya jiyarci tsakiyar zuciyarta,tareda muradin kareta a ta kowacce fuska.
Idanuwanta ta sauƙe akan jar fuskar jinjirar,wadda yake ɗauke da ƙankanin kyau mai tafiyar da duk mai kallonta.
Hancinta babu makawa kowa yakalleta yaga na ubantane,sai bakinta kuma data biyo irin na mahaifiyar ta ɗan ƙarami,motsashi take a hankali tana neman inda zataji abincinta ya isa gareta,wanda hakan yasa ainihin Cute feature ɗinta fitowa fili.
Boyayyan murmushi Daneji tayi ganin halittar yar tata farincinkinta tareda gode ma Allah daya azurtata da itah.
Maman ta buɗe na hannun dama inda yarinyar take,tareda ƙokarin saka mata a baki da taimakon iya mai ganye wacce take tsaye a kanta.
Saida taga yarinyar takama nonon kafin tabi bayan Inna laari zuwa wanke kayan data bata.
A hankali take jan ruwan nonon cikin rashin iyawa zuwa cikin bakinta,yayinda ita kuma Daneji ta tsareta da ido,ko da wasa ta gagara ɗauke idonta daga kanta.
Idonta ne yafara motsawa alamar zai buɗe,wanda hakan yabata mamaki matuƙa,yarinyar da aka haifeta yanzu tana shirin buɗe ido,kawar da hakan tayi a ranta ganin daƙin da duhu,sannan kuma idan aka buga larasi da ƴaƴan zamani hakan bakomai bane.
“Daga haihuwarki yau har kina ƙoƙarin buɗe idonki,lallai kina da wayo sosai t……….”
Tsaida maganar tayi a ƙasan maƙoshinta,ganin launin idon dayake kallonta,ba baƙi ba ko kuma mai ruwan ƙasa ƙasa ba,da ake samun wasu yaran sukan zo dashi,nata launin idon shuɗine ne siɗik,kaman ba idanuwan bil’adama ba,duk wanda yarinyar takalleshi da idanuwan idan bayyi jarumta ba zai iya jefarta yagudu,saboda yanda suke ɗauke da wata haiba a cikinsu,da ko babban mutum bazai samu ba.
Wata irin mummunar faɗuwar gaba ce ta jiyarci danejin a karo na ba’a adadi,ganin irin halittar da ƴar tata take ɗauke dashi,wanda tayi amanna tunda take bata taba ganin irin ta ba a rayuwarta.
Duk yanayin buɗe idon kaɗan kaɗan take irin na jarirai,amma hakan bazai hana mutum gano abinda yake tattare da yarinyar ba.
Runtse idonta tayi na wasu mintina kafin tasake sauƙesu akan ƴar,wacce zuwa yanzu ta rufe idanuwan da alama tayi bacci a bakin nonon. Cireta tayi a hankali,ta sake lullubeta a cikin zanin da take,kafin ta maidata wajen da take kwance ɗazu..
Tashi tayi tafara gyara ɗakin tareda ɗauko kayan dazata saka,har sannan jikinta a sanyaye yake na abinda tagani,a jima kaɗan ta kalli wajen da yarinyar take,a jima kaɗan ma ta kalleta,abin ya tsaya mata a rai takasa fitarwa.
Tana cikin hakanne malm Ahmadu ya shigo ɗakin kaman an jehoshi,labarin sauƙarta lafiya ya risƙeshi a waje.
Kai tsaye wajenda take ya nufa tareda ɗaukota ya rungume a jikinsa da rawar jiki.
Sumbatarta yafara ta ko’ina kafin yafara yimata ƙiran sallah a kunne.
Itadai Daneji tana tsaye da tsintsiya a hannunta bata ce komai har yagama rawar jikin.
Ɗagowa yayi ya kalleta da murmushi akan fuskarsa yace.
“Mashaallah nayi mata huɗuba,sannan kuma nasaka mata sunnan mahaifiyata MARYAMAH”
“Allah yaraya ta bisa imani,sannan kuma Allah yasa halin mai sunanta ya bita”
“Ameen ya Allah,kema Allah yayi miki albarka yabaki lafiyar shayarwa”
“Ameen kasake yiwa Addah laari godiya da ƙoƙarinta a gareni”
“Shikenan”
Kafin dare yayi mutane ƴan uwa da abokan arziƙi suna ta zuwa ganin Ƙaruwar haihuwar da akayiwa malam Ahmadu,wannan su shigo wannan su fita.
Har ƴan uwan su inna laari ma saida sukazo daga ƙyauyensu,Amma babu wanda yazo akace daga bangaren mai jego,duk da kowa yasan ƴan uwanta basanan amma abin yayi mata ciwo sosai,rashin danginka a kusada dakai abune mai ciwo matuƙa.
Da daddare saida Daneji tasha kukanta ta ƙoshi na rashin danginta,babu wanda zai zauna a gunta daga bangaren yan uwanta,sai dole yadikon su malam akan ce wata tsohuwa tazo yi mata zama.
Gashi yanzu tafara tara dangi itama nata na kanta,shin wa zata nunawa Ƴar ta a matsayin danginta zuwa gaba,ko kuma haka zata tashi batasan kowa nata ba,wanda itama tanada yaƙinin nangaba zata iya mantasu idan lokaci ya tafi.
Har akayi kwana uku da haihuwa babu wanda yagane cewar idon Jinjirar bana mutane bane,sai iya daneji ce kawai tasani,har yanzu kuwa babu wanda ta faɗawa,kullum fargabarta shine idan mutane sun gano mai zasuce gameda hakan.
Abinda yafi bawa Daneji mamaki shine idan har ita datake bata nono tagane ƙalar ƙwayar idanunta inaga mai wanka kumafah inna laari,tana da tabbacin Inna laari taga abinda tagani gameda yarinyar,amma ko kaɗan bata nuna tagani ba,ko kuma bata gani bakai?
Ita kaɗai take tambayar kanta take bata amsa a ranta,abinda yashare mata tantama shine,lokacin da jinjirar ta shaƙi sabulu ta buɗe idonta kuma akan idon inna laari,amma batayi mamaki ba ko kuma nuna alamar zata sanar da wani abinda tagani.
Duk abinda take bata kulada Daneji tana kallon sanda taga idon yarinyar ba,hakannne yakara tabbatar mata ba lokacinne kallonta na farko ba a gameda lamarin,tasani tunda farko,boyewa kawai takeyi,to miyasa?.
“Addah Laari shin bakiga wani abu a tattare da yarinyar nan ba wanda ba irin na mutane ba?”
“Nagani mana,ƙwayar idonta ba kalar ta mutane bace,saidai babu yadda Allah baya halittar sa idan yaso,shi yayi nufin yaganta hakan,dan haka babu mai ja da ƙudurarsa”
“Hmmm hakane kam,nayi mamakine da kika gani amma bakice komai ba”
“Uhm mai zance Daneji,saina bi duniya nayi ta yaɗawa ƴar mijina an haifeta da wani irin ido?ribar mai zanci akan hakan,innayi hakan nima ai kaina na tozarta ba kowa ba,sannan ya mutane zasu kalleni kenan,idan Allah yayi kwananta ta fita kowa ma zai gani,fatana shine Allah yasa mutane su gane halittar Allah ce itama kamar su,karsu nuna ƙyamatarsu gareta”
Maganar da inna laari tayi baƙaramin faranta ran Daneji tayi ba,sai ta nemi kashi hamsin na fargabar halin da yar tata zata shiga ta rasa,yazamana itama tasaka a ranta cewar Allah ne mai halitta,kuma shi yayi nufin ya ganta a haka ba kowa ba.
Ranar suna gadan gadan aka hau abinci da yanke yanken kaji,bayan tunkiyar da aka yanka na aƙiƙa.
Mutane an ciki gida maƙil,a lokacinnne kowa yashaida yarinya taci suna Maryam,mahaifiyar malam Ahmadu.
Bakinnan kaman gonar auduga,kowa rana yasan malm Ahmadu yana cikin farin cikin marar misaltuwa.
Duk abinnan da ake Daneji kaffah kaffah take da Maryam,wanda tafara ƙiranta da BOMBEE,saboda kar mutane sugani su tsegunta,ana tsaka da taro kowa yaɗauka a ƙirƙiri abinyi na gulma.
Dan haka sai itada inna laari suka haɗa baki akan yarinyar bata lafiya,kowa idan yazo saidai ya kalleta daga nesa,itama data rufa musu asiri wuni tayi tana bacci.
Bayan anyi taro an watsen makwanta su larai suka tsayah aka gyara gidan tareda su,kafin bayan magriba sukayi mmusi sallama suka nufi nasu gidan.
Dare yayi gari yafara shuru Bombee tace batasan kwanciya ba,dawa Allah ya haɗata idan bada kuka ba.
Tun tanayi Daneji na rarrashinta har abu yafara fin ƙarfinta,dan shiɗewa take muryarta har dunshewa take dan Kuka.
Shikansa malm Ahmadu take ɗakin inna laari yayi sawu yakai sau uku,kl yaushe idan yazo sai yace tabata tasha,tun tana ce masa taƙi karba har ta rabu dashi.
Ruwa ta ɗebo a kofi tana tofi tana shafe mata jikinta,tunda ta kula babu zazzabi a jikinta,sannan cikinta bai kumbura ba bareta ce ciwo yake mata.
Haka tayi ta shafe ta da ruwan addu’o’i,sai kuma tayi sa’a tafara sauƙe ajiyar zuciya lokaci lokaci,can wajen asuba tayi ƙitt kaman an kashe rediyo.
Ida tai Daneji yanda taga rana haka taga dare,ga gajiyar bikin suna,sa’arta ɗaya ma Ba sallah zatayi ba ko girki,dan haka da rana ta samu damar rama baccin.
Wasa wasa an kusa shafe wata ɗaya dayin suna,kullum babu fashi sai Bombee ta kwana tana ihu,idan asuba kuma tayi tai shuru kaman ruwa ya ɗauke.Tun abun suna ɗaukarsa kukan jinjirai har abun yafara sakasu dasa ayar tambaya. Bangaren Daneji kam harta fara mantawa da wani baccin dare yanzu.
Bankaɗa labulen ɗakin tayi zata shiga ta fito daga wanka,turuss tayi a bakin ƙofar ganin malm Ahmadu rike da Bombee a hannunsa yana kallon idonta,ita ma kallonsa take da shuɗayen idanuwan nata na yara,kana kallon kan fuskarsa zaka hango tsagwaron mamaki da kuma irin mutum yaga abu a karon farko.
Ɗago fuskarsa yayi ya sauketa akan Daneji wacce ta shigo daƙin jikinta yana ɗigar da ruwan wanka.
Saurin sunkuyar da kanta tayi bata bari sun haɗa ido ba,dan babu alamar wasa a idanuwannasa,tambaya ya jeho mata kai tsaye.
“Fatima menene wannan?”
“Idanuwanta ne”
“Dama haka suke tun farko,kokuma yanzu sukayi?”
“Haka take dasu aka haifeta”
“Meyasa kuma ina matsayin mahaifinta baki taba faɗaminba,kenan da bangani ba shikenan harsai ta girma ta fita naji a bakin mutane kome,idan kuma hakan ciwone kika barta dashi ya wuce gaban kwatance fah,yakike ganin za’ayi,kullum ina faɗamiki banason wannan shuru shurunnki,zai iya kaiki ga aikata danasani”
“Kayi haƙuri banason ka shiga damuwane idan ka gani,sannan bansan ta yanda zan sanar dakai ba,na faɗawa addah laari ma tafaɗa maka tace baruwanta”
“Eh baruwanta mana,ke kinga laifinta a ciki,tazo ta faɗa ace dama Allah allah take ya faru ta faɗa? Maza saka kayanki mutafi wajen maganin gargajiya da kuma na nasara,wannan abin ai bana zama bane,waya sani ma ko bata gani ke baki sani ba,inaga ma yanada alaƙa da kukanta da daddare,ko ciwo ma suke mata”
“Tana gani fah dasu”
“Taya kika san tana ganin”
“Idan nasaka mata haske ina tafiya dashi tana bin hasken”
“Ni ban yarda da wannan zancen ba,maza shirya mu tafi asibiti a ji shin mai yake damunta”

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤13🖤

Babu ‘bata lokaci daneji ta shirya domin su tafi asibitin,har sannan Bombee na hannun mahaifinta,motsi kaɗan idan tayi ya leƙata,gani yake tamkar ƙwai ne a hannunsa,zai iya fashewa a kowanne lokaci.
Ƙosawa yayi darashin shiryawar tata da sauri,dukkuwa da yanda take iya ƙoƙarinta wajen yin saurin,gani yake kaman jinkirinta a lokacin wani abun zai iya faruwa.
Fitowa sukayi daga ɗakin tareda yiwa Inna laari sallama kana suka kama hanyar asibitin a mashin ɗinsa.
Yana tafiyah yana waiwayen ƴar tasa.
“Ki kulada ita fah kar wani abu yasameta kafin mu isa…….yi shuru uwata kinji,bari muje a baki magani su daina yimiki ciwo,irin wannan ido haka akan wane daliline bazayyi ciwo ba,hmmm Allah dai ya kyauta.”
Magana yake tayi shi kaɗai,itadai Daneji bata cemasa ci kanka ba,sai rarrashin ƴarta da take tayi,har suka isa asibitin wanda bashida nisa da anguwarsu.
Kafe mashin ɗin yayi,ya kar’bi ƴar suka shiga asibitin..
Nan ma dayake litinnin ne layi har bakin asibitin,kasancewar kuma yahaɗa yanayi da damina,jinyace jinyace sunyi yawa.
Wani bakin banci yasamu a gefe ya nunawa Daneji ta zauna,kafin yabada yarinyar ta riƙe,shikuma yashiga ciki domin yayiwa likitan magana akan lalurar tasu.
Feeder Daneji ta fitar tana bawa Bombee ruwa,wacce taga kaman alamun fatar bakinta ya bushe babu ruwa. Dadai lokacin ne kuma wata mata itama da goyo tazo ta zauna zata since yaron ta tabashi abinci..
Daneji bata kulada ita ba sai gani tayi ta miƙe dasauri,hannunta yana rawa ta toshe bakinta.
Ja da bayan da takene tana nuna inda Daneji take,yasa kowa hankalinsa yadawo wajen da sauri.
Bakinta yana rawa tafara cewa.
“Wayyo ba mutum bace,wani abu nagani a radu a hannun matar nan”
Kowa maida idonsa yayi kan Daneji,wacce tasake rungume ƴar ta a jikinta,tareda sunkuyar dakai,ji tayi kaman ƙasa ta buɗe ta nutse ciki,mai aka ɗauki ƴar tane,bayan zuwanta duniya su kaɗaine suka san lalurinta,yau ɗaya wata tagani harta tozartasu. Shin itama ba uwa bace da ɗa a hannunta,bata kunyar yiwa wata uwar haka a matsayinta na uwa?
Suna cikin hakanne ana ta hayaniya malm Ahmadu ya dawo wajen,inda ya tarar kowa yana nuna Daneji wacce take zaune kaman mujiya ta rungume Bombee.
Bankaɗe mutane yayi ya isa gareta,tareda tambayar ta mai yake faruwa.
Zayyana masa abinda yafaru tayi cikin ƙaramar muryah mai cikeda damuwa.
Aikuwa cikin tunzura ya juya ya kalli matar,wacce take tsaye tana zayyana yanda taga idon Bombee.
“Uhm malama na tambayeki mana,shin wannan da kike riƙeda shi ɗanki ne?”
“Eh ɗanane mana”
“Idan ace misali lokacin dayazo duniya sai kika kulada cewar gashin kansa korene,sai kike saka masa hula a koyaushe idan zaku fita waje,to ƙwatsam watarana sai wata mata itama mai ɗa,ta fara nuna ɗanki a bainar jama’a tana cewa…..wannan ɗan mayene ba mutum bane,dukkan mutane sai suka yi caaa sai sun ga ya ɗanki yake,wasu ma har zakinki suke.
Ita kuma tana tsaye a gefe tana sake bayyana yanda ɗanki ba mutum bane,shin ya zakiji a ranki a lokaci?”
“Meyasa kayimin wannan misalin,amma dai amsa a bayyane take,yanda nake son ɗana zanji tamkar ta daba min mashi a cikin zuciya,sannan zanji baƙin ciki a matsayinta na uwa bata gani ba take tozarta nawa ɗan”
“Alhamdulillah kinbawa kanki amsa,to waccer matar da kike tozarta ƴar ta fah,ita yazataji a ranta?.
Ita ɗin matata ce,yarinyar da kike ƙira kuma mayyace,ƴata ce ita ɗin,haka aka haifeta watan baya da kalar nata halittar idon,shin akwai mayen da ake ganeshi ta halittar idone,dan kawai ƙwayar idonta shuɗine sai aka ce itaba halittar Allah bace?.
Ita kin muzanta tata yarinyar,kuma sannnan ko kunya bakyaji kina tsaye kina ƙara maida bayanin,a matsayinki na uwa kuma tirrrr da halin wasu matan”
Malam Ahmadu yana gama faɗamata hakan ya nufi inda Daneji take sunkuye tana kuka.
Yayinda ita kuma kowa idonsa yakoma kanta,itama ta sunkuyar da nata kan cikeda kunya da nadamar abinda ta aikata.
A hanya suna tafiya malm Ahmadu yasamu waje ya faka mashin ɗin.
Itama Daneji ganin hakan yasa ta saƙƙo daga kan mashin ɗin tana kallonsa.
“Wai yaushe zaki bar wannan kukan iyee,shin kukanne magani komai,tun yanzu ma kina kuka inaga idan ta girma tafara shiga mutane fah,idan ta shigo gida an ƙirata da mayyah kuka zakiyi kaman yanzu?”
Jijjiga kai tayi alamar ahaha,sai can kuma kaman bazatayi magana ba tace.
“Mai likitan yace toh,sannan meyasa muka taho”
“Yace zuwa yanzu bazayyiyu muganshi ba,sannan ni daga ganin abinda ya faru nafara tunanin inaga abin bana asibiti bane,saboda babu wata jinya da yaro ke zuwa da irin wannan ido,nafi kyautata tunanin shafen aljanu ne,dan haka gidan Malam ALWASU zamu je,ya duba yaga koda maganin dazai iya bamu.”
“To shikenan hakan ma yayi,nima dama bana tunanin abin asibitine wannan,bata kuka fah sai dare yayi,sannnan ………….”
“Sannan me inaso ki fadamun mai kika gani bayan nan”
“Idan …..idan na haska fitila ko zan ɗauketa…..sainaga idon yanayin haske a cikin duhu,kaman idon kuliya ko kura idan an haska da daddare”
Cikin kiɗima mlm Ahmadu yazaro ido,jin abinda Daneji ta faɗa,tohhhh ikon Allah.
“Maza maza hau kan mashin mu tafi asibiti,wannan ba abune daza’a zauna ba,tabbas dagaji aikin aljanu ne”
Tafiya mai nisa sukayi kafin suka iso ƙofar gidan mlm Alwasu,tundaga bakin ƙofar gidan mutum yana gani yasan gidan mutanene rabi bokaye rabi kuma suna fakewa da harkar malantaka.
Almajiraine a ƙofar gidan birjik sunata karatu,sai ƙofar gidan a tsakiya,daga can kefe kuma wani ɗan zaurene na kasa,an lanƙaya su jajayen ƙyalle a jiki da baki,kowanne anyi masa rubutun larabci,duk maitarka baka isa faɗin mai aka rubuta ba.
Wani yaro suka tasa daga cikin masu karatun,tareda tambayarsa inda Mlm Alwasu yake.
“Kai ina mlm yake?”
“Yana cikin zaurensa suna ganawa da hajiya,zaku iya jira ko kuma ku dawo idan an jima”
“Ahah bari mu jirashi ba matsala,ku cigaba da karatu koh”
Suna nan tsaye wacce aka ƙirada hajiyan tafito daga cikin zauren. Tabbas Hajiya kam,dan itace mai neman kujerar chairman na Sardauna LGA a lokacin.
Ƙarisawa su mlm Ahmadu sukayi suma daga ciki,domin kaiwa tasu buƙatar.
Shiga sukayi tareda zama akan buzun dayake gabansa.
Har kusan tsawon mintina biyar da zaman su amma bai ce musu komai ba,yana zaune a inda yake ya rufe ido,hannunsa kuma ɗauke da wani zankaɗeɗen carbi yana ta ja.
Abinne yabasu mamaki,wanann ya kalli wanann wannan yakalli wannan.
Mlm Ahmadu ne ya buɗe baki zayyi magana,dan yafara ƙosawa da zaman,saidai tun kafin ya buɗe baki mlm Alwasu ya katseshi ta hanyar ɗaga masa hannu.
“Hmm karkace komai,barina gama da wannan tukunna”
Saida yagama ɗin kafin ya buɗe idonsa akan su.
“Inajinku yanzu mai yake tafe daku,na raka Hajiya ne ta addu’a har saida tabar yankinnan,shiyasa kuka ganni nayi shuru,amma yanzu ina jinku”
“Allah gafarta mlm dama lalurine yasamemu na aljanu,yarinya ce aka haifeta,amma kuma sai tazo da wani irin ido kaman na karashiya,sannan innarta gata tacemin bayan launin idon,har haske yake irinna kuraye idan aka haska da fitila da daddare,kuma kwana take bata bacci kullum.
Kaga kuwa wannan ba aikin kowa bane sai aljanu,shiyasa mukazo koda taimakon dazaka taimakemu dashi”
Ƙarisa magana mlm Ahmadu yayi ta sigar roƙo a wajen mlm Alwasun,wanda yayi shuru yana jin bayani.
“Miƙomin yarinyar naga mai yake damunta,tabbas daga bayaninka kam abin yayi kama dana aljanu,saidai shikansa shafen aljanu kala kala ne,bazamu gane wanne daga haka ba.”
A jiye yarinyar yayi akan cinyarsa,tareda dafa kanta sannan ya rufe idonsa.
Ya daɗe a haka can ya buɗe ido da ƙarfi akan su mlm Ahmadu,hannunsa rawa yakeyi da kuma bakinsa,sai can kuma ya tsime kaman bashi ba.
“Tabbb tabbas abinda kuke tunani hakane,yarinyar tana ɗauke da baƙaƙen aljanu masu haɗarin gaske,saidai ba a jikinta suke ba,ajiya sukayi a cikin idanuwanta,shiyasa suka sanja kala,kuma take gani tamkar irin na aljanun”
Bazai yiyu mu iya cire ajiyar ba batareda mun tsire idon ba,saidai amma zamu iya ‘boye ajiyar a jikinta,ta yanda bazasu tuno da ajiyar ba har abada,ta hakane zasu manta da lamarin su barta tayi rayuwarta.
Saidai da sharaɗin karku dinga barta kullum cikin fushi,sannan kada ku barta takai farmaki akan komai,daga lokacin da tayi ƙoƙarin buɗe wanann ajiyar da kanta,to fah kuma babu komawa da baya,dole saidai ku sallama ta,domin zata kasance tamkar mabuɗar bala’i a gareku.
Sai ku zaba shin ayi aiki ko kuma kar ayi?”
Tsuru tsuru su mlm Ahmadu sukayi,suna jin bayanin da mlm Alwasu ya basu,dama su tun wuri sunyi tunanin aljanu ne gareta,biri kuwa yayi kamada mutum,yau ya zasuyi a wannan duniya ta maliki yaumiddini.
“Mlm a boye ajiyar dayake jikinnata,zamu yi ƙoƙarin rainonta akan kartayi fushi kokuma shiga damuwa,bazan juri ganin an ciremata ido ba gaskiya,tunda dai kace bazasu san inda take ba to inaga hakan ma yayi”
Daneji ce tafaɗa tana matse guntun hawayen dayake idonta.
“To shikenan tunda kun zabi hakan za’ayi aikin daya tace,akwai maganin dazan baku yanzu a dunga zubawa a ruwan wankanta,sannan kuma dana turare wanda za’a dunga yimata da daddare.
Bayan sati ɗaya kuma zaku dawo ayi yanka ayi sadaka,sannan ayi anihin aikin daza’a boye ajiyar jikinnata”
“Mungode mungode Mlm Allah yasaka da Alkhairi,yanzu kenan nawane kuɗin abin sadakar”
“Abin sadaka sai nan da kwana bakwai idan nagama aikin,yanzu za’a fara shirye shiryen haɗa duk abinda ya dace”
“To shikenan mlm muzamu tafi,sannan za’ayi yadda kace,sai nan da zuwa ranar bakwai ɗin”
Daneji ce ta karbi yarinyar wacce take bacci abinta daga hannunta mlm Alwasu suka tafi”
Sai bayan sun fita da kaman minti talatin mlm Alwasu yasaki ajiyar zuciya.
“Tabb yau wannan yarinya mainene takamai mai abinda yake damunta,ni kaina duk iya ƙoƙarina duhu kawai nake gani,amma zanyi iya ƙoƙarina dai daga nan zuwa satin a gani”

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤14🖤

A haka suka koma gida cikeda ta’ajjibin abinda aka faɗa musu. Sannan kuma Daneji tacigaba dayi mata wankan maganin da mlm Alwasu yabasu.
Bayan sati daya dayin hakan suka sake komawa,aka yi yankan sadaka da kuma sauƙar karatu,sannan ya kuma basu wani maganin wanda za’ayi mata.
Sai a sannan ne hankalin su mlm Ahmadu ya kwanta,amma ba duk ba,saboda har yanzu idonta babu abinta ya sauya daga shi,saidai sun samu kwanciyar hankali jin cewar ta rabu da aljanun da suke jikinta.
Wasa wasa abu yayi ta tafiyah,har an shafe watanni biyar,tun su Danejo na boye Bombee idan sukaji sallama,har yazamo mutane sun gane abinda yake tattare da ido.
Dama ance idan rana tariga ta fito,tafin hannu bai isa rufeta ba.
Kuskus a cikin jama’a har zance yabaza gari ko ina ya ɗauka ƴar gidan mlm Ahmadu mayya ce,tun Danejo batajin mai yake faruwa har zance ya dawo kunnenta.
Inna laari tana sayar da kayan miyah,wanima da gangan yake tsallake anguwarsu yazo gidan su siyan abu,badon komai ba sai don yaganewa idonsa labarin abinda yakeji a gari.
Itakam inna laari cinikinta nunkuwa yake a kullum,ko kyaushe cikin siyeda siyarwa takeyi,kowa kuma idan ya shigo idonsa yana kan ɗakin Danejo,domin yaga ta inda zaiga Bombee.
Kullum a rana Danejo bata da aiki sai boyeta a cikin daƙi,saidai yanzu abin yayi mata wuyah,dan tafara rarrafe,ga ta da rawar kai bataji ko kaɗan,kota ajiyeta a ɗaki saita fito waje,wani lokacin inta takura bazata fita ba tasaka mata kuka,har abin ya isheta ta daina hanata fita wajen.
Batada ikon rufe bakin mutane ko kuma idanuwansu,amma kuma tana damar rufe nata idon da kuma bakin,shiyasa tasakawa idonta ƙyalle ta rufeshi,kunnenta ma ta tosheshi daga abinda zataji akan ƴar tata.
Inna laari ce take ƙirga karago itada mai talle…..basu fargaba sai ji sukayi yarinyar ta junduma ihu ta fita gudu waje.
Gefe suka kalla inda Bombee ke zaune kayan duk ya baci da rarrafen datayi,ashe mai tallan ta dafa zata tashi,itakuma kallon idonta yasa ta fita dagudu.
Shuru sukayi daga Danejo har inna laari,wannan abin ba barauba kenan a gidannnan.
Babu yanda inna laari batayi da ita tazo ta ɗauki kayan tallanta ba,dole sai ita ce taje zauren takai mata tukunna.
A bakin ƙofar ta haɗu da muruje yashigo cikin gidan,tundaga baƙin ƙofah yake tafi da hannunsa,itama Bombee da take zaune tana kwaikwayonsa,koyaushe tana zaune babu mai ɗaukarta ko yi mata wasa a yara saishi,shiyasa idan taganshi tayi ta ɗaga hannun ya dauketa.
“Ina mai idon kuliyar,kamata kamata gatanan gatanan,zatasha alewa?”
Waka yaketa reramata itakuma tana dagalemasa baki da haƙora biyu a ciki.
Kinkimarta yayi zai fita waje Danejo tayi saurin cewa.
“Muruje ina zakujene haka?”
“Gidanmu zan kaita wajen umma,mu bamuda yarinya a ɗakinmu,nasan inna zata karbeta”
“Ahah muruje ku zauna a nan kuyi a wasan,karka fitada ita kaji”
” toh Innar Bombee amma bari muje zaure toh”
Fita sukayi suka zauna a zauren,inda yahaɗa abubuwan wasa kala kala,shikaɗai yaketa maganarsa ita saidai ta bishi da ido,ko kuma inya haɗa abin wasan ta rugujemasa da ƙiriniyarta,gata da kazar kazar da zafin hannu.
Ɗaukar buta tayi bayan tagama shanyar kayan da Bombee ta bata tashiga banɗaki. Bayan ta fito sai taji babu motsin muruje da Bombee a zaure inda ta barsu.
A jiye butar tayi da sauri ta nufi zauren domin leƙosu,amma babu su babu ɗuriyarsu,gabanta ne yafaɗi rass,a ranta tace shikenan ta faru ta ƙare.
Kama katanga tayi ta leƙa gidanna su.
Yana nishi daƙyar ya ƙarisa zuwa cikin gidannsu yana cewa.
“Kai sule kagani nima nasamo tawa ƴar,daga yanzu inzamuyi wasa bakai kaɗane mai ƴar wasa ba,nima ina da ita”
Yaƙarisa maganar yana kallon sulen ɗan gidan larai,yanayi yana zukuɗa Bombee wacce tayi masa nauyi saboda ƙibarta dumur dumur.
Larai ce ta bankaɗa lalubulen dakinta ta fito,aikuwa carabb idonta ya sauƙa kan na Bombee wanda suke shining suna ɗaukar hasken rana.
“Lahh ilah haillallahu yau mai zangani,yanzu wannan mai idon mayun kaje ka jajibomana cikin gidan,a garin wato cusuwarka irinna uwarka koh,wannnan ɗa zakayi abu da yawa a rayuwarka.
Wato kalan ta lashemu dukka ku babu tsiyarku,…….uhmm wayasani ma abu a duhu ko kuiɗn tsarkakkune,dan dama ance duk inda mayu suke sunajin ƙanshin mutanensu idan suna kusa dasu,babu mamaki biri yayi kamada mutum kake nanewa a gidan wannan mayyar yarinyar. Maza tun kafin raina yabaci kafitamin da wannan annobar a cikin gidannan,kafin ma ta kawo mana baƙar sa’a”
Shatu ce datake ɗaki tana famada tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe taji hayaniyar taƙici kuma taƙi cinyewa.
Ja tayi da ƙyar tafito daga ɗakin dan ganin mai yake faruwa,dan tasan kullum zancen dai ɗayane baya sanja zani.
Larai ce itada muruje,ita ko kunya ma bataji,kullum idan aka jita to ita yarane ,tun yaran suna tsoronta har yazamo yanzu sun maidata tamkar mahaukaciyah.
“Kai muruje mai yafarune ,mai kayi kuma yanzu”
“Inna Bombee fah kawai na ɗakko zamuyi wasa,shine inna larai tace wai na maidata,kuma wasa kawai zamuyi,ba kuka take ba”
“Kaga maza kaita wajen innarta kartayi kuka kaji,kadaina ɗakkota,ka dunga zuwa can ɗin kuna wasanku kaji?”
“Toh inna”
Daga haka ya juya da Bombee tiri tiri zuwa gidanna su.
Duk abinda yafaru akan idon Daneji,wacce take tsayen tana kallon su larai,hawayen dayake kwaranya a idonta ta share tareda sauƙa akan katangar,bayan taga muruje yafita zai dawo da Bombee.
A bakin zauren ta tsayah,yana shigowa tasa hannu ta karbeta,tun kafin tayi magana muruje ya sunkuyar dakai tareda bawa Danejo hakuri.
Tausayinsa ne yakamata,ganin ashe shima koƙari yake yakai wacce zasu dunga wasa a gidannsu,saidai a halin da ƴar tata take ciki bazata iya yin wasan dashi ba yanda yakeso,dan tata ƙaddarar ne warewa daga cikin mutane,saboda halittar da take ɗauke dashi.
Ko a haka ma yaron yana burgeta sosai,yanda koda darana ɗaya bai taba nunawa ƴar tata ƙyama ba,saima burinsa shine yadunga fita da ita wasa,shima a ga tasa ƙanwar,kallonta yake a matsayin kanwarsa wacce bashida itah.
“Babu komai muruje kaji,nasan kanason fita da ita,amma baka ganin yanda take ne,mutane zasu gudu idan suka idonta,dan haka ku dunga wasan iya a zaure kaji,yanzu jeka gidan kar innarka ta nemeka”
Ɗaga kai alamar yaji kafin ya tafi yanayi mata bye bye,itama tana miƙa masa hannu alamar zata koma.

___***____***____***___

Wata ƴar fara yarinya ce bazata wuce shekara biyar ba tashigo gidan tana kuka,babu ɗan kwali a kanta,silifas ɗinta a hannu,jikinta yayi butu butu ta ƙasa.
Kana ganinta kasan tuburbuɗata akayi a cikin ƙasa,kai tsaye inda Danejo take ta nufah tana mitsitstsika ido.
Tsayawa tayi da busar hatsin datake ta kalleta tundaga sama da ƙasa tareda jijjiga kai.
Bata tsayah wani bata lokacinta ba wajen jin mai yake faruwa,domin abin kullum ne kamar faɗar Allah.
Tunda Bombee tayi ƙafa tana fita waje,kullum kwanan duniya saita dawo gidan cikin kuka,wani lokacin an fasa mata vaki,a kwai lokacin dazata dawo ma jikin jini yara sun jefeta da dutsi,kowa yana cewa ga mayyah tazo.
Duk yadda kuma Danejo tayi ta hanata fita abin ya gagara,kullum tana wajen cikin yara,a cizeta a jefeta a tumurmusata,amma hakan bazai hana idan an jima ta koma ba,haka zatayi tayi har sai dare yayi ta kwanta,tun Danejo na tambayar ta mai ya faru harta daina ma tambayarta,dan zancen kullum ɗayane.
Yanzun ma jawo tayi kusada ita,tareda matsar da garin tuwon dayake gabanta tana tankaɗe. Kama gefen zaninta tayi ta kaɗe mata ƙasar jikinta,har sannan idonta yana manne tana kuka.
“Saikiyimin shuru ai,buɗe idon naga miye a ciki”
“Inna inna ƙasa ce a ciki,shule(sule )ne ya zubamin,wai idona ya rife ya daina ganinsa,shannan kuma ya tureni a ƙasha dannan karbi abin washana a wajen rahama”
“To naji kiyi shuru kinji,kullum ina faɗamiki,idan kinga zasu dakeki ki gudo gida kinji,sannan kuma ki ƙyalesu,wanda yadaki wani bai ramaba allah zai saka masa”
Rarrashinta Danejo ta dungayi,daƙyar ta samu tayi shuru ta manta da zancen,jikin dukk tabon dukane da kuma rauni,inda yara sukayi mata,abinka dama da farar fata.
Suna cikin hakanne inna laari tafito daga banɗaki tana tura ciki,haihuwa ko yau ko gobe.
Da farko jinya tafara,wasa wasa abu ya dunga yin gaba,har mlm Ahmadu ya ɗauketa zuwa asibiti,aikuwa gwajin farko aka ce cikine da ita,murna a wajen mlm Ahmadu nan ma kasa misaltuwa tayi.
Tunda aka dawo gida yayi wanan yayi wannan,haka inna laari tacigaba da rainon cikinta,wanda kallo daya zaka mata kasan tanajinsa har a cikin ranta,sannan kuma tayi godiya ga Allah,da itama yayi mata kyautar da bata taba zaton samu ba,bayan tsawon lokaci data ɗauka da cire rai.
Danejo ma a fili takeyi mata murna tareda ƴan uwa da abokan arziƙi,lokacin da labarin ya isa ga mutane ,gidan cika yayi maƙil da mutane,wai ma ba haihuwar ba kenan,inaga idan haihuwa kuma tayi?.
“Bombee mai yafarune naji kukanki daga banɗaki,ko yauɗin ma dai jiya i yau,ke bazaki rama ba kenan,taya zaki kare ƙanwar taki kuma ko ƙaninki uhm?”
“Jan dukasu idan suka tabamiin ƙanwa,bajan barsu ba Inna yaari”
Dan murmushi inna laarin tayi tareda cewa,
“Ko kefah,haka ake son babba da jarumta kinji,ki bar kukan haka,barina kawomiki ƙarago,ko bakya so kai?”
“Inasho”
“Tam barina kawomiki mutumiyar,ladan samomin allura da kikayi,wacce nake nema jiya a ɗaki”
Tsalle Bombee tayi jin za’a bata ƙarago mai suga,ita kuma murmushi tayi sannan ta shige ɗaki.
“Karfah kiyi fada a waje fah,ina kinajina koh,duk wanda yayi miki abu kizo ki faɗamun kinji,karnaji kinyi faɗa”
Danejo ta faɗawa Bombee fuskarta ɗauke da damuwan halin ƴar tata.
“To innah bazanyi ba”

…….to sai muce Allah ya sauƙi inna laari lafiyah………

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤15🖤

Tun safe inna laari take abu ɗaya a ɗaki,Allah ya haɗata da doguwar naƙuda.
Danejo kadai ke kai kawo a tsakar gidan,sai Bombee wacce take wasa a zaure,fuskarta bushe da hawaye tayi sabbabben nata wato kuka,a rana tayi kuka yafi sau a kirga,wani lokacin har zazzabi takeyi.
Larai ce tafito daga ɗakin inna laarin ɗauke da ledar mabiyya a hannunta,saida tatsayah tayi shewa tayi guɗa kafin ta kalli inda Danejo take.
“Mashaallah yarinya ta faɗo duniya,kyakykyawa fara jinin fulani usul,kuma Alhamdulillah idonta garau yake kaman na sauran mutane,da alama bayan wacce ta kawo baƙar kaddara ita kuma wannan ɗiyar albarkar farin haske ta kawo cikin gidannan”
Danejo tana jinta bata kulata ba,saboda tasan duk maganar datake da ita take.
“Iyar sule tunda ta haihu ko a zubo ruwan kai?”
Abinne ya ƙular da larai,ganin bata biyeta ba,saima sauya zancen datayi.
Ganin larai bata amsa mata bane yasa ta ɗebi ruwan tashiga dashi.
A zaune inna laarin take akan kujerar tsugunno,jaririyar kuma tana kan gado a naɗe da zani.
“Sannu addah laari,an samu kai kalau?”
“Lafiya kalau Danejo sannu fah da hidima”
“Lahh bakomai,barinaga ƴar tawa”
Cikin zumuɗi da farincikin Danejo ta nufi kan gadon da ɗauko jaririyar,buɗe fuskarta tayi,ba laifi kam kyakykyawa ce kaman yanda larai din ta faɗa,saidai bata da fari da kuma manyan ido irinna Bombee,saika kula ka gano kamanninsu,shima dan hancin baban su dukka suka iya shiyasa.
“Tufarkallah gatanan kam kyakykyawa da ita,addah laari kefa ta iyo,munsake samun Budurwa a gidan,allah ya rayata bisa imani”
Murmushin jin daɗi inna laari tayi,jin yadda ake gwaɗa ƴar tata.
“Ameen ya Allah Danejo,Allah ya bamu ikon rainonsu a bisa daidai dukkansu”
“Ameen”
Suna cikin zancene larai ta dawo ɗakin,harara ta watsawa Danejo,tunda ga kallonta zakasan bata sonta.
“Laari na kaimiki ruwan banɗaki,iyah maiganye ma tana hanyar shigowa yimiki wankan”
“To sannu da kokari larai”
Suna cikin hakane Bombee ta shigo ɗakin jikinta duk ƙasa,taga tsakar gidan babu kowa shiyasa tabiyosu.
Danejo ce takalleta tareda cewa.
“Yaki zokiga ƙanwarki ta iso to yau,kina ta tambayar yaushe zata zo,gashi tazo yau”
Aikuwa tana jin hakan ta taho gudu har tana zubar da kayan tasuke gabanta,wajen Danejo take rike da yarinyar ta nufah,inda itakuma Danejo ta iyo kasa da ita yanda zata ganta dakyau.
Hannu takai abinka da yaro zata tabata,larai ce tayi saurin cewa.
“Tsaya tsaya menene haka Danejo,saikace bakya kula,jaririyar da ko suna ba’ayi ba zaki bar wanann ƴar taki ta daba,idan kuma ta shafamata wannan idonnata fah,ni wlh yanzu haka a takure nake data shigo ɗakin,inaga kuma jaririyar da aka haifa yau”
Dagowa daneji tayi ta kalli larai tareda rike hannun Bombee wacce take ƙokarin taba fuskar jinjirar.
Cikeda bacin rai Danejo tace.
“Wai nikam larai mai na taremiki a rayuwane,koyaushe cikin jifana da kalam mayu kikeyi,ina kawar da idona ina raga miki domin girmanki amma bakya gani koh,fisabilillahi banda abinki yaushe wannan yarinyar tasan kalmar maita. Dazakice zata shafamata idonta,itakuma waya shafa mata kenan?.
Ni inada imani da tawakalli sannan kuma na yarda Allah ne yayi ta haka,domin haka yaso ya ganta,ina da labarin duk izayar da kike saka ƴaƴanki suyi mata a waje,na barine saboda fitina bbau daɗi………”
“Aikin banza kin daɗe baki bari ba,dan Allah ki ɗau mataki kinji,ke bakisan kema ragamiki ake saboda darajar mlm Ahmadu ba,banda haka da tuni an daɗe da korarku daga garinnan keda wannan mayyar ƴar taki,waye bai san irinku da harkar maita ba. Kullum saiki tura ta tana shiga cikin ƴayanmu kalan ta cinye su,hakan bai miki kin kawota kusada jinjira saboda ta lashi samuwar kuruwa koh?”
Suna cikin maganar ne Danejo ta manta tasaki hannun Bombee,aikuwa kaman jira take itama tarigima ta ɗora hannun akan jinjirar.
Tana ɗora hannun yarinyar ta callara ƙara kaman an zare mata rai lokaci guda.
Zaro ido Danejo tayi tareda kallon mai yafaru,dama haka larai take jira,aikuwa da sauri ta sure jinjirar daga hannun Danejo.
“Kingani koh kinga ni ko akan idanki,ke kuma laari barsu su kashe miki ƴa tun bakiji ɗuminta”
Buɗe baki Danejo tayi zatayi magana,inna laari tayi saurin cewa”
“Danejo kiyi haƙuri,amma larai gaskiya tafaɗa,bai kamata a dunga barin Bombee tana zuwa kusada yarinyar ba,musamman da yanzu tana jinjirar,saboda gudun kar wani abu ya faru,idan gaba ta girma babu matsala saita rabeta”
Lokacin da inna laari ta baɗi hakn,daneji ji tayi kaman an doka mata guduma a ranta,saidai yazatayi gaskiya suka faɗa,kowama inshine bazai yardaba,musamman yanda tayi shekara da shekaru babu haihu,lokaci ɗaya Allah yabata,zata iya komai domin kare ƴartata da mungun abu irin ƴar tata.
Ƙoƙarin maida hawayen idonta tayi,tareda jan hannun Bombee suka fita daga ɗakin,wacce take ta yunƙoron kamo jinjirar daga hannun larai,buge hannunta larai tayi tareda gallamata harara.
Hanyar ɗakinta tanufah idonta yana zubar da hawaye.
Zama tayi akan kujera tareda saka Bombee a gabanta tana kallonta.
Duk wanda yaga Bombee zai iya ɗauka cewar badaga nigeria take ba,farace sosai mai kyau,kana ganinta kaga fulani,bayan idanunta wanda su suka rana kamanninta da ƙasar tata,dan idan tana kallonka,mus

musamman idan ka zuba mata ido na wani lokaci,kana ganin yanda ƙwayar idon take girma sannan kuma tana ƙanƙancewa gwargwadon yanayin hasken dayake wajen,ga ƙwayar idon blue shar,kullum sake clear take da tana girma.
Babu wanda zai kalleta yace ba a ƙasashen turawa aka satota ba.
Kama hannunta Danejo tayi ta haɗasu kafin tafara magana cikim karayar zuciya.
“Zakiga jarrabawa a ratuwarki kala kala Bombee,amma kiyi haƙuri ki daure kinji,nidai fatana shine ki dunga haƙuri idan anyi miki abu,wanda yajefeki da sharri ki mayar masa Alkhairi,wanda yaƙyamaceki karki ji haushinsa,kiyi nesa dashi kawai saboda karya cutar dake,idan kinje wajen da bana tareda ke,ki tuna Allah na tareda ke kinji”
Tana gama faɗin hakan ta rungumota jikinta,tareda ƙara sautin kukanta.
A cikin kunnenta tajiyo ƙaramar muryar Bombee.
“Inna ki daina kuka,ko su sulene suka dukaki,insun dukaki bazan barsu ba,saboda dukan su da ciwo sosai”
Ƙara ƙanƙameta tayi jin abinda take cewa.
“Ahah basu dukani ba,in sun dukani ma zai wuce watarana,idan ban ramaba Allah zai ramamin,kuma inya tashi ramamin da zafi zayyi musu,suma suyita kuka”
Ƴar dariyah tayi kafin tace.
“Heer kuma nayi ta musu dariya yanda suke min idan ina kuka koh?,uhm inna barina je wajen yarinya”
“Ahah karkije wanka ake mata,sannan babu kyau a je wajen yarinya idan tana ƙarama,saita girma tukunna sai a goyamiki ita,ina kinaso koh”
“Eh inaso,zan jira ta girma toh saimuje wasa,nima shikenan nasamu ƴar wasa irinna su Sule”
A hankali da lallami Danejo ta dunga amfani da hankalin Bombee,har ta koyamata kartaje kusada ɗakin inna laari,saboda gudun abinda zaije ya dawo.

Ranar suna biki da bidiri akayi,inda yarinyah taci suna khadijah,mahaifiyar inna laari,ana ƙiranta da Innayi.
Haka akaci aka watse kowa yakama gabansa,aka bar mai jego da rainon ƴarta.
Haka rayuwar tasu tacigaba da kasancewa tareda ƴaƴannasu,Danejo ce mai yin girki kasancewar inna laari tana jego.
Ko yaushe idan ka jisu itada Bombee to akan taje wajen innayi ne,sau goma zata shiga ɗakin sau goma zata korota,tun abin yana da damun Danejo har tashafawa ganta lafiyah ta zuba musu.
Duk sanda a yanzu mutum ya zauna da inna laari batada aiki sai zancen ƴar ta,wani lokacin a shiryata a kaita gidan larai,sai tayi kuka a saka sule ya kawota.
Itadai Danejo ido ne nata kawai,dan tafi danganta hakan da inna laari tana son ƴar ne bata son Bombee ta rabeta.
A bangaren mlm Ahmadu kam,tabbas yayi murna ta haihuwar innayi sosai,amma kuma har yanzu soyayyar Bombee a ransa ta dabance,don ko boyewa baya iyayi,abin kwanciyar hankalin ma shine inna laari batada dakuwa da hakan sosai,ita indai tana son ƴar ta shikenan.
Ranar daya gane inna laari bata son Bombee ta dunga kusantar innayi abin yabaci haushi,hakan yasa ya ƙirasu dukka a turakar sa,kallonsu yayi cikin kulawa kafin yace.
“Uhm uhm toda farko dai inason yimuku ƴar nasihane.
Duk garinnan babu wanda baya yabonku a zaman lafiyah,amma kuma sainaga abinda ya batamin rai,shine kuna ƙoƙarin raba kan ƴaƴanku da kakanku,musamman daga bangarenki Laari,kuma wai kece babba,hakan bai dace ba.”
“Mlm kayi haƙuri,gani nayi data tabata ranar haihuwarta tayi kuka,kuma sannan larai tayi min kashedin na kiyaye”
“Saboda ita larai ɗin itace tafiki sanin yakamata,idan akwai abin citarwa a jikin Bombee kaman yanda mutane ke faɗa,ke ya kamata ki rigasu sani. Dan Haka dan Allah karku bari wasu su ruguzamin zaman lafiyar gidana,ku haɗa ƴaƴan ku ku rainesu tare,su tashi cikin ƙaunar juna”
Tundaga wannan lokacin inna laari ta daina abinda take,dan har ƙiran Bombee take tasaka mata ita akan cinyarta. Wannan abin yayiwa Bombee dadi sosai,don sakawa tayi a ranta wataƙila lokacin yayi da innarta tace za’a dunga bata itah.

Shigowa tayi da gudu tareda ɗanewa mlm Ahmadu wanda yake zaune a kan tabarma yanajin rediyo.
“Baba nayi ta ɗaya a makarantar Mlm Alwasu,kagama ya bani biscuit,sai mu raba nida innayi koh”
Tafaɗa tana nuna mlm Ahmadu allonta cikin murna”
Hannunta yakama wanda Allon yake tareda share ƙasar dake kan ciwon wajen,wanda yake fitar da jini.
Cikin tausayawa ya kalleta tareda cewa.
“Wannan kuma uwata a ina kikaji,faɗuwa kikayi?”
“Ahah su bello ne suka tureni akan itace suna cewa ‘mayyah taci na ɗaya’,baba wai sunana mayyah?”
“Ahah ba sunanki mayyah ba,mai kika ce musu toh”
“Ban kulasu ba,kawai cewa nayi idan ban ramaba Allah zai ramamin,yanda inna tace na dunga faɗa”
Kanta yadafa cikeda tsantsar ƙauna kana yace.
“Hakane uwata,hakane ɗiyar albarka,wanda aka zalunta bai ramaba Allah zai saka masa,kinyi daidai kinji,haka nakeso ki kasance kullum,ina alfahari dake uwata,Allah ya albarkaci rayuwarki”
Duk abinda suke su inna laari suna kallonsu,suna gyaran ganyan shayin mlm Ahmadun.
Sai bayan sun gama taɗinsu irinna uba da ƴa kafin ta nufi wajen su danejin ta nuna musu.
Kafin daga baya ta miƙawa innayi nata biscuit ɗin.

*forseen*
…………..Babu wanda yake sonki,kifara son kanki,duk wanda ya ɗaga miki hannu ki karyashi,ke ba sa’ar su bace,muna tare dake fansa fansa fansa
Shuru tayi tanajin maganar da sheɗaniyar muryar takeyi a cikin kanta.!!!……………..

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤16🖤

Saka ƙafa yayi yaƙara takata a ƙasa haɗeda cije baki.
“Faɗamin ina so ki amsa cewar ke mayyace,baƙar mayyah babu abinda ya dace dake sai duka dakuma hantara,kar ma ki sake gigi cigaba da zama a ajinmu.
Kunkoroki munyi miki komai amma kinƙi barin ajinmu ko,saboda ki nuna mana halinki na mayu,to idan muka koma gobe naganki a cikin ajinmu sai dakaki”
“Zulaiha ce taƙarisa faɗin hakan,ƙanwar bello abokin sule.
Da Bombee a primary 5 A take,saboda yanda suka maidata kaman jakarsu,yasa mlm Ahmadu yaroƙi alfarmar a maidata primary 5c.
To shiɗinma ajin su Zulaiha ne ƴan anguwarsu,duk yanda Bombee take iya koƙarinta wajen ganin ta ƙauracewa masu cutar da ita,abin yaci tura,kullum cikin fuskantar ƙalubale take.
Fatarta tayi baƙiƙƙirin,banda tabon izayar da mutane sukeyi mata babu komai a jikinta,tun tana kuka tana kaiwa Danejo kukanta har ta daina,ganin babu wanda zaima dubeta ballantana yaji kukantan ko kuma tausayinta.
Mata biyune a tsawon rayuwarta suke dubanta da idon rahama,daga Inna shatu mahaifiyar muruje sai kuma Innarta. MURUJE shine wanda takejin daɗin zama a kusada dashi,to shikuma yatafi boarding karatu,shekararsa biyu kenan da tafiyah.
Ɗago fashashshiyar fuskarta tayi tana kallon zulaiha,wacce tsayah akanta da hijabinta a ɗaure a kunkuminta tana rawar masifah.
“Ƴar gidan mayyah,daina kallona da wannan idanuwannnaki,kurwa ta kur in faɗamiki”
Tashi tayi tafara kaɗe uniform ɗinta tareda sake kallon Zulaiha.
“Menene kalmar mayyar nan da kowa ke bina dai tane,wane yaro naci a garinnan da wanann sunan yadace dani,hmm ke innayi zo mu tafi gida kar a ga mundaɗe bamu dawo ba”
Kama hannun innayi tayi wacce take tsaye da jakkunnasu a hannunta,ita ajinta biyu a primaryn,dan haka duk abinda ake bata saka baki,duk da itama wani lokacin tana karbar nata dukan,a matsayinta na ƙanwar Bombee.
“Idan kika kuskura kika bita,kema saina miki duka,inaso ki kalli cikin idonta ki faɗamin wacece Bombee”
Hannunta ta cire daga na Bombee tareda kallon idonnata.
“Uhm mayyace”
Zaro ido Bombee tayi jin sunan da ƙanwar tata taƙirata dashi itama,abinda tunda take bata tana zaton zataji ba,tun tasowarta bata san komai ba sai soyayyar ƙanwarta ta,a ganinta ko kowa yaƙita ita bazata juya mata baya,saboda ita jininta ce,shiyasa wani lokacin idan yara sunayi mata tsiyah fuk yanda zatayi takan kare ƙanwartata,amma kuma yau abinda taji daga bakin ƙanwartata ya kwance mata ƙwalkwalwa fiyeda tunanin mai tunani.
“In…..nayi kema …..mayyah kike ganina kuma …..dodanniyah?”
“Hhhhhh da alama bakisan mai ƙanwar taki take ba koh,to koda kinje wani waje kin buyah ita take zuwa ta faɗamana inda kike,komai da saka hannunta,mai kike tunani zaki samu wanda sai kareki wai ……….ke ba mutum bace,babu wanda zai yarda dake,ko uwarki ma nasan ba sonki take ba,dan haka idan zakiso kanki kiso kanki”
Rufe ido Bombee tayi gam,lokaci guda kanta yafara wainawa,wani tururi mai cikeda baƙin duhu yafara tasowa daga cikin kanta zuwa sassan jikinta.
Gabaɗayah abubuwan da akayi mata tsawon rayuwar ta tafara tunowa,duk lokacin da aka zalunceta babu wanda taba rama mata.
“…..ni mayyace,babu wanda yake sona,dole naso kaina kuma na ɗau fansa……..babu wanda zan ragawa daga yau koshi waye……..sai na ɗau fansa…….saina rama”
Tunanin cikin kantane yafara cuɗanyah yana zama duhu,yayinda lokacin guda tunanin ta yatashi daga positive zuwa negetive.
Tafi minti biyar tana sauraron zugon da wata shaiɗaniyar murya take yima ta a cikin kanta,kana daga bisani ta buɗe idonta.
Sauƙeshi tayi akan Zulaiha wacce tayi shuru tana kallon ta tun sanda ta rufe idonta.
Zaro ido Zulaiha tayi ganin idon Bombee ya tashi daga Blue mai haske zuwa blue mai duhu,sannan kuma ga wani murmushi akan fuskarta kaman baƙin aljani yafito daga wuta.
Ja da baya tafarayi ganin tana tunkaro ta,cikin murya mai ɗauke da muradin ɗaukar fansa tafara magana.
“Bakince ni mayya ce ba,sannan kuma kinbani amsar dogon tunnain dana daɗe inayi a rayuwata,shine naso kaina babu mai sona.
Daga yau nafara son kaina,kuma babu mahaluƙin daya isa hanani ɗaukar matakin duk abinda wani yayimin.kema …..kuma a yau banga shegen da duk faɗin gembu zai ceceki a wajena ba,saina yimiki ƙasa ƙasa anan wajen”
Daidai da lokacin data gama maganar ta iso kaman Zulaiha,tamkar ƙaramar baƙar kububuwa.
Hannun Zulaiha ta kama tareda juyata ta baya,babu bata lokaci kuwa ƙashin hannunta na dama yabada ƙarar ‘ƙarallll’
Bata barta iya haka ba ta bita duka ta ko ina kaman an aikota,tun Zulaiha tana kuka har ta daina sai nishi take kawai na wuyah.
Wani babban mutum ne zai wuce yakalli abinda ya faru,da sauri kuwa ya isa wajen ya dauke Bombee daga kan Zulaiha,wacce idonta ya rufe da muradin ɗaukar fansa.
Faɗa mutumin yafara yiwa Bombee,amma ko kallonsa batayi ba ta fisge jakarta daga hannun innayi tayi gaba.
Baki ya saki galala yana kallon yarinyar da ko kaɗan bata ɗaga ido,yau itace ta gallah masa harara hmmmm.
Juyawa yayi kan Zulaiha wacce take kwance sai zuba nishi take kaman mai shirin haihuwa.
Ɗaukarta yayi a kafaɗa ya nufi gidansu da ita.

“Haba gaji haba gaji,yau ki duba kigani,wai abinci kike rabawa,nan Robar kashice yara sunyi ba’a zubar ba,suma kuma ba’a wanke musu ba.
Ga ƙwanukan wanke wanke tun safe ƙuda yake bi amma ba’a wanke ba,sai yanzu da za’a raba abincin kafin ake wankewa ra ruwan ana zubawa.
Wai yaushe zaki gyara ne idan baki gyara yanzu ba?”
“Haba mlm nifah ka dameni ehe,kullum faɗan yau daban na jiya daban na gobe daban,baka ganin banida lokaci ne iyae,dawa zanji,dakai zanji ko kuma da ƴaƴan ka koda sana’a ta.
Da ciyar damu ya ishemu mana,idan ka wadatar damu aiki ya ragumin saina gyara,amma aikin banza babu zuciya sai shegen surutu,to karka dameni ni”
Tana cikin masifar ne kan gari ya gari sukaji sallama a wajen.
Mlm idi dama neman hanyar zillewa masifar Gajin yake,dan haka da sauri ya fita wajen.
Bai daɗe ta fitaba sai gashi ya shigo hannunsa riƙeda Zulaiha rai a hannun Allah yana salati.
“Ya ilahi gaji kinga fah,yanzun nan wani bawan Allah yaganta a hanyar makaranta ƴar gidan mlm Ahmadu ta hau kanta sai dukanta takeyi.”
“Naaa shiga uku ni gaji,yau mai zan gani haka,ai wanann mayyar yarinyar,ko ba itaba kai?”
“Eh itadai,da farko nima saida nayi mamaki,yarinyar dako magana bata cikayi ba,wai itace tayi wannan aikinta.
Sai yacemin dayayi mata magana ba harara ta zabga masa tayi tafiyarta”
“Kai malm dubafah hadda karayah tayi mata,kan ubancan ni kuwa zanga shegen dazai rabani da su,shari’ah daga nan har gaban sarki,banza na haifawa ƴar dazata mata wannan aika aikar”
Tunda suka kamo hanyar gidan Bombee batace komai ba,itama Innayi bata kulata ba,tunda taga abinda tayi koh jerawa da ita taƙiyi.
Lokacin da suka shigo gidan ma Bombee batayi sallama ba,iya Innayi ce kawai tayi a ƙasan maƙoshinta.
Inna Daneji ce take rarraba abinci,yayinda inna laari kuma ta fito daga banɗaki ɗauke da buta a hannunta,shikuma mlm Ahmadu yana alwala zai tafi masallaci.
“Yau ma faɗan kuka sakeyi koh,waye kuma ya dakeki yau”
Daneji ta tambayi Bombee tana cigaba da aikinta,kana ganin fuskarta zaka hango tsagwaron tausayin ƴar tata,amma kuma bata da ikon yin komai akai.
“Ahah ba wani ne yadake ta ba,itac……..”
Tun kafin innayi taƙarisa magana Bombee ta ɗauketa da mari tassss.
“Munafuka kawai,dankinga nayi shuru ban kulaki ba shine har kika samu bakin magana koh,kisake cewa wani abu saina yimiki fiyeda nata,kuma daga yau kika sake yin munafurcina a ko ina ne saina yanke miki baki”
Tana gama faɗin hakan tayi hanyar ɗakinsu tareda barin innayi a tsaye a tana kuka ta dafe kuncin.
Kowa daga cikin mutanen gidan,baƙaramin kaɗuwa yayi ba da abinda yafaru,babu ma yah Daneji wacce take ganin shikenan ta faru ta ƙare,komai ya gama faruwa.
“Ke innayi mai ya faru faɗamin”
Saurin jijijjga kanta tayi jikin yana karkarwa.
“Baba bazan iya faɗaba,tace zatayimin irin abinda tayiwa Zulaiha,baba wannan ba addah Bombee bace”
“Naji to kekuma mai kikayi mata taƙiraki da munafuka uhm”
Nan ma shuru innayi tayi kanta a sunkuye,da alamar rashin gaskiya a fuskarta.
“Ki fadamin mai yasa tace miki munafuka”
“Uhm dama…..dama….nice nake faɗawa su Zulaiha inda Bombee take idan suna neman ta”
“Meyasa kike faɗamusun toh,waye yace ki dunga faɗamusu,sune suka sakaki”
Girgiza kai innayi tayi,tareda ƙara sautin kukanta,hsr mlm Ahmadu ya buɗe baki zayyi magana inna laari tayi saurin katseshi tareda yin magana,dan dama tun sanda Bombee ta mari innayin tafasa shiga ɗakinta.
Tabbas kana kallon fuskarta zata tabbatar bataji daɗin marin da Bombee tayiwa ƴar ta ba,amma haka ta daure tareda cewa.
“Mlm yanzu dai duk wannan bashine abun yi ba,yakamata aji ita tabakin Bombee mai yake faruwa,saboda bata taba shigowa gida a haka ba.
Ke kuma innayi shiga ɗakina ki sanja kayan,karkije inda take yanzu saita huce.
Jijjiga kai mlm Ahmadu yayi tareda numfasawa,da alama ya yarda da abinda inna laarin tafaɗa.
Duk abinda ake Daneji batace komai ba,ta lume cikin kogin tunani,sai daga bayane ta tashi ta nufi hanyar ɗakin su Bombee.

………mai zata gani??!!!!!😲😲😲.
Ku biyoni muje mugani gobe…….

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤17🖤

Jikinta sanyi kalau tashiga cikin ɗakin su Bombee,domin batasan mai zata ganewa idonta ba,saidai duk da hakan tana fatan Allah yasa karta ga abinda zuciyarta take raya mata.
Labulen ɗakin ta ɗauke ta rataye ,hasken rana yashiga ɗakin,domin yabawa ɗakin ishashshen hasken dazata ganta dakyau.
A kwance take ta rufe idonta kaman mai bacci,saidai kana gani kasan ba baccin take ba.
“Bombee”
“Na’am ta amsa a dake”
Shuru Daneji tayi kaman mai nazari kafin ta zauna a kusada ita.
“Shin menene ya farune kika sanja a lokaci guda,duk abinda akayi miki nasha faɗamiki kiyi haƙuri,karki bari bacin rai ya sanja miki rayuwa,abinda kikayi kimsaka mu damuwa gabaɗaya,so kike kijawo mana magana.
Yanzu inaso ki faɗamin mai kikayiwa Zulaiha danaji innayi tayi maganar?”
“Karya mata hannu nayi,sannan kuma nayi mata duka kaman yanda itama tayimin,sannan bandamu ba tacemin mayyah,amma ke tacewa mayyah,sannan tace inna isa nanuna ina son kaina,shiyasa na nunmata ina son kaina ɗin”
“Me Bombee karya mata hannu kikayi,wai nasan gaji bazatayi shuru wannan zancen ya tafiba saita ɗau mataki”
“Tsawon lokaci ai nima Zulaiha tana dukana baki taba cewa komai ba,shine ita danna rama saita ɗau mataki,to ta ɗau matakin mana”
“Kee Bombee yaushe kika fara yin maganar manya da wannan rashin ladabin haka,karki dauki wannan halin ki saka ranki,hakan babu kyau musamman ga mace”
Cikin halin damuwa Daneji tafara yiwa Bombee nasiha dajan hankali. Tun bayan kwana uku dama ta kulada yanda Bombee tafara sauyawa,koyaushe tana cikin fushi,abu kaɗan idan akayi mata saita ɗaukeshi da zafi,sannan idan abun mugunta yafaru tafi kowa dariyar mugunta.
Jiya da ragon mlm Ahmadu ya sunkuci inna laari a kunkumi,data fara dariyah har faɗuwa saida tayi,sabanin da da idan hakan yafaru saidai tayiwa mutum sannu.
Tun a lokacin Daneji tafara kula dacewar ba lafiya ba,kwana tayi tana sallah da daddare,tareda kaiwa kukanta ga Allah,akan Allah ya kare mata rayuwar ƴar tata.
Muryar Bombee ce tadawo da ita cikin tunanin data tafi,wanda hakan yasa tayi zumbur ta kalli Bombee,wacce take kallonta da mamakin wane tunani take haka.
“Inna nasan kina iya ƙoƙarin ki wajen nuna min rayuwa,sannan kuma keda baba ku kaɗai kuke nunamin so kaman yanda iyaye kewa ɗansu,nasan kuma kin kulada canzawa ta a yanzu wanda nima naji,saidai babu yadda zanyi inaga yanxu ne yanda nake,ba yanda kuke son na zama ba dafarko.
Bazan boyemiki ba,amma daga yanxu kaff garinnan samun zaman lafiyar yaro shine kar yashiga harkata,bazan iya yimiki alƙawarin zan ƙyaleshi ba”
Tun kafin Daneji tabawa Bombee amsa taji sallamar gaji a cikin gidan,wacce tajita dumm a ƙirjinta kaman ganga.
Har ta fita tadawo wajen Bombee tareda yimata gargaɗin akan karta kuskura tafito komai taji.
“Salamu alaikum ina mutanen gidanne ina ta raraka sallama,ehh zakuyi shuru mana sabo dodanniyar ƴar ku taje zata kashemun yarinya a banza. To bilahillazi bazan yarda ba,ko ni ko ku ne a cikin garinnan,mlm Ahmadu yazo yanzunnan yabani kuɗin ɗori da kuma nasiyan magani”
Tana cikin zazzaga masifarne Daneji tafito daga ɗakin su Bombee tana kallonta.
Tsayawa tayi bata ce uffanba har saida gaji takai ayah a kan masifarta tukunna.
“Naji duk abinda kikace gaji,haƙika yarinya bata kyauta ba,amma inshaaallah za’a ja mata kunne,dan Allah ayi hakuri a sasanta a hankali”
“Sasanto? Ke kika sanshi nibansanshi ba,yanzu haka ma nasaka mlm idi ya nufi gidan mai anguwa yafaɗamasa,dan baza tabs yarda ba,wannan abu ke keganinsa ƙaramar magana,amma a wajena tafi dutsen dala”
“Haba gaji,menene na kaiwa ƙara kuma,abunnan fah yara ne suka aikata ba masu hankali ba,kuma inshaaallah zan ja mata kunne bazata sake shiga harkar ƴar ki ba daga yau”
“Hmmm ke kuma tashafa,nidai sai an biya kuɗi a radu,kuma wlh zata fito waje ai saina saka an babballamin ita,gayyar tsiyah kawai”
Tana gama faɗin hakan taja tsuka tareda yin hanyar zaure,zaninta a hannun sai kuncewa yake tana gyarawa.
Kafafun nan furuuru,kana ganinta kasan daga gaban murhu ta taso.
Sai wajen goshin la’asar kafin mlm Ahmdu ya shigo gidan,suna can wajen mai gari kan case ɗin karayar da Bombee tayiwa Zulaiha.
“Sannu mlm ka dawo?”
“Eh sai yanxu muka samu ƙurar ta lafah”
“To Allah ya kiyaye ta gaba,ka basu kuɗin gyaran ina?”
“Ban basu ba,cewa nayi bazan bada ba ai tsautsayine,sannan kaff anguwar nan babu wanda bai san irin izayar da ƴayan mlm idi ke ganwa Bombee ba tun tana ƙarama,haka mukayi shuru muka kauda idanuwan mu,sai yanzu kuma dan tayiwa ƴar su ace nabada kuɗi,suma suje suyi jinyarta suji idan da daɗi”
“Amma mlm bakace haka ba,kafi kowa sanin irin hatsarin dake tattareda yarinyar nan idan zata dunga ɗaukar hukunci,bai kamata muyi shuru bamuyiwa tufkar hanci ba,saboda da alama tafara warewa daga yanda muka tukata”
“Zancenki haƙƙune,amma to yakike ganin zamuyi,mlm Alwasu yariga ya faɗamana akan kar mu kuskura mu koma gareshi,amma zan leƙa ta wajensa nayi masa bayani,wataƙila bazai rasa wani abu dazayyi mana ba”
Shuru sukayi jugum kowa yana saƙa abu daban a ransa.
Saida aka ɗauki kwana uku ana case ɗin Zulaiha da Bombee kafim abin ya lafah,itadai an barta da ciwon hannu,babu damar zuwa makaranta.
Yanzu Bombee ta ɗan samu lafiya a wajen yan ajinsu. Tunda ga wannan lokacin Bombee ta daina kula kowa,koyaushe harkar gabanta take,makaranta ma ba hanya ɗaya suke bi da innayi ba,da alama inna laari ta gargaɗeta akan karta dunga shiga harkarta.
Saida akayi darasi ɗaya aka sakeyi kafin Bombee tashigo ajin,da alama wani wajen tabi ,dan tunda wuri innayi tashigo makarantar.
Batayiwa kowa magana ba ta nufi wajen zamanta,haɗa ido sukayi da Zulaiha wacce har yanzu hannunta yana saƙale da wuyanta.
Wani mungun murmushi Bombee tayiwa Zulaiha,mai ɗauke da gagarɗi a tareda.
Aikuwa da alama saƙon ta dake son isarwa ya isa inda takeso,don lokaci guda jikinta yafara rawa,tayi saurin sunkuyar da idonta.
Bombee tana zama taji muryar malaminnasu yana magana.
“Ke Bombee tashi ki fita daga ajinnan,dan iskanci sai yanzu kike zuwa makaranta”
“Kayi haƙuri mlm,innata ce ta aikeni,kuma anyimin horon makara a waje”
“Babu ruwana da wannan horon,ki fitamin a aji yanzu nan,dama ana faɗan ke hatsabibiya ce ashe dagaskene,dolema ki bar makarantar nan”
Kallon mlmin Bombee take,tareda yin tunani a ranta. Kenan shima dama baya ƙaunarta kaman sauran mutane,saboda tanada ilimi shiyasa yake kulata ashe,duk wannan tsawon lokacin kallon hatsabibiyah yakeyi mata.
“Shikenan mlm zan fita,amma kaman yanda na aikatawa Zulaiha yauma zanyiwa Abdul ɗan nursery 3 a hanyar tafiyah,inya tambayeni menene dalili saina ce jawo maka akayi.
Yanzu hakama idan na fita ƙiransa zanyi muyi wasa a can gefe”
Zaro ido malamin yayi jin Bombee ta ambaci sunan ɗan sa dayake ji dashi,yaushe yarinyar nan tazama haka?
Ya faɗa a ransa,zaman sa lafiya ya rabu da ita,idan takaryawa abdul ɗinsa hannu yau ya zaiji.
“Ahah babu komai koma kiyi zamanki ma,basai kin fita ba”
Jijjiga kai tayi tareda faɗaɗa murmushinta kana ta zauna.
Kamo hanyar gida tayi ita kaɗai,bata da abokiya ko kuma aboki,iya ƙanwarta ce,itama kuma anrabasu tun ranar da abinnan yafaru,bazata iya cigaba dajanta jikinta ba,bayan tasan basonta take ba.
Maganar bello taji a bayanta,wanda hakan yabata mamaki,musamman da taji da ita yake,rabonta dashi tun sanda yayi mata duka wancan watan.
“Ke ki tsaya a inda kike,hhhhh bantaba zaton yanda kike har zaki iya karya wani ma,waninma ƙanwata,ke wacece face dodanniya abar kawarwa. Bakiyi mamaki ba daban tareki ba kaman ko yaushe a hanyar gidanku,gaji ce ta hanani sumar dake tun wancan lokaci,saboda abinda kikayi yana sabo,amma yanzu zanga wazai ƙwaceki a wajena,mutuwa ma zaitayi shakkar ƙwatarki yau a wajena,saina saitamiki notin dayake son kuncewa a cikin kanki.
Duk maganar dayakeyi Bombee batace masa uffanba,sai binsa kawai take da idonta a duk lokacin dayaje ya zagayota.
Abinda bai kuladashi ba shine,yanzu idonta a tsaye yake babu alamar tsoro ko firgici sa’banin da,da yanzu ta tsugunna tana bashi haƙuri.
“Ohh ashe naga da alama har ƴar jarumta kika samo koh?”
Toshe hancinta tayi da hannunta tareda cewa.
“Banta’ba kulaba sai yau,ashe kai mungun ƙazami ne,bnada ɗoyi babu abinda kakeyi,ga baki a dafe kana yaro ƙarami ka fara shaye shaye,shayeshayen ma na ƙananan ɗan iska,banza shashasha.”
Daga bellon har su sule shuru sukayi suna kallon Bombee,wacce ta kafe bello da ido tana zubamasa magana babu alamar tsoro.
Hannu ya ɗaga ya zanga mari mari a fuska.
Haka tayi ƙiƙim bata matsa daga inda take tsayeba,tofar da yawun dayake bakinta tayi mai haɗe da jini.
“Waifah irin wannan marin kakemin da sainaji tsoronka koh,ashe ma bakada ƙarfi,duk yunwa da sigari ta cinyeka,amma bari kaji nawa yayake?
Tun kafin yagama haddace mai tace a ƙwaƙwalwarsa yaji wani mari a kuncinsa,ba iya marin ba harda wani zafi daya jiyarceshi a wajen.
Tangal tangal yayi kafin yasamu ya cake,hannunsa yasaka a wajen tareda zaro ido lokacin dayayi arba a hannunsa,jinine jajur a hannunsa.
Hannayenta biyu ta saka a wuyansa,ta nutsa faratanta a wajen.
Ihu yasaka iya ƙarfinsa saboda ciwon daya ziyarceshi.
“Banfara ɗaukar mataki ba saida nashiryah,ko babban mutum idan yanason cin galaba a kaina bazai iya ba ballanta ku ƙananan ƙwari,kusaka a ranku bazaku iyah cin galaba a kaina ba ko kaɗan,mai son gwadawa kuma ga wajenan,mai tsoro ka fasa”
Sakin wuyannasa tayi,ta barshi a tsugunne yana tarin wahala,kan kaceme jini ya wanke gefen rigarsa inda ta karzamasa zanen faratunta.
“Ana zugaka shugaban yara,nibanga sarauta anan ba,dan haka na karbi sarautar daga yau,ko kanaso ko baka so ka bani matsayinka,Sannan babban jan kunne kar kowa yasake ɗagamin yatsa cikinku,idan kunji kun tsira”
Tana maganar tana fita cikin murya kaman ba tata ba,sannan kuma tanayi tana wata irin dariyah kaman shaiɗaniya.
Kallon sule tayi wanda tun ɗazu ya jefar da bulalar take hannunsa ta dukan Bombee ɗin.
“Ka tahomin da jakata gida,sannan duk wanda yakeda niyyar ɗaukar mataki akaina shima kada ya fasa”
Daga haka ta bar lungun ta nufi gidansu.

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤18🖤

Wulgawar Bombee innayi tagani tana cin abinci, yaukuma ta dawo da wuri.innayin tafaɗa a ranta,kullum sai yamma liƙis take dawowa idan ta tafi makaranta,wani lokacinma sai dare yayi tukunna.Sau uku mlm Ahmadu yana kamata yana dukanta,amma ko kuka batayi,sannan kuma bata faɗi inda take zuwa ba,sannan kuma bata fasa kaiwa daren ba.
“Inna Daneji Addah Bombee tadawo tana ɗakinmu”
“Yauɗin kotaji magana babannku kai,amma a wanne yanayi tashigo”
“Uhm hannun duk jini har ya bata mata uniform ɗin jikinta”
Innayi ta faɗa a hankali,cikin sigar gulma,saboda kar addar tata tajiyo ta,aikuwa Alƙalamin ya ƙarye,dan duk maganar da takeyi a kunnenta sarai.
“Jini kuma wanne iri,yauni kuwa mai zangani a duniyar nan,hadda jini”
“Ahh toh Bombee ai tazama abinda tazama sai du’a’i,ke kuma ban hanaki shiga harkarta ba ne,sai tazo tana dukanki koh”
Inna laari tafaɗa tareda zabgawa innayi harara,yanzu kowa yasan inna laari haushin Bombee takeji,saboda a rana idan ta duka innayi yafi a ƙirga,wani lokacin ma wai dan kawai ta kalleta,a wajen kwanciya kuwa wajibine saita yi mata na bacci. In abun bai zo ba kuwa saitayi sati bata kulata ba.
Hanyar ɗakinnsu Daneji ta nufah tareda tsayawa akan Bombee,wacce take zaune a tsakiyar gadon ta bawa ƙofah baya.
Zaro ido Daneji tayi data kalli yatsun Bombee,dan dama su tazo gani domin da ta tabbatar da zancen innayi,aikuwa hakane farcenta zaƙo zaƙo duk jini a jikimsu tamkar faratun mayu,yaushe ta tara wannan faratun haka babu wanda yasani.
“Bombee menene haka a hannunki kaman jini,na wanene?”
“Jinin bello ne,yatareni zai ɗau fansar abinda nayiwa ƙanwarsa,nikuma na yanka masa fuska da farcena”
“Yanzu dan yazo ɗaukar fansa saiki yanka masa fuska,bazaki kawo ƙara ba gida,kinkuwa san hukuncin hakan”
“Nasani kuma babu abinda ya isa yayi daga shi har iyayensa,idan aka sake nima zan sake,batun nakawo ƙara kuma menene amfaninsa,shin tunda nake an taba ramamin idan wani ya zalunceni,saidai a bani haƙuri zancen ya wuce,dan haka ni gaskiya bazan sake yarda da wanannan tsarin ba,dole na kawo nawa tsarin nima”.
Dan takaici Daneji bata sake cewa komai ba,saima fita da tayi tabar ɗakin,abin yafi ƙarfinta yanzu kam.
Fitowa tayi daga ɗakin tana miƙa tareda yin hamma,ruwa ta ɗiba a bokiti tashiga banɗaki tayi wanka. Lokacin data fito innayi tashiryah cikin kayan islamiyyarsu da jakarta a hannu.
“Ke wato ina jinki kina gulamata ɗazu koh,idan kin dawo daga makarantar ki wankemin kayana,idan basu fitaba kuwa……..hmmmmm bazan ƙarisa ba”
“Bazata wanke ba idan ke kika haifamin ita,ko wankin kayanta banfara bata,amma ke kin fara bata naki dan mugunta”
“To karta wanke,wannan bai dameni ba,tunda na riga na faɗa mata shikenan”
Da sauri innayi tayi magana cikin muryar kuka kafim inna laari tasake cewa wani abun.
“Ahah inna zan wanke mata kayan idan nadawo daga islamiyya,na iya wanki fah”
Cikin takaici babu yadda zatayi ta jijjiga kai.
Riga da wando tasaka irinna pakistan,wanda mlm Ahmadu yasiyo musu a taraba dayaje kasuwanci,hula da saka kanta kawai,babu hijabi tayi hanyar waje.
“Ke ina zakije haka babu hijabi,dama ba islamiyyah zakije ba naga kinyi wanka”
Daneji ta faɗa,tun dazu sai yanzu tayi magana,dan tasan idan tayi ma aikin banza tayi,an doki kashi.
“Wancan Alwasun yace karna ƙarayin kusada makarantarsa satin daya wuce,nice dama nacigaba da zuwa,saboda akwai abinda nakesom ƙarisawa,yamzu kuwa na gama.
Yawo zanje kawai cikin jeji idan wani abune a aika innayi takirani,tasan inda nake.
A bakin ƙofar gidan sukaci laro da gaji,aikuwa caraf tariƙe kunnen Bombee suka shigo gidan tare.
“Dan bantan ubanki mai kikayi wa bello a fuska,dan tsabar abinnaki yawuce gona da iyaka shine kika yimasa yanka da wuƙa a fuska ko,da nayi haƙuri,amma yanzu kam bazaja sabu ba,kotu zan yi kararku a zo a daureki,abun ai yayi yawa shege da hauka,gabaɗaya a kwanaki kaɗan kin dasawa ƴaƴan anguwa tsagwaron tsoronki?”
Tunkuɗa Bombee tayi a ƙasa a gaban Daneji,har sannan bata bar masifa ba ita ƙarfinta.
Zagi takeyi da uwa ta uba,inda tashiga batanan take fitaba,bakinta har kumfah yakeyi dan masifah.
“Wallahi bazan yarda ba,ku jirayi sammaci a gobe,ƙara zan kai gobe,bama a cikin garinnan ba can Sardauna zan kaiku ƙara kuma da kuɗin tara mai yawa.
Har ina da wannan abun,yaro yana can fuska tayi sumtum idon wajen ko gani bayayi tashi,jiki ya dau zafin zazzabin wahala kamar motace ta bugeshi.
Kuma a goben saita fadawa Alƙali mai tayi masa,daga nafara maganar ɗaukar mataki jikinsa zai fara rawa,yarinya ƙarama tasakashi a cikin asirinta,dolen uwarki ma idan kikaji wahala zaki kunceshi da kanki”
A haka tagama faɗan ta son ranta tafita ta bar Daneji ta sharar ƙwallar baƙinciki,hararar Bombee tayi wacce zaune a ƙasa idonta a soye kaman faɗan ba’a kanta akayi shiba.
Ɗakinta tashige tafara ribzar kuka kozata samu ta huce da suyar da zuciyarta take mata.
“Mtswww ji yanda ta batamin kaya kuma tasaka innata kuka,aradu zanyi maganinki ne,bar ganin ki tuleliya bai dameni ba”
A hankali tayi maganar tana tura baki,kafin tajuyah tabar gidan,ta nufi inda tayi niyyar zuwa tun farkon barinta gidan.

Sallama Daneji tayi a gidan gaji da sassafe washagari,dan dama sunyi magana da mlm Ahmadu da daddare akan zataje sasanto gaji kan abinda yafaru.
Wata ƙatuwar tukunyace akan murhu ann ɗumame yara zasuci su tafi makaranta.
Ga gidannan duk tarkacen kayan wanke wanke.
Faɗa gaji take rabawa tsakanin Zulaiha da yayarta akan kunun wai,fa’izah taɗau Zulaiha bayan itace na ashirin ta siyo bana talatin ba.
Sallama Daneji ta cigaba ta kwararawa amma har yanzu gaji bata jitaba,saida wani yaro yakirata tukunna kafin tajuyo takalli danejin.
Ɗan alamar tsorone akan fuskarta amma tayi saurin kawar dashi tareda ƙaƙalo murmushin dole.
“Ahhh Daneji kece sannu daxuwa,ga kujera zoki zauna a zubo miki ɗumame”
“Ahh nagode ma,an tashi lafiyah ya gidan”
“Gida kalau,lafiya naganki da sassafe haka,hala dai mutane gidan kalau”
Abinne yabawa Daneji mamaki har takasa boye mamakin nata akan fuskarta.
“Uhm gaji nace ba,akan zancen kaiwa kararnan nazo,dan Allah a ƙara haƙuri,a sansanta cikin rufin asiri,kaiwa kotun bashida daɗi.
Mlmn ne ya turoni nasake baku haƙuri,sannan za’a biya kuɗin maganin inyaso”.
“Laah karki damu bakomai fah,faɗan yarane dabaka iyarmusu,babu komai yawuce bazai sake faruwaba,ki faɗawa mlm Ahmadu bakomai ya wuce baza’a sake ba”
Kasa jure tantamarta tayi,hakan yasa ta tambayi gaji mai yafaru.
“Amma gaji dan Allah mai ya faru naga kin sanja daga iya jiya,ina fatan dai hakan bayada nasaba da Bombee koh”
“Uhm Daneji kibar zancennan dai kawai,amma tunda kin matsa saƙo daya nakeso ki kaimata,dan Allah ya kice mata ƴaƴana bazasu sake shiga harkarta ba,itama ta taimaka tafita daga rayuwar mu,kowa hadu da daidan sa a yanzu”
Baki sake cikeda mamaki Daneji ta baro gidan gaji,a hanya babu sakar jakin da batayiba akan shin mai Bombee tayiwa gaji da ƴaƴan ta kuwa,kodai zancen mutane dagaskene kai,kai anya kuwa,in akwai wanda yasanta to bayana ne ai,kuma a sanina da ita bata tsafi bare nace shi tayi musu,to mai yake faruwa?
Tana cikin hakanne ta isa gida,zuwa lokacin rana ta fito yara sunata tafiyah makaranta,suma su Bombee sun shirya zasu tafi makaranta.
Daneji bata ‘baata lokaci ba takama hijabin Bombee tareda janta cikin ɗaki.
“Maza maza ina jinki yimin bayani mai kikayiwa gaji naga ta sanja a dare guda?”
Ɗan murmushin dama nasan haka zata faru tayi,kafin ta jijjiga kai.
“Ni babu abinda nayi musu mai zanyi musu”
“Bombee ki faɗamin gaskiya mai kikayiwa gaji take haka,tabbas akwai wani abu,kuma kece kikayi ba kowa ba”
“Inna baki yarda dani ba ne?”
“A da kenan,amma vanda yanzu dakika sauya daga yanda kike”
“Eh to ba wani abu bane babba,kawai dai na ɗan leƙa gidansu ne da daddare nayi musu gagarɗi”
“Gargadin me,ke ƙarama dake zaki iya bawa wannan ƙatuwar matar gargaɗi,ai koni ban isa yimata kashedi ballantana ke,ki faɗamin mai kikayi musu Bombee,ni yanzu kin fara bani tsoro da halayyarki”

…………Daren jiya……….

Karfa labari ya gundureku kunga an tsaya a waje guda ɗaya,komai da sannu ake warwareshi.
Dafatan zakuyimin hakuri dai….😏😊😊😊.

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤19🖤

A zaure mlm ya hadu da Bombee tashigo gidannasu,shikuma zai fita sallahr magriba.
Kallonta yayi na ɗan sakanni kana ya jijjiga kai,inda duka da faɗa suna yin aiki,da sunyiwa Bombee a ƴan watanninan,amma abinnata gaba gaba ma yakeyi kaman ana watsawa wuta fetur.
Shuru tayi taji mai zaice,saidai ga mamakin ta,waucewa yayi batareda yace mata komai ba,sauƙyƙyƙyiyar ajiyar zuciya tasaki,dan dama hakan takeso kada yayi mata maganar.
Kao tsaye ɗakinsi ta wuce tacire kayan jikinta,ta canza wasu daban,sallah tayi kafin tafito wajen cin abinci..
Ƙwanon nata abincin ta ɗauka a gaban Daneji wacce take zuba miya akan tuwon dawar da sukayi.
“Hmmm wai ke bana mijiba,amma saiki saka kai kifice daga gida sai magriba ki dawo,idan kika saka masa ciwon zuciya ya mutu ai saiki nemi wani uban koh?”
“Inna daga yau bazan sake fita da yamman ba,nagama fitan yamman dama yau”
“Ohh duk maganar da akayi baki dainaba saida kikaga dama tukunna,kenan bama bacin raina ne ba yanaki fitar,gama fitar kikayi?”
Shuru tayi bata amsawa innartata maganarta ba,inda wani ne dai da yanzu ya karbi amsa.
Cikin dare can misalin ƙarfe sha ɗayah Bombee ta tashi innayi wacce tayi nisa cikin Bombee.
“Ke dallah tashi ki rufe ƙofah ta ciki zan fita”
“Amma addah in baba yakamaki watarana kina fitar darennan fah,ko shiyasa kikace kin daina fitar yamma kin dawo ta dare?”
“Ina ruwanki toh,sauran naji ko wani zance mai kamada shi,saina babballaki a gidannan”
Gadon Bombee innayi ta kalla,inda ta haɗa tsummokara kaman itace akai a kwance,saboda ko baba zai iya leƙosu cikin dare.
Tashi tayi tabi bayan Bombee ta rufe ƙofar bayan ta fita.
Baƙaƙen kayane a jikin ta riga da wando sai hula,rufe idonta tayi kafin ta buɗe su a duhun gidannasu,ga gari yayi baƙiƙƙirin abinda da damuna.
Dan murmushi tayi ganin idonnata yamayar mata duhun zuwa haske,tarau take gani kaman safiya.
Kama katangar gefen ɗakinsu tayi ta ɗale kaman biri.
Kai tsaye gidan su bello ta nufah,nan kam bata tsaya bata ƙarfinta wajen hawa katanga ba,ta ƙofa tayi shigowarta,kasancewar ba ƙyaurene dasu ba,wani ɗan buhu kawai aka saka a bakin ƙofar gidan.
Tumaki suna kwance a tsaƙar gidan ta tsallekesu ta wuce ɗakin gaji.
Ƙyauren ta tura a hankali,tayi sa’a kuwa babu sakata,dan tsabar rashin tsoro duk barayin da ake fama dasu a garin amma ko sakata basu da ita a jikin gidansu.
Gaji ce a kwance ita malm idi akan gadon,ƙasansu kuma ƴaƴane guda uku anyi musu shimfiɗi suna bacci.
Babu abinda yake tashi a cikin ɗakin sai ƙarar gwartin gaji da kuma idi,ƙaremusu kallo Bombee tayi a duhun ɗakin,tareda yamutsa fuska tana toshe hanci,hamamin damuna da warin fitsari ya haɗu da ƙarnin jikinsu,da kuma warin bakinsu da miyar kuka yabada wani irin mummunan wari mai tada zuciya.
Kai barina gama abinda yakawoni nabar ɗakinan,irin wannan wari haka?”
Tsallaka wa tayi kansu tareda hawa kan ruwan cikin gaji,wacce take ɗaya bangaren akan gadon.
Cikin bacci gaji jin an hau ruwan cikinta tafara cewa.
“Kaifah mlm tsiyata dakai kenan,banda jaraba bakada aiki,yaushe ma kayine dazaka sake dawowa,so kake saika tsamamin jiki nakasa sana’ar gobe koh”
“Ba mlm ɗin bane buɗe i donki kiga waye”
Ihu gaji taso kurmawa lokacin data buɗe ido taga Bombee akan a zaune.
Kafin tace wani abu ta tura mata zanin data ɗauka a tsakar ɗakin.
Wuƙar Daneji ta zaro a kunkuminta ta mannawa gaji ita a wuyanta,wacce dama tun jiyan take kaifata,tayi kaifi sosai sai ƙyalli takeyi.
Wani yawun tashin hankali gaji ta haɗiye muƙutt tana zazzare ido.
“Tashi mijinki yanzu nan,sonake nayi muku kashedi kiji shima ya ji,kuma idan kikayi ihu saina girba miki wukar nan a wuyah,zanga dawane kan zaki dafa abincin siyarwar gobe”
“Dan Allah karki girbamin wannan wuƙar,ki bari tsaya yanxunnan na tasheshi,m…alllammm malam ka tashi”
“Uhn menene kike tashina ne,banace miki idan akayi ruwa bazani masallaci ba,ki bari da safe zanyi sallahr”
“Dallah ba sallah bace,in sallah ce ina ruwana dakai,kabarinmu ɗaya,sanda lawakiri yake tafkarka mai ya dameni,wannan rayuwata ce,katashi ka gani ni lusari kawai”
Idonsa ya buɗe yana rarraba ido,tareda lalumo fitila gefensa ya kunna.
Wani madoki ya ɗakko a gefensa tareda buge Bombee dashi saida ta faɗa ƙasan gadon.
sai a lokacinne gaji ta tashi ta zauna tana maida numfashi,.
“Ahh mlm ashe kai jarumine bansani ba,yaudai kayi abin kai,kullum ina cewa kadaina kawomin madoki ɗaki,ashe dai zayyi amfani”
“Me yarinyar nan take a ɗakinna da wannan dare haka”
“Ina zansani nikuma,yanda ka ganta nima haka na bude ido na ganta a kaina ta saka min wuƙa a wuyah”
“Wuƙa kuma mekika mata haka”
“Ina zan sani,inaga danna yiwa innarta kashedin zamukai ƙarane shiyasa,da Alama kasheni tazoyi”
Suna cikin maganar ne Bombee ta tashi ta tsayah tana jujjuya wuyah inda mlm idi ya ɗan sameta.
Hasketa yayi da fitilar hannunsa,take kuwa idonta yakama hasken fitilar,lokaci ɗaya shima yakoma tamkar fitilar dan haske.
Murmushi Bombee tayi jin yanda suke bada sautin mamakin abinda suka gani,amafani tayi da hakan ta wafce fitilar da take hannun mlm idin.
Maida hasken tayi kansu tana enjoying tsoron dayake kan fuskarsu,wanda yake sauƙar mata da nishadin a cikin ranta.
“Hhhhhhh daga kallon idona harkun razana dayawa haka,ohh dama duk gulmar da kuke yaɗawa akan idonnawa na mayune,bakuma gama saninsa ba.
Wani abun dazai ƙara baku mamakin shine,bakwa tunanin yaakayi na fito daga gidanmu da wannan duhun har nazo nan batareda fitila ba……saboda inagani a duhu tamkar rana.
Mai zai faru idan na kashe fitilar ni ina gani ku kuma bakwa gani,sannan kuma ga wuƙa a hannuna?”
Tana gama fadin hakan kuwa ta kashe fitilar ƙitt,duhu ya gwauraye ɗakin,wani irin ɗurar ruwa cikin gaji yayi,sai karkarwa take tana hada gumi.
“Hmm baban Zulaiha ka ajiye wannan itace takake saitawa,ohhh baka yarda dani ba danace ina kallonka,ko na fara faɗamaka a duk lokacin daka motsa,ko kuma idonka ya ƙifta?”
“Wannan ƴa kekuwa mutum ce?”
“Nima ban tabbatar ba tukunna,saidai ku kunriga kun yanke hukunci ai,cewa ni mayyace ina koh?”
“To ina wani abu kike,meyasa kika tsallake gidaje dayawa kika shigo mana nan,mai muka miki,sannan mai kike nema”
“Hhhhh abu daya kuka min sannan abu biyu nake nema.
Innar Zulaiha taje har gida taciwa innata mutunci,dan kawai narama abinda ɗanka bello yayimin,har tana cewa zatakai kotu.
Abinda nakeso shine ta fasa kaiwa ƙarar nan,sannan kuma babu ita babu gidanmu,idan su bello sukayimin abu kuwa babu mai hanani ramawa.
Wannan shine abinda nake nema,inkuma naga sabanin abinda na nema,zan dawo watarana,inna dawo kuwa duk ɗakinnan sai yankaku kuna bacci baku sani ba,kuma bazan bar shaidar ninayi ba,ko an kamani ma kukam kun tafi ai”
Ta karisa maganar tana dariyah.
“Munji hakan ma bazata faruba aniyarki tabiki,dan Allah kuma ki ƙyaleni nida ƴaƴana,yau na yarda ke wacece kam”
“Yarjejeniya ta ɗauru,ni barina tafi gida kar a gane bana nan”
Tana faɗin hakan ta fita daga ɗakin,hankalin ta kwance aikin ta ya kammala.

An dawo labari………

Tunda wanann abin yafaru babu yaran dayasake tsayawa a hanyar Bombee,komai ta fadawa yaro da sauri yake yi babu bata lokaci. A da itace ke shan azaba a wajen yara,amma yanzu tashi ɗaya ya juyah itake zaluntarsu,idan yayanka ya daketa tasake kamaka ta dakaka,haka za’ai tayi har sai kahana yayannaka da kanka,uwar ɗa ma idan taga abin yaƙi dole ta zubawa sarautar Allah ido.
A makaranta kuwa tana shiga aji zayyi tsit,lokacin da takejin yin magana haka zata saka su suna bata labari,idan bataga dama ba babu wanda ya isa ko motsin kirki yayi a ajin.
Ta daina jarrabawa,karatu kam da su jinga ba’a magana,bata komai saidai tazo ta zuba tantirancinta ta tafi gida.
Bata cikin prifect ɗin makarntar,amma hatta head boy saitaga dama yayi abu.
An sha kaita office ɗin head master za’a koreta. Haka zata ce idan aka koreta saita bunkawa office ɗinnasa wuta da daddare,haka dole suka rabu da ita,a samu a tama gama kowa ya huta.
Shiyasa maganin hakan kowa ya daina shiga harkarta,take cin karenta babu babbaka.
Shirye shiryen fara exam ɗin common akeyi a makarantar su,tun waccan shekarar tayi da ƴan ajinsu bata ciba,hakanne yasa mlm Ahmadu sakata akan tasake jarrabawar,yayi niyyar makarantar kwana zai kaita kowa ya huta,shima ya huta da karbar ƙararta,dan abin ƴar tasa yazama sai zubawa sarautar Allah ido. Suje can suyita mata horo kowa ya huta.

Forseen

……..”kee Bombee yanzu dan zabar baki ɗaukeni da daraja ba,ashe dana sakaki kije ki zana jarrabawar bakiyi ba,kika cemin kuma kinyi?”
“Danajene an gama shiyasa”
“Hmm to shikenan,ki rubuta ki ajiye,aure zan miki kawai na huta dake,tunda kinƙi karatu saiki tafi gidan miji?”
Ƴar dariyar tayi irin bata ɗauki maganar da ɗumi ba kafin tace.
“Aure kuma baba wai niɗin?”.

😁😁ya kukace toh mutanen bombee?😁😁

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤20🖤

“Nayi wa headmaster ɗinku magana,kan cewar zakije kosake rubuta common,tunda wancan din sun bata miki ita saboda tantirancinki,na roƙeshi ya yarda,dan haka ki shiryah kije ki rubuta,idan kinci zan turaki makarantar kwana”
“Baba waini bokonnan dolene ne,duniyar ma fah takusan tashi kowa yasan inda zai shiga”
“Yanzu duk abinda nayi haka kika ce,wai tukunna ma kinji mai nacene.
Idan duniyar ta tashi ai irin bakwa cikin rabo,ki faɗamin wane abin arziƙi kikeyi guda ɗaya da za’a shaideki da ita”
Yamutsa fuska Bombee tayi tareda tashi daga tabarmar mlm Ahmadu.
“To shikenan baba zanje nayi jarrabawar tunda haka kakeso,babu matsala”
“Yawwa uwata kin kyauta,gwanda kiyi karatu hakan zaifi kyau”
Tundaga wannan zancen mlm Ahmadu yayiwa headmaster maganar jarrabawar tata,ranar daza’a yi kuwa ta shiryah tasaka uniforma ɗin da mlm Ahmadu ya ɗinka mata,dan cewa tayi fafur bazata saka tsoho ba wanda aka aro mata a anguwa.
Dole sai sabon akayi mata,idan tasaka saita bawa innayi shi.
Fitowa tayi daga ɗakinnasu ranar jarabawar,tasha sabon uniform da sandal da safa,sai goge kayan take da handkerchiep kaman gaske,kayan kuwa blue Burberry ne yayi mata kyau sosai.
A bakin ƙofar gida ta hadu da mlm Ahmadu yana zaune a majalisar dattijai,nufarsa tayi tana bubbuɗawa,kana ganinta kasan anyi marar ji,ga kyau irinna maciji.
Sallama tayi a wajen tareda tsugunnawa a gavan su.
“Baba zan tafi jarabawar,a bani kuɗin cin abinci,dan sai yamma nadawo”
“To shikenan kokefah uwata,hakan ai yanada kyau sosai,maza ki rubuta mai kyau saboda kiciyo makaranta mai kyau,nasanki da ƙoƙari dama”
Ɗari biyar ya ɗauko a aljihunsa ya damƙawa Bombee,tasa hannu biyu ta karba tareda yin godiya,kafin ta juya ta tafi.
“Ahh ikon Allah anya kuwa itace?”
“Mlm Audu baban su muruje yafaɗa yana jijjiga kai”
“Ita ce mana,girma ne yafara zuwa an fara hankali”
Mlm Ahmadu yafaɗa ɗauke da murmushi akan fuskarsa,saboda jin daɗin yadda Bombee ta nuna hankalin nata a gaban dattijan. Addu’a yayi a ransa akan Allah yasa tacigaba a haka.
A bangaren mutuniyar kuwa tana shan kwanar gidannsu maimakon ta ɗau hanyar gidansu sai tayi hanyar jeji.
A hanya tashiga wani gini ta sanja kaya,daganan kuma tayi cikin jejin kanta tsaye.
Tadaɗe tana tafiyah a cikin jejin kafin ta iso wani gida a dokar jejin.
Hayaƙin dayake tashine mutum zai gane cewar akwai mutum a ciki.
Sallama tayi a bakim ƙofar gidan,muryar wata mata ce ta amsa mata dattijuwa.
“Bombee kece da hantsinnan,shugabannki baya nan yashiga jeji ɗazu”
“Gabas yayi ko yamma?”
“Ahah Bombee bazaki bishi ba ke kaɗai kina mace,kinfi ni sanin bayason kina shiga cikin dajinnan ke kaɗai batareda shi ba”
“Haba Inno har yanzu na,babu indan bansani ba a jejinnan,bariki gani”
Tun kafin wacce aka ƙira da inno tace wani abu Bombee ta nausa cikin jejin da gudu.
Gudu takeyi ta hanyar gabas maso kudu a cikin jejin,daga yanda take gudun tana tsallake itatuwan da suke kan hanya mutum zai tabbatar tasan takan hanyar gaba da baya.
Catt taja ta tsayah tanacikin gudun,kaman wanda wani yabata umarnin hakan.
Shuru tayi na wasu ƴan mintina tareda rufe idonta na ɗan wani lokaci.
Sunkuyawa tayi har saida ta fadi a ƙasa,mashin dayazo ta samanta kuma yah caki a jikin bishiyar gefenta.
Tashi tayi tareda yamutsa fuska tana duba bayan rigarta da lakar wajen ta ‘bata mata.
“Haba shugaba,kasa na bata rigata a cikin wajennan”
Wani mutum ne mai tsantsan jiki,farin bafulatani ne,amma kana ganinsa kasan ƙaƙƙarfane sosai,duk cewa shekaru sun fara nunawa akan fuskarsa.
Dariya yakeyi tareda tafa hannyensa alamar jinjinawa.
“Da kyau ashedai bakya training a banza,menene yasa kika biyoni cikin daji,sannan ya akayi kikasan ina nan”
“Uhm na karbo kuɗin siyan nima kwari da bakata,tsawon lokaci ina tara kudi yau nagama tarawa…..tabb har yanzu bansan inda zan sameka ba,yau fah litinin,nasan dama tanan zaka iyo ai”
“Hmmm da alama ba iya idonki ne yafina sauran mutane fah harda jinki da kuma tunaninki,kinyi ƙoƙari dakika kaucewa harina,ya akayi kika lallami Babanki har ya baki kuɗinnan”
“Uhm bani yayi na siyah kayan kwalliyah,shine na taho nan”
“Meyasa bakya son yin abinda iyayenki suka ce toh,kullum ina faɗamiki kinada lokacin sanja ra’ayi akan bin hanyata,saboda ke macece ba namijiba”
Shuru Bombee tayi baya amsa masa ba,shima dama yasan bazatayi maganar ba,duk sanda yayi mata maganar tasanja ra’ayi.
Abu ɗayane yasa bai koreta ba shine,yasan idan ya korata gida ma bazata haƙura ba,zatabi wata hanyar ne inda babu mai kallonta ballantana ya kulada itah. Shikuma haka kawai yake jinta a ransa kaman ƴar sa wacce shi Allah bai bashi ba.

______****______***_____

Tun ranar da jarabawar su Bombee ta fito yake ta jelen wajen dubawa jarrabawar sa.
A zuwansa na ukune gidan headmastern,ganin abin yazama haka ya faɗamasa gaskiyar abinda yake faruwa.
“Mlm Ahmadu nasan kanason maryam (Bombee)tayi jarrabawa domin tayi karatu,amma fah ita ba karatunne a ranta ba,dan dama haka mukayi ta fama da ita lokacin tana gabanmu,tayin wani lokacin sati ma zatazo makarantar ba,duk lokacin data zo kuwa ba iya ɗalibai ba,mukammu saita caja mana ƙwaƙwalwa.
Badan mutuncinka ba dama bazata gama a makarantar muba korarta zamuyi,to yanzu ma zancen danake maka batayi jarabawar taka roƙa tayi ba.
Ko mai kama da ita bamu gani ba a wajen jarabawar,dan haka saikaje ka tambayeta da kanka.
Amma karka ce nina gaya maka,dan tace sai tayiwa ɗana duka idan na faɗamaka bata zoba,saboda nasan zata aikata yasa nayi shuru. Amma ganin yanayin daka shiga yasa na faɗamaka”
Yana gama faɗawa mlm Ahmadu haka yakoma cikin gida yabarshi a tsaye.
Haushine ya kama mlm Ahmadu jin abin Bombee tayi masa,wato dan iskanci babu wata makaranta da taje,shine harda karbar dari biyar babu ko kunya taje ta kashe.
Hanyar gidannsa ya nufa yana saƙawa yana kuncewa. Dabb dazai shiga gida dabara ta faɗo masa. Murmushi ganin yasamu mafitar tunanin dayake ciki.
Yana shigowa gidan yau ko sallama bayyi ba idonsa ya sauƙa kan Bombee,wacce taketa wurga sakwarar da inna laari tayi musu da ranar.
Daneji da Laari kwanonsu ɗaya tare suke ci,sai innayi kwanonta daban itama Bombee haka,da farko tare sukeci,tashi ɗaya Bombee ta tada tsiyah sai an raba musu kwanon abincin.
Masifah mlm Ahmadu yafara,ta inda yashiga batanan yake fita ba,kana ganinsa kasan ransa ya baci sosai.
“kee Bombee yanzu dan zabar baki ɗaukeni da daraja ba,ashe dana sakaki kije ki zana jarrabawar bakiyi ba,kika cemin kuma kinyi?”

“Aure kuma baba abokaina ma fah ba amusu aure ba?”.
“Su suna da hankali,sun ɗauki iyayensu da mutunci,sannan kuma dasuka sakasu makaranta sunyi,basuyi taurin kai ba kamar ke,dan haka ko kinƙi ko kinso aure zan miki da ɗan gidan Jauro da suke ƙauyen gefenmu,BUBA,dama yace yana sonki nace karatu zakiyi,shima kuma ɗan tijarane kaman ke,saiku haɗu kuyi da rayuwa tare har lokacin nutsuwa yazo muku.
Ke kuma saiki fara shirye shirye,nan da wata ɗaya zansaka bikin,yanxu haka ma wajensa zan nufah”
Yana gama faɗin hakan ya kaɗa babbar rigarsa ya nufi waje.
Daneji takai lomar abinci bakinta,bata ƙarisa taunata ba ta tashi a wajen cin abincin,abin duniyah duk ya isheta.
Zama tayi a bakin gadonta tayi shuru tana kallon tagar ɗakin,rayuwar ta a baya tafara tunawa,yanda ta taso a gidansu cikin kulawa da kuma gata.
Bata taba tunanin zata tsinci kanta a irin wannan rayuwar ba,da farko batayi tunanin yin aureba ba acikin danginsu ba. Haka ta wayi gari tana wajenda babu danginta ko ɗayah,idan wani abu ya sameta,batada kafaɗar dazata jingina tayi kuka,har yau ta gagara sabawa da kaɗaicin datake ciki.
Aka zo zuwa lokacin data samu ciki,farincikine ya kamata,ko ba komai zata bude ido taga jininta a gefenta. A haka tafiya tayi tafiyah lokacin guda ta buɗi ido ta kalli ƴar ta kuma jininta a hannunta,a sannan tayi tunanin wahalar ta yanke zata raini ƴar ta cikin gata da soyayya kaman yanda ta samu,Saidai bata saniba ashe tsugunne bata ƙare ba. Sai ƴar ta tazo duniyah ta wata halitta taban,wanda tun a lokacin ta fara hangon irin ƙalulabalen dazasu fuskanta itada ƴar tata,musamman daya kasance cewar dama bakowane ya yarda da ita ba,kullum cikin zargi take akan ita mayyace.
Cikin dadi da babu daɗi ta raini ƴar tata har zuwa girmanta,a tunanin idan ƴar ta jure wahalar yarinta watarana sai labari.
Tashi ɗaya sai rishe ya juye da mujiya batareda tayi zato ba,sai yazamana abinda take gudun shiya afku.
Wato ƴar tata tayi nasara buɗe shaiɗanin dake cikin jikinta,wanda sukayi iya ƙoƙarinsu wajen binneshi a jikinnata.
Maimakon zaluntarta da yara sukeyi,sai ya zamo yanzu yaro idan bata ga dama ba ko fita daga cikin gidansu bai isa yi ba.
Abinda take gudun a ƙira ƴar ta dashi yanzu ya gauraye bakin mutanen garin.
“MAYYAH HATSABIBIYA”
To bayan wancan kuma ga wata sabuwar itama ta ‘bullo,auren rashin gata mijinnata ke shirin yiwa ƴar tata,duk da tasan laifin na ƴar tata ne,amma kuma zuciya babu ƙashi,takasa daure hakan a cikin ranta.
Yanzu fargabarta ma ɗaya shine,shin Bombee zata yarda ta zauna a gidan auren idan ayi mata,babu abinda ya canza a halittar jikinta na ƴan adam ta take fuskantar haka,inaga kuma ita a wani yankin daban.

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤21🖤

Bombee ce tashigo ɗakin,ta iske innar tata zaune cikin tunani,batasan mai take saƙawa ba,amma tasan bazai rasa nasaba da auren da baba yake shirin yimata ba.
“Inna……inannnaaaa”
Zabura Daneji tayi tareda ɗagowa ta kalli Bombee wacce take tsaye akanta. Alamar itama damuwa ce akan tata fuskar,don duk abinda take bata son kuma abinda zai saka innarta cikin damuwa,musamman idan yazamo wani ne taban yayi sanadiyyar hakan,kowaye shi saitayi maganinsa.
Kasancewarta ba babba ba,amma tana maganin manyan ta hanyar baraxana akan ƴaƴannasu,dan ta kula mutanen agwagine,basu san komai ba sai soyayyar ƴaƴan su.
“Inna ki daina wannan damuwar haka,indai akan wannan aurenne ni zan iya sakawa a fasashi idan bakyaso”
“An zo wajen,ba auren dazai miki ne abin tashin hankali na ba,ke abinda zakiyi a aurenne abin tashin hankalina”
“Kaman yaya inna,taya zanyi shuru amin wai aure,wazai ganni yace nakai aure,ni babu abinda nasani akan wani aure,dan haka kuma bazanyi shi ba”
“Kinga koh,do wannan ne yasakani damuwa ba aurennaki ba,inkinason farincikina kuma ki daina ganin dakuwa ta,to ki dunga jin duk abinda babanki ya umarceki dashi,bana son kinayi masa musu akan abinda yasakaki”
“Hmmm nifah bawai inason yimasa gardama bane,kawai ni banson duk abinda nakeso shikuma yahanani,abinda bana so kuma kullum shi yake sakani,ni bana so ana shiga rayuwata irin haka,abinda ma yafi bani haushi shine,sai munyi magana dashi akan zanyi wani abu ya amince,daga baya kuma sai yaxo yacemin abinnan bai yarda dashi ba.
Taya inna kike tunanin zan yarda kullum yadunga yimin haka kuma……..”
“Saurin buge bakin Bombee Daneji tayi,tareda yin magana cikin bacin rai”
“Wani nikam yaushe zakiyi hankali ne kam,kullum kina girma kina cin ƙasa,wannan harkar maganar tantiran zaki zo kina min anan kina cije min baki,kuma wai duk da mahaifinki kike. Kenan bashida ikon sakaki abu komai koke nufi?.
Aure kuma saura naji kinyi wata tsiyar akai nida kene dan kinga ana ƙyaleki koh? Tashi ki bani waje,aure babu fashi”
Cune baki Bombee tayi tareda barin cikin ɗakin.
Sauke ajiyar zuciya Daneji tayi,tabbas dolene tayiwa tufkar hanci,idan tana son su shiryah da Bombee da kuma ubanta.
“Allah kayi mana maganin matsala”
Tafaɗa cikin kasalalliyar murya.
Shirye shiryen bikin Bombee aka farayi da GOJE ɗan gidan jauro,wanda suke wata Ruga nesa dasu kaɗan.
Goje mutum ne majanuni,saidai shi ƙarin tsiyarsa harda innarsa wacce take ɗaure masa gindi,kullum idan yayi abu sai tace bashi bane,daga kan satar gaji ya fara,har yaxo kan satar shanu suje su sayar.
Yanzu har ta kai yana haɗa baki da ƴan daba ayi babbar sata,wani halinsa ma na takaici shine har fyaɗe yanayiwa ƙananan yara,idan an kai ƙara wajen HARƊO sai ya shafe zancen,saboda maƙudan kuɗin da Goje yake bashi.
Tun Bombee tana yarinya goje ya ganta yace yana sonta,da jauro yazo ya samu mlm Ahmadu da zancen ya fatattakeshi,akan ƴar sa saliha babu abinda zatayi da wani goje. Haka jauro yakoma yafaɗawa ɗansa abinda mlm Ahmadu yace,duk da shikansa da farko dama yasan abin bayyi ba,DAYEE ce matarsa ta dameshi saida yaje,wato mahaifiyar goje.
Yanzu kuma kwatsam jauro yana wajen shanu saiga mlm Ahmadu yazo ya sameshi,nan yake faɗamasa cewar ya amince da auren Bombee da goje,abin yabawa jauro mamaki,saidai yayi shuru bai ce komai ba,a ganinsa koma menene bazai zafafa ba,dan burinsa shine ɗannasa yayi aure kozai shiryu yazama mutum.
Lokacin da aka faɗawa goje baƙaramin farinciki yayi ba,danshi saboda kyanta dakuma idonta yake sonta,dan dama shi mutum ne mai son kayansa yazama daban dana kowa,lokaci guda aka tashi gyaran ƙofar gojen wacce take cikin gidansu,yaransa kullum cikin gyara suke duk na zuwan amaryar tasa nan da sati biyu masu xuwa.
“Goje ana maka sallama a waje”
“Wanene?”
“Bansani ba yace dai jauro yake nema,to da nace masa baya nan saiya ce kazo kai ɗin”
“Buge Indo yayi ƙanwarsa wacce tace anayi masa sallamar kafin ya fita waje”
Hayaniyace ta fara tashi a wajen,kana jiyo muryar goje dakuma wani daga cikin gida.
Inna dayee ce tayafa mayafinta tareda nufar ƙofar gidan.
“Kai goje mai yake faruwane,kaida waye haka,kace musu jauro bayanan yatafi Gassol jiya”
Idonta ne ya sauƙa kan wata yarinya a bayan wata mata,shikuma namijin sunata magana shida goje.
“Zakace haka mana ka bata mana yarinya,gatana ai bazata yi maka ƙarya ba,ka musa idan bakayi mata fyaɗe,aradu daga nan wajen jauro zan wuce nayi ƙararka”
“Ƙara akan me naji ana zancen ƙara kuma,wani akayi maka,kayanka akaci Mlm?”
“Ina kayana ɗanki yaci ai da sauƙi,ƴata ya lalatawa rayuwa,in baki yarda ba kata ki tambayeta,kaita lungu yayi yai mata fyaɗe,sannan kuma ya gargaɗeta akan kada ta faɗa.
Jiya yarinya tafara amai ashe ciki gareta,saida nabata azaba kafin ta faɗamin gaskiya. To bazan yardaba aradu sai anbimin kadu.
Kuma yarinya dole ya aureta tunda ya lalata ta”
Dariyar rainin hankali inna daayi tayi,tareda tafa hannaye.
“Heeee sai yanzu ka sosa inda yake maka ƙaiƙayi mlm,kace kawai ƴar ka tagama yawon dambaɗewa kanason mannawa ɗana ita saboda kaji zayyi aure,to ahirrr dinka munfi ƙarfinka munfi ƙarfin wanda ya tsaya maka ma.
Ba wajen jauro zaka kai ƙaraba ka kai cikin gari ma idan kanaso,haka kawai kowa sai yazo yana laƙawa yaro sharri,dan kawai kunga yayi farinjini yaki auren ƴaƴan ku,duk ina sane da abinda kuke ai,kowa so yake ƴarsa da auri goje saboda ta haifamuku ɗa namiji kuci dukiya,toh aradu baku isa ba.
Kaikuma ka bacemin daga ƙofar gida,ko kuma nacewa arɗon kunzo har gida kunyimana sharri.
“To shikenan tunda haka zakice,kowa a rugar nan yasan tsiyar da ɗanki keyiwa Al’umma,amma saiku danne kurufe,saboda kuna da hanya a wajen Manya,babu komai a akwai Allah,zakuga yanda zaku ƙare dashi.
Lalatacciyar uwa mai boye laifin ɗanta,zaki samu wanda zai yi maganinsa kuma babu yadda zakiyi”
Mahaifiyar yarinyar ce tafaɗawa inna daayi cikin muryar kuka,hannunta rikeda dana yar tata wacce itama take kukan.
Dan takaici shi uban ko magana bayyi ba,sai turasu dayayi suka tafi. A hakan ma daayi bata barsu ba tana iyowa daga bakin ƙofar gidanta.
Sai bayan sun ‘bacene Inna daayi ta juya takalli goje wanda yake yangara hakora yana hura hanci,shi a dole an bata masa rai,amma kana ganin idonsa kasan bashida gaskiya a lamarin.
“Yanzu duk yanda nayi dakai akan kadaina wanann halin yanzu aure zakayi baka daina bako,a hakan kake tunanin zasu baka auren idan suka san haka kake?”
“Na nawa kuma ai sun riga sun sani,a tunaninki haka kawai zasu bani aurenta tana hankali, hmmmm itama tantiriyace lamba ɗaya.
Saikiyi shirin karbar tantiriyar suruka inna”
Zaro ido inna daayi tayi tareda jan ajiyar zuciya.
“Kuma kasan hakane ka nace saiak aureta,yanzu duk ƴaƴan dana kawo maka ka aura kaƙi,dama dan ka auromin irinka ne cikin gidannan,aikuwa zan saita mata zama,dakanta zata bi yanda kowacce mace take a gidan aurenta”
“Hhhh a tunaninki zan kawo matata ki dunga yimata izaya ina kallo,ba iya son Bombee ne yasakani aure nan ba,saboda naga yanda zatayi dake a cikin gidannan ne,baki san halinta ba sunanta kikeji,amma kije ki buncika ki gano da kanki”
‘Dama hakane ?’ ta faɗa a ranta.

_____*_____*_____*___

“Ungo karbi kisha yanzu nan”
“Wannan ɗin menene inno?”
Bombee tafaɗa tana yamutsa fuska
“Kinci gidanku banace karki tambaya ba,ki shanyeshi yanzu nan,wacce zatayi aure ai saida gyara,kuma gobe ma ki tabbatar kin dawo,sannan dama na riga na hanaki bin Shugabannki jeki,karki ƙara yin tsalle tsallen nan bana mata bane”
Duk abinda inno tak faɗa Bombee tana jinta,ba abinda takeyi sai dariyah ƙasa,ita mantawa ma take da zancen sai anyi maganar tukunna.
Haka gidama tashi ga tafita,sunata aikin shirye shiryen biki. Jiya fitowar ta takalli ana shigowa dakayan gado cikin gidan,babu abinda take ayyanawa a ranta sai irin kuɗin dazasuyi idan ta siyarsu.
“Lahh inno gwanda dakika tunamin,dama fah inason naje nayi ɗan bincike akan shi wannan gojen”
“Ahah karki je dakanku,ki bari Mlm yasaka ayimiki,wai sau nawa zan faɗamiki ki daina hakane kam,tashi ki tafi gida ma ya isa haka,sai gobe kuma”
Tashi Bombee tayi batareda tayi musu ba takaɗe rigarta,wajen da yayi ƙasa.
Hanyar ƙofar gidan tayi batace komaiba ta kamo hanyar barin jejin.
Jijjiga kai inno tayi tareda yin ɗan guntun murmushi,duk cewa batayi mata musu,amma hakan bashi ke sakawa tayi abinda tasakata ba. Tasan ko tsafi take da zaba Bombee bazata haƙuraba sai tayi binciken dakanta.
Haka take wata irin murɗaɗɗiyar yarinya ce itah,da kaɗan kaɗan tsoro sai barin cikin idanuwanta yakeyi,a hankali take sauyawa zuwa wata macen taban.
Da farko abin kaman ƙuruciya,amma kuma tana girma tana ƙara fitar da halayyarta na tsayawa akan ra’ayinta.
Duk da kasancewarta ba mai sabo da mutane ba,amma haka kawai Allah ya haɗata da jinin Maharbi Uwaisu,shida matarsa inno,basuda ɗa ko ƴa shiyasa sukejin Bombee har cikin ransu,duk su kansu sunsan batada daɗin sha’ani.

Hasashen inno bai tashi a banza ba,maimakon Bombee takama hanyar tafiyah gidansu,saita kama hanyar da zata kaita rugar su goje a ƙafa.
Tana tafiyah tana ƴar waƙa,irin wanda takeji a gidan rediyo,harta isa ga rugar.
Lokacin anyi magriba duhu ya kawo kai,wani mai gasa masara ta haɗu dashi a bakin hanyar yana da aikinsa.
Tsugunnawa tayi kaman abin arziƙi tace.
“Uh dan Allah bawan allah idan bazaka damuba tambaya nake”
“Allah yasa na sani toh”
“Inaso ne ka faɗamin duk abinda kasani gameda Goje dake rugar nan,kama daga mugayen halayensa harma da abinda yake aikatawa”
Kallon bakida hankali yayi mata,tareda yin dariyar rainin hankali.
“Mai yasa kake dariyah,bazaka faɗamin ba ko kuma kana tsoro”
“Tsoro? wazanji tsoro,tambaya ma kike akan meyasa bazan faɗamiki,dallah tashi ki bani waje tunda bakida hankali”
Kama bakin tiren gashin masarar tayi kaman mai shirin watsa masa garwashin a jikinsa.
“Ke me kike haka?”
Rashin hankalin nakeso na nuna maka banida shi kaman yanda kake tsammani,shin zaka faɗamin ko kuma sai na gasaka kaima da abinnan.
Zaro ido yayi tareda cewa.
“Keee ki bari aradu ina tsoron faɗamiki,zance yadawo ace a wajena kikaji”
“Tom tunda tsoro kake sai zabi na biyu,kwatanta min gidansu”
Kwatancen yafarayi mata batareda musu ba har ya gama.
Tashi tayi zata tafi,maganar sa ce ta ƙatseta ta tsaya catt.
“Mm….me zakiyi a gidansu,yarinya bazai ƙyaleki bafah idan wani abu kike nufinsa dashi,sannan kuma innarsa ta ɗauremasa gindi,ko ƙara kika kai baza’a saureriki ba”
“Wow kaga ka bani amsoshin tambayoyina dayawa,karka damu ba wani abu zanyi masa ba,kawai zanje gun innarsa ne na tambayi waye shi,dan nasan tafi saninsa fiyeda kowa”

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤22🖤

Kwatancen da mai masarar ya gwada mata tabi tiryan tiryan har ta samu kanta a ƙofar gidan su goje.
Tsayawa tayi a bakin dangar gidan ta riƙe kunkumi tana kallon gidan.
“Hmm wai nan gidan baba yakeson nazo na zauna na ƙare rayuwata,nida nakeda burin fita daga nahiyar nan,shine zanzo wannan wajen na zauna,lallai baba yanzu na tabbatar ya rainamin hankali ba kaɗan ba,shi bayyi zaman irin gunnan ba saini Bombee?”
Maganar ce daga bazata kaita ba,dan haka kawai tasaka kai cikin gidansu goje babu ko sallama.
Inna Daayi ce a zaune akan tabarmar datayi sallah tana cin tuwon da indo ƙanwar goje ta kawo mata gabanta.
Ɗaga kai tayi cikin bazata ta kalli yarinya a kanta,yatsine fuska tayi kafin ta ɗora cewa.
“Ke lafiya yarinya kika shigo ko sallama babu,kufah yaran zamaninnan haka kuke,gabaɗa kaman an saka ku a kwano an raba,ba’a jin daɗinku sam.
Idan cukui kikazo siya babu saina kaɗa gobe in allah ya kaimu”
Duk surutunna da take Bombee batace kanjil ba,hannunta riƙe a kunkuminta tana nazartarta.
Saida ta gama kafin ta zauna a kujera ƴar tsugunno dake tsakar gidan.
“Uhhh in kingama surutun inna dama wajenki nazo,tambayarki zanyi,kina amsamin zan tafi…..amma kafin sannann dan Allah zanyi sallah,kuma yunwa nakeji,ƙanshin miyarki yasa cikina yayi kuka yana neman abinda zai haɗiya.”
Kamar wanda akayiwa asirin wucin gadi,haka inna daayi tabawa Bombee buta tayi alwala,ta ɗau hijabin inna daayi tayi sallah,sannan indo ta zubo mata tuwon taci tayi nakk.
“Yawwa Alhamdulillah ciki ya ɗauka,ki faɗa yar ki ta iya abinci,da alama baza’aji kunya ba”
“Ke yarinya wai daga ina kikene,hala ba batan hanya kikayi ba?”
“Babu wani batan hanya,ina kece Daayi matar jauro uwar Goje”
Ɗaga kai inna daayi tayi,duk da taji haushin rashin kunyar Bombee na ƙiran sunna su ba sakayawa.
“Na shigo garinnnan ne saboda naji waye goje,mai yake taƙama dashi da har yake shirin shiga min hanci da ƙudundune,to wlh kijawa ɗanki kunne hawainiyarsa takiyayi ramata,tun muna shaida juna nida shi,idan ba haka ba kuwa dagake harshi zakuji babu daɗi,dan kun tabo marar daɗin.
Naji ance taƙadari ne,to duk tsiyarsa na fishi aradu,karya ganshi zabgege ya gannni kaman itace karmami yanemi ya rainani,shaidar ɗan maciji da kyansa tamm”
Duk magana tanayi ne idonta ɗaya a kanne,yatsa ɗaya kuma tana nuna idon inna daayi bako tsoro.
Saida tagama tass kafin tamiƙe tayi hanyar waje tana faɗin.
“To nina tafi badan dare yayimin ba saidan kar inna ta nemeni,hhhhhhhh wai amaryar daza’a saka lalle wani satin tana yawo”
Ita kanta saida abin yabata dariya,ƙarin mamakin ta ma wai ta yarda ayi auren.
“Yarinya wai wacece ke,sannan menene ma’anar wannan gargaɗin dakikayi,kina cikin wadda goje yayi wa fyaɗe ne? Inma kina ciki ina faɗamiki tun wuri kisan me kike,dan bazaki iya ja dashi ba,kuma shi aure ma zayyi wani satin.
Inso kike ya aureki ma tun dare bai miki ba kima wani hannun”
“Fyaɗe???? Tabbb ya isa ma dan ubansa,yama fara mana…….so kike kisan wacece ni? Sunana Bombee ƴar gidan mlm Ahmadu kuma wacce Goje zai aura nan da wani satin.
Nasan dole dama kunyi mamakin meyasa babana ya yarda da auren koh,bayan yasan tantirancin goje,. Saboda kar tasan kar ce,niba banida daɗi ra’ayina nake bi naci karena babu babbaka,tunda ɗan ki kuma yaɗau kasadar son shiga rayuwata bismillah.
Ni nayi nan sai mun haɗu wani satin kuma Su…..ruuuukkaata DAAYI hhhhhhhhh.
Wai ikon Allah Bombee da suruka kaman mafarki”
Ita kaɗai bayan tagama tujarar tafara tambayar kanta na shaƙiyanci tana bada amsa.
Buta ce a gefen ƙofar gidan,da alama ta jauro ce an cikata da ruwa.
Kallon butar tayi tareda yin bolll da itah ta wajen saitin inda daayi take zaune.
Da sauri kuwa ta matsa ruwan ta zube akan tabarmar,bayan butar ta fashe.
“Karbi wannan kafin nazo ki dunga tunawa karki barshi ya goge innar mijina”
Tana gama faɗin haka tajuya ta bar gidan.
A hanyar fita sukayi kicibis da jauro zai shiga gidan.
Ko kallo na biyu bata sake masa tunda tayimasa na biyu,dan dama ba wajensa taxo ba.
Kai tsaye ta tasamma dajin dayake gabanta babu koh ɗar bare alamar fargaba.
Bujen wandonta ta naɗe zuwa ƙwanji kafin ta nausa da gudu cikin jekin kaman lokacin rana,abin ya haɗu mata biyu,ga sanin jejin ga kuma ganin idonta daya ƙaramata taimakon gani a cikin duhun daren.

“Ahh ke Daayi inata magana nadawo kinyi shuru,sannan wannan yarinya ƴar inace marar ɗa’a,munyi karo da ita amma ko sannu batayiminba ta fita.
Ke indo miƙomin buta nan na wanke hannu”
“Ga nan butar a kusana”
Daayi tafaɗa tana haska masa butarsa wacce Bombee tafasa,duk ruwan yajiƙa tabarmar daayin”
“Ahah wannan kumafah,ko indoce ta jefar ta”
“Hmm surukarka ce ta ta cankofa tun daga hnayar mashiga,itace wacce kake cewa kun haɗu bata kulaka ba”
Nan take Inna daayi ta kwashe abinda Bombee tayimata ta faɗawa jauro.
Jijjiga kai kawai yayi,saidaga baya yayi magana bayan yagama gajeren tunani.
“Hoɗaan wato goje yagamu da gamonsa kenan!”
“Oh hakama zakace jauro,to aradu kuwa tunda tazo tayimin wannan ɗanyen aikin saita zama abin tausayi a cikin gidannan,da nayi niyyar nuna mata soyayya saboda tana matar goje,amma yanzu na fasa,saina koyamata hankali”
“Ahh to ga fili nan kuma gamai dokinnan saura sukuwa muke jira mu kallah,ni bari kiga nayi masallaci kar ayi sallah bandani,da ina faɗamiki ki daina yiwa yarannan riƙon sakainar kashi amma ƙinƙi ji,yanzu gashinan goje ya zame mana Ciwon ido sai haƙuri,sai yanzu da muke son maganin abin kuma Alƙalami ya riga ya bushe.
Sai muzuba sarautar Allah ido kawai mu basu waje muga wacce wainar za’a toya,danni kam dama bani cikin sha’anin zaman sa da wannan yarinya,kece sai yau kikaji labarin ta,ni dama naji labarinta tun ranar da mlm Ahmadu yace wai ya amince ƴarsa ta auri goje,na tabbatar akwai lauje cikin naɗi,dan ruwa baya tsami banza”
“Toh Allah ya kyauta wai rago yasha ƙida”

Cikin sanɗa ta shigo gidan siƙaff siƙaf,har takai bakin ɗakinsu zata shiga taji murya a bayanta.
“Daga ina kike,bana hanaki fitaba tun wancan satin,wai kekam wacce irin yarinyah ce ne,daba dama a faɗamiki abu kiji,kullum idan bakiyi wata tsiyar ba bakyajin daɗine”
Sauke ajiyar zuciya tayi irin ta faru ta ƙare dinnan tunda an kamata,jefar da takalmanta tayi wanda take rikeda su a hannunta.
“Yi haƙuri bazan sake fitaba daga yau shikenan,”
“Baki amsa min tambaya ta ba,daga ina kike a wannan tsohom daren,tukunna ma kinyi sallahr magriba da isha,bata zancen la’asar da azahar ma akeba,wanda bana tunanin kinyi su”
“Wai inna nace miki ina sallah,dukkansu nayi su,isha da magriba ma sukam ƙasaru nayi…..”
Tana faɗan hakan tayi saurin rufe bakinta tana zaro ido,ganin su’butar bakin da tayi.
“Ƙasaru wanne gari kikaje da ƙasaru takama ki,kiyimin bayani naji”
“Uh….uhm rugar su goje naje,acan nayi sallah harma naci abinci”
“Rugar su goje,ni ɗiyar nan mai kikaje yi a rugar su goje da wannan daren,kai kai wai nikam mai kikeso ki jawomin ne a wannan rayuwar Bombee,zo nan biyoni yanzu nan,maganar bata waje bace,saikin faɗamin wane halin kikaje kika nuna a gidan surukan ki uhmmm”
Daneji taƙarisa maganar tana tafa hannaye cikin kiɗima da abinda taji Bombee ta faɗa.
“Babu fah abinda nayi,kawai zuwa nayi naji waye shi a wajen innarsa”
“Kuma yanzu dan zakiji waye shi ki rasa mai faɗamiki waye shi sai innarsa Bombee,wannan tsaurin ido damai yayi kama haka?”
Fincikar Bombee Daneji tayi cikin bacin rai suka shiga ɗakinta,jangwabata tayi akan gado da ƙarfi kafin ta zauna a bakin kujera suna kallon juna.
“Gobe za’a fara sha’anin bikinki,kuma daga goben gidannan zai fara samun mutane,banida lokacin yimiki wata muhimmiyar magana,shiyasa dama na yanke yau zan miki. Amma saboda rashin hankali irinnaki tun safe bakya gidannan sai yanzu kika dawo,abinda kikeyi ko na miji bayayin irinsa,ki fice sanda kikaga dama,ki dawo sanda kika dama saikace shikan wawa.
To ki buɗe kunnenki kijini da kyau,Aure ba abin wasa bane,karki ga yanzu kinada ƴan cinki,idan akayi aure komai naki yakoma ƙarƙashin mijinki.
Yi nayi bari nabari,banda musu kuma ƙorafi ko kuma ƙiwuyah. Sannan kiyiwa uwar mijinki biyayya tamkar ita tahaifeki,ki rungumi ƴan uwan mijinki ki nuna musu soyayya,banda shashanci Bombee ina faɗa miki……”
“Inna dare yayi yakamata ki kwanta,ba’ayi aurenba tukunna kike wanann zancen,ina auren kawai akace nayi to zanyi,amma gaskiya sauran abubuwa kuma banyi alƙawarin zanyi yadda akeso ba,yanda nakeso zanyi su.
So ake yayimin abu na ƙyaleshi,shima fah ba mutuncin ne dashi ba,sai a dameni ƙadai,komai ni”
Cikin bacin rai tagama maganar,Daneji tana ganin hakan tace.
“Tashi ki tafi mukwan lafiyah,Allah ya shiryeki”
“Ameen”
Babu buƙatar sake magana bayan abinda ta faɗamata,dan tasan ko tsafi take da baƙar jaba bazatayin ba tunda tace haka.
Abinda aka sakawa lokaci bashida wuyar zuwa,Auren Bombee ya kam kama ka’in da na’in da angonta goje.
Duk da rashin abin hannu da kuma rashin ƴan uwa a kusa na Daneji,hakan bai hanata taka rawar gani wajen gyara ƴar tata ba.
Tun ana sauran ƙwana uku da aure aka farayi mata wankan madarar shanu,sannan kuma takoma ruwan shanta.
Bata zuwa ko ina koyaushe tana ɗaki,abinka da fata dama haka take. Nan da nan tayi wani haske fatarta tana sul’bi da sheƙi.
Ranar Asabar aka ɗaura auren Bombee da goje a masallacin ƙofar gidansu,kan sadaki Dubu talatin lakaɗan ba Ajalan ba.
Babu laifi kuwa ya tara ɗumbin mutane masu shaiɗa daurin auren,kasancewar shima mlm Ahmadu ba baya ba wajen mutane.

To an ɗaura Auren Bombee da goje,sai muce Allah ya basu zaman lafiya…..😀😀😀….

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤23🖤

Ana gama ɗaura auren yaji wani nauyi ya sauƙa a ransa,duk da cewar ba haka yaso auren yar tasa yazo ba,amma kuma yaji daɗi ganin ya aurar da ita kafin tagama fin ƙarfinsa.
Yaso tayi karatu tazama wani abu a wannan rayuwa saboda takare kanta,amma kuma kana naka Allah yana nasa,inaga wannan shine tata kaddarar ba wacce yake zata mata ba,fatansa shine allah yabasu zaman lafiya da mijinnata.
A ranar kuma Daneji ta haɗu abun bazata,wanda bazata ta’ba mantawa ba.
Shatu ce tayi mata magana daga ɗaki kan tafito tayi baƙi.
Yayunta ne biyu maza da kuma dadarta wacce take auren ɗan Yayan baffansu da ƴaƴanta itama masu aure guda biyu.
Kasa gasgata ta tayi,dan har ta fito ta tsayah a gabansu gani take kaman idonta ƙarya yake faɗamata gameda bayyanar tasu.
Saida ta tabbatar da gaskene kafin ta fashe dakuka ta faɗawa tayi kam Addar tata,wacce dama kusan ita tarene ta ba innarta ba.
Fillanci aka juyeyi na ɗan wasu lokuta,kafin tajasu ɗakinnata tafara basu labarin abinda yafaru,yawancin labarin ma bata basu ainihin yanda yakeba,ta boyemusu abubuwa da dama.
“Ahh Danen Baffah kene da auren ƴa ohh,aida mai saƙo ya iskemu wai inji mlm Ahmadu cewar za’ayi auren Bombee munyi mamaki sosai”
Kallonsu Daneji tayi da alamar tambaya,mlm Ahmadu kuma? Dama yasan inda suke?”
“Kinga bai san inda muke ba,inaga yatura masu saƙone da dama wani ya iskemu ya fadamana. Da Allah yasama zamu iso akan lokaci kinga ashe damu za’ayi”
“Koma ta ina yasameku gaskiya naji dadin ganinku,ina innatah tana lafiyah”
Shuru HADIZA tayi Addar daneji jin tambayar da danejin tayi mata.
“Kiyi haƙuri Daneji amma inna kam tayi shekara kusan goma da rasuwa,saidai muyi mata Addu’a Allah ya jiƙanta”
Shuru Daneji tayi tareda sunkuyar dakai,sai can kuma tashare ƙwallar idonta tareda ƙaƙaro murmushi,shikenan babu komai,amma da ansamu wani ai yazo ya faɗamin lokacin?”
“Kiyi haƙuri,amma baffah ne yace kar a faɗamiki lokacin,kema ga ga halin kaɗaicin dakike ciki,kiyi haƙuri kiyi mata Addu’a kawai,dan shi take buƙata a yanzu.
Ina Amaryar ne tunda muka shigo banganta ba”
“Gaban Daneji ne yafaɗi,ita kwata kwata ta manta ma da bikin ƴar akeyi,tsabar ganin ƴan uwanta ya kaɗe mata hankali”
Toh fah ina Amaryah manya,bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida…….!!!
Tashi Daneji tayi tanufi ɗakin su Bombee domin ƙiranta.
A kwance take tana taunar cingam irin na aurenta wanda ta zaro kwali guda ba’asani ba.
Babu kowa a ɗakin sai innayi wacce take taya shatu gyarawa Bombee kayanta.
“Addah Bombee a saka wannan ko kin ban shi”
“Ahah ban baki ba,wai wayace ma ki tattaramin kayana ne dukka,cewa aka ce miki bazan dawo na tafi kenan saikace ɗaukar rai”
“Inji waye yace zaki dawo toh,koni kinga na koma gidanmu,canne gidanki daga yanxu,nasakeji kinyi zancen dawo zaki gamu dani,kenan da shekara ma idan na ganki a gidannan zakiga yanda zanyi dake”
Daneji ta amshe maganr wacce shigowarta kenan tazo ƙiranta,shatu tana ta aikin gyaramata kayan dazata tafi dashi batayi magana ba,dan tasan halin Bombee ba ragamata zatayi ba,wanda bai bar iyayensa ba wazai bari kuma.
“Sannu Innar muruje da ƙoƙari,kina fama da ita koh?”
“Uhm lahh ba komai itada ƴar uwartata ne suke gardamar bankwana,zatazo kuma tayi kewarta nan gaba”
“Hmm batada hankali ai,tana girma tana cin ƙasa,wai wannan akayi aure….allah dai ya kyauta kawai,tashi kixo wata innar taki tana ƙiranki,addah ta Hadiza sunzo dasu kawunan ki,harda ƴaƴan ta,addodinki”
“Hmmm yanzun mai yakawosu kuma,duk tsawon lokaci dakikayi kina tunaninsu da kewarsu basuzo ba sai yanzu,mai yahaɗani dasu mai zasumin?”
Bombee tafaɗa tana yatsina fuska tareda tauna cingam ɗin bakinta yabada ƙarar ƙasss”
Duk Daneji takaiwa Bombee a bombom dinta,dan dama a kwance take tayi bake bake akan gadonnata,wanda zata barshi yau.
Saurin tashi tayi tana zumbura baki,tareda gallawa innayi harara wacce suka haɗa ido,da sauri kuwa ta ɗauke kanta,dan tasan tsaff zatayi mata dukan bankwana kafin ta tafi.
“Dallah wuce muje ki gaishesu,ƴan uwannawa kikeyiwa wannan maganar,sauran kuma idan kinje ki nuna musu ban isa dake ba”
Boll tayi da kayan dasu innayi suka gyara kafin tafita daga ɗakin,itama Daneji tabi bayansu yana jijjiga kai na takaici.
A bakin ƙofar ɗakin ta tsayah,saida ta ƙaremusu kallo kafin ta taka ƙafa zuwa shiga ɗakin.
Wata mai kamada innarta fitik ce,saidai tafi innartata ɗan duhu da kuma manyanta,sai kuma wasu mata guda biyu,wanda a kallah ƙaramar ma zata bata shekara biyu a haife. Dukkan su fararrne ƙall jinin fulani gaba da baya.
Murmushi babbar tayiwa Bombee,da alama tanada sanyin rai ba kamar ƙaramar ba. Suna haɗa ido tasake murtuƙe fuska,ita a dole innarta ta daketa akansu.
A kan kujerar ɗakin ta zauna tana binsu da ido ɗaya bayan ɗaya,sai can kaman bazatayi magana ba tace “ina Wuni” a cikin ƙaramar murya.
Yanda ta kalli Addah Hadiza taƙasan idone kawai zai nuna da ita take,shima dan sun haɗa ido da Daneji ne,wacce take bakin ƙofa ta kafeta da ido.
“Lafiya”
Ta faɗa cikeda mamakin Bombee,sukuwa sauran ko kallonsu bata sakeyi ba.
“Su baki gansu bane ko bazaki gaishesu ba?”
“Inna sufa yarane ba iyayena ba,kuma…..kinsan rabona da gaisuwa na daɗe,ni na manta yanda akeyi ma,tunda sun ganni ai shikenan,basu zo lokacin ina kan gaisuwata ba da sun shata har sun ƙoshi”
“Ohh wato kinsan da kina gaisuwar kenan?”
“Nasani mana,lokacin tun shaiɗan yana dan ƙyauye bansan mai nake ba lokacin,amma yanzu kam hmmmm…….”
Dukkan su zuba mata ido sukayi kaman sun samu TV,yanda Daneji ta basu labarinta ma har yafi haka.
“Amma Ƴar uwa Bombee kina gani sosai kuwa da yanayin idonki?”
Babbar ƴar Hadiza mai Sunan Bombee wato Maryam ta tambayeta.
“Lalumen katanga kikaga inayi dana shigo?”
“Kinga tashi kije zaure wajen kawunan naki suma ki gaishesu,Dan Allah kuma kiyi aikin hankali,banda shiririta”
“Tom”
Tana faɗin haka zuruff tafice,dama kaman akan ƙaya haka take jinta,gabaɗaya an cika gidan da hayaniya,idan akwai abinda ta tsana bai wuce tarin mutane ba,shiyasa tafi kare rayuwarta a jeji gidan Maharbi Uwaisu. Musamman idan dare yayi halittu suna fitowa kala kala,wasu har wajenta suke zuwan sunyi zaton bata kallomsu kaman sauran mutane,yanayin yana yimata daɗi sosai.
Tun yamma gidan yafara karbar baƙuntar mutane ƴan ɗaukar amarya daga rugar su goje,dan dama su sannan ne bikin zai fara idan dare yayi.
Shirye shiriye aka fara na kaiwa amaryah da misalin ƙarfe 11:30 na dare,hakanma dan mlm Ahmadu ya nuna cewar bayason ɗaukar darenne tukunna.
Ɗakin mlm Ahmadu dake zauren Daneji ta rakata,babu kowa a ɗakin daga mlm Ahmadu sai inna laari,saikuma Daneji ta itama ta zauna a ɗaya gefen mlm Ahmadun.
Ita kuma uwar gayyar tana tsugunne a gabansu an rufa mata farin mayani akanta.
“Toh bismillahi da Sunan Allah……Maryama kamar yaune aka haifeki na riƙeki akan tafukan hannuna ina murna da zuwanki duniyah,bayan tsawon lokaci dana fidda rai da rabon ganin jinina a duniyah. Yau kuma gashi na ɗaura miki aure zaki tafi kema gidan mijinki inda zakiyi taki rayuwar.
Nasihar dazanmiki shine,kizama mai haƙuri da kuma biyyah sannan da juriyah,sauran halaye kuma idan ke mai yawo ce nasan kingama ɗaukar su daga wajen innarki a yau da kullum.
Duk da bakan abokiyar zama za’a kaiki ba,amma ina shawartarki da ki kwantar da hankalin ki idan wata taxo ta sameki cikin gidanki,kiyi koyi dasu innarki anan gida,yanda suka haɗe kai suke zaune ƙalau.
In bada ƙwaƙwƙwaran dalili ba banyadda naga ƙafarki cikin gidannan ba dasunan kinkawo kara ko kuma kinyi rigima,sannan karki yarda yakawomin kararki nan. Idan hakan yafaru bazan hanaki zaman gidannan ba a matsayin ki na mace,amma zan fita lamarinki bani bake,dan haka kizauna lafiya da mijinki da kuma ƴan uwansa.
Wannan shine iya abinda zan faɗamiki a matsayina na mahaifi”
Bayan yagama yimata jawabin,itama inna laari tayi mata nata na jan hankali,inda ita harta kara dsyimata bayanin haƙƙin miji dake kanta..
Duk abinda suke faɗa Bombee tana zaune gungurun,bata motsa ba sannan kuma batace uffan ba har suka gama.
Inna laari kam itada Daneji harda ƴar ƙwallarsu,da alama sun tuna sanda suka bar nasu gidan,amma ita wannan mai tafiya yanzu ma,tana zaune kaman dutsi,duk maganar da akayi mata babu wacce tashigeta kaman an tsikari kakkausa.
Inna laari ta tashi ta kama hannunta suka fita,dan dama itace mai rakata ɗakin itada Inna Hadiza.
Babu laifi kofar tata an gyara to sosai,dan ginin bulon siminti ma yayi mata,gashi an ja ƙofar an kewayeta daga cikin gidan.
Kayama mlm Ahmadu yayi mata masu kyau an saka mata,kowa sai yaba kyan ƙofar yake da yanda tasha kaya.
Ɗakine guda ɗaya sai kicin da gefe da kuma banɗaki,saidai ɗakin babbane sosai,dan yacinye dukka kayan harda sauran fili.
A kan kadonnata aka zaunar da itah,wannan aikin inna laari ne,ita ta matsa dole saida aka yimata jere kafin akaita,kuma hakan yakawomsu sauƙi,dan babu wani sake yin jere washegari.
“Toh Bombee ga ɗakinki mun kawoki,mu yanxu zamu tafi,dan mlm yace karmu makwana komin dare mu koma gida. Dan Allah kiyi amfani da abinda aka faɗamiki jiya kinji?”
Shuru Bombee tayi bata kulata ba,saima wangale mayafin da aka nannaɗeta dashi take ƙoƙarin yi.
Da Sakeena suka haɗa ido ƴar gidan Shatu wacce take kusan sa’ar Bombee ce,da kaɗan Bombee tafita dama. Ita kadaice wani lokacin suke maganar arziƙi da Bombee,shima dan tanada shuru shuru ne bata biyeta,hakan ma ba koyaushe take kulata ba,saidai idan tayi wani abun ta tambayeta itakuma da bata amsa.
“Hmm kinajin tanayi miki magana kikayi banza da ita Bombee?”
“Sau nawa zan faɗamiki cewar matar nan batayimin ba,haka nakejin bana sonta a raina yanxu”
“Dama wakikeso tunda kika zama haka bada kanki,ni barikiga na tafi,saina zo miki”
“Dama yanzu zan koreki in baki tafi bama,kinsan ba abinda na tsana kaman wannan wa’azin,inkikace zaki dameni to zan daina kulaki”
“Hmm nina tafi kafin ki huce akaina saikin ganni”
“Hhhhhh wani saikin ganni,saikun ganni dai,nufinku shikenan daga nan na tsayah daga farawa,mai ma nayi toh”
“Bombeeeee!!!! Kinji fah mai Babanku yace idan kikayi wani abun?”
“Ina ubana kikace ba ubanki ba uwar iyayi”
Gum sakeena tayi da bakinta tareda barin ɗakin tabi yan rakiyar amaryah.
Tana ganin sun tafi babu kowa tasake ajiyar zuciya tareda kwantawa akan gadon.
Baje ƙafafunta tayi,ita kaɗai ta saka dariyah kaman mahaukaciyah sabon kamu.
A haka bata saniba har bacci yayi awon gaba da ita…..

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤24🖤

Bugun ƙofar da ake ne yafarkar da ita daga baccin gajiyar daya ɗauketa.
A hankali take buɗe idonta har ta waresu akan rufin ɗakin,wanda aka haɗa da zare da kuma jarida.
Tashi tayi ta zauna a tsakiyar gafon tareda yin wata kyakykyawar hamma,kaman wanda ta shekara bataci komai ba.
Kallon gabas da yamma kudu da arewa tayiwa ɗakin,ta tabbatar dai ita kadaice ta kwana a ɗakin kenan,angonnata bai shigoba da alama,to mai yahanashi zuwa ta faɗa a ranta,ganin hakan zai bata mata lokacin yasa ta bar ma zancen.
Sake bugun ƙofar akayi a karo na ba adadi,sai sannan ma ta tuna da abinda ya tasheta.
Cikin kasalalliyar tafiyah ta nufi ƙofar tareda buɗewa.
Da indo suka haɗa ido tana rike da kwano a hannunta,saida tayi mata kallon sheƙeƙe kaman bata girmeta ba kafin ta ce.
“Menene kike ta bugun ƙofah kaman naci muku bashi,dama ake yiwa baƙo ne?”
Kallon ta indo tayi na ƴan sakanni kafin ta ajiyemata kwanon ta tafi,danta kula neman magana ne a gun amaryar yayannata,dan tun ranar datayi tujarar nan tasan an kawo musu wata alaƙaƙai ɗin,gwanda ma tayi aurenta ta tafi ta huta,banda mutuwar da mijinta yayi na farko ma da bazata ganta ba bare tayi mata.
Sai bayan taga ƙulewar indo tukunna ta tsugunna ta ɗauki kwanon tareda buɗewa.
Doyace da ƙwai aka soyata sai ƙyalli take,haɗiyar yawu Bombee tayi kafin tace.
“Hhhhh nasan ba wannan abincin suke ci ba ni akayiwa saboda ina baƙuwa,hmmm kar nake ma ko sunsaka guba a ciki fah….kai yaushe zasu saka guda hauka ma suke.
Kai koma menene ciki aradu sainaci,inabanci ba gaba ba samu zanyi ba,kuttt sai yanzu ma na tuna,ance ana kaiwa amaryah kaza in ankawota,dan tsabar iskanci shine suka kawomin iyah doyahhhh wlh sun rainani”
Ai tana gama faɗin haka ta rufe kwanon tareda yin cikin gidan,dan sauri kaman zata tashi sama.
Jauro shida iyalinsa suna karyawa kawai sai ganin Bombee sukayi a kansu rike da kwanon da indo takaimata yanzu.
Suma abinda aka kaimata suke ci,da alama ƙwan irin na kajin gidanne ta ci karo dasu sunata yawo.
Jauro ne yaɗaga kai dan tana kusada shi yace,
“Yarinyah lafiyah koba kya cin doyar ne a samo miki wani abun”
“Da ansan da wani abun aka kawomin doyar,ni nayi zaton nikadai ma akayiwa ashe hardakuma ita kukeci…….kowacce amarya ina ance kaza ake bata idan an kawota sai taci ta ture,shine ni za’a kawomin iya doyah dan an rainan”
“Tohh yarinya wannan fah abincin karyawa ne,kaza kam ina mijinki yakai miki jiya da daddare koh?”
“Jiya yaushe aka kaimin wata kaza,an kaimin zanyi karyane,ni banga wata halitta ba a ɗakin nan bayanni,bare kuma wani abu waishi miji”
Jauro yanajin abinda Bombee tafaɗa yajuya ya kalli Inna daayi da Alamar tambaya.
“Kee daayi yarinyar nan dagaske take goje bai dawo gida ba jiya?”
“Eh….eh to mlm ni banganshi ba nima bai faɗamin inda yaje ba”
“Yanzu a ɗaura masa aure jiya a kawo matar amma kuma yazagaya yayi tafiyarsa,saboda ya maidamu ƙananan mutane kon”
Saida yagama faɗansa Bombee tana tsaye kam batada alamar tafiyah,juyowa yayi ya kalleta tareda cewa.
“Kinga kiyi hakuri yanzun kije kici wannan ,in yaso yanzu zansa Indo ta dafamiki kazar akawo miki,karki damu zan yi masa faɗa kinji,kuma don Allah kar iyayenki su san wannan maganar”
Lallaba Bombee jauro yafarayi,saidai ita duk maganar dayayi bata dameta ba,abinda yafaɗa wanda tagane shine dayace za’a daho mata sai taci ta ture,shine abinda yasakata tafiyah tabasu waje.
Ruwa ta kandama a randar inna daayi tayi wankanta da safe,da ɗauko sabon kaya daga cikin kayan da akayi mata saka.
Doguwar rigace sai mayafinta data ɗora a kanta,takalmi ma sabo da tasaka,daga nan tafito zata fita wani wajen.
Indo ce taga zata fita,da gudu taje da faɗawa inna daayi abinda yake faruwa.
“Inna ga can Bombee fah zata fita waje”
Zaro ido inna daayi tayi tareda saurin fitowa daga ɗakin.
Hanyar wajen ta nufa daidai lokacin da Bombee take shirin fita.
“Ke mekikeyi haka, zaki fita daga kawoki jiyah,anya kuwa baki samu tabun kai ba wannan?”
“Hhhh tabun kai,ai kannawa ma inaga a rushe yake ba tabun kai ba,miye laifi a ciki dan an kawoni gidan jiya zan fita yau,kuɗin wani naci daza’a tuhumeni,ko kuma da wanda nace yaraka ni wani wajene?.
Kinga dan Allah kina bata min lokaci,ina da wani abu dazanyi ne ba zan daɗe ba,inkin dafamin kazar a jiyemin a ɗakina”
“Huh to in daga gidanku aka kawo kazar saikisaka a dafamiki ai,ƴar rainin wayo kawai”
Indo ce tafaɗa cikin hassala,dan taga abin Bombee yawuce a zuba mata ido,tunda take bata taba ganin wacce aka kawota gidan miji jiya da daddare ba,kuma da safe tashirya ta fice,abin ai ko hankali ma bazai dauka ba.
“Badaga gidanmu aka kawo ba,amma tunda ubanki yace a dafa sai an dafa,wlh idan nadawo ba’a dafamin ba,duk saina kashe kajin gidannan a yau basai gobe ba,in kuna tantama ku gwadani dan Allah”
Cikin gadara take maganar tana nuna garken kajin dasuke wani fili a cikin gidan.
Haka ta fita tabarsu basuda ko bakin magana.
Tunda tafita da safe ba ita tadawo ba sai bayan la’asar. Kofar ta tawuce kai tsaye bata ko shiga cikin gidan ba.
Da kwano taci karo a bakin ƙofar ɗakinnata,tana buɗewa kuwa taga farfesun kaji ne guda biyu manya,wani murmushin jin dadi tayi tareda cewa a ranta.
Ashe kuna son kajinnaku da alama,da karku yimana ku gani,banda shiga shirgin mutum ina ruwanku da fitata,ko baban bai isa hanani fitaba ballanta ku.
Zama tayi baje baje taci tayi nakk ta kora da ruwa,kafin ta tuntsire a wajen sai bacci,da alama dama a gajiye ta shigo gidan.
Lokacin data buɗe idanuwanta duhu ya fara,rana tana shirin faɗuwa,tashi tayi ta cire kayan jikinta tareda sake yin wani wankan kafin magriba tayi.
Ana sallahr magriba taji muryar wani gardin a tsakar gida,kana jin maganar kaji irinta tantirannan wanda suke yinta a shashshaƙe cikin isa da gadara.
“Huh inna kenan me kike so kicemin ita harta ta isa ma tafice batareda izinina ba,menene take taƙama dashi dan babarta a garinnan,hmmm zakuwa ta yabawa ayah zakinta,ki barni da ita,zanyi maganinta,zatayi laushi ta yanda sai abinda naga dama zata aikata”
“Yawwa goje nasan bazaka bani kunyah ba,so nake kamaida ta komai na gidan nan ita zatayi shi,badai tana ji da yarinta ba.
Yawwa wai ina ka tafine? Ran mlm ya baci sosai da fitar ka jiya.
Bai kamata ace a kawomaka amaryah jiya baka nan ba”
“Kinga inna wai miyene za’a takuramin dan kawai nayi aure,nine fah nace zanyi aurennan ba wani ne yasaka ni ba,dan haka abinda naga dama zanyi.
Sannan naji kina wani zancen zata dunga yi muku aiki,kar na sake jin wannan zancen,nina kawota gidannan,nikaɗai nake da ikon sakata aiki ba wani ba. Tana ina tadawo ko kuma har yanzu tana waje?”
“Bamu sani ba,da babu wanda yaga shigowarta”
Bagazam bagazam yayi hanyar ƙofar tasu kaman zai tashi sama.
Duk abinda suke Bombee tana jinsu,wani murmushin gefen baki tayi tareda cize baki jin furucin mijinnata. Tana nan tsaye a baranda kuwa ya shigo ƙofar yana muzurai.
“Oh kin dawo ma kenan,nasan duk abinda nake faɗa kina jina,ina so kifaɗamin gidan uban wa kikaje dazu,sannan kuma da izinin wa kika fita?”
Shuru yayi domin bata damar amsa tambayarsa,amma har tsawon minti biyar Bombee bata ce komai,saima juyawa datayi tashige ɗakin.
Hakan datayine yaƙara ƙular da goje,dan dama a sama yake ya bankami angurrr.
“Ke ina miki magana kika yimin banza,da uban me kike taƙama”.
Nan ma batace masa komai,hakanne yasa cikin bazata ya sauƙe mata mari a kuncinta na hagun.
Dafa wajen tayi da hannunta na daman,tareda saka manyan idanuwan ta a cikin jajayen nasa idon.
Ko ba’a faɗaba duk wanda ya kalli idon nata a bayyane zai hango tarin baƙin cikin dayake ciki.
Rintse ido tayi tareda haɗiyewa abinda yake shirin taso mata,matsawa tayi daga gabansa takoma bakin gadon ta zauna tana kallon wani wajen daban.
Har sannan bata buɗe bakinta ba ballantana wani harafin yasamu damar fita.
Takowa inda take yasake yi tareda shafar gefen fuskarta,sannan kuma yafara magana cikin sanyin muryah mai cikeda yaudara dakuma son cikar muradi.
“Ohh kiyi hakuri fah,kece kika batamin rai sannan kika kaini bango,amma idan ba haka ba mai zai sa nakai hannuna kan wannan lallausar fuskarta ki da niyyar cutarwa.
Saidai karki damu,indai zaki kasance mai biyayya hakan bazai sake faruwa ba,idan san ladabtaki ma ta hanyar jin daɗi,nasan zaki so hakan koh??,har yanzu ban huce da fitar dakikayi ba,saboda bansan wajen wa kikaje ba,saidai zan hukunta ki fa hanyar samunki akan shimfiɗina.
Banajin zan iya binki ta hanyar sauƙi,duk da kuwa kedin sabon hannunce,dan daga ganinki zakiyi daɗi sosai,dannasan baƙaramin shirya min ke akayi ba”
Yana maganar yana matsowa inda take,har saida yazamo ya zauna a bayan ta yana shafa bayan ta.
Saƙalo da hannunsa yayi zuwa cikinta,a hankali yaɗaga rigar ya zura hannunsa yana shafa fatar cikinta.
Saurin buge hannunsa Bombee tayi tareda tashi ta tsayah tana kallonsa,jin yana mika hannunsa sama zuwa ga albarkatun jikinta.
Sai a sannan Bombee take ƙaremasa kallo saboda hasken da fitilar ɗakin tabayar ta batir.
Farine tass yana da gashin baki,sannan kuma yana ɗan jiki sosai,musamman ma tasaman ƙirjinsa,kana ganinsa kasan ƙaƙƙarfane sosai,kuma babu alamar mutunci a tattare dashi.
Murtuƙe fuska yayi ganin yanda Bombee ta buge hannunsa lokacin dayake tabb ta kaiwa ga muradin ransa.
Tashi yayi yafara takawa zuwa inada take,yana nufarta tana matsawa harsaida yakaita bangon ɗakin.
Kallon idonsa takeyi wanda suka fara ƙaduwa ganin yanda Bombee take sauke numfashi kirjinta yana ɗaga tacikin rigar dake jikinta.
Bata ankara ba sai gani tayi ya sutale dogon wandon dage jikinsa,zaro ido tayi kaman zasu faɗo ganin abinda tayi arba dashi.

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤25🖤

Sauƙe ajiyar zuciya tayi ganin ashe akwai ƙaramin wando a cikin dogon daya cire,saidai kuma an gudu ba’a tsira ba,gani tayi wandonnasa yana ɗagawa kaman wani abune yake motsi a cikinsa.
Dariyah ya kece dai ta ganin inda idonnata ya sauƙa,wato kan hajiyar sa.
“Hhhh ƙwaila kenan,tun ba akai ga komai ba harkin fara karayah,ima tsiwar taki da aka bani labari toh,ki shiryah yanzu zanyi miki abinda nake wa sauran ƴaƴa wanda kike ji da kunnenki a gari.
Naji dama ance kinzo gidannan neman sanin wayeni koh,to inaga bakya bukatar sanin mai zai faru.
Yanzu nan zan aikata miki abinda nake aikata wa,saidai ke ta hanyar au…………”
Bata bari ya ƙarisa faɗin abinda yake shirin amayarwa ba tazage iya karfinta ta cankeshi a gabannasa,bayan ta tabbatar yagama sake lagonsa.
Giff ya rufe bakinsa baikai ga karisa maganar dayake mata ba,lokaci ɗayah abubuwa dayawa suka shiga kwakwalwarsa,Azaba,razana da kuma yanda abin yazo masa a bazata.
Kafin yayi wani yunƙuri ya sheme a kasa warwars ko motsi bai sakeyi ba na kirki. Babbar alama ta nuna baƙaramin lahani Bombee tayi masa ba,sanadiyyar dukan data kai masa.
“Yanzu sai naga wane abun zakayi mana abinda kake iƙirarin aikatawa ai,da tunaninka tun farko tsoronka nake,hmmm da alama baka je ka tambayi wacece ni ba,bayan ni nasan waye kai”
Tsugunnawa tayi wajen saitin fuskarsa ta wanke shi da mari tasss.
“Marina dakayi na rama,ina ka mutu ma bana binka bashi,dan hakan sai ya dameni,idan na tuna ka mareni ka mutu ban rama ba”
Mayafinta ta ɗauka yafa kafin ta dauki duk abinda tasan tana buƙata ta tsallakeshi ta bar dakin.
Batareda kowa yaganta ba tafita daga gidan sai cikin garinsu.
Lokacin data isa dare ya ɗan yafara.
Babu kowa a tsakar gidansu lokacin data shiga,dan haka kai tsaye ɗakinsu ta wuce,babu kowa a ciki da alama innayi tana ɗakin innarta.
Gadonta ta kaɗe hankali kwance ta kwanta.
Sai muce saida safe…………………

Da safe indo ce yauma takawo musu abinci kaman jiya,mamaki tayi ganin ƙofar wangale ko turata ba’ayi ba.
Har ta juya zata tafi sai kuma tagano kaman ƙafar goje yana kwance a tsakar ɗakin.
To shikuma yau kwayar kwanciyar ƙasa ta gara masa,hmmm ko ya murƙushe ƴar mutane har saida yagaji kai,maganinta ai ba ita marar kunya ba.
Ajiye kwanon tayi zata tafi,har ta bar ƙofar saikuma ta dawo tafara kiran Bombee.
Kira uku tayi mata amma shuru ba’a amsa mata ba.
Uhm barina duba koya jimaya rauni,ƴar mutane ta mutu mana mushiga uku.
Tura ƙofar ɗakin tayi ta leƙa kan gadon,amma babu kowa akai,sannan babu alamar an kwana ma akai,dan shinfiɗinsa yana nan rass.
Wajen banɗaki taje nan ma babu alamar mutum a ciki,hakanne yasa ta dawo ɗakin ta sauri domin ta tashi goje.
Shurarsa tayi taƙafarta amma shuru bai tashi ba,hasalima ko motsi bayayi,kuma numfashinsa ma baya fita kamar na mai bacci.
Jini ta gani yafito ya bushe a ƙasan gajeren wandonsa dayake mai haske ne.
Ihu ta kurma iya karfinta tana ƙiran inna daayi.
Jin ƙiran bana lafiya bane yasa ta taho da gudu zaninta ma a hanya ta karisa gyarashi,don ita duk a zatonta ma goje ne yayiwa Bombee aika aika,dan dama tun jiya sun saka tsammanin faruwar hakan.
Saidai tana zuwa wajen saita tarar sa’banin abinda take tsammani.
Indo ce akan goje har sannan tana jijjigashi amma yaƙi tashi,sai ihu take tana ƙiran sunansa.
Suna cikin hayaniya ne jauro yashigo wajenna su jin suna kiran sunan goje suna salati da kuma ihu.
“Yau nashigesu ni daayi,mlm zoka gani anya kuwa ba barayine suka shigo gidanann ba,shi yana kwance da alama dukansa akayi,itakuma Bombee batanan,kar ko ɗauketa sukayi kai?”
“Kinga bar wannan zaton,maza maza ɗakko mayafinki barina je wajen garba yazo da motarsa mukaishi cikin gari asibiti”
Cikin ƙanƙanin lokaci jauro yadawo suka ciccibeshi zuwa cikin motar sai asibiti.
Suna zuwa kuwa aka shiga dashi ɗakin gaggawa,zuwa lokacin ya farfaɗo,amma daƙyar yake motsi,kana ganinsa kasan yana cikin mawuyacin hali.

Tun takwas suka kawoshi asibitin,sai wajen goma kafin ya farka sosai,shima dan anyi masa alluraine dakuma bashi magunguna da karin ruwa.
Dan sanda jauro yaɗakko domin abin dole saidasu a ciki,saboda ana buƙatar sanin wanda yayi masa wannan lahani har cikin ɗaki.
Tareda ƴan sandan dakuma jauro aka shiga ɗakin asibitin inda goje yake kwance.
Dare ɗaya har ya rame ya fita a hayyacinsa,silin yake kalla yayi shuru,da alama yatafi kogin tunani,cinyoyinsa kuma an ɗaɗɗauresu da wasu karafuna a jikin gadon.
Dan sandanne ya kariso inda yake a hankali cikin jimamin halin dayake ciki.
“Sannnu fah ya jikin,dan Allah idan bazaka damu ba shin zaka iya faɗamana mai yafaru?”
“Bbboombiiii”
Dukkansu zaro ido sukayi,dansun fahimci inda zancennasu ya dosa,dan dama likitan yafadamusu farmakarsa akayi a gabansa da duka,wanda hakan ya jawo masa matsala,har sannan basu gama gano mai yake faruwa ba.
“Wacece Bombee kuma,ko wacce nasani ƴar gidan mlm Ahmadu??”
“Eh ita fah,kuma matarsa ce jiya shekaranjiya aka kaita ɗakinsa”
“Tohh abin daban mamaki,yanzu dai muje gidannsu muji mai ya faru,dan bazata wuce gidan ba,tunda mungane ba wasune suka farmakesu ba”
“Hoɗan wannan yarinya anya kuwa mutum ce?”
Jauro ya faɗa cikin mamaki.
“Aiko aljanace sai tasan tayi wannan aika aikar,kuma fah babu itace a ɗakin wanda ta dakeshi dashi”
“Hakane kam inna,ita sai anyi mata hukunci daidai laifinta,ni da kasheta ma sukayi”
Inna daayi ce ta kwabe mata bako ganin dan sandan yana wajen.
Shawarar ɗan sandan suka bi,ita inna daayi da indo suka zauna a wajensa,shikuma jauro da ɗan sandan suka nufi gidansu Bombee.
Tunda ta nuƙo hayar kyauyennasu tashigo gidansu ,data kwanta ba ita ta tashi ba sai ƙarfe goma.
Buɗe ɗakin tayi tafito daga tana mika tareda yin hamma,alamar mutum yayi bacci ya more.
Da inna laari suka haɗa ido tana bakin ƙofar ɗakinta.
“Innalillahi wa inna ilaihi ra ji’un mai zan gani haka ni laari,ko gizo ne take min kai”
“Mai ya faru yawuro kike wannan salatin,gamo kikayi da safiyah”
“Malm inaga gamo nayi,Bombee fah nake gani tafito daga ɗakinsu,anya kuwa kalau nake”
Daneji dake daki tana shiryawa Addarta Hadiza kayansu zasu tafi,batasan lokacin da ƙirjinta yai wani daramm ba,duk da hakan ba abune da zata gasgata ba,saidai kuma hmmm Bombee ce fah?
Maryam ce tashigo ɗakin bayan ta ajiye butar hannunta tareda cewa cikin hausarta mai haɗe da fillansi.
“Inna Daneji dagaske fah take Bombee ce a tsakar gida,kuma daga yanayinta kaman a gidanann ta kwana,dan fuskarta yayi kama da wacce ta tashi daga bacci”
Tun kafin Daneji tagama jin ƙarishen maganar ta daka tsalle sai gata a waje.
Haɗa ido sukayi da Bombee wacce tayi saurin dauke idonta tana kallon kasa.
Shurune ya ratsa wajen na ƴan wasu mintuna,kowa yarasama mai zaice mata.
Ɗaga idonta tayi a hankali tana ƙarewa mutanen dasuke wajen kallo,ƴan gidannasu ne dukka inka ɗauke innayi datake makaranta,sai kuma ƴan uwan Daneji dasuke shirin tafiya a lokacin. Daga gefe kuma Hajiya Dadda ce yayar babansu wacce take zaune a taraba,itama shirin tafiyar take a ɗakin inna laari,tajiyo wani sabon batu wai amarya a gidan ta kwana,sai yanxu suka ganta kwatsam da safe.
Mlm Ahmadu ne ya buɗe baki zayyi magana bayan yagama shurun takaicin.
Baikai ga cewa komai ba sukaji muryar Jauro a ƙofar gida,da kuma muryar wani mutum daban da basu wayeshi ba.
Fita yayi wajen gun sallamar,dan yasan bazai wuce ta dalilin Bombee ba.
Shigowa yayi dasu cikin gidan,dan inya tsayah yi musu magana ma bai san mai zaice musu ba,wataƙila ma sunfishi samun masaniyar abinda yake faruwa.
“To ga surukinki nan,saiki faɗamana meyasa kika dawo gida,kuma ma dan iskanci wai a gidana kika kwana ban sani ba,bayan na kaiki ɗakinki shekaranjiyah”
“Hmmm mlm Ahmadu kenan,ɗazu fah naji kururuwar iyalina,ina zuwa na tarar da goje a kwance kaman gawa. Nan muka ciccibeshi sai asibiti,da farko nayi tunanin wasune suka kawo masa farmaki.
Amma abin mamaki daya farfaɗo sai yake faɗamana wai matarsa ce tayi masa haka wannan aikin.
Zancen danake masa yanzu haka likita yabamu bayanin da ƙyar ya iya haihuwa,saboda dukan datayi masa a gabansa da daddaren”
“Meeee????”
Dukkansu suka haɗa baki suna kallon Bombee wacce ta cuno baki,lokaci ɗaya kuma tafashe da kuka kaman ba ita ba,ihu take jikinta har rawa yake,cikin marairaiciyar murya ta kalli babannata tareda cewa.
“Baaaba wlh kaman yanda nace muku na yarda ayi auren banyi niyyar yin komai ba. Ranar da aka kaini baidawo gidan ba,sai jiya da daddare yashigo min ɗaki yana maganganun maye na shaye shaye,bance masa komai ba yah wanka min mari,kaga ma wajen.” Ta faɗa tana nuna marin dayake kwance a fuskarta.
“Daga nan kuma yafara tahowa inda nake ina matsawa har jikin bango,ni bansan mai zaimin ba sai yacire wandonsa yana dariyah.
Abin mamaki yabani ganin babba yacire wandonsa,kuma sai ya fara maganar data bani tsoro.
Wai abinda yakeyiwa mata a gari nima shizaimin wato fyaɗe,cikim tsoro saboda na kare kaina nakai masa duka a wajen,saboda a ganina hakan zaisa ya ƙaleni. Bansan zai faɗi ƙasa ba aradu……kkkuma tsoro naji danaga yanda yayi wa Atika akace ta suma ankaita asibiti,shiyasa na kaimasa naushi,daga haka ban kwaɗa masa komai ba,inaga bayan na tahone saboda kar ya tashi ya rama,wani kuma yaje ya dakeshin….”
Ƙarisa maganar tayi tana share hawayen dayake fitowa a idonta.
Duk wajen a yanda suka saurari zancennata sun tabbatar,batada ilimi akan abinda goje ke shirin yimata,sannann batayi tsammanin dukan datayimasa zai masa illah haka ba.
Inna laari ce takalleta tareda cewa.
“Kina nufin kice bakisan abinda goje zai miki,shin ina maganganun dana faɗamiki kafin akaiki gidannaki?”
“Iyeee nifah banji mai kuke cewa ba a ɗakin baba rannan,dan kafin mu shiga na toshe kunnena,saboda kar naji abinda kuke faɗa nayi kuka. Ji nayi ana cewa wai duk wanda yaji abinda ake fada masa kafin akaishi gidan miji to zayyi ta kuka,nikuma banason nayi kuka shiyasa na toshe kunnena”

Toh fah ga wata katobarar ta kawo kai,Bombee bataji hudubar da akayi mata ba🤣🤣🤣🤣.

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤26🖤

Dukkansu sakin ajiyar zuciya sukayi na takaicin sakarcin Bombee ɗin,saidai babu yadda zasuyi ba laifinta bane,tunda kowa yasan ita yarinya ce,sannan a yanda take da kasada,da kuma yanda goje ya farmaketa,koma waye iya abinda zayyi kenan.
Malm Ahmadu bashida zabi illah ya ɗora kusan dukkan laifin a kansa,tunda shine ya aurarta batareda tasan komai ba.
Shiryawa yayi shida su jauro suka nufi asibitin,domin ganin jikinsa tanan kuma zasu wuce police station akan case ɗin.
Bombee kuwa ganin kowa ya dauke kansa daga kanta bai sake cewa komai ba,yasa ta tabbatar labarin data basun ya samu karbuwa a xuƙatansu,dan haka itama sai tasaki ranta,tareda ɗiban abincin karyawa ta shiga ɗaki, dama yunwa ce ta tasheta daga baccin.
Bata ƙarisa gama cin abincin ba sakeenah tashigo cikin ɗakin ɗauke da sallama,amma mutuniyar ko amsawa batayi ba,duk da tasan sakeenan ce.
“Hmmm sallamar ma bazaki amsa ba Bombee,mai yayai zafi haka?”
“Wutah…..wuta ce tayi zafi,mai ya kawoki wajena da sanyin safiyar nan?”
“Kutt yanzu ne safiyar kuma ma zuwa wajenkine laifi komai,…naji abinda yafaru tsakanin ki da mijinki,gabaɗaya gari ya ɗauka Bombee tadawo gida bayan kwanan ta ɗaya a gidan miji?”
“Wata tsiyar ce dan nadawo to,ina kema kikace mijina bana wani ba,mutanen garinnan allah suna shiga hancina da ƙudundune,ke kuma ga munafurfur shine kika taho da rawar ƙafa ki faɗamin ko”
Juya ido sakeenah tayi tareda hararar Bombee,haka kawai jininsu ya haɗu,amma ko yaushe Bombee cikin nunamata isa take a dole ta fita da wata biyar.
“Kaiii ke wallahi Bombee tsiyata dake wanda yadamu dake ma baki barshi ba,koda yake laifina ne danake biyemiki”
A zuciye ta tashi zata bar ɗakin,Bombee tayi caraff ta rike mata hannu tareda cewa.
“Keɗince shegen surutunki ya miki yawa,naji menene yakawoki toh wajena,nasan dole akwai dalili”
“Hmm wai kura ce zatace da kare ya maye,kawai zuwa nayi tayaki zaman jimami,duk da cewar ko kaffara bazanyi ba nasan da gangan kika lahanta goje badan yakawo miki farmaki ba ko kuma dan kina tsoro ba,dama kin shiryah hakan tun sanda kika yarda da aurensa”
“To kin sani miyasa kike sake tambaya dama”
“Saboda share tantama ne”
“Hmm wato dan kiji daɗin zuwa kice ita tafaɗamin da bakinta dagangan ta maujeshi”
“Hhhhhh kinsan bazanyi hakan ba,nidama duk shirin auren da akeyi nasan bakiyi kama da wacce zataje ta zauna ba,ki kallifah kayanki na gida,duka sunanan babu abinda ya samesu baki bayar dasu ba ko kin tafi dasu…….ahhh to kayan auren fah,kinsan tunda baki daɗeba dole zasu karbi abinsu”
“Hhhh daga baya kenan,jiya naje nayi ciniiki na karbi kuɗinsu,yau zasuje a matsayin barayi suɗau kayansu yanda na tsara”
“Innalillahi keee Bombee to idan goje yaƙi sakinki fah yazakiyi”
“Hhhhhhh lallai kema gara ce,to ko kudin hajji aka bashi nasan bazayyi gigin ƙin sakina ba,kijira kiga zuwan takardar tawa,ɗan iska yaje yagama akuyancinsa da wasu,kuma tsabar dan ya raina rayuwata yace zan buɗe masa cinyata?….shi a dole wai ga miji ahh ubangida kai,tauren banza tauren wofi,na tabbatar yanda nayi masa dukannan bazai ƙara moruwa ba ta wannan fuskar kan,shida haihuwa kuwa saidai yaga anayi,naga da yanda zai sakeyiwa ƴaƴan mutane ciki”
“Kutt waikina nufin kinsan komai dama tsiyace”
“Da a tunaninki bansani ba,me kika ɗaukeni ne,dan kawai nace bansani ba shiyake nuna bansani,ke karki dameni bacci zan koma,ki tafi naki harkar.
Zan zauna a gida na sati ɗaya,daganan naɗora daga inda natsayah”
Takarisa maganar tana hamma tareda sake miƙewa akan gadon.
Jijjiga sakeena tayi tareda ficewa a ɗakin,Bombee ta wuce duk yanda take tunani.

Lokacin da suka isa asibitin su daayi sun ɗan tada goje da pilo,ana zubamasa ɗan ruwan shayi a baki yana sha.
Sannu da jiki mlm Ahmadu yayimasa,ya amsa daƙyar,inna daayi kam ko kallon sa batayiba.
Dan sandan ne ya matso inda goje yake tareda cewa.
“Goje yanzu muka dawo daga gidan su matarka,ga surukinka nan ma kana gani,munyi mata tambsyoyi da dama,amma a yanda ta bamu labarin abinda ya faru,alamu ya nuna cewa batasan komai dayake faruwa ba dangane da zaman aure. Tace mana tunkarota kayi kana ce mata zakayi mata irinna sauran matan datakejin labari,wanda hakan yasaka ta shiga cikin tsoro ta farmakeka domin kare kanta. Saboda a baya taga yanda matan daka lalata suke shiga cikin wani hali na damuwa,kuma yanda ake bawa mata labarin fyaɗe,abune da ake nuna musu mutuwa ce kawai tafishi.
Shin dagaske ka farmaketa ko kuwa”
“Ehh to lokacin dana dawo gidan ina cikin fushi ancemin tafita da safe,to…..shiyasa nace mata inna fara babu wanda zai iya ƙwatarta a wajena,na nufeta domin nasaka ta jin tsorona,daga nan bansan miyasa ba ina dabb da kaiwa hannuna kanta saijina nayi a wata duniya daban ina juyawa”
Ajiya zuciya ɗan sandan yasake tareda cewa.
“Alamu yanuna kenan labarin data bayar da gaskene,sannan koda ankaita kotu baza’a ɗaureta ba,saboda an tabbatar batada masaniya gameda abinda yake cikin aure,wanda iyayenta sun amsa cewa hakan laifinsu ne. Sai nabiyu kuma ta kaimaka farmaki ne domin kara kanta daga fyaɗen da take tunanin zakayi mata”
“Amma kowa yasani tunda matata ce,ai ba fyaɗe zanyi mata ba”
“Eh kowa yasani,amma ita da batasan komai ba akan auren bata sani ba,laifi nakane goje,dana iyayenta kuma. Dan haka mlm Ahmadu zai biya komai daya danganci maganin ka har ka warke”
“Wannan zancen banzane,wacce bata san komai bane zata iya wannan aika aikar,zancen nan dasake,inma mlm Ahmadu cin hanci yabaka domin ka faɗamana haka to bazan yadda ba”
Jauro ne yasaka hannunsa akan kafaɗar inna daayi tareda cewa.
“Kinga kibar wannnan kumfar bakin,babu wani cin hanci haka zancen yake”
“Huuh haka kam,Dan Allah kuyi haƙuri da abinda yafaru mlm jauro,haƙiƙa abu bayyi daɗi ba,saidai babu yanda za’ayi tunda yafaru,yanzu zancen gida nakawo kuɗin da akayi zan bayar,ayi hakuri dan Allah.
Yarinya kuma kozata koma gidanta ba yanzu ba saitasan komai tukunna”
Tun kafin mlm Ahmadu yagama bayanin dayake goje ya zare ido tareda cewa.
“Wacce yarinyar kake zance,banason sake ganinta a rayuwata,wannan ba mutum bace,in aurena ne dayake kanta ake haɗani da ita,to na sake ta saki dubu ma idan anayi,bana som hanya tasake haɗani da ita ta arziƙi saita ɗaukar fansa”
Hannu Inna daayi takai zata rufe masa baki,amma ta makaro ya aikata abinda take gudun.
“Kai shashashan inane,karka manta fah yanzu tamaida ka musaki wanda bazai ƙara haihuwa ba,daka saketa wacece kuma zata zauna dakai,amma da ka barta ina dole ta zauna dakai. Yanzu kuwa zataje tafara sabuwar rayuwarta hankali kwance”
Kuka inna daayi tafashe dashi tareda cewa.
“Burina shine naga kayi aure ka haihu,amma wannan burin yanzu yakau har abada babu shi. Zabin daya ragemin shine naje na tattaro ƴaƴan daka raba a titi na riƙe,dan sukaɗai yanzu suka rage,wani bazai zo ba………wannan yarinya kwai tsinanniya,bantaba zaton idan ka aureta nakasa ka zatayi ba,ita ma dolene taga karshenta aradu”
Ganin fallashe fallashen da inna daayi take tana kuka ne yasa mlm jauro jijjiga cikeda takaici,jan su mlm Ahmadu yayi waje suka gama tattaunawa,daga nan zance ya wuce,aka bar goje da wahalalliyar jinyah.

Cikin ƙankanin lokaci zancen Bombee ta lahanta mijinta a daren farko ya karaɗe garin gembu,kowa sai mamakin labarin yake.
Ita kuwa Bombee yakan ko kaɗan bai dameta ba,dan dama da gangan tayi hakan saboda tasaka tsoron son aurenta a zuƙatan mutanen garin.
Aikuwa tayi nasara,dan tundaga wannan lokacin koshi mlm Ahmadu bakinsa yayi mutt dayi mata zancen aure.
Zuwa jeji kuwa wajen su inno bata fasaba,sukansu basuji daɗi abinda tayi ba,amma ya zasuyi macece da ba’a sakata tayi saitaga dama.
Babu abinda yafi damun Daneji da lamarin sai yanda Bombee tabata kunya a gaban ƴan uwanta,suka zama ganau ba jiyau ba akan abinda Bombee tayi.
Har kusa sati guda da faruwar hakan Daneji bata kalli inda Bombee take ba,saboda takaicin abinda tayi. Tana sane da fushin da innartata take da ita,duk da yana damunta amma ta basar,dan tasan zata hucene nan da wani lokaci.
Tana tsaye a bakin gadonta tana shirin fita Daneji tashigo ɗakin cikin ɗaure fuska.
“Ina zaki da yamman nan?”
“Uhm zan ɗan……”
“Jeji zakije koh,kafin ki tafi jejin bani kuɗin kayan ɗakinki da kika siyar,zan mayar wa ubanki kudinsa”
“Inna ni ban……”
“Nima ƙarya zakiyimun kaman yanda kikayiwa mutane lokacin da kika kashe mijinki a tsaye,a tunaninki bansan duk abinda kikeyi ba,harda zuwanki wajen maharbi uwaisu ba,nice nacewa inno Ta dunga saka ido akan ki.Hmmm nifa na haifeki Bombee mai zaki boyemin dangane da rayuwarki.
Ba wannan ne yakawoni ba,ke yashafa wannan rayuwarki ce,amma kuɗin kayan dakin kam banaki bane bani su nan”
“Dama inna kin…kinsan…..amma ina baki fadawa baba ba ko?”
“Meyasa zan faɗamasa,mekike nufi,sai na buɗe bakina na tozartaki a duniyah bayan wanda kike ciki. Nima ba auren da akayimiki nakeso ba,sanann kowa yasan halin goje ya cancanci fiyeda haka,amma ba goyon bayanki nake ki aikata wani irin sa ba.
Ki kulada duniyah dakuma wanne mutane zaki fuskanta a duk inda kike,jikina yana bani rayuwarki bazata tsayah iyah garinnan ba,zaki shiga duniyah da nisa,dan haka idan hasashena yabbata ki dunga tunawa mutunci yafi kuɗi,sannan ki maida Alkhairi idan akayi miki,kuma ki tuna abu uku.
Duk da bawani sanin mutuncin kanku kikayi ba,ku tuna cewar ke musulma ce kuma macece sannan kuma bafulana,kinuna asalinkin a ko ina”
Ƴar dariyah Bombee tayi,haka halin innar tata take,tana yimata hanya a cikin duhu tana takawa batareda tasani ba,….ko dabbar da aka haifa yau kuka take ƙoƙarin yi na neman uwarta,ko ɗan banza yana san uwarsa,komin ƙarfinka wajenta zaka nufa in duniya tayi maka zafi,Allah yamu ikon kyautatawa iyayenmu,idan ƙasa ta binne idanuwansu kuma Allah yayi musu rahama da jin ƙai.
Ciro kuɗin Bombee tayi a ƙasan kayanta ta miƙawa Daneji,karba tayi ta ƙirgasu tareda kallon Bombee.
“Komai zakiyi a duniyah kisani Sata bata bawa mutum daraja,ki samu naki koda kuwa ta wuyane,karki dauƙi na wani,kisa a ranki kinfi ƙarfin hakan,saikiga zuciyarki da sane da abin hannun mutane”
Ɗaga kai Bombee tayi cikeda jin daɗin maganar mahaifiyar tata,wanda lokaci guda tayi musu matsugunni a cikin taswirar rayuwarta.

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤27🖤

Bayan shekara biyu………….

Kyakykyawa kana farar budurwace sanye da riga da wando farare,tayi ɗamara da wani jan ƙyalle a mulmulallen kunkuminta wanda yabaje yabada siffar mata masu cikakken diri,saidai daga ganin jikin kasan ana yawan motsashi,dan a tsikeyake tsama.
Juyi take tayi gaba tayi baya da sanda a hannunta,wanda take tafiyar dashi a iska cike da bajinta da kuma ƙwarewa.
Tayi kaman sa’a guda tana yi,amma batada alamar dainawa ko nuna gajiyarwata.
Sai can kaman da daƙiƙa uku ta tsayah tana maida numfashi sama sama.
Duk da rigar wuyanta nada ɗan sama,amma kasantuwar tsallan data sha nakusan awa guda,yasa wuyan rigatata yin kasa,da yanda mutum na iya kallon saman fararen albarkatun ƙirjinta.
Jan rigar tata tayi tagyara,har sannan bata daina fidda nimfashi ba sama sama.
Nufar wajenda ta ajiye kayanta tayi tareda ɗaukar gorar ruwa takafa a bakinta.
Da yawa tasha ruwan kafin tasaki ajiyar zuciya nauyayya..
Shuru ta ɗanyi kaɗan jin wani motsi yana nufo inda take,idonta ta buɗe a wajen da kunnenta yajiyo mata motsin..
Kasantuwar girman tafara suma idanuwannata sun samu damar ƙara yin dara dara farare tass,ƙwayar idonta kuma yanzu tasake yin wani shuɗi mai sheƙi sosai,Motsi shuɗin cikin idon yake yi,daga ƙarami yakoma babba daga babba yakoma ƙarami,sakamakon daidaita hasken ranar dayake haskawa zuwa cikinsa,wanda ganyen bishiya yake mata inuwa kuma yana karkaɗawa.
Dan shi kansa ganinta saidayi training sosai akai,yanda zata saita kallonta da rana da kuma dare.
Motsin datake jine yafara yawa kana kuma yana matsowa kusada ita..
Cikin zafin nama ta cafki kwari da bakarta tareda saita wajen da idonta ya tsaya akai.
Sauke kwari dabakar tayi tana kallon wani ɗan matashin yaro dabazai wuce shekarunta ba wato sha biyar.
Ɗaga hannu yayi sama alamar yayi sarranda lokacin data nunashi da kwarinnata,sai kuma yayi murmushi tareda jingina a jikin bishiyar da take kusada shi.
“Waye kai?”
Bombee tafaɗa cikin tsare fuska,alamar babu wasa a gameda tambayar datayi masa.
Takowa yafarayi a hankali har zuwa kusada itah,kana yasaka hannunsa yana shafa jikin kibau ɗim dake kan kwarin.
Har zuwa lokacin murmushin dayake kan fuskarsa bai bace ba.
“Shin zaki ajiye kwarin idan nace ni aljani ne?”
“Bana san shashanci ka faɗamin kai waye,ko kuma duk abinda nayi maka karka ga laifina akai”
“Ba shanshanci bane nima tambaya nayi miki,amma karki ɗau da zafi,sunana Aliyu,amma ana ƙirana da haidar,ina so muyi abota ne dake,shin zaki yarda dahakan”
Sake daure fuska Bombee tayi jin maganar wanda yakira da kansa haidar ɗin ya bafaɗa.
Harara ta gallamasa tareda sauƙe kwarinta tayi wajen da ta ajiye kayanta.
Ɗauka tayi ta saƙala a kafaɗarta tareda yin hanyar inda zata fitar da ita daga cikin dajin.
Binta yake a baya yana magana,amma ko waiwayowa batayi ba ballanta na ta kulashi.
Hakanne yasa ya dakata da binta,tareda yin dariyar gefen baki,shareshin datayi karon farko na haduwar ta dashi sai yaji ya burgeshi.
Tun sati daya dayayi yana yimata la’be yana ganin mai takeyi dama yayi tunanin hakan daga gareta.
Tunda yake bai taba haɗuwa da macen data burgeshi kamarta,ta yarda da kanta,sanann kuma bata kunyar nuna jarumtarta,duk da kasancewarta kuwa ƴa mace.
“Zamu sake haɗuwa Bombee dole sai na miki abinda zaki kulani”
Daga haka ya juya yayi wata hanyar daban yana jijjiga kai.
Itama Bombee a nata bangaren mamakin yaron data hadu dashi take,shin anya kuwa mutum ne,bata taba haɗuwa da wanda yakalleta batareda tsoron halittarta ba sai yau,idan tacire goje wanda shi bata sakashi cikin jerin mutane.
In mutum ne mai yakeyi a cikin jeji…..kai itama ai mutumce kuma take zuwa jejin,mutum ne ma dam bataji wani yarr a jikinta ba,irin wanda take ji idan mai aljanu ko kuma wajen da aljanu suka wulga ba.
Yanda taga shigar kayansa da kuma yanayinta,su kansu basuyi mata kamada irin na mutanen yankin su ba.
“Haiiidarrr???,koma waye kai bai shafeni ba,inka shiga gona ta ba raga maka zanyi ba”
Tafaɗa cikin ƙwarin gwiwa(confidence).
Gidan inno ta nufah,saida taci abinci tayi sallahr azahar kafin ta nufi gidansu.
Ko salama batayiba ta shiga gidan,babu kowa a tsakar gidan,dan haka ɗakinsu ta wuce kai tsaye.
Innayi ce a kwance kan gadonta ta tsuga mata sayi na baccin rana,dan dama ita tana fitsarin kwance.
Kallonta take tareda kama kunkumi tana kallon innayin,babu abinda yake tasomata a zuciya sai takaici.
Gashi dama babu wuyah sai ranta yabaci,ita kanta tana mamakin yanda koyaushe sanzawa take daga yanda take a baya.
Wani lokacin bata ganin laifin mutane idan suna aibatata,dan tasan tanayi musu abin muzgunawar ba bayanda zasuyi,saidia itama babu yanda zatayi,in anyi mata laifin daya bata ramaba ji take kaman zatayi hauka,muryar datake zugata a cikin kanta bazata taba barta tayi bacci cikin salama ba.
Dawo da tunanin ta tayi kan innayi wacce take jagab cikin fitsarin datayi mata kan gado.
“Yau zakici bantan innarki laari a gidannan innayi,dama ina taraki da gulamar dakikeyimin a cikin gari,shegiyar yarinya kai”
Takarisa magana tareda ficewa daga ɗakin tana cijan baki.
Fitowar inna laari daga ɗakinta taga wucewar Bombee cikin ɗakinsu ta bulali a hannunta dogaye guda biyu tana yimusu tuka.
Zaro ido tayi dan tafi kowa sanin mai Bombee zatayi dasu.
“Keeee Bombee wazaki daka da wannan bulalin haka?”
“Ki zuba ido kiga wa zan daka dasu mana,miye kike wani gaggawa”
Ta ƙarisa maganar tana watsawa inna laarin harara.
Tana shigewa ɗakin ta rufo ƙofar kirif,ko minti biyu ba’ayiba ƙarar dukan bulala ya jiyarci kunnenta,da kuma kukan ƴar tata wacce take har ƙasan maƙoshinta.
“Wayyo ku ceceni zata kasheni wayyo,innata innata ki taimakeni innaaaa”
Ganin inna laari bazata jure ihun ƴar tata ba yasa ta nufi ɗakin Daneji wacce itama take bacci,ga kwanannnan laulayin ciki take mai wahala,har ya yi wata biyar amma wahalar sa taƙi barinta ta huta.
“Daneji bakyajin Bombee ne zata kashe ƴar uwarta a ɗaki”
Zabura Daneji tayi ta tashi dakyar tareda nufar ɗakin su Bombee,wacce bakajin komai sai ƙarar bulalin dakuma ihun innayi wanda yafara dushewa.
“Ke Bombee ki buɗe ɗakinnan nagayamiki,wai meyake damunki nene kam a gidannan,anya kuwa kanki daya,ki bude dakinnan kafin raina ya baci inagaya miki”
Buɗe ƙofar tayi tana huci kaman sunyi dambe da bijimi,kanta a ƙasa bata bari sun hada ido da Daneji ba,wacce in kallo yana huda mutum daya hudata a lokacin.
“Mai tayi miki kika mata wannan mummunan dukan?”
“Fitsari tayimin akan gado,bayan tasan na hanata hawa min gado”
“Yanxu dan kawai rayi miki wannan lafin shine kika yi mata duka haka,”
“Faɗamata dai,anyi mata aure ta kasheshi da baƙin halinta,ta dawo gida ita ba auruwa zatayi ba tana musgunawa ƴan gidan.akan fitsari shine zakiyimata wannan dukan dan baƙin hali,nasan ma ba iya akan fitsari bane akwai wani mugun nufinki dai daban”
“Ehh akwai mungun nufin,tunda take zuwa tana munafurcina ko kuma takemin raini kin taba hanata ne,shine danna ɗau mataki za’a ga laifina,in kinji haushi ki rama mata mana,kiga in ban kasheta a gidannan ba muss har lahira kum……….”
Fasss bata gama kaiwa ayah a maganar tata ba taji Daneji ta wanketa da wani zazzafan mari a kumatunta,kafin ta juyo tasake daɗa mata a ɗayah kuncin.
Idonta har kanƙancewa yakeyi jikinta yana rawa saboda bacin rai,nuna Bombee tayi da yatsa tareda cewa.
“Bombee……..yanzu har kinyi girman da a gidannan zaki buɗi baki ki faɗawa addah laari haka,ehh lallai yau na tabbatar da baka haihuwar ɗa kuma ka haifi halinsa,kin nuna min iyakata tabbas,kuma naji daɗi da nunamin wanann halin da kikayi kinji”
Kecewa da kuka inna laari tayi jin abinda Bombee tafaɗa mata akan idonta,wanda suna cikin hakanne mlm Ahmadu shima ya shigo gidan.
Tambayar mai yake faruwa yayi,amma babu wanda ya tanka masa,ita Daneji tana faman yiwa Bombee faɗa,yayinda ita kuma inna laari take aikin share hawayen idonta da gefen zaninta,itakuwa wacce tafi dakuwa kukanta yafi na kowa yawa a gidan.
Larai kuma taga kan katanga tana sallallamin jin abinda Bombee tayi ɗin,dan tun ihun innayi na biyu take kan katangar.
Shi mlm Ahmadu dayake ta faman tambayar mai yake faruwa,bai samu sanin hakan ba daga wajen su,sai a wajen inna larai wacce take kan katanga tana kwararo masa bayani kaman recorder.
Tun kafin tagama faɗamasa mai yake faruwa ya zari igiyar awakai dake gefensa ya hau Bombee da duka,wacce take tsaye ƙinkam yana dukannta.
Tun yana dukannata da igiyar har saida ta yayyage ta baje a hannunsa,amma Bombee tana tsaye ta rufe idonta,sai ya zabga mata bulalar taɗan runtse ido kaɗan.
Shatu ce itama dake kan katangar tasamu damar faɗin
“Yanzu Bombee bazaki gudu ba irin wannan duka da ake miki”
Bayan ita babu wanda yayi magana,kowa baki ya buɗe yana kallon Bombee,yayinda shikuma mlm Ahmadu duk bayan duka ɗayah sai zuciyarsa ta ƙara tafasa.
Jefar da igiyar yayi yasake tsinkar tashanyar su ya cigaba da dukan Bombee da ita.
Wanda ita kuma a nata bangaren ba dukanne yake wahalar da ita ba,illah ƙoƙarin datake wajen cin galaba akan muryar datake yimata amo a cikin kanta.
Ba abinda take umartarta dashi illah tarama dukan da mahaifinta yake yi mata a lokacin,wanda har abada bata fatan taga hannuwanta sun aikata hakan.
Salatin dataji su inna laari sunayine yasakata buɗe idanuwanta da sauri,ba komai ta hanga ba sai mahaifinta kwance a ƙasa yana dafe da zuciyarsa,wanda tasan ko tantama bazatayi ba ta sanadiyyartane hakan ta faru.
Abin haushin kuma duk yadda taso ƙwakwalwarta tasaka zuciyarta jin haushinta abin ya faskara,saima haushin mahaifinnata daya turnuƙeta.
Tsugunnawa tayi a hankali zatakai hannunta kansa,caraff taji an rike mata hannu.
“Karki kuskura ki taba shi,wlh bakida wannan damar,ki bacemin daga gani yanzunnan”
Daneji ce tayi maganar wacce idonta yayi jajur ta tsanar halin Bombeen.

Ohhhh nagaji……i hope dai yana sugar littafin koh????

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤28🖤

Miƙewa tayi gwiwa a sabule jin abinda innar tata tafaɗa.
Hanyar waje tafita kanta a sunkuye,tana jiyo maganar mutane a bakin kofar gidan,wanda tuk yawancin maganar ta ne da abin tirrr da Allah wadai datayi.
Sauri take tayi nesa da maganganun,dan ba komai suke kara mata ba sai dake daskarar mata da zuciya,maimakon suyi tasiri wajen saka zuciyar laushi.
Sai dare yaraba tukunna tashigo gidannasu,sassafe kuwa kafin kowa yatashi ta fice a gidan.
A gari taji labarin an kai mahaifinta asibiti jininsa ya hau,saidai ba’a bashi gado ba gida suka dawo,tunda bayyi tsanani sosai ba.
Amma tunda suka dawo da la’asar har yanzu bai sake magana ba.
Runtse ido tayi lokacin da labarin ya riski kunnenta,babu makawa tasan itace silar hakan.
Saurin kawar da fuskar tausayin datake ciki tayi,tareda jan numfashi dogo kana ta furzarshi.
Kai tsaye cikin daji ta nufa ta mungun gudu,wanda kowa yakalli hakan yasan da gangan takeyi saboda ta gajiyar da jikinta,aikuwa abinda take nema ta samu,dan daƙyar da ƙarisa filin yin gwajinnata tana maida numfashi.
Idonta ne yasauƙa akan haidar wanda yake zaune akan reshen bishiya yana jin tuffah(Apple)a hannunsa.
“Wow irin wannan gudu haka kaman barewa,daga nesa fah nakejin ƙarar gudunki,anya kuwa ke mutumce,karfah nace da aljana nakeson yin abota”
Tubbbb ta tofar da wayu tareda watsa masa harara tace.
“Wai miye hadina dakaine,sannan da izinin wa kakeson shiga gonata?”
“Gona kuma,bakiyi shuka a wajen ba fah,in ma akwai ni bangani ba gaskiya”
Yakarisa maganar yana duban wajen a cikin fuskar zolaya.
Zaro ido yayi tareda matsar da kansa gefe guda,cattt kuwa ƙaramar wuƙar ta caku a jikin bishyar dayake kai.
Kafin ya dawo hayyacinsa sai ganinta yayi akan reshen a gefensa,fuskakokinsu suna tabb dana juna,ta zuba masa wannan fitinannun idanuwannata masu launin shuɗi a cikin nasa.
“Kutt kasheni zakiyi,sannan kuma yaushe kikazo wajennan iyeee?”
“Ba wannan na tambayeka ba,meyasa kakeson shiga rayuwata,wani ne ya aikoka? Sannan mai kake so dakake bibiyata,na daɗe ina kulada kai a wajennan tsawon sati guda,da farko banyi zaton nikake bibiya ba,sai daga baya na kulada hakan,waye kaiiiii?”
Tafaɗa cikin tsawa tareda dasa masa wuka a kan wuyansa.
“Habaaaa Bombee mai yayi zafi shiba wuta bane,babu abinda nake binki dashi,jarumtarki da kuma yanayinki ne kawai yake birgen,shiyasa nakeson ƙulla abota dake,bayan hakan kuma dama banga kowa a cikin wajenba wanda zanje wajensa”
“Daga ina kake?”
“Kaman yanda na faɗamiki sunana Aliyu,ni ɗan gidan General Muhammad Bello ne. An kawoshi nannne saboda wani case ɗin manyan yan fashi dayake wakana”
Gidanmu nacan ɗayar hanyar ba wacce kikebi idan zaki je gidan maharbinna ba.”
Sauƙowa tayi daga kan bishiyar ta soke wuƙar a kumkumin ta inda tacireta.
“Kaine mutum na farko daya tunkareni da niyyar abota batareda wani dalili ba,kodayake yanada nasaba da cewar baka sanni ba”
“Menene yasa baza’ayi abota dake ba,you are very “interested lady”
“Wanne yarene haka kayi magana dashi,uhm kaman yana kama da wanda malamai da copper ko kuma masu bibiyar wannan jejin suke magana dashi”
“Kutt bakisan turanci ba kina nigeria”
“Nasanshi yanda kayine yamin kama da ba irin na sauran ba”
“Hhhh inaga saboda ba a ƙasar nan nake zaune bane,nazo hutune na shekara guda shiyasa na biyoshi nan domin naga ya wajen yake. Baki amsamin tambaya ta ba,meyasa suke tsoronki”
“Kai baka gani ba,a ganina dai kaiba makaho bane,suna ganin kaman ni ba mutum bace saboda idanuwana”
Dariyah Haidar ya sheqe da ita,wanda hakan yasa Bombee binsa da kallon kaman yasamu tabin hankali.
“Wani blue iris ɗinki,da farko nayi mamaki kam sosai,amma kuma nida na zauna a ingland naga masu irin idonki da yawa,hmmm saidai gaskiya nasu baya shining kaman naki,amma duk wanda yagani yasan ai normal ne,akwai masu abubuwa rare da dama a duniyah”
zaro ido Bombee tayi jin daya faɗa mata cewar akwai masu irin halittarta a cikin duniyar nan a wani wajen nesa da ita,lokaci guda sai kwaɗayin da haɗu dasu yafara shiga cikin ranta.
Tambayoyi Bombee take yimasa yana bata amsa,wani yayi mata dariyah wani kuma kawai yabata amsa.
Lokaci ɗaya sai tasamu kanta da sakewa dashi batareda ta sani ba.
Shikuma ganin tasake tana maganar arziki dashi,hakan ba ƙaramin dadi yayi masa ba haɗeda dauke kewa.
Basu ankaraba suna ta surutu sai gani sukayi rana tayi sosai.
Tashi Haidar tayi taga bakin ruwan dayake zaune ya kalli Bombee.
“Nikam barina tafi,sai anjima zan dawo,daganan zaki fara koyamun wasannan dakike da sanda”
Dariyah tayi tareda cewa.
“Lallai kuwa wasa,abinda nake yayi maka kama da wasa koh?”
“Komai dai menene nina tafi”
Ya juyah zai tafi saikuma taga ya tsaya,kasancewar ruwan take kallah batasan mai ya gani ba.
Muryar da bazata taba mantawa ba taji ya daki dodon kunnenta.
“Heheehhe iyeeee kice kin samu duniya kam,tunda har ɗan matashin saurayi kikayi bansani ba,da izinin wa kike gara rayuwarki haka”
“Da izinina mana,da dana wa zanyi,sannan menene ya kawoka inda nake?”
“Saboda na kwashi romon da bankai ga shaba kika katseni”
Ƴar dariya Bombee tayi tana kallon goje wanda yake tsaye tareda maza gudan huɗu ,bibbiyu a kowanne gefe.
“Ta yaya marar ƙafa zai hau tsani(bladder)? Uhm”
“Idan an hau masa ai ya wadatar,koda shi baxai iya hawa ba,a tunaninki dan bazan iya farmakarki ba shikenan zan bar abinda kikayimin ya tafi a banza ne,yau babu mai ƙwatarki a hannuna,saina maidake abun tausayi,abinda zanyi miki sai ya kafa tarihi a garinnan,dan ba’a taba yiwa wani mahaluƙi irinsa ba”
Yana maganar gashin bakinsa yana ɗagawa,sannan yana haɗawa da dariyar mugunta. Tashi Bombee tayi daga inda take tareda kallon Haidar.
“Haidar kabar wajennan yanzunnan kar abinda zai faru yashafeka,karka damu bazan bari su bika ba,kabi ta bayana ka gudu”
“Ke kuma fah,kina ganin zaki iya da wannan mutanen,su waye su ɗin,sannan me suke nema a wajenki”
“Karka damu dani,zancen suwayd kuma bazan samu damar baka bayani akai ba yanzu,amma idan na rayu ko mun sake haɗuwa za faɗamaka”
Tana gama maganar ta turashi ta bayanta tareda yimasa kallon umarnin dole ya bar wajen.
Yana tafiyah kuwa taji muryar goje yana cewa
“Iyeee kice dagaske ashe kina sonsa tunda har kareshi kike,karki damu babu abinda zanyi masa,zaifi ciwo ma idan yaga masoyiyarsa anyi mata fata fata,zan in yanada wayo shin zai ƙara sonki? Ku lahanta min ita tukunna mazaje”
Yafaɗa cikin gunji.
Farmakarta sukayi a tareda da nufin kaimata mungun duka,saidai cikin sa’a tasamu nasarar tsallakewa ta hanyar yin tsalle tareda riƙe rishen bishiyar da take samanta.
Wuƙar kunkuminta taciro ta sokawa ɗayah a gadon bayansa,aikuwa yafasa ihu yayinda yaji azabar ta ratsashi.
Komawa dabaya sukayi ganin an shafe kusan daƙiƙa ashirin basu samu nasarar tabata ba.
“Kai ogah yarinyar fah ta iya faɗa da alama,ya kake ganin za’ayi?”
“Kuje mata kuma salon dabara mana”
Suna cikin hakanne goje ya sanɗeta tajuya baya ya sake mata sanda a gadon baya,kasa jure zafin dukan tayi,dan haka tafaɗi kasa tana maida numfashin wahala.
Wani sandan goje yasake narka mata a ciki,tasaki kukan mai nuna Alamar dukan ya shigeta.
“Wai ke mai iya faɗa koh,birice ke yau taki taƙare”
Duka yacigaba da kaimata ta ko’ina,babu tausayi babu imani. Tun Bombee tana nishi har yazamo jin dukan take kawai yana shiga jikinta.
Tsugunnawa yayi saitin fuskarta yana kallonta ɗauke da murmushi mugunta akan fuskarsa.
“Kai tulezi ku buɗemin ita ku fara yimata fyade har saina ce ku daina tukunna”
Rufe idonta tayi kirif tana jira taji ta inda zasu shigeta su keta mata mutunci. Duk iya kokarinta wajen ganin ya motsa gabobin jikinta abin ya faskara,dan kamar basa karbar saƙonta ma ballantana su motsa ɗin.
Shirinyewa tayi ta saddaqar tata taƙare daga wajen,a sama sama tajiyo hayaniyar mutane da kuma sautin takalmansu,wanda ta tabbatar bana masu yimata aika aikar bane.
Sakin ta taji sunyi sun nausa cikin jejin,yayin da karar sawunsu yake yin nisa,ƙarar na wasu kuma ya dunfarowa inda take kwance………bata san shin masu cetonta bane ko kuma masu cutar da ita.
Ɗagata taji anyi an sakata a cikin wani abu mai tafiyah.

Sorry ayi hakuri a barshi haka,🤣🤣🤣🤣 bansan mai zance ba

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤29🖤

A hankali take bude idanuwanta wanda sukayi mata nauyi tamkar anɗora mata dutsi akai.
Saurin yunƙurawa tayi zata tashi,amma saitaji jikinta tamkar an ɗaɗɗauresu da wasu boyayyun zarurruka.
Ɗakin haskene dashi amma bana hasken rana ba ko kuma fitila,sai na tsabar farin fentin cikin ɗakin.
Alamar motsi tafaraji a kanta,a hankali take daga kannata harta sauƙeshi akan fankar datake wainawa tana bawa ɗakin wadatacciyar iska.
Baki tasake cikeda mamaki ,dan tunda take bata taba kallon waje mai irin haka ba a rayuwarta.
“Na ɗanɗin inane,sannan kuma waye ya kawoni wajen?”
Ta faɗa sanyaye,bata kai ga tantance hakan ba daga mariƙar ƙofar ya murɗa,wanda lokaci dayah ya murɗa da tunaninta,dan kuwa batasan wata ƙofa mai hannu yana motsi ba.
Haidar ne yashigo ɗakin,fuskarsa ɗauke da mamakin ganin idonta a buɗe.
Ɗaga murya yayi yanda na wajen ɗakin zai jiyoshi yace.
“Mommy kizo da sauri ta farka”
Ƙarisowa yayi cikin ɗakin tareda zama a gefen gadon da take kwance.
“Sannu Bombee yakinki,amma wannan mutane basuda imani a ransu”
“Meyafaru bayan wanda ya auku a jejin,sanann inane nan haidar ka kawoni”
“Muna zuwa mutanen suka gudu,sannan yau kwananki uku a kwance,nan kuma gidanmu ne”
Yana cikin yimata bayaninne wata ƴar dattijuwar mata ta shigo ɗakin,a kallon farko zaka hango kamanninsu da haidar ɗin,saidai matar tafishi hasken fata da kuma manyan idanuwa.
Murmushi tasakar wa Bombee mai taushi tareda zama akan kujerar dake madaidaicin ɗakin.
“Sannu yarinya yajikinnaki,gaskiya a yanda suka dake gidannan kinji jiki sosai,mai kikayiwa wannan mutane haka?”
“Babu abinda nayi musu Mommy,yaran tsohon mijina ne da muka rabu shekara biyu baya”
Tare haidar da mahaifiyar sa suka haɗa baki wajen cewar.
“Tsohon mijinki shekara biyu baya,yanzu ma nawa kike daza’ace shekara biyu baya kinyi aure?”
“Uhm hakana babana ne ya auraminshi saboda naƙiyin jarabawar tafiyah makarantar kwana,to a ranar farkon aurenmu ne…….yazo yimin fyaɗe na farmakeshi shine……….aka raba auren. Yanzu kuma yazo daukar fansar abinda nayimasa,saboda illar danayi masa na bazai sake haihuwa ba”
Dakatar da Bombee Hajiya tayi da maganar,dan tun a bayani farko tagano abinda ya faru,ita kanta tayi mamakin karfin halin Bombee ɗin,amma kuma saita barshi akan tayine dan ƙoƙarin kare kanta.
“Kinga ki daina yawan magana dan baki gama warkewa ba,Allah ya kiyaye nagaba,haƙiƙa kinyi bajinta sosai,dan dama haidar yasha bani labarinki tun kafin yamiki magana,koyaushe sai yazo yacemin yaga mace a jeji tana koyon faɗa.
Yanzu dai ba wannan ba,yakamata ki faɗamana gidanku domin a sanar da inda kike,danna san dole zasu nemi sanin mai ya faru dake”
Shuru Bombee tayi tareda tafiyah tunanin abinda yafaru kafin zuwanta jejin a ranar,abinda ta aikata a gidansu tasan babu wanda zai nemi sanin inda take,kuma ba wannan ne ma babban abin dakuwar ta ba. Ita kanta innarta fama take da lalurar rainon ciki,sannan asibiti sun tabbatar ba’ason ta dunga shiga damuwa,sannan kuma ga uwa uba abinda tayiwa mahaifinta.
Babu abinda take sakawa iyayennata sai tashin hankali,dan haka lokacin yayi daya kamata ta dakata da wannan abin haka.
Numfasawa tayi kafin tace.
“Iyayena basanan,a wajen maharbi uwaisu nake zaune”
“Uhm kaji ba dama saida nace maka mukaita can kace wai bananne gidansu ba,kana ganinta tana shiga gari”
“Eh inazuwa gidan yan uwana ne s garin”
Bombee tayi saurin kare kanta kafin wani ruwan yasake bullowa.
“To shikenan amma tunda yanzu kika tashi,ki bari nan da gobe sai mu maidaki can ɗin,yanzu zansaka haidar yaje ya faɗamusu abinda yake faruwa”
“Ahah Hajiya nagode da ɗawainiyar da kukayi dani na wannan lokacin,amma inason tafiya yau”
Hajiya Zulaiha ce mahaifiyar haidar ɗin ta taimaka mata tayi wanka da dabara. Saboda har yanzu akwai ciwuka a jikinta sosai,ƙarfin hali kawai take danta nuna taji sauƙi.
Abinci Ta haɗamata marar nauyi taci,tareda magungunan da mahaifin haidar ɗin ya siyo mata wato Janar Muhammad Bello.
A leda Hajiya Zulaiha ta ɗaure mata maganin dakuma wasu abubuwan makulashe wanda zasu tafi dashi.
Ɗakin da take kwanca ta shiga,suna ta hira da Haidar cikin raha da nishadi,kaman sun shekara da sanin juna.
Dukkan hiran dayake mata bai wuce na labarin yayunsa biyu mata ba,da kuma ƙannesa ma biyu mace da na miji,wanda suka tafi makaranta basu dawo ba.
“Uhm kace kana da yan uwa sosai,ni kam mu biyune kawai a wajen mahaifinmu,daga ni sai ƙanwata,itama tana wajen innarta”
“Bombee kin shiryah tafiyar kuwa yau,bazaki sake yimana kwana ɗaya ba”
“Ahah zan tafi ai zan dunga kawo muku jiyara”
“Wai ai inaga nanda sati ɗayah zamu tafi,kafin sannan kam ki kawo mana ziyara idan kin samu sauƙi,yanzu ki fito Baban su haidar na nemanki a falo,zai maidaki gida shida Haidar”
Ɗaga kai tayi cikin girmamawa alamar taji abinda Hajiya Zulaiha tace.
Mutum ne mai yawan murmushi kaman haidar ɗin,sannan gashi dogo kakkarfah……uhm soja mazan fama kenan.
Tsugunnawa Bombee tayi kaɗan ta gaisheshi cikin girmamawa.
Ga mamakin ta kuwa bai ƙyamaceta ba kaman ƴan garinsu,dan da fara’ah ya amsa mata. Har yana tsokanarta wai tafi ɗannasa jarumta.
“Da haidar yabamu labarin yanda kika tareshi har ya samu guduwa a lokacin naji kin burgeni sosai,kuma fah ko kunyah bai jiba yana namiji wai mace tatare masa faɗa,mai makon ya tsayah yaji dasu……”
Dariyah dukka wajen aka saka banda haidar wanda ya cune fuska kaman ƙaramin mai yaro mai feeder.
Kuɗi ya ciro ya miƙa Bombee,amma juyin duniyar nan taƙi karba,dan ita tun lokacin da Innarta tayi mata magana akan kuɗi,sai ya zamo bata fiyeson ko kyauta tadunga karba a hannun mutane ba,ballanta na kuma sata.
Haka dole ya ƙyaleta ganin duk ƙoƙarinsa amma taƙi karba,Hajiya Zulaiha yabawa a ƙarshe kan tayimata siyayya to takaimata.
Da haka Bombee tayi sallama ta matarda taji tashiga ranta,bayan innarta da kuma inna shatu Hajiya Zulaiha itace mace ta biyu data jita a ranta.
A bakin ƙofar gidan suka ajiyeta,bayan Haidar yabata ledar ta Hajiya Zulaiha tace yabata.
Inno tana tankaɗen tuwo taganta tashigo tana tafiyah a hankali,alamar babu lafiya,dan dama kwana biyu tana cikiyarta shuru.
“Ahhh Bombee mai ya sameki haka?”
Bata kai ga amsawa ba taji muryar Haidar yana gaisheda inno,mamaki tayi dama biyota yayi?
“Uhm baka tafi bane dama?”
“Ah iya abbane ya tafi,ni sai anjima zan tafi idan naci tuwon inno”
Yakarisa maganar yana ƙifta mata ido,bai san mutane ba amma har ya shige gaba,ta faɗa a ranta,a fili kuma tana binsa da harara.
Shine yabawa inno labarin abinda ya faru,inda suka jajanta sosai.
Sai bayan ya tafi da daddare Uwaisu yanayimata sirace na maganin gargajiya yake cewa.
“Kwananki uku kenan a gidansu,amma kuma maimakon ki wuce gida sai kika iyo nan meyasa,innarki fah jiya taxo nan tana tambayar ko kinzo nan,inno tace mata kinzo amma kin fita.
Nasan tayi hakanne domin ta kwantar mata da hankali,nima tun a jiyan nake nemanki”
“Ahah baffah bazan iya komawa gida yanzu ba,saina samu sauƙi tukunna,Saboda abinda na aikata,wanda kuma duk inna laari ce ,ni banason matar nan wlh,inna kuma ji takeda ita kaman innarta,shikuma goje…….hmmmm”
Tafaɗa tana cizon baki.
“Kee Bombee to miye dalili ciki danta ji da ita,ke kanki shaidace yanda ta riƙe innarki hannu bibbiyu sanda aka kaita gidanku,kowa yana shaidan halinta na kirki”
“Eh kowa yana shaidanta,amma ni zuciya ta abu daban take faɗamin gameda itah,kuma da sannu zan gwadata domin share tantamata. Shikuma goje aradu ko banyi masa komai ba dolene na ajiye masa Gargaɗi mai tsaurin gaske”
Shuru sukayi babu wanda ya tankama ballantana ya bata yawun bakinsa.
Washagari da safe Bombee ta tashi da ƙarfin jikinta ba kaman jiyan ba,saboda magungunan da take sha akan lokaci.Ranar bata fita taje ko ina ba.
Da daddare bayan anyi isha inno ta shiryah domin zuwa sanarwa innarta labarin ganin Bombee.
Bata hanata yin hakan ba saboda itama tanason kar innar tata tashiga damuwa sosai na rashinta.
Tare suka fita da inno har zuwa ƙofar gidannsu kafin tajirata tashiga tafito.
Duk wanda zai shige tana daga zaune tana kallonsa,harda mahaifinta wanda yadawo daga masallci. Ƙureshi tayi da ido har yashige gidan.
Tunawa tayi da idan yadawo daga isha a irin daidai wanann lokacin yake sake niyamata karatu,sannan suci abincin dare tareda.
Runtse ido tayi tareda saurin kawar da tunanin hakan a ranta,dan a ganin ta bashida amfani a wajen yanzu ba,domin ba komai zai ƙaramata ba sai baƙin ciki.

A zaune suke a bakin ruwa inda suka saba zama kullum,dan tun bayan abinda yafaru da ita,bata koma gidaba yau sati guda kenan.
Haidar ne ya kalli Bombee tareda cewa.
“Yanzu kam kin samu sauƙi sosai koh,dan Allah kidaina yawan biyewa mutane,wanda yanuna baya ƙaunarki ki ƙaurace masa kawai shiyafi,bakiyi tashin hankali dashi,ki tuna koma mai zai faru kefah macece”
“Bakaine nafari wajen faɗamin haka ba,sanin ni macece yasan ma nakeyin hakan,duk rintsi bazan bari wani yaci mutuncina yanda yake so ba,sannan duk wanda yayimin abu naji bazan iya bariba to saina rama ”
“Oh mai yayi zafi ni bance kada ki rama ba,kawai dai ina faɗamikine saboda jibi zan bar garinku ba,wanda nasan banida tabbacin sake haɗuwa dake nan gaba”
“Hmm kuma wannan shine maganar bankwanar dazaka min,maizai hana kacemin duk wanda yayi miki ki rama.
Jiya danaje gidnasu na kula Abba naso kazama soja,a haka zaka zama da wannan zuciyar?”
Dariyah haidar yayi tareda cewa.
“Hhhh shiyasa fah inaga jininku yazo ɗaya da Abbanmu saboda kinada zafin zuciyane wanda ake so a wajen sojoji.
Yanzu ya maganar tsohon mijinki,i hope zaki barshi ya wuce koh?”
“Babu wannan maganar,yau zanje izuwa gareshi kuwa da daddare”
Zaro ido haidar yayi daga nan bai sake cewa komai ba.

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤30🖤

Sauri take tayi cikin duhun dare,da alama fitsarine ya kamata sosai.
Tazo daidai hanyar shiga banɗakin taga alamar wulagawar mutum a sashen goje.
Ƙiftawa ido tayi tasake ƙiftawa,dan zaton ko aljani tagani,saidai kuma ta kawar ta hakan a ranta ta wuce banɗakin.
Bayan tafito harta nufi ɗakinsu saikuma tashi alamar motsi a sashen kumadu.
“To waye ne yashige sashen goje,shekara biyu kenan yadaina kawo mata,tunda kowa yasan babu abinda zai iya yi musu,to waye kuma a sashennasa?”
Harzata shiga ɗakin kuma wata zuciyar tace baritaje ta duba tagani.
A hankali cikin sanɗa ta nufi sashennasa har ta samu shiga.
Kofar abuɗe take,hakanne yasake tabbatar mata cewar akwai mutum a cikin ɗakin.
A baƙin kofar ta tsayah tana shirin leƙawa,bata ankara ba sai ganin mutum tayi yafito daga ɗakin da sauri cikin baƙaƙen kaya.
Shima bai kulada indo a wajenba dan haka sai suka yi karo tareda faɗuwa a tare.
Mayafin fuskar mutumin indo takama saboda karta faɗi,aikuwa tajawoshi zuwa hannunta.
Hasken farin watane yasakata gane waye a gabanta.
“Bombee!!!!?”
Tafada cikin sanyin murya haɗe da razani kuma.
“Shiitttt tace tareda shaƙe wuyan indon. “Eh nice,kuma naji labarin kinganni a gidannan zakiga yanda zan miki ehe”
Taƙarisa maganar tana boye wukar datake hannunta duk jini a jikinta.
Tsallaketa tayi ta fita daga gidan da sauri,indo na nan zaune a wajen bata samu damar tashi ba har kusan Assalatu,dan tsoro takema karta tashi Bombee tadawo tasake yimata wani gargaɗin.
Ita kuwa tana fita daga gidan jeji ta nufah gidan su inno.
Har tazo shiga ɗaki taji uwaisu yana cewa.
“Ke Bombee daga ina kike da tsohon darennan,keda ba lafiya ce take ba sosai?”
Mayafin data rufe fusakarta haɗe da sukar ta boye a bayanta tareda cemasa,
“Bakomai baffah,kawai kawai wani ɗan abu nayi a jeji”
“To shikenan,amma jejinnan fah ki kiyayeshi Bombee”
“Tamm”
Daga haka ta wuce ɗakinta,bukkar datake gefen tasu.
Jijjigata taji anayi.
A hankali ta buɗe idonta tana kallon inno dakuma uwaisu a kanta,idanuwansu ɗauke da tashin hankali.
“Ke Bombee jiya ina kikaje da daddare dana ganki”
Shuru tayi bata basu amsaba,sai daga baya kuma tabuɗe baki a hankali tace……
“Uhm gidan su goje naje”
“Mekikayi masa a gidansu da tsohon dare”
“Uhm…uhm..”
Tana cikin inyinar ne goje nuna mata wuƙarta da kuma mayafinta na jiyah,wanda tana zuwa kwanciya tayi bata tsayah wanketa ba.
“Bombee na riƙeki tamkar ƴa ta,inda wani ne yazo yafaɗamin abinda kikayi,ba wai nina gani da idona ba,bazan taba yarda ba,Bombee kisa kisa fah kikayi,ina zakije da ran dayah rataya a kanki yanzu.
Duk wani rashin jikinki haka naji nagani na ɗauka,saboda nasan yarinta ce watarana zaki daina,amma kisa Bombee bazan iya rufemiki ba,inna faɗamiki zan taimakeki akai nayi ƙaryah”
Shuru Bombee tayi tanajin mai yake faɗa,runtse idanuwanta tayi da alama tatafi cikin wani tunanin.
“Yanzu bazancen bata lokacin bane,Bombee yakamata ki fita daga gidannnan ki buya wani wajen,domin indo tasanarwa ƴan sanda taganki kin fito daga ɗakin goje da tsakar dare,ɗauke da wuƙa mai jini.
An bazama ko ina ana nemanki tun safe,nan ma ba wajen buya bane zasu iya zuwa,domin gidanku sunsan kina nan wajen.
Dan Mlm ma yace gidanku sunce kina nan wajen,nasan bazai wuce innarki ba,dan ita kaɗai tasan inda kike”
Tasho Bombee tayi cikin sanyin jiki ta yafa gyale akanta,wuƙar tata dake gefen Uwaisu ta ɗauka ta saƙala a kunkuminta.
Bakin ƙofa ta nufah kafin tayi magana cikin sanyin rai.
“Nagode da hidimarku a rayuwata,haƙiƙa a yanzu nakai matakin da bazan kusanci masoyana ba,saboda suma bazasu iya tsira daga kaidina ba.
Ni makashiya ce yanzu a idon kowa,dan haka wanda yarabeni ma za’a fara ganin sa a matsayin hakan.
Nizan tafi sai wata rana”
“Ina zaki tafi yanzu”
“Inno ta faɗa cikin raunin murya”
“Can da nisa,inda nima bansani ba,amma zanyi iya koƙarina wajen ƙauracewa nan wajen”
Daga haka tasaka kai tafita a cikin gidan.
Saida tayi gudu mai nisa kafin tajuyo ta kalli gidan da yake ɗauke da rabin yarintarta,motar ƴan sanda taga ta nufo gidan,hakanne yasa ta tabbatar da maganar baffannata,kuma bazata ga laifinsu ba gameda furucinsu gareta,ta cancanci fiyeda hakan ma a gun kowa.
Cikin dajin ta nausa ta gudu,ko ganin gabanta batayi sosai,har saida takai gejin iya yanda jikinta zai iya ɗauka.
Gari ko ina ya ɗauka cewar Bombee takashe goje har cikin ɗakinsa,dan da safe ana zuwa aka sameshi anyi masa yankan rago a wuyah.
Bayan an ɗaɗɗaureshi da igiyah anyi masa duka.
Abu wasa wasa yakai ga ko ina labari ya watsu,Bombee kuwa anyi neman duniyar nan babu ita babu labarinta,ta bace battt kaman bata duniyar.
Mlm Ahmadu tunda yashigo da safe bayan labarin ya riskeshi yake cikin ɗakinsa,ko fitowa bayyi ba ballantana yace wani abun.
Danejo ce ta tashiga ɗakinnasa,yana zaune akan dadduma yayi shuru.
“Sannu mlm,baka ce komai ba shin anganta ne”
“Hmmm ina za’a ganta,ni ina kyautata zaton ma yanzu haka bata garinnan,domin bayan yanka shi datayi,wai hadda kuɗi ta ɗiba maƙudai a cikin ɗakinnasa,kinga kuwa mai zata zauna tayi a garinnan”
“Kuɗi?…..hadda sata kenan aka a ɗakinnasa?”
“To yanzu ai ba ta sata ake ba,ta kisan da akayi ake,wama yake ta wani kuɗi yanzu”
Shuru Danejo tayi tana maimaita ɗiban kuɗin a ranta,saidai bata ce komai kawai ta tashi tabar ɗakin.
Yanayin damuwar data shiga da ita ɗakin taragu daga kaso Ɗari zuwa kusan kashi talatin,dan tunda taji zancen hadda sata tasakawa maganar ayar tambaya.
Taga haka bata sake bi takan zancen ba ta nufi ɗakinta.
Saida Bombee tabari dare yayi kafin ta fito daga maboyarta.
Babban hijabi ta zunduma har ƙasa haɗeda nikaf.
Hanyar cikin garin ta nufah domin gani mai yake wakana.
Can nesa da ƙofar gidansu ta tsayah,yara sunata wasan dare.
Ahhh kaman hakan bai faruba a rayuwarta,saidai ta sabanin farincikin da sukeyi itakuma cikin baƙin ciki take. Koyaushe saidai ace mata zai wuce,bata taba tunanin dagaske bane sai yanzun daya wuce tagani.
Wani yaro da ƙira yazo wuce ta gefentada kwano a hannunsa.
“Kai dan Allah ɗan zo na aikeka gidan can mana”
Zuwa yayi ya tsayah a gabanta,wata takarda ta fitar a nannaɗe a cikin hijabinta tabashi.
“Ka shiga gidan ka tambayi wacece Danejo,sannan sai ka bata,karka bawa kowa sai ita kaɗai”
Ɗaga kai yayi alamar yaji,daga nan yashiga gidan.
Jimm tatsaya tayi domin jiran fitowar dan aikan,bata ga ɗan aikaba shuru har na wani lokaci.
Wasu mutane tagani samari guda uku suna iyo hanyar da take,sannan kuma da yaron a bayansu yana yi musu magana.
Dan murmushi Bombee tayi ganin sakarcin da suke nuna mata,a zotonsu shin wayo suke mata zasu kamata,da alama labarin tana kallo da daddare bai gama karaɗe garin ba.
Saurin juyawa tayi tana tafiyah da sauri sauri tanufi jeji,suma suka bita a baya.
Sun danyi tafiyah mai nisa,dan zuwa yanda gudu suke itada dasu na tafiya.
Da alama ga wanda zata bawa saƙon subawa mutanen gari,ta faɗa a ranta.
Su su biyar ne,kasancewar darene kuma basanin hanyar wajen sukayi ba,nan da nan tayi nasarar rarrabasu a jejin.
Bayan wani ta dawo yana dube dube ta kifa masa naushi a kusan wuyansa,hakanne yasa ta jube yana dafe wajen.
“Kayi haƙuri da dukan danayi maka zaka warke,ni zan tafi daga garinnan,ina so kaje ka sanarwa gari bai ƙare iya nan ba ina nan dawowa watarana”
Daga haka tayi saurin barin wajen kafin abokanannasa su tarar da ita.
Hanyar gidan su haidar ta nufah,ta zauna a can nesa da gidan,tana jiran wani a cikin gidan ya fito,amma shuru har bacci ya ɗauketa a wajen.
Ba ita tafarka ba har saida alfijir ya keto.
Mahaifinsu Janar Muhammad Bello tagani ya fito daga gidan ɗauke da wani abu kaman drawer,a wajen motarsu ya ajiyeshi inda wasu kaya suke,da alama tafiyar zasuyi kenan.
A cikin booth ɗin motar yasaka inda wasu kayan suke,dayake Helux ce tanada ishashshen wajen ɗinban wasu kayan.
Duk abinda yake Bombee tana kallonsa har yagama ya koma cikin gidan.
Lallabowa tayi har zuwa bakin motar.
Idan tashiga motar nan zata samu damar barin garinnan batareda matsala ba,kuma dama batasan hanyar dazata bi ta tafi ba.
Cikin booth din motar da tsilliga tareda shiga ƙasan drawer daya saka a cikin motar.
Tana gama shiga kuwa haidar yazo da wata jaka ya ɗora a saman,yanda yayi mata sauƙi wajen buyar batareda gajiyah ba.
Sauƙe ajiyar zuciya tayi tareda fatan Allah yasa hakan da tayi shine daidai kuma mafita kaɗai a gareta.
Muryar haidar taji yana cewa.
“Bombee??me kike a cikin mota kuma,hakan ma a drawer,tsawon wannne lokacin kike ciki?”
Saurin buɗe idanuwanta tayi ganin hasken rana akanta,ga kanta wanda yakeyimata azabar ciwo,saboda gangarar dataji anayi a hanyar tafiyar har yasakata yin suman wahala.
Bata iyah buɗe baki tasake yimasa magana ba tafara komawa wata sumar,saidai taji muryar Hajiya Zulaiha tana cewa.
“Abban haidar kawai kashiga da ita cikin jirgin,bamusan mai yasa ta zabi biyomuba amma tabbas akwai dalili,kuma a yanayinta yanzu tana buƙatar hutu,mu kammu mun jijjaga da hanyarnan inaga ita”
Tana gama jin maganar taji an ɗagata ciɗak zuwa cikin jirgin.

__________DAWOWA WAJEN SU HAJIYA ZEENAH__________

Tunda aka tafi bada labarin,hajiya zeenah tareda idi masu yi wani kyakykyawan motsiba har aka gama.
“To wannan shine labarin rayuwar Bombee a garinnan tundaga tashinta,kuma itace wacce kuke nema,duk da bansan mai yasa kuke neman ta ba,amma wancan tana yarinya ne kukaji”
“Kan buuuuu Hajiya Inaga mukoma ki huta gobe mu ɗau hanyar gida kawai”
“Iliyah yafada yana dauƙe ajiyar zuciya”
“Ahah Muruje to ina kuma labarinta a wajen su Hajiya Zulaiha ɗin,sannan kuma ya akayi ta dawo garinnan har kacemana tana cikin garinnan?

Todai nasan kuma zakuso ku sani koh?????😂😂😂

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤31🖤

“Uhm karki ce mai yasa na tambayeki,amma menene haka kike nema a wajen wannan yarinyar,abinfah ya wuce yanda kike zato.
Bayan bacewarta daga garinnan komai yafara tafiyah normal,saidai kuma mahaifiyar ta inna Danejo bata manta da batan ƴar ta ba,dakuma mummunan zagin da ake binta dashi. Hakanne yasa abin yafara damunta da kaɗan kaɗan,ga kuma dama ciki mai wahalarwa.
Ba a tashi sanin mai ya faru ba har saida tazo haihuwa matsala ta tashi gadan gadan. A nanne mlm Ahmadu ya kaita asibiti amma tagagara haihuwa,dole sai dawowa gida sukayi,dan su inna laari sun matsa kan ayi na gida mana.
An fara na gidan,a daren ta haifi ɗa namiji wanda dama ya daɗe da mutuwa a cikimta,dan har hakan ya shafi mahaifarta itama tabiyo ɗan tare.
Jinya tafarayi duk da bayan rashin ɗan.
Koyaushe tana ɗaki komai sai anyimata na taimakawa.
Sai bayan wani lokaci abin yaƙi mlm Ahmadu ya maidata asibiti shida inna laari,a nanne aka tabbatar masa da cewar ta kamu da matsanancin hawan jini.
Wanda shiya taba mata ƙwalkwalwa da kuma idanuwanta,wanda sanadiyyar kullum da zurawa waje ɗaya babi ƙiftawa har suka mutu suka daina gani.
Magana kuwa duk abinda za’a faɗa babu wanda zata amsa,shima duk yanada nasaba da ciwon daya sameta”
Lokacin da muruje yafaɗawa su Hajiya zeenah matsalar Danejo haƙiƙa sun tausaya mata,kuma daman sun ganta a hakan ai lokacin da suka shiga gidan.
“Wai amma tayi tsawon rai,hawan jini yayi mata wannan cin amma tana raye?”
Hajiya zeenah ta faɗa cikeda mamaki.
“Shekara uku kenan data samu lalurar,dan tadaɗe tana jinyah kafim hakan yasameta,kuma har yanzu ana yimata maganin gargajiya dana asibitin”
“To ya Bombee kuma tayi data dawo taga yanda innarta ta koma,sannan yaushe ta dawo”
“Hmmm Bombee fah watan ta kwata kwata biyu da dawowa garinnan da zama, dan da zuwa tayi ta koma a cikin mission ɗin aiki, shima kuma daman ba’a gidansu take zaune ba,dan mlm Ahmadu yace badai gidansa ba,farkon dawowar a gida ta sauƙa,wani abu da tayi masane yace bazata zauna a gidansa ba.
“Mai tayi masa?”
Hajiya zeenah ta faɗa cikim zaƙuwa.
“Ummm bayan dawowarta garinnan tayi taimako ɗayah amma kuma tayi lahani shima.
Zuwan ta ne takafah ƙungiyar Black blood,wanda tayita da taimakon wasu mutanenta fararen fata guda biyu da kuma masu baƙar fata guda uku,dukkansu kuma matane masu jarabar ƙarfi.
Duk wanda yashiga ƙungiyar zai dunga yin tuƙin hawan mambila,ita kuma in yana wajenta babu wani ɗan fashin dazai tareshi a hanya,da sharaɗin zai kaimata kuɗin ta itakuma duk wata.
Matasa ƴan iskan gari da sukaji haka tuni suka shiga,aka basu training ɗin tuƙi na musamman,ga kuma yanda take basu lasisin yin abinda suka ga dama,indai ba gonarta suka shiga ba,nan da nan tafi uwarsu ma muhimmanci a zuƙatansu.
Ta gina wani gida a can cikin duhuwar daji,inda take masa laƙabi da yankinta kuma fadarta,saidai har sannan bata komaba”
“Meyasa to ta ginashi idan ba shiga zatayi ba”
“Zuwan ta shekara biyu baya kafin ta ginashi a gidansu ta zauna,wanda dama wannan ba zuwa tayi zaman dindin ba.Tazone kaman gida daga aiki,wanda aka turo ta garin tareda wasu sojojin. A lokacinne ma tafara kafah kungiyar dana baku labari a bayah”
“Eh munji labarin wannan kungiyar muma shigowar mu cikin garin a bakin wani mutumi toro”
“Hakane tana da mutane masu tarin yawa a ƙarkashinta”
“Dawowarta zaman dindin shine ko dariyah bata fiye yiba,sannan kuma bakowa ne yake kallonta ba saida gaske,ita kaɗai ta dawo daga ita sai wata matsashiyar budurwa kaman sa’arta,sannan yanayinta batayi kamada ƴar ƙasar nan ba.
A lokacin ko sunan sojiji batason a anbata a kusada ita,bamusan dalilin ba,wata biyu kenan da faruwar hakan.

______***DAWOWAR BOMBEE GEMBU***_____

Shaƙar iska tayi a bakin ƙofar shigowa garin daga cikin baƙar motarta ƙirar daraja😀.
Hakan dataga bayyi mata ba fitowa tayi daga cikin motar ta tsayah tana kallon wani dutse dayake gabanta,wanda yayi kore sharr dashi. Idonta a rufe tajiyo muryar HILYAAAN daga cikin mota tanayi mata magana da hausarta da bata gama iyawa ba.
“Anty Maryam (Bombee),shin zan sanarda su Zeezah da Khamees shigowarki ne?”
“Ahah kyalesu ba fadata zan tafiba tukunna,zanje gidane,sai an koroni saina tafi nawa gidan da dalili”
“Kaman ya ban gane ba,sai an koroki kuma,ai gidanku a cikin garinnan da waccer shekarar mukaje?”
“Eh shifah can zan tafi in sun koremu saimu shige can ɗin,karki faɗamusu zuwana,duk da nasan inashiga garin zasusan isowata,inasone naje naga wanne aiki sukayimin a wajen,sannan wannene kuma a cikin dajin ya tsallake umarnina,uhhhhh kinsan inason naga mutum yayimin kuskure,na matsu naje naga wannne irin gini sukayimin.
Saidai nafison naje naga ya fuskar tsofin can zatayi idan suka ga mai zan kai musu hhhhhh”
“Toh shikenan,ya labarin wannan matar kuma dakikace zakiyi maganinta,koba yanzu bane lokacin?”
“Ba yanzu bane lokacin,sai nan da zuwa wani lokaci kaɗan………..ina baby boy ɗina yayi bacci yanzu ko har yanzu bai koma baccin ba?”
Juyawa Hilyaan tayi bayan motar inda kyakykyawan jaririn yake kwance yana zuba baccinsa hankali kwance.
“Yayi bacci,saidai kinsan jikinsa yayiwa wajennan kaɗan,satinsa fah biyu,kema kuma bakisha maganinki bah na 4:00 pm.”
“Mtsww nagaji da wannan maganin wlh,jiri yake sakani sannan kuma yana ƙaramin yawan jin yunwa”
“Uh ai dole kisha tunda wannan kika zaba,babu yanda dr Na’im bayyi ba wajen karkiyi zirga zirga amma kinƙi ji”
Dawowa motar Bombee tayi tashiga,kafin Hilyaan ta tuƙa motar zuwa cikin garin.
Tun a nesa da bakin kofar gidan Hilyaan ta ajiye motar,tareda ɗakkowa jinjirin a showel dinsa tabiyo Bombee a baya,wacce har ta fara tafiyah zuwa cikin gidannansu.
Wani yarone yasha gabanta tareda cewa.
“Lahhh Bombee soja ta dawo ta dawo”
Cakk Bombee ta tsayah jin abinda yaron yafaɗa,hannunsa ta riko tareda juyashi kansa yana kallon ƙasa,yaran wajen ta kalla tareda cewa.
“Wani ya ƙiramin uban yaronnna lo uwarsa yanzu nna”
Da gudu kuwa labari ya iske larai saigata ta fito,dan jikanta ne ɗan ƴar ta wanda yake wajenta.
“Ke wane shegene zai kashemin jikan……..”
Kirifff taja bakinta ganin Bombee ta ɗaga yaro yana wutsil wutsilll.
“Ohh ashe kece kika dawo,dan Allah meya miki haka yaro dashi”
“Tambaya ma kike mai yayimin,amma a sanina kinsan halina,bana tsallakewa daga ƙarami har babba koh. Ƙirana yayi da wancan sunan,wanda yanzu na tsaneshi fiyeda mutuwata……..misali zanyi akan sa kowa yagani,idan na kuskura naji wani yakirani da wancan sunan uwarsa ta haifi wani a garinnna kowaye shi kuwa”
Taugunnawa larai tayi tana roqon Bombee,amma haka tayi mursisi tasaki yaron yafaɗo takayi,larai dama tana ganin idon Bombee ta saita faɗowar sa,dan haka da sauri tayi kifiyah ta cafeshi a hannunta,jikinta har rawa yake saboda tsoron Bombee da kuma tashin hankalin data gani.
Dauke kai tayi tashiga gidannansu,wanda kafin sannan har labarin isowarta cikin garin da abinda tayi ya zagaya a bakin magulmata,kuma daman takeso.
Yanzu zuciyarta tayi baƙi ta dafe,batajin ƙwarin gwiwa sai mutane suna yaɗa abinda ta aikata,tun gulma tanayi mata tabo har tazamo maganinta nasha a yanzu.
Ko sallama batayi ba tasaka kai cikin gidan,bata samu kowa ba dan haka ta wuce ƙofar ɗakin innarta.
A zaune take akan kujerarta ta zubawa gabas ido.
Bombee ta daɗe a bakin ƙofar ɗakinnata tana kallonta batareda tace komai ba.
Muryar inna laari ta jiyo tafito daga ɗakin girki,da alama abinci dare takeyi,dan laasar tayi sosai.
“Wanake gani a ciki gidannan yau mun shiga uku”
“Ba tara ba iya uku kika shiga laari,niɗince dai ganinan da raina ina shaƙar iska”
Tafaɗa tana jan iskar da ƙarfi,tareda yin wani dan banzan murmushi.
“To komai kikazo dashi ma munfi ƙarfinki,ta allah bataki ba,tun wurima kizo ki fice daga gidannan”
“Saboda gidan ubanki nake ciki,saiki bari mai gidan yazo ya koreni da kansa,hhhh kika ce wai kin fi ƙarfin abinda nazo dashi,wannan kuma zancene,abinda na zo dashi baki tabayi ba laari,saboda nafiki iya shege ta wata sigar,duk da nasan ta wani gun kinfi gaban kwatance,saboda keɗin kurace da fatar akuya kike zaune a garke”
Zaro ido inna laari tayi baki sake tana kallon Bombee,anya kuwa bata shaye shaye take gaya mata wannan maganganun.
“Bombee kekuwa ɗiyar arziƙice,karki manta fah innarki tana jinki kike wannan maganganun”
“Saime dan tanaji,tunda bazata iya hanani ba kuma bazata ganni ba ina amfani jin toh,keda kike ji dake nake”
Yaron dayake hannun Hilyaan ne yafara kuka da alama ya tashi.
“Ohh laari bani kujera zan zauna na shayar da jaririna mana”
Bata ɗauki maganar Bombee da wasa ba dan haka ta gara mata kujerar cikin gatse dan a tunaninta Bombee duk iya shegenta ne.
Ga mamakin ta kuwa ta zauna a tsakar gidan babu ko kunyah a ƙarkashin inuwar bishiyar gidan tafara bashi mama,bayan ta ɗan ɗage gyalen dayake wuyanta.
Zaro ido inna laari tayi tareda cewa.
“Yau ni laari mai zangani,ƴar nan ɗan me nake gani haka”
“Ɗana ne mana,mata mazace ni danna haihu kike mamaki,shikenan mutum bazai iya haihuwa ba,ko ke kaɗai ce mace kai. Zaki wani tambayi tayaya,ta yanda mlm Ahmadu yayi miki cikin Innayi mana,nima ta haka nayi cikin nawa ɗan tareda wani daga cikin mazajena”
Mari inna laari takaiwa Bombee cikin zafin nama,jin abinda Bombee take fadamata,wanda ko kare bazai ciba.
Saurin riƙe hannunnata Bombee tayi tareda wullata can gefe tafaɗa cikin kwatar dake wajen wanke wanke.
Tashi tayi daƙyar saboda yanda kwankwasonta yabugu,daidai lokacin tana ɗagowa ta hangi mlm Ahmadu wanda yake tsaye yana kallon su.
Kuka inna laari tasaka tareda fitowa daga wajen.
Hanyar ɗakinta tayi tareda cewa.
“Mlm barin na tattara kayana natafi garinmu nikam,kishiya bata fiddani ba,amma wannan ƴa kam bazan iya da ita ba dam annoba ce”
“Ina zaki laari,duk naji munanan kalaman data faɗa,basai an maimaitamin ba,miye na tafiya tunda bada ita na gina gidan ba ai yanzu zata barshi basai anjimaba.
Kizo ki fitamin a gida na sallamaki,sannan abinda kika zo nunamin naganshi na kuma gode,bana son duk abinda zai tunamin ke daga yau”
Wani murmushi Bombee tayi mai dauke da ma’anoni kala kala.
“Har zan wuce gidana na tuna cewar karka bar gida har sai an koreka,shiyasa nazo a koreni na tafi fa dalili,amma kafin sanann bari ɗana ya ƙoshi tukunna.
Kayi haƙuri baba da naso yimaka mai suna,sai kuma nasaka masa sunan…….kodayake shikenan dai”
Tafaɗa tana jan numfashi,a yanda take magana kaman ba ita ubannata yafaɗawa kalmomi masu girgiza duk wani ɗa ba,musamman ƴa mace.
Miƙewa tayi tareda miƙawa Hilyaan ɗanta Haidar,wanda take ƙira da young Haidar.
“Toh baba ni zan wuce saina shigo garin sainaxo mu gaisa,Laari karki manta fah wasa tsakanina dake bai soma ba tukunna…..sai wani jiƙon”
Duk maganar datake mlm Ahmadu bai cemata kanzill ba dan takaici,mai zaice mata da wannan maganar,shi bai taba ganin wannan iftila’i ba a rayuwarsa,idan wani yace masa Bombee zata zama haka zai iya buga ƙasa yace bai yarda ba.
Daga haka tafita daga cikin gidan cikin izza da ƙasaita.

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤32🖤

Hamma Hajiya zeenah tayi tareda kallon muruje wanda yakai karshen labarin dayake basun.
Kuɗi ta ciro daga cikin purse ɗinta ta miƙamasa tareda yimasa godiyah.
“Mun gode da wannan labarin daka bamu,koba komai yanzu munsan mai yake wakana,mu bari mutafi gida,yamma tayi bazamu hau cikin jejin yanzu ba”
Zaro ido muruje yayi tareda cewa.
“Hajiyah wai har yanzu baki haƙura da zuwa wajenta ba,bazan tambayi mai kike nema ba a wajenta,nagode ni bari na tafi”
Fita muruje yayi daga cikin motar yakama gabansa,yabar su Hajiya zeenah cikin nazari.
Iliyah ne yakalli Hajiya zeenah tareda cewa.
“Hajiya gaskiyar wannan ɗan yaron fah,kinaga bazamu hakura dazuwa wajenta ba kuwa,ni aradu bana fatan ma nahaɗa hanya da ita tunda naji labarinta,batayi kama da wacce wani zai haɗa hanya da itah,kinaji fah ko iyayenta ma ba a bakin komai duke ba a wajenta”
“Kai rufemin baki,dama kaine kasakani zuwa wajennan komai,rashin mutuncinta danaji dama shiyasaka nazo nemanta,dan naji labarin hakan bashine zaisa na janye daga kuɗirina ba,saidai idan itace da kanta taƙi amincewa da buƙatata”
Daga haka iliyah bai sake cewa komai ba yaja motar suka bar anguwar su Bombee zuwa gidan su Iyani.
A hanyar sune ta dawowa Hajiya zeenah ta kira Jabeer.
Yana zaune sun gama hayaniya da lubna idonsa a rufe ya jiyo ƙarar wayar.
Da kaman bazai duba ba saikuma yaga an rubuta “Mommah”
Sallama yayi,tun kafin ta amsa sallamar tafara faɗamasa dalilin ƙiran.
“Jabeer shin private plane yana nan kuwa?”
“Ehh yana nan hajiya,ban fita ko ina na ina nigeria”
“Toh karka fita dashi nan da sati,dan zan kiraka a cikin satinnan azo a ɗaukeni a Gembu”
“Gembu kuma,dama can kikaje,wajen wa kenan?”
“Uhmm naje yin wani abune wanda zai taimaki rayuwarka,Aure zan yimaka wanda sandiyyarsa zaka rabu da wannan jarababbiyar matar taka,sannan idan nadawo ma zamuyi magana.
Zaka koma ainihin Side dinka na gidan,zaka barwa su Abdulmaleek wajensu”
“Amma Hajiya naga basu tashi aure ba,sannan kuma wancan side din ya fiye girma dayawa sannan yayi ciki kaɗan,sannan………”
“Sannan me Jabeer bazanyi abinda zai cutar da rayuwarka ba,yarinyar nan baka buƙatar sakata cikin rayuwarka,zatazo ne domin kawar da lubna a rayuwarka.
Bangama tsaida abun ba tukunna,zai iya yiyuwa a fasa,yansu dai jirgin nafi buƙata a ready idan zan dawo,dan bazan sake bin wannan hanyar ba karna mutu.
Komai yafaru zan ƙiraka ko abbanka gobe”
Tana gama faɗin hakan ta kashe wayar.
Ɗan murmushi yayi yana kallon sunanta a gaban wayar tasa,yayinda cikin ransa kuma yacika da matuƙar kaɗuwar jin abinda mahaifiyar tasa take shirin yi.
“Hmmm dama kina tsoron mutuwane Ummah….kai Allah ya kyauta.
Daga nan side ɗinsu yawuce wajen abbansa,saboda ƙarajin labarin a wajen,dan yasan bazai rasa sanin mai yake wakana ba.

______*****______

Biron dayake hannunsa ya ajiye,ganin yayi kusan minti talatin amma yagagara yin signing ɗin da bazai daukeshi sakanni ba,saboda yawan tunani dayake fama dashi a kodayaushe.
Ƙarar bugun kofar da akayi ne yasashi jefar da biron akan paper tareda jan ɗan ƙaramin tsaki.
“Banda kaima kasake ɗoramin wani tension din,a tunanina dai baka buƙatar saina cemaka ka shigo koh?”
Cikin kasala yayi maganar kamar shima buɗe bakin aikine a gareshi.
Khaleel ne ya buɗe ƙofar ya shigo yana murmushi,akan kujerar datake kallon table ɗin Jabeer ya zauna.
“Mai ya farune mutumina,yanzu kullum haka ake ganinka,yakamata fah kaga likita idan wani abune yake damunka,An tafi wata uku da mutuwar Hafsa amma kaƙi barin lamarin a cikin ranka”
Ya mutsa sumar kansa yayi tareda fesar ɗa iska,dan jijjiga kai yayi alamar shima kannasa ciwo yake yi masa.
“Hmmm Khaleel ba iya wannan ne matsalata ba,inaga Hajiya so take takasheni tun kwanana bai ƙara ba,nifah inaga bata kallona mutum,tafi tunanin ni robot ne”
Ƴar dariyah Khaleel yayi jin furucin abokinnasa,wanda bazai ga laifinsa ba akan maganar kam,dan ko mahaukaci ya kalli Jabeer yasan yana cikin yanayi na buƙatar hutu ba kaɗan ba,sannam kuma yanada buƙatar wanda zai kwantar masa da hankali.
“Menene yafaru kake wannan furucin Jabeer,komai zai faru kasan Hajiya mahaifiyar kace,sannan kuma kasan bata nufin ka mutu ta kowacce siga”
“Hmm baxaka gane bane,kasan yanzu zancen danake maka kwananta uku kenan bata gida,wai tatafi yimin aure a can gembu,ka duba yanayin danake ciki ban gama warwarewa da mutuwar matata ba,ga ita wancar har yanzu nagagara jin daɗinta dama,yanzu kuma ta tafi can uwa duniyah zata auromin wata,wadda ni bansan ma ita mai zan tarar a gareta ba.
Kuma wani abin tashin hankali ma Khaleel,auro waccar ɗin fah dan na auri Jawaheer ne fah?”
Zaro ido Khaleel yayi jin abinda Jabeer yafaɗamasa.
“Jawaheer kuma,ehh nasan yarinyar tana sonka kam,amma banyi zaton dagaske abin yake ba”
Ƴar dariyar takaici yayi kafin yaƙara da cewar.
“Khaleel kenan,to tunda aka haifi Jawaheer Hajiya rabi tabani ita,rashin aurenta da banyi ba saboda suna tsoron kar lubna tayi mata illah ne,yanzu kuma idan suka auramin wata anan zasu samu hanyar yanda zasu saka Jawaheer a gidana”
“Tohh gaskiya abinkan ba ƙarami bane,toh amma kai taya kasan hakan dukka”
“Jiya ta ƙirani take faɗamin wai na shirya jirgi za’aje dakko ta a gembu.
Abin yabani mamaki,akan mai takeyi a gembu,nan take faɗamin wai aure taje yimin,kaji fah irin wannan zancen Khaleel,dan ta sameni mai yimata biyayya akan buƙatarta,bai kamata kuma ta dunga yin biriss da abinda zuciyata keso ba”
“Eh to hakane,amma kuma kacigaba da haƙuri,inshaaallah biyayyar dakake mata ma bazai bari ka dawwama a cikin wannan halin ba,inshaaallah allah zai kawo maka mafita”
“Ba wannan ba ma Khaleel,karka manta bafah iya anan abin zai kareba idan ta kawo wannan. Duk neman mafita ne na yanda Jawaheer zata zauna a gidana,nakasa cire tunaninnan a raina tun daren jiyah”
“To a ina duk kaji wannan ne,zai iya yiyuwa ita Hajiya kawai Lubnah ce bataso a cikin rayuwarka,ka rabu da itamana kawai,ni inaga Jawaheer ɗin ma tafi maka lubanan”
“Inda zan iyah sakin Lubnah da tuni na rabata da rayuwata kodan saboda sabanin danake samu da dangina akanta,amma abin ya ci tura duk iya koƙarin danayi. Hmmm Jawaheer din ma dakake gani ba kanwar lasa bace wajen rashin daɗin zama,tsawon rayuwarta ba’a cemata tayi tayi,taya kake gani zan sakata abu tayi,ko kuma zatayi wani abun amatsayinta na matar gida. Sai uwa uba ita wacce ake shirin mannamin banma santa ba kwata kwata”
“Uhmm kaman kace Hajiya tafaɗamaka zaka koma Ainihin side ɗinka,meyasa kenan”
“Baka san meyasa ba,saboda yana babbane yana ɗauke da Side guda huɗu,tana shirin yimin tanadin zama da mata uku,shiyasa ta buƙaci nakoma can”
“Mashaallah nabaka wata shawara mana?”
“Hmmm wacce shawara ce zatayi maganin wannan abin dayake shirin tunkaroni a yanzu”
“Mezai hana tunda kace side ɗin na ɗauke da bangare huɗu,kuma mata uku take son saka zama dasu. Kaikuma saika auro kamilar yarinyar mai addini da nutsuwa wacce tasamu tarbiyya ka aura,kaga idan sun kunna maka wuta zaka samu wajen zuwa a kwantar maka da hankali”
“Hhhhhhh amma Khaleel yau na yarda kai mungune,ina koƙarin janye jikina daga wanann matan kaikuma kana shirin ƙaromin wani bala’in,kajanye wannan shawarar tun batayi nisa bama”
“Nizan tafi Jabeer Allah yakawo maka sauki akan lamarin nan,amma dai kayi tunani akan abinda na faɗamaka,inaga idan kasamu wata yarinya a rayuwarka kaman hafsa abin zaizo da sauƙi,koda wancan din suna nan”
“Hmmm naji abinda kace,yi sauri ka fita ka bani wajen Khaleel,nakula bazaka gane yanakeji ba”
Jijjiga kai Khaleel yayi ya fita a office din,cikeda tausayin abokinnasa wanda yagamu da Jarabawar mata a rayuwarsa.
“Nakaro aure bayan waɗannan……….kai wannan ba shawara bace ma,gwanda nacireta cikin raina kawai”
Daga haka shima ya tattara shirginsa ya bar companyn ma gabaɗaya,bai koma gidaba wata hanyar yakama zuwa wani wajen daban,wanda yake ɗaya daga cikin sirrinsa da yabarshi a iya saninsa kaɗai sai mahaliccinsa.

_____*****______****_____

A bangaren su hajiyah zeenah bayan sun karya suka fito daga cikin gidan su iyani.
Ƙaryah sukayiwa mahaifiyar iyani,dan idan tagane Daji zasu shiga inda gidan Bombee yake,koda wasa bazata barsu su shigaba.
Key iliyah yayi wa motar,amma kuma baisan ina zai dosaba daga haka.
“Hajiya ina zamu nufah daga nan”
“Meyasa kake tambaya ta,nima nasani,nansan kuma da wuyah a samu wanda zai rakamu wajen cikin garinnan”
“Ahh Hajiya ranar da muka shigo Toro yabamu number sa akan ko zamu koma zai maidamu”
“Mezamuyi da wannan yaron kuma yanzu,ko karen hauka ne yacijeni ai bazan yarda nasake gangarawa ta wanann hanyar ba”
“Ahah ba zancen komawar ba,gani nayi kaman fah yana daya daga cikim yaran Bombee,kin manta mai gace mana,cewar a jeji gidanta yake,kuma itace shugabar kungiyar su ta BB. Kaman yayi kama da labarin kungiyarta da Muruje ya bamu jiya”
“Ehh kuma fah hakane,iyani tayi gaskiya Hajiya”
“To danna ki ƙiraman shi,yafaɗamana inda take”
Fita iyani tayi daga motar tashiga gida dakko inda tarubuta number tasa.
Sakawa tayi tareda miƙawa iliya ya ƙirashi.
“Salam ina magana da toro ne?” mune mutanen da ka shigo dasu rannan,dan Allah muna tambaya ne akan inda shugabar ku take,muna son zuwane”
Bayan ɗan wani lokaci iliyah ya sauke wayar a kunnesa yana kallon hajiyar.
“Mai yace bazai faɗamana ba?””
“Ahah yace wai gashinna zuwa yana kusa danan wajen,amma fah da alama yanace wani abu zamuyi mata,bakya ganin bazaiyi shunen mu ba a wajenta”
“Haba dai wane irin shune kuma,tun kafin Hajiya zeenah tayi magana taji bakin bindiga yana zungurar ƙeyarta ta window mota……..

Tohhh fahh🤣🤣🤣🤣

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Page 🖤33🖤

Muryar wani mutum taji daga bayanta yana cewa.
“Ku shiga ciki ku ɗauresu,sannan ku zubaminsu a bayan mota,karku manta da ɗauremusu fuskokinsu”
“Okay toh”
Mutane guda biyune suka shigo motar tareda ɗaure musu hannayensu da igiyoyi,bakin kyalle aka saka a fuskokinsu,daga aka tasa ƙeyarsu zuwa cikin wata motar.
“Maza kai toro jawo motar tasu ku tafi,zamu miƙasune ga itah,sai sun faɗi dalilin dayasa suke nemanta,sannan kuma wanene ya aikosu”
Daga haka su Hajiya zeenah basu sakejin komai ba sai gungurawar motah.
Tafiyah akayi mai nisa dasu zuwa wani waje daban wanda basu samu damar sanin inane ba,sauƙa akayi daga motar aka fara zansu zuwa wata hanyar. Nan ma saida akayi tafiyah mai nisa kafin aka basu damar tsayawa.
Jikin su Hajiya zeenah banda rawa babu abinda yake,dan sun saddaƙar gidan yankan kai aka kawosu.
“Yau nashiga uku nakawo kaina kabarina da kaina”
Hajiya zeenah tadaɗa a hankali,muryah murdaɗɗen mutum taji yana cewa.
“Mun iso ku ciremusu ƙyallen fuskarsu”
Kafin ya rufe baki sukaji an fizge yadin dayake fuskarsu,kamar za’a rana kansu da gangar jikinsu.
A hankali suke saita hasken wajen da kuma ƙarfin idonsu,babu wani haske a wajen,saidai saboda yawan ƙofofi da wajen yakeda shi,kai tsaye mutum sai ƙarewa abinda yake wajen kallo.
Wani irin ɗakine mai girman gaske,babu abinda yake jikin bangon ɗakin sai hotunan mutane kala kala anayi musu azaba salo salo.
Wasu irin winduna ne a cikin ɗakin ƙanana kuma a can saman silin ɗin ɗakin.
Ga mutane masu baƙaƙen kaya guda kaman goma a gabansu sunyi cirko cirko.
Kallon ɗaya mutum zaiyiwa ɗakim hantar cikinsa ta kaɗa,dan kana samunka cikin ɗakin karon farko zakayi tunanin ba a duniyah kakeba.
Wani na daga cikin mutanen ya matso gabansu ɗauke da zarto a hannunsa babba.
Cikin kakkausar muryah yafara magana mai amsa amo.
“Shin bazaku faɗamin maiyasa kuke neman shugaba ba,ku faɗamin wanene ya aikoku yanzu nan,kafin na gundule kan tsohuwa”
Kunna abin hannunsa yayi yafara ƙara,wanda kowanne ƙara ke sake gusar da ɗan nutsuwar zuciyar dake jikin su Hajiya zeenah.
Cikin karfin hali da tattaro dukkan jarumtarta tayi magana,wanda take ganin ita kaɗaice zata ceceta a halin da take ciki.
“Bada niyyar cutarwa muke neman Bombee ba,saboda wani taimako dazatayiminne. Sannna babu wanda aikoni,buƙatata ce ta kawoni wajenta”
Tsayawa yayi cakk jin abinda Hajiya zeenah tafaɗamasa,
“Shin kozaki faɗamana dalilinnaki?”
“Zaifi kyau idan iya nida ita mukayi maganar,abin bai shafi wani abin cutarwa ba,inzaka iya ka haɗani da ita akan maganar”
Suna cikin hakanne wata farar matashiya tashigo wajen,
“Khamees ka tsayah da wannan abin,Anty maryam ta buƙaci ganinsu a sashenta yanzunnan”
“Meee daga zuwansu har zata gana dasu…..”
“Haka tace na sanar dakai”
Sauƙe makamin hannunsa yayi yana kallon su Hajiya zeenah ƙasa ƙasa,juyawa yayi yabar wajen sauran ma suka bishi a baya.
Sauƙe ajiyar zuciya Matashiyar tayi tareda kallon su Hajiya zeenah tasake tattausan murmushi.
“Hmmm karku damu yanada saurin fushine,kuyi haƙuri da abinda yafaru….sunana Hilyaan,ko zaku iya biyoni zuwa wajenta”
Lokaci ɗayah Hajiya zeenah taji hankalin ta ya kwnata,saboda abinda yarinyar tafaɗamata.
Cikin sanyin jiki suka fara bin bayanta zuwa barin wajen,har sannann hankalin su bai kwanta ba.
Bayan sun fita daga ɗakin wata hanya sukabi wacce tayi hanyar wani ɗan ƙaramin gida a can gefen inda suka fitan.
Suna tunkararsa ƙyansa da kuma ƙawatuwarsa yana ƙara fitowa fili,babu wanda zai ce akwai irin wannan gidan a jejin inba gani yayi da idonsa ba.
Dan haka yakasance tamkar an ɗakkoshi an ɗorashi a wajen.
Suna shiga cikin wajen wani ƙyatacce ƙamshi yayimusu sallama a cikin wani mayalwaci falo.
Nuna musu wajen zama tayi kafi tayi wata hanyar da wani corridor yabi.
Bata dade ta tafiya ba wata mata mai dan shekaru ta shigo falon dauke da tiren kayan marmari a hannunta.
Ajiyemusu tayi cikin sakin fuska kafin tabar wajen.
Haɗiyar yawu iliyah yayi ganin yanda kayan marmarin suka nuna lutsa lutsa,tashi ɗaya sha’awar ya luma haƙoransa a cikin tuffan(apple) dayake gabansa ta taso masa.
Hannu yakai a hankali zai ɗauke,Hajiya zeenah ce tayi saurin buge hannunsa tareda yin magana ƙasa ƙasa.
“Wannan a kwaɗayinsa sai ya jawo mana abinda zai kashemu,wani inya ganshi zaicd bayacin kayan gabass”
“Ko ɗayah bazai mutu ba dan yaci wannan abin,shin a yanda kukaji labarina nayi muku kamada wacce zata sakawa mutum guba a abinci ta kasheshi……ahah ahah bana kaiwa farmaki ta baya kaman matsoraciyah ta gaba nake tunkarar koma waye,konayi nasara koshi yayi ni hakan shine nasarata”
Dukkansu ɗaga ido sukayi a tare suna kallon mamallakiyar muryar datayi maganar.
Fara ce sol amma ta sirka yellow bakaman fatar masu jan kunneba,tanada tsayi da kuma mulmulallen jiki wanda babu alamun tarin tsokar ƙiba a jikina.
Duk inda aka zayyano fulanin usul akan siffanta su da kyansu daidai gwargwado,ita baza’a cireta daga irin nasu kamanninba,saidai ita koma bayan su ,tana ɗauke da shuɗiyar ƙwayar ido,wacce tabata kamanni irinna turawan yamma,harma yafinasu yin kala da kuma radiating ɗin haske.
Idanuwannata dara dara ne farare,da suka samu baƙin ƙwalli da shudiyar ƙwaya,saita bayyana kaman ba daga duniyar tamu tazo ba.
Shuɗiyar doguwar rigace a jikinta,amma bata kamata har can ba,tana jingine a bakin ƙofar shigowa falon,da alama bata cikin gidan yanzu da shigo.
Ɗauke hannunta tayi daga bakin ƙofar inda ta dafa,kafin ta ƙariso cikin falon,a kan kujera mai ɗayah ta zauna wacce take facing ɗinsu.
“Sannunku,bansan ku suwaye ba,amma labari yazo kunnena tun lokacin da kuka buɗi baki cewar kuna neman Bombee a karo na farko. Lokacin danaji labarin wai wasu sunxo nemana nayi mamaki.
Mai kuke nema a gareni haka, dahar kukebin gari kuna nemana,koma menene nasan babban abune. Dan a lokacin da muruje yabaku labarina nayi zaton zaku haƙura kukoma inda kuka fito,saikuma kuka bani mamaki,dasafe ma sai aka ganku kunsake fitowa nemana”
Tsuru tsuru sukayi,lallai wannan matar taci wannan labarin da sukaji,wato duk yawon dasuke na nemanta tana sane kenan.
Har Hajiya zeenah ta buɗi baki zatayi magana kukan yaro ya ƙatseta,wanda Hilyaan ta shigo dashi tareda nufar inda Bombee take zaune.
Hannu ta miƙa ta karbeshi tareda tambayar Hilyaan ɗin.
“Mai yasameshi hakane,baya kuka irin haka akai akai,kuma likitan yazo ya dubashi kaman yanda nace?”
“Eh ya dubashi,inaga fah kaman ɗan zazzabine yake damunsa,sannan kuma kaman madarar da aka fara bashi jiyane yajawo hakn”
“A daina bashi madarar nan sai yayi wata shida tukunna,har yanzu bai girmaba,nidama nasan madarar nan rayiwa jikinsa girma,ki fita da ita daga gidannan,nafasa bashi ita,zan rage aikin zirga zirga na dunga shayarshi kawai,he need my time too,not only my matter”
Karban yaron tayi tana shirin fitar masa da mama,Hajiya zeenah ce tayi sauri bugar iliyah akan yabasu waje,da sauri kuwa yatashi bayan ya suri tiren kayan marmarin.
“Ohh sorry fah,banida manner ne sosai wani lokacin”
Bombee tafaɗa ko a jikinta lokacinda take sakawa yaron abincinsa a baki.
“Uhm ……uhm bakomai ne ya sakani tasowa daga inda nake nazo wajennan ba saidan wani taimako danake son kiyimin”
“Taimako wanne iri kenan kuma a guna?”
“Inasone ki auri ɗana na wani lokacin ƙayadadde,daga baya kuma sai a raba auren”
“Aure nikuma????? Kinsan mai kike cewa kuwa?”
“Ehh aure,karki damu babu abinda zai haɗaki da ɗana idan shi kike tunani,aikin dazakimin ba akansa bane,akan matarsane”
“Hhhhh nikuwa nasan ba abinda zai haɗani da danki,a labarin da aka baki da kuma wanda kika gani,kin shaida inada ɗa batareda aure ba,babu uwar dazata yarda ta haɗa ɗanta da mace irina,dole akwai abinda kike buƙata gameda kalmar auren.
Karki ɗaukeni jahila kaman yanda kikaji labari,wancan a dane ba yanzu ba,ki tafi kaitsaye ki faɗamin me kikeso”
Taƙaitaccen labarin lubna Hajiya zeenah tabawa Bombee,da irin ƙarfin ikon ubanta da kuma abinda take aikatawa. Sannan kuma taƙara da cewa.
“Ta hanyar aurene kawai zaki iya min maganinta,kasancewar ubanta yanada babban matsayi a kotu,idan abu kikayi mata ta hanyar kishi baza’a zargeni da komai ba.
Tana da ƙarfin hanya ta kowacce siga,idan nace zan turasashi yasaketa kuma tayi masa asirin dazai mutu a ranar,dan haka nayi bincike naga ke kaɗaice nakeda wacce zaki iya yimata abinda dakanta zata nemi sakin batareda matsala ba”
Ɗan guntun murmushi Bombee tayi,danta fahimci inda zancen Hajiya zeenah ya nufah.
“Hhhhhhh kuma a yanda kika ban labari sai kikaga nayi kama da wacce mutum zai taso yazo yasakani abinda yake so na matsalarsa na magance masa,shin kama nayi miki da mai taimakon gyara aure?”
“Ba taimakona zakiyi kawai ba,aiki na kawomiki,auren iyah Wata shidane kawai,ko kuma gwargwadon yanda kika karya lagwonta,sannan zan baki Miliyan Ashirin idan kikayi min aikim”
“Hhhhh miliyan Ashirin?? Kibar wannan zancen,nizan tsara komai yanzu,shin na yarda da zanceki ko kuma akasin haka.
Hilyaan zata karbi bayanan komai danake buƙata gameda lamarin,zanyin bincike nan da gobe.
Ki saurari aikana daga nan zuwa goben,na sallameku zaku iya tafiyah idan takarbi bayanin danake so”
Daga haka Bombee ta ɗauki ɗanta tayi wata hanyar daban.
Bayan tafiyar tane Hilyaan ta zauna da labtop ta karbi duk wani abu daya shafi Lubnah da kuma shikansa Jabeer ɗin.
Mota Bombee tasaka aka maida su Hajiya zeenah inda aka ɗaukesu,inda suka shiga gidan da jiran tsammanin sako daga Bombee ɗin.
“Wai amma fah Hajiya tanada kyau sosai,yanda aka bada labarinta kuwa haka take”
“Hmm kyan ɗan maciji ba,kyanta bazai ruɗeniba kamar kai, tana gama abinda zatayimin zata ƙara gaba,kasuwanci ne zai haɗamu kawai. Na kula shima shegen ɗannata irin idonta ne dashi”
“Wai Hajiya anya kuwa bazaki kai tashin hankali ba gida,karki manta fah da ɗanta zataje,sannan yanda iliyah yafaɗa tana kyau,kar aje a samu matsala fah da Yallabai(Jabeer).
“Kumin shuru ko karen haukane yaciji ɗana mai zayyi da wannan matar,bayan haka ma anayin wananan ma zai aure wacce tun farko tadace dashi ai Wato Jawaheer,wannan bakomai bace illah Mai aiki wacce aka ɗakkota damin tayi a biyata. Mujira dai muji mai zata ce gobe,koma menene ni bazan fasaba daga kan ra’ayina”

……ku garzayah arewabooks domin Samun Cikekken labarin da kuma yawan pages fiyeda wanda kuke samu nan.

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

_Mashaallah A yau Allah ya ara mana lokaci mun gama littafin BAƘAR AYAH na farko._
Ga duk ɗaukacin masoyana ina godiya sosai.
Gobe in allah ya kaimu zan fara post littafi na biyu a AREWABOOK.
Sannan kuma a ranar zan buɗe group a whatsapp.

Duk mai buƙatar littafi na biyu zai turo Naira *300* ta Wannan jaddawalin kamar haka.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Masu turo da kati zasu tura katin mtn ta nan

09035784150

Mutanen niger zaku tura *300f* ta wannan layin.

+227 97 21 16 15

Mai ƙarin Bayani ya tuntubeni ta layina

09035784150

Ko direct whatsapp message

https://wa.me/message/MAPXUDCCPXCGP1

______________****_______________

Page 🖤34🖤

Wani yarone ya shogo gidan da takarda a hannunsa cikin envolope,Innar iyani ya fara gaisarwa,wacce take zuzzuba abinci a kwanuka.
“Uhm dama watace ta aikoni gidannan wai nabawa Hajiya zeenah abinnan”
Iyani tanajin haka tayi saurin karbar takardar tareda cewa.
“Wacece matar,tana waje har yanzu?”
“Tasaka nikaf,tana bani takardar tajuyah ta tafi”
“To shikenan jega an gide,bari dama zan kaimata abin karyawa saina tafi mata dashi”
“Wani kallon mai kuke ƙullawa innartata tabita dashi,ganin bazai kaitaba ta ɗora dacewar”
“Wani kam iyani mai kuke ƙullawa da wannan matar ne kam,kardai kicemin dama wani abu zakuyi da ita shiyasa kikaxo,naga tunda kikazo garinnan ko gidan su iyah bakijeba,in kuka fice a gidannan da safe bakwa dawowa sai dare,gashi kince jibi zaku tafi”
“Ahhah bakomai fah karki damu,yau dama zan shiryah naje musu,har gidan Addah Sa’ade zanje”
Daga haka tayi saurin kawar da zance tayi ɗaki,inda Hajiya zeenah take.
Tana shiga ta maida labulen tareda ƙarisawa inda Hajiya zeenah take zaune da sauri.
“Hajiya an kawo wasiƙa,inaga fah daga wajen Bombee ne”
Tafaɗa tana miƙa mata wasiƙar.
Karba tayi cikin sanyin jiki ta buɗe.

_Na amince da aikinki,saidai bisa sharaɗin nan masu zuwa. Maimakon miliyan ashirin zaki bani miliyan Hamsin,sannan kuma ba wata shida nake buƙata ba shekara gudan nake buƙata,idan kafin sannan nafitar miki ita daga gidanki contarct yaƙare daga nan,idan kuma na haura shekara guda ban fitarta ba nan ma contract ya rushe,zan kuma maido miki da kuɗinki.
Inkin amince da sharaɗina gobe za’a ɗaura auren a address ɗin dana rubuta,wata masallacin juma’ar garinnan.
Waliyyin ɗanki yazo gobe za’a ɗaura auren bayan sallar juma’ar,akwai wanda nakeso yaji aurenne,kekuma bakida haɗi sa hakan tunda ba garinnna kike ba.
Bayan ɗaurin auren Hilyaan zasuje itada khamees suyi duk abinda nakeso wajenda zan zauna yakasance.
Niba yanzu zan biku ba saina gama wani abun,kuma yarona bashida kafiyah a yanzu ,baxanyi tafiyah dashiba_

Wannan shine bayanina inkin yarda akwai takarda a ciki kiyi sign,akwai nawa sign ɗin a jiki,idan kuma baki yarda ba karkiyi sign ki dawomin da takardar haka.

From BB

Ajiyar zuciyah Hajiya zeenah tasake tareda miƙawa iyani takardar itama ta karanta.
“Inkinada biro kawomin zanyi sign”
“Hajiyahhh wai kin yarda da abinda tace,miliyan hamsin fah kuma kiji wasu sharudda kamar uwar mutane”
“Ki miƙomin biro kawai na amince dasharaɗinta,sa’a tace dana samu ta amince,idan bata amince ba inaji a jikina ciwo zuciyah zai kamani na takaicin lubna,wanda inna kwanta in miliyan ɗarine ma zan cinye ban warke ba. Dan haka ki miƙomin biro da kuma wayata,zan ƙira alhaji kan batun waliyyin Jabeer ɗin”
Daga haka iyani batasake cewa komai ba,sai miƙowa Hajiya abinda ta buƙata din.
Allah sarki bawan Allah da bai ɗauki duniyah a bakin komai ba,yana zaune akan kujerar sa bayan Madeenah ta gama Kawo masa maganinsa yasha bayan ya karyah.
Wayarsa ce tayi ringing,yana dubawa yaga sunan matar tasa,murmushin manya yayi kafin ya ɗauki ƙiran.
“To mai kuma yafaru uwar yara”
“Sai abu ya faru kafin na ƙiraka,yajikinnaka,ina fatan dai suna kulada maganinka akai akai”
“Ko kinannan ma dama ai suna kuladashi sosai,ya abinda kikaje nema,kinyi nasarane”
Eh ta amsa masa a hankali,dan tasani sarai ya ɗagota ganin ƙiranta yanzu,sabanin yanda take kirannnasa sai dare kawai tun zuwanta gembun”
“Nayi nasarar samun amincewarta,yanzu aure za’a ɗaura gobe,kayiwa Baffansu magana akan yin walin,inyaso saisu taho a jirgin dazaizo ɗaukar mu”
“Ahah Karki saka Abdullahi kan wannan maganar taki,kinfi kowa sanin yanda abin zai kasance,kedai ki bari akwai wanda zan turo goben idan jirgin zai taho. Saidai har yanzu kina ganin yin wannan auren shine mafitar wannan matsalar? Kaman yanda kika faɗa nabar miki ragamar abin,na zuba miki idone naga wanne irin gyara zakiyi?…”
“Komai yana tafiyah daidai, na tabbatar komai zai tafi yanda na tsara”
“To shikenan Allah ya baki sa’a,kin faɗawa shi ɗannaki abinda yake faruwane na aurennasa gobe?”
“Karka damu zan sanar masa a goben idan an ɗaura auren,kuma ma aiba yinsa zanyi dan……..shikenan nan dai komai zaizo daidai”
Daga haka Hajiya zeenah tayiwa mijinnata sallama ta kashe wayar.
Kallon wayar yayi bayan takashe
“Hmmm idan na faɗamiki ki kwantar da hankalin ki bakyajin magana,yaronnan ya girma,amma har yanzu son zuciyarki ya hanaki kigani,muje zuwa,ina fatan wannan abin dakika ɗakko dakanki yayi silar gane kurenki batareda wata babbar matsala na,nasan idan nahanaki yanxu damuwa zakisa a ranki dazai jawomiki ciwo……kai Allah ya kyauta”
Ƙara daga wayar yayi yasake ƙiran wani manager amininsa a company,wanda yasaka a boye ya dunga kulamasa da mai ake a wajen.
Magana sukayi akan yashirya zuwa gembun sannan kuma yazama waliyyin Jabeer ɗin a auren,Babu yanda zayyi,yasan idan yaƙi saka hannunsa yabarta taje tayi yadda taga dama,zata iya jawo matsalar dasai tafi bai saka hannunba.
A ranar su Hajiya zeenah basuje ko inaba,dan haka iyani ta samu damar fita zuwa ga danginta,itakuma Hajiya zeenah tasamu damar hutawa na zirga zirgar da tayi.
Washagari Ranar juma’a bayan an gama sallahr juma’ar ne mutane sukaji ana sanarwar ɗaurin auren.
Sunan da aka ambata shiya girgiza mutane ba kaɗanba,wai Bombee zatayi aure,shikansa uban amaryar bai san da zancen ba sai dayaji an ambaci sunan.
“An ɗaura auren JABEER ALIYU da kuma MARYAM AHMAD.kan sadaki Dubu hamsin”
Nan da nan kuwa kaman iska labarin auren Bombee yazagaya waje da dama,wasu sai murna suke zata bar garin tatafi. Yayinda wasu kuma har sannan basu gama yarda da lamarin ba.
A zaune take tana kallon window tayi shuru alamar mai tunani.
Hilyaan ce tashigo ɗakin tareda cewa.
“An ɗaura auren kaman yanda kika faɗa,amma miyasa ba aure bane normal kikayi shi cikin jama’a ba’a sirriba,mutane sai labarin auren sukayi”
“Saboda sonake kowa yashaida auren,musamman gidanmu,akwai wanda nakeso su sake ransu cewar na tafi,daga baya kuma saidai suga bayyanata batareda sunyi tsammani ba”
“Uhm toh shikenan yanzu kuma saime za’ayi,naji kince zamu farayin gaba kafin ki taho ko”
“Eh zakuje kuga wajen da tace zan zauna,inda matsala ku ƙira ku faɗamin,sannan ku saka duk abinda nake buƙata,nan da kwana uku zan taho idan nagama abinda nake”
“Hmmm yanda suka bada labari kaman matarsa batada mutunci”
Ƴar dariya Bombee tayi tareda cewa.
“Wannan yana ɗaya daga cikin abinda yasa na karbi aurensan,na daɗe bansamu abin nishadi ba kaman wannan,har na matsu naga abinda zai kasance,sannan kuma bayan lokaci mai tsayi finally zan koma garin Abuja”
Dan jijjiga kai Hilyaan tayi tareda fita zuwa ɗakinta,saboda tattaro kayanta,dan an sanja tafiyar daga gobe zuwa yau. Babu zancen bata lokaci yanzu zasu tafi tareda su Hajiya zeenah.

Tafiyah yake a mota yana jin labarin da ake a gidan rediyo,hankalin sa yayi nisa wajen sauraron shirin da ake na Filin zamantakewar aure.
Ƙarar wayar sa ce tashashi ɗauke kansa daga kan hanyar ya kalli mai ƙiran.
Sunan Mommah yaga akan wayar,hakanne yasaka ta a jikin mota wajen ƙiran waya. Sallamar ta yaji ta doki dodon kunnensa,a ransa yace yau kuma koda wannne tazo?
“Hello Jabeer kana jina?”
“Eh ina jinki Mommah”
“Tamm Abbanku ya turo mana da jirgi ɗazu,yanzu haka muna hanyar dawowa,na sanja dawowar sai gobe,kaje gida ka faɗawa su Madeenah dawowa ta,na ƙira wayarsu bata shiga”
“To shikenan dama ina hanyar gidan zan faɗamusu”
“Ohh bazaka tambayi ya abin ya kasance bane?”
“Mekenan dama ba fasawa kikayi ba,shiyasa zaki dawo?”
“Ka taba ganin nasa abu a gabana na fasa,ai ka kwantar da hankalin ka,nayi nasarar shawo kan matar danaje aura maka,yanxu haka an ɗaura auren muna hanyar dawowa,ka fara ƙirgawa ka kusa rabuwa da wannan jarababbiyar matar”
Bata gama faɗin bayanin datake som ƙarisawa ba Jabeer ya kashe wayar,saboda wani bugu da kirjinsa yayi batareda ya shirya ba.
“Innalillahi Allah gani gareka shin wa nafi tsorone a cikinsu,Ummata ko kuma Matata,ga ………..”
Bai gama maganar ba yaji alamun yabuge wani abu a gabansa,da sauri yaja burkin motar,amma duk da haka daga yanda yaga mutane suna taruwa a wajen yasan akwai abinda ya bige.
Saurin fitowa yayi daga motar tareda ture mutanen da suka taru a wajen.
Bayan mace yake kallon sanye da milk ɗin hijabi,kowa sai sannu yake mata,ita kuma ta sunkuyar dakai batace komai ba.
“Subahannallahi baiwar Allah bakiji ciwo ba dai koh”
Ɗago darara dararan idanuwanta tayi farare tasss ta sauƙe su akan fuskarsa,daga kallon zubin yarintar fusakarta bazata wuce shekara 17 ko 18 ba,kyakykywace ajin farko idan ana samun irinsu,ɗan ƙaramin bakinta ta tsuke tareda sauƙe idanuwanta tana kallon hannunta wanda yake dauke da ciwo a jiki amma ba mai yawa ba.
Wani irin yarr haɗe faɗuwar gaban Jabeer yashiga a lokacin guda,wanda tunda yake bai tabajin yanayin ga Wata mace na,harda kuwa marigayiyar matarsa hafsah.
Gabaɗayah notin kansa ya kunce,baisan lokacin da yakai hannu kan inda ciwon yake ba,tana ganin hakan tayi saurin ɗauke hannunta tareda cewa.
“Karka ta’bani”
Cikin wata murya mai ma’abocin taushi da sanyi.
“Jaleelah mai yasameki haka dama ke aka buge naga mutane,kinji ciwo sosai”
“Ahaha Fareeda ba sosai bane,mugafi gidamana kar dare yayi mana a waje”
Tafaɗa tana tattaro litattafanta da suka zube akan titi.
Dogon hijabi ne har ƙasa,sannna kuma akwai rubutun larabci a jiki hakanne ya tabbatar daga islamiyyah suke.
Ko kallo dayah basu sake yiwa Jabeer ba suka kama hanyar zuwa gida.har sukayi nisa Jabeer yasaka motsawa bare yayi ƙoƙarin basu hakuri ko yimusu magana,tun lokacin da muryar yarinyar tashiga kunnensa.
Shawarar da Khaleel yabashi Kwana biyu da suka wuce ya tuna….
“”””Kasamu wacce zuciyar ka takeso ka aura,mai ilimi da tarbiyya,wacce zata kwantar maka da hankali idan suka tayar ma””””
Ɗan murmushi yayi tareda shiga motarsa yafara bin bayan ƴan matan………

Kashshshsshshshhsshh Makaranta,anan muka kawo ƙarshen littafi na ɗayah a cikin Labarin Baƙar ayah.
Domin Samun cigaban labarin da kuma tambayoyin da suke cikin kanku,ko kuma son jin wacce chakwakiya ce zata faru kaman haka

__Menene maƙasudin abinda yafaru da mahaifiyar Bombee?
___shin kuna zargin inna laari kaman yanda Bombee ke zarginta?
___miliyan hamsin bashine kaɗai abinda zai iya sakawa Bombee ta amince da ƙudirin Hajiya zeenah ba,sannan kuma ta buƙaci shekara guda maimakon wata shida meyasa toh?
_____Ga Luban….Ga Bombee…….Ga Jawaheer……sannan kuma ga zabin shi uban gayyar wato ……..Jaleelah!!!!!

Wacce chakwakiyace zata balle tsakanin wannann matan idan suka kasance ƙarƙashin inuwa guda,gasuda halaye mabanbanta???

Sannan waye uban ɗan Bombee,shin Jaan family zasu yadda tazo musu da shege cikin gida???kuma shin zata iyah maganin Lubna kaman yanda tace………..
Masu magana sunce BAƘAR AYAH…….Itama cikinta farine. Shin wacece baƙar ayah a cikin matannan,anya kuwa zata kasance farar kaman sauran Baƙaƙen Ayar???
Kaɗan kenan nasan daga amsoshin da suke cikin kanku,Amma karku damu duk zaku samesu cikin sauƙi idan kuka cigaba da bibiyar littafin a Arewabooks.
Ku sauƙe app ɗin kana kuma kuyi search littafin BAKAR AYAH zai fitomuku waral domin karantawa.

Ga wanda basu ganeba domin ƙarin bayani su tuntubeni ta wannan layin

09035784150

Wanda bazai iya karantawa ba a arewa book shima yayi min magana domin shiga group ɗin littafin,idan an gama kuma sai ya siyah littafin document a wajena.

SADI-SAKHNA najiran isowarku makaranta❤❤❤❤ mu haɗe a littafi na biyu,ina yinku cikin carbi🤣🤣🤣

Alhamdulillah Alah kulli halin

___****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK 2_ 🖤

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
Shaida tanan
+227 97 21 16 15

______________****_______________

Page 🖤1••2🖤

Tafiyah suke Jabeer yana binsu a baya bataresa saninsu ba har suka kai gida.
Kallon ƙofar ya tsaya yi yana nazarin tsarin gidan daga cikin motar.
Wai dama akwai irin waɗannan gidajen a garin abuja?? Kodaga nesa mutum zai gane yanayin rashi da ma’abota gidan suke dashi.
Katangar gidan duk ta zube ta wani wajen saboda rashin ƙarfinta,kuma ya haɗu da yawan ruwan sama dayake kwaranyah a kanta na tsawon lokaci.
Kofar gidan babu wani ishashshen makari,wani langa langane a gefe,da alama dashi ake amfani wajen kare gidan da daddare.
A taiƙacedai gidan na masu ƙaramin ƙarfine sosai.
Numfasawa Jabeer yayi bayan ya gama kallon gidan,inda ba biyota yayi ba yaga tashiga gidan,bazai taba cewa daga nan ta fito ba.
Abinda yafi bashi mamaki shine yanda taƙi karbar taimakonsa,bayan kuma tana rayuwa a gida irin haka.
Fitowa yayi daga cikin motar ya nufi gidan,waigawa yake domin samun wanda zai aikata cikin gidan,idonsa ne ya sauƙa kan wani yaro yana riƙe da kwanon a hannunsa,fuskarsa dama dama da miyar tuwo,da alama tunna jiyane,dan tuwon bayyi kamada wanda aka dafashi sannan ba.
Cikin ɗauke kai daga kallon fuskar yaron ya fara magana.
“Uhm mutumina nace zona aikeka mana,shin nanne gidan su Jaleelah koh?”
“Eh nanne gidan su ina anty hafeezah koh?”
“Eh inaga itace,shiga kace ina sallama da mahaifinta idan yana nan”
“Nawa zaka bani to idan na ƙiramaka shi?”
Mamakin maganar yaron Jabeer yayi,yanzu wannan yaron har yakai bazayyi abuba sai an biyashi?
“Karka damu shiga ka kiramin shi tukunna”
Hanyar gidan yaron ya nufah,bayan wani ɗan lokaci sai gashi sun fito tareda wani farin dattijo mai kamala da dattaku.
Gaisawa sukayi cikin mutunta juna,maganar yaronce ta katsesu da cewa wani abu bayan sun gaisa ɗin.
“Malam baka bani kuɗin ba toh”
Kafin Jabeer yayi magana Dattijon yace.
“Wanne kuɗin za’a baka,har yanzu baku bar wannan ɗabi’a ba koh,ohhh wai yaro baisan a sakashi abu ba sai an bashi kuɗi? Wuce ka tafi gida”
Da sauri yaron ya wuce yana zumbura baki,sai bayan ya tafi tukunna Dattijon ya dawo da kallonsa kan Jabeer.
“Yaro baka faɗamin mai yake tafe dakai ba har yanzu”
“Ehh dama yarinyar gidan na buge da mota a can kan titi,nayi mata magana mutafi asibiti a duba taƙi amincewa,shine nazo naji shin lafiya dai koh?”
“Jaleelah kenan kake nufi,dan itace ta dawo daga makaranta ɗazu,data shigo kuma batace komai ba,babu wanda yasan mai yafaru”
Kasa boye mamakin sa yayi jin wai batace komai ba a gida,kulada hakan da dattijon yayi ne yasashi cewa.
“Yaro karfa ka damu,haka take dama ta saba,kuma tunda har bata nuna ba inaga ba wani abin damuwa bane sosai,kayi tafiyar ka zanje na dubata inna shiga gidan,mungode sosai da kulawarka Allah ya tsare gaba”
Kuɗi Jabeer yafitar ko ƙirgawa bayyi ba ya miƙawa mutumin,tun kafin ya kaishi kusada shi ya ture hannunsa tareda cewa.
“A’ah karma ka ɗorawa kanka nauyi akan wannan,kayi tafiyar ka babu komai kaji yaro”
Daga haka ya shige gida yabar Jabeer a tsaye,dama ana samun irin waɗannan mutanen har yanzu,basuda shi amma kuma sunada wadatar zuci?
Kallon sama yayi ganin rana tayi shirin faɗuwa,gari yafara duhu,yasan zuwa yanzu wataƙila Hajiya zeenah sun dawo.
Wani idan su Hajiya zeenah sun dawo yanzu,toh fah lubna zataji labarin auren da aka ɗaura masa,kuma yasan da gangan Hajiya zeenah zatayi abinda zata san da ɗaurin auren.
Wai yazayyi kenan bai faɗamata ba saidai taji a wani wajen,yasan tashin hankalin dazai tarar ba kaɗan bane.
Saurin dafe kansa yayi,zuwa ɗazu daga haɗuwa da waccar yarinyar har ya manta da damuwar dayake ciki,ya shanye lokacinsa a nan wajen.
Hanyar inda ya ajiye motarsa ya nufah da sauri,yana bata wuta kuwa yanufi gida,a ransa yana addu’ar Allah yasa Hajiya zeenah basu dawo ba tukunna.
Tun kafin ya isa sashen Hajiya zeenah ya hango mutane a wajen,wanda hakan yabashi tabbacin ta dawo kenan.
“Tafaru ta ƙare….”
Yafaɗa cikin kasalalliyar muryah,fita yayi a motar ya nufi sashennata,yasan dole amryar da akayi masan tana sashinta yanzu,tunda baici ace an gama gyara ainihin sashennasa zuwa yanzu.To ma shi baiga wani dalilin komawa wannan sashen ba,kawai dai rigimar Hajiya ce.
Da Maleekah ya haɗu a falon ta ɗauko faranti a hannunta zata shiga ɗakin Hajiyan.
“Ke zo na tambayeki”
Cikeda tsoro da kalleshi,fuskarnan a tamm da ita babu alamar fara’ah.
“Yaushe Mommah ta dawo,tana ina kuma?”
“Uhm batafi minti talatin da isowa bama,tana daƙinta itada amaryar”
“Amarya,kowa yasan da zancen amaryar kenan?”
“Eh mommah tana shigowa ta tara dukkan ma’aikata ta shaida musu cewar kayi sabon Aure yau,kuma dama tana nemanka idan ka dawo”
Dafe kansa yayi ta gefen dama,jin ɗanyen aikin da mahaifiyar tasa ta aikata masa a karo na babu adadi,ko shakka babu yasan da gangan tayi hakan saboda lubna ta sani.
Bai sake kallon inda Maleekah take ba ya wuce ɗakin Hajiya zeenah,itama binsa tayi a baya,dan dama can zata nufah.
A can ƙasan maƙogaronsa yayi salllama kansa yana kallon ƙasa,kana ganin haka kasan yana cikin yanayi marar daɗi.
A ɗaya daga cikin kujerun ɗakin ya zauna,yaga alamar wata farar mata a zaune gefen Hajiya zeenah suna magana,amma ko kallonta bayyi ba,dan yasan itace matar da aka aura masan.
“Ahh Jabeer kaida nace ka kira su Madeenah ka shaida musu zuwana sai yanxu ka shigo”
“Nasamu wani ɗan ƙaramin hatsari ne a hanya”
“Ohh to Allah ya tsare na gaba,shin an gyara sashennaka ne ko kuwa har yanzu”
“An gyara saidai bansan ko sun gama ba,amma naga wancan ɗinma danake ciki akwai parta empty a ciki”
“Nasan da haka,akwai dalilin daya saka na zabi wancan ɗinne,kuma nasan kaima kasan dalilin. Yanzu dai ba wannan ba,mun taho da baƙi,wannan itace……..”
“Please dan Allah mommah kibar wannan bayanin,inkin faɗama ba ganewa zanyi ba,inade part ne,za’a gyara taje da zauna kaman yanda kike buƙata,daga nan kuma fah saime takeda buƙata”
Cikeda bacin rai da ƙosawa yayi maganar,shuru Hajiya zeenah tayi,dan ita kanta tasan takai ɗannata bango,amma shima bazai gane bane,kullum cikin fargaba take da matarsa,gani take da dai da rana dayah idan ta zauna tayi shuru lubna zata cutar mata da ɗa.
“To naji,dare yafara nasan ka gaji,kaje ka huta sannan ka sanarwa matarka cewar yanzu ba ita kaɗai bace,karta sakankance kamar da”
Har yakai bakin ƙofa yasake juyowa ya kalli Hajiya zeenah.
“Amma mommah shin indai yanda kuke faɗan haka take,bakya ganin cewar itama wannan bazata……..”
“Kaga ya isa haka kaje saida safe,sannan karka sa damuwar wannan auren cikin ranka,yanada dalilinsa daban wanda bai shafeka ba”
Akwai tambayoyi a cikin kansa kala kala,amma yasan koda yayi su bata lokacinsa kawai zayyi,dan haka yabarsu a zuciyarsa kawai ya fitah.
Jan numfashi Hajiya zeenah tayi bayan ya tafi,maida kallonta tayi kan Hilyaan wacce take zaune hankalin ta kwance akan kujera tana kallon abinda yake faruwa.
“Kiyi haƙuri fah nasan munyi tafiyah kun gaji,shi abokin tafiyar taki ankai shi masauƙin baƙi,ke kuma zaki iya kwana a ɗakin Madeenah,ko kuma a baki ɗaki daban”
“Ahah karki damu Hajiya,duk inda kika bani ma ya wadatar,na kwana ukune ai kawai kafin Anty maryam tazo,sannan ma ba zama mukazo yi ba ai,zamu fita kasuwa ne da khamis gobe”
“Medame kuke buƙata haka,babu ba abinda zaku siyah na kayan gida,gyaran daza’ayiwa part ɗin komai za’a saka shi”
“Eh dama ba wai kayan normal na gidaba,akwai abinda take buƙatar a saka na ra’ayinta ne,……
Uhm wannan shine Angon Antyn?”
Hilyaan tafaɗa,badan komai ba saidan ta kawar da zancen da ake a lokacin.
“Eh fah shine,amma bawani buƙatar ta sanshi ai ko ya santa,kafin tazo zanyimasa bayanin ainihin dalilin auren,karku damu da wannan”
Hmmm ba laifi kyakykyawane kam sosai,kaman yanda itama take mai kyau,ina gujemiki aikinki yajuye ba yanda kike so ba. A fili kuma tace
“Ahh babu wani abin damuwa sosai,naga shima bayada interesting akan auren,ko kallon inda nake bayyi ba,yayi zaton inaga nice amaryar”
Hilyaan tafaɗa ɗauke da ɗan ƙaramin murmushi akan fuskarta.
Kayan marmarin da Maleekah ta kawo ta ajiye tafara ci. Dan ita iyani mai aikace aikacen sashen a gajiye take saboda bidirin da suka sha.
“Hmmm da alama wannnan yarinyar da Hajiya ta auramin batada kunya ko kaɗan,wato tafi ƙarfin gaisheda mutane ma,oh kodayake hakan ma yafiye mata,dan wahala zata sha idan tayi ƙoƙarin shiga rayuwata”
Yana cikin zancen zuci bai sani ba yanayinsa a fili,har ya isa sashen Lubnah.
Bai sameta a falo ba,dan haka ya nufi ɗakinta,a tsaye take tana kallon window da Ƙaramin wando a jikinta,rigar ma iyah rabin cikinta,indai ba sannan tasaka kayan ba yasan dasu tayi yawon a falo babu abinda ya dameta.
Sallama yayi a bakin ƙofar,duk da a hankali yayi yasan tajishi sarai,shurun datayi kaman gunki bata amsa ba ya tabbatar masa da labari ya isa ga kunnenta kenan na auren.
Ajiyar zuciya yasake,zuciyarsa tana tsalle a cikin ƙirjinsa,shikansa yasan tsoron ta dayake bana lafiya bane,saidai babu yanda zayyi da hakan.
“Luban!!!”
Ya ƙira sunanta cikin sanyayyiyar muryah.
Bata amsa ba sannan bata juyo ta kalleshi,shikansa yasan bai isa misalta abinda yake cikin zuciyarta ba a yanzu.
Takawa ya farayi a hankali zuwa inda take tsaye a jikin windown,duk da shareshin datayi baiji daɗiba,amma yasan rabin abinda ya faru larfinsa ne dana mahaifiyar sa,ko mace mai sanyin rai ba kowace zata yarda da irin auren da akayi masa ba,miji bai sanar dakai zayyi aure ba,saidai kawai kaji a bakin masu aiki. Mai yafi haka ciwo,musamman idan aka danganta da zafin kishi irinnata?.
Hannunsa ya saƙala ta ƙasan tumbinta,duk da bawani mai yawa bane amma zaka jishi,saboda ƴar ƙibar datake da itah.
Kansa ya kwantar a kafaɗarta,sunkai kusan minti biyar amma har sannnan yagagara cewa komai .
“Dagaskene kayi aure yau”
“Kinga ba…….”
“Kawai tambaya nayi,shin dagaskene yau an daura maka aure ko ahah?”
“Eh da gaskene,amma ba yanda kike tu…….”
Buge hannun Jabeer tayi daga jikinta tareda fuskantarsa cikin bacin rai.
“Bana son jin komai bayan gaskiyar danaji,duk ƙoƙarina a koyaushe baka gani sai kayi ta kawomin mata cikin gidana koh,bayan kasan babu abinda na tsana kaman na buɗi ido naga wata halitta wai ita mace a gefen mijina”
“Oh gosh wai lubna yaushe zaki daina irin wannan abinne,eh aure da gaskene an ɗauramin aure yau,amma ki tsaya kiji ni nawa bayanin mana,Nifah banine naje dakaina nayi aurennan ba,Mommah ce ta yimin aurennan ki fuskanta mana”
“Wacce fuskantar zanyi,koma wanene yayi maka auren aidai kai akayi wa,mijina akayiwa ni akayiwa kishiyah,ni wannan kawai nasani ba wai wanda yayi aurenba,akan me akayi shi nasan bazai wuce ace dan ka samu ɗa ba,koba dan haka bane. Ko kace baka santa kaman yanda kayi sauran,kana ganin ta samu ciki shikenan saidai na ganka kana lailayata kaman ka samu ƙwai,koba haka bane?”
“Kaiiii lubna bafah haka bane”
“To idan ba haka bane,yanzunnan kaje ka bata takardarta basai gobeba,shine zan yarda dakai toh nasan babu hannunka a ciki”
“Mee naje na bata takardarta,yakikeso kenan na fuskanci Mommah idan na aikata hakan”
“Ni wannan bai dameni ba,kaita shafah”
“Dan kinsamu ina lallabaki shine kika faɗamin abinda kika ga dama koh,ni bazan iya aikata abinda kike so a yanzu ba,idan har abinda na faɗamiki baki yarda ba shikenan”
“Haka ma zakace aikuwa gidanmu zan tafi bazan zauna ba,inka fitarta daga cikin gidannan saikaje kayi min bayani”
“Fine ga kofa nan,dama konayimiki shamaki da ita bakya daina tsallakata,yanzu ma kuma ƙofarki a buɗe take ki tafi,sanda kika ga dama saiki dawo,dama ba yau kika fara ba ai”
“Zan tafi amma karka damu dakanka zakaxo kana rokona kafin na dawo,itakuma matarka ka faɗamata tashirya dawowa ta bazai mata daɗi ba,saita fuskanci abinda bata taba ganiba a faɗin rayuwarta”
Tana gama faɗin hakan tafara tattara kayanta cikin zuciya,tsayawa yayi yana kallonta,dan shi yanzu ta daina bashi ma mamaki.
Jin ana shirin shiga sallah ne yasashi faɗawa banɗakin dakinnata domin yin alwala.
Lokacin daya fito bata nan itada akwatinta,jan ajiyar zuciya yayi kafin yace.
“Jeki na samu na huta naji da wani abun kafin ki dawo”
A zaune take ta dafe kai tana kallon Haidar yanata yimata kuka,tun yamma take fama dashi yaƙi shan nono kuma yaƙi yin bacci,gashi ta duba jikinsa babu zazzabi.
Sakashi tayi a gaba tana kallonsa har wuntsilawa yake yana shiɗewa saboda kuka.
Ƙarar wayarta ne yasaka ta dauke kanta daga kansa ta mayar kan wayar.
Sunan Hilyaan ne ya bayyana akan screen din,hakanne yasa takai hannunta ta ɗauka a kasalance.
“Hello Hilyaan yaya kun isa koh”
“Eh mun isa anty,yanzunnan ma aka kawoni dakin dazan zauna kafin ki taho”
“Toh ya gidan tsarinsa yayi yanda nakeso,kunga inda zan zauna a gidan”
“Ehh komai yayi sosai,gobe zamuje da khamis muyi order duk abinda kike so a saka…ɗazu naga Mijinnaki gaskiya ya haɗu sosai,saidai da alama fah shima yana ji dakansa,daya shigo wajen mahaifiyar sa ko kallona bayyi ba,yayi zaton nice amaryar”
“Kinga niba damuwa ta ji da kansa ba,inyana so ma yaji da cikinsa ba kansa ba,bai dameni ba danshi zanje garinba daga shi har uwartasa,to ya matar tasa taji labarin auren ko kuwa”
“Eh kaman taji,dan muna zuwa Hajiya zeenah tasaka a shaida mata mun dawo,kaman yadda ta faɗa dagaske bata son ta kam”
“Wannan kuma tsakaninsu,nidai bazan yadda su yimin abinda banaso ba kaff gidan,ita kanta matar tasa ba yanzu zanyi maganinta ba sainazo tafiyah a ƙarshe tukunna,abinda yake raina shizan fara”
“To shikenan Allah yabaki sa’a,yadai naji Haidar sai kuka yake lafiya”
“Hmmm ai Hilyaan kina ƙoƙari sosai da yaronnan,wlh iya yau duk narasa yadda zanyi dashi,ko fita zuwa training na gagara zuwa fah yau,gashi khmis ma bayanan,waɗancan direbobin sai signarsu nake gani a cikin jeji”
“Hhhhhh gwanda ki saba ai,karki manta fah ke uwace, yakamata ki saba da ɗawainiyar danki”
Hilyaan ta karisa maganar cikin dariya.
“Zanyi wanda nayi,in yagaji ai zayyi shuru,gobe zan shiga cikin gari wajen mutanen gidan can,ki tabbatar fah ki tafiyar da komai yanda ya kamata”
“Karki damu anty zamuyi miki yanda angonki yakeso,ni ina ganin ma kina ganinsa ki faɗa soyayyar sa”
Zaro ido tayi jin maganar takaicin da Hilyaan take yi mata,tun kafin tayi magana taji ta ƙatse ƙiran ƙitt,da alama dama tsokanarta tayi.
Duba wayar tayi taga ƙiran ya katse,cije baki tayi tareda cewa.
“Lallai kinga gadon baccina dayawa,na faɗa soyayyar sa,wannan maganar kuwa zata barni nayi bacci yau?”
Bombee tafaɗa cikin cije baki tana dunƙule hannu.
Da safe data tashi har mai aiki tayiwa haidar wanka ta dafa abinci. Wanka ta shiga,bata daɗeba tafito tana tsane ruwan dayake jikinta.
Riga da wando tasaka kaman na pakistan baƙaƙe,da alama irin shigar yana burgeta,kuma yana daukar jikinta dakuma dirinta ba kaɗan ba.
Zama tayi tashi abinci sosai,dan ma yanzu tarage yawan jin yunwar datake kwanaki..
Ɗaure dogon gashinta mai walwali tayi da ribbon,kafin ta yane kanta da mayafin kayan.
Wani baƙin glass ƙato ta toshe dashi a fuskarta. Kallon madubin dake gabanta tayi na dan wasu mintuna,itada kanta tasakawa kanta dariyah ganin shigar datayi.
Belt ta ɗauka na goyon gaba ta ɗaura,kana tasaka haidar a ciki,wanda yake ta daga ƙafa akan gado,shima yasha baƙaƙen kaya masu tsada.
Baƙar motarta tashiga tayi mata key,bayan ta bata wuta yanda ya kamata ta ƙujeta sai cikin gari.
“To mutanen gida dana gari harda maƙwanta,ganinan zuwa muku bankwana kafin na tafi……..”
Ta faɗa cikin sautin dariyah mai ɗauke da nishaɗi.
Kaman kullum inna laari ce kawai a tsakar gidan sai innayi tana tayata Gyara ganyen shayi,suna cikin taɗinsu na uwa da ƴa sai ganin Bombee sukayi a kansu carr ta saƙala hannunta na hagun a jikin igiyar belt din abin goyon,dayan hannun kuma tana kakkaɗa key din hannunta,dan jijjiga take da alama tana lallaba ɗanta wanda yake ɗaure a kan ƙirjinsa,hankalinsa kwance bamu mai iya tabashi saidai abinda ido baya iya gani.
“Sannunku iyalan Mlm Ahmadu,nagaban goshinsa abin alfaharinsa,ga baƙuwa tashigo gaisheku”
A tare suka sauke idonsu a kanta,tambayar su daya mai takeyi a wajennan bayan an ɗaura aurenta jiyah.
“Mamakin ganina kuke koh,to ban tafiba bare kusaka ruwa a kasa kusha dan daɗi,uwata nazo gani shin zan samu ganin ta ko ahah banida ikon hakan”
Cikin izzah ta alamar babu wasa take maganar.
Innayi ce ta tashi tareda kallon Bombee tana murmushi.
“Ahh Addah Bombee kawoshi”
Yar dariya Bombee tayi tareda cewa.
“Haka aka koyamiki ki faɗa kuma yanzu,kiyin sakin fuska nabaki ɗana shima ku kasheshi a tsaye koh?”
“Kee wai menene Burinki ne haka,kishigo gida babu sallama babu komai ki hau yiwa mutane tujara,bada sa’nninki ba komai ba,na miki shamaki da cikin gidannan amma kin ƙiji,ki faɗamana mai kikeso ne wai a wajenmu,duk abinda kikayi ta jawo mana a gari na tsawon shekaru bai isheki ba ne”
“Bai isheni ba laari,sai ranar danaci ribar abinda nake,sannan kuma kowa ya tone abinda ya shuka kafin zai saurara,banyi komai bama tukunna,ina jiran lokacin dayafi daidai ne,yanzu gargaɗi kawai nake aikawa kafin sakamakon ya iso.
Bombee zata bar garin gembu amma ba wai ta tafi bane shikenan,kai tsaye zata dawo tasake bayyana,domin akwai aikin data bari bata ida kammalashi,aikin dazanyi a can shine akan layi hakan shikaɗaine sa’arki,kafin sannan ki gama shiri iyah shirin dakike bukata”
Duk wannan maganganun a daidai fuskar laari take faɗansu tana kallonta ido cikin ido.
Wani kallon inna laari tayi mata mai cikeda yarinya baki san komai ba,yayinda itama tayi mata kallon kin sake wuyana yayi kauri yafi ƙarfin yanka.
Muryar mlm Ahmadu sukaji yana cewa.
“Mai kuma wannan halittar takeyimin a gida,duk yanda na kai da ƙin korarki saida kika tilastani na aikata hakan,yanxu kuma mai kike min a gida”
Maimakon Bombee taji haushin abinda ya faɗa,saima murmushi da ta zabga mai armashi da nishaɗi.
Toh mu hadu a page na gaba……

_*SADI-SAKHNA CEH*_

Page 🖤3••4🖤

“Karka damu baba dama bakwana kawai nazoyi,hankalin ka zai kwanta sosai,domin a kallah kusan Shekara guda ban juyo ba”
“Hmmm wannan auren ma kenan niyyar kasheshi kikayi koh”
“Ahah baba dama ba aurene irin kowanne ba,na yarjejeniyane akwai ranar mutuwar sa”
“Kai Addah Bombee ko shiyasa wannan matar tazo nemanki ran…..”
Kafin tagama magana inna laari ta buge bakinta tareda zabga mata harara.
“Kaga malm ba wannan ba,tazo ta fice daga gidannan,bankwanan ya ishemu haka,kada ta shafa mana tsiyar datake tattareda ita”
Runtse ido Bombee tayi jin abinda inna laari ta faɗa,saidai maimakon hakan yasaka shiga yanayi na baƙin ciki ko kuma karya lagonta,saima tunzurata daya sakeyi,bude shiɗayen idanunta tayi akan inna laari tareda cewa.
“Ke na gama yimiki bankwananki,amma bangamawa wacce tayimin shamaki da ɗaiɗaita birbishinki ba wato innata,dan haka inaga ko kinfi kuturu naci baki isa hanani shiga na ganta ba,kokai kin ƙarisata bansani ba?…… Inaaa bakida wannan ƙarfin gwiwar tukunna,har yanzu dai ina matsayin ƙadangariyar data zauna a miki akan tulunki”
Hanyar dakin innarta tanufa,wacce take zaune kaman koyaushe akan kujera tanajin abinda Bombee takeyi,saidai batada ikon kallonta ko kuma maida mata magana.
A gabanta ta tsugunna tareda daukar hannunta tariƙe akan nata.
“Inna ni zan tafi,amma zan dawo ko domin ke,dan bawai natafi kenan ba,duk yadda zanyi sainayi wajen ganin nagano mai yake damunki,wannan shine kaɗai burina daban cikaba a wannan garin”
Jijjiga kai Danejo tayi da sauri,tareda matse hannun Bombee cikin nata,ma’ana karta dawo kenan kaman yanda take ikirari.
“Ahah inna zan dawo,ko badan aure bama saidan idan lokacinsa ya ƙare,domin ba aurene dama na zama ba,kedai kijira dawowata inna,kafin na tafi zan tabbatar bata isa yimiki komai ba har na dawo,ni banyadda da wannan matar ba sam inna,mutanene ke ganinta ta arziki,amma jikina yana faɗamin sai an bincika garinnan kaf kafin a samu ya ita wajen shu’umanci,tana da baƙin ruhi a tattareda ita,wanda inajinsa idan mutum yana aiki da aljanu,ko kuma akwai shihiri a jikinsa”
Itadai inna Danejo duk abinda Bombee take faɗa tana jinta,amma batada ikon maida mata magana,har tagama sambatunta a cewarta bankwana takeyiwa innar tata.
Saida ta gama kafin ta tashi tafito daga ɗakin,lokacin data fito mlm Ahmadu bayanan ya fita,kokuma ya shiga ɗakinsa. Harara inna laari tasake mata itama ta rama,hadda nunawa da hannunta inta dawo zata yanke mata kai.
Inna laari tana ganin Bombee tafita a gidan tasaki wata ajiyar zuciya.
“Lallai tsugunne bata ƙareba,da sauran rina a kaba”
Ajiye wankin datake tayi tareda tashi tsaye,lelleƙawa tayi ta tabbatar babu kowa a kusada ita kafin tashige ɗakinta da sauri.
Gadonta na ƙarfe ta ɗaga tareda ɗakko wata baƙar tukunyah dakuma wani ƙaton madubi,wanda yayi mutum a tsaye tsayinsa.
Jinginashi tayi a jikin katangar ɗakin,kana ta buɗe jan ƙyallen da aka rufe bakin tukunyar dashi.
Wasu kalmomi tafara karantawa cikin wani yare mai kamada da dalasumai,kafin wani lokaci kuwa tukunyar tafara tafasa shuuuuu wani abu yana fita daga cikinta kaman baƙin hayaƙi.
Shiga madubin dayake gabanta yafarayi,wanda kana gani kasan ba madubine na Allah da annabi ba,domin koda mutum ya tsayah a gabansa baya bada hoto kaman sauran madubai.
Wata mata ce tafara bayyana a jikin madubin,tana ɗauke da jajayen kaya masu kamada na saƙi,ƙyaƙyƙyawace da kana gani kasan ba kyaune na Zahiri ba,sannan fuskarta tana ɗauke da kalar mugunta sosai,wanda baƙin kwallin datayi ado dashi ma yaƙarawa siffartata fitowa da ainihin mungun kallonta bayyana a fili.
Kallon inna laari take wacce take tsugunne a gaban madubin tayi sujjada tamkar taga kashi.
“Meyasa zakiyi ƙirana a yanzu ina tsaka dayin wani aiki?”
“Eh ranki yadaɗe shugabar matsafa ZILIYYAH nabar kowa nabiki ke kaɗai,dama wannan yarinyar ne da kikayi aiki a kanta tsawon lokaci,ta fitine ni kullum barazana takemin idan muka haɗu,wannan dalilinne yasa na saka Mijina korarta,to wani lokacin har a mafarki take zuwamin”
“Hhhhhh laari tun ba’aje ko ina ba harkinyi nadamar zabinki??,duk aikin daza’ayi miki zabi biyu ake baki,kike daukar daya. Lokacin dazan fanɗarar da yarinyar nan nasaka mungun halinta ya zaga duniyah,saida na cemiki shin na tura mata aljanu ko kuma na kasheta? Kika zabi na juyah tunanin ta,haka ma ga mahaifiyar ta,muncemiki mu kasheta komu nakasa ta,kika zabi a nakasa ta.
Jaririn da aka haifane kaɗai kika buƙaci a kasheshi mu kwashe jininsa,kuma munyi miki hakan”
Cikin rawar murya da shiga ha’ula’i Inna laari tasake ƙasƙantar dakai tareda cewa.
“Tabbas nina zaba kam,saboda a lokacin so nake su wahala basuyi mutuwar sauƙi ba labarinsu ya shafe,sona ke suyi dasunsanin shiga cikin gona ta nida mijina,amma yanzu ita yarinyar baza’a iyah kashemin itaba?”
“Wai meyasa kike manta sharadin da muke bakine,kinsan fah duk abinda kike mana na sakarci ƙyaleki mukeyi saboda jikin ƴar uwarki dakika bani nake amfani dashi ta fitowa a gaban ku…..idan na kashesu yanzu to fah duk abinda yake jikinsu kanki zai dawo dukka,shin kin yarda da hakan”
Saurin girgiza kai tayi tareda cewa.
“Ahah ranki ya daɗe banason hakan,shikenan babu dama a kawar dasu yanxu,dana sani da tunda aka kashesu ma”
“Hhhh karki damu munji barazanr da tayimiki,kuma inamai tabbatar miki dagaske takeyi zata aikata,yarinyar tana da ƙarfin ruhi,duk da baƙin Aljanu suna riƙeda ragamar tunanin ta,wani lokacin takan iyah turasu baya,amma zamu kafeta a garin dazata ce mu hanata dawowa harsai kinsamu abinda zamu umarceki ki samo.
Da sune kaɗai zamu iya amfani mu kasheta,batareda aikin damukayi musu yadawo kanki ba”
“Yawwa nasan babu abinda zai gagareki a faɗin duniyar nan(Azubillahi),to shikenan a kafeta a garin,nikuma koma menne zanyi ƙoƙarin samowa kafin ta dawo”
“Wata bishiyace datake rayuwa a Sahara,tanayin aƙalla shekara ɗari biyu a raye,sannan takanyi fure duk bayan shekara biyu,wannan shekarar tayi furenta,kuma nayi amfani dashi a wasu,dan haka dole saidai kijira zuwa nan da wani furen bayan shekara biyu tukunna”
Kana ganin fuskar inna laari kasan abinda aka faɗa bayyi mata,saidai babu yadda zatayi dole tayi jiran hakan. Koƙarin kawar da zancen tayi ta hanyar cewa.
“Uhm nace ba maganin farin jinin innayi fah har yanzu ba’a samu ba”
“Wannan kuma nan da wata shida zanyi miki magana,akwai abinda na shiryah akan ta,inajinta tamkar ƴa nima,ko kinmanta da ƙoƙarin dalasimaina aka samu cikinta….sannan kuma akwai alƙawarin damukayi dake gameda ita tun kafin haihuwarta…..!?
Shuru inna laari tayi tana zazzare ido,wanda yake nuna ta tuno wani abin tashin hankali daya faru da ita,saidai duk da hakan bata tanka dan tasan maganar matsafiyar gaskiyane……(toh fah yaya takene?)
“Hhhhhh nasan bazakice komai ba,saidai abu daya nakeso ki sani shine ba’a tsallake maganata koma waye,sannan ba’ayin yarjejeniya dani a saba,batun wanccar yarinyar kuma ki zuba ido gobe zata bar garinnan,ba jibi ba kaman yanda tace”
Jingina kanta tayi bangon ɗakin tana ɗan jijjiga haidar dayake kan cinyarta,baccine yafara daukarta,can cikin bacci taji ana cewa.
“Kibar garinnna bamason garinnan saikin bar garinnan zaki bar garinnan…………hhhhh mutafi bazamu zauna ba”
Buɗe ido tayi tareda tafe kunnuwanta guda biyun wanda maganar take shiga ciki,ta haddasa mata barazanar fashewar kanta da kuma ciwon kai mai tsanani.
Cize baki tayi har fatar bakinta tana fashewa saboda sakata datayi tsakanin haƙoranta.
“Ku dakata haka ya isahhhh!!!!!”
Tafaɗa da ƙarfi a cikin kanta ba’a zahiri ba,dan hakane kaɗai ta koyi control ɗin muryar datake zugata a cikin kanta wani lokacin.
Jin maganar bata daina bane yasa ta ajiye yaron dayake kan cinyar ta a gefe. Zaman dirshan tayi a tsakiyar gadon tareda rufe idonta kana kuma ta dunƙule hannayenta.
Tunani tafarayi tayanda zatayi blocking maganar da akeyi mata.
“Kudaina damuna kuna takurawa rayuwata,nasan turoku akayi domin ku fitar dani daga garinnan,saboda naje nayi mata gargaɗi koh,hmmm ashe dai tana tsorona. Babu wanda ya isa fitar dani daga cikin garinnan har saidai idan nice nayi niyyar tafiyah”
Bombee tafaɗa cikin kanta cikeda taurin zuciya,wata ƴar dariyah ce ta jiyarci kunnanta mai kamada munafurci.
“”””Haaaar idaaan muka cuutarr da wannnanan…..yyyyaaaarooonn maa baaazaaaki tafiiiibaahhhhh hhhhhhhhhhhh””””
Aka ƙarisa maganar cikin dariyar mugunta.
Saurin buɗe ido Bombee tayi tareda saukeshi akan ɗannata farincikin rayuwarta.
Aikuwa taga alama,dan lokaci guda ya callara ƙara tareda saka kuka a zabure.
“Ahah kubari kada ku tabashi zan tafi,amma fah sai gobe ba yanzu ba,dan yanzu dare yayi”
Haɗiye yawun baƙinciki tayi tareda cigaba da jijjigen ɗannata,dan kana gani kasan batayi niyyar tsayawa da wasan ba,saidan ya hau kan rayuwar ɗantane,ta yarda komai suyi mata akan su tabashi.
“Matsorata kawai,mai yin barazana da wani abun ma yana tsorone”
Bombee tafaɗa a hankali kan fatar bakinta.

Washagari da sassafe Bombee ta shiryah ita da yaronta suka kama hnayar barin garin gembu cikin motarta,saboda ko badan itaba tana tsoron rayuwar ɗan ta,yanzu babu abinda yake cikin ranta sai muradin rabashi daga cikin garin,saboda tasan sun riga sunsan shine masomin karya lagonta a yanzu.

Lubnah ce a kwance akan gadon ta na gidansu tana danne danne a waya, hankalin ta yayi nisa wajen hirar dasuke da ƙwayenta. Ƙara ƙwanƙwasa ƙofar ɗakinne yasaka jan tsaki tareda kawar da dogayen kitson attach ɗin take kanta,kana ta juyo ta kallo ƙofar.
“Miye kuma,ba yanzu kika sharw ɗakin kika fita ba?”
“Ahah hajiya ba wannan bane,wata mai aikice ta zo nemanki daga Gidan mijinki”
Saurin tashi tayi ta zauna tareda fitowa wajen,dan tasan bazata wuce Bishirah ba,dan dama kafin tahowarta jiya tasaka ta kawo mata rohoton duk abinda yafaru a gidan.
Aikuwa ita ɗince tana zaune a ƙasan carpet ɗin falon,tasaka hannunta tana wasa da zare zaren carpet ɗin.
Muryar Lubnah ce tasakata saurin ɗagowa tareda gyara zamanta kaman mai shirin karbar gafara.
“Yaya mai ya faru bayan tahowata daga gidan”
Lubnah tafaɗa bayan ta zauna akan kujerar dake gefenta,cikeda zumuɗin son jin abinda ya faru.
Bishirah bata kai ga magana ba wata dattijuwar mata tashigo falon,tadan manyanta,Barr Na’imah Hashim kenan,mahaifiyar Lubnah.
(Sorry a baya nace mahaifinta ne brr amma mahaifiyar ta ce,shi mahaifinta General ne babba a barikin sojoji Gen Abdu Manga)
Duk da ta manyanta,amma kanaganinta zaka san cewa anyi boko harda bokoko ma. Itama zama tayi a kujerar dake facing ɗinsu,laptop ɗin dake gefenta ta dauka ta ajiye a kan cinyarta,tareda gyara ɗan karamin glass ɗin dake idonta.
“Wannna kuma wacece Daughter?”
“Uhm mommy wacce nasaka ta dunga kaomin rahoton abinda yake faruwa ce,yanzu tazomin inaga da wani labari ne,ke ina jinki mai ya faru bayan na taho?”
Gyara zama Bishirah tayi jin an bata lasisin yin magana.
“Ai wato hajiya dazu naji wani zance wai an gyara anihin sabon part ɗin yallabai na gidan,a can wai amarya zata zauna,har yau ma’aikatanta sunje sun ƙawata part ɗin yadda take buƙatarsa. Sannan wai tunda wacce Hajiya ta taho da ita ba amaryar bace,amaryar bata zo ba sai gobe zata iso tukunna,kuma naji ance hajiya ma shakkarta take,yanda takeyin nan nan da yaran da suka zo dasu”
Zaro ido Lubnah tayi lokacin da mummunan labarin ya doshi kunnnenta,sabon part??? Ita bata koma part ɗin ba tsawo zamanta gidan sai wata kucaka data zo yanxu itace zata buɗe wajen?
Lubnah ta faɗa a ranta cikeda takaici.
Tashi kije zan biyaki idan na dawo,yanzu banida kuɗi a hannuna.
Tashi Bishirah tayi ta rawar jiki tabar gidan bayan tayi musu sallama.
Lubnah kaman jira take,tana ganin tafita tasaka kukan sakarci.
“Ahahahha mommy kingani koh,Allah zan kashe wannan uwar tasa daga ita har wacce ta aura masan,nagaji da kaicinsu danake sha gaskiya”
Hmmm karma ki soma,saboda bakida hankali kina ganin in wata matar tasa ta mutu baza’a zargeki ba ne,meyasa mahaifiyar sa bata aura masa Wannan yarinyar ba(Jawaheer),sai suka aura masa wata can daga wani gari,wacce bata san mai yake faruwa ba,saboda suna so itama ki kasheta ne,wanda baya zarginki ma daga lokacin yafara idan yaga mata uku sun mutu a jere. Kinga lokacin dazasu ɗaureki da igiyar da bazaki iya kuncewa ba,sai su aura masa ita suyi zaman ƙalau an kawar dake,dama suke shayi zan tsayamiki a shari’ah,amma daga lokacin da kika kashe wannan da kuma uwar mijinki to fah abin nima zaimin wuyah. Sauyah salon zamanki dasu zakiyi yanzu,karki kashe kowa,yanzu kiyi amfani da kissa bayan zulungum ma,ki tafiyar da abu tayanda babu mao zarginki,sannan idan sukaga baki kashe wannan ba,to zasuyi ƙoƙarin Jawaheer ma,wanda nasan kinfi tsanarta,a nanne zaki tafiyar da ita a boye batareda kowa ya sani ba,ke daka Kashe mutun shikenan gwanda ka haɗashi da abinda sai ya ƙwammaci ya mutu ma”
“Eh kuma fah hakan mommy to yanzu yakike ganin zanyi kenan”
“Keba mace bace,bakisan yanda zakiyi komai sai kisa kawai,saboda matsoraciya ce ke,bakya tunkarar abu saidai kaimasa hari ta baya,halin ubanki ne sakk dake”
Lubnah taji haushin maganar mommyn tata,amma kuma tasan gaskiya ta faɗa,ita bata jurar bin abu a hankali,takanyi duk abinda zuciyarta ta raya mata ne.
“Toh…. Toh…kinaga fah nadawo gidannan ma har yanzu bai zo nemana ba,taya zan koma kenan?”
“Haka dai zaki ƙare,nace miki komai yafaru ki zauna a gidanki kiga mai akeyi,sannan ki kasa ki tsare amma kinki ji,saiki dawomin kina min kukan sakalci waike kin gaji,kinada kafafu biyu ai kiyi amfani dasu mana ki koma”
“Toh mommy yakike so nayi,aure fah wai ya ƙara,kuma nace yasaketa yaƙi sakinta,idan nayi masa magana bayajin maganata,kaman yanda abbah yake jin taki,narasa yanda zanyi dashi,sainayi da gaske wani lokacin nake samun kansa,gashi inasonsa banison wata a kusada shi,kiji wani sabon tsirin wai a sabon part zata zauna”
“Ke ma saiki koma gobe da wuri ko rigata komawa,ko wanda tazaba kikeso dole tafita kishiga tunda kece babba a gidan,yanzu kiyi shiri ki koma gobe da safe,da badan akwai abinda nakeson haɗamiki ba,da a darennan ma zaki koma”
“Yawwa mommy,zaki kaini wajen bokanyarki,ni wancan zulungum ɗin yanzu bani sonsa sosai”
“Ahah ni kaɗai zanje bazaki bini ba,har yanzu bakiyi wanann girman ba na ganinta,sannan kinsan kafin ki yakice zulungum a jikinki zaki daɗe,tunda yasan yana samu daga gareki,kuma karki damu shima aikinsa yana ci sosai,kece ma zaki bawa wasu labari”
“Ni naso yazo dakansa ya ɗaukeni,baya wai na koma dakaina ba,bari zan ƙira Yaseerah tazo mu tafi tare da safen,kutt harma wani ta zabi part banida masaniya”
“Hmmm dama ki tsayah kallon ruwa,shidama kwaɗo ai ƙafa zayyi miki”
Barr Na’imah tafaɗa tareda cigaba da abinda take a labtop ɗin gabanta.

Har Hilyaan tafara bacci da daddare taga ƙiran Bombee,dagawa tayi tareda yimata sallama.
“Hello inace dai lafiyah,ko haidar ne ya hanaki yin bacci kai?”
“Ina cikin abuja yanzu haka,na sauƙane a hotel,da safe zan shigo gidan,dan haka kituro min address ɗin zanyi installing ɗinsa a kan Motata zuwa safe”
Tashi Hilyaan tayi ta zauna cikeda mamaki tace.
“Abuja kuma,meyasa kika taho yau ina sai gobene zaki dawo”
“Menene kuma na razanar shin ban isa sanja ra’ayi bane saikin tuhumeni iyee,ko akwai abinda baku gama bane kike tsoro”
“Ahah mun gama komai,mun zabamiki part ɗin dayake gefen lambun wajen,ta ƙofar baya zaki shiga,sannan yanada girma daidai gwargwado,mun shuka wasu fulawoyi ma wanda bazasuyi wata biyu ba zasu girma,amma dan Allah meyasa kika taho yau,ko kin matsu kai kiga angonnaki ne?”
“Hilyaan zan…….kidaina shiga hnacina fah da zancen rijalun ɗincan tamm,batun dawowata basai kinjiba daliline boyayye,wai hadda fulawa kaman nace muku ina buƙata?”
“Kai anty maryam nifa dama nasan zaki ce haka,amma ki bari saikin gani da idonki,ina tsoron shiga fah Bad side ɗinki,anyi komai yanda ya dace. Matar tasa ma naji ance wai batanan tunda taji zancen ƙarin aurensa”
“Tafiya kuma,batasonsa ne ta tafi tabarshi,ko kuma taji tsoro? Ashe ma ƙaramar ƴar isaka ce”
“Amma nikuma nafi zaton ko tafiya tayi tasake shiryowa zama dake,tunda ance bata ragawa kishiyoyinta”
“Hmmm ba shiryawa ba intanaso ta ɗauko mai yimata aikin ma su dawo gidan,hakan bai shafeni ba,tun bansan kaina ba ake bankamin,dan haka an shanin na warke,ki bari ina shigowa cikin gidan da safe”

To matan fah zasu shigo a tare kenan,ku jirayi na gaba domin haɗuwarsu a bakin ƙofar jaan estate.😂😂😂

Page 🖤5••6🖤

“Wai luby lafiyah kika tasoni da safennan wai zaki koma gidannan,haba bansanki da wannan,wannan ba girmanki bane mana big elegant woman”
“Kimin shuru Yaseerah eh haka naga dama,komawa zanyi,dama ai bashi ya koreni ba nice dakaina na taho”
“Kutt wannan yajin fah ko sati bakiyi ba shine zaki koma,naga wani lokacin har wata kinayi a gida,ko kai dagaske dan kina tsoron wannan matar ne kada ta mallakemiki miji”
“Kaii wai Yaseerah da wanne zanji ne,dake koda mijina,ko kuma da mommy tada koroni iye,koma mai zai faru kekam ki zuba ido mana kigani,inda tani ce da tuni na kasheta tun kafin ta shigo cikin gidana”
“To meyasa kika fasa hakan”
“Mommy ce ta hanani mana,a cewarta sunyi hakanne domin na kasheta su sakani cikin tarko,idan inaso na kawar da ita saidai na yi amfani da kissa da kuma aiki a boye,wanda ba kowa zai kulada abinda na aikata ba,kaman haɗata da wani ciwo,saka mata wari ko kuma saka wa Jabeer tsanarta,ke yanda nakeji ma koda ban kasheta da asiri ba zan yi hayar ƴan fashi wanda zasu shigo suyimin daga daga da ita…..”
Tana maganar ne numfashinta yana cikowa saboda tarin baƙin ciki da tsanar amaryar mijinnata da take cinta.
“Kinga ki kwantar da hankalinki haka mana luby,batun kawar da ita wannan dolene,tunda har tayi nasarar shiga rayuwarki,bazamu taba barta ba,yanzu dai mu shiga gidan muga sabon part ɗin daza’a kaita,nasan wannan tsohuwartata ce tayi hakan saboda tana tsoron abinda zakiyi mata.”
“Nasan dama shine dalilin,sannan a cikin wajen a kwai part din dayafi girma,yaɗan shiga cikin lambun gidan,sannan yana ɗan nesa da sauran parts ɗin,kaman anyishine domin babbar matar dazata zauna a wajen,wanda nce kenan mamallakiyarsa”
“To yanzu idan mukaje kuma taɗauki wannan part ɗin fah,ya zamuyi mata kenan”
“Hhhhh har tambaya kike ma mai zanyi mata,kaff gidannan banga mai sakani barta ta zauna a wannan wajen ba,da banyi niyyar zama a wajen ba,amma tunda naga tace anan amaryarsa zata zauna,nima a can zan zauna,kuma wannan part ɗin nakeso”
Ƙarisa maganar tayi cikeda shirin abinda zata aiwatar idan ta shiga cikin gidan.

Daidai isowarta ƙofar gidan,wanda take da tabbacin shine gidan da take nema,saboda nan Gps ɗin motarta ya nuna.
Kashe ƙarar motarta tayi tana kallon get na shiga estate ɗin. Ko ba’a faɗawa mutum ba daga ganin mashigar zai tabbatar da cewa wajene babba kuma ƙawatacce sosai.
Ƙara horn ɗin da ake mata da motane yasaka ta ɗauke kanta daga kallon mashigar ta maidashi kan motar dake gabanta.
Farar mota ce mai kyau tashiga taro ta faso kai ta shigo wajen,har Bombee tayi niyyar jan motarta baya domin bata damar shigewa,saikuma taji ana ta jera horn akallah kusan biyar,tun ma kafin ta motsa motar tata.
Komawa tayi ta zauna shuru ta zubawa motar gabannata ido,batareda tasake motsawa ba,jira take taga wanne shafaffe da mai ne yake tunanin zata yimasa abinda yake so ta ƙarfi.
Bayan kaman a ƙalla minti biyar,wanda zuwa sannan lubna tayi horn yafi sau a ƙirga,jan tsuka tayi tareda bugar sitiyarin motar da hannunta,idanuwanta har sunyi ja dan baƙinciki.
“Wai wannne ɗan***** ya taremin hanyar shiga ne,waye mai kuma yake taƙama dashi”
“Inaga saidai ɗan gidann mana,abin da rainin hankali kam a ciki,amma bari naje na duba”
“Ahah yi zamanki basai kinje ba,daga gani baɗan gidan bane,domin bansan mai irin ƙirar motar nan ba”
“Ahh a yanda suke kam ko jiya zasu iya order sabuwar mota,kokuma Abdulkareem ne kai ya dawo?”
“Ba Abdulkareem ba inma Abdullahi ne dakansa bazan ɗauki wannan rashin mutuncin ba,yaushe har lagona ya karye suke wannan wasan dani”
A zuciye lubna tafito daga motarta ta tunkari inda Bombee take zaune a cikin tata motar.”
Kwantar da sit ɗin drivern tayi tareda yin miƙa,lokacin da taga lubna ta tunkaro inda take,dama jira take daga wanene a cikin motar da har zai mata waɗannan horn ɗin kaman ya samu dabba akan hanya.
“Ohh dama kece mai yimin horn ɗin mrs Jabeer? Banyi tsammanin haɗuwar mu yanzu ba,wow very interesting and nice meet”
Bombee tafaɗa cikeda nishaɗi kana ta karisa maganar da hamma.
Ƙwanƙwasa glass ɗin kusada ita taji lubna tayi,nan ma saida tayi shan ƙamshi na ɗan wani lokacin kafin kafin ta sauƙe glass na motar.
In ana magana takaici ranar Lubnah ta shaƙa,da taga macece ma cikin motar,kuma dan iya shege a kwance ma take batada niyyar tada motar,wato ƙalau motar ma take da gangan taƙi tayar da ita ta matsa mata.
“Wacece keee!?”
Lubnah ta faɗa tanayiwa Bombee kallon ƙasa da sama,wacce idon yake rufe kaman bada ita take ba,inda bata buɗe mata glass ba sai tayi tsammanin bacci take,ji take kaman ta saka hannuwanta ta cakumo wuyanta tacikin motar.
“Mai kike taƙama dashi da har ina miki magana kina ji iyee,waye ubanki cikin garinnan,koma menene alaƙarki da gidannan bai dameni ba,amma ki sani ko ƴan gidan nafi ƙarfin su rainamin hankali ballantana kuma keh”
A kasalance Bombee ta buɗe idonta tajuyo ta kalli Lubnah,a yanayin data juyo cikeda jan magana,sai ya ƙara fito da ainihin Kyawunta.
Gaban Lubnah ne ya buga datayi arba da fuskarta,sai taga kaman ta taba ganin mai kama da ita,amma ina ga kamace,ta faɗa a ranta.
“Ku mutane kunada damuwa,dole saini ƴar wanice kafin zanyi abinda naga dama,akwai wanda aka hanashi motsi yanda yake sone,to meyasa sai ƴan wanene zasuyi yanda sukeso,sha kuruminki ni ba ƴar kowa bace,amma tunda kikayimin horn fiyeda ɗaya kafin na matsamiki,to a lokacin na yanke hukuncin sai kinyi minti talatin kina tsaye kafin ki shiga gidannan,in kinga na matsa a wajennan to lokacin dana yanka ne ya cika,ko kuma mota mai haƙora kika ɗauko ta dauƙe motata,amma idan biyunnan wani bai faruba,tsayuwar banza kikeyi a wajenann,dan abinda kike bazai sakani sanja ra’ayina ba,gwanda ma ki koma motarki ki zauna”
Bombee tana kaiwa nan ta bayaninta ta maida glass ɗin motarta ta rufe.
Wata jijjiga Lubnah tayi,tama rasa mai yake mata daɗi,wai wannan yarinyar ce take mata magana haka,tukunna ma wajen wa tazo a cikin estate ɗin,yanayinta ne yasa tayi tunanin wataƙila baƙuwar Lylah ce,sai kuma wata zuciyar tace ta ƙira securtyn gidan.
Allah sarki bawan Allah,chiep securityn yana ɗagawa lubna tafara balbaleshi da masifah,ta inda take shiga bata nan take fitaba.
“Uban me kukeyi,menene ma aikinku a gidannan,maza kazo da kanka ka gani,wata banza ta hanani shigowa ciki,da saka motarta a bakin ƙofa,kuzo kuyimin waje da ita”
“Ranki ya daɗe kiyi haƙuri bari muduba CCTV camera,inaga kuma wajen wani tazo a cikin gidan,kada muyi mata magana yazama matsala”
“Matsala… Ina ruwana da wajen wa taxo tunda ta nuna min ta isa dan tasamu shiga wajennan sai tasan matsayinta yanzunnan,ku zaba shin fitar da ita daga baƙin ƙofar nan ko kuma Aikinku?”
Ai tun kafin Lubnah tasake cewa wani abun yayi saurin cewa.
“Aikina na ɗauka Hajiya,gani nan zuwa dakaina yanzunnan basai anjima ba”
Kashe wayar tayi tana jiran isowar tasu kaman yanda suka faɗa.
Yaseerah ce ta fito itama daga motar tazo inda lubna ke tsaye tana jijjiga kaman an jona mata wutar lantarki.
“Ƙawass mai yafarune,waye a cikin motar ko baci tayi?”
Duk maganar datake Lubnah bata kulata ba,har sannan tana sama,ƙarar fitowar motar securityn ta jiyo,saidai suma bayadda zasuyi su fito,dan Bombee ta tare hanyar fitowar daga waje.
Sagern Hudu ne ya fito daga motar,wanda shine shugaban security na estate ɗin gaba dayah,wajen motar Bombee ya nufah tareda ƙwanƙwasa mata ƙofah.
Zugewa tayi tareda haɗe fuska tace,
“Wai menene kuka dameni,idan kukayi haƙuri ma minti talatin na cika zan matsar da motata,basai kun takurawa rayuwata ba”
Kallon mamaki ya bita dashi tareda cewa.
“Kee wacece ke,shin tukunna ma mai kikazoyi gidanann,danni ban taba ganin mai kamarki ba a wajennan”
“Kai kai wai duk gidannan haka kuke ne,kowa inzai buɗi baki wacece ke,dole saini watace zanyi haka,kenan ban isa ɗaukar mataki ba idan akayimin wani abun?”
Tsawa Lubnah ta dakawa sagern hudu daga inda take tsaye,
“Lallabata ma kakeyi,yanzunnan kuyi waje da itah,ko tsoronta kukeji kai”
Sagern hudu yanajin maganar Lubnah ya ƙara ƙaimi tareda ficcina ƙananun idanunsu.
“Kinga madam koma me kike takama dashi ki fito daga motar nan yanzunnan,a matsar da motar”
“A kuda kuke so na matsar da mota meyasa kuma zan fito?”
“Ahhh wannan kuma madam daga baya kenan,dole zaki fito ki faɗamana menene dalilinki na zuwa nan wajen”
Shuru Bombee tayi bata bashi amsa ba,daidai lokacin da ta ƙayyade suna cika taga hannun sagern hudu yana shirin cakumo kirjinta,cikin zafin hannu ta riƙe a hannunsa tareda yimasa kallo mai ɗauke da alamar tambaya.
Idonsa tagani yana kallon kan ƙirjinta,tashi daya ta gane ba iyah niyyar fitowa yake da ita daga motar ba,harda wani mungun nufinnasa ma.
Yatsun hannunsa guda biyu na ƙarshe ta rike ta malƙwasa,nan da nan yabada ƙarar ƙass ta ƙaryasu.
Ƙarar azaba ya saka tareda fizge hannunsa yaja gefe yana kallonta cikeda mamakin karfin dayaji ta saka masa.
Key tayiwa motar ta bata diri,hanyar get ɗin ta nufah inda sauran securityn suke tsaye,nufarsu tayi da niyyar bi takansu ta shiga gidan.
Da farko basuyi tunanin zata cigaba da tafiya ba duk da sun tsayah….amma ganin tsakaninsu baifi taki ɗaya ba,kuma bata da niyyar tsayawa yasaka su bajewa da gudu,ɗaya kam har yatsansa t taka na ƙafah.
Tsalle yafara ya ihu tareda bin motar tata da kallo,wanda har ta bace a cikin gidan.
Saida ta ƙule tukunna sagern hudu ya juyar da kallonsa ga Lubnah,wacce itama tatsayah tana kallon abinda Bombee tayi.
Hannunsa yasake ɗunlewa tareda cewa.
“Hajiya kiyi haƙuri bari mushiga cikin muga wajen wa tazo,karki damu yanzu zamu koreta”
Bai tsaya jin abinda zatace ba yashiga motarsu suka shiga cikim gidan.
Itama Lubnah ganin cizon yatsa bazai kaita ya sakata shiga tata motar itada yaseerah suka bi bayansu.
A bangaren Bombee kuwa hankali kwance take tafiyah akan titin dake cikin estate din,har ta isa ga bakin part ɗin su Hajiya zeenah,dan shine a farko daga an shigo da kuma na su Lylah daga ciki kaɗan.
Parking motarta tayi a wajen da taga wasu motoci,wayarta tafitar tareda dannna sunan Hilyaan.
Ringing biyu da daga tareda yimata sallama daga ɗaya bangaren.
“Kinga babu bata lokaci sonake na kwantar da yaronnan,ya gaji da kwanciyar mota ga bayanin daɗi,ki fito ki nunamin part ɗin dazan zauna,ko kimin kwantance idan wani abu kike,zan wuce daga nan”
“Lahh anty maryam harkin shigo wai,kina ina kenan a cikin gidan?”
“Uhmm ina bakin wani part wanda shine na farko idan aka shigo ciki”
“Ohh part ɗin Hajiya zeenah kenan,muna ciki ai barina sanar mata da isowarki,mijinnaki ma yana wajenta yanzu ya shigo gaishe da ita”
“Kinga ni Hilyaan bana son wannan maganganun wanda naga kin koya tun zuwanki wajennan,inma wani abun suka baki kika sauya ni bai dameni ba,kawai ki fito ki nunamin masauƙina inason na huta,badan hotel ɗin dana sauka ana event a wajen ba maizai fitar dani da safennan kamar na ciwa wani bashi?”
“Sorry sorry Ogah ganinan fitowa yanzu nan karki damu”
Bayan kashe wayar Bombee a ƙalla tayi tsuka sunfi uku,ƙarar motoci taji sun faka a kusada ita,sa alama mutanen ta ne na bakin get suka iso.
Tana kallonsu dukkansu suka fito daga motar,shikam sagern hudu har sharce yake,saboda azabar data haushi na gurɗiyar yatsunsa guda biyu.
Fitowa itama tayi daga cikin motar tana kallon Lubnah wacce take tsaye tana zabga mata harara kaman zata cinyeta da ido.
“Ohh wato ke baƙuwar matar nan ce,no wonder kikejin haushina duk da bansanki ba mana”
Lubnah tafaɗa tareda yin murmushin gefen baki .
“Amma kaman banice dajin haushinki ba,ina fah kece kika dau da zafi daga farko,kuma har yanzu ma kinanan dajin haushinnawa,shin bakya ganin kallon da idanuwanki suke yiminne madam luban,ko aikamin kallon suke batareda izininki ba kai……..ohhh kuma akan kawai na hanaki shigowa ciki sai lokacin dana shata sun cika,abin burgewar kuma saida suka cika kika shigo ɗin,common ƙaramar dokata kin kasa karyawa inaga babba kuma…….chchchchchc am feel sorry for you”
Bombee tafaɗa cikeda sigar zolayah,harda wani cuna baki kaman na kifi,hakan datayi ne lokacin ɗaya mutum zai dauka innocent ce.
“Sannunki da isowa”
Hilyaan tafaɗa fuskarta ɗauke da fara’a lokacin da suka iso wajen da take itada khamees.
Daga kai Bombee tayi wa Hilyaan kafin ta kalli khamees cikin kame fuska,kaman ba ita ke zolayar Lubnah yanzu ba.
“Barka da isowa yakk ya hanya”
Khamees ya faɗa cikin girmamawa,murmushi Bombee tayi masa tareda cewa.
“Hanya normal ne kasan dawar,ykk hope komai ya tafi normal koh?”
“Yeah komai kalau,amma nayi mamakin isowarki da safe haka”
Wani rolling manyan idanuwanta tayi,wanda hakan yasake bawa ƙwayar idanuwant show up,kafin tace.
“Jiya na shigo garin,so na tsayane a hotel badan hayaniyar dasuke yahanani sakewa ba,da bazan shigo yanzu na sai yamma”
Hajiya zeenah ce dake tsaye tayi magana cikin dan ɗaga murya yanda kowa zaijita a wajen,harda su Bombee da suke magana itada mutanenta.
“Toh amaryarce ta shigo da wuri haka,hala a gari kika kwana amma?”
Tsayawa tayi da maganar da suke da khamees ta ƙarisa inda Hajiya zeenah ke tsaye itada su Madeenah,harda Jabeer wanda ke tsaye a gefe kaɗan yana waya,saidai duk abinda ake akan idonsa a wajen.
Doguwar rigace baka a jikinta har ƙasa irin Butique ɗinnan,tasaka belt a tsakiyar rigar,wanda ya fitoda anihin shafe ɗinta,dama gata doguwar mace,mayafi tayafa akan rigar shima baƙi.
“Eh na iso ina fatan dai hakan bai zama muku matsala ba ina,irin na al’ada haka nan”
Bombee ta faɗa da ɗan murmushi kaɗan sannan kuma tana nunawa da hannunta.
Cikin dariyah irinta wayancewa Hajiya zeenah tace.
“Ahhh ehh babu komai,bari a rakaki an gyara komai ki huta kafinnan saiki shiryah kizo mu gaisa”
Daga kai Bombee tayi tareda kallom Hilyaan.
“Mu tafi koh kina tsaye”
Kallon Jabeer tayi juyawar datayi,idanuwansu ne ya sarqe da juna wanda shima kallon wajen dayayi kenan,wani kallon ƙasƙanci yayi mata yana bin kayan jikinta da kallo kaman yaga karya. Hakan ya batawa Bombee rai,amma sosai ba dam dama tayi tunanin hakan. Kallon kayi kaɗan tabishi dashi tareda juya idonta zata wuce,kamar irin takalli abinda bata buƙatarsa a rayuwarta tayi masa kallon kuskure.
Har suka shiga mota suka nufi sashen da ainihin part ɗin Jabeer yake Lubnah bata motsaba,yau taga wani abu waishi tashin hankali.
Sai bayan sun bar wajen taja wani mungun dogon numfashi tayi baya zata fadi.
Yaseerah ce tayi saurin riƙeta ganin tana shirin yin suman tsaye.
“Kambuuuuu menake ji kuma nake Yaseerah ni Lubnah,anya kuwa ban mutu ba ina raye??”
“Wanne irin mutuwa Lubnah,kina raye da ranki sarai,ki kalli kallon da Hajiya zeenah take miki ma,dan haka ki saita kanki karki nuna mata karyewarki nan da nam”
Ɗaga ido tayi ta kalli Hajiya zeenah wacce take yi mata kallon kaɗan ma kika gani daga aikina. Kafin ta juyah itada yaranta suka koma ciki.
“Yaseerah muje part ɗin da waccar matar ta nufah,taci nasara ta farko idan taci ta biyu zataga gadon baccina,dan haka yanzunnan ki wuce dani part ɗin basai anjima ba”
“Hmmm Lubnah kibari ba yanzu ba,saboda bakida wani makami a hannunki yanzu dazaki tunkareta,dan naga babu alamar tsoro a fuskarta,amma idan kika samo Jabeer a hannunki zuwa goben,shida kansa zai sakata tafita a ciki tunda zamansa takeyi”
Dahaka Yaseerah ta samu da ƙyar ta lallaba Lubnah ta yarda da shawarta suka bar wajen suma.
Shima dama Jabeer tun haɗuwar da sukayi a hanya shida Bombee da zata wuce yashiga motarsa ya bar gidan,cikeda sabon wani tashin hankalin dayasan zai dawo ya sameshi ko ina yaje.
A zaune take ta tattara hankalin ta gabaɗaya wajen bawa haneef break fast ɗinsa,kasancewar daƙayar yakesha saida dabara tukunna.
Mai aikinta ce ta shigo falon da rawar jikinta fara gaisheta.
“Ahh indo kece da sanyin safiyah haka,wata sabon gani kenan,ban ƙiraki ba kikazo da wur”
“Uhm Hajiya Lylah dama wani abune yake zagawa a cikin gidan,shine nace barinazo na shaida miki nasan baki sani ba”
“Mai ya faru haka da safennan, ince dai ba wata satar mai aiki tasake yiba?”
“Ahah ko ɗaya ba wannan bane,dama amaryar da Hajiya zeenah ta aurawa Yallabai ce ta zo gidan yanzu da safennan,naji ma har tana maganar wai a hotel ta kwana jiya kafin ta iso gidan”
“Mee amarya da safe,hotel dai,yau itada wa suka zo haka har suka kwana a hotel,tana amaryar da aka ɗaura aure kwana uku da suka wuce?”
“To kowama haka yace,kuma abin mamakin ma bata gaisheda Hajiya ba,shikansa yallabai bata kulashi ba,kuma naji Sagern hudu yana cewa wai ta takawa yaransa yatsan kafa da mota a shigowa”
Shuru Lylah tayi tana jin abinda indo take faɗa har takai ayah kafim ta sheqe da dariya tana cewa.
“Hhhhhhh kice Hajiya zeenah ta ɗebo ruwan dafa kanta,wannan shi ake ƙira da an gudu ba’a tsira ba kenan.
Kinga bar wannan zancen bana nan bane,bari na je sashen Iyah sayyada na sanar mata,cigaba da kulamin da Haneef kafin na dawo.
Tana gama faɗin haka da rawar jiki ta nufi sashen Sayyada-tateen,cikeda zumuɗin yafa mata wannan labari dataji,wanda tasan idan taji ba ƙaramin daru za’a yi a gidan ba,dan akwai ta dasan mata masu al’ada da kuma tarbiyya,idan taji irin wacce Hajiya zeenah takawomusu cikin zuri’ah,za’a kwashi ƴan kallo.

Page 🖤7••8🖤

Lokacin data shiga Sayyada-tateen tana zaune akan carpet ɗin falonta,da kwanon tuwon semo a gabanta miyar kubiyah,kana shiga warin yajin daddawa zai bugi hancinka.
Labari suke tayi da wata mai aikinta wacce take itama dattijuwace ta manyanta,labari suke tayi tana warfa lomar ɗumame hankalin ta kwance kaman tsumma a randa.
A bakin ƙofah Lylah tayi sallama tareda shigowa cikin falon,kallo daya Sayyada-tateen tayi mata tacigaba da taɗinta wanda sukeyi akan Ruwan kogi na ƙauye.
“To dakika shigo bazaki zauna ba kika tsayamin akai kaman naci miki bashi,mai ya kawoki wajena ma da sanyin safiyar nan oho,dan nasan ta Allah bata kawoki ballanta ta annabi,saidai ta allaro”
Duk sababin da Sayyada-tateen takeyi babu wanda Lylah ta tanka,don ba wannann ne ya kawota ba,burinta shine bata Hajiya zeenah a wajen Sayyada-tateen ɗin,ita kuma tasamu shiga sosai,ta hakkanne take ganin zata fara takunta na farko,wajen karbar ragamar gidan daga hannun ta.
“Uhm iyah ya ƙafar taki,ina fatan tayi sauƙi koh”
Miƙa ƙafar Sayyada-tateen tayi tana kallonta,wacce take luwai da ita kaman bata tsofi,magana tayi da tuwon a bakinta.
“Hmmm ƙafata bazata durƙushe da wuri ba,domin nayi mata horo mai tsanani na tafiyah,dan daga ƙyauyenmu har Samunaka nake zuwa a ƙafah…..ohh wato soma kuke nima na koma kaman Aliyu ku samu yadda kuke so ko,ta Allah to ba taku ba ehe”
“Ahah iyah niba wannan ne yakawo ni na,dama wani zancene nake tafe dashi mai muhimmanci wanda naga yakamata ki sani”
“In ma wannan zancenne da audillahi yayi min na zakiyi aiki a company bazan yarda ba,nice nan nace ban yarda ba,inkuka shiga aikin maza wazai kuma rike muku gidan,matan da suke gidannann bazasuyi aikin gwannati ba,dan kunka daulah bazaku kawomana tsarin nasara ba sam….. Yo ke Laure mai za’ayi da matar datake aiki a wajen maza,mu zamanin mu ina muka san haka sai su,su a dole ga ɗaliban nasara”
Shuru Lylah tayi tana kallon Sayyada-tateen,gaba ɗaya ta hanata tayi mata bayanin abinda ya kawota,in tafara magana saita cafe tayi wani layin daban,abin duk ya isheta.
“Iyah nifah ba wannan ne yakawoni ba,Hajiya zeenah tana can ta aurowa Jabeer wata mata daga can Gembu,yarinyar bata san tarbiyyah,yanzu haka zancen danake miki yanzunnan shigowarta cikin gidannan,wai tun jiya tabaro garinsu ita kaɗai,a hotel ta kwana na cikin gari,yau kuma tashigo cikin gidan. Ko Hajiya zeenah bata gaisar ba tanufi sashenta,shikamma mijinnata aka ce koh Kallonsa wai batayi ba,har fah mai aiki ta takawa ƙafa a shigowarta”
Shuru Sayyada-tateen tayi da kunne tanajin maganar da Lylah take da zubomata,wanda ta tariyo da wajen mai aikinta indo.
Tana gama bayanin Sayyada-tateen ta tafa hannu tafara sallallami.
“Lahaula wala ƙuwata yau ni Sayyada inagani abu,ke laure wai wannan zance haka yake?”
“Eh ƙwarai kuwa Hajiya sayyada,ɗazu kam naji ma’aikata suna maganar shigowata nan wajenki zan kawomiki yaji”
Shuru Sayyada-tateen tayi dan yanzu tarasa ma kuma abin bafah,a jima tace uhmm……in anjima tace uhmmm. Sudai sunyi shuru suna kallonta sai ajajjaba abin takeyi.
“Wannan shine uhm inji kuturu,ke La’ilah(Lylah),tashi tashi muje yanzunnan ki rakani sashen ita zeenatun naga yarinyar,bazan lamunta ba,wannan ai shine iya shegen wai layyah da kare,muje ki rakani yau zata san takawo mana tantiriya zuri’ah,yo ko ƴar aikice ai ban lamunci wacce zatazo ta ruguza tarbiyyah ba,ballanta matar gida,hakan ma kuma ta Jabiru,shida yake babba a yaran gidan. Abin ai zai mana yawa shege da hauka,ga wata can bamu gama hucewa da tujararta ba,za’a sake takalomana wata kuma,so ake a maida min gidan ƴaƴa sansanin barikin taƙadarun mata?”
Tana tafe a hanya tana sababi,itadai Lylah bata ce komai ba sai binta take a bayah,banda dariyar jin daɗi ƙasa ƙasa babu abinda take.
“Ke la’ilah wai ina baban gidanne da jikinsa?”
“Kai iyah,nifah sunana Lylah,miye kuma wani la’ilah kaman zakiyi salatin,shekara da shekaru amma kinƙi kama sunan common suna”
“Kee Butar Ubaki,miye kuma comon wato zagina kikayi koh,dama kema bawani son ki nake ba,saida na hana audinllahi auroki ya tuƙe,da ƴar kyauyenmu ya aura da tuni suna nan da yaransu ina,Amma yaje ya auroki kin Haifi ɗa kaman gammo duk a kanannaɗe,ke anya kuwa Iskokai basabin danginku ma?”
Harara Lylah ta makawa ƙeyar Sayyada-tateen,wacce take gaba tana tafiyah tinkis tinkis sai surutu take zubawa kaman rediyo,dan takaici ma shuru tayi bata tanka mata ba.
Hajiya zeenah ta tashi kenan daga dinning zata shiga ɗakin ta Sayyada-tateen ta rafka sallama a ƙofar falon.
Maleekah ce ta taho da gudu tareda hugging ɗin Sayyada-tateen.
“Ohh my dear kakus,biyoni kikayi kinga banzo ba?”
“Hmm ai barni ɗiyar albarka,ba biyoki nayi ba nasan ai zaki je,wajen wannan tujararriyar uwar taki nazoni,naji wani mummanan batu yana zagawa”
Cuno baki Maleekah tayiwa Sayyada-tateen,dan dama daga ita sai Abdulmaleek,sukadaine ke shiri da ita a gidan.
“Haba kakus kodanni bazaki daina yiwa mommy haka bane,zanyi fushi dake fah”
“Ke kijim yarinya,yau ɗin hadewa zakiyi da iya kinunamin ni barece,yo yi fushin mana ai inada Audu ma idan kika tafi,bariki ga na zauna kafar nan tawa sai a hankali”
Kujera ta samu a falon ta zauna,gyalen dayake wuyanta tacire ta ajiye tareda kallon Hajiya zeenah.
“To haziƙa mandiyah babu iso kuma babu sannu da zuwa,gaisuwar ma saina roƙa ko me?”
Matsowa inda take Hajiya zeenah tayi tareda gaisheta,bata amsa gaisuwar ba dan dama ba ita ta kawo ta ba.
Ɗauke kanta tayi tareda kallon Madeenah wacce take tsaye tana kallonsu,dan ita dama bakasafai take shiga shirgin mutum ba ,inya shiga natane dai bazaiji da daɗi ba.
“To sarauta nima sarautancin zakiyi min,narasa cikinki ke da jabiru wayafi iyah shege”
“Hmmm kinga iya ni makaranta zan wuce inada defend dazanyi kanki ake ji,inna gaisheki ma naga ba amsawa kike ba,ina san gaisuwata saina ajiyeta saboda gaba”
Daga haka ta saƙala jakarta tabar falon,dama iliyah yana jiranta a mota.
“Ke zeenatu wajenki nazo naji dahirr daga bakinki,shin da gaskene kin aurowa Jabiru taƙadariyar mata? Kuma bada izinin kowa ba,bansani ba dangi basu saniba,yaushe yaron yazama naki ke kaɗai,a iska aka miki cikinsa bashida uba?. Wai kekam wacce iriyar uwace kam,kinfiso yaronnan yayi ta fama da bauɗaɗun mata”
Shuru Hajiya zeenah tayi tanajin Sayyada-tateen tana ta masifah,itadai batace komaiba.
“Kiyi haƙuri iyah yanxu kam koma menene yariga ya faru,sannan a matsayina na uwarsa inada dalilina akan hakan,saboda in matsala ce ba a taimakonka,in kayi ƙoƙarin gyarawa kuma sannan za’aje ana zundenka a gaba,ko kunya ba’aji”
Takarisa maganar tana kallon lylah,wacce take zaune a kujera tanajin abinda yake faruwa.
“To maganin haka iyah a kiramiki yarinyar mana ki ganewa idonki da kanki idan ƙarya akewa mutum”
Lylah ta fada da biyu,dan itama dama tanaso taga ya yarinyar take da idonta.
“Hakane kam zancenki la’ilah,ke Maleekah kije kice mata ina ƙirnata yanzunnan a nan sashen tazo ta sameni”
Amsawa Maleekah tayi tareda toh,ta fice daga falon.
Bayan kaman minti talatin suna zaune tadawo daga inda aka aiketan.
Shuru tayi tana kallon wanda suke falon tana zare ido,alamar taga abinda yashiga hankalin ta,tsaida idanuwant tayi akan mahaifiyar ta,tareda yimata alama da ido kan tayi magana? Ɗaga mata kai tayi da eh,wanda hakan yasa Maleekah tamayar da idonta wajen Sayyada-tateen,wacce tayi ƙamo tana jira taji mai za’ace.
“Uhmm Iyah naje nasameta a falo tana bawa wani yaro a cinyarta nono,……uhm ……uhm danace mata wai kina ƙiranta sai tace wai…..”
“Saitace wai me,anya kuwa ita kika gani,yanzu haka shirmenki ne,wacce amarya ce kuma budurwa za’a kawota da jinjiri”
“Wlh iyah itace wacce tashigo gidannan ɗazu a mota,bamuga dan bane inaga dan yana mota.
Cewa tace wai bataga wanda ya isa yasakata tashi tazo ba Ɗan ta bai ƙoshiba,saiki jira idan tagama kulada shi yayi bacci sai tazo,inkuma bazaki iyah jiraba ki haƙura”
Saurin tashi Sayyada-tateen tayi daga inda take zaune,saida Lylah dake gefenta ta maidata ta zauna,kuma daga yanda Maleekah ta faɗamata zancen tasan bazatayimata ƙarya ba.
“Yaunake ganin abu ni Maryamu,yau mai nakeji da kunnuwana,haka ta faɗamiki ki faɗamin,kin faɗa mata wacece ni a gidannan kuwa?”
“Eh nafaɗa mata Iyah,wani juya ido tayi ma da alama hakan bai dameta ba”
“Zo muje ki rakani wajennata dan malafar ubanta”
“Ahah iyah Sayyada,bai kamata kije ba,tunda tace zatazo ki bari tazo ɗin,daga nan sai a nuna mata iyakarta ,amma wannan kam bata goyu da zaniba”
Lylah tafaɗa tana alamun taya Sayyada-tateen jimami,nan kuwa a cikin ranta murna ce fall ganin faɗuwar guntun fadar Hajiya zeenah na tabb da rushewa a wajen Sayyada-tateen.

Duk gaisuwar da mutane ke aikamasa babu wacce yasamu damar amsawa,kansa ya asama yake tafiyah har ya nufi office ɗinsa.
A hankali ya tura ƙofar ya shiga,bai zauna a kan kujerar aikinna sa ba ta hutu ya nufa ya zauna,ganin zaman bazai yi masa ba ya kwana yana kallon cilin,yarasa mai shin wanne tunani zayyi a lokacin.
Ya kai akallah awa guda a hakan,har bacci yafara ɗaukarsa,a sama sama yajiyo murya Khaleel yana bugar kujerar dayake kwance.
Ɗan firgita yayi ya farka tareda ware idanuwansa a kansa,tsuka yasake bamai sauti sosai ba.
“Khaleel yaushe ka shigo ban kulada kai ba”
“Uhm ina zaka kula kana bacci,mai cewa a dage da aikine yake bacci a office?”
“Kamawa tayi shiyasa,akwai wani abune?”
“Ahah bakomai,kawai lekowa nayi mu gaisa,sai kuma na ganka a kwance,amaryar taka ta iso ne”
Yamutsa fuska Jabeer yayi tareda kallon gefe,kana gani kasan baima da niyyar bawa Khaleel amsar dayake bukata.
Dariyah kana ya ɗora dacewar.
“Ashe Maleekah ba kayar take ba,data shaida min zuwan amarya,yanzu gashi nayi comferm da kaina”
“Kaga Khaleel serious mafita nake nema,inaga wancan shawarar daka bani zanyi amfani da itah,dan bazan iya rayuwa tsakanin wadancan matan ba,ni daga ganinta ɗazu sainaga ma kaman gwara Lubnah da ita,gabaɗaya batayi kamada mata masu zaman aure ba,beside ma tafi kama da sojoji ko kuma masu aikin bodyguard”
“Hhhh bodyguard kuma? To maizaihana ta dunga binka duk inda zaka tana baka kariyah,ni wlh dakukayi maganar ta har naji inaso inganta”
Shuru Jabeer yayi bai sake cewa komai ba,dan dama shi doguwar magana ba’a jininsa take ba,don Khaleel ɗinne ma shiyasa ya zauna yake masa maganar.
“Ni banajin zan iya wai abuma yanzu,idan babu abinda kake dan Allah kozaka rakani wani waje,akwai abinda nakeson nuna maka”
Fitowa sukayi daga suka office ɗin suka nufi wajen parking motoci,a motar Jabeer suka fita dan dama a kusa yayi parking ba wajen da ake yi ba.
Hanya suka hau suna tafiyah,Khaleel ne kaɗai ke surutunsa shi yana jinsa,saidai ko yaɗanyi dariyah ko yace uhm,babu abinda yake buri da muradi illah ya haɗu da ƙyaƙykyawar yarinyar data sace masa nutsuwa,bashida abinda yake so a yanzu illah tozali da fuskarta.
Ɗan murmushi yayi shikadai Lokacin daya tuno sanda ya kaɗeta,duk yadda yayi da ita ya taimaketa ƙin bashi dama tayi,hakan ba karamin burgeshi yayi ba. Yana cikin duniyar tunaninne yajiyo muryar Khaleel yana tambayarsa dalilin dayasa ya kawo su ƙofar gidan.
Bai sani yana cikin tunani she sun iso gidan.
Fitowa yayi a motar yanufi ƙofar gidan,yasan idan yaga bai bashi amsa ba ai zai biyoshi.
Hakan kuwa akayi biyo bayansa yayi daidai lokacin da wani yaro mai kimanin shekara goma yafito daga gidan,tsaidashi Jabeer yayi tareda tambayarsa babansa.
“Yana ciki barina ƙiramuku shi ”
Yana faɗin haka yakoma cikin gidan”
Bai daɗe ba suka fito a tare,yana ganin Jabeer ɗin yasaki fara’ah,yayinda shikuma yagaidashi cikin girmamawa.
“Ahh kune da safiyar nan,gidan ƙalau koh”
“Lfy ƙalau baba ya mai jikin toh”
“Jiki alhamdulillah dama ba wani ciwo ne sosai”
Bayan gaisuwar suna tsaye sunyi shuru,sunkuyar da kai Jabeer yayi yana sosa ƙeya,da alama akwai magana a bakinsa wacce yagagara furtawa.
Kulada hakan ta Malm Umaru yayi yasakashi cewa.
“Ahh yaro shigo daga ciki mana nan turaka ta ku gaisa da mai jikin koh?”
Aikuwa dama kaman Jabeer jira yake,da sauri yayi na’am da haka,ransa ƙall cikeda farinciki.
Duk abinda ake shidai Khaleel a tsaye yake tun bayan gaisawar da sukayi da mutumin.
Jan hannun Khaleel Jabeer yayi babu ko kunya suka shige cikin gidan.
Wani ɗaki aka kaisu na ƙasa,mai gajeren saman rufi,saida mashaallah a share yake tass babu ƙazanta a cikinsa.
Malm umar yana fita Khaleel ya zunguri Jabeer,dan dama jira yake dattijon ya fita. Cikin raɗa yafara tambayar sa cikeda muradin son ƙarin bayani.
“Kai bangane ba wai meyake faruwane,nan ɗin inane”
“Kai kam katsaya mana ka gani,”
Cikin ƙankanin lokacin Jabeer yabashi labarin haɗuwarsa da Jaleelah a taƙaice”
A zaune take a ɗakin mahaifiyar ta Inna Mairo,karatun hadda take wacce zata bayar da yamma.
Muryar babansu taji ya yana nemanta,hakanne yasa ta rufe ƙur’anin tafito.
Cikeda ladabi ta tsugunna tareda cewa cikin muryarta mai sanyi marar hayaniya.
“Baba gani”
“Yawwa dama wannan yaron daya kadeki ne yazo duba jikinnaki,ganin yanason magana dake yasa nace masa su shigo shida abokinsa kije ku gaisa ”
Shuru Jaleelah tayi kaman bazata ce komai ba,sai daya gama kafin tace toh.
Tashi tayi tashiga dakinsu ta ɗauko hijabinta,hanyar ɗakin babannata ta nufah,cikeda itama fargabar sake haɗuwa dashi a karo na biyu,tun ranar da suka haɗu yayi mata gizo dama.
Suna cikin magana tayi musu sallama cikin siririyar murya taahiga ɗakin kanta a sunkuye.
Shuru sukayi yayinda hankalinsu yakai kanta,amsa mata sallamar sukayi daidai lokacin da ta zauna a can nesa dasu.
“Yawwa ya jikinnaki,i hope babu wata matsala sosai koh”
“Eh babu,ban wani ji ciwo ba ai sosai,Allah ya tsare,nagode da kulawa”
“Ohk ba komai,banji sunan marar lafiyar ba”
Ɗan murmushi tayi wanda yasaka dimple ɗinta motsawa kana tace.
“Sunana Jaleelah”
Daga haka hirar ta ƙare sukayi sallama bayan Jabeer ya ajiye mata bandir ɗin kuɗi,shima bata karba ba,bashshi yayi a wajen suka tafi bayan sunyi musu sallama.

Shuru Hilyaan tayi tana kallonta,dan taga mai zatayi idan ta gama bawa haidar abicinnasa,abinda tayi tunani ne ya faru,dan Bombee batada niyyar kiran da kakar mijinnata tayi mata.
“Amma anty maryam kinsan fah tana can tana jiranki,kuma kincemusu kina zuwa”
“Ohhh wai har yanzu suna jirana,kaii nifah tunda nayi tafiyar nan bansamu wani hutu ba”
“Idan kikaje kika dawo ai saiki huta,dan allah karki fara daga yanzu mana,tunda shekara zamuyi ki dan bari a ja lokaci mana kafin a fara”
“A fara me,me kika maidani ne,jarababbiya? To naji barina je naji mai zata bani take nemana”
Sungumar ɗanta tayi a kafaɗa,har taje bakin ƙofa taga Hilyaan bata tashi ba”
“Yana ganki a zaune,bazaki jeba ne”
“Ahah jeki dawo dangin mijinkine,ni inanan kidawo ki sameni,Allah ya takaita abinda zai faru a wajen”
Hilyaan tafaɗa tana dariyah ƙasa. Taƙaitacciyar harara Bombee tabata kafin ta nufi sashen Hajiya zeenah,inda Sayyada-tateen take zaman jiranta.
Shuru kakejin falon babu mai cewa komai,ajima kaɗan Sayyada-tateen taja tsaki,a ƙallah tayi sunyi cikin carbi.
Tashi laylah tayi tareda cewa.
“Uhm inaga wannan amaryar fah bazata zo ba tafi ƙarfin amsa ƙiranmu, nibarin tafi toh haka”
Tashi tayi zata bar falon,har taje baƙin ƙofar suka haɗa ido da Bombee,wacce ta dakko danta daga cikin mota ta nufo hanyar shiga sashen Hajiya zeenatun.
“Toh ga amarya nan ta amsa ƙiran bayan tagama shan ƙamshin”
Komawa tayi ta zauna babu ko kunya,saboda yanda gulmar san ganin mai zata kasance take cinta.
Kujerar da take facing Sayyada-tateen Bombee taje ta zauna,idan ido yana kisa daya kashe ta,amma ko a jikinta kaman an tsikari kakkausa.
“To kun ƙirayeni gani nazo,mai zaku bani”
Tafaɗa bayan tasaka ɗan ta cinyah tana kallon Sayyada-tateen.
“Kuyi sorry fah barku kuna jira,ɗana ne yake bukata ta,kunga kuwa bazan barshi ba nazo wani ƙiranku”
“Ɗanki wanne irin ɗa?”
Sayyada-tateen tafaɗa tana kallon Bombee dakuma Hajiya zeenah,wacce tayi shuru kaman ruwa ya cinyeta.
“Ɗa mana irin kowanne,ƴaƴan kala kala ne dama”
“Ton ina ubansa ko dangin ubansa dazakizo mana da ɗan wani cikin gida,oh yanzu dama zeenatun bazawara ta aurawa ɗannata,wanne wace irin badaƙala ce”
“Kinga ni bansan ubansa ba ballanta na wasu dangin ubansa,ni kaɗai yakeda kuma zan tsaya masa,menene a ciki ,sauran zancenki kuma bangane su ba”
“Bakisan ubansa ba,kina nufin kice mana shegene?”
“Haka dai kika ƙirashi,ni ɗa nake gani a gabana ,shege kuma ai zagine kawai”
“Hoɗan kekuwa ƴar nan suwaye iyayenki,sannnan wacce irin tarbiyya sukayimiki da ko ƙasashen Aranaku ba’ayinsa,aradu basai gobe ba gidannan zaki bari,tunda nake bantaba ganin tambaɗaɗɗiya yake ba,shege zaki kawomin cikin zuri’ah….hhhhh Kai Kai kai ke Maleekah ƙiramin meeting yanzunnan inason ganin kowa”
Ganin Sayyada-tateen tafara kuka ne yasa Bombee ɗaukar ɗanta,kana ta kalli Hajiya zeenah.
“Wainikma Hajiya zeenah aiki nazo miki kokuma fama da matsalar iyalanki? Tun wuri ki sanar musu su daina shafani cikin lamarin rayuwarsu,nima kuma batasu zan shiga ba,idan kuma ba haka ba zan nuna musu kala ta banida daɗi,musamman tsohuwarnan,haka kawai nagidanmu basuyimin ba wasu bazasu dameni su takuramin ba,kowa yayi rayuwarsa”
“Gabaɗaya suka kalli Hajiya zeenah tareda maimaita kalmar …”Aikeeh “… A tare.
Batada lokacin su ballantana samun lokacin yi musu bayanin tambayar dasukayi wanda dama bada ita suke ba,dan haka ta ɗora danta a kafaɗa tayi hanyar waje hankalin ta kwance kaman tsumma a randa.

Page 🖤9••10🖤

A ranar Sayyada-tateen wuni tayi tana maida labarin abinda Bombee tayi mata,wacce a ƴan shekarunnan babu wanda yataba yi mata,ga kuma babban abin takaicin har sannan Hajiya zeenah batace komai ba,duk yadda takai ga yimata kashedin da koreta,zance ɗaya take faɗamata shine akwai dalilinta na aurota cikin gidan.
A zaune take laure tanayi mata tausa itakuma Maleekah tanayi mata fifita,duk AC dayake kaɗawa a ɗakin bai ishetaba sai an mata fifita da mahuci.
“Kai iyah yakamata ki daina wannan ɗaukar zafin da shekaru irinna ki,tunda tacemiki tanada dalilin kawota inaga akwai dalilin,kibari mana ki gani”
“Bawani dalili,ta rainani ne kawai saboda taga ƴaƴan ta sun kawo kai cikin gidannan suna rikeda komai,shima Aliyun da kaina zanje na sameshi,akan me zai dunga barinta tanayin yanda taga dama a gidannan,idan nayi magana dukku haɗu ku rufemin baki kuga munafukai masu uwa koh,to bazan bar wannan ya wuce ba,dole zata bar gidannan,bari ayi meeting nan da wani satin zan saka a zartar da hukuncin korarta tunda ta kalli tsabar idona tayi min tujara,…….hmmm harda shigomana da shege cikin gida,kaman tasamu gidan gala a agege”
Dariyar da Maleekah take rikewa ce tasamu damar ƙwacewa,aikuwa kaman Sayyada-tateen neman inda zata huce takeyi,duka dakaiwa Maleekah a baya timm,wanda hakan yasaka ta sakin nishi tace.
“Kai iyha naga bani nakar zomonba,wlh tafiyata zanyi na barki,tunda nazo ina miki dannar fushin ma baki ganiba,mun bata dake nayi fushi,zanga mai yimiki kunun turawan idan dare yayi ai”
Tashi Maleekah tayi tabar ɗakin tana cuna baki.
Zaki Sayyada-tateen ta malmala mata,da alama sun bata ɗin,laifin uwarta ya shafeta itama.
“Ke kaure barmin kafar nan haka,tashi kibani waje zan kwanta,wannan mutanen gidan na kula so suke su kashe ni dan kwanana bai ƙare ba,Haba har ina matsala daga wannnan sai wannan? Ohh ni mairamu Sayyada”
Fadawa tayi kan laullausar katifarta mai kamada ta jarirai,ita kaɗai a hankali tana magana.

Madeenah ce zaune a garden tana duba abinda da aka ce takai na defence ɗinsu,dan dama rukuni rukuni akayi,sai yanxu nasu yazo,hankalin ta gabaɗaya ya tafi kan abinda zata faɗa idan lokaci yayi..
Jitayi kaman a sama an fixge takardar datake hannunta.
Dagowa tayi suka haɗa ido da Jawaheer,wacce tasha riga da wando irin falazo ɗinnan pink,sai mayfi karami data naɗe iyah kanta dashi,dan kyau kam tayi kyau,ko mahassadi zai yaba mata,saidai gabaɗaya yanda akayi shigarne indai tanada mai ƙwaba bazata fito da ita ba.
Ƙare mata kallo Madeenah tayi tarda cewa, wai hakan ƴar hausawa ce,Allah dai ya shiryah. A ranta.
Miye kike kallona kinga ajin dayafi naki koh,saura ma shigowata cikin gidanku matsayin matar yayanki,shine wancan lokacin har jimin ciwo koh,saboda kiyimin lahani kina baƙincikin haskawa ta,to ta Allah bataki ba Jawaheer tana nan ƙalau”
Ƴar dariyar rainin hankali Madeenah tayi tareda cewa.
“Hhhh matar yaya manya,kai da alama matan yayan dayawa,indao wannan matar tasa ce dana gani da safe,bazaki kai labari ba a hannunta,bismillah ka wajennan”
“Yeheyeh kullum zancenta kadai ake ji,to waye yafaɗamiki ina jin tsoronta,wanann lokacin da shirina zan tunkare ta,bazan taba bari ta mallake shi ita kadai ba,sonsa a jinina yake gudu,babu jada baya kijira kiga,ina gama school nanda 6 month zakusha mamaki”
“Ohh wai Lubnah kike zance ne yanzu,hala dai mai ɗaure miki gindin batasan cewar Masoyinnaki yayi sabuwar amarya ba koh,ai yau ma tatare da safe,ke kiji wata zazzafar soyayya dan allah”
Wani zare ido Jawaheer tayi tareda zare karamin glass ɗin dake idonta.
“Whatt mai kike cewa aure,no no badai my JJ ba,bazai sake wani aurenba saini,itama tsohuwar matarsa fita zatayi ballanta kuma wata tashigo”
“Zancen kikeso kiyita ji,wai ance da gwauro ya iyali,zaikije kiyi zazzafan bincike kiga shin har kin isama nayi miki ƙarya a munzalinki”
Fizge takardunta tayi a hannun Jawaheer din,wacce gabaɗaya ilahirin jikinta ke zuba rawa.
Juyawa tayi ta nufi hanyar barin garden ɗin,har tana tuntube a hanya da dogon takalminta mai tsini,wani kallo Madeenah tabita dashi tareda cewa.
“Wahallalliya” a hankali.
Ikon Allah ne kaɗai zaikai Jawaheer inda ta nufah lafiya.

** ** **

A zaune take a kan kujera guda ɗaya dake jagaye a falon,waya ce a hannunta tana magana,daga yanda takeyi mutum zai gane da masu harkar kasuwanci takeyi.
Dariyah take darewa dashi,tareda jijjiga manya manyan sawunta masu kama da tuke. Da alama wayar tanayi mata daɗi,ta samu riba a kasuwanci.
Ƙarar fashewar abun glass taji a gefenta,tana waiwayawa tayi arba da Jawaheer tana fasa tambulan ɗin da akayi ado dasu a bakin shigowa falon.
Tashi Hajiya rabi tayi da hanzari ta nufeta,ganin ƴar tata tana koƙarin yiwa kanta illah,riketa tayi tareda duba hannayenta wanda tasamu ƴan yankuwa a jiki.
“Ke Jawaheer mai yafaru haka”
Shuru Jawaheer tayi tana wani fisfigewa kamar ƴar yaye.
“Bakyajine kiyimin magana mai yake faruwa da har zaisakaki yiwa kanki illah haka”
“Mom kibarni ki ƙyaleni shin kinsan abinda najiyo kuwa,wai wai………”
Sake fashewa tayi dawani kukan batareda ta ƙarisa ba,saida Hajiya rabi tayi da kyar kafin ta cigaba da bayanin.
“Mom kinaji wai Jabeer aure yayi yau ma amaryar tazo gidan”
“Me aure kuma wanne iri,kai haba haba duk wanda ya shaida miki wannan zancen yayi ne domin yasakaki jin haushi”
“Wlh mom da gaske nakeyi,Madeenah ce fah tafaɗamin yanzu a makaranta,ko ajin ma banshiga ba na dawo,ni wlh mom kisan yadda zakiyi,ni shi nakeso na aura mom in bakiso na mutu da ciwon sonsa to kiyi wani abu akai”.
Kama hannunta tayi daga tsayen ta zaunar da itah,har sannan tunda ta kama kasan bakinta batace komai,jan ajiyar zuciya tayi tareda shafa kan Jawaheer.
“Tabb lallai hajiyah Zeenah tayimin abinda ban tsammata ba daga gareta,aure?? Yo yaushe ma hakan ta faru bansani ba ina zaune. Yi shuru autana haka kinga duk kin yanke hannunki jini yana zuba,ko asibiti kai zamuje……”
Jijjiga kai Jawaheer tayi fuskarnna shabe shabe da hawaye.
“Ni bazan je ba,mom kefah kika ce Nice matarsa,yanzu kuma gashi can ya auri wata matar bayan waccar,ni nagaji da jiran dakuke cewa nayi,ina gama makaranta zaki auran shi”
Tana maganar ne tana sake matso wani hawayen,wanda hakan yake sake ruɗar da hajiyah rabi.
“Kinga jeki ɗaki maza ki gyara fuskarki kizo muje asibiti a gyara miki hannun,ta can sai mu wuce gidan Hajiya zeenatun,dan ƙiran wayama bazai yi ba dole sai naje,amma kafin sanann barina ƙirata naji shin dagaskene. Maza jeki shiryah,wannan abinda kika fasaɗin kuma masu aiki suzo su fita dasu,ki kwantar da hankalin ki autanah”
Tashi tayi dasauri ta nufi dakinta,musamman da taji har gidan zasuje.
Barinta wajenne itakuma ta samu damar ƙiran Hajiya zeenatu.
Ƙiran Hajiya rabi taga ya shigo wayarta bayan shigowarta ɗakin ta dawo daga Aliyu.
Tana ɗagawa tun kafin ma sallama tajiyo muryar Hajiya rabi cike da magana a bakin.
“Hajiya zeenah mai nakeji ne haka yarinyah tazo tana shaidamin wai Jabeer yayi aure,dagaskene ko ahah”
“Eh dagaskene hajiya rabi,amma ba yadda kike zato ba,shima duk yana cikin plan ne,inaga konayi maganar waya bazaki fahimta ba”
“Ahh menene na damuwa ga mota cikeda mai,Jawaheer taji labarin a makaranta wajen Madeenah,tadawomin gida harda yanka hannu,bari idan na kaita asibiti aka duba hannun zamu shigo. Dole kan zanso jin mai zaifaru,sannan ya akayi kika yi komai banma sani ba”
“Hajiya rabi dakin bar dukkan maganar nan saikinzo ɗin,hakan danayi nayine domin ƙarin nasarar aurensa da Jawaheer”
Daga haka suka kashe wayar akan komai sai an haɗu a tattauna.

** ** **

Ganin sun tafi kuma basuda niyyar ɗaukar kuɗin da suka ajiyene yasaka saka hannu ta daukesu,fitowa tayi daga ɗakin ta nufi inda inna mairo ke har haɗa mata wanke wanken dazatayi kafin ta fito daga wajen gaisawa dasu Jabeer ɗin.
Mika mata kuɗin tayi tareda cewa.
“Inna gashi suka ajiye a ɗakin baffah,nace musu ma su barshi amma saida suka ajiye”
Ɗagowa inna mairo tayi daga sunkuyen tareda amsar damin kuɗin.
Ɗan murmushi tayi tareda cewa.
“Ayyah yaran kirki harda wahala haka,bari a ajewa baffanku,ya fita sun fita ai tare dasho,anya kuwa iyah bugewar hatsarin ce Jaleelah”
Tafaɗa tana kallon Jaleelah cikin sigar zolayah,.
Murmushi tayi tareda jawo gyalenta tashige ɗaki da gudu.
Tana shiga kan katifarta ta faɗa tareda sakin murmushi,wayarta ta ɗakko a gefen katifar ƙaramar nokia,sunan Fareeda ta dannawa ƙira.
Daga can ɗaya barin aka farayin magana..
“Yadai hafeeza Jalee kewata kike hakane bazaki bari muje makaranta ba,yah mai yafaru nasan inaga akwai batu”
“Uhmm wannan wanda ya kaɗeni ne yazo gaisheni yanzu,sunansa Jabeer bakiga ba yanada kirki sosai”
“Lahh farkon sunan ku ma ɗaya,To amma ke mai zakiyi dashi,ko kinfaɗa soyayyarsa kai?”
Fareeda ta faɗa cikeda mamaki
Shurun da Jaleelah tayi batace komai ba yasata tabbatarwa maganarta gaskiya ce kenan.
“Kibari zamuyi maganar kawai a hanya,koma wanne hukunci na yanke zakiji,amma mu baridai sai yasake zuwa kuma yazo da zancen tukunna”
“Uhm uhm Jaleelah karfah ki cuci ɗan mutane,maza nawa kika ƙi amincewa dasu”
“Ehh to saina amince da kowa koh,kekam ki zuba ido ki gani mana”
(Toh idan ana ustaxiyah da smiling ga ustaziyah da loving).
Sauƙe wayar tayi tareda kallon window na tsawon lokaci.
“Kai Madeenah koh,shine wato taje tasau baki tafaɗamata komai,gashi ban shirya sanarda hajiyah rabi abinda na shirya ba sam,yanzu babu yadda zatayi illah ta tunkareta suyi maganar kawai”

Tsakanin wayar tasu ba’a dadeba taji tsayuwar motarsu a bakin sashenta..labulen ɗakin ta ɗaga tana kallon su,daidai lokacin da Hajiya rabi ta fito tareda matsawa inda Jawaheer take tsaye,sai wani narai narai take da fuska. Kama hannunta Hajiya rabi tayi tana yimata sannu suka shigo.
Maida labulen tayi ta mayar,ita kanta tasan abinda haniya rabi takeyiwa yar ta baya dacewa,sannan batayi kama da matar dazakayi fatan da haifamaka jika ba.
Saidai muradinta shi ya dushe daka waɗannan kurakan tunda da farko. Kasantuwar alƙawarin da hajiya rabi tayi mata tun lokacin da aka haifin Jawaheer,kan cewar idan har Jabeer ya aureta,toh itakuma zata haɗe companynta na Royal fabric da Jaan Company su zama abu guda,wannan nasara da Hajiya zeenah tagano shiya rufe mata ido tasaka ganin duk wani abu da hajiya rabi zata aikata.
Yayinda itama a bangare ɗaya akwai dalilinta nayin hakan,tayi bincike da gano cewar Lubnah bata haihuwa,idan ta aurawa Jabeer ƴarta ta haɗe compnynsu,tasan sai bunƙasa fiyeda yanzu,kuma in ƴar ta haihu a gidan,tunda sune dalilin bunƙasar dole jikokinta ne zasu kulada komai a companyn,shiyasa lokacin da hafsa ta mutu itada yaronta har cikin ranta taji daɗin hakan,nunawa ne kawai batayi ba a fili.
Sallama tayi a falon farko,Hajiya zeenah na jinta tafita taryota,tun a bakin ƙofar bayan gaisuwa suka fara maganar datayi maƙasudin haɗuwar su a wajen.
“Mainnkeji haka ni Hajiya rabi daga wajenki,kaddai tun ba’aje ko inba shikenan kin ruguza abinda muka daɗe muna shiryawa a tsakanin yarannan?”
“Kibari kuje ciki,koma mai ake ciki duk zakiji,ba yanda kike zato bane Hajiya rabi”
Zama sukayi Hajiya zeenah ta bata labarin abinda ya faru tunda ga farko har ƙarshe,harma da matsayin auren da komai da komai.
Ajiyar zuciya Hajiya rabi ta sauƙe tareda faɗin
“Yawwa yanzu naji batu,amma cewarta na shekara ɗaya zata aureshi bai tasoba,wata shidan dakikace shi za’ai,ta gaggauta fitar mana da matarsa itama kuma tafita,tunma kafin ayi aurensu da Jawaheer ɗin,tunda itama nanda wata shida zatayi graduate”
“Ehh to yanda kika ce,amma bakya ganin idan aka faɗamata bazatayi shekara ba kada ta fasayin aikin,dan nikaɗai nasan wahalar dana sha kafin ta amince,yarinyar batada sauƙi ko kaɗan fah,bakiji fah labarin yanda suke da iyayenta bane”
“Kai rashin daɗina dake tsoro wani lokacin,kinason yin abu wani lokacin kina tsoro,ninasan zaman dakene yasa ma har kika iya kawota. Yanzu dai ki bari basai kin kawota ba,saidai kiyi ƙoƙarin faɗamata a dabara cewar tafara miki maganin kishiyarta da wuri,idan muka samu tagama da ita ko baikai wata shidan ba sai muce aikinta yaƙare kenan”
“Ehh to Hajiya rabi kin kawo shawara,kai tun safe kaina yake kulle,sai yanzu yafara suncewa,bari zan ƙirashi da daddare nayi masa bayanin matsayin auren danayi masa,dan baisan da zance ba tukunna,itama kuma zan faɗamata aikin da nakeso tafara min.
Amma bayan ni dake dakuma masu aikina amintattu babu wanda yasan da matsayin auren,kinaga mu sanar dashi domin karma yakai hankalin sa garets?”
“Ahhh haba haba Hajiya zeenah yaushe zaki fara wannna aikin,idan kuma matarsa ta tambayeshi matsayinta fah,munfiso kada kowa yasan yarinyar mai tafiyace wani lokacin,tahaka ne kawai zamu samu Lubnah taɗau zafi da itah sosai.
Amma idan tasan tafiya zatayi dariyama zatayi mana,kibar zancen iya mu sai mutanenki da mutanen,sannan ki shaida mata bakyaso kowa yasan matsayinta a gidannan,ta hakanne zamu samu komai ya tafi yadda muka tsara”
Shawarwarinsu suka cigaba dayi,duk akan yanayin yanda abubuwan zasu tafi musu ne.
A bangaren Jawaheer kuwa da suka barta a falo,maimaikon ta yi sashen su Maleekah,sai ta nufi lambun gidan,wanda yake a gefen new side na Jabeer.
Bata ɗauki mota ba takawa tayi a kafa tana kalle kalle har ta iso wajen sashen.
Har zata shige cikin lambun sai kuma tagano wulagawar mutum ta windown kitchen ɗin side din dake kusada da itah.
Mamaki abin yabata,dan duk zuwan ta gidan tasan ba mutum a bangaren,takawa take a hankali ta nufi sashen domin ganin waye a ciki.
Ƙwararrawar bakin ƙofar ta danna,kaman da minti ɗayah taji an buɗe bakin ƙofar.
Hilyaan ce ta buɗe mata ƙofar tana yi mata kallon mamaki kaman yanda itama takeyi mata,dan bata ganta a cikin yaran gidan ba,sannan a binciken da sukayi babu mai irin fuskarta.
Cikin ɗaure kai Hilyaan ta tambayeta.
“Shin……kozan iya sanin wacece ke,sannan kuma wa kike nema?”
“Sister ke zan tambaya wacece ke,yaushe kika shiga nan wajen,domin da babu kowa a ciki”
“Ikon Allah don da babu kowa a ciki sai akan ce yanzu za’a rasa wasu a ciki,matar wajence a ciki mana,dama ba domin a zauna akayi shi ba,to miyasa zai cigaba da zama haka bayan mai wajen tazo”
Daga yanda Hilyaan ta bawa Jawaheer amsa,lokaci ɗaya tagano wato itace amaryar da aka kawo kenan,wani kallon kanne ido Jawaheer tayi mata mai cikeda raini kana ta ɗora da cewar.
“Ko kece amaryar danaji labari ankawo gidan,to indan kinzo gidannanne kinga an baki nan side din kike wannan ƙafafar,da sannu zaki tattara bijenki ki bar gidannan,domin akan shanyar wata kika ɗora taki,ke in taƙaice miki ba iya shanyar ba,shikansa filin na wani ne.
Ɗan murmushi Hilyaan tayi,dan sai yanzu ta tuno akwai hoton ta a wanda aka turo musu,itace Jawaheer wacce za’a haɗasu aure da Jabeer.
“Kinga ki tattare kayanki ki cigaba da riƙewa,domin basu tsinke a gindin kaba ba,amma idan kina ganin zasu miki wahalar rikewa,to ga can kabar a ciki jeki kwance mata su”
Hilyaan tana karisa faɗin haka ta shige ciki batareda ta rufe ƙofar ba,saboda Jawaheer zatayi ra’ayin shigowa,aikuwa yanda tayi tunani ta shigo ɗin.
Bombee na zaune tana ta plan ɗin yanda aikin dazata gabatar a garin zai kasance.
Rigace a jikinta t-shirt pink,sai blue rabin wando itah gwiwa,santala santalan ƙwanjinta suna waje,wanda suka sha gyara da kuma hutu.
Headphone ne a kunnen,wanda ta ɗorashi akan gashinta da ko parkin batayi masa yana kafaɗarta,kana ganinta bazakace ba mutanen yamma bace,saidai gashinta ne da girarta su baƙaƙene ba ja irinnasu ba.
Gabaɗaya duk abinda Hilyaan take da Jawaheer batasani ba sam. Saidai Hilyaan ta ɗauki wayarta ta kashe abinda take ji tukunna. Ɗagowa tayi tambayarta dalilin kashewar,a nanne idonta ya sauƙa kan Jawaheer wanda itama take kallonta da ido a zare,da Alama idonta ne yasakata yin hakan,itama Bombee ta kulada hakan,saidai abube daya zamema jiki ai.
Wani kumbure kumbure ta fara da zare ido tana ƙarewa wajen kallo.Kana ganin fuskarta kaga jinin tsiwa da rashin kwaba.
Tsayawa sukayi suna kallonta batareda sunce komai ba,itama ganin basu tanka mata ba kaman yanda tayi zato yasata zama akan kujerar dake kusada ita.
Kallon Bombee tayi cikeda raini tace.
“Ohhh kece ma’aikaciyar da aka kawo tayimin aikin waccar matar?”
(Tana cikin tafiyah zuwa wajen hajiya rabi tayi mata text ta shaida mata kan cewar ta kwantar da hankalin ta,ba an kawo Bombee bane domin Jabeer yana sonta,sai dan takori Lubnah itakuma ta aureta,amma basu faɗamata auren yarjejenya bane)
Kallon mai kike nufi Bombee tayi mata kafin taja ajiyar zuciya”
“Inna fahimci mai kike kinaso ne kice,kece amaryar masoyina,wacce aka kawo tafitar da tsohuwar matarsa,wacce ta takuramasa nikuma matsoraciya ce bazan iya ba,daga baya kuma bayan ta tafi dan rashin kunya sai naxo ina cewa ina sonsa”
Bombee tayi maganar cikeda maida mata magana,kana ta ƙara da yin murmushi a ƙarshe.
Aikuwa kaman yanda tayi tunani Jawaheer taji haushin maganar sosai,dan lokaci ɗaya ta hassala tafara magana cikin baƙincikin data shaƙeshi a makaranta dasafe bata samu damar amayar dashi ba dukka.
“Hmmm ke kinsan kuwa wacece ni,wlh banda aiki ne yakawoki da kin isa ko hanya ma ki haɗa dani,kuma bar cika baki kina wani cewa ke amaryarsa ce kina wani taƙamada kyan fatarki,wannan jikin babu tasirin dazayyi akan JJ ,keda banza duk ɗayane a wajensa”
Tana maganar ne tana nuna Bombee dayatsa,carfah kuwa takama yatsan tayi shuru.
Hakan datayi ne yasaka bakin Jawaheer mutuwa tana zazzare ido cikeda tsoro,musamman ganin yanda Bombee tahade fuska babu alamar wasa.
“Inda wanda kike magana akansa yana sonki da bazayyi aure har guda uku ba yana barinki,sannan zuwankin nanɗin yatabbatar kina cikeda jin haushin kasancewata matarsa… To ki buɗe kunnuwanki kiji da kyau,ba ayimin ɗaya na bari babu ɗaukar mataki,ko mata ɗari masoyinki ya aura idan ana aure,kedashi dasu baku isheni kallo ba,amma kaff cikinku har matar tasa wacce tayimin kan kara zanyi mata na itace,wannan sunnah tace hakan.
Kema zan barki ne danna farko kikayi,kuma batake nake,ki bari idan so kike ki tanka ki shigo gidan matsayin matarsa tukunna,amma yanzu nafiki iko da gidannan,ke ko karan gidannan ma yafimin daraja dake,bare kuma masu aiki ko mutanen gidan. Ki bacemin dagani yanzu kinada hayaniya zaki tayarmin ɗa daga bacci,aikin banza ku mata bakuda aiki sai faɗa da hayagaga akan maza kaman wasu kaji.
Ƙarisa maganar tayi tareda sakin yatsan Jawaheer kana taja guntun tsaki..
Maida hankalin ta gabadaya kan abinda takeyi,ko kallo na biyu batasake bin Jawaheer dashi ba lokacin datake barin falon.

Page 🖤11••12🖤

“Tunda muka fito daga gidan baka sake cemin komai ba,shin zuwa gaisuwar jiki ce ko kuma dai akwai wani dalilin a ciki”
Duk maganar dayake Jabeer bai kulashi sai murmushi dayake shikadai batareda yace komai ba.
Hakan dayayine kaɗai yabawa Khaleel amsar abinda yakeson sani.
“Ya dai wai ina zamujene naga baka kama hanyar zuwa office ba”
“Ohh sorry da gida zan wuce dakai ai”
Sakin baki Khaleel yayi yana kallonsa,wai dagaske yake sai ya wuce dashi bayareda ya sani ba,anyah kuwa abokinnasa baya cikin illusion.
“Kai wai serious duniyar soyayyar yarinyar can ka tsunduma da gaske?”
“To menene bata cancanta bane,ko haramunne kai”
“Kuttt yaufah amarya ta iso gareka amma kuma ka folawa wata a can nesa,kuma son aurenta kakeyi dagaske”
“Hhhhh amarya,wancan abinne amaryar,kaini fah inka dauramin waccar mai kama da aljanun zan tsinketa,kallo daya nayi mata naji bakin jininta yashiga raina,gabaɗaya mommah ce take rawarta take kidinta ita kadai,kai duk halin Lubnah wlh gwanda min ita sau dubu akan ta,ni bantaba ganin macen dabana ƙaunar kallon fuskarta kamarta ba”
“Hmmmm mutumina kadaina cika baki mana haka kayi shuru kawai da bakinka,to yanzu yazakayi da wannan wacce ka ƙira da Jaleelah ɗin,kasan fah ga Jawaheer ma a gefe”
“Ahhh ni yanzu nadaina damuwa,zuba musu ido kawai zanyi,kaman ta shawarar daka bani kan na auri wacce zuciyata ke so,ta hakane zan samu kwanciyar hankali”
“To ya batun adalci kuma inka makale a iya sashen wacce ranka keso,kana ganin su zasu amince da hakan”
“Ahhh wannan kuma yana ga mommah tunda ita ta aurosu”
Shuru Khaleel yayi da zancen,dan da alama abokinnasa yasha giyar soyayya maganganu yake kaman ba shiba,saidai yana fatan Allah hasa hakan shine sanadiyyar farincikinsa.
Nikam maidani na dau motata a office,kuma ma inada aikinyi,nasan Madeenah tana makaranta,da don ita zanje gidan”
Komawa sukayi companyn ya sauƙe Khaleel,daga nan yashige gidansa na sirri.
Hanyar kamar fita daga gari ya nufa,inda sabin anguwanni suke,wani gida ya nufah ɗan karami madaidaici kana kuma ƙayatacce.
Falor guda daya sai ɗakuna biyu a gidan da banɗakunan su,saikuma kitchen shima karami,filin gidan kuma shine na saka mota.
Gidan a share yake fess babu datti,saidai babu alamun mutum a gidan da alama ba’azama a gidan sosai.
Ɗaya daga cikin ɗakunan gidan ya shiga ya zauna a bakin gado.
Drawer gefensa ya jawo wacce take ɗauke da magunguna pills dayawa a cikin robobinsu.
Roba ɗaya ya ɗauka ya jajjagi kwayoyi guda biyar ya zuba su a bakinsa, gorar ruwan dake kan drawer wajen ya dauka yabi su dashi.
Ajiyewa yayi yana maida numfashi bayan ya haɗiye,tareda komawa ya kwanta akan gadon.
Bayan kaman mintunan dabasu fi uku ba kuwa yafara lumshe ido bacci yayi awon gaba dashi.
Misalin ƙarfe takwas anyi sallahr isha,text ɗin Hajiyah Zeenah tagani tana kan sallayah tagama yin sallah,ko addu’a batayiba ta ɗauke sallayar ta ajiye gefe,kana gani ma dama kasan sallah kawai akeyi domin tazama dole.
Karanta text ɗin tayi,kan tana nemanta yanzu a part ɗinta akwai maganar dazasuyi.
Yar ƙaramar tsuka tayi,da bazata jeba,saidai kuma tana bukatar miƙe ƙafa,kuma Haidar yadaɗe dayin bacci a ɗakin Hilyaan,dan yanzu daya shiga wata na huɗu madarar tafara ƙarbar jikinsa,matsalarsa ma na laushin ƙashi tafara raguwa.
Doguwar rigace a jikinta,dan haka hijabin datayi sallah jundumeme har ƙasa yana jan ƙasa a mayar.
Tafiya take tana bubbuɗawa a cikin hijabin,kai daga nesa saikace aljana,ita kanta yanayin shigar tata yabata dariyah,wayaga da rana ayi shigar gyale da daddare kuma ayita burmemen hijabi.
Tayi ta kalle kallenta a hanya kafin ta isa sashen hajiya zeenatun..
Babu ƙowa a falon,dan haka kao tsaye dakinta ta wuce dan tasan tana can tana jiranta..
Ko sallama batayiba ta samu kujera ta zauna bayan ta naɗe hijabinta wanda yataru a ƙasa.
“Naga kin daɗe baki ƙariso ba,baki hau mota ba da darennan bakya tsoro?”
“A ina kika ganni kika bani aiki,a cikin gari kika gannin cikin gidan kaman sauran mata? Banji tsoron daji ba sai wannan cikin gidan,yanzu dai ba zancen nadaɗe ban iso ba,menene dalilin wannan ƙiran”
“Amma dai yakamata ki dungayiwa manya magana da kaurin lafazi,kada ki manta fah ɗana kike aure?”
Wata dariyar shaƙiyanci Bombee tayi tareda cewa.
“Idan akwai wanda yasan wacece ni a gidannan to bayanki ne,hasalima wannan halayyar kika gani kika nemeni. Hajiya zeenah kada ki manta wacece take gabanki,ke yakamata kisan dawa kike hulɗa,yaushe ma kika samu dama har zakiyimin ƙira da daddare kuma nazo,dan kinga inayimiki laushi?.”
Cikin ɗaure fuska da tsayayyun ido takarisa maganar,ba wuyah sai ranta ya baci..
Shakkarta ce tashiga Hajiya zeenah wanda sai yanzu taga hakan,wai chakwakiyah tun ba’aje ko inaba anya kuma batayi kuskure ba. Share tantama tayi a ranta tareda cewa.
“Yanzu dai ba wannan ba,dama ɗazu na yi shawara,shin maizai hana ki fara dayimana maganin matarsa a cikin wata shida na farko idan babu damuwa”
“Meyasa kika ce haka,sannan wai ni meyasa bazakuyi maganin ta da kanku bane tunwuri”
“Nariga na faɗamiki halin da ake ciki,so nake da furta dakanta cewar ya saketa,idan ba haka ba inna tilasta shi ya saketa to zai mutu…..idan mukayi maganinta da kanmu kuma uwarta bazatayi shuru ba,wato Brr Na’ima.
“Brr Na’imah Hashim wai”
“Eh itafah kinsan ta ne?”
“Uhm amma basosai ba shikenan zanyi shawar ni barin na tafi”
“Yawwa bayan wannan kar Jabeer yasan dalilinki na zuwa gidannan,ta hakanne sirrin mu zai rufu sosai”
“Uhm bakuso yasani itakuma yarinyar dazai aura yaakayi ta sani ”
Alamar rashin sanin mai take faɗa Hajiya zeenah ta nuna,ta hakanne tagano cewar Hajiya rabi ce tafaɗawa ƴar ta kenan,saboda kartayi mata kallon matar masoyinta. Komai yana rufe a gidannan.
“Lahh shikenan karki damu ma bakomai ni na tafi”
Daga haka Bombee ta tashi tanufi hanyar nata side ɗin.
Dariyah ta sheqe dashi tareda cewa.
“I solved some puzzle,hmmm Hajiya zeenah kenan,idan bangane mai kuke ƙullawa ba basunana Bombee ba wacce sunan ke zama kan harshen duk mutanen data zaga.
Kin bukaci na yimuku maganin Lubnah da farko saboda kufitarni daga shirinku a cikin wata shida nan gaba,wanda shine daidai lokacin aurawa Jabeer Jawaheer. Sannan bakuso shi yasan matsayina a gidanann saboda kada matarsa taji. Wannan duk plan ɗin Hajiya rabine,amma kuma ta sanarwa da ƴar ta saboda ta kwantar da hankalin ta.
Ke kuma Lubnah wato ke ƴar barr Na’imah ce da kuma Gen Abdu manga.
Wow puzzle ɗina ya warware cikin sauƙi,shirina yana tare a waje ɗaya batareda na saniba,am sorry Hajiya zeenah,kin kawoni cikin gidannan,amma abinda naga dama dakuma tsarina zanyi,in takanki ya biyoma saidai kiyi sorry”
Tafiyah Bombee take tana fara’ah da nishaɗi,da alama tasamo bakin zaren matsalolinta,tasamu fili tasamu doki,saura sukuwa kawai yarage mata.
Ba ita ta isa part ɗinta ba sai wajen 9:30pm,tana shiga taji shuru tsitt,da alama su Hilyaan sunyi bacci itada Haidar kenan.

Safah da marwa take a tsakar ɗakinta,taje kana ta dawo,tarasama mai yake mata daɗi a duniyar nan ta maliki yaumiddini,ƙarfe kusan goma amma Jabeer bai dawo gidaba,kaddai ya dawo kai ya tsayah a sashen amaryarsa kaman yanda tun ɗa zu zuciyarta ke raya mata ammma taƙi bata hadin kai.
Wani irin bugawa ƙirjinta yayi,data fara gasgata hakan,mayafinta ta ɗauka ta fitah da gudu zuwa sashen Bombee.
Saidai har taje bakin ƙofar kuma sai tadawo wata zuciyar tace mata,karkuma kije kiyi mungun ganin dazai rikita miki ƙwaƙwalwa.
Turus tayi a bakin ƙofah tareda komawa cikin sanyin jiki,jidake banda tafarfasa babu abinda zuciyarta keyi,gaba ɗaya ko wata huɗu batayi ba da fita a cikin ƙangin kishi har takoma wani.
Ganin idan takoma cikin ɗakinma ba bacci zatayi ba,yasa kawai ta nufi wajen motarta a daren ta nufi sashen da Bombee takeyi,ba mungun gani ba inma aljanin ganine gwanda tayi data kwana da wasiwasin kar ko mijinta yana wajen wata,watan ma wacce tayimata cin fuska a lokacin farko.
Bombee wacce bata dade da shigowa ba,tasaka kayan bacci kenan taji anan ƙwanƙwasa mata ƙofar bakin part.
Jim tayi kan wanene yake buga ƙofah haka a zuciye?
Ganin zai tayar da masu bacci yasakata nufar bakin ƙofar,ko ɗankwali bata ɗaura ba gashinta yana ɗaure ribbon.
Ta na’urar jikin ƙofar ta leƙa domin ganin wanene,Lubnah ce a tsaye ta kama kunkumi tana jijjiga tareda tsumayin a buɗe ƙofar.
Tun kafin ta buɗe ƙofar taji Lubnah tasake buga ƙofar tareda cewar.
“Ki buɗe ƙofar nan kifito min da mijina,munafukar Allah nasan daga kallon dayayi miki da safe badai kan yabiyoki dan Allah ba saidan nemarsa dakikayi”
Dan murmushi Bombee tayi tareda zare ribbon ɗin dayake kanta kana ta barvaza gashin kannata a gadon bayan da ƙafaɗunta.
Yamutsa rigar jikinta tayi tareda ɗageta ta sokata a tsakanin mamanta,ta yanda cibiyarta zata buɗe ana kallonta..
“Let have some fun”
Tafaɗa tareda buɗe ƙofar,hammar ƙarya tayi tareda kallon Lubnah ta lumshashshun idanuwa cikin maganar hamma.
“Baiwar Allah lafiyah,mai ya kawo ki side ɗin amarya dawannan daren,wani abun kike nema?”
Sake hassala Lubnah tayi tareda ƙarema Bombee kallo,wacce take tsaye a gabanta gashi a babbaje,ga matarta a mai laushi dakkyau cikin kayan bacci masu ɗaukar hankali,kana ganinta kam babu shakka kasan sun fagen soyayyane tafitar hankali,dan jikinta ya nuna hakan da muryarta.
Cikin shaƙyaƙyƙyiyar muryar tace.
“Ina mijina yake?”
“Ohh mijinki yana cikin ɗaki yana jirana,amma kuma yau a aikinsan ba mijinki bane koh,saiki bari idan mungama yabani madara na bashi mun more,in Lokacin ki ya zo saukusha naku”
“Jabeer Jabeer!!!”
Lubnah da ƙwallah masa ƙira a can ƙasan maƙoshinta tamkar mahaukaciyah.
“Shiiitt ko ya jiki bazai fito ba,domin na cemasa yayi zaman inazuwa,kinga ma ni tafiyata,inkinaso kiyi ta tsayuwa a wajen har hudowar rana”
Bombee tana gama faɗin haka maida ƙofar tarufe tana dariyar ƙasa kasa ta mugunta.
A ranar yanda Lubnah taga rana haka taga dare tana saƙe saƙe da shirye shiryen dawowar Jabeer gareta,ina kwana daya ma yayi a can amma ji take kaman an tsunduma ta a kogin ruwan zafi,taya zata iyah barinsa yayi sati a wajen wanann mai zubin karuwan,ita yanzu ma yakejin mai nene wani abu waishi kishi,da wasanta tayi kawai.
Maganin da Mahaifiyar ta bata gobe zatayi aiki dashi,itakuma a hankali zata kai sunanta wajen Boka zulumgum suyi aiki babba a gunta.

A bangaren Jabeer kuwa bashi ya tashi ba sai wajen karfe huɗu na dare.
Yana tashi kansa ya dafe na yan wasu mintuna kafin ya tashi daga kan gadon.
Kai tsaye banɗaki ya nufah ya iyo wanka haɗeda alwala.
Sallolin da ake binsa na ranar ya rama kafin ya fara nafilfili yana jiran shiga Sallar asuba.
Kasancewar baccin dayayi ba karami bane yasa daya gama sallar akan sallayar ya zauna yana karanta ƙur’ani a cikin wayar tasa.
Ƙarfe shida daidai ƙira ya shigo masa wayar na neman gaggawa da akayi a wani company dayake da share a ciki a kasar Roman,ƴar ƙaramar tsuka yayi kafin ya tashi zai shiryah.
Wardrobe ya buɗe inda yakeda extar kaya a shirye a ciki,ɗauka kawai yayi yasaka tareda zaran keyɗin motarsa.
Gida ya nufah kai tsaye sashen sa dayake part ɗin da Lubnah take,dan part ɗinsa dake side ɗin Bombee bai fara amfani dashi ba tukunna,har akayi gyaransa aka gama bai saniba,shin anakai wasu kayansa can ko ahah bai saniba.
Har yazo leƙa ɗakin Lubnah sai kuma yafasa,yayi mata text kawai,dan yasan comfirm ne bata tashi tayi sallah i yanzu ba,dama yaya bare iya tazo,yana nan ma sai yayi dagaske tukunna.
Inaga bayanan,yasan sai ya Allah jaka a ɗaki.
Ko Hajiya zeenah bai samu damar ganiba ya wuce,da niyyar ya ƙirata ya faɗamata,don zuwan na zayyi a ƙallah sati ɗaya ko fiyeda haka a can.
Jabeer bai tashi yiwa Lubnah text ɗin ya tafi ba sai kusan 12 na rana,iya kuluwa ta ƙulu,wato jiya yana sadi din Bombee bata ganshi ba,yanzu kuma yayi tafiya sai a waya ya faɗamata.
Hannu tasaka a kai kaman mai shirin rusa ihu,dan sannan ne sauƙowarta daga kan gado,shima dan yunwa ce ta tasheta.
Wurgi tayi da wayar ta bugu da kunnen gado,fuuuu tashiga banɗaki kaman zata tashi sama,tana banɗakin tana surutu ita kaɗai kaman tababbiyah.
Sai bayan ta shirya taci abinci kafin ta ɗauko wayar.
Key ɗin motar ta ɗauka ta nufi waje a zuciye,ta motsa da alama an tafi wajen zulungum👀.

A safiyar ta kama hanyar barin gari tareda nufar zulungum da tarin buƙatunta.
Gudu take a mota tana tunanin irin cin fuskar da Jabeer yayi mata.
“Inaa dole ma nayiwa tufkar hanci,duka duka jiya fah ka kawota cikin gidan,har ka fara juyamin baya kaman wata kayan wanki,zakuwa kuga aiki da cikawa daga kai har ita ɗin”
A haka ta isa cikin dajin inda iya motarta zata iya shiga.
Takawa tafarayi da ƙafah tana ɗaɗɗage skirt,ita kaɗai tana tsuka kaman ansaka dole harta isa wajensa.
Tun daga nesa take gano hayaƙi yana tashi daga gefe bukkar,da alama wani abun yake dafawa.
Wata buta ce ta ƙarfe akan wuta tahaɗa ɗauda ko ganeta bakayi dakyau,kallo ɗaya tayiwa butar tashiga cikin bukkata,tun daga dosar ɗakin takejin gurnani kaman zaki. Yasake baki sama yana bacci kaman busuru,banda wari idan yasaki numfashi babu abinda yake fita daga bakin.
Wani kwano tasamu a wajen ta shamba da ƙafarta,aikuwa nan da nan yayi firgit ya tashi tareda ambaton sunan wani aljani a bakinsa(auzubillahi).
“Hmmm kai har bacci ma kake,muhimmin abune ke tafe dani wajenka tashi kayimin aiki yanzunnan”
“Ke yau ba ranar aiki bace,uwar matsafa ta bani hutun aiki yau,sanann karki damu kin kawo kukanki inda ya dace,An kawomin labarin sabuwar kishiryarki,saidai babban abin mamakin duk yanda naso samo sunanta cikin madubina ban samuba. Amma kibari zan baki wani magani wanda zakiyi amfani dashi..
Bazan faɗamiki mai maganin zayyi yanzu ba,saboda ƙa idarsa kenan.
Zaki dunga ɗiga masa jinin baƙar kuliyah duk bayan sati guda,har na tsawon wata uku. A wannan lokacin da maganinnan yake shan jini,ba’a yarda mijinki ya kusance ki ba sam harsai kinyi amfani da maganin tukunna. Inkuma kika kuskure toh fah zaki mutu mushe.
A sanann koh ƙafarki kikace ya tsugunna lasha,ke ko kashinkine tofah sai ya lasa dolensa””
Karbar maganin Lubnah tayi cikeda murmushi tasaka a jaka.
“Amma a ina ka samoshi,bayan kacemin yau ba aiki”
“Kedai kije ki jarraba maganinnan tukunna,kaman na sakinnan shima kedashi mutu ka raba ne…….!!!!”

** * **

Khamees ne yashigo sashen Bombee da wani labari na uzula,wanda ya samo a daren jiyan.
A zaune yake riƙeda document a hannunsa yana duddubawa kafin tafito.
Fitowa tayi sanye da riga da skirt a jikinta ƴan kanti,da haidar a hannunta yake gilu gilu da kai alamar bai tsayaba.
Hannu khamees yasaka ya karbeshi yana yimasa wasa,sai bangala dariya yake.
“Ahh lallai my boy ka samu sauƙi,gashinan idonka yana ƙarayin irinna mommynka sak blue”
Rolling Bombee tayi da ido tareda yin ƙaramin murmushi.
“Yah Khamees ka tashi lafiya,naji ƙiran gaggawa daga zuwa jiya,mai ka samo mana gameda su?”
Maida haidar yayi kan cinyarsa ta gefe,tareda miƙa mata file ɗin dake kan cinyarsa.
“Nasamo gidan su haidar bashi nisa daga nan,sannan shikuma uban gayyar target ɗinmu na samu bayanan komai nasa,gidansa companynsa harma da labarin iyalansa dukka”
“Ehh nima nasamu wasu bayanai dan gane dashi,amma ƴaƴan sa nawane?”
“Uhm ukune kacal,biyun mazane kuma basa ƙasar,ƙaramar cikinsu itace wacce mijinki yake aure,kinga kun haɗu a waje ɗaya kenan,saidai kiyi taka tsantsan kada tasan koke wacece,hakan zai bada matsala babba.
A yanzu bamu gama shiri sosai ba,dan haka bamu da buƙatar fara komai yanzu”
“Ehh nasani,tun jiya dama nasan wacece itah,kaga kenan bazan yi aiki da tsarin Hajiya zeenah ba kenan,muna buƙatar lokaci sosai akan hakan,domin suna da matuƙar iko. Kaifah ya yanayin zamanka a garin,baka ganin za’a samu matsala,tunda har yanzu baka cire siginal ɗinka ba,deactivate ɗinta mukayi,a kowanne lokaci zata dawo aiki idan tayi kusada na’urarsu,inaga kawai ka koma gembu,ni zanji da komai”
“Ahah ahhah Maryam bazaki iya ke kaɗaiba,sannan karki manta nima abinnnan yashafeni ba iya ke kaɗai bace,dan haka yanzu ma nayi secret booking na body checiking daza’ayimin,wannan karon zanyi nasarar cirewa inshaaallah”
“Hmm idan kuma ka gano a wajen zuciyarka take fah kamar………”
Bata ƙarisa sunan ba gabaɗayah yanayin fuskarta ya sauyah,ƙokarin haɗiye hakan tayi tareda sauya alakalar zancen.
Shima khamees shuru yayi bai bata amsa ba jin Mummunan labarin data ɗago mai cikeda abubuwa marasa daɗinji.
“Ya batun familynsa shin suna cikin ƙoshin lafiyah koh?”
“Lafiyansu kalau,na haɗu da ƙanwarsa ma jiyah a makaranta Nu’aimah,nasaka fuska bata ganeni ba,amma dai alamu sun nuna tana cikin ƙoshin lafiyah”
“Hmmm kenan alamu sun nuna sun ƙyale familynsa,dan haka bazamu kusancesu ba kada musake jawomusu wata matslar,mu barsu suji da rashin dasukayi ma a baya.”
Cije bakinta Bombee tayi tareda dunƙule hannunta. Hilyaan wacce take bayan ta ne ta dafata a kafaɗa cikin sigar lallashi.
“Kiyi haƙuri anty Maryam,suma inshaaallah saisunga ƙarshensu”
“Wannan yazama wajibi,indai ina numfashi saina yi daiɗai da zuri’arsu ko bara sai nayi sanadiyyar data gagaresu.
A yansu basai wani lokacin ba wasan zai soma,ba gudu babu ja da baya,lokacin dazasu girbi abinda suka shuka yayi,saina saka wuƙa na yaga bargon mutuncin ƙaryar dasuka yafawa kansu,saina bankaɗo abinda suke boyewa mutane suna zaluntarsu. Khamees kayi koƙarin fitar da baƙar alamarsu a jikinka,idan kuma baka samu damar cireta ba ka koma kada kaima ka rasa rayuwarka,ka barni naji dasu,aradu ko ni kosune a garinnan,saina shayar dasu ruwan mamakin da suka daɗe basu kurba ba a rayuwarsu”
Kafin ta kaiga ƙarisa maganar idanuwanta sun kaɗa sunyi ja.
Tashi tayi kaman an cillata ta nufi ɗakinta. Jijjiga kai khamees yayi shida Hilyaan,dan su kansu abin yatabasu bare kuma itah,abin kawai cin rai sosai.

_*RAYUWAR BOMBEE A BARIKIN SOJOJI*_

Page 🖤13••14🖤

_*RAYUWAR BOMBEE A BARIKIN SOJOJI*_

Saida Bombee tashafe kusan sati guda kafin ta warware daga shock ɗin zaman motar da tayi,dama kuma kafin sannan ta jigata da rashin cin abinci datayi a Lokacin.
Iduwanta da farin POP ɗin dakin tafara tozali,zaro ido tayi cikeda tunanin shin yau kuma wacce duniyar ta kawo kanta,kodai kai buguwar datayi a cikin motar nan ta mutu,amma kuma a kawo ta farin waje irin wannann kaman wacce take aikata daidai,yanzu haka fah da laifuka masu yawa tabaro garinsu,taya kuma zata dace da wannan rayuwar.
Duk a kanta take wannan magananun,abu daya yadawo da ita zahiri shine muryar Hajiya Zulaiha dataji,wacce takeyiwa wata yarinya mai suna Nu’aimah.
Sauƙe ajiyar zuciya tayi tareda cewa. Inaga to a cikin mafarki take idan ta farka komai zai zo daidai.
Mikewa tayi daga kwancen da take tana dafe da kanta,wanda har yanzu bai daina yimata ciwo ba.
A hankali ta zaro kafafunta daga kan gadon ta saƙƙo.
Cikin sanyin jiki take tafiya har fito falon,a nan kallo yake wajen Bombee,dan sakin baki tayi dagaske tana kallon sama,inda decoration lamp take lanƙaye a sama.
Muryar Hajiya Zulaiha taji tana ƙiran sunanta cikeda dariyar ganin abinda Bombee take,ta saki baki galala.
“Bombee kin tashine,naga kin rike kai har yanzu yana miki ciwo ne?”
Sakin kan tayi tareda ɗaga kai a hankali,jawo hannunta Hajiya Zulaiha tayi ta zauna tareda kawo mata abinci,babu bata lokaci kuwa ballanta fulako ta hau kansa kaman gareshi aka aikota.
Saida Bombee tasake sati a gidan su haidar babu wanda ya tambayeta dalilin biyosu da tayi,sosai hajiya Zulaiha ke kulada itah. Babu laifi tasake dasu sosai,musamman Haidar shida ma tasanshi,sai Nu’aimah itakuma kanwarsa,da kuma Farouq sai Nabeelah. Rayuwa suke gudanarwa mai abin sha’awa da tsari,sannan kuma ga kayan alatu komai yaji,kasancewar Gen Muhammad Bello babbane sosai a barrake na sojoji dake abuja,Aikin dayaje gembu ma na shirye shiryen ƙara masa girma ne.
Yau tunda safe Hajiya Zulaiha ke jirga jirga a kitchen itada Nu’aimah. Saboda dawowar Gen Muhammad daga Rasha,wanda yatafi kaiwa wani result ɗin case daga headquarter su wancan satin.
Haidar kuma shida Bombee suna game a falo na combat,gabaɗaya sun cika wajen da hayaniya.
Kallonsu Hajiya Zulaiha tayi daga kitchen ta jijjiga kai,dan takula Bombee akwaita dason gagara da kuma shirgi na maza,shiyasa ma tasu tazo ɗaya da Haidar,musamman da baya da abokai dama sosai,saboda rashin zaman sa a ƙasar.
Babu yadda Gen Muhammad baiyyi dashi ba akan su tafi tareda tunda a can Rasha yake karatu amma yaƙi tafiyah,ganin sannan Bombee bata tashi ba,sai kawai ya fake da cewar ai hutunnasa bai ƙare ba da saura.
Da murna Farouq suka taroshi daga waje bayan drivernsa ya ɗauko shi daga airport. Duk murnar taryarsa da suke Bombee tana kallonsu daga inda take zaune,ɗan murmushi kawai tayi tareda sha’awar ganin kansu a haɗe,abinda ta tashi tarasa tsakaninta da ƴar uwarta kenan wato shaƙuwa,tun ranar data gane cewar munafurci takeyi mata bason gaskiya ba.
Saida yaran suka gama murnar oyoyon kafin Bombee tayi masa sannu da dawowa,da fara’a ya amsa kaman ko yaushe,sai kace ba soja ba.
Bayan komai ya lafah yayi wanka ya huta aka fito cin abinci gabaɗaya,su Nu’aimah sai labarin makaranta suke masa da kuma tambayar tsarabarsu..
Magabar da baban su haidar ya jeho mata bayan gama cin abincinne yasakata cikin nazari kafin ta bada amsa.
“Maryam kin shiga motarmu kin boyimu amma har yau baki faɗamana dalilin hakan ba,munyi shuru bamu tambayeki ba saboda kada kiji babu daɗi a zamanki tareda mu,shin mai menene yasakaki barin danginki kika zabi biyomu nan?”
“Bana biyo bane domin naƙi mahaifata inason zama dakuba,nabiyokune saboda banida wani zabi dazayyi sanadiyyar fitata daga garin saiku kaɗai. Sannan kuma inada muradin mallakar ƙarfi da kuma iko,ta hakanne kaɗai zan kare kaina akan gaskiya ta,harma da innice da laifin. Wannan shine maƙasudin shigowa rayuwarku danayi,Dan Allah abban Haidar kasakani inda zan samu training na ƙarfi wanda zan yi amfani dashi wajen kare kaina da kuma rama abinda akayi min. Inason koda zan koma garina sainayi ƙarfin dana fi gaban nuna yatsa balllanta zartar min hukuncin da banida masaniya akai. Ka taimakeni da hakan koda yana nufin akwai abinda zan biya dashi”
Sauƙa Bombee tayi daga kujerar tana roƙon abban haidar a ƙasa har cikin ranta.
Hajiya Zulaiha ce ta tashi daga kan kujerarta ta ɗagata,dan shikammma yarasa mai zaice illah gyaɗa mata kai dayake cikeda alfahari da zancenta,domin haka yake son yaga mutum da zuciya.
“Karki damu yarinya naji batunki,kuma indai maganar dakika faɗa hakane tabbas zan taimakeki,nima kukana zaki sharemin lokacin da nima zan sharemiki naki,shi wannan nayi nayi dashi yaɗau fagen daga a makarantarsu,amma sai ya ɗauki fannin masu aiki da na’urah. Karki damu zanyi iya ƙoƙarina wajen taimakamiki akan cikar mafarki inshaaallah”
Godiya Bombee tafara suburbuɗawa Gen Muhammad kaman yabiya mata kyautar makkah.
Tundaga ranar Bombee taƙara sakin ranta a cikin sosai,saidai kusan ko yaushe bata gida tabi gen Muhammad barrak,dan wani Lokacin tun kafin ya isa motama ta rigashi shiga,haiƙan take shiga cikin masu training,wani Lokacin ayita mata dariyah amma baruwanta. Shima kuma gen Muhammad hakan ba ƙaramin burgeshi yake ba,dan sai ya zauna yayi ta mata zancen abinda yashafi yaƙi da sojoji kaman ya samu abokiyarsa.
Wasa wasa an ja lokaci,haidar yana shirin komawa makarantar sa ta horon sojoji tundaga matakin yarinta.
Kullum maganar sa shikenan zai koma,ita kuwa Bombee hankalin ta gabaɗaya ya karkata a zuwan barrak ɗin datakeyi,dan a ganinta wanann zuwan da take anan zata koyah.
Kaman kullum yauma tabiyo gen Muhammad itada haidar,kalle kallen wajen takeyi cikeda shauƙi,matsawa gefen haidar tayi tareda cewa.
“Naga yawancin sojoji anan gidansu yake,maiyasa ku naku yake cikin gari toh?”
“Hakan ra’ayin abbane,bayason zama cikin barrak ,inta kama ma shikaɗai yake zuwa ya zauna har yagama abinda zayyi,ummah ce take tsoron zaman nan ɗin,tun tana amarya aka taba kawo hari,to datagani shine sai tasamu trauma da zaman barrak”
“Ohh na fahimta,shiyasa idan ana zancen zuwa bata magana”
Ɗaga kai haidar yayi tareda yin murmushi daya tuno irin tsoron ummansu gameda wajen.
“Oh na manta yau anan training na harbi, da kuma faɗa,ko zamuje mugani?”
Da hanzari ya nufi wajen da ake gudanar da gwajin,dan yasan dole Bombee zata biyoshi domin ta gani.
Raba mutanen wasa akayi gida biyu,maza sune keyin na faɗa,yayinda mata kuma suke na harbi,kalar harbin akwai na Bindiga,na kwari da baka,da kuma danƙo.
Sukuma maza akwai dambe,langa da kuma Kabali.
Lokacin da su Bombee suka isa wajen anyi wasu wasannin tuntuni,dan haka basufi saura guda biyu a gamaba.
Daga langa wacce ake a lokacin, saikuma Na kwari da baka shine a ƙarshe.
Abin hari suka saitah inda aka bada alama kafin suka harba.
Ansamu ta uku da kuma ta biyu,amma sai na ɗaya mutum biyu sukazo daidai,wanda sune suka samu nasarar sakawa a zagayen da jan launi yake.
Domin sake tantancewa sai akan matsar dashi nesa fiyeda na da,nan ma kuma sai ya zamo sun sake sakawa a gida iri ɗayah.
Sake matsar dashi akayi nesa sosai,wanda hakan yasa suka tsayah kallon kallo,kowa tana tunanin ɗayar ta fara.
Alamar farawa aka basu,inda kowa ta harba,amma babu wacce nata ya isa ga kan abin,hakura akayi kan za’a raba musu kyautukan kawai daidai da daidai.
Bombee dake gefen haidar ta kalleshi tareda cewa.
“Kai ina son nagwada harbawa a inda abincan yake,kana ganin zasu barni nayi?”
Uhm alamar tunani ya tafi kafin daga bisani yace.
“Ehh toh amma jirani barina faɗawa abbbah ko zai tambayesu”
Wajen da manya ke zaune haidar ya nufah tareda yiwa abbannasu magana a kunne,Bombee daga inda take tayi shuru tana jiran taji ko shin zai amince.
Murmushi yayi tareda ɗaga kai kana ya kalli inda Bombee take,suna haɗa ido ta sumkuyar dakai cikin jin kunyah.
Tashi yayi tsaye tareda gayyato hankalin mutanen wajen kansa,dayake shine babban baƙo na wasan nan da nan aka bashi haɗin kai.
“Ku dakata haka,ƴa ta tabuƙaci a bata dama tagawada harbi,shin ina fatan hakan bazai zama matsala ba koh?”
Alƙalin wasanne ya kunna mic tareda cewa.
“Hakan bazai zama matsala ba yallabai,ina take ta shigo filin wasa,bari a matso mata da abin harin kusa”
“Ahah ku barshi inda yake,ganin nisan dakuka sakane yasata jin sha’awar gwadawa”
Shuru wajen yayi bayan sunji bayanin Gen Muhammad,kowa burinsa bai wuce yaga mai harbin ba.
Alama gen Muhammad yayiwa Bombee akan tafito,aikuwa kai a sunkuye tashiga filin kaman mutuniyar arziki,dan dama akwaita da iyah saka fuskoki kala kala.
Mai kulada wasanne wanda kuma shine coarch ɗin dake horar da harbin ya miƙomata kwari da bakar,wacce take ɗauke da kibau guda uku aciki.
Karba tayi tasaita mata riƙo a hannun.
Wani shu’umin murmushi tayi tareda cewa “An dade ba’a haɗuba” a ranta.
Zaro kibau ɗin tayi dukka ukun ta saita su akan tsirkiyar kwarin,muryar Alƙalin wasan taji yana cewa.
“Uhm guda ɗayah zaki saka a jiki ba uku ba”
“Dokace dole sai guda ɗayah,idan ba doka bace karka damu zan iyah harba dukka ukun a lokaci ɗayah,ina harba biyar ma ba iya uku ba”
Shuru yayi mata tareda bata waje badan ya yarda ba.
Karkata kanta tayi tareda lumshe idonta ɗaya domin tasamu damar saita wajen,aikuwa tana dawowa da kanta tasakesu a tare..
A tare suka sauƙa a kan alamar jan dake tsakiyar allon harin dukka su ukun..
Lokaci ɗaya kuwa wajen yaɗauki shewa,kowa na yaba bajinta da kuma ƙwarewa irin ta Bombee.
Gen Muhammad shine yafara tashi yayi tafi,kafin sauran mabiyansa ma suka farayi cikeda jin daɗin su.
Coarch ɗin da kansa ya ɗauki kyautar na ɗayan ya lanƙaya wa Bombee a wuyah,sukansu wanda suka yi wasan ta burgesu matuka.
Haka taron ya watse kowa na zancen harbin da Bombee tayi,yanda suke mamakin ita batayishi har haka ba,dan ko kaɗan bataga nisan idan suke tunani ba ita.
Suna shigowa gida haidar yafara bawa ummansu labarin abin yafaru.
Dariyah tayi tareda tayata murna amma taƙara da cewa.
“Uhm nida kitchen tashiga ta haɗa wani abincin sabon samufuri da saitafi burgeni sosai”
Matsowa inda take Bombee tayi tareda cewa.
“Karki damu ummah shikansa girkin zan baki mamaki akan sa,ba iyah wannan ba kaɗai”
“Wow mashaallah dakuwa kin burgeni sosai,mace duk inda takai da ƙwarewa kan wasu abubuwan,to a sameta ta bangaren girki ma ƴa ta,koba yanzu watarana hakan zai miki amfani a gaba ina faɗamiki”
Ɗaga kai Bombee tayi alamar taji.
Gen Muhammad dake baƙin ƙofah abin dariyah yabashi,kuma shi kansa Bombee baƙaramin burgeshi tayi ba yau ɗin,lokacin da aka juyo ana tayashi murnar samun jaruma kaamarta,cike da alfahari yake amsawa,danji yake tamkar ƴarsa ce ta cikinsa.
Wata takarda ce a hannunsa,wacce ya biya ya karba suna tahowa.
Miƙawa Bombee yayi tareda cewa.
“Ga kyautata ta musamman bisa bajintar da kika nuna a yau”
Tun kafin ta karba Haidar ya karba tareda buɗewa,takardune a ciki wanda suke ɗauke da sunan Bombee.
“Wow wow Bombee admission ne makarantar mu a Rasha Abba yabaki,kema yasaya miki form yabiya kuɗin makaranta da komai”
Zaro ido Bombee tayi jin maganar da haidar yake faɗa tamkar a mafarki yake yi mata ita,zamewa tayi kamar mutum mutumi,ta kalli wannan kana ta juya ta kalli wanann,tarasa ma shin mai zatace gameda labarin dataji,makarantar sojoji yasakata,hakan ma ba a ƙasar nan ba inda ɗansa yakeyi?
“Ƙwarai Maryam dagaskene abinda yafaɗa miki,munyi magana dama da aminina dake can wanda haidar take wajensa,nayi masa bayani akanki da kuma kuɗurinki na son cikar mafarkinki,a jiyan yagama cike ciken komai da komai na shigarki makarantar.
Dama akwai abinda zai maidani ƙasar,dan haka zamu tafi tareda a gama komai da komai kifara karatu da kuma karbar horo a can,duk da yakamata ace kinshiga tunda wuri,amma munyi musu bayanin ƙwarewarki kuma nasan zaki nuna musu hakan bazaki bamu kunya ba.
Yaraf ta zube akan gwiwoyinta akan abban tareda riƙe ƙafafunsa.
“Mezai sakani baka kunya da irin abinda kayimin abba? Ai ina mai tabbatar maka baxan taba baka kunya ba saima mamaki,Zanyi matuƙar ƙoƙarina nayi amfani da wannan damar daka bani.
Saidai gameda godiya bansan mai zancen ba akai,banida kalmomin dazasu isheni wajen godiyar. haidar Ummah ku taimakeni wajen godiyar wanann gagarumar kyauta dayayimin”
Dukkansu ɗagowa Bombee sukayi daga ƙasa,inbadan idonta ya daɗe da ƙaiƙashewa da kuka ba dayanzu ta zubar da hawaye yayi cikin kofi.
“Baki buƙatar yimin godiya maryam,ni kin wadatar dani dakika nuna ra’ayin yin aikin,saidai abu ɗaya nake so kiyimin alfarma shine……Duk da cewa muradin rankine yasaka ki yin wanann aikin,ina so ki saka muradin kare ƙasarki a farko kafin naki muradin,ta hakanne zaki zamo jarumar a ƙasarki ta gado,kuma ki zamo kariya ga rayukan al’umma.
Idan kikayi hakan kigama yimin godiya akan abinda nayimiki”
“Angama zanyi yadda kace abbah,daga yau zan ajiye muradina har sai na yiwa ƙasata aiki tukunna,na tsaida gaskiyah da kuma adalci tukunna,sannan zan tsayah na kare ƙasata da kuma rayukan al’ummata da rayuwata”
“Shikenan ku shiryah tafiya to Allah yamiki albarka”

Shiryen tafiyar su Bombee aka farayi,dan gabaɗaya gidan suka tafi,inyaso sai su dawo bayan angama komai.
Kaman yanda gen Muhammad ya faɗamata kuwa saida akayi mata gwaji wanda zai tabbatar shin zata iyah ajin da haidar yake,wato division 2C.
Duk da tasha wahala amma kuma tayi nasara,don saida tayi sati guda tana training tukunna.
Satinsu gen Muhammad biyu suka jiyo,bayan sun tabbatar babu wata matsala,kusan haidar yafi kowa murna da zuwan Bombee ɗin,wanda bai taba zato ba.
Bayan shekara Uku da zuwan Bombee Ƙasar rasha zuwanta nigeria baifi Sau uku,kowanne kuma hutun,shima dukka hutun ƙarshen shakane da ake basu. Abubuwa da dama su faru,ciki harda Nasarori data samu da a mission masu yawa da ake yawan turasu kasashe.
Ta girma kwarjini da haiba sun bayyana mata,Iduwanta sun saje da yanayin kasar,inba tayi hausa ba bazakace dama baƙar fata bace.
Tana farin jinin mutane sosai,saidai kuma kowa yasanta bata ɗaukan raini,mussaman ga waɗanda suke a ƙasanta a makarantar.
A cikin shekaru goma sha takwas tayi nasarar shiga matakin finale divition,wanda zasuyi shekara ɗaya a ciki kafin su gama.
Shikuma Haidar yagama nasa karatun wannan shekarar,saboda dama shi nasa bangaren na abinda ya shafi na’ura ne dakuma su haiking ko detecting,shiyasa dole zai koma gida ya barta.
Da farko yaso zama har sai ta gama,kuma dama Air force na yankinsu sun nemeshi yayi aiki dasu,Gen Muhammad ne ya nuna ƙin amincewarsa,kan cewar saidai su dawo gida suyi aiki a inda yake wato Abuja.
Hakanne yasa yataho barta saita gama tukunna.
Kuma dama a lokacin ma bata ƙasar sun tafi practical training a ƙasar Iraq. Wanda aka turasu duk yana cikin Exam ɗinsu.
“Wonder woman nikam zan tafi gida,abbah yacemin nakoma basai na jiraki ba”
“Dama menene najirannawa kaman wata jaririyah,Man a ɗaga hanya ayi gida kawai,saina iso nima inaga zanyi koƙarin gama aikina zuwa nan da wata shida”
“Haka ma zakice bakya kewata koh?”
“Nayi kewarka,Haleesa ce ni(Wata ƴar Lebanon ce a division ɗin su Bombee ta nace shi take so,hakanne ma yasa ta mannewa Bombee tana ce twin sister ce) dazanyi kewarka iyeee?”
“Mtsww dan Allah kibar zancennan mana,wai serious baki damu ba zan tafi na barki”
“Dama dani kazo,ina ka rigani zuwa,nayi ƙoƙari ma daya zamo iya ratan shekara guda zaka bani……kai sai anjima muna cikin sahara ga zafin rana,kayi distarcting ɗina,bakajin ƙarar bullet ne?”
“Inaji mana i know is normal ai,menene na ɗaga hankalin kece fah,Captain ta farko a School ɗin mace mai shekara goma sha takwas”
Yaƙarisa maganar yana dariyah.
“Gerrot bakada aikinyi Ka gaida su ummah,ina bata kewata danna buge mata yara wancan hutun koh”
“Ohh wannan keda ita”
Katse wayar tayi tareda yin ƙaramin murmushi tana tuno Alkhairin familyn gareta,wanda duk tsiyarta bazata manta ba.
Wanda gashi sanadiyyarsu tana shirin cika muradinta na zama jaruma,wacce zata ƙwaci kanta idan za’a zalunceta.

BAYAN WATA SHIDA

A cike filin yaye ɗaliban da ɗumbin mutane,wasu na farincikin gamawar ƴanuwansu,yayinda wasu kuma nasu ƴan uwan sun mutu a practical ɗin dasukayi.
Ƙiran sunaye ake ana basu certificate ɗinsu na shaidar zama cikakkun sojoji.
Anƙira mutane da dama wanda yawanki dukka mazane..
Ana zuwa rukunin mata itace sunanta yazo a na uku,bayan wata ƴar rashan sai kuma ƴar sudan sai ita.
Ita kaɗai tazo ta karbi nata Certificate ɗin cikin sarawa da nuna girmamawa ga manyan nasu.
Kai tsaye tana karba Dorm ɗinsu ta wuce na mata taɗauki ɗan ƙaramin akwatinta.
Daga nan kuwa tajawoshi zuwa waje.
Sa haseela suka haɗo daga gani dama ita take jira.
Gaisawa sukayi kafin tacewa Bombee. (Cikin harshen turanci)
“Maryam yana ganki ke kaɗai,bazakiyi party ko kuma irin hotuna da Familynki ba,zuwa gobe saiki tafi”
“Ahah bana buƙatar wannan abubuwan,family nama basusan da dawowata ba saina isa tukunna su ganni, Dan sunyi zaton ina cikin Masu fita ne nanda shekara guda”
“Eh haka ne,amma ainihi da sai wani wata shidan zamu fita dake,gaskiya keme sa’a ce maryam”
“Kuma jajircewa,dan saida na jajirce tukunna ba iya sa’ar ba,kinga tafiyata nan dama tunjiya nayi booking na jirgi”
“Ehh am maryam Uhm Haidar…….?”
“Ki ƙirashi idan nemansa kike kin matsu,natafi tacan tacan”
Bombee taƙarisa yimata maganar tana cikin tafiya,saida tayi nisa ta ɗagomata hannu batareda ta juyoba tafiyar kena……

Ƙarfe 2:00pm Agogon nigeria Da Niger Jirgin su Bombee ya sauƙo daga rasha,kasancewar tana cikin guda uku na rukunin mata,yasa a cikin kyautar jinjinawarta kawai tiket dama na jirgi.

Bayan ta jo fitowar daga jirgin saida ta tsayah tukunna ta shaqi iska na daƙiƙu.
Murmushi tayi tareda cewa.
“Na dawo da wacce kuma za’a fara Allah masani”
Sanye take a kayan sojoji,ko sanjawa batayiba daga inda ta aka sallameta,After long dress ta ɗora akan kayan baƙa,sai ta saka hulama baƙa akanta,mai makon Jar hularta ta uniforma.
Boot ɗin sojojine a kafar ta,wanda take tafiya kaman tana faret saboda tsabar sabo.
Ga fatar jikinta tana nan da farinta,saidai kana gani kasan bawani jin dadi ta samu sosai ba.

Page 🖤15••16🖤

Mutane da dama a wajen idonsu na kanta,musamman ganinta da Kayan sojojin rasha ɗin,kuma ga idonta ya nuna daga can ɗin take.

Taxi tazo tara,tana saka hannu zata shiga motar taji anyi mata magana a bayanta.
Security su uku maza. Turanci suka farayimata dan a tunaninsu batajin hausa.
“Am madam daga ina haka,shin zamu iya ganin katin Visa ki?”
“Eh akawai visa amma akwai wannan ma”
Ta mayar musu magana da hausa tareda miƙamusu ID card ɗinta na Shaidar ɗan ƙasa.
“Ko kunfi buƙatar visa kai ba ID card ba”
Taƙarisa magana a zuciye,shuru sukayi cikeda mamaki,wanda hakan yasa itakuma ta juya tashi taxi ɗin.
Kwatancen inda zai kaita tayi masa,tareda kwanciya a jikin kujerar motar tana sakin ajiyayyen numfashi na gajiyah.
Kaman ance da Nu’aimah ta ɗaga kai,tana taimakawa mai aikinsu bawa shuka ruwa,ido biyu sukayi da Bombee wacce take a tsaye a gabanta ta naɗe hannu tana kallonta.
Mitstsika idanuwanta tayi domin shin taga dagaskene Bombee ce a gabanta kowa.
“Addah Bombee dagaske kece nake gani kuwa”
“Uhm ko kin taba ganin wata aljanar dama mai kama dani?”
“Ummah addah Bombee tadawo,wlh dagaske nake kin ganta a waje.
Hajiya Zulaiha ce suka fito a tare itada Farouq.
“Ƴa ta wannan tafiyar kuma fah,ko matsala aka samu a makarantar kika dawo yanzu?”
“Ahha ummah na gama,jiya akayi bikin yayemu ma,a sannan na hau jirgi na taho gida”
Ƙarisowa wajen tayi tareda kama hannun Bombee ɗin
“Naji daɗi danaji cewar kin gama cikin sa’a,saidai banji daɗin yanda kika ɗaukemu ba,tunda har za’ayi bikin gamawarku ki taho batareda munsaniba”
Ɗora ɗaya hannun nata tayi akan na Hajiya Zulaiha kafin ta ɗora da cewar.
“Ahah ummah banason ɗoramuku nauyine dayawa a kodayaushe,inada kuɗin dazanyi amfani dashi na taho shiyasa kawai ban damu abba ba,nasan idan na faɗa zai iya cewa ma shizai ɗakkoni,bayan busy yake da aiki. Karki damu komai lafiya tunda na dawo zance wuce ummah”
Bombee taƙarisa maganar cikin sigar neman afuwar abinda tayi.
“To shikenan,amma kinyiwa kanki saidai ki zauna a ɗakin Nu’aimah,tunda naki kam baa gyare yake ba,babu wanda yasan da dawowarki”
Daga haka Hajiya Zulaiha tajuya ta shiga cikin gidan suma suka bita a baya,tun a hanya Nu’aimah tafara bata labarin abinda tayi missing.
Bayan taci abinci tayi wanka lafiyar gado tabi,bata daɗe da kwanciya ba su Haidar suka dawo daga waijen aiki shida Abbansu,Hajiya Zulaiha ce ta sanar dasu dawowar Bombee ɗin. Suma sunyi mamakin hakan,duk da zuwa yanzu sunsan halin kayarsu.
Deciding sukayi kan bazasu tasheta ba,gwanda ta huta tukunna.
Hakanne yasa basu haɗuba sai a wajen cin abincin dare.
Hirar yaushe gamo aka fara bayan an gama cin abincin dagannanne kuma magana mai muhimmanci ma tashigo na gameda matsayin Bombee a yanzu,dakuma abinda yadace tafarayi a lokacin.
“Toh maryam yanzu dai tunda kin dawo lfy ɗauke da sakamakon da ake so shine abin farincikin.
Saura kuma aiki,nayi magana da gen captain ɗin dake division ɗina,Zai adding sunanki da ɗaya daga cikin Captain din dake ƙarƙashinsa,idan kinje saiki ga yanda abin yake,domin za’a baki wanda zasu kasance a ƙarƙashinki”
Murmushi Bombee tayi kafin da ɗora dacewar.
“Nagode abbah da duk karramawarka a gareni,inshaaallah zanyi aiki da gaskiya kaman yanda nayi maka alkawari,bazaka taba samuna da wani mungun nufi ba”
“Yawwa naji daɗi hakan,kisake zuwa ki huta kafin zuwa goben to,akwai kyautar dazan miki na wannan gagarumin jarumta da kikayi”
Dare yaɗan raba an daɗe da isha,baccine yagagareta duk yanda taso da tayishi,hakanne yasa ta fito filin gaban gidannsu tana kalle kalle,dama ga farin wata ya haske ƙasa daga sama.
Riga da wandone a jikinta,amma basu kamata ba,sai ƙaramin hijabi data saka ita kafaɗa.
“Ka fito najika”
Fitowa haidar yayi daga inda ya labe yana ganinta,nufar ta yayi yana murmushi na ganinnata,dan dama yaso tunda ta dawo suyi magana amma basuyi ba.
“Ke ma kinkasa baccin koh,hmm har yanzu horon rashin bacci da daddare nima baibar jikina ba,inaga kuma yake?”
“Haka fah,dan ni nafijin daɗi bacci da rana akan dare,ganinsa nake kaman shine lokacin aikina,musamman dama daya zamo ni basuda wani banbanci sosai a wajena”
“Oh wanann ganin darennaki koh,shin ne Dagaskene abinda mutanen garinku ke fada akan idonki ko kuwa”
Ƴar karamar tsukar takaici Bombee tayi kafin tace.
“Hmmm ƴan ranin hankali ba,naje nayi bincike akan hakan,matsalar aljanuna bata shafi idona ba,kowanne zaman kansa daban,kuma kowanne nasan dalilinsa”
Zaro ido haidar yayi tareda cewa
Kina nufin dagaske suke ba kalau kike ba”
“Kana tsoron karna cutar dakaine wata rana?”
Jijjiga kai yayi cikeda jin kunyar zaburar dayayi.
“Ahah idan cutarwane ai da kin cutar dani tun a baya,sannan kuma nine dakaina na tunkare ki ai,duk da nasan kinsha banban da sauran yaran danake gani a lokacin,musamman a cikin mata. Amma yaya idonki kuma menene dalilin dayasa aka haifeki dashi a haka”
Yafaɗa tareda ƙoƙarin kauda wancan zancen.
“Ka fiye tamabaya Haidar,inka matsu kaje kayi bincike akai kaman yanda nayi,shin mai yasa idona ya kasance a haka.”
Ta ƙarisa maganar tana ɗaga masa gira,alamar tana challenging ɗinsa,da haka ta bar wajen ta kyaleshi.
Jijjiga kai yayi tareda cewa.
“I love this nature of you maryam,you are amazing”

Washagari da safe tare dukkansu suka nufi barrak din,karon farko tun a ganin level ɗin aikinta ta samu matakin captain batareda matsala ba,zabi aka bata na ta karbi gida ko kuma zata zauna a side din captain dake dorm ɗin mata.
Da farko gen Muhammad yaso ta zauna a gida ta dunga zuwa,musamman dan haka ya bata sabuwar mota dalleliya a matsayin kyautarta,amma haka taja ta tsayah akan a barrack zata zauna,dan haka dole ya ƙyaleta,saita dunga zuwa musu da yawo.

Kayan jikinta ta cire,daga ita sai towel mai adon zanen kakin sojoji,banɗakinta ta nufah na cikin dakinnata,kira ta jiki ba’a magana,musamman kuma jikin daya samu fitaccen workout yanda ya kamata.
Minti biyar ma basu cikaba ta fito daga wankan.
Sharp sharp tasaka kaya ta nufi kitchen ɗinta dake cikin side ɗinta na dorm ɗin.
Omlett ta haɗa na kwai gashashshen biredi sai ruwan tea.
Cikin ƙanƙanin lokacin ta gama komai tayi niyyar fita.
Mai yi mata aiki ce tashi tafara,dan ta faɗamata kan cewar sai tagama komai kafin tazo ta gyara.
Kai tsaye division dinsu ta nufah,inda zata ga ƴan team dinta da suke karƙashinta.
Mutane biyar ne,mata uku maza biyu,wanda Haidar ne yazaba mata da kansa,da alama dama yasansu kenan,itace baƙuwa a cikinsu,daga yanda suke magana da dashi kafin ta iso.
Ɗagowa yayi ya kalleta tana tsaye ƙiƙam tasaka hannun a aljihun wandonta.
“Haidar sannu da aiki,da abokanka ka haɗani ko kuma da waɗanda zasu tayani aiki?”
“Da dukka biyun na haɗaki,kuma zasu taimaka miki fiyeda yanda kike tunani,wannan abokina ne munyi wata shida dashi tare,Shine second captain Wato Khamees ,sai sauran Mabiyan a hankali zaki sansu dukka”
Ƙaremusu kallo Bombee tayi na dan lokaci,kaman yanda yafada kam basu da matsala daga ido,amma dai lokaci ne zai bayyana komai.
Tundaga wannan ranar Bombee takama aiki haikam babu kama hannun yaro,wanda har takai tayi shekara guda tana aiki. A iya cikin wannan lokacin tayi aiki na bajinta da dama,wanda hakan yasa gen Muhammad yakeji da ita da kuma alfahari da ita.
Lokacin tantance Field marshal yayi,za’a dauki ɗayah tsakanin Gen Muhammad da kuma gen Abdu manga.
Kowa a yanzu iya ƙoƙarinsa yake wajen ganin ya kai abokin takararsa ƙasa,shikuma yayi nasara,domin tsawon lokaci aikinsu a kunnen doki yake tafiyah,dole ana buƙatar zakaran dafi.
Harbi ne yake tashi a ta kowanne sako a cikin dokar daji,inda aka tura su Bombee aiki wannan karon.
Ƙirane ya shigo wayar Bombee ta sojoji,saurin dannawa tayi taji muryar Khamees.
“Hello Captain An samu matsala fah,maza kuyi gaggawar barin wajennan muma gamunan tahowa”
“Mai yafaru captain Khamees?”
“Makamanmu dukkansu basuda,mutanenmu da dama sun rasa ransu,ciki harda yan team ɗinmu guda biyu,Saikin kai hari kiji bindigar taki harbawa,kokuma kayan mu ba bullet protection bane mai kyau,idan bullet biyu suka sameshi yagewa yake,akwai matsala sosai,muyi gaggawar juyawa da wuri,Fitilar ma ɗaukewa suke na goshinmu kum…….”
Tun kafin yagama magana wayar ta katse,zaro ido Bombee tayi tana kiran sunansa amma shuru bai amsa ba.
Kallon Sojan dayake gefenta tayi,yana da ƙoƙarin saita kunamar bindigarsa amma taki yin aiki,ga fitilar sa ta mutu.
Wani ta gano a nesa ya saita shi,da sauri tayi super a kansa suka faɗi tare.
Hularsa ce ta cire taga wanene.
“Hilyaan dama kece,ina sauran suke,sannna mai yasamu bindigar kika saka harbi”
Saita ji muryar kafin tace.
“Captain inaga da matsala,fitilunmu duk sun mutu,bindigogin ma basa aiki fah”
Ɗaga ta Bombee tayi tareda runtse ido kana ta buɗe,maza ki koma da baya ki faɗawa saura su koma maboyarsu,bari zanje na taho da Tawagar su Captain khamees.
“Ammma captain maryam bakida fitila a hannunki,taya zaki bani taki”
“Dama riketa nayi ba amfani nake da itaba,kedai kiyi yadda nace kawai,maza ki koma”
Tana gama faɗamata haka ta nausa cikin duhuwar dajin kaman an cillata.
Da ƙyar da siɗin goshi suka samu damar barin wajen,bayan wasu a cikinsu sun rasa ransu.
Sati guda akayi ana zaman makoki na rashin Abokan aikinsu da sukayi. Duk da kowa bai kawo komai ba a rashin nasarar,amma su Bombee sun sakawa abinda ya faru ayar tambaya,hakanne yasa suka fara bincike a boye batareda sanin kowa ba.
A zaune take itada khamees a ƙaramin office ɗinta na division din,haidar ne yashigo da kayan aiki a jikinsa,ɗazu yaga ƙiran Bombee bai samu damar zuwa ba sai yanzu.
Gaisawa sukayi da khamees hannu da hannu,sai kuma salute daya mikawa Bombee na wasa.
“Yah captain naga kirnaki inakan aiki,meyake going haka?”
“Uhm inason sanar dakaine cewar,muna buƙatar taimakonka na wani abu dayake faruwa gameda barrack”
Labarin mai suka fuskanta a wajen yaƙi ta faɗamasa dukka,shima kansa yayi mamakin hakan,babban abin ayar tambayarma shine yadda a cikin manya babu wanda yace wani abu kan lamarin.
Ajiyar zuciya ya sake tareda cewa.
“Shikenan naji abinda kukace,inshaaallah zanyi iya ƙoƙarina wajen na taimaka,akwai abokiyar aikina danake son na shigo da ita ciki,tana da jajircewa,kuma taƙware wajen binciken irin waɗannan abubuwan”
“Uhm bazan hanaka kawota ciki ba,amma baka ganin akwai matsala kuwa musaka wata bare?”
“Kai Bombee kidunga koyon yarda mutane mana”
“Ohk shikenan Allah ya taimakemu,amma koma wani bazai taimaka nikam bazan bar rayuwar mutanena ta tafi a banzaba haka nan”
Su shidane sai wacce suke aiki tare na binciken na ura wato Sameerah,sai kuma kuma Bombee da khamees,Hilyaan da kuma Bilal Ɗaya abokinsu daya rage.
A cikin sirri suke aikin batareda sanin kowa ba saisu kaɗai,suka fara gudanar da aikin binciken.
A wani bincike da haidar suke gudanarwa da daddarene suka samo wani clue a cikin daji da daddare,domin akwai motoci dake shigowa suna fita,basa yin hakan kuma sai cikin dare,wanda suke da tabbacin cewar yanada nasaba da bindigoginsu,domin bayan yin yaƙin,tun a hanya wata mota tazo ta tafi da makaman dukkansu,kuma sunga shigar motar wajen a Camera.
A dare suka sanar da su Bombee abinda yake faruwa wanda sun tsayar da shawarar da gobe zasu nufi Cikin dajin inda Nau’urarsu ta nuna musu.
Gen Abdu manga ne a zaune yana kurbar lemo a kofi a cikin office ɗinsa.
Sameerah ce tashigo tareda sara masa,saida yayi mata alamar hannu kafin ta gyara tsayuwarta.
“Mai kika samo wannan lokacin kuma?”
“Sir yanzu kam nasamo wani abun,wanda ina mai tabbatar maka dazamu yi nasarar kaiwa Gen Muhammad ƙasa da tawagarsa,sannnan kuma ina mai gargadinka da cewar,Captain maryam tagano cewar,makaman dakayi order wannan karon Basuda kyau,idan takai wanann rohoton division,ina mai tabbatarmaka da zata ga bayanmu,ba iya ga babbar kujera ba,harma ga rayuwarka saita shiga haɗari,domin sanadiyyar amfani da makaman yajawo rashin nasarar da Rukunin sojoji tayi a harin daya gabata,yanzu haka sun nufi black room domin gano shaidu akan aikin da muke aiwatarwa.
Saurin ajiye cup ɗin dake hannunsa yayi tareda tashi ya tsayah,dunƙule hannunsa yayi tareda cije baki.
“Wannan yarinyar wai ya zanyi da itane,tun zuwanta wajennan na tsawon shekara guda,babu abinda take sai kawomin cikas,da kuma kawoma gen Muhammad nasara,da farko nayi zaton ƴar sace,sai daga baya na gano cewar riƙonta kawai yayi.
Yanzu toh ya kike gani,ta wacce hanya zamu bullo musu?”
Dariyar gefen baki tayi kafin tace.
“Karka daku yallabai baza’a samu matsala ba,sun riga sun gama amincewa dani,basuda masaniyar ina tareda kai,inaga kwantan bauna zamuyi musu,mu biyo musu ta bayan gida.
Kaman yanda suka ce zasu black room mu barsu suje ɗin,Akwai Detect camera da zamu saka a jikinmu domin gano inda muke,iyah haidar ne yasan yanda ake kasheta da kuma yanda ake Kunnata,tanada amfani da yawa kana kuma tana da matuƙar hadari.
Idan aka danna danger alarm ɗinta,to zata rarwatsa tsokar jikin mutum a area datake,idan aka sakata a wajen zuciya to mutuwa ne direct in aka hareta.
Nida haidar ne kaɗai mukasan yanda ake Hari da ita,zan baka controller a gobe inshaaallah,kafinnan zamu tsara yanda komai zai tafi”
Tafi Gen abdu manga yafarayi irin na alamar jinjinawar nan,Haƙiƙa ina Alfahari dake,zan haɗaki da mutanen dazasu taimaka miki,wannan karon ki tabbatar kinyi nasara,idan har hakan ya tabbata,to zan baki matsayin da kika daɗe kina nema”

Kaya suka gama sakawa baƙaƙe wanda zasu saje da aikin dazasu fitan.
Rataya bindigoginsu sukayi,saida suka tabbatar kowa ya shiryah kafin suka fito daga cikin inda suka buyan.
A hankali suke tafiya cikin sanɗa,kowa yana kallon inda kowa yake,saboda abinda suka saka a jikinsu,tafiya sukayi mai nisa suna bin na’urar datake nuna musu inda zasu nufa.
Wani waje suka iso a tsakiyar dokar dajin,ba gidane haka normal ba,haka yake square na ƙarfe,kallo kallo suke kafin suka rarrabu kowa ya saita,wasu kuma daga cikinsu suka shiga,saida na wajen suka tabbatar komai normal kafin suka shigo.
Ɗakuna a cikin wajen sukan guda goma,saikuma filin tsakiyar wajen wanda yafi ɗakunan girma,babu koma a cikin wajen sai warin tsatsa da kuma motocin yaƙi guda uku.
Duddubawa suka farayi kowanne daki,abinda suka samu ya basu mamaki matuƙa.
Dukka cikin wajen makaman yaƙi ne kala kala,harda wanda ba’a yarda ayi amfani dasu ba.
Hakan bai basu mamaki ba kaman ruwan wasu allurai dasuka samo a wajen.
Kawosu sukayi kan wani babban tebur a tsakiyar wajen sukayi,kowa ya zubawa abubuwan ido baya cewa komai.
“To yanzu waɗannan alluran akan wa za’ayi amfani dasu kenan,tabbas gen abdu manga ba baƙaramin murum mai hatsari bane,dolene mukai wadannan abubuwan zuwaga headquarter,domin ayi mummunan bincike akai”
“Hakane dama dole mu fitadasu bilal,ta hakane za’a yanke masa hukunci,sannan kuma mu ɗau fansar abokanmu da suka mutu a wajen yaƙi saboda mummunan aikinsa,irinsune suke sakawa a zagi sojoji kuma a dungayimusu kallon Azzalumai”
Fara tattara kayan sukayi da niyyar tafiya dasu,duk abinda suke Sameerah na tsaye tasaƙala hannunta tana kallonsu,saida suka gama haɗa komai kafin ta sheqe da wata arniyar dariyah tana tafa hannu.
“Captain maryam,da kuma captain haidar kuda mutanenku haƙiƙa kunyi ƙoƙari sosai,da tun lokacin da kuka fuskanci akwai wata matsala kukayi shuru,da baku kawo kanku mahallakarku ba,amma yanzu kam aikin gama ya riga yagama kun haƙa raminku da kanku.
Kuskurenku ɗaya shine bari da kukayi na san shirinku.
Saitata da bindiga bilal yayi zai harbeta,da sauri Bombee tayi saurin riƙeshi ganin abinda take riƙe dashi.
“Yana harbina zan dannan abinnan,duk wanda nice na saka musu na’ura ba haidar ba to zata tarwatse a cikii ƙirjinsu tareda Zuciyarsu”
“Me kina nufin a wajen zuciya kikayi injecting ɗin na’urar Sameerah,amma kinsa ba’a saka waje mafi hatsari,shiyasa dana cemiki wajen ƙirjina naga ciwo kikace cokata kikayi baki sani ba?”
Da murmushi ta daga masa kai alamar eh.
Juyawa yayi ya kalli inda Bombee take,fuskarsa dauke da nadamar abinda ya faru,domin gani yake duk laifinsa ne Sameerah tasan shirin su,da kuma abinda zasu aikata.
“Karki damu maryam,har yanzu muna da damar yin nasara,karku damu ku banasaka muku a wajen da zatayi muku illah ba,sannan nariga na danna tawa na’urar,nasan division ɗina sun karbi sakon,kuyi saurin barin wajennan yanzunna kafin lokaci ya ƙure”
Jijjiga kai Bombee tayi hawaye na ziraro mata,ba abinda taki jini irin ganin haidar ɗin a haɗari.
“Hhhhhh kunfah riga kunzo hannu,babu wanda zai tsira daga cikinku,bari kuga na fara da wasu”
“Tana gama faɗin hakan ta danan jar danjar datake hannunta,tass kakejin a ƙara a ƙirjin mutane biyu,da bilal da kuma Haidar”
Wata irin gigitacciyar ƙara Bombee tayi tareda ƙiran sunan sa kaman maƙogaronta zai fice.
A
Da gudu ta nufi inda ya tsaya akan gwiwoyinsa dafe da ƙirjinsa,kallonta yayi da idanuwan da suka rasa rayuwa a cikinsu,
“Bombee ƙawata,naso maidaki matata saidai hakan bazai taba yiyuwa ba,da alama banine mijinki ba Bombee,koma waye zai kasance mijinki kice masa yayi sa’a, Bombee kiyafemin abinda nayi miki daga haɗuwata dake,sannan ki nema min gafarar iyayena ma,ina sonki sosai”
Daga haka yafara faɗan kalmomin da batajin abinda yake faɗa har yayi shuru.
Jijjiga kai tafarayi tareda cewa,
“Bazaka mutu ba Haidar ina alƙawarin da kamin na ganin ranar dazan dau fansa,indan naƙi aurenka ne ka tafi,zan aureka Haidar kada ka barmu banida tamkar ka a wannan wajen,bazan juri rashinka ba,karkamin haka na roƙeƙa haidar,nima inasonka a har cikin raina”
Tana tsugunne a wajen taji khamees yana kiran sunanta.
“Maryam maza ki bar wajennan akwai haɗari”
Kafin ya rufebaki taji alamar samu mutane suna shigowa,saitata Sameerah tayi da bindiga zata harbeta,tun kafin ta harbetan ita ta fasa mata hannun da take ɗauke da bindigar,kafin ta karamata taji khamees ya fizgeta sun bar wajen.
Ƙoƙarin kwacewa take tana kallon wajenda gawar haidar take,
“Khamees kabari na ɗakko shi tukunna,sannann nayi daga daga da tsokar waccar tsinanniyar,sannan ne zan bika mubar wajennan”
“Kai Maryam ki fahimata mana,muna cikin yanayi mafi muni,dolene mubar wajennan,shikansa haidar idan yana raye zaiso ki bar wajennan”
Yayi maganar yana share guntun hawayen dayake zubo masa.
“Inji uban waye ya mutu,bazan bar wa…….”
Ɗan duka yakai mata a wajen ƙasan kunnenta,nan da nan kuwa tayi shuru ta suma,kinkimar ta yayi yanufi fita da ita daga wajen.
Muryar Sameerah yaji wacce take ihun hannunta tana shunensu.
Shida Hilyaan ne kadai idonsu biyu,sai Bombee wacce yasaka a kafaɗa,gudu suke falfalawa a cikin daji har saida suka gaji suka tsayah.

A bangaren Sameerah kuwa sojojine suka shigo wajen,domin saƙon Haidar ya isa garesu,iya Sameerah ce kawai a wajen tana riƙe da hannunta,tana ganinsu tasaka kuka tareda cewa.
“Yallabai ka taimakeni,captain maryam ce ta kasheshi tareda ɗaya Sojan,nima dan bata sameni bane wajen makasa da ta kasheni,inbaka yarda dani ba ka duba bullet ɗin da shaidar dukka natane,a ƙirjinsu dukka ta harbesu”
“What ina take,sannan mai kuke a wajennna”
“Uhm in labene jiya sai naji suna zasu jawoshi wajennan su kasheshi,to dana biyosu saina ga sun harbeshi,shi wancan yana cikinsu,amma sai yace bazai yi shuru ba,shine shima suka kasheshi,danayi kokarin cetansa nima ta harbeni,tana shirin kashenine haidar yace ai yatura saƙo division ɗinmu,shine sukaji tsoro suka gudu”
“Itada waye a tareda ita?”
“Uhn…….uhhh itada Mataimakinta ne captain Khamees”
Sameerah tana gama basu labarin ƙaryar ta suma,gawar haidar da bilal suka ɗauka inda a daren aka baza neman su Bombee a cikin garin abuja da kewaye.
Labari yana isa kunnen gen Muhammad yafaɗi jininsa ya hau,da farko bai gaskata abinda Bombee ta aikata ba,saida shaidu suka fito,kuma ta rashin bayyanar Bombee yasa yafara yadda hakanne,saidai duk yadda yayi tunanin menene dalilinta na hakan yakasa ganowa.
A kwana basufi uki ba labarin abinda Bombee tayi ya karafde cikin barrack da kewaye,kowa banda tsinuwa babu abinda yake yimata.
“Lokacin da Bombee ta farfaɗo a cikin kogon da suka buyah,taji labarin abinda yake faruwa,wanda Hilyaan ta jiyo musu,tunda ita babu wanda ya zargeta,zuciyarta ba ƙaramin tafarfasa tayi ba.
Yanzu kenan da wanne ido zata kalli iyayen haidar,bayan suna mata kallon wacce ta kashe musu ɗansu.
“Khamees inada wajen dazamu je,dolene mu bar garinnan kafin komai ya lafah,dolene na dawo na ɗauki fansa,ke Hilyaan ki koma bakin aikinki kawai”
“Ahah cap……anty maryam,na ajiye Aikin soja harsai ranar da sunanki ya wanke zan kasance taredake idan harkika bani damar hakan”
Shuru Bombee tayi batada abin cewa,dan gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi a lokacin,haka zata ƙare rayuwarta kenan ana yi mata sharrin kisa,anya kuwa zata iya sake yarda da wani ma????……

***DAWOWA LABARI***

Page 🖤17••18🖤

***DAWOWA LABARI***

Shirye shiryen komawa new side Lubna takeyi,dan bazata fara sabon aikin da boka zulungum yabata a wajenba.
Gobene kuma dawowar Jabeer daga Tafiyar dayayi,kuma goben takeso tasakashi ya kori Bombee daga side ɗin da take,dan da ita yadace badawata can banza ba.
Haka ta wuni tana saƙawa da kwancewa ita kaɗai.
Muryar Bishirah ce ta katseta daga tunanin abinda tashirya gobe tayi,
“Uhm ranki yadaɗe an samo baƙar kuliyar kaman yanda kika ce”
“Yawwa Bishirah na gode,dafatan dai babu wanda yaganki da ita koh”
“Eh babu wanda ya ganni,a cikin kwali na shigo da ita,nasaka mata maganin bacci a kifin kaman yanda kika ce”
“Shigomin da ita yanzunnan”
Fita Bishirah tayi,bata daɗe ba sai gata da mage a hannunta,ta langabe sai bacci takeyi.
Duk da tsoron dayake cinta haka ta daure ta karbi magen tareda nufar ɗakinta da ita,bayan tayiwa Bishirah gatgaɗin kartaji wannan zancen.
Banɗaki ta nufi da ita inda ta ajiye suƙa da kuma maganin. Wanda yake cikin kasko.
Hannunta yana rawa yana komai haka tasaka wuƙar ta yanka wuyan magen,jini ne yafara zuba a cikin kaskon,inda magen tafara shure shure,amma haka ta riƙeta gam da hannu biyu jinin yana ɗiga,a duk Lokacin daya ɗiga sai yayi cuuu kaman ruwa ya ƙone ajikin abu mai zafi. Da haka har ta gama tass kafin ta jefa gawar magen a cikin leda tasaka a durt bin.
Ɗaukar kaskon maganin tayi ta maidashi inda tayi masa kyakykyawar ajiyah.
“Anyi ɗayah,hmmmm duk wanda kuka rabi Jabeer kun shiga uku da baƙin ciki,zanso naga idanuwanku ranar dazanyi masa asirin da ko lasar ƙafata nace yayi sai yayi batareta musu ba. Wuyar wata ukun tacika,zakuga abin mamaki da idanuwanku”
A zaune yake akan gado yasaka fararen kaya marasa nauyi masu laushi na bacci.
Waya ya danna tana ringing amma har yanzu ba’a ɗauka ba,tun kwana uku da zuwansa yagama abinda ya kawoshi,da gangan yaki komawa saboda abinda zaije ya tarar,musamman daya samu suke waya da Jaleelah,koyaushe suna maƙale suna zubawa juna soyayyah.
Wannan lokacin yayiwa Jabeer daɗi da har bayason su shige daga cikin rayuwarsa.
Yana cikin saƙar zuci Jaleelah ta ɗaga ƙirnnasa.
Da sauri yakai kunnensa domin kar yayi Missing zazzaƙar muryarta,aikuwa kaiwarsa keda wuyah yayi kicibis da itah.
“Assalamu alaika masoyina”
Saida ya lumshe ido na tsawon lokaci kafin ya amsa sallamar
“Wa’alaikissalam Sarauniyar zuciyar Jabeer”
Daga nan suka cigaba da hirarsu kaman kodayaushe,maganar aure ta sako masa akan Mahaifinta yace ya turo.
“Yah Jabeer idan har dagaske sona kake babana yace katuro ayi maganar aurenmu,domin na faɗamasa cewar muna soyayya dakai,kuma ya yaba da abin har yayi bincike akan ka”
“Uhhh to shikenan karki,nafiki zaƙuwa wajen ganin na mallakeki a matsayin matata,bakisan yanda nake jinki a cikin zuciyata bane shiyasa,ina mai miki alkawarin cewar dana koma gida zan samu abba da maganar,inshaaallah aurenmu bazai wuce nan da nan Wata uku ba”
“Dama nasan bazaka ƙi amincewa ba,kaman yanda kake son kasancewa dani nima a wajennawa hakan take,ina sonka sosai,ka burgeni matuƙa daka fara zuwaga iyayena kafin a tunkareni,hakan maxa dayawa suka kasa aikatawa”
“Amma nafaɗamiki fah cewar inada mata biyu,kina ganin hakan babu matsala”
“Babu wata matsala nidai a wajena,dan haka kada ka damu,nasan kanada damar riƙesune shiyasa ka auresu. Allah da kansa yahalattawa na miji auren mata huɗu,idan har zai iya adalci a tsakanin su,dan haka indai zakayi adalci a tsakanin mu shikenan”
Da farko Jabeer baiji daɗin yanda bata nuna kishi ba,duk da kuwa hakan yake fata,amma kuma dayaji bayaninta sai bai kawo komai a ransa ba.
Hirar su suka cigaba dayi har lokacin da zuciyoyinsu suka raya musu su bari.
Wayar ta ce tayi ƙara da misalin ƙarfe takwas na safe,juyawa tayi tana lalumar haidar,bata jishiba dan haka tayi tunanin ko Hilyaan ce ta ɗaukeshi.
Wayar ta ɗauka tareda zame bargon dake jikinta kaɗan.
“Yadai khamees da safennan?”
“Hmm yanzu ne safen koh,koda yake ashe amarya ce fah.
Binciken danakeyi ya kammala,Gen abdu manga shije na biyu a kason Share mai yawa na companyn mijinki, meeting ɗin daya gudana ma kwana uku da suka gabata yaje wajen,wanda inada tabbacin akwai abinda yake saƙawa”
“So yake ya ƙwace companyn daga hannun Jabeer,da farko yayi shurune saboda in Lubnah ta haifi yara one day sune akai,amma yanzu ya sanja plan saboda ƴar sa bata haihuwa dagaske kenan……..sai kuma me,kayi nasarar cire na’urar jikinka?”
“Uhmm nayi nasara,nawa tana hannun dama ne,nikuma ina checking na hagun”
“To yayi kyau”
“Uhm tun kwana uku baya aka gama meeting ɗin,amm mijinki bai dawo ba sai yau,bazaki bincika mai yake ba a wannan lokacin”
“Wannan kuma kofin shayinsa ne,ruwansa yasha ruwan tea ko kuma yasaka madara,baya cikin lissafina a yanzu,bari zanyi plan da wanne zan fara ƳAR KO UBAN.inbaka da abin faɗa zan koma bacci”
“Kutt bazaki fara shirye shiryen taryarsa ba bacci zaki……”
Tun kafin ya gama Bombee takashe wayar tayi jifa da iya,tareda maida pillow ta kwanta.
Abinci na gani na musamman Lubnah ta jaɗawa Jabeer domin taryarsa.
Yana shigowa mamaki ne yakamashi ganin a side ɗinsa tahaɗamasa girkin,taji kwalliya cikin wata doguwar riga ja,ba lafi tayi mata kyau sosai.
Murmushi tayi masa maiɗan ɗauke da alamar takaici,saurin gusar dashi tayi tareda takowa inda yake.
“Sannu da dawowa farincikin ran Lubnah,nasan dama bazakake kaga halin danake ciki ba,side ɗinka zaka fara shigowa,shiyasa nayi komai a nan wajen”
Alama ya nuna narashin kyautawarsa akan hakan,atleast tunda zamansa take,yakamata ya je ya ganta tukunna.
“Kiyi haƙuri luby na gajine shiyasa ban je wajenki ba,amma nayi niyyar idan nagama shiryawa zan shiga ai”
Karya kai tayi irinna ƴan duniya kafin tagyara annunrin fuskarta.
“Shikenan na karbi uxurinka,yanzu tunda ka gani muje na tayaka shiryawa ko?”
“Bayyi mata musu ba,dan yanada buƙatar hakan sosai. Ita ta taimaka masa ya cire kayansa,kana ta haɗa masa ruwan wanka mai ɗan zafi,babu yadda bayyi ta ita ba kan tazo ta tayashi wankan amma taƙi.
Abin tsoronta ɗaya shine kada taganshi yana wanka zuciyarta ta jata ta aikata abinda boka ya mata gargaɗi akai,na kada ta kuskura ta bashi kanta har sai ta gama wata ukunnan tukunna chass.
Taya fito daga wanka ma bata ɗakin,tana can wajen shirya masa abinci,wanda shikansa yasan ƴan aikine sukayi,ba itace ta dafaba.
Duk yadda taso nuna kisisinarta kan yaci abincin kaɗan yaci ya tashi.
Sashen su Hajiya zeenah ya nufa domin ya gaishesu,A wajen Alh aliyu mahaifinsa yafi tsayawa suna ta hira,daga baya ya ɗau mota ya nufi wajen Khaleel,zai rakashi gidansu Jaleelah.
A hanyar zuwa gidan ya tsaya yayi siyayya mai matuƙar yawa kafin suka nufi gidan,dama tasan ta isowarsa.
Sauƙa ta musamman akayi musu,basu Jabeer ne suka baro anguwar su Jaleelah ba sai bayan isha,salloli ma duk a unguwar sukayi.
Shikansa Khaleel yana jinjina irin soyayyar da Jabeer yake yiwa Jaleelah.
Lokacin daya shigo sashen Lubnah tana kwance da waya a hannunta,ta saka kayan bacci tana kan gado.
Ɗan zabura tayi tareda ɗagowa takalli Jabeer ɗin,dan gabaɗaya bataji shigowarsa ba sam.
“Uhmm kina wannan chatting ɗin inata sallama koh”
Cikin kasalalliyar murya mai cikeda alamar gajiya da buƙata yayi maganar.
Gaban Lubnah ne ya bada sautin dumm kaman ganga,ganin Jabeer da kayan bacci,dan tasan mai yakawo shi.
Matsowa yayi inda take da niyyar kama hannunta,saurin matsawa tayi kaman taga aljani.
Wanda hakan yasashi yin mamaki matuƙa.
“Lubnah lafiyan ki kuwa?”
“Iyee na’am dama …..dama ina period ne”
“Hmmm period a wannan lokacin,har yanzu bansan yaushe kike period ba,idan akwai abinda yafaru ko wata matsala ki faɗamin ina jinki?”
Yana cewa matsala wata idea tazo kanta,saurin saitawa tayi tareda yin magana cikin sigar tausayi,yanda tasan zai yarda da ita.
“Kayi haƙuri dama banason sanar dakaine kada kaji babu daɗi,na kamu da ciwon sanyine a tafiyar dakayi,to shine dana je wajen maganin gargajiya suka bani wani nayi amfani dashi na tsawon wata uku,amma a wannan tsawon lokacin kada na bari ka kusanceni.
Kayi haƙuri ni kaina da farko nayi tunanin hakan zaisa na shiga haƙƙinka dan haka……….”
“Ahah karki shiga damuwa,lalurine yana iya hawa kam kowa,indai wannan ne babu matsala,Allah ya baki Lafiya,Yakuma kaimu har sai kim warke ɗin.
Ni barina tafi side ɗina toh”
Yaƙarisa maganar yana sumbatar goshinta.
Tashi yayi ya nufi ƙofah,har yayi nisa ya juyo tareda cewa,
“Amma bakya ganin bazamuje kiga likita ba gobe?”
“Ahah sunce kada nayi amfani dana likita har sai na gama tukunna”
Ohk”….yafaɗa cikin sanyin gwiwa,a yanda yake ji yayi zaton zata taimakeshi da wata hanyar,amma sai tama koma kan wayarta hankalin kwance,hakanne yasa shima yabar ɗakin ya nufi nasa sashen.
Da safe bai samu tashi da wuri ba,kasancewar yanda yakai dare bayyi bacci ba yana fama da laluri.
Sai wajen ƙarfe goma ya shirya ya fito.
Da Lubnah yauma yasake yin karo tayi kwalliya cikin lace tana tsaye a bakin dining,wanda yake cikeda kayan karin kumallo.
Murmushi tayi masa tareda tambayar ya tashi lafiyah,shidai a mamaki ya amsa,dan bai saba ganin hakan ba.
Surutu take tayi masa yana cin abincin har ya gama tukunna.
Yatashi zai tafi sai yaji tace.
“Amm Honey Dama magana nakeso muyi mai muhimmanci”
Komawa yayi yazauna domin jin mai zataje,dama yayi tunanin hakan,domin ruwa baya tsami banza.
“Shin idan kanada mata guda biyu,waye yakamata yafara zabar abu a cikinmu?”
“Kece yakamata ki fara zaba”
“To amma meyasa wancar matar taka tafara zaban wajen zama a new side kafin ni”
“Uhm wacce matar kenan”
Dan shi har cikin ransa yamanta wacce take magana akai,saida ya tuna da auren da Hajiya zeenah tayi masa kafin abi ya faɗo cikin ransa.
“Ohh nunamin zakayi ma kaman baka san wa nake nufiba,taje ta ɗauki side ɗin dani naji shinake so a wajen,dan haka yau ka faɗamata tabar cikinsa ta ɗauki wani,dan wannan nakeso”
“Ina side huɗune,ki dau wani mana a wajen,kowanne ma naga yana da ƙofa ta cikin side ɗina,babu wanda yake gefe,dukka a round suke a wajen”
“Nidai shinake so,domin yafi kusada lambun shaƙatawa,iskarsa ma tafi ta sauran daɗi,kawai ni yafimin shi nake so”
“Uhm kin faye fitina Lubnah keba yarinya ba,wannan side ɗin ba yafi gefe fiyeda sauran,a haka kike sonsa?”
Hanyar ƙofa ta nufa zata fita yayi saurin riƙota.
“Dama babu wanda ke sona a gidanan,a wajenka kaɗai nake samun sukuni,kaima kuma yanzu karamin abu amma ka kasa yimin shi,shikenan to naga matsayina”
“Kibar wannan zancen,indai sashen ne muje yanzu na fitarta a wajen ki shiga,shikenan?”
Goge hawayen Lubnah tayi tareda jijjiga kai,kana ta ƙanƙame hannunsa daya saka a cikinta.
Makullin motarsa ya ɗauka tabishi a baya tana murmushin cin nasara,ba koranta ne batada hanyar yi ba,tafison tasaka mijinnata datake taƙama dashi ya koreta da kansa,taga yaya zatayi.
Shiga motar itama tayi yaja zuwa sabon wajen,a cikin ƙanƙanin lokaci suka kai gurin.
Lokacin sha ɗaya tayi rana tafito sosai.
Itace ta fara fitowa daga motar ta ƙwanƙwasa kofar kafin ma ya kashe motar.
Hilyaan dake jijjiga haidar a hannunta taji ana buga ƙofar.
“Ohh wai har yanzu anty maryam baki gama bane,wasu sunzo nemanki a waje to,ga haidar yana ta kuka shima.”
Hanyyar ƙofar ta nufa tareda buɗe musu ƙofar.
Lokacin data buɗe ƙofar da Jabeer suka haɗa ido,wanda zuwansa wajen kenan ya kashe mota.
Kallo ɗaya tayi musu tareda cewa.
“Ku shigo”
Binta sukayi a baya har tsakiyar falon,wajen zama ta nuna musu tareda dan ɗaga muryarta.
“Anty maryam serious yanzu kam baƙi kikayi,gashi nace miki yaronnan kuka yake tayi”
Muryarta suka jiyo tun kafin tashigo falon.
“Ohhh baby yana missing mommy,Hilyaan ki ɗan bashi ruwa mana,ba yunwa yakeji ba,yaushe ma na zauna yasha”
Shigowa falon tayi ta dawo daga backyard ɗin gidan,tana goge gumin dayake fuskarta da wani ƙaramin towel.
“Kayan workout ne a jikinta baƙaƙe,riga iya rabin ciki,sai kuma wando iyah gwiwa,gashinta kuma ta kama shi da ribbon irin kayan,shima yana dauke da adon fararen star dake jikin kayan.
Kayan sun matseta,sosai fittet ɗin farar fatarta ya bayyana a ciki,ga kuma gumi dayake bin jikinnata.
Kallon mamaki tabi su Lubnah dashi wanda suke tsaye. Yayinda suma suke aikamata nasu kallon mamakin,musamman ma Jabeer dashi ganinta biyu dashi kenan.
Basar da kallon dasuke mata tayi tareda dan juya blue idonta.
“Ohh baƙi mukayi haka,sannunku da zuwa,saidai naga baku zauna ba”
“Hmmmm dama tun kallon danayi miki ranar a bakin gidannan,da kuma kallon danayimiki da daddare,nasan ke ba ƙaramar tatacciyar ƴar bariki bace. Ba kince ranar sai abinda kika ga dama zayyi ba,harda wani ranann nazo nemansa kika ce bazai fitoba,inna isa nima nasaka shi yayi yanda nakeso in yana wajena,to yanzu gashi na sakashi,korarki yazo yi a wannan side ɗin yanzunnan,saboda ni matarsa uwargidansa wannan side ɗin nakeso”
Zaro ido Jabeer yayi tareda kallon Bombee,jin abinda Lubnah take faɗa wanda bashida masaniya akan sa,ko kuma yaushe akayi shi. Ita ɗinma shi takalla tareda yimasa kallon basai ya sani ba.
Cikin ƙanƙanin lokaci tajuye zuwa nata salon.
Hannu tasaka a kunkuminta tayi wani malƙwaɗa tareda turo ƙirji gaba kaɗan. Yanda tayi sigar ko ƙwararriyar ƴar bariki albarka,musamman kuma data ƙara dawani rishe ido.
Lokaci ɗayah Jabeer yaji kamar wutar lantarki ta huda daga kansa har ƙarkashin ƙafarsa.
Lanƙwasa harshe tayi tareda yin taku biyu zuwa gaban Lubnah daff,harsun jin hucin juna,bakinta takai kan kunneta tareda yimata magana yanda babu wanda zaiji,tanayin magana idonta yana kan Jabeer wanda takafe idonsa a cikin nata,ta yanda bashida ikon ɗaukewa.
Saurin matsawa tayi da baya tana jijjiga kai.
“Wlh baki isa ba,ina ina kinyi kaɗan”
“Nayi kaɗan,to faɗawa mijinnaki kiji idan ƙarya ne,in kuma bazaki faɗamasa ba to yana nuna kin yarda dabinda na faɗa kenan.
Shin ya shiryah korata na bar shashennan?”
Harara ta bankawa Bombee tareda shikansa Jabeer ɗin,kana ta bangajeshi tabar shi a tsaye anan kaman mutum mutumi.
Bayan ta tafi idonsa ya maida kam Bombee tareda tunanin shin mai ta faɗawa Lubnah daya sanja ra’ayinta haka.
Itakuwa tana ganin Lubnah ta tafi ta maida ainihin fuskarta ta Bombee kaman ba itace take rausaya ba.
Samun waje tayi ta zauna tareda karbar haidar a wajen Hilyaan.
Nono tacire tasaka masa a baki nan da nan kuwa yayi shuru,faruwar hakan duk akan idon Jabeer,da sauri ya runtse idonsa ya bar falon bayan idonsa yayi tozali da abinda bai kamata ya ganiba,wanda yake da tabbacin yanda ƙwaƙwalwarsa tayi record ɗin hoton,ba lallai ya bace nan kusa ba,musamman dayake matse dama a kwanannan,Lubnah ta baro masa ruwa.
A haka yabar wajen kansa cikeda tambayoyi fall na mai yake faruwa,tukunna ma shin wannan amaryar tasa wacece ita?…
Bayan sun tafi kallon alamar tambaya Hilyaan ta jefi Bombee dashi,
“Anty maryam me yake faruwa mai kika faɗamata haka,kuma shikansa mutuminnaki naga da alama so kike ki jurashi a tarko,shin kin sanja plan ɗinki ne”
“Uhmm kinada tambaya Hilyaan,so nake kawai naga ya zayyi,sannan daga kallon danayi masa kamar Lubnah bata bashi lokacinta yanda yadace,duk wacce take son cafkar zuciyarsa zata samu a yanzu cikin sauƙi.
Magana kawai na faɗa mata,kuma da alama tayi tasiri a ranta fiyeda abinda kowa zai faɗamata.”
Lokacin data kai bakinta wajen kunnen Lubnah,ƙankance murya tayi tareda cewa.
“Wai har yanzu baki ɗago lamarin bane uwargidan angona,a tunaninki idan kika koreni anan bazai so hakan ba,zamu baje lokacin mu tareda shi a sashena,sannan kuma idan kina nan ma duk lokacin dayake wajenki,zan yi irin wanann shigar nazo wajennan da suna motsa jiki,kaman yanzu daya kafeni da ido,kina ganin zaki iya jan hankalin sa ya ɗauke kannnasa daga gareni uhm?”
Juyawa Lubnah tayi ta kalli idon Jabeer wanda yake tsaye kyam a cikin na Bombee,take wani ƙululun baƙin ciki ya shigeta,ganin tafara samun galaba akan ta yasa ta ƙara dacewar.
“Shikenan zan koma sashe na gaba wanda yake kusada shi,sannan zan dunga zuwa nan ina motsa jiki a bayan sashenki,wazai ƙi lokaci guda biyu na mijinsa. Hakan zai mana daɗi nida shi,in kuma baki yarda ba ki tambayeshi yanzu kiji,shin idan nazo motsa jikin bazai tayani muyi ba ranar dayake wajenki uhm”

Dariyah Hilyaan ta fashe da ita dataji abinda Bombee tafaɗawa Lubnah.
“Uhm na gane,wato zakiyi amfanine da kishin dayake mata ki wanata a haka koh?”
“Yess haka abin yake,tunda zata dawo nan ,dole shima nasan zai dawo nan,abin zaifi tafiya yanda nakeso”
Takarisa maganar tareda dariyar da ita kaɗai tasan ma’anarta.

Tuƙin tuwo take magriba ta gabato,rana tayi ja a yamma.
Murya taji kaman ana ƙiranta a bayanta,bata kawo komai a ranta ba tacigaba da tukinta,domin tasamu ta gama da wuri,tsayawa tayi ta juyah muciyar tareda zare ido.
“Laariiiiii nasan kinji kirana,amma kike so ki juya bayanki daga gareshi,maza kizo ga kirana yanzunnan,ranar wanka tazo ta,duk yadda kika so da boye cibi a yau bazai boyu ba,inaso ki zo kiga mijin Innayi a yau”
Jikin laari rawa ya kama kaman mazari,jijjiga kai tafarayi hawayen takaici na zuba mata,amma tasan a gaba jeji baya tsiyaki take,babu hanyar dazata bi wajen bullewa daga halin ƙaƙani kayan data tsinci kanta ciki,wanda daman tasan da zuwansa tun ran gini da kuma ranar zane.
Hnayar dakinnata ta nufah tana jan kafa kaman ƙwai ya fashe mata a ciki.
Cikin sanyin jiki ta dauki tsinken turaren ta kunna,yana bugar madubin kuwa Zilliyah ta bayyana a jiki tana dariyar mugunta.
“Laari kenan,nayi zaton ai bazaki amsa kirana ba tunda nayimiki rana?”
“Ina na isa uwar matsafa mai daraja,gani gabanki na miƙa wuyah”
Innayi wacce sai yanzu tashigo gidan ta dawo daga gidan ƙawarta,duk yawancin ƙawayenta anyi aurensu,itace kawai tasaura a gida,ko kare bai taba shinshinarta ballanta na kuma murum yace yana so.
Abin ya daurewa mutane da dama kai,ganin gata kyakykyawa dakuma ilimi,batada makusa ko kaɗan,amma yanzu ko magana mutum bayaso mlm Ahmadu yayi masa akan Innayi,saboda yana tsoron kada yace yabashi ita.
Tukunya ta gani akan wuta da tuwo a buɗe ba a gama tuki ba,waigawa take ko zata ga inna laari amma bata ganta ba,ɗakinta ta nufah,har zata shiga saikum taja ta tsaya jin tana magana da,wata mata da bata san muryarta ba.
Abinda taji an faɗane yasaka gwiwarta yin sanyi tareda zubewa a wajen,ko kaɗa kunnuwanta sun kasa gasgata mata abinda take jiyowa.

Page 🖤19••20🖤

“Kindaɗe kina min magana akan auren ƴarki to ranar tazo,inaso ki shiryata tsaff ranar gobe da daddare zan turo a dauketa.”
“Ammma shin shugaba zilliyah ina Zaki kaita kenan,dan Allah ki barmin ƴata a gabana,ita kaɗai taragemin wacce nake da”
“Yimin shuru laari,har yanzu baki san dalilin dayasa bata samu miji ba ,saboda na hana kowa ya kalleta da fuskar so,ita ɗin matar ɗanace,tunda aka haifeta ya nuna yana sonta daya ga hotonta,itace tayi daidai da wacce zata haifamin jikan dazai gajeni,dan haka zaman ta cikin mutane da kuma a gari ya ƙare,saina daji tareda aljanu,wanda nan gaba zasu kasance sune ahalinta”
Hawayene yake zubuwo a fuskar laari,lokacin dataji zilliyah tana zayyanomata Kaddarar data zabawa yar tata,wanda batada ikon magana akai ballantana kuma hanawa.
“Shikenan shugaba zanyi yanda kikace,indai ina tareda ke nasan bazan tagayyaraba,babban abin alfaharina ne na haɗa zuri’ah dake Shugaba,amma zan iya ganin surukinnawa ko a hoto,kwanaki naji kince bashida rabin fuska,sakamakon yanda wani aljani yakai masa farmaki”
“Eh bashida rabin fuska,shiyasa ma baya fitowa ga halittu suna kallonsa,ko kema bazaki ganshi ba,iyah matarsa ce zata ganshi idan an kaita gareshi,karki ji wai dan ya nakasa kiyi zagon bashida amfani,kasancewar bazai iya gadona ba yasan na yanke hukuncin samun jika wanda zai gajeni,dan haka ki yi gaggawar cika umarnin dana baki.
Ganan magani a cikin kasko,kiyi mata turare dashi,ta hakane idan na turo aljanun zasu samu damar ganinta a duniyar mutane su ɗakkomin itah”
Tana gama fadin hakan ta bace batt a jikin madubin kaman bata wanzu ba a jiki.
A bangaren Innayi kuwa tana gama jin abinda Aljanar tace taja ƙafafunta batareda sun ji ta ba tabar wajen.
Ɗakin Danejo ta nufah,tana zaune kamar kullum akan kujera ta saka gabanta gabas.
Tsugunnawa tayi a gabanta tareda kama hannayenta dukka biyun ta riƙe.
“Kiyi hakuri Inna Danejo,ki yafemin abinda nayi miki tsawon rayuwata,wlh dukka inna ce take sakani nayiwa Addah Bombee,nasan cewar itace tayimiki haka,kuma tayi sanadiyyar zaman Addah Bombee haka,amma banyi zaton abinnata har yakai haka ba.
Duk da cewar na kasance mai son kai,duk abinda take ban taba fitowa na sanarwa da kowa ba,saida a yau danaji tana da niyyar hallakani tukunna,amma duk da haka ki amincemin dama taƙarahe wajen gyara kuskurena,kodah kuwa zan mutu a hanyar hakan.
“Inna Danejo inason zan gudu daga gidan ubana,saboda abinda innata zata min,saidai bazan zama mai son zuciya ba a karo na biyu,inason na tafi tareda ke cikin duniyah na nemo Addah Bombee na kaiki gareta,daga nan saina nufi wani wajen daban.
Ta hakanne kawai zan iya gyara kaɗan daga abinda na aikata,Ki amincemin hakan kibini mutafi inna Danejo”
Innayi taƙarisa maganar tana sakin kuka tareda matse hannun Danejo a nata hannun.
Jijjiga mata kai tafarayi tareda ƙoƙarin zare hannunta daga nata,alamar bazata bita ba kenan.
“Shikenan tunda bazaki amince ki bini ba,tunda har bazaki tsallake taki wahalar ba meyasa zan tsallake tawa wanda bata ma zo ba,nayi alƙawarin bazan tafi batareda ke ba,dan haka zan zauna inna ta auramin ɗan matsafiyarta,idan na mutu ta sanadiyyar hakan kiyafemin abinda nayimiki a baya”
Tashi tayi zata bar ɗakin Danejo ta riƙo hannun ta.
Tsayawa tayi tareda juyowa ta kalleta.
Hannunta ta miƙa a gefen Kujerar ta,tafito da wata farar takarda daga ciki. Hannun Innayin ta kama ta saka mata ita a ciki.
Mamaki ne ya cikata amma dai sai ta buɗe takardar.
“Addaress inda nake aure inna ,14 way JAAN ESTATE Abuja”
“Inna Danejo wannan address ɗin na inda Bombee takene?”
Saurin jijjiga mata kai tayi alamar eh shine,dunƙuke takardar tayi tareda cewa,shikenan na fahimta inna,duk da cewar a bansan yanda zan kaiki ga garin abuja ba a yanzu,amma zanyi iyah ƙoƙarina wajen kwatantawa. Barina ce wajen Alhaji labaran na aro kuɗi da sunan Inna,idan muka tafi nasan dole zata biya kuɗin.”
Jijjiga kai nan ma Danejo tayi tareda zaro wata jaka ta miƙawa Innayin.
Kuɗine a cikin sabbi masu dumbin yawa,wanda tana tabbacin Bombee ce ta bata su ba kowa ba.
“Da ban so karbar kuɗinki ba,amma tunda na kula bakyaso na ranto kuɗin wani to zamuyi amfani da wannan kuɗin na kaiki wajen ta Da yardar Allah,abin ya isa haka.
Yanzu bari naje na nemo motar daxata fita da sassafe,saimu buyah a daji, su samemu a wajen su ɗaukemu”
Tana gama faɗin hakan tafita daga ɗakin Inna Danejo zuwa waje.
A Lokacin ana ta kiran sallahr magariba.
Sai bayan isha tukunna ta dawo gidan,kicibis sukayi da Mlm Ahmadu ya dawo daga masallaci.
Faɗa yafarayi mata a kan ina taje bata dawo gida ba har dare yayi.
Inna laari tana tsaye da buta zatayi alwala suka shigo mlm Ahmadu yanata faɗa.
“Baba kayi haƙuri,dama na dawo daga islamiyya ne shine na tsayah gidan Addah Ramma yin hadda,to da tsayi sosai shiyasa bamu gama da wuri ba”
“To naji,koma dai menene ki daina kawai dare a wajen irin haka kinji?”
“Eh baba zan kiyaye”
Hakan da tayi shiya hana inna laari zarginta dajin abinda suke,wanda hakan yabata damar yin shirin ta a cikin dare batareda kowa yasani ba.
Bata ɗebi kayan su dayawa ba,kaya kala bibbiyu ta saka musu a jaka,sai kuma wanda yake jikinsu.
Wajen takai kayan wajen drivenr dayake shiga cikin Jalingo,su kuma zasu fita da daddare sai ya samesu a can gaba.
Can cikin dare da misalin ƙarfe 1:00am Innayi ta buɗe ɗakinta siƙaf ta shiga ɗakin inna Danejo.
Bubbuga kafaɗar ta tayi ta tashi,dan har ta fara bacci ma.
Riketa tayi suka fito daga ɗakin,suna tafiyah a hankali har suka samu damar fita daga cikin gidan.
Duk da Inna Danejo bata gani,amma a tare suka juya suka kalli gidan,ita gidan ubanta da aka haifeta a ciki,yayinda ita kuma yake gidan mijinta,wanda aka kawota tun batasan mai yake mata ciwo ba,gashi yau zata barshi bada an saketa ba,saidan neman mafita,dan tasan idan har tabi zabin zuciyarta taƙi fita kaman yanda tayi alƙawari,toh rayuwar innayi kuma zata shiga cikin hadari wannan dalilinne yasa ta amince zata bita.
Juyawa suka yi tareda barin gidan,dukkansu badan zuciyoyinsu na so ba,saidan fitinar da take gidan wato inna laari.
Tafiya suke Innayi tana haska musu hanya har saida suka fita daga cikin garin.
Kafin asuba tayi sunyi tafiya mai nisa har zuwa inda Sukayi da drivern zai samesu.
Ruwa suka ɗiba a wani rafi dake wajen sukayi sallah,kafin gari yayi haske ma har drivern ya iso wajen,kasancewar dama fitar wuri yakeyi.
Fitowa yayi ya taimakawa inna Danejo ta shiga motar,saida ya tabbatar sun zauna kafin ya ja suka bar cikin garin tareda saita hanyar Jalingo,inda zasu samu motar Abujan su shiga.
A bangaren Mlm Ahmadu kuwa asuba tanayi ya nufi ɗakin Innayi domin ya kwanƙwasa mata tafito tayi sallah,jin yayi bugu har uku bata motsaba yasa yayi zaton ko tana Hutun wata ne,dan haka yayi tafiyarsa masallaci.
Har 10 tayi shuru innayi bata fito ba,inna laari harta haɗa abin karyawa,ga wanke wanke ƙudaje nata bi,kuma so take dama tayi mata turaren yanzu,kafin zuwa dare ya bi jikinta.
Hanyar ɗakinnata ta nufa tana magana.
“Wai nikam innayi wanne irin bacci kikene haka,ai kamata zuwa yanzu kam kin tashi kin fito koh kuma ga………”
Maganar tace ta katse lokacin datayi arba da ɗakin innayi tace ɗaukeni a hankali,dan babu ita babu alamunta a ɗakin,sai wata fara takarda a kan gadon.
Fitt ta fito daga ɗakin tana salallami kaman an jeho ta,turakar mlm Ahmadu ta nufah tana ihu .
“Mlm maza fito innayi ta bata banganta ba,da alama bata kwana a gida ba,babu ita babu alamunta sai wannan takardar,yau ni laari naga takaina”
Duk ihun da inna laari take bayyi magana ba,saima takardar hannunta daya karba ya buɗe.
“Aslm baba kayi haƙuri ka bawa inna ma haƙuri.
Amma bazan iya zama ba saboda wani dalili wanda bazan faɗeshi a yanzu ba sai nan gaba idan har na rayu.
Na tafi nida inna Danejo zan kaita wajen Yar ta addah Bombee,ta hakanne kaɗai zan rage laifin dana aikata”
Ninke takardar yayi tareda nufar ɗakin danejon,wanda itama inna laari tabishi kaman jela.
Kaman yanda ta faɗa a takardar kam Danejo ma bata nan,ya tabbata sun tafi tare kenan.
Sauƙe ajiyar zuciya mlm Ahmadu yayi,yarasa ma mai zaice,banda Inna laari wanda tasaka hannu a ka tana ihu,yagagara cemata komai.
Fita waje yayi ko za’a samu mafita,domin zaman sa cikin gidan babu abinda zai haifar,tunani ne fall a ransa,musamman daya tuna shekaru dasuka wuce a baya,Lokacin da ƴaƴan sa suke ƙanana,yayi rayuwar farincikin da bai taba zaton zayyi ta ba,a yau kuma sai gashi ya rasa komai na farincikinsa. Tabbas yasan hakan jarrabawa ce daga Allah,shiyasa ma yake fatan Allah ya bashi ikon cin ta.
A wajen inna laari kuwa ba kukan Batan ƴata bane yafi damunta,kukan wanne irin tashin hankali zata fuskanta ne a wajen ZILIYYAH,sannan kuma ga Danejo ma ta tafi,idan Bombee tayi nasarar samunsu,tasan idan suka sake gamuwa saita Allah,wai Jaka a ɗaki.
Saboda gudun da Drivern yake kuma ya kware sosai,da rana tsaka suka isa Tasha a cikin jalingo ina zasu hau motar taraba.
Masa innayi a siya musu a wajen da ruwa a cikin kuɗin suka ci.
Kana suka yi sallah tareda samun dan hutu,kafin a gama yin lodi a motar dazasu shigan.
“Inna Danejo kin gaji koh,kiyi hakuri yanzu zamu shiga mota,inshaaallah muna isa abuja sai mu bawa masu mota address ɗin su kaimu,da sannu nasan zata nema miki magani ki warke inna”
Tana jin abinda innayi takecewa,amma batace komai ba,dan itama har ga allah tayi kewar ƴar tata sosai,abin tsorom shine bata san a wanne yanayi zata sameta ba ne.
Suna nan zaune sukaji ana ƙiran sunansu,innayi ce ta taimaka mata ta tashi suka nufo motar,dan tun ɗazu suka biya kuɗin motarsu dama.
Ƙara nausawa sukayi kan hanya,tareda kama niyyar barin nahiyar su ta taraba.
Tafiya ce aka farata kaman ta yada dan shege,sannan abinka da basabunba tuni bacci mai nauyi ya ɗebesu a motar.
Basu suka buɗe idanuwansu ba saida muryar yaron motar ta jiyarci kunnensu.
“Ke ƴan mata,iya maza tashi zamu kai mota wajen ajiya mu kulleta”
Firgit innayi tayi takalli yanda gari yayi duhu,ga babban titi motoci suna ta wucewa sun haska danjar su.
“Mlm ina ne nan kuma,mun iso abujanne”
“Yo wannan kuma na nawa,har fasinja kowa yakama hanyar gabansa,bakusan inda zaku bane kome?”
Saurin tashi tayi ta duba jakar kuɗinsu dake kunkuminta,amma babu ita babu alamarta.
Kallon yaron motar tayi ido a zare tace.
“Mlm ina jakar kuɗina toh,bangata ba ina ta kayanmu ma?”
“Haba Hajiya ni da nake gaba ina zansan inda jakar kuɗinku take,kayanku gashinan na saka muku a gefenku,dan Allah ku tashi zamu rufe mota”
Hawayene ya jirarowa Innayi lokacin data gano cewar wani ya ɗauke musu jakar kuɗinsu,gashi suna wajen da basusan kowa ba,takardar da inna Danejo ta bata tafara lalumawa domin ta nunawa yaron drivern,ita taji wayam babu ta fadi.
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.
Shine abinda bakinta kaɗai yasamu damar furtawa,dan tasan sun shiga tsaka mai wuyah.

“Shugaba Zilliyah ki taimakeni kiyimin rai n roƙeƙi,wlh bansan cewar zata tafiba kinsanni kinfi kowa sanin halina,bazan barta ta tafi ba inda na sani”
“Kiyimin shuru,banza marar amfani,taya kika bari har tasan dashirin mu ta gudu,lokacin da burina yake dabba da cika komai ya watse,idan har itama waccar yarinyar tasan cewar Uwarta bata hannunmu,kina ganin zata zuba ido tayi shuru ne iyeee.
Dolene kisan abunyi,na baki nan da sati guda ki nemo,idan kuma ba haka ba……sainayi miki abinda bantaba yiwa wani yashi muniba.
Koda yake bata lokacina kawai zanyi,idan na barki babu abinda zaki iya akai,dan inaji a jikina sunyi nisa,gashi bakiyi mata turaren ba tun dare dana baki,saboda kinaso ƴar ki ta gudu koh.

Naaa tsinemiki laaarrii bazaki tana ganin daidai ba daga yau.
Nida kaina zanje na nemo su,dakaina zan je inda suke na ɗauko suruka ta,ita din mallakina ce,dukka su ukun nawa ne,nafara aiki akan su to kuwa bazan taba ja da baya ba.”
Tana gama ƙarajin da ihun ta bace bata daga jikin madubin,bayan ta fesawa inna laari wani abu a jikinta.
Ihu inna laari tafara tana roƙon Zilliyah agazi,amma maimakon tajita,saima madubin dayayi fass ya fashe gida dayawa ya tarwatse.
Yana tarwatsewa kuwa inna laari tasaka ƙara tareda bingirewa tafara burburwa a wajen.

Zaune yake a personal gidansa ya rike kofin ruwa a hannunsa,da kuma magani,shibai sha ba shikuma bai ajiye ba.
Tunani biyu ne a cikin ransa,na farko shine na amaryartasa da Hajiya zeenah ta auramasa,duk yadda yaso ya fahimci ita wacece abin ya ci tura.
A yanda yaganta rannan zai ya rantsewa cewar bata haɗa hanya da hausawa ba inba dayaji tayi hausarba,sannnan a yanda ya karanci jikinta macece mai ƙarfi kuma jaruma.
Shikansa bazai yiwa kansa ƙarya ba yasan kyakykyawa ce fiyeda sauran mata daya taba haɗuwa dasu,a duk lokacin da idonsu ya haɗu dana juna sai yaji wani abu ya tsirga masa,ko dan saboda idanuwanta wasu iri ne shiyasa yakejin wani yarr idan ya kallesu.
“Hmmm kuma ma wai hadda yarone da itah,haba mommah meyasa kike min haka,taya zaki auramin matar da take ɗa hakan ma ɗan karami,bazawara ce ko kuma shegene ɗan bansani ba. Shin haka na koma kowa ma sai a auramin ita,”
Cikeda takaici yake maganar shikaɗai batareda mai sauraro ba.
Tunani na biyu kuma Jaleelah,iyah haɗuwa dakuma hada abinda ake so a wajen mace tagari dukka tana dashi,tunanin sa ɗaya shine auren,mata uku taya zai iya fuskantarsu ma tukunna.
Wata zuciyarce tace masa,kawai ka aureta,ai an auramaka mai ɗan ma a wani wajen dabaka san wacece ba ka rayu,sai wannan ne zai gagareka.
Ajiye maganin yayi da ruwan ya tashi ya saka kayansa,baiso komawa gidan yau ba,dan yau ɗinne Lubnah takoma sashenta sabo,wanda yasan shima an kaimasa kayansa can ɗin,ko sha’awar wajen bayason kalla bare kuma zama a cikinsa,idan yaki komawa kuma yasan bai dace ba ace matansa na wani waje daban shima yana wani waje daban.
Lallai Hajiya zeenah tagama tsara taswirar rayuwarsa a hannunta,wannan karon zai gwada ƙwatar ƴancinsa koda kuwa kadanne.
Tafiya kaɗance takaishi gidannansu,direct sashen iyayennasa ya nufah,baisani ba shin abban nasa zai amince ko kuwa ahah,dan karyace ai bai daɗe dayin sabon aure ba.
Su biyune a falon,daga Hajiya zeenah sai shi,da alama zance suke akan wani abun.
Ita kuma Hajiya zeenah da saƙa ta ulu a hannunta tanayi domin samun abinyi.
Bayan ya gaishesu zama yayi yai shuru,shibai tafiba shikuma bai ce komai ba.
Dariyar dattako Alhj Aliyu yayi kafin yace.
“Babban mutum yadai naga kayi shuru,kuma alamu sun nuna akwai abinda yake cikin ranka,mai nene a haka ka faɗa min ko mai nene.
Kobaka so faɗane a gaban mahaifiyar taka kanajin kunya”
“Ahhh nizaiji kunyah,saidai ko nauyi tayi masa kai a baki,idan kunyace kuma to barina baku waje ku tattauna,idan tayi wari ai zanji”
Hajiya zeenah tafaɗa tana dariyah zata bar ɗakin.
Saurin dakatar da itah Jabeer yayi tareda cewa.
“Ahah mommah ki zauna kawai,dama……dama inaso na faɗamuku ne cewar zan ƙara aure,akwai yarinyar danake so to kuma mahaifinta yace na turo ayi babbar magana”
Ɗan taƙaitacce bayanin Jaleelah Jabeer yabawa su Hajiya zeenah.
Jimm sukayi dukkansu kafin Hajiya zeenah tafara magana,wanda dama tunda yafara maganar ta tsaya da abinda take.
“Aure kuma yanzu,habadai aure ina kuma Auren shi……..”
“Kinga kinga Momyn yara,kada ma ki ɗakko wannan zancennaku da kuke ta maimaitawa shekara da shekaru,bazan hanaki yabi umarninki ba,saboda ke kika haifeshi,amma kuma wanann karon bazanyi shuri ki tauye masa haƙƙinsa ba.
Duk tsawon lokaci ke kike aura masa wacce kika ga dama,wannan karon yazo miki da wacce yake so,dan haka bincike yakamata a ayi,idan har gidan mutuncine nizan saka ayi bincike akan hakan.
Godiyah sosai Jabeer yayiwa abbannasu,dan bayyi tsammanin zai amince tashi ɗaya ba.
Duk da cewar Abbannasa ya tari bakin Hajiya zeenah,amma yasan bazatayi shuru iyah hakanan ba.
Dole saita yi wani abun akai,shi hakan bai dameshi ba tunda mai nemo masa auren ya amince.

Bayan Jabeer ya tafi nasiha Alhj Aliyu ya zaunarta yayi mata akan lamarin da take tafiyar da rayuwar ɗanna ta,amma hakan bayyi mata ba.
Tana shiga dakinta tace “chabɗijan aure,yar uban wanne matsiyacin ce,daga yanda yabada labarin ɗiyar talakawa ce,waton sunganshi da alrziƙi da matsayi zasu mallakeshi koh…..hmmm dani kuke zancen.”
Wayarta da ɗauka tana neman Number Hajiya rabi,domin susan abinyi.

Page 🖤21••22🖤

“Me kike faɗa haka Hajiya zeenah bana jinki,aure kuma wanne iri?”
“Hmmm yadda na faɗamikinnan haka naji nima,yanzu haka na saka ayimin binciken yarinyar da iyayenta,abu daya na sani shine ƴar talakawa ce sosai”
“Talakawa kuma,da girmansa kuma ya ɗauko ƴar talakawa,ga waccar wadda kika ɗauko bata fara aikin komai ba,meyasa abu yake nema ya fita a hannunmu ne kai. To shin bakiyi ƙoƙarin hanashi ba kuma?”
“Uhm hakan bazai yiyu ba sam,domin duk abinda nake abbansu baya sakamin hannu,amma wannan karon yatsaya akan idan bai ga wata matsala ba,to zai aurawa Jabeer zabinsa.
Ni inaga mu zuba ido muga shin mai zasuyi kawai,idan an saka bikin kafin JAWAHEER tagama makaranta,to saimu matso da natan,idan kuma sun saka dayawa saimu jira”
“Ai babu wani zancen jira,makarantar banza makarantar wofi,Ki bari muji wanne lokaci suka saka muma sai mu saka daidai dashi.
Batun ita yarinyar kuma,saimu ƙarawa waccar yarinyar kuɗi tayimana dukkan maganinsu kafin ta tafi.
Ya kikaga hakan toh,kinga in ta gama dasu itama ta tafi,shikenan mun huta,makaranta kuwa idan so take,ko ƙasar wajene ma ai sai ya kaita tayi”
“Eh hakan yayi sosai,bari na zuba musu ido su gama shirin,sai ranar auren yaji mai na yanke”

Daga inda yaron drivern yabar su innayi basu motsaba,sai faman aikin neman Jakarta take,amma babu ita babu alamunta,haka ta gaji tabar neman ta fawwalawa Allah.
Alfijir ne yaketo gari ya fara haske,mutane masu rumfa a wajen,musamman ma ƴan abinci sun fara fitowa.
Wajen wata mai abinci innayi taja Danejo suka nufah,domin samun ruwan Sallah.
Daga ganinta musulma ce,amma kuma batayi kama da bahaushiya ba.
“Amm barka da safiyan Madam,dama ruwan sallah muke nema nida innata ko zaki taimaka mana dashi?”
Kallon bakusan mai kuke ba tayi musu,tareda cigaba da hura wutarta.
Maimaita maganar innayi tayi,wannan karon maimaikon tayi shuru,masifa tafarayi da hausarta wacce bata ishi bakinta ba,gwanda ma ta innayin mai surkin fillanci.
“Ke yarinya bani wajenan idan ke bakida aikinyi,ruwan haka yake a banza kaman kogi,kuɗi fah na saka na siyah”
Hannun innayi Danejo taja,alamar tazo su tafi daga wajen.
Hanyar wani layi suka nufa,suna tafiya kaman bazasuyi ba,abin duniya duk ya ishesu.
“Inna Danejo yanzu kenan a in zamu samu Addah Bombee,takardar ma ta faɗi banganta ba,gashi bamusan kowa ba a garinnan. Abu ɗaya na rike a takardar shine JAAN Estate,bayanshi na manta komai a jiki”
Tafiyah suka har aka fara shiga Sallah a masallatai.
Wani masallaci suka kawo sun shiga Sallah.
Ranadar masallacin innayi ta nufah ta ɗebomusu ruwan a cikin butar da tagani a wajen.
Kawomusu tayi sukayi alwalar suka sha sauran.
Zaninta ta shimfiɗamusu sukayi tada sallah. Suna cikinyi mutane suka fara fitowa daga masallacin,kasancewar haske yafara kowa yana kallonsu.
Wani dattijo ne suka fito daga masallacin shida wani matashi suna magana.
Idonsa ne yakai kan su innayi wanda suka sallah a harabar masallacin,tsayawa sukai suna kallonsu har suka gama.
Innayi ce data kuladasu ta taso ta ƙariso wajensu,tsugunnawa tayi har ƙasa ta gaishe da dattijon kafin saurayin.
“Lafiya yarinya na ganku anan,maikuke anan wajen da wannan lokacin,sannna kuma da alama ku baƙine koh”
“Eh baba mu baƙine,munzo neman ƴar uwata ne nida innata,saikuma mukayi rashin sa’a wasu suka ɗauke mana kuɗinmu a mota,shine mukazo nan domin muyi sallah saimu samu inda kuma zamu nufah”
“Innalillahi ana gamuwa da bata gari kam sosai,shin inane ita inda yayarta ki take?”
“Ehh takardar data bamu na address ɗin itama ta bata,abu ɗayah na sani a jikin takardar shine JAAN Estate”
“Wai yarinyar taya zamu gane kawai daga suna gidan,inda akwai address ɗin anguwarne dai da dasauƙi toh”
Jimm Innayi tayi daga inda take tsugunne,tarasa ma yake mata daɗi,inda zasu nufah ma shine babban tashin hankalin ta. Daga cikin tunanin tajiyo muryar dattijon
“Tunda kince baki san kowa ba,sannan kuma babu kuɗi a wajenku ballantana ku koma,gaki ɗiyah mace ita kanta innartaki naga kaman bata gani”
“Ehh baba bata gani sannan kuma bata magana,saidai tanajin abinda ake faɗa”
Jijjiga kai yayi cikin halin tausaya musu.
“Idan bazaki damuba akwai gida gefe da masallacinnan,yanada ƙofah tawaje da kuma ta cikin gidana,daki daya ne dashi sai banɗaki.
Ku shiga keda innartaki ku zauna,zan saka yusufu ya bincikomin inane jaan Estate ɗin sai ya kaiku,tunda shima tuƙin Taxi ɗin yakeyi.
Ku zauna wajen yafi muku yawon da baku san hannun wa zaku faɗa ba. Inyaso sai ki dunga ɗebo mana ruwa kina gyara masallaci dakulada shi kafin lokacin,dama maiyin aikin yarone ya tafi makaranta,sauran yara kuma sun zama na zamani”
Tun kafin ya gama bayanin innayi ta tsugunna tafarayi masa godiya kaman zata kifa,saida ya dakatar da ita tukunna.
Wajen inna Danejo ta nufah ta shaida mata abinda mutumin yace,da farko taji jimm kafin ta ɗaga kanta,amma kana ganin fuskarta kasan bataji daɗin yanda suka ƙare ɗin ba.
Dakansa ya Mlm Tijjanin yaraka su gidan,dama na mahaifiyar sa ne data rasu.
A lokacin innayi tashareshi ta shimfiɗamusu tabarma a ciki wacce ya aiko yaro ya kawomata,ta gama gyaran kenan aka sake turo musu da ɗumame na abin karyawa.

Wasa wasa anyi sati guda da dawowar Lubnah sabon sashe.
A iyah wannan lokacin anyi abubuwa da dama,ciki harda tambayo wa aure da aka yiwa Jabeer,take aka saka rana nan da wata uku. Itama hajiya rabi tana jin haka tace a haɗa dana ƴar ta.
Nan da wata uku kenan za’ayi tare,lokacin da Lubnah taji wanann zancen ƙaramar hauka ce kawai batayiba,musamman ma zancen Jaleelah wanda bata san dashi ba.
A bangaren Bombee kuwa hakan zai wani dameta ba,tayi sati ɗaya kenan a gidan,dan haka lokaci yayi dazata fara nata moving ɗin.
A zaune suka a harabar da yamma suna duba bayanan da khamees ya turo ma Bombee ɗazu.
Wajen a ƙawace yake da kujeru da kuma rumafah irinna zaman shaƙatawa,da alama dai domin zama a huta akayi shi.
Su ukune a wajen,Hilyaan Bombee saikuma Haidar wanda yake cikin Holding bed ɗinsa yana wasa a gefensu.
Shuru kakeji dukkansu babu wanda yayi magana,sun maida hankalin su kan document ɗin dake gabansu.
“Anty maryam banji kinyi zancen sabin amarennaki ba dazasu zo”
Hilyaan ta faɗa cikin sigar zolayah,kallon rabin ido Bombee tayi mata tareda yin ƙaramin murmushi.
“Wai meyasa Hilyaan kike abu kaman baki san komai ba uhm,dama nasan da zuwan Jawaheer koba daɗe da jima,amma kuma itama Waccar ɗin nayi tunaninta tun ranar dana ganshi yana duba Sashen dayake kusada shi.
Na gansa kusan sau uku yana shiga wajen shida wasu ma’aikata yana dubawa,sannan kin manta lokacin da Lubnah take da faɗan bai kwana a gidannan ba?,na tabbata ba a gidan Su Jawaheer ya kwana ba,saboda kallo daya zakayiwa sha’anin kasan cewar ba soyayya a tsakani,Hajiya zeenah da kawartane suke rawarsu suke kiɗansu.
Da farko nayi zaton a gidan su yarinyar ya kwana,danayi bincike jiya kuma na gano gidansu sunada kamala sosai,to ɗayan biyune yake faruwa……”
“Kutt taya kika shirya waɗanann labaran,ɗayan biyun wannene”
“Ko akwai wajen wata daban dayake zuwa idan yana cikin matsala,ko kuma akwai wani waje boyayye dayake zuwa,wanda bayason kowa yasani,a yanda kuma naji labarin a mutuwar matarsa Hafsa an rasashi a gida na wani lokaci kafin ya dawo cikin mawuyacin yanayi.
Tabbas akwai wani abu dayake boyewa wanda babu wanda yasani,harda iyayensa ma”
Tafi Hilyaan tafara yiwa Bombee na alamar jinjina,sanann kuma takara dacewar.
“Gaskiya na jinjina miki,amma inaga wannan binciken da a akan Lubnah da familynta mukayi,ba’a kan Jabeer ba,saboda naga kaman baya cikin target ɗinmu koh?”
“Baya cikin target ɗinmu a zahiri,amma a boye shine babban target ɗinmu.
Kowa dayake cikin wasannan ƙarshen target ɗinsa kan Jabeer yake yin birki.
Hajiya rabi nata shirin shine ƴarta ta aureshi ta haifi ƴaƴa,itama kuma hajiya zeenah shirinta shine ta haɗe companyn hajiyah rabi dana Jabeer saboda JAAN yaƙara power.
Ita kanta Lubnah ba itace ta haɗu da Jabeer ba,iyayenta ne wanda suka haɗa komai,domin itama ta haifi ƴaƴa a gidannan,dasuka ga bazata haihu ba sai Gen Abdu manga yakeson Mallakar companyn yanzu.
Kuma ina mai tabbatar miki kwanan zai fara moving ɗinsa akan hakan. Sannan shikansa gidan da kike ganinsa akwai Akwai abinda yake going a cikinsa.
Zaro ido Hilyaan tayi tareda cewa.
“Ba…..bbban fahimceki ba Anty maryam”
“Meeting ɗin dayaje a wancan satin Gen Abdu manga shima yaje wajen,kinsan meyasa?”
“Ahah bansani ba?”
“Saboda shine nabiyu mai kaso mafi yawa na share companyn,a kowanne lokaci zai iyah ƙarbe shi daga hannun Jabeer”
“To abin da ɗaure kai,saboda taya Zasu bar wani yayi kusa da mai company a yawa share?”
“Ba a mutum ɗaya ya siya share ɗin ba,ya mallakesune da sunayen mutane a ƙallah Gudan goma,kuma shima kansa Juyashi ake yakeyin aikin, babban kifin yana duhu,shiyake juya komai.
Alhj Abdullahi ƙafafa yake yana tunanin shine da babban share na companyn,saidai ba haka bane.
Wannan ne dalilin dayasa matarsa take Nata aikin da daddare batareda kowa ya sani ba a boye,da alama mijinta take tayawa yaƙi.
Tohhh kinga anan wajen shin wanene Target ɗinmu idan muna son ruguza kowanne?”
“Jabeer!!!!”
“Done Plan yayi solving toh”
“Amma taya zamu solving a kansa,shi baida laifin ballantana mu kamashi”
“Akwai hanyoyin saka mutum a cikin tafin hannunka,basai da Laifi ba kokuma Soyayya”
“To taya zak…….”
“Wait and see Hilyaan,lokacin zai faɗamiki koma menene”
Suna shirin tattarewa yamma tayi motar Jabeer tashigo harabar wajen baƙa siɗik da ita ƙirar daraja.
A hankali yake tuƙin irinna ƙasaita har ta kaita wajen parking inda sauran motocin suke.
Buɗewa yayi ya fito tareda nufar hanyar sashensa,maganar Lubnah ya jiyo wacce taji muryasa tafito daga sashenta,shi duk yayi zaton ma bata gidan tunda taji labarin auren dazayyi.
English wear ne a jikinta tasha ado sosai,tundaga nesa take fuɗemasa baki kamar gobar auguda,saidai daga yanda take dariyar zatakasan cewar bahar zuciyarta bane.
Takowa take cikin tafiyar mai son jan hankalin wanda ake yiwa.
“Honey ina kuma zakaje,tun ɗazu fah nake jiranka,kuma saika wuce batareda kaga ya nake ba koh”
Tayi maganar cikin karayar zuciya,dan ita gabaɗaya a tunanin ta sashen Bombee zai shiga daya nufi wajen.
A yanda tayi abun kwata kwata bayyi mata kyauba,shikansa Jabeer sakin baki yayi yana kallonta, “Mata iyayenmu” yafaɗa a ransa.
Kasa rike dariyarta Hilyaan tayi,ganin tafiyar da Lubnah takeyi,aikuwa tunda babu wanda ya ɗauremata baki tasaki dariya.
A tare Jabeer da Lubnah suka juya inda Su Bombee suke zaune,danshi sai yanzu ma yagansu.
Idonsa akan Bombee ya sauƙa,wadda fatarta take sheƙin yamma,ga kayan sun amshi jikinta sosai.
Gajeran kallo ta aika masa na dan mintuna tareda murmushi,kana kuma ta maida kanta kan system .
Kansa ɗaurewa yayi,yarasa shin murmushin dawa take,dashi take data kalleshi kokuma da abinda Lubnah tayi ko ga mai aikinta.
“Kuttt yaushe har kina matsayin ƴar aiki kika samu damar yin dariyah a inda nake,yau saikin faɗamin dawa kike,barganin kina aiki a ƙarƙashinta kuma tare kuka zo,ko uwarta ce bazan ɗau raini daga gareta ba ballantana ke”
Hilyaan ce ta kalli Bombee wacce bata ɗago ba,amma kuma fuskarta ya nuna Ranta tafasa yake,dan ita kanta Hilyaan sai tayi shakkar fuskartata.
Takowa Lubnah tayi zuwa inda suke.
“Kifaɗamin dawa kike a wajennan dahar kika samu damar dariyah,ko wacce kike zaune dominta bata isa ballantana ke”
Yanda Lubnah take maganar ne da izzah yabawa Hilyaan haushi,ɗaure fuska tayi ta tashi zata mayar mata martani(abin sojoji ya motsa).
Tun kafin ta miƙe taji shugabar tata tayi magana.
“Don’t,ke yanzu in kare marar sarka a wuya yayi miki haushi saiki juya ki rama?”
Ɗan murmushi Hilyaan tayi bayan ta watsawa Lubnah kallon baki kaiba.
Hakanne yasake ƙuleta ta hassala zata fara faɗa.
Buga tebur ɗin Bombee tayi tareda miƙewa suna kallon kallo a itah.
“Lubnah kowa kike ya isheki haka,da akayi kason haƙuri kaɗan aka bani,to tun ɗazu zakika zageni kika Ɗebeshi,karki bari ki shiga list ɗina tun lokacin shigarki bayyi ba,hakan bazayyi miki daɗin.
Kije can ga mai riƙe da igiyarki yana jiranki,idan kika tasarmin yaro daga bacci wlh bazakiyi baccin daren yau ba. Idan kina musu try me please”
Yanda take bata saƙon kausashe nan da nan yakai inda takeda muradin yaje.
Jabeer ne yayi gyaran muryah bayan gama jawabin Bombee ɗin.
Tunda suka fara ƴar tsamar yana tsaye ya haɗe hannu yana kallon su,haka kawai yaji yanada buƙatar yasan wacece amaryar da mahaifiyar sa tayi masa,idan yanada buƙatar hakan dole sai ya matsa jikinta yasan ya take.
Beside tunda zai haɗa mata huɗu,dolene ya dunga tsayawa yana ganin mu’amalar dake tsakaninsu. Duk da yasan dana ba kyau zatayi ba koda yace zayyi koƙarin gyarawa.
Ɗan jijjiga kai yayi bayan ya kalli inda yaron yake kwance,babu abinda yake tsaye a ransa kaman zancen yaron,ko ya akayi ta samu yaron tabbas yanaso ya sani dole.
Ba su Bombee ne suka bar inda suka zaune ba har sai wajen magriba tukunna,zuwa lokacin sun gama tsara yanda komai zai tafi..
Misalin wajen ƙarfe tara khamees yaƙirata,ɗauka tayi batace komai,komai ya faɗamata daga ɗaya bangaren ta tashi da sauri ta zauna.
“Me kake cewa? Inna da innayi sun gudu daga gida sunzo nemana? Ohh shittt ya akayi ma ban ƙira Muruje naji ya suke ba…..tsawon wanne lokaci….”
“Sati ɗaya,shin kana ganin suna cikin garinnan kuwa?”
“Ehh to in suna cikin garin yaci ace ai sunzo wajenki koh,tunda kince kin bawa inna Address ɗinki”
“Hmm ba lallai sunada address ɗin ba,in babu damuwa inaso ka ɗan nemo min clue na inda suke, kasan basu taba fitowa ba sai wanann karon,kada a samu matsala”
“Ohk shikenan kada ki damu,inshaaallah baza’a samu matsala ba”
Jefah wayar tayi akan gado tareda zama ta dafe kai na ɗan wasu mintuna,da taga hakan bazai mata ba ta barbaza gashin kanta tareda jan gwauron numfashi.
“Why innayi mainene haka yasakaku baro gida ku biyu meye dalili ,wa yace kuzo nemana,inada dalilina na barin inna a can,meyasa zaki kawo ta nan? …..to inna laari fah taya innayi zata gudu lokaci guda ta………….akwai abinda yake faruwa,ɗayan biyu.
Tabbas innayi taga abinda Inna laari take,ko taji zata kashe Innnata ko kuma zata kasheta itah.
Shiyasa suka gudo nan kenan?”
Ta daɗe ita kaɗai tana maganganu kafin ta tashi tanufi bayi..
Ruwa ta watsa a jikinta saboda zafin da ake,da alamar hadarine yake haɗuwa.
Kayan Patrol tasaka baƙaƙe misalin Wajen sha ɗaya zata fita.
Karo sukayi da Hilyaan tazo dama madarar Haidar,saboda kada ya dameta da kuka.
“Anty maryam lfy ina zakije haka da Darenan ana shirin yin ruwa?”
“Wani wajen zanje,yanayin a haka yafi daɗi ai,bakiji ance Duhun Damina itace sa’ar barawo ba,to hadda irinmuma masu bincike.
Waje tafita tabar Hilyaan a tsaye kaman gunki,dan ita yanzu ta daina bata mamaki ma sai tsoro.
Kai tsaye sashen su Lylah ta nufah,kaman yanda tayi tsammani kuwa akwai hasken fitila a store ɗin wajen.
“Yaune 18 ga wata,baki saba ranar da kika saka ba rannan kenan?”
Daidai kaiwa kunnenta taji ana magana.
“Ga takardun yabani,ka tabbatar ka musanya takardun project ɗinsa da waɗannan,karka taba bari a samu matsala,kaine secatrynsa nasan ya yarda dakai sosai bazai zargi kaine ba.
Na zabi haɗuwa dakaine anan saboda Karka a ganni a wajen na haɗu dakai,ka fahimta dai koh?”
“Ehh na fahimfa Hajiya,amma wannan abun fah hadda mijinki da duk companyn zai shafa,domin zai fita ne daga hannunsu ya koma wani wajen daban”
“Ina ruwana toh,nidai tunda zai biyani maƙudan kuɗaɗe ko gidannan ya karba mana ina ruwan ni.
Ina ganin kuɗaɗen a hannuna zanyi fiyattt na bar ƙasar shikenan”
“Uhm zan fita ni yanzu,idan nayi mintuna goma da tafiya saika bar wajen,saboda kar in case wani ya ganmu”
Tana gama faɗin hakan siƙaf siƙar ta maida lullubin kanta ta fita.
Saida Bombee tajira tabar wajen kafin ta shiga cikin store ɗin inda mutumin yake tsaye.
“Madam akwai wani abune bayan……”
Tun kafin ya gama maganar Bombee ta kifah masa naushi a fuska,faɗuwa yayi yana dafe ta inda takai masa hari.
“Bani takardun Yanzunnan”
Tafaɗa tana miƙa masa hannu.
“Wacece ke?”
“Shine yafimaka amfanin ka sani a yanxu,zaka miƙomin takardun ko saina cewa wannan ya aikata abinda na sakashi”
Takarisa maganar tana nuna masa matarsa da ƴarsa an sata wuƙa a wuyansu suna bacci a gida.
Zaro ido yayi jiki yana karkarwa ya miƙa mata file ɗin.
“Yawwa yaron kirki,yanzu kaje gida ka kwanta da iyalanka sannan kuma kace mata kayi yadda tace,idan kuma tasake saka ka wani aiki ka tabbatar saina sani tukunna.
Kuma daga koda wasa naji kayi wani abun dazai cutar da companynnan saina saka fetur kuna bacci na ƙoneku. Dafatan ka jini sosai”
“Ehh…. Aradu na jiki,in so kike ma zan faɗamiki duk abinda nasani yanzu da kuma wanda yake sakamu,nidai kiyimin lamuni nabar garinma”
“Babu inda zakaje kana nan,batun wanda yake sakaku kuma nasan waye yake shi basai ka bata yawun bakinka ba”
Hanyar side ɗinsu ta nufah,zuwa lokacin har an fara yayyafah mai ƙarfi.
A ledar data zo ta ita ta saka takardun sannan tafara gudu gudu sauri sauri zuwa sashensu.
Kasancewar da ɗan tazara kafin ta isa har ta jiƙe zaraff,daidai shigowarta harabar wajen ta cire baƙar hular da take kanta,jiƙeƙƙen gashin kanta ya kwanta a fuskarta da ƙafaɗarta..
Hannayenta ta ware a cikin ruwan yana bin ko ina a jikinta,komai ta tuna ita kaɗai tafara murmushi idanuwanta suna rufe.
“Hmmm fashi kika iyo mana a cikin gida na ganki da kaya irinna barayi?”
Cikin sanyi yayi maganar a kusan kunnenta,dayaga har ya zo kusada ita batasan yana wajenba,ta tafi duniyar tunani.
Zabura tayi zata matsa sulu ya ɗebe ta,dan bata tsammaci kallon ɗan adam a wanann lokacin ba,hakan ma kuma kusada ita,bataji motsin zuwansa ba saboda ruwan da ake.
Saurin riƙota yayi ya ranƙwafah bata kai ƙasa ba..
Kallon fuskarta yake wadda hasken ƙwoyayen wutar wajen suka haske.
Yayinda itama shiɗin take kallo da nata zararrun idanuwan.
“Sakeni”
Tafaɗa a kausashe,bayyi mata musu ba kuwa ya saketan,jin tana shirin Kiss ta ƙasa yasaka ta jawo rigarsa suka faɗi tare cikin ruwan.
Tashi sukayi tana riƙeda hannunta wanda ya bugu,kallon hannun yake yanda tariƙe gwiwar wajen,kuma shima yaji ƙarar da hannun yayi.
“Am sorry barina gani”
“Kaga me,saikace kana magana da ƙaramar yarinya,ai duk laifin ka ne,menene na zuwa kusada ni kayi magana”
“Dannaxo kusada ke nayi magana sainace kiji tsoro,ke mekike a tsakar dare da baƙaƙen kaya?”
“Ina ruwanka da abinda nake zaman ka nake komai,saika barin in kaji ance an sace wani abu ko yanka wani gobe,saika tuhumeni”
Hannunta takama da ɗayan taja saida yayi ƙara,jijjiga shi tayi tareda miƙewa tsaye.
Duk abinda take Jabeer yana kallonta,yanda tagyara buguwar tashi ɗaya yasa ya share tantamarsa,tabbas ta taba aiki a wani wajen masu horon.
“Baki faɗamin sunanki ba miss sannan kuma idan bazaki damu ba inason mu haɗu akwai tambayoyin dazan miki,sannan haka kike a kowanne lokacin bakya shakkar nuna sassan jikinki a gaban mutane,hmmm ba mamaki naga hadda sakamakon hakan kikeda shi.
Juyowa tayi cikin ƙosawa,takowa tayi har zuwa inda yake.
Gabaɗaya kayan jikinta sun lafe kana ganin komai nata a fili,sakamakon ruwan daya jiƙa ta jarabb,wata tafiyar girgiza take da gangan wacce batayiba ɗazu.
Tsugunnawa tayi a inda yake zaune bai tashi ba.
“Mutum yagani ya ƙyasa ma bai da ikon tabawa horone,ohh dama karkatacciyar bishiyar kuka ka ɗaukeni mai daɗin hawa ga kowa,wai ……..to tun dare bayyimaka ba ka sanja wannan karatun gamedani.
Ni bishiyar giginya ce,sai jarumine zai iya kaiwa ƙarshe bai faɗo ba. Batun ɗana kuma kama dauke kanka daga gareshi,in ma bincike kake ka gano ubansa ba samu zakayi ba,nice nan mai shi ba wani ba”
Bata bari Jabeer yaƙara cewa wani abu ba ta kama hanyar sashenta,har tayi nisa ta juyo ta kalleshi,zuwa yanzu an fara taƙaita ruwan.
“Husbyy in magana kake so dani zanzo gareka,kawai ƙira na zakayi zaka ganni,zan turo maka numberta byeee”

Page 🖤23••24🖤

Ajiyar zuciya yasake bayan tabar wajen.
“Wai mommah anya kuwa ba aljana ta auramin ba,wannan ce har uwa zata zaga uwa duniya ta auro maka ita,ita da take jin haushin halayyar lubna batada tarbiyya amma kuma ta auro wannan,indai nayi tunani daidai wannan tafi ma lubna rashin daɗin zama.
Babu shakka akwai dalilin daya saka mommah ta kawota cikin gidannan,duk yadda zanyi nasan bazata faɗamin ba,wannan kuma batayi kama da wacce zan tambayi abu a wajenta ba..
Tashi yayi taga cikin ruwan inda suka faɗi shida Bombee ya nufi sashensa,dan dama baccine yagagara kamashi shiyasa ya fito.
Gabaɗaya ya rasa gane wanne irin ciwone Lubnah,duk lokacin dayazo mata da buƙata sai tayi nesa dashi,yafaɗamata su je asibiti amma taƙi amincewa.
Duk da ma ba wani gamsar dashi take sosai ba,amma dai yafi babu da halin dayake ciki.
Ga waccar fitinanniyar yarasa dalili sau uku kenan haɗuwarsa da ita,amma kowanne idan sukayi sai yakasa ɗauke kansa daga gareta.
Yana cikin tunanin ne ya iso ɗakinsa,har yasaka kai zai shiga bayi yaji alamar ƙarar massage.
Dubawa yayi yaga number ce da kuma massage a ƙasa.
“Yane sai yanzu kasamu damar barin wajen,abinnan yana bani mamak,mai mata biyu yana shirin sake yin wasu mata biyun,amma kuma abu kaɗan sai yasakashi hawa on.
Uhmm da alama kenan ko matarsa tagaja kokuma shiɗin nada doguwar ƙishirwa,ohhhh karfa kace nafiye surutu,aje ayi wanka da ruwan sanyi naji ance yana taimakawa.
Saida safe Mai shirin zama angon mata huɗu”
Tsuka yaja ya jefarda wayar,ko mai yasa ma ya tsaya karanta message ɗin oho.
Banɗakin ya fada a zuciye,wato ma duk da duhune har tagane yanayin dayake ciki,kodah yake ƴar duniya ce mai buɗaɗɗen ido.
Har yagama wankan yafito ya kwanta yana tunanin abinda ya faru tsakaninsa da Bombee ɗazu.
Lubnah ce a zaune akan dinnng tana zubawa Jabeer abinci,wanda yake ta danne danne a waya.
“Honey ina ta magana baka jini ba,yaka kwana jiyah?”
“Yanda kike so na kwana mana Lubnah,bahaka kike so na dunga kwana ba kaman marar mata”
Wata dariyar jin daɗi tayi,jin ashe yana sonta ya damu da ita,kuma yanzu tagano ba abinda yake haɗa tsakaninsa da Bombee.
A ranta tace”ashe dai maganin ya fara aiki tun kafin ma na kammala aiki dashi”
“Ahhh honey karka ce haka,kasan nima na damu dakai,kawai dai lalurine yasaka,amma kasan yanda nayi kewarka kuwa,kaima ai zakamin shaida akan haka”
Bayan ta gama zuba abincin miƙa masa plate din tayi gabansa,kallon abincin yayi kaman bazai ciba saikuma ya dauki cokalin.
Fiiii yaji an ƙwace cokalin dayake hannunsa,yayi zaton Lubnah ce,saikuma yaga ta gefensa aka karbi cokalin.
Jiyawa yayi suka haɗa ido da Bombee,wacce ta cuke fuska tareda ɗaga masa gira,alamar yane.
Lubnah ce ta tashi daga kan kujerar da take,dan tsabar masifa tana cinta.
“Kututu ke wacece da har zakizo cikin sashena batareda izinina ba,kuma ki karbi cokali daga wajen mijina,mai keki nufi da hakan,kina zargina ne da saka masa wani abun dazaki hanashi ci?”
Dariya Bombee ta shaƙe da itah kana ta ɗora da cewar.
“Kinga niba wannan ce takawoni ba,bance ki fallasa kanki tun banzo kan wannan aikin ba.
Dalilin zuwana shine a ina aka ce yazo sashenki yaci abinci ranar girkina,kodan banyi magana ba sai ayimin abinda aka ga dama?”
Taƙarisa maganar tana ɗaure fuska tareda naɗe hannayenta a kan ƙirjinta,kallon Jabeer ɗin take wanda yariƙe kansa,da kuma Lubnah wacce ta tsaya sheƙeke ta saki baki na mamakin Bombee ɗin.
“Hhhh ranar kwananki wannan kuma ke kika sanshi,Jabeer bai tana yin matar dana raba kwana da ita,sanda nagana dama ina neman sa babu ruwana da kwananki,kaman yanda yanzu anan yazabi yaci abinci kuma baki isa ki hana ba”
“Zakuwa a fara rana kwana daka kaina,kuma wlh in kinga yaci abincinnan ban ɗau mataki ba to ƙaddara na mutu,in inada rai kuwa hakan bazai faru ba.
Mijina tashi mutafi nayi Girki tun ɗazu nake jiranka,yau ranar kwana nane,daga nan har zuwa sati guda masu zuwa,saboda karka manta bakayimin sati guda ba yadda akeyiwa kowacce mace,idan kuma zaka tsallake hukuncin mai sama toh,in ra’ayinka ne bazakaci abinci na ranar girkina to kaje kaci a waje,idan kuwa kazo sashen ta kaci abinci a ranar………..karkuyi ma hasashen hukuncin dazan ɗauka akan hakan”
Ajiye cokalin tayi a kan tebur ɗin tareda nufar hanyar waje.
“Lallai nayarda wuyanki yakai yanka bakisan dawa kike karawa ba”
“Lubnah ce wacce take kashe kishiyoyinta saboda tana tsoronsu,abinda ni kunya ma zai bani da wannan tsoron,innaga dama yanzu ma zan iya kasheki,dan haka bashine farau ba a wajena,nakashen rayukan da bazan taba iyah ƙirgawa ba,kuma na mutane,keda kika kashe guda biyu kinsan bazaki haɗa kanki dani ba,dan ko iyayenki ma a tafin hannun suke”
“Hmmm kinzo kina tadamin jijiyoyin wuya akan kwananki,kinsan ranar kwanannaki ne kika barshi ya kwana a sashensa jiyah?”
Hannun tasaka a bakinta tareda kallon sama,kaman mai wani muhimmin tunani.
“Uhm Lubnah kenan,duk wanda yaga mijinki yasan bai samu nutsuwar iyali ba na kusan sati guda. To ke mai kike kenan haka ta faru.
Ina mai gagaɗinki fah,sama tayiwa yaro nisa saidai ya kalla da ido.
Husby ina jiranka kada abinci yayi sanyi”
Taƙarisa maganar tana huro masa air kiss.
Duk abinda suke har suka gama in dutse yayi magana to Jabeer ma yayi musu.
Komawa Lubnah tayi ta jangwaba akan kujera,lallai Bombee tana bata mamaki,dama akwai irin waɗannan mutanen?.
Tashi Jabeer yayi ya nufi bakin ƙofah,da gudu Lubnah tazo kusada shi tana narai narai da ido.
“Wai naka nufin wajenta zakaje kenan,bazaka ci nawa abincin ba”
“Kinga ni office zan nufah inada abinyi,wannan childish ɗinnku karku sakoni ciki,kinga nayi muku magana tunda kukeyi”
Ajiyar zuciya Lubnah tayi lokacin dataga ya shigo motarsa yabar wajen.
Hilyaan dake tsaye a bakin labulen windowan juyowa tayi inda Bombee take zaune.
“Anty maryam ya tafi bai shigo yaci abincin ba”
“Eh nasan dama bazai shigo ba,amma itama baici nata ba”
“Uhm fitowarsa kam baikai ace yaci abinci ba,abinda yabani mamaki shine,baya cikin agendarki kuma basonshi kike ba meyasa kike shiga lamarinsa saboda Lubnah toh?”
“Saboda shine ma babbar agenda ta kaman yanda na faɗamiki jiyah,ina son kullah alaƙa dashi koma wacce iri ce,ko ƙiyayya ko kuma soyayya,tahakane zan san mai yake faruwa cikin sauƙi.
Ƙarfe huɗu yake dawowa na yamma,kafin sannan ina buƙatar yimasa girki”
“Mee girki,yau kece mai yin girki anty maryam,uhm wanda ke abincin ma bai dameki ba. Da alama su miji an samu ɗageshim”
Harara ta watsa mata,da sauri tabar wajen tana dariyah.

“Iyani inason ki samomin mata mai ɗan shekaru,da kuma maza biyu wanda zasu dunga kula da sashen Jabeer,saboda babu masu aiki a sashen”
“Hajiya basu yakamata su samu masu aiki ba,kowaccensu naga kaman tana da mai aikinta fah”
“Ba irin wannan mai aikin ba,inason wacce zata dunga kulamin da shige ta ficensun tana kawomin labarin.
A ganinki nakai wannan hatsabibiyar yarinyar sai nayi shuru na zuba ido,tunda tazo gidan yau satin guda kenan banji tace komai ba.
Ina ta buƙatar saka wacce zata dunga kawomin mai take ƙullawa itada lubanan”
“To shikenan Hajiya na fahimta,zan bada cikiyar mai aikin,mai ɗan shekaru wacce bazata bada matsala ba koh”
“Ehh inkin samo kimin magana”
Da jaka a hannunta dama taci ado,da alama wani waje zata je.
Ƙarfe uku tanayi Bombee ta shiga kitchen tayi abinci mai rai da lafiyah,a haka babu wanda zai kalleta yace tashiga makarantar koyon abinci,wacce Hajiya Zulaiha tasaka su itada Nu’aimah,banda wanda suke a gida.
Jijjaga kai tayi tareda yin ɗan guntun murmushi,lokacin data tuno maganar Hajiyan.
“Ki koyi iyah abinci da sarrafashi maryam,duk da kina ganin ke sojace amma ai ke macece,watarana hakan zayyi miki amfani,ita zuciyar namiji da kike ganinta,ana iya kamata da abinci. Bakisan shiyasa na kama ta babanku ba,innayi magana ta zauna kawai”
Bayan barinta barrack shiyasa batason yin abinci,saboda duk lokacin datazo yi sai hakan ya tuna mata da Haidar da kuma familynsa,wacce har yanzu takasa yarda cewar ba itace silar shigarsu cikin halin ni ƴasu ba.
Da wuri tagama abincin tazuba a kuloli,wanda tun zuwanta sashen sai yanzune tayi amfani da kitchen ɗinma sosai.
Ɗaukar abincin tayi ta nufi ƙofar dake corridor ɗin gefen ɗakinta,wacce zata kaita sashen Jabeer ɗin.
Ajiye abincin tayi ta buɗe wajen da makulli kana ta shiga.
Kalle kallen sashen takeyi,babu laifi kam ya haɗu matuƙa,kuma yayi daidai ta sashen namiji.
Ƙofofi shidane a falon,huɗu wanda suka haɗa sauran sashenne,ɗaya ta shigowa daga waje,saikuma ɗaya wacce zata shigar da kuma wani fili,inda anan ɗakuna biyu suke,oppsite ɗinsu kuma kitchen ne da dining a wajen.
Gun ta nufah ta ajiye abincin a dinning table.
Fridge ɗin wajen ta buɗe,tayi zaton zataga abubuwa dayawa,ga mamakinta babu komai sai ruwa kawai sunyi sanyi sosai.
Komai na sashen kaman bamai mataba,babu datti kam amma kuma babu gyara ma,da alama inya shigo yayi abinda zayyi ya fita shikenan,dan babu abinda aka taba a wajen.
Fitowa tayi daga sashen ta koma nata.
Hilyaan ce akan machine na gudu tasaka earpiece a kunne.
Saida ta kashe abin kafin tajita.
“Ohh sorry anty maryam ban jiki ba”
“Naga alama ai,shin akwai sauran snack ɗinmu dakikayi mai yawa?”
“Ahah babu sosai sai gobe zanyi,mai zakiyi dashi?”
“Nasamo hanyar kama wancan mutumin a hannuna ne batareda wata wahala ba”
“Kaman ya?”
“Kedai ki bari,gobe akwai aikin dazamuyi”
Yamma lilis Jabeer yashigo gidan,dan yau gabaɗaya basu zauna ba shida Khaleel da kuma managenrsa,kan projest ɗin da companynsa yakeyi.
Har yayi hanyar sashen lubna yadawo ya shiga nasa,yanda kansa yake yi masa caji,yasan ba komai zata ƙara masa ba sai ciwon kai.
A kasalance ya shiga falon kaman koyaushe,har yazo shiga ɗakinsa sai kuma idonsa ya hango masa kulolin dake kan dining ɗin.
Da farko yayi zaton na Lubnah ne,saikuma ya tuna bata kawo masa abinci,saidai yaje sashenta yaci.
Takawa yayi a hankali zuwa wajen kilolin ya buɗe guda ɗayah.
Farar shinkafa ce zara zara da itah,an dafata da dankalin turawa da kuma karas da green beans.
Ƙaramae ya buɗe inda lafiyayyiyar miyar nama take,lutsu lutsu da ita tasha mai sai kamshi take.
Ga kuma jug na lemon kwakwa da abarba.
A yanda yaga abincin bayyi masa kamada na Lubnah ba,sannan yasan Hajiya zeenah ma bazata kawo masa abinci nan ba.
Ɗakinsa ya nufah yayi wanka yasaka kaya marasa nauyi,kafin ya dawo wajen abincin domin ya ɗan taba,dan inyace bayajin yunwa yayi ƙarya,irin zirga zirgar daya wuni yana yi.
Wasa wasa shida zaici kaɗan saida yakusa ganin bayan abincin,dan babu laifi yayi masa daɗi sosai.
Ruwan lemon ya tsiyaya a cikin cup shima ya kora,har lumshe ido yayi,yanda ƙamshin sa yabugeshi a hanci.
A bangaren Lubnah kuwa dama bata wani ajiyemasa abinci ba,dan tasan ba lallai yake cin abinci ba a yanzu,kota kawoma sai yace yaci kafin ya taho,shiyasa tana gama abinda zatayi ta hau danne dannen wayarta.
Washagari yafito zai tafi office yaga an ɗauke kwanukan jiya,an saka wasu sabi daban.
Da sauri yanufi wajen ya buɗe.
Egg rolls ne da kuma bread anyi masa suyar ciki da kwai mai haɗi,saikuma kunun gyaɗa mai zafi.
“Uhm duk yadda akayi waccar fitinanniyar ce ke ajiye abincinnan,kuma nasan dole akwai wani dalili nata,dan batayi kama damai biyayyar gidan aure ba sam.
Koma menene a ranta ni gaba takaini,wanne darene jemage bai gani ba”
Kafaɗasa ya ɗaga alama ruwanta,ba kunya ya zauna yaci abincin ya ƙoshi yauma.
Sashen Lubnah ya nufah bayan yagama domin yaga ya take,yanason shiga sashen Bombee domin sauƙe haƙƙinta koda kaɗanne,amma kuma haka kawai bayason abinda zai haɗasu da ita sosai,dan kwata kwata batayi kama da irin matan dayake so ba sam.
Babu kowa a falon wayam,yau ba abin karyawar kenan,da alama tayi na marmarin ta bari.
Ɗakinta ya shiga tana kwance tasake baki sama tana bacci.
Ƙarisawa inda take yayi ya bubbuga gadonnata,shuru bata tashi ba saida ya buga da karfi tukunna.
Firgit ta tashi ta zauna tareda kaiwa iska duka.
“Wayyyo iyee na’am ya akayi”
Jijjiga kai yayi na takaicin rashin ilimi irinnta na addini.
“Haba Lubnah kin tashi a bacci maimakon kiyi salati kuma?”
“Uhm bansan kai bane shiyasa,amma irin wannan tashina dakayi sassafe,mai yake faruwane”
“Dama na shirya ne zan fita nazo ganinki,kinyi sallar asubu ma kuwa?”
“Uhm nayi mana mai ka gani”
“Vakiyi kama da wacce tayi sallahr bane shiyasa na tambaya,please ki dunga kulada da addini Lubnah”
“To shikenan zan kulada shi,saika dawo ni zan kwanta”
Tana gama faɗin hakan tasaki wata hammar tareda komawa baccinta,dayaga haka shima yabar ɗakin ya tafi aikinsa.

“Amma fah anty maryam ya bani mamaki,serious banyi zaton zaici abinnan ba jiyah,kinga kaɗan ya bari a kwanukan. Kai lalle na jinjinawa hannunki a girki,bari kuma zuwa anjima muga mai yarage a na safen shima”
“Shikuma karki je kiga babu komai mana”
“Wai aikuwa daya bani mamaki fiyeda wannan,yawwa naji muryarsa inaga ya tafi barinaje na ɗauko kwanukan”
Ajiye haidar tayi wanda yake a hannunta akan kujera tayi hanyar ƙofar dazata kaita sashen.
Itadai Bombee tana ta aikin ta a kitchen ɗin,tayi ƙwabin fukawa kala kala,da alama abubuwa zatayi dayawa.
Hilyaan ce ta shigo da kwanukan tana dariyah.
“Lahhh anty maryam wlh zancenki gaskiya,kaɗan yabari fah,ashe kice Mr CEO ɗin yanada cin abinci,saiki dage dayin girki kenan,tunda Allah ya haɗaki da miji mai cin abinci”
Barin kwabin datake tayi tareda kallon Hilyaan wacce takeyimata dariyah.
“Waini dama Hilyaan haka kike da surutune ban taba saniba sai yau,nayi zaton fah ke shuru shuru ce. To idan kingama zubar ɗauke min ɗa daga kujera kimaida shi ƙasa,kinsani sarai yanzu sai ya faɗo daga kai,shima kin koyamasa rigima irin taki”
A haka suna aikin suna wasa da dariyah har suka kusan gamawa,sauran wasu abubuwan kuma da babu da aiki Hilyaan tasiyo.
“Uhmm anty maryam tunda mukazo gidannnan baki taba fitaba,bakyajin wani iri na rashin fitar?”
“Uhm idan inaji ma yazanyi toh,duk sona da fita bazayyiyuba yanzu,saboda hakan akwai haɗari sosai,kinaso na fitane na ruguza mana shirinmu tun kafin lokaci yayi.
Ko kin manta yanda nafita daga garinnan kai.
Kekamma inaga da komawa bakin aikinki kikayi,kinga tahakane zaki samomin bayanin mai hake faruwa a wajen yanzu”
Jimm Hilyaan tayi,da alama batason maganar da Bombee tayi mata
“Kona koma ma bazayyi amfaniba,ko kinmanta cewar wanda sukayi abin basa nan,shikuma gen abdu manga shine babba a barrack ɗin yanxu,kona koma bazan iya dosar office ɗinsa ba ballantana kuma nasan mai yakeyi”
“Ehh to hakane kam,Abba (baban haidar)shikuma naji ance baya ƙasar ma tun lokacin da mutuwar ɗansa da kuma abinda team ɗinsa suka aikata yabaza duniyah,shikenan sai hope ɗinsa na ƙarin girma ya warware.
Hilyaan har yanzu na gagara yarda cewar banice silar wargajewar farin cikin wannann ahali ba,kona ce zan yafewa gen abdu manga da familynsa nayi ƙaryah”
“Kiyi haƙuri da sannu komai zai fito fili,bayama wannan Sameerah wacce kiji dan munafurci wai general ce ita yanzu,kuma amintacciyar Field marshal,kiji fah yanda suka karbi manyan kujeru suna zuba maguɗinsu yanda suka so”
“Kai Hilyaan ki shirya dole ki koma barrack,ina buƙatarki a can kota wacce hanya gaskiya”
“To shikenan tunda kince haka zan koma kodan a fito da zaluncin da akayi mana,amma fah idan komai ya warware bazan sake zama ba”
“Hhhhh ehh naji,saina turaki ƙasarki Cameroo koh?
“Tabɗi ai ƙafata ƙafarki anty maryam”
“Uhm idan kikayi aure ai dole ki rabu dani”
“Wannan kuma daban ai”
Snack sukayi kala kala,su cake,donout,cin cin dadai sauransu.
Saikuma handa made juice suma kala kala.
Bayan sun gama kinkima sukayi zuwa sashen Jabeer ɗin.
Zaman jerawa sukayi a cikin fridge ɗinnasa,komai da wajensa,saida suka cika shi famm tukunna.
Hilyaan ce tafara gyara sashen,ita kuma Bombee ta tafi yin abincin rana.
Kafin zuwa ƙarfe biyu sun gama komai,sun gume sashen da turaren wutah mai daɗin ƙamshi.
Ko ina sai ƙyalli yake da sheƙi kaman bashiba.
“Kai amma fah munyi aiki fah,nadaɗe banyi aiki irin wannan ba,”
Hilyaan ce take wannan zancen tana zaune a ɗaya daga kujerar falon.
Bombee ce tafito daga cikin ɗakinsa ɗauke da babban duvet (bed sheet)a hannunta ja.
Wurgawa Hilyaan tayi wacce take kwance.
“Raguwa kawai,maza karbi wannan kisaka min shi a washing machine ina zuwa”
“Wayyo ni na gaji,wai anyah kuwa bani ake sakawa a babai ba,daga gani kinason bawan allah nan,ji wanann irin uban aiki da muƙe niƙa tun safe,maza badai ƙazantaba da muhalli aradu.
A ina kika samu makullin ɗakinsa ma oho.
“A jikin makullin da aka bani yake,idan kin gama surutun kije kiyimin abinda nasakaki,sannan basai kin dawo ba,kiyiwa haidar wanka kawai ku kwanta tacan,hmmm zaki koma barrack ai zanga yanda zakiyi ,da alama tsokar jikinki tayi laushi tana buƙatar sabon horo”
Karba tayi ta nufi hanyar sashennsu,yayinda ita kuma uwar gayyar ta koma ɗakin cigaba da aikin.
Saida ta tabbatar tayi ma koma gyaran daya kamata kafin ta rufe sashen ta fita,ɗan murmushin gefen baki tayi tareda cilla makullan tana canfkewa.
“Mr Jabeer ka ƙaddara kawai kazo hannun Bombee,hmmm plan yafara aiki”

Shigowa yayi da mota cikin harabar gidan,bayan yayi parking ya daɗe bai sako ƙafah waje ba,da alama magana yake da wani mai muhimmanci.
“Karki damu idan nazo gobe zan taho miki dashi,bayan nam ma idan da wani abun duk ki faɗamin.
Yau da daddare iyayena zasu zo nema min aurenki,wannan ranar jinta nake sosai a raina Baby,da sannu zaki kasance mallakina,nasan zan zama tamkar namijin dayafi kowa sa’a a rayuwarsa.
Bye I love you too baby take care”
Daidai ajiye wayarsa itama Bombee daidai ajiye Recoder datasaka a kunnenta,wacce take ɗakkomasa duk wata waya zadayyi a cikin motar sa.
Wani lokacin idan taji sirrinsa ne dabai shafi aikinta ba bata kunnnawa,wannan ne ta tsaya taji abinda yake faɗa.
Wani zirin haushin Jaleelah ne ya jiyarci zuciyar Bombee a lokaci guda,wanda ita kanta bata san kona menene.
“Jaleelah…..hasashena ya tafi daidai,duk matan dake kewaye da shi kece a ransa,sannan daga gani ko tsohuwar matarsa bayyi mata wannan son ba. Dole kema bincikena yabi takanki kenan,saboda zaki iya batamin budget”
Tafaɗa a hankali tana jijjiga ƙafah akan gadon.

Page 🖤25••26🖤

Saida ya sauƙe wayar daga kunnensa kafin ya kashe komai na motar ya fito waje.
Maida murfin yayi ya rufe tareda nufar sashennasa yana ɗan Jijjiga key ɗin dake hannunsa.
Ɗan sauri yake da alama so yake ya sanja kayansa yabar gidan.
Hannu yasaka ya buɗe ƙofar shiga falon,sai kuma ya tsaya ya kalli wajen tukunna,domin yayi tunanin koba sashennasa bane,saboda ƙamshin ɗaɗɗan turaren daya tunkari hancinsa.
Ƙafarsa yasaka cikin falon,inda sanyin tile ya ratsa tafukan ƙafafunnasa,yayinda hankalin sa kuma da idanuwansa suka bazu cikin falon suna karemasa kallo.
“Anyah kuwa nawa sashen na shigo”
Yafaɗa a ransa.
Komai yayi ƙal ƙal kaman glass,kujerun ma kaman basuba..
Idonsa ne yakai kan kulolin abinci,kaman jiya yauma an ajiyesu a dinning ɗin.
Nufar inda suke zai buɗe yauma yaga menene a ciki..
Da ƙaramar takarda yaci karo a wajen an ninketa.
Buɗewa yayi domin ganin kai ta ƙunsa,rubutune bamai yawa ba
“Ban ajiye Juice akan dinning ba yana cikin fridge.Sannan inkana buƙatar wani abu ka dunga rubutawa kana ajiyemin”
Ajiye takardar yayi ya nufi ɗakinsa domin cire kayan aikinsa,har sannan sauyin dayagani a sashennasa bai bar cikin kansa ba.
Nan ma wani abin mamaki yayi arba dashi,an sanja bedsheet ɗinsa da kuma duvet,kayansa dasuke hanger an ɗebesu,an share an saka room freshner mai ƙamshi.
Jan dogon numfashi yayi tareda sakinsa hade da murmushin dabai san ma yaƙwace masa ba.
Banɗakin yashiga shima a gyare,dama yayi tunanin hakan.
Taƙaitaccen wanka yayi kafin yafito zai saka saffan kaya a jikinsa.
Shima wardrobe ɗin an masa gyara na musamman,wajen kayansa na yadi daban,suit daban,hakama na bacci da kuma na shan iska.
Da sauri yagama shiryawar yafito wajen abincin,dan na jiyama har yanzu ɗanɗanonsa bai barshi ba,ga kuma wani zai sake ɗanɗana.
Bayan yagama buɗe fridge yayi zai ɗauki juice ɗin data faɗa.
Anan kam harazana yayi tareda matsawa baya,wai anya kuwa ba mafarki yake ba?
Abubuwan sunyi wuya a ƙirasu da gaske ne,yanda yaganta batayi kama da matar gidan dazatayi waɗannan abubuwan ba,duk yasan tabbas akwai dalilinta nayin hakan,amma yagagara daina bashi mamaki abin.
Duk girman fridge ɗin an cikashi tamm da sinadaran motsa baki,kaman a super market
Snacks jucicess kala kala,kowanne kala da inda aka shiryasu..
Hannunsa yakai ya ɗauki wani cup da farin abu a ciki,anyi seeling bakin da ledar cup ɗin.
Buɗewa yayi ya zuba abakinsa,daya kafa bai ajiyeba saida ya kusa shanyewa,saboda yanda ƙamshin ayaba da kuma madara ya ziyarce shi ga kuma sanyi.
“Anyah kuwa wannan ba asiri tayimin ba nakejina kaman a wata duniyar daban,abin kaman yawuce ace ƙwaƙwalwa ta ɗauka,irin waɗannan abubuwan ko asiri takemin takeyi babu abinda zai dameni,in mutuwa ce ma tasameka a daɗi ba’a wuyaba.
Ɗakinsa ya sake komawa har sannan kofin yana hannunsa yana kurba,takarda ya ɗauka da biro ya dawo falon.
“Na dawo gida na tarar da abin mamaki wanda na daɗe banga irinsa ba,koda akwai wani dalilinki nayin hakan,amma nidai a zuciyata naji daɗin hakan,in bazaki damuba inason na haɗu dake zamuyi magana”
Yana gama rubutawa ya ajiye a inda ta ajiye nata kana ya fice daga sashen cikeda na nishaɗin tarbar daya gani.
Bai nufi sashen Lubnah ba sai ya shiga motarsa ya bar wajen,dan dama tun safe ta ƙirashi a office cewar bata nan,inda sabo ya saba sai tayi tafiyarta kafin tace masa ta tafi,tun abin yana damunsa har ya daina ma sakashi cikin ransa.

Tun sanda taji wayar da Jabeer yayi a shigowarsa cikin gidan,har sannan bata motsa ba tana zaune,Hilyaan ce tashigo da sauri tareda cewa.
“Anty maryam yadawo ya sake fita fah”
“Eh nasani”
Daga haka batasake cewa komai ba ta nufi sashennasa,shurun data tsinci kanta dayi,da kuma shiga nazari yabata mamaki matuƙa,meyasa to zataji babu daɗi akan hakan.
Ahah ba babu daɗi taji ba,kawai yarinyar ce bata kwanta mata a rai ba sam,dolene tayi ƙwaƙwƙwaran bincike a kanta.
Ga wannan aikin data ƙirƙira nayiwa mutuminnan,badan komai bane saidan tashiga ɗakinsa tasamo bayanai gameda mai yake wakana,amma babu komai daya shafi abinda take so a ɗakin.
Haushine ya ƙulleta ɗazun ganin aikinta ya tashi a banza.
Yanzu batada zabi illah tasake shiga jikinsa sosai,ta hanyarsa ne kawai zata iya yiwa Gen abdu manga burki batareda ta saka mutanen ta a haɗari ba,itama kuma bataje ta aikata ba.
Wajen data ajiye abincin tanufah,kaman yanda tayi tsammani ya ajiye takarda kuwa.
Bayan ta gama karantawa mitstsiketa tayi tana cije baki.
“Ina ruwana dajin daiɗinka,yafimaka dakasan da wata manufa nayi badan kaji daɗiba,wato kaji daɗin abinda nayi a banza ni ban samu abinda nakeso ba koh? Hmm”
Kulolin abincin ta ɗauka tafito,tana murmushi wanda bawanda yasan ma’anarsa sai ita.
Jaleelah ce a zaune akan tabarmar daƙinsu itada Fareeda,suna ta taɗi akan ya aurenta zai kasance,dan yaune mutane zasuzo daga gidan su Jabeer.
“Iyeee nifah ban taba kawowa a rainaba Jaleelah zakiyi aure ba,ballanta kuma nan kusa,shikenan wato zaki tafi ki barni koh?”
Fareeda tafaɗa kaman zatayi kuka.
Kama hannun Fareeda tayi tareda yin guntun murmushi.
“Haba sweetynah inna tafi ai ba munrabu bane,nasan zaki dunga zuwamin koh,alaƙarmu bazata tatsayaba dannayi aure na tafi na barki ba ai”
“Eh naji dai,da alama wannan mutumin yaciri tuta tunda ya saye zuciyarki daga bayyanarsa lokaci guda.
Inna tace tundaga yanzu za’a fara shirye shirye,dan Baba bazaisaka doguwar rana ba sosai”
“Uhm hakana naji an faɗa,nima kaina auren a bazata naji yazomin wai zanyi aure,ko yaya ƙawayenmu zasuji”
“Ahh ya zasuji kuwa,yanda naji mana”

Hira suka cigaba dayi,gabaɗayah mutum bazai gane suna san auren yakasance ko ahah ba.

Tarba mai kyau akayiwa ƴan uwan Jabeer a gidan su Jaleelah,a mutunci da komai aka gama tsaida magana,nan da wata uku masu zuwa Auren Jaleelah da Jabeer,ba’a saka dayawa ba sannan kuma ba’ayita a ƙurraren lokaci ba.
Lokacin da Jabeer yaji wata uku aka saka baiji daɗi ba sosai,don yayi tunanin baifi wata guda ba.
Amma kuma su iyayenta suna buƙatar shirye shirye na aurar da ƴar tasu,sannan koda yace basai sunyi komai ba yasan bazasu yarda ba,shiyasa kawai ya haƙura tareda cewa Allah ya kaimu.

“Hajiya hajiya hajiya…..!!!!!”
Wata mai aikice take runtumawa Hajiya rabi ƙira a zaune,wacce tashigo sashennata da sauri kaman zata kifah.
“Ke Lu’ube mai yasameki haka kaman kinga Aljan”
“Hajiya…..hajiya Jawaheer ce hajiya,ta yanka tsintsiyar hannunta jini yana ta zuba,tana riƙeda wuƙar ta hanamu mu isa inda tak…..”
Tun kafin tagama Hajiya rabi ta mangajeta ta nufi sashen Jawaheer ɗin da gudu,tun kafin ta isa take jiyo jan ajiyar kukan Jawaheer,da alama kuka tayi har ta godewa Allah.
Kaman yanda Lu’ube tafaɗa tana riƙeda wukar a hannunta,jini kuwa yanata zuba a hannun ba tsayawa,abinka da jikin hutu cikeda jinin lafiyayye,yasamu hanya ai ba tsayawa.
Wani jirine yake ɗiban Hajiya rabi saboda zunzurutun tashin hankalin datayi tozali dashi a yanzu.
Cikin rawar jiki take takawa zuwa inda ƴar tata ke tsaye,wanda itama jirin take saboda rashin jini.
“Jawaheer ƴata mai yasa haka,mai yayi zafi,mai kika rasa a duniyar nan ki faɗaminshi dahar kike ƙoƙarin tafiya ki barni akan sa?”
“Jabeer mommy,mommy kinkasa bani Jabeer,mutumin da tunda na buɗi ido na tashi da sonsa,kin kasa bani shi kullum sai kwana kwana kukemin.
Yau kawai saijin labari nayi wai an bashi mata ansaka rana,nikuma ina nan ina dakon soyayyarsa wacce take cin raina kullum.
Tunda bazaku banishi ba gwanda na mutu na huta kawai”
Tana gama faɗin hakan yafaɗi yaraff a ƙasa. Da sauri Hajiya rabi ta kinkimota daga ƙasan tana sharbar kuka kaman ƙaramar yarinya.
Ihu take tana ƙiran driver wanda yashigo ya taimaka mata suka kinkimeta zuwa mota sai asibiti.
Sai bayan Hajiya rabi taga anshiga da ita emargency an tsaida jinin kafin tasamu nutsuwar ƙiran wayar Hajiya zeenah.
Tana ɗagawa tunma kafin tace wani abu tafara zazzaga masifa_
“Kin kyauta Hajiya zeenah,ɗanki zai angwance nan da wata uku,nikuma ƴata zata mutu kafim sannan”
“Innalillahi hajiya rabi mai kike faɗa haka,van fahimceki ba wlh”
Labarin abinda ya faru ta maida mata ta waya,da sauri kuwa tashiryah zata taho asibitin,dan abin babbane sosai.
Hajiya rabi tana nan tana safa da marwa Hajiya zeenah tashigo aaibitin.
Da saurinta kaman an jehota,wajen ta nufah fuskarta itama ɗauke da tashin hankalin
“Yayah jikin yarinyar ta farfaɗo?”
“Ina kuwa ta farfaɗo Hajiya zeenah,har yanzu likitoci basu cemin komai ba,tun sanda nayi miki wayah nake zaune wajennan ban motsaba”
“Ahah aikuwa yakamata ki dan zauna ki samu nutsuwa,inshaaallah kyakykywan labari zamuji,kada ma ki damu kinji.
Ruwa ta dauka a fridge na wajen tabawa Hajiya rabi tasha,sunan zaune babu mai cewe komai wata nurse ta fito.
“Hajiya karki damu ta samu sauƙi sosai,saidai dayake jikinta yayi weak,to tana buƙatar ɗan hutu kafin ta dawo normal”
“Yanzu bacci take kenan babu abinda ya damet”
“Eh babu wata matsala,zaku iya shiga ma,amma kada ku tasheta daga baccin”
A tare suka shiga ɗakin da Jawaheer ke kwance,ita kaɗaice a ɗakin kasancewarta VIP patient.
Kaman yanda nurse ta faɗa bacci take hankali kwance,hakanne kuma yasake kwantar da guntun tashin hankalin ta hajiya rabi ke ciki.
“Da alama ta samu sauƙi,amma menene abinyi na gaba kenan?”
Hajiya rabi tafaɗa tana dafe da hannun Hajiya zeenah.
“Abunyi ɗayane shine mudawo da aurenta zuwa lokaci ɗaya da waccar matsiyaciyar yarinyar kawai,ta hakanne kawai zamu ceceta daga sake cutar da kanta.
Ajiyar zuciya ta sake jin abinda Hajiya zeenah tafaɗa,kuma dama abinda take so taji kenan tun dazu.
“Shikenan hakan yayi kam,yanzu idan tatashi zan sanar da ita,saiki sanarwa Abban shi Jabeer din ya turo kawunnanasa kumadu a saka itama wannan ranar”
“Karki damu da hakan,tamkar ya farune,dama ai babu wanda bai san da zancen ba,kawai a saka ranar dukka lokaci guda,kinga daga nan saimusan yanda zamuyi da ita waccar ɗin”
“To ya zancen waccar yarinyar kuma da kika kawo,bakya duba mai takeyi kina ganin hakan ba matsala”
“Nima nayi tunanin hakan,shiyasa ma na saka iyani tasamo min dattijuwa wacce zata dunga kulamin da shige da ficensu dukka,saboda barinta tayi abinda taga dama batareda sanina ba akwai hatsari sosai.
“Gaskiya kam,yanzu idan ta tashi sai a fara maganar shirye shirye toh”

Daga haka hankalin Hajiya rabi ya kwanta,dandai bazata so ciwon ƴar ta ba,amma jin labarin abinda Jawaheer tayi ga kowa yasa An saka ranar fiyeda yanda take ma tsammani,da alama burinta zai cika na ganin Ikon Jaan family a hannun ƴar ta,zatayi komai kuwa wajen ganin sauran matansa biyu basu haihu ba kafin ƴar ta,dan ita Lubnah bata kawo mata treating kaman Bombee da Jaleelah.

Mutane basu yi tsammani ba sai jin labarin wani baikon sukayi na Jabeer,wato dai nan da wata uku mata biyu zai aura lokaci guda kuma rana ɗaya.
Surutu kuwa babu mai tsayar dashi na wannan labari daya taso.
Ko kaɗan Bombee bataji komai ba dataji labarin,dan dama tayi tunanin hakan daga Jawaheer ko Hajiya rabi,a duk lokacin da labarin baikonsa da Jaleelah ya isa garesu.
“Toh so funny,ashe gidannan zai zama filin nishaɗi kenan?”
Bombee tafaɗa tana ƙaramar dariyah.
“Meyasa kika ce haka anty maryam?”
“Ohh ke baki gani ba,mata uku a waje daya ai zansha kallo,kuma kowaccensu tanaji da nata salon”
“Naji kina zancen mata uku,amma nikuma mata huɗu nake tunanin zasu zauna a nan ɗin koh,beside ai kallo yana ga dramar dazakiyi dasu ,ni wannan zata fi burgeni”
Hilyaan tafaɗa tana kallon wani waje daban,yayin da a wani bangaren kuma tana dariyah ƙasa ƙasa.
“Hmmm karki sakani cikin jerin matansa masu zama suyi kishi dominsa,ni mai tafiyace inna gama abinda zanyi”
“Anya kuwa tafiyar zata yiyu in zuciyar mai tafiyar takafe anan din?”
“Hilyaan!!!”
“Yi haƙuri na daina,barima naje haidar ya tashi,haidar zakasha kallon faɗan mamarka da kishiyoyinta kenan”
Tana daga hanyar corridorn take iyo maganar,wanda yasaka Bombee yin murmushi tana Jijjiga kai.

“Maleekah ina faɗamiki ki bani hanya naje wajen ubanki. Ban cika Sayyada-tateen ba idan har na bari suka kashe min jika,mennene amfanina kenan a gidan.”
“Iyah meyasa kike hakan,tun jiya da daddare nake fama dake,matan fah yana sonsu,kuma shizai zauna dasu,kemai naki a cikin to fisabilillah”
“Mai nawa a ciki,kinci gidanku da mai ruwana a ciki Maleekah.
Mata huɗu russ a tare,ta ina kunkuminsa zai gamsar da mata huɗu yana kuruciyah shiba sadauki ba,duk da kakanku jarabbene zai iya gado amma inashi ina Mata huɗu.
Saboda suna haifeshi saina barsu su tsufarshi da wuri.
Duk wannan ba laifin kowa bane sai zeenatu,munafukar mata,ta maida yaronnan kaman injinnnan mai kamada mutane nacikin Telebijin(robot).
Allazee aiki,inazaka aiki ina ka fito aiki,saisun nakasashi tukunna zasuji daɗi?”
Kanta Maleekah ta kama tana runtse ido,gaba ɗaya kanta ciwo yake na masifar da Sayyada-tateen ta kwana tana balbala mata,ita bata ci zomo ba amma kuma itace da gudu.
“Maleekah yanzu ina magana kikayi kunnen uwar shegu dani koh?”
“Mai zance miki toh Iyah,nayi iya yina,inkinka zakije to kije,amma karki manta idan abba yaji hayaniyah suma yakeyi saboda ciwonsa,kina zuwa kikayi hayaniya zai suma sai an kaishi asibiti”
Zaro ido tayi tareda yin gajeran tunani.
“Asibiti kuma ke ƴar nan,jikinnasa ne ya tashi kaddai”
“Jikinsa bai tashi ba,amma idan kikayi je kikayi hayaniya zai tashi”
“Ahah nikuwa ina zan bar jiki ya tashi ƴar nan,abinda ake neman lafiya tasamu,toh bazajen sashennaku ba,amma ki ƙiramin ita uwar taki,tacan kisaka ayimin kunun tsamiyah ki kawomim.
Ina nan ina jiranki,saura kuma ki maidani goruba ki shanya baki dawo ba”
Taƙarisa maganar tareda zama akan kujerarta tana hamma.
Jijjiga kai Maleekah tayi tana dariya ƙasa ƙasa,dan kuwa kaman tasani bazata dawo ɗin ba,kunun ma aikowa zatayi a kawo mata,bazama ta dawo sashen ba saita manta da zancen auren Jabeer ɗin tukunna.
“Haba fitinnanniyar tsohuwa kai,saida nace abba ya barni na bar kasarnan na tafi karatu yaƙi,babu abinda nake fuskanta a gidannan sai fitinar rigima.
Su ya Abdul sunji daɗinsu basama ƙasar,yah Jabeer ne kaɗai ke shan wahala damu.
Wai meyasa mommah ma take ta auramaka matannan oho,bazata barka ka huta ba.
Barina shiga sashennasa naga mai nene a ciki”
Ƙarisa maganar tayi cikin damuwa tareda yin hanyar dazata kaita sashen Jabeer ɗin.
Tafiyah take tana kalle kalle har ta isa wajen.
Wulgawar mutum tagani tacikin bishiyoyin wajen,saida tasake dubawa taga ashe mata biyune suka nufo hanyar da take,suma da alama sashen zasu shiga.
Tun daga nesa tayi tsammanin dama Matar yayannata ce da mai aikinta,dan su kaɗaine a wajen sai Lubnah,ita kuwa tafi haka girma sosai.
Suna iso wajen Maleekah ta kalli wani wajen,dan bata san mai zatace ba, cikin ƙaramar murya tace.
“Matar yah Jabeer ina kwana”
“Lfy”
Shine abinda Bombee tafaɗa mata a taƙaice kana tayi hanyar shiga ciki.
Binta tayi kallo tace a ranta.
“Daga ganinta kam dama batason mutane”
Hannun taga Hilyaan ta miƙomata tana murmushi,wacce bazata wuce sa’arta ba.
“Barka da Maleekah ykk”
“Uhm barka amma taya kika san sunana?”
“Lahh yaza’ayi ina zaune a gidannan matsayin mai yimata aiki kuma nakasa sanin familyn mijinta”
“Kenan itama tasanmu dukka”
“Babu wanda batasani ba gameda danginku. Karki damu da yanda tayi miki,batada saurin sabo da mutane,amma yanda kika ganta ba haka take ba,tanada kirki sosai antynnaki,kema zaki gane hakan wata rana”
“Uhm nagani kam,kowa yana cewa batada mutunci,amma nikuma sainaji ta burgeni kawai,barina tafi,amma bansan sunanki ba.
Dama lambunsan zai shiga”
“Ni sunana Hilyaan,tunda har kinzo nan kizo mushiga ciki mana ki huta”
“Ahah babu komai”
“Wacce irin ƙanwace bazata shiga gidan yayanta ba,zo muje ciki kada ki damu”
Hannun Maleekah Hilyaan taja suka shiga sashen Bombee.
“Yawwa tunda kingama surutun kinshigo ki ɗauko haidar ya tashi naji kukansa. Ni barina ɗebo kulolin abinci,nasan zuwa yanzu yagama dasu”
Saida tagama maganar ta kulada Maleekah wacce hannunta ke riƙeda na Hilyaan ɗin.
Saurin cire hannunta tayi daga na Hilyaan ta sunkuyar dakai,dan tasan matar yayannata bata tsammaci ganinta a falon ba.
Bata ce komai,duk da tayi mamakin ganin Maleekah ɗin,saima buɗe ƙofar da tayi na sashen Jabeer ɗin tashiga.
“Karki damu ba abinda zatace,zo muje ɗakina”
Binta tayi a baya kaman jela ,saida ta ɗauki haidar a ɗakin Bombee kafin suka nufi nata ɗakin.
Kuka yake lokacin data shiga,amma tana ɗaukarsa yayi shuru yana ƙinkishi.
“Shima idonsa irin na uwarsa”
“Uhm idonsu iri ɗayane”
Daga haka Maleekah bata sake tambaya ba,itama kuma Hilyaan batasake bata ƙarin bayani ba.
Wanka tayi masa a bandaki ta fito,tana shiryashi suna magana haka sama sama da Maleekah,wacce take zaune a bakin gado.
“Naga yau da makaranta ko bakije bane?”
“Uhm banida lecture yau,iyah Madeenah ce takeda,tun ɗazu ta tafi,kefa wacce makaranta kike?”
“Hhhh ni iya diplomer nayi na gama”
“Ayyah kuma kinaso kici gaba?”
“Eh to ina aiki ai bayan nayi karatun,na ajiyene saboda wani dalili”
“Ayyah da alama kinaji da matar yah Jabeer,dan naga tsakaninku kaman ba mai aiki da uwargidanta ba”
“Sai yaya da ƙanwa koh?”
“Ehh mana haka nagani?”
“Kusan hakan muke,dan Allah duk abinda kika gani a sashennan kada ki faɗama kowa mai yake faruwa a wajen,in ban roƙa dayawa ba hadda Hajiya zeenah ma”
“Lahh kada kidamu inshaaallah bazan faɗawa kowa ba,naji daɗin yanda kika sakemin karon farko daga haɗuwa”
“Nima naji daɗin maganarki,let be friend”
“Dama kuwa kaman kinsan banida ita,indai banida lecture zaman gidannan gundurata take,saina rasa mai zanyi,wayama gajiya nake da dannawa. Yanzu nasamu abokiyar hira.
I hope dai bazan takura miki ba koh?”
“Bawani takura,nima nasamu abokiyar hira ai da daɗi sosai”
Bombee ce ta turo ƙofa suna tsaka da hirar .
Suma itan suke kallo.
“Miƙomin ɗana inkin gama shiryashi,duk sanda kuka gama hirar saiku fito ku sameni”

Page 🖤27••28🖤

Bayan sati guda da yin baikon mata guda biyun,abubuwa da dama sun faru,ciki harda shaƙuwar data wanzu tsakanin Hilyaan da Maleekah,ga mamakin su kuwa Bombee batayi musu magana ba.
Kullum indai tana nan zatazo suyi girki su gama hirarsu,wani Lokacin ma suke kaiwa Jabeer nasa,ga gulma dasuke na zubawa Lubnah ido..
Shekaranjiya ta tafi gidansu har yanzu bata dawo ba.
Hilyaan ce ta kalli Bombee wadda take zaune tana aikinnata na gado,wato dube dube a system,kana ganinta kasan zaman waje dayan ya dameta,abinka da bata saba ba sam.
Tun ɗazu tana jin su Maleekah sunata hira,bata saka musu baki ba,saida Hilyaan ta kira sunanta tukunna kafin ta ɗago.
“Anty maryam”
“Na’am”
“Nace yau ma da yah Jabeer za’ayi abincinne”
“Ahah badashi zakuyi ba,ai banice kuma mai cidashi kullum ba,nawa lokacin dana ɗibawa kaina ya ƙare,iya mu kawai zakuyi”
“Amma anty maryam Lubnah fah bata nan kuma kinsan yasaba a gida yake cin abinci bakya ganin……”
“Bana ganin me,daɗin nice mai kulada abincin sa ko yaushe,menene aikin matarsa toh.
Kodan kuyi abincin ku zuba a kuloli,amma kada ku kai ku barshi a wajen”
“Kallon kallo Hilyaan tayi itada Maleekah,basudai ce komai ba”
Kaman wani abu Maleekah ta tuna,dan haka ta gyara zama tareda cewa.
“Niii anty maryam kaman mommah ce tayi sanadiyyar auroki koh?”
“Eh ma kike gani”
Ajiye system din tayi tareda maida hankalin ta ga Maleekah,kaman dama tsawon satin wannan lokacin take jira.
“Kwana huɗu da suka wuce tagane cewa ina zuwa sashennan,shine tacemin akan nasaka mata ido,a duk lokacin da naga wani abu yahaɗaki da yah Jabeer na faɗamata,kafin ta kawo mai aikin dazata kulada shige da ficen matansa.
Mai hakan yake nufi kenan,abin yabani mamaki?”
Ɗan murmushi Bombee tayi kafin tace.
“Kenan kin faɗamata cewar ina bawa yayanki abinci”
“Ahah ban faɗamata ba,kullum halin da Jabeer yake ciki yana bani tausayi,burinmu mu ƴan uwansa Allah yabashi macen dazata kulada rayuwarsa,tunda yatashi a rayuwarsa ba abinda yasani sai aiki kawai,in yadawo gida bai san daɗi ba,saboda matar da Allah ya haɗashi da ita.
Daga baya Allah sai ya bashi matar dazai ji daɗin kasancewa da itah. To ance Allah baya barin wani dan wani,sai ya dauke abarsa.
Yanzu kuma dana ganki anty maryam saina Allah ne yadubeshi yabashi matar data dace dashi,wacce irinta yake buƙata a rayuwarsa,mai kulada shi sannan kuma jajirtacciyah wacce zatayi maganin maƙiyansa.
Kota wacce fuska ni kin burgeni,burinsa shine Allah ya shirya tsakaninku,naji daɗi sosai dana ga kina jawo ra’ayinsa da wanann abincin.
Dari bisa ɗari inkina buƙatar taimakona zanyi miki.
Batun kaiwa mommah kuma wannan labarin bazata taba jinsa ba daga bakina dai kam,intana wani abunma na kawo naƙasu a rayuwarku zanyi iya ƙoƙarina akai.
Dan haka anty maryam ki yarda dani,sannan koda kinada wani dalilinki na Kusantarsa,nidai a matsayina na ƙanwarsa ina mai roƙonki da koda na dan wani lokaci ne ki duba halin dayake ciki,sannan kuma ki tuna cewa yanada buƙatarki a rayuwarsa,koda kuwa bazai fito ya furta miki ba”
Hannayenta ta haɗa waje guda tana maganar tundaga cikin zuciyarta.
Sauƙe ajiyar zuciya Bombee tayi tareda barin falon ta shige ɗakinta.
Tashi Hilyaan tayi daga kan kujerar da take ta nufin inda Maleekah take.
“Taji abinda kikace Maleekah,kuma in mai tabbatar miki bazata taba cutar da ɗan uwanki ba,sannan sai inda ƙarfinta ya ƙare idan taga za’a cutar dashi.
Ita ɗin BAƘAR AYAH CE,amma itama cikin ta farine kaman kowacce Ayah.
Abinda mutane suka kasa fahimta shine,tana tsoron da batason wani ya kusanceta har yagano karyayyiyar zuciyarta,kuma yaci galaba akanta.
Amma ina mai tabbatar miki kaman yanda yah Jabeer ke buƙatarta a rayuwarsa,itama tana buƙatar kafaɗar dazata jingina tayi kuka akai,wanda naga hakan a tattare da mijinnata”
“Naga ta tafine batacemin komai ba,ina fatan dai ba bata mata rai nayi bako?”
“Ko ɗayah,da alama abinda kika ya tuna mata abinda yafaru a bayane,amma kada ki damu”
“Abinda yafaru a baya?,wani abune ya sameta?”
“Uhm abubuwa ma ba guda ɗayaba,in badan tanada jarumar zuciyaba da bazaki ganta haka ba,kedai kawai kizuba ido komai zai zama normal inshaaallah”
Cigaba da ƙarƙafawa Maleekah gwiwa Hilyaan tayi,har ta manta abinda ya faru tacigaba da tayata aikin..
Saida suka gama abincin suka gyara ko ina kafin Hilyaan ta raka Maleekah hanya ta tafi.
A bangare Bombee kuwa tunda tashi ga ɗakinta nata tayi shuru na wasu mintuna,ta zubawa window ido batacewa komai.
Abubuwa dayawa ne suka fara dawo mata cikin kai wanda suka faru baya,haƙiƙa kulawar da Maleekah ta nunawa dan uwannata ta burgeta,kuma ta tuna mata rayuwar datayi da tata ƙanwar,da kuma wadda tayi da haidar da ƴan uwansa,sun zauna da ita tamkar ƴar uwarsu ta jini.
Koda dai da rana ɗaya basu taba nuna mata bambanci dasu ba,sai gashi Lokaci guda ta sanadiyyarta sun rasa ɗansu,yaran sun rasa yayansu.
Mai yasa duk abinda ya kasance nata sai yah bacewa ganinta,mai yasa duk inda ta nufah sai wata masifar tafaru a wajen,inaga dagaske ƴan garinsu sukeyi,ita mayyace ba mutum.
A da bata yarda dasuba,yanzu kam tafara yarda da hakan,gaba ɗaya bata abu irinna sauran mutane,duk yadda taso dayin abu daidai abun ya faskara.
Kafin tazo duniyah iyayenta na zaman mutumci zaman lumana,sai kwatsam tashiga rayuwarsu,da farko koyaushe cikin bakin cikin ganinta tana wahala a hannun yara sukeyi,sai gashi daga baya kuma tazame musu fitina wajen dukan yaran kuma.
Tun tasowarta babu wanda tajawowa Alkhairi sai akasinsa,shikansa Maharbi uzairu saida ya koreta daga rayuwarsa tukunna.
Ubanta yashiga mawuyacin hali hakama innarta,hakan bai ƙareba yanzu gashi innarta ta shigo duniya neman ta rasa hanya,batasan a wanne hali take ciki ba.
Bata komai a yanzu a wajenta sai yaronta,wanda bazata iyah buɗar baki tafaɗi ubansa ba,dan itama har yanzu bata san waye ba tukunna,shin da wanne bakin zaya sanar dashi shi waye in ya girma ya tambayeta,tasan dole gudunta zayyi shima,bayan soyayyarsa da aka narka a cikin ranta,batajin dadai da rana ɗaya zata gaza wajen kareshi da dukkan wani mungun nufi.
Dashi aljanun jikinta suke samun galaba take ajiyemusu makamanta idan suka buƙaceta dayin abu.
Batagama da wannan ba kuma ga wani nashirin shigowa rayuwar tata..
Har cikin ranta tasan abinda take son yi ba daidai bane,wato yaudararsa da soyayyarta,amma kuma ta wata fuskar hakanne kadai damarta na samun ɗaukar fansar kisan Jabeer.
Tayi tunanin abun zai tafi normal,saikuma yanzu zuciyarta ta karye dataji roƙon ƙanwarsa.
Allah kaɗai yasan yanda soyayyar ƴan uwa ke burgeta,shiyasa dataji roƙonta lagonta ya karye.
Dafe zuciyarta tayi tareda saurin ɗauke hawayen dayake ƙoƙarin sauƙa.’
‘Karkiyi kuka Bombee,bake yakamata kiyi kuka,haramunne kuka a gareki har sai kin ƙaddamar da aikinki,zuciyarki dolene takasance a bushe,ta hakanne kawai zaki iyah kare wandanda kikeso’
Ɗaga kai tayi alamar ta yarda da maganar zuciyar tata,duk da ta wata sigar tasan ba iya zuciyar bace,hadda shaɗanu wanda suke burin suga tana ɗaukar mataki.
Barin bakin window tayi ta taka zuwa inda haidar ke kwance yana wuntsila ƙafafu,yaron ya girma yayi wayo sosai,saboda kulawar dayake samu.
Zama tayi a kusada shi tana ƙarewa blue ɗin idonsa kallo,wanda basuda maraba da nata. Dariyah yake mata irin ta yaran da basusan mai duniyar take ciki ba.
Wanda hakanne yasa ita uwar tasa yin dariyar.
“Ka cigaba da dariyarka yarona,ko kowa yaƙika a duniyah momy tana sonka kaji. In anƙi Bombee to anƙi Haidar ɗinta,wanda yakeson Bombee yanason boy ɗinta. Nasan dole zakaji babu daɗi rashin uba,amma ni zan zameka dukka biyun,babu mai ɗagawa dan Bombee yatsa ya kwana da yatsan.
Kayi farincikinka,momy jaruma ce zata kulada komai kaji”
Ita kaɗai take yiwa yaron magana,wanda shi baima san mai take nufi ba,kawai dariyarsa yakeyi.

Rana ta ɗago tafara zafi,anguwar tsit yara sun tafi makaranta safe.
Innayi ce a bakin rijiyah tana jan ruwa tana ƴar waƙa.
Zamansu a wajen yasa har ta saba da aikin datakeyin na kulada masallaci.
Dasafe zata kaɗe tabarmai ta share ta cika butoci dukka.
Inta gama tashiga ta karbo musu ɗunmame a gidan liman,idan suna yin aiki ko wani abun kuma ta taya matan gidan.
Bayan tagama cika butocin tas ta tabbatar ta gama tukunna ta tafi.
Kayansu da ɗebe a katanga tashiga musu dashi cikin ɗakin.
Kamar ko yaushe Danejo na zaune a tabarma ta tsurawa waje guda ido.
“Sannu inna Danejo”
Ɗaga mata kai tayi tareda yimata itama da hannu
“Jiya munyi magana da yusuf yace min yaji wasu na maganar wajen,daya tambaya aka gwada masa anguwar.
Dayake dare yayi shiyasa ya bar maganar,amma idan zai fita aiki zan sake tuna masa”
A karo na biyu nan ma ɗaga mata kai tayi alamar taji abinda tace.
Abincin karyawarsu tashiga ɗaukomusu bayan sun gama magana da inna Danejo.
Gaisar da matan gidan tayi cikin ladabi,su ukune a gidan kowa da gayyyar ƴaƴan ta,basu da wani ƙarfi sosai,amma kuma akwai rufin asiri.
Ta sunkuya zata ɗauki kwanon tuwon taji wata tsuka a samanta..ɗagowa tayi suka haɗa ido ta wata yarinya wacce zatayi ƙanwa da ita sosai.
Kallonta innayi take cikeda mamaki,dan bata san mai tayi mata ba.
“Aikina banza,ni bansan meyasa baba yake yayibo mana ƴan maula ba,haka kawai baka san mutane ba ka kawo su gidanka kana ciyar da ƙatti,nagida dama bai ƙoshi ba,inaga kuma an sake kawo karoro”
Tsawa wata mata tayiwa yarinya wacce take shanya kaya.
“Ke faɗima wannan wane irin sakarcine,sa’arkice kike faɗamata wannan maganganun,kefah dama bakida kunya da tarbiyyah”
Meyasa zata faɗi haka?,aikuwa uwar faɗima dake ƙofar ɗaki itama ta hayayyaƙo.
“Ahah kinga tsayah Innar yusufu,menene kuma na kawo rashin tarbiyya a ciki,a wani gida daban naje na raineta,inadai tare ta tashi da sauran ƴaƴan. Kuma ai gaskiya tafaɗa,kowama yagaji dabawa wasu ƙatti can abinci,kawai dai haƙuri ake dasu ya ciwon ido,tunda mai gidane ya kawosu”
Masifah suka fara abu ƙarami yanason zama babbba.
Fasa ɗaukar kwanon tuwon innayi tayi,ta koma inda tafito.
Saida ta tsayah a hanya tashare hawayen daya fito mata kafin ta shiga gidan.
Wai da gatansu da komai a wajen ubanta,yau sun ƙare a garin wasu ana yimusu gorin tuwo,badan komai ba saidan dalilin mahaifiyar ta. Wai su kenan da yanzu ta ɗan gani,inaga kuma Bombee wacce tabar gida a ƙananan shekaru,ga kuma innarta wacce take ɗauke da munanan lalurai na tsawon shekara da shekaru?
Bata taba jin tsanar inna laari a zuciyarta ba irinna yau.
Muryar yusuf tajiyo a bayan ta yana ƙiranta,tayi nisa da tunani ma bata jishi ba.
“Innayi innayi”
“Na’am hamma yusuf ina kwana”
Bai amsa mata ba sai tambaya da yayi mata.
“Me kike tunani haka inata ƙiranki baki jiba?”
“Uhm babu komai banji bane kawai”
“Ohk ki ɗauko kayanku kiyiwa cikin gida sallama,zamuje wajen mugani,inshaaallah inada tabbacin wajenne”
Murna ce tacikata fal ciki,jin labarin dayazo mata dashi,dan dama burinta tabar wajennan,suma mutanen suka takurawa su huta.
“Mungode mungode maka Allah yasaka da Alkhairi,babu abinda zamuce dakai sai Allah yajiƙan mahaifa yabaka masuyi maka”
“Kibar godiyar nan haka kije ki ɗauko kayanku,karki damu anyine Dan Allah”
Kaman jira take kuwa da sauri ta nufi gidan da aka basun..
Danejo na zaune sai jin gudun innayi tayi,tana shigowa tafara haɗa kayansu waje guda,kaman tasani kuwa tayi musu wanki.
“Inna Danejo Allah ya karbi addu’ar mu,yau zamu bar wajennan,barina baki mayafinki ki saka mu tafi inna”
Cikin murna take maganar,wanda har hakan yasaka Danejo yin murmushi itama..
Kasancewar basuda kaya dayawa,nan da nan ta haɗa kayan tafito dasu waje.
Kaiwa tayi motar yusuf ɗin ta dawo da rawar jiki.
Inna Danejo taraka mota ta zauna kafin ta shiga cikin gidan su yusuf ɗin,ɗunkule hannu tayi tareda jan numfashi,dan Allah yagani batason hulɗa da mutan gidan.
Sallama tayi basu ma jitaba,har yanzu faɗan da aka fara da ita bai ƙarisa mutuwa ba.
Wajen babbar matar gidan ta nufa tareda cewa.
“Innar yusufu mu zamu tafi,hamma yusuf ya samo gidan da addah ta take”
Tun kafin wacce aka faɗawa tayi magana sukaji ance.
“Allah yayi lokaci yayi,allah ya tura ƙeyah abu yayi kyau,ni dama tunda kuka shigo gidannan na ƙyalla ido na ganki hankali na bai kwanta ba,nasan ko yaushe za’a iyamin shigo shigo ba zurfi,amma tunda zaku tafi na saki raina,kuje umma da gaida ashshe”
Matar yusufu ce mai maganar tana tafa hannu,fitowarta kenan daga ƙofarta taji maganar innayin,dan ko bacci bata iyawa sosai,tayi ƙiru da kunne tana jira taji ta inda mijinta zai aureta,saikuma taji zancen tafiyarsu.
Jijjiga kai innar yusufu tayi tareda yiwa innayi fatan Alkhairi.
Rashin basu san tafisu matsuwa tabar musu gidanba.
“Shikenan mu zamu tafi,dan Allah kiyiwa mallam godiya,mungode sosai da taimako”
“Bakomai innayi ki gaida Addar taki kinji,Allah ya tsare”
Da sauri tabar gidan saboda zumuɗin su tafin.
Tana shiga motar kuwa yusuf ya tada motar,dan dama ita yake jira ta fito su tafi.

“Kin tabbatar kuwa yadda yafaɗamiki haka kikeyiwa maganin”
Brr Na’imah ce tayi maganar,tana tsaye a bakin ƙofar ɗakin Lubnah na gidansu,ta jingina da jikin ƙofaj.
“Eh mana mom,nazuba jinin na farko,nanda sati biyuma zan sake zubawa,inayin yadda ya faɗa.
Aina matsu nagama haɗin maganin naga wanne iri aiki zayyi.
Mom yakike ganin tasirinsa toh”
“Maganine mai ƙarfi,koda de da rana ɗayah kada kiyi wasa dashi,sannan kuma inkikayi amfani dashi to fah ki tabbatar bakiyi sati guda ba batareda kinga wanda kikayiwa ba,shima kuma ya ganki,idan ya wuce sati guda baku haɗuba,to fah ƙarfin maganin zai fita daga jikinsa,har sai kinsane ƙunzugu dashi yasake kusantarki tukunna.
Yawwa dafatan kina sane da kashedin daya miki koh?”
“Tabb ina zan manta,ina sane dashi,wow i can’t wait na mallakeshi a hannuna,kice na kwantar da hankali na ma matannsa su xo,ta hakane zan baza mulki a tsakanin matansa yanda nakeso”
“Hakan kam ƴa ta,nima zanso ganin ranar dazaki fito tamkar jaruma a cikin matan,sai abinda yace zasuyi,matuƙar suna san zaman gidansa,yayinsa shi kuma sai abinda kikeso zayyi”
“Kai abin yayi wlh”
Lubnah tafaɗa tana buga hannu akan kujera cikeda jin daɗi.
“Nima zanso ki mallakeshin a yanzu,tunda zulumgum yake son baki wannan maganin nahanashi,saboda amfaninsa baizo ba,sai yanzu tukunna”
“Amfani kuma mom,mai haɗin maganina dakuma wani abun”
Shu’umin murmushi brr Na’imah tayi tareda kallon fuskar ƴa tata,wacce take cikeda mamaki.
“Amfani kai dear,bakince kina son zama manager na accesory a companynba,shikuma abbanki so nake na ɗorashi akan CEO na companyn,ta yanda idan ya sauƙa yayanki zai ɗora..
Da nayi tunanin na bar mijinki akai,tunda idan ya sauƙama jikokina ne zasu hau,saikuma abinda yazo bakya haihuwa Lubnah,nikuma Muradina shine ganin jinina akan kujerara wanann companyn.”
Sakin baki tayi galala kaman yawu zai zubo.
“Taya hakan zatayi yu kenan mom,Jabeer fah shine mai kaso mafi yawa na share company,sannan bayanshi sai baffansa Abdullahi,saikuma saura ƙannansa”
“A tunanin ki kenan yarinyah,akwai wanda sukeda share mai yawa a companyn wanda duk sunan bogine ƙarƙashin ikon mahaifinki,daga lokacin dayazo moving plan ɗinsa yana zai maidasu illegaly kan sunansa,nikuma zanyi amgani da shari’ah wajen bashi dama.
A bangare ɗaya kuma kema sannan zaki amfani da mallakar da kika masa,wajen miƙomin takardun companyn daga wajensa.”
“Mom kina ganin zai bani takardun idan na tambayeshi kuwa”
“Idan har maganin dakike shirin yi ya hau kansa,ko hanjinsa kikace ya jaro ya baki kiyi igiya,tofah bashida zabi illa aikata hakan,inaga kuma takardun company?”
Ke dai ki zuba ido kiyi kallo,duk abinda suke kiyi kaman basayi,dasannu zasu zama abin tausayi a hannuna,one day one time sai wannan babban companyn ya daina amsa sunan Familynsu saidai namu Familyn”
Tashi Lubnah tayi daga kan gadon ta rungume mahaifiyar tasu,wacce take ganin itace maganin matsalarta a faɗin duniya.
“Wow mom Ina ji dake,ni ina nan ina damuwa ashe kingama tsara komai,to Bro AMMAR fah yaushe zai shigo garin,matsalar auren turawa kenan,bazasu barshi yazo ƙasar ba.
Amma mom tunda business ya karanta,bakya ganin idan kikace yazo ya hau kujerar zai dawo,ni wani lokacin har mantawa dashi nake a ahalinmu”
“Uhmmm kuma kin kawo shawara,i think zaifi yimin yadda nakeso fiyeda abbanku”
“Eh mana mom,shi abba mai yasani banda wannan fama sa sojojin.
Nasan bakwa shiri da Bro tun lokacin aurenta a Julie amma yakamata kibar komai ya wuce,kiyimasa wannan albishir ɗin,nasan zai dawo nan da zama mom”
Cikeda shagwaba Lubnah take maganar kaman ƙaramar yarinyah,da alama tana son dawowar ɗan uwannata sosai.
“Shikenan zanyi tunani akai,ki tattara ki koma gidanki,banason kina tahowa gida,nafison komai zai faru a gidan ya faru akan idonki kinajina”
“Naji mom yanzu zan tafi,amma saina biyah shagon Surrry tayimin ƙitso tukunna”
“Kice sai dare kenan ki koma kawai”
“Wata ƙila,inna kwana ma nothing inside,he is not a child zai kulada kansa”
Juya ido brr Na’imah tayi irin ke kika sani ɗinnan,kafin ta dau case ɗinta tabar gidan,dan dama fita zatayi tatsaya yin magana da Lubnah.

Page 🖤29••30🖤

Da dauki akalla daƙiƙu masu yawa tana jujjuyawa,amma kwata kwata bata kulada mutumin dake zaune akan gefe da itaba bisa kan kujerar roba fara,shima kaman ita ƙananan kayane a jikinsa,saidai nasa basu kamashi ba kaman ita.
Tunda tafito idonsa yake kanta ƙyam bai ɗaukeba,lokaci bayan lokaci yana ƙurbar lemon dayake hannunsa,wanda yana daga cikin waɗanda tasaka masa a fridge.
Gabaɗaya yarasa mai yake damunsa,idan yace badan ita yazo wajennan ba,ko kuma bata burgeshi to yayi ƙaryah,abubuwan datakeyi abin yaji takaicine kuma yaji haushi,musamman daya san ta taba yin masha’arta harda sakamako na yaro.
Amma kuma yarasa mai yasa ya gagara jin haushinta kaman yanda yake son yayi.
Ɗan murmushi yayi wanda hakan yasa ya ƙwaru da abinda yake shirin haɗiyewa,ganin tayi ƙoƙarin damewa akan ƙafafunta takasa kaiwa ƙasa,yanayin yanda ta cune fuska tayi haushine kaman an ƙwacewa yaro alewa yasashi yin dariyar.
Dara daran idanuwanta ta watsomasa,da alama bata kulada shi a wajen ba.
“Barka da safiya mrs workout,waike kullum kina cikin motsa jikine,da alama akwai aikin dakikayi wanda ya haɗa da hak?”
“Tambayata kake yanzun ko kuma bawa kanka amsa.
Ina mamakin mutum ya auri mace amma kuma bai san ita wacece ba,abin tausayin gareka kuma nina san waye kai sosai”
“Hmmm kinfi kowa sanin ta wanne irin aure kika shigo gidannan ai,banda haka inaga ko gari ɗaya bazamu taba haɗawa”
“Hhhhh mundaɗe da haɗa gari ai Mr CEO,koda ƙaddarar aure vata haɗamuba dama dole zakaji labarina koda ana gaba idan abin hakan yafaru”
Ɗan tafiyah tunani yayi na ɗan lokaci kafin ya taso daga kujerar dayake ya taho inda take tsaye.
“Wacece ke? Shin dama a garinnan kike,sannan mai kike shirin aikatawa? Shin kinzone domin ki saci zuciyata kicika muradinki?”
Ƙarisawa tayi kusada inda yake har suna jin numfashin juna,idanuwansu na saƙaƙe.
“Tambayoyinka sunsa naji kaman ƙwari na yawo akan fatata,kaman Mr CEO na company guda,kamata yayi ace bani zakayiwa wannan tambayar ba,saidai kawai kayi bincike ka gano gaskiya.
Uhm duk da nina faɗamaka cewar kayi bincike,amma zanso kada kasan koni wacece ko kuma mai nake shirin aikatawa a yanzu.
Komai na rayuwata sirrine Mr CEO,sannan a kowanne mataki dazaka hau na sanin koni wacece bazai maka amfani a yanzu ba saima ƙara maka Wasiwasi fiyeda wanda yake ciki a yanzu,domin kai ɗin kana cikin yanayin da ko marar zuciya a ƙirjinsa sai tausaya maka, kayi sa’a daka saka zuciyar dutsen dake cikin ƙirjina ɗan motsawa har takalli halin dakake ciki da kuma wanda zaka shiga.
Dan haka abinda nakeso kayi min ba a matsayin Wacce baka saniba zanyi maka maganar ba,sai a matsayin matarka wacce har yanzu bakayi mata kallo goma ba da shigowarta gidanka.
Shine ka jure zuciyarka kada kayi binciken koni wacece,sannan in wani abu danake yaci karo a wani waje dazan ganka kada kadamu dasanin mai nakeyi ko kuma yin bincike akai.
Nasan bazaka taba amincewa dani ba ammma…….”
“Na yarda dake”
“Me mai naji kace ka yarda dani?”
Bombee ta faɗa cikin kaɗuwa tana ja da baya,da dai duniya bata taba tunanin jin wannan maganar daga bakin mutumin da ta sani a lokaci ƙalilan.
“Bansan meyasa ba amma zuciyata ta amincewa da cewa bakida niyyar cutarwa a gareni,nima ina mamakin hakan amma haka nake ji.
Bansani ba ko kulawar dakikayi da rayuwata a kwanakinnan ne yasakani jin haka,amma koma menene kada ki daina yimin abinda kika fara,shin zaki iya cigaba hakan,idan zaki cigaba dayimin nikuma bazan taba damuwa da sanin koke wacece ba.
Saidan inason duk ranar dakika ji ra’ayin sanar dani sirrinki a shirye nake da saurarar menene.
Ɗaga masa kai Bombee tayi,saboda bakinta yagagara furta komai,bata taba tunanin haka zata sameshi da sauƙin kai ba,tayi tunanin mutum ne mai kuɗi mai jiji da kai,baidamu da abinda naƙasa dashi suke ba..
Lokacin data fara jan ra’ayinsa da gyara da kuma abinci,tayi zaton sai ta ɗau lokaci tanayi kafin ma yasan tanayi,sai gashi a sati guda har yana faɗamata jin daɗinsa akai,abin ƙarin mamakin ma wai ya yarda da ita.
Anya kuwa da irin wannan zuciyara gen Abdu manga zaisha wahalar ƙarbar kujerar nan,kokai saboda tsawon rayuwarsa bashida masu kulada yaya yake,shiyasa ta narkar da zuciyar sa a ƙurarraren lokaci.
Ɗan murmushi ya sakar mata alamar baiga abin mamaki ba.
“Da alama maganata tasakaki cikin bazata wanda nasan kina buƙatar nazari a kebance,amma kisani kada ki damu,komai dayake faruwa a duniyar nan yanada dalilinsa,in har na yarda da zabin mahaifiyata kuma nayi mata biyayya akai to na yarda dake,saboda nasan bazata kawo abinda zai cutar da rayuwata ba”
Yana gama faɗin hakan yasaka hannunsa a aljihu ya bar wajen.
Binsa tayi da kallo,har yanzu ta gagara fitowa daga mafarkin data shiga ɗaxu.
Gabaɗaya sai taji babu daɗi da abinda take shirin yi,wanda tasan dole sai ya shafeshi,amma kuma in ƙaddara ta nufo ka dole ka fuskanceta inkana so kayi nasara,koda kuwa zaka fuskanci ƙalubale gameda hakan.

“Toh munshigo anguwar da mutumin ya faɗamin anan estate ɗin take.
Ku dan zauna a mota barina tambayi mai shayin can tukunna”
Fita yusuf yayi daga taxi ɗin ya nufi masu shan shayin,yabar su innayi a motar sai zazzare ido take tana ƙarewa anguwar kallo.
Tun shigowarsu bataga mutane ba sai a wajen masu shayin,shima kuma ba wajene haka irinna cikin anguwa ba.
Sunan zaune ya dawo tareda tada motar.
Inda suka kwatanta masa yafi,har ya tsinci kansa a bakin shantamemen Estate ɗin..
Kallon innayi yayi tareda cewa.
“A yanda suke kwantantamin nanne wajen,amma kuma anya kuwa kina ganin nanne?”
Innayi bata amsa masa ba,sai fitowa datayi tana kallon get ɗin dake gabanta.
Shima yusuf biyota yayi ya tsaya wajen yana nazari.
“Hamma yusuf kana ganin zamu sameta anan wajen kuwa,duk da cewa ba abune dabazai iya faruwa ba samun addah Bombee anan wajen ,amma kuma abin da matuƙar ɗaure kai,gidan yayi girma ace tana cikinsa”
Kafin yusuf yabata amsa sukaji maganar wani mutum yafito daga gidan.
“Bayin Allah me kuke anan wajen,in motace ta baci muku kuyi hanzarin gyarawa ku matsa,domin dokace ba’a tsayawa a nan”
“Ba motar muce ta baci ba yallabai,wata muke nema a cikin gidannan mai suna Bombee,kasanta dan Allah?”
Nazari yatafi kafin yace.
“Ahah bansan ta ba,bamma tabajin sunanta ba a cikin gidannan.
Amma bari na duba datar sunayen ƴan gidan nagani,ku jirani ina zuwa.
Juyawa yayi ya koma,ya ɗan daɗe duk suna tsaye kafin ya dawo.
“Baiwar allah munduba gabaɗaya amma bamuga mai sunannan ba a ciki. Kiyi haƙuri kutafi ”
“Bawan Allah kasake dubawa dai,indai nanne JAAN Estate to na tabbatar tana ciki,dan bazata bada address ɗin karya ba”
“Wai me kike sone baiwar Allah,dui yadda nake binki saikin ƙureni tukunna,na faɗamiki babu wata mai irin wannan sunan anan,Kaff cikin ƴan aiki na duba bangani ba.
Haka kawai yanzu haka ƙarya kuke danku shigane”
“Kinga kiyi haƙuri innayi,inaga tunda yafaɗa ba’anan take ba wataƙila”
Har sun fara tafiyah tasake juyowa,shikamma securityn har ya fara tafiyah.
“Ahh yallabai naji kace sunayen ma’aikata ka duba koh?”
Tsayawa yayi bai juyoba,sai itace ta je inda yake ta gabansa.
“Yallabai addahta ba aiki taxoyiba,ta auri ɗan gidanne wata ɗaya daya wuce”
“Uhm daga Gembu kuke garin Hajiya maryam?”
“Ehh eh daga can muke,ni ƙanwarta ce kuma hakane sunanta na gaskiya maryam”
Cikeda zumuɗi innayi tafara bashi bayani wani nabin wani.
“Uhm duk da haka bazan barku kushiga ba,bari naɗau hotunanku na tura mata,idan tace tasanku saina barku ku shiga”
“To shikenan muna jiranka dan Allah”

A kwance take tayi biris tanajin Hilyaan tanayi mata magana,amma sai tayi kamar bacci takeyi,saboda a yanda take batajin son magana tunda ta tashi da safen.
Gaba ɗaya yanda zata tafiyar da rayuwar tata ne a ranta,jiyq bata kaiwa Jabeer abinci ba,tasani sarai yazo yaga babu abincin,haka kawai tunanin ya zaiji yasakata cikin wani yanayi na musamman.
Komai yasama take saka wannnan bawan Allah a ranta oho,ita ji take anya ma kuwa ita ce,kaman wanda aka sanja ta,tsoronta ɗaya kada zamanta cikin gidannan yasa tafara mantawa da ɗaukar fansar dake ranta.
Inaaa hakan bazai yiyuba bata fatan tabar mutuwar abokinnata ta tafi a banza.
“Anty maryam inata magana nasan kina jina ba bacci kike ba,daga motsa jiki yanzu sai bacci,ko zaman gidanne dukka yamaidaki haka”
Cikin kasala ta buɗe idonta a hankali tareda ɗorasu akan Hilyaan.
“Wai nikam Hilyaan yaushe muka fara wasa ne dake,duk zaman waje ɗayanne yakawo haka,tabbas na sanja kam tunda har ake ganin fuskar tsokanata,ke barin gidannan zamuyi,bazan zauna zuciyata ta sanja ra’ayi ba,dolene na ɗau fansa”
“Kiyi haƙuri anty maryam amma wanene yahanaki ɗaukar fansa?”
“Wani yanayi nakeji yana shiga raina wanda yake son fitarda Muradi na daukar fansa a raina,me kikega zanyi yanzu?”
“Uhmm mai yafaru haka,ko……..ko kinfara developing feeling ba Jabeer kai,shiyasa na haidar ke ƙoƙarin fita daga ranki,na tabbatar haidar ma zaiso hakan,ki bar ɗaukar fansar nan ki tafiyar da rayuwarki yanda kowacce mace takeyi”
Wani saurin tashi Bombee tayi daga kan kujera kaman zata haɗiye Hilyaan da Idon takaici.
“Me kike cewa Hilyaan? Nabar komai ya wuce sun kashe banza kenan,inaaa bazai taba yiyuwa ba,koda abinda kike faɗa gaskene bazan taba bari abinnan yatafi a banza ba”
Tana maganar tana nuna Hilyaan da yatsa,kaman itace ta kashe mata aboki.
Sai bayan tayi ya isheta kafin ta kulada faɗan ta takeyi marar dalili.
Ruwa ta tsiyanya mata a kofi ta bata,bayan ta kulada ta sarara tayin faɗan.
Ƙarbar ruwan tayi ta shanye tareda runtse ido,da alama kanta ciwo yake sosai.
Hannu tasa ta rufe kunnenta na wani lokaci kafin tayi collapse akan kujerar tana maida numfashi.
“Ɗazu kince akwai abinda kike son faɗamin,menene shi?”
“Uhm dama security ne suka ce wasu sunzo neman Bombee a bakin ƙofah,budurwa da kuma Makahuwa kurmiya,to nayi zaton ko su innayi ne shiyasa nazo faɗa miki.
Zabura Bombee tayi ta miƙe kaman ba itace ke magana a kasalance ba,zaro ido tayi tareda cewa.
“Kuma shine baki faɗamin tunda wuri ba,maza kicemasa ya shigo dasu siɗe dina yanzunnan”
“Okay to bari na faɗamasa”,karbar tablet ɗin hannnun Hilyaan tayi tasake ganin hotunansu,suiɗinne ba gizo take gani .
Ajiye tayi akan kujera tareda nufar waje inda motarta take,tun daga bakin ƙofah ta buɗeta taja sai bakin get ɗin.

Securty na jiran yaji ƙira daga wajen Bombee sai ganinta yayi da kanta,buɗe mata get ɗin yayi tafito inda su innayi ke tsaye.
Tun kafin ta buɗe motar ta fito ta ganeta,saidai wanda yake tsaye a gefenta be bata sanshi ba.
Kasancewar tajuya bayanta bataga isowar Bombee ba,saida yusuf ya fadamata tukunna.
“Am innayi inaga kaman yayar taki ce ta ƙariso”
Da sauri tajuyo tana karewa Bombee kallo,kaman wanda ta shekara bata haɗu da itaba,gaba daya mantawa tayi da basa shiri da yayartata,cikeda zumuɗi ta rungumeta kaman haɗe jikinsu waje daya.
Duk abin yayi mata banbarakwai amma bazata iya cewa baya ji daɗi ba,rabonda tayiwa kanwar tata haka tun tana ƴar ƙaramar yarinya,ita kaɗai tasan son datayiwa mata,sannan kuma tasan zafin abinda tayi mata na yaudara.
Saidai yanzu ganin yanda taketa garuruwa domin neman ta yasa tafara mantawa da abinda yafaru.
Kaman bazatayi magana ba ta furta.
“Innayi lafiyah na ganku anan,mai yafaru kuka baro gida,bayan kinsan hatsarin hakan”
Maimakon tabata amsa saita fashe da kuka,wanda ta daɗe tana tarashi.
“Kiyi haƙuri Addah kiyafemin abinda nayi miki ko……”
“Kinga nifah ba wannan na tambayeki ba,yanzu dai ina inna naji ance da ita kuka taho?”
“Ehh tana cikin motar yusuf,yawwa gashi ma ku gaisa,a gidansu muka zauna shikuma yana nema mana inda kike”
Kallonsa Bombee tasakeyi jin abinda yayiwa ahalinnata..
“To yanzu dai ku shigo ciki tukunna,ke shiga motata inyaso shi saiya biyomu ciki”
Hakan akayi yusuf yabi Bombee a baya har bakin side ɗinnasu.
Itada kanta tariƙe inna Danejo suka shiga ciki..
Sai bayan sunsha ruwa an maida labari kafin yusuf yatafi,bayan Bombee tayi masa godiya sosai,tareda cewar zataje har gida ta gaida Malm tijjani.
“Inna ya bakyacin abincin,ko kin ƙoshi kai?”
Tayi maganar cikeda tausayawa dakuma kulawa.
Ɗaga mata kai tayi bayan takama hannun Bombee ɗin ta rike,duk da bata gani ballanta na maida magana,amma yanayinta ya nuna yanda take son ƴar tata sosai.
Kama hannunta tayi suka tashi.
“To inna barina kaiki ɗakina ki huta kiyi wanka”
Za tayi tatsaya ta daina motsi jin maganar da Bombee tayi,a fuskarta ya nuna bataso maganar ba sam.
Alamu sun nuna bazata shiga ɗakin Bombee ba,duk da yanayin daya shiga amma dattako na fulaninnan yana nan babu inda yaje.
“Oh nagane,to muje can Sashen inda ɗakin Hilyaan yake,karki damu akwai wasu ɗakunan ai”
Duk abinda suke su Hilyaan da innayi suna kallonsu har suka ƙule.
Shuru an daɗe Bombee bata dawo ba,ganin suma rashin maganar ya ishesu yasa Hilyaan ta tashi tafara tattara kwanukan wajen zata wanke.
Tashi innayi tayi tafara tayata,duk da a cikinsu babu wanda yayi wani magana.
Sun gama kenan sukaga Bombee ta dawo tana riƙeda kai.
Zama tayi akan kujera bata ce komai ba.
Wajenta suka matso suna karantar yanayinta,sai bayan wani lokaci ta ɗago ta kalli innayin da kuma Hilyaan.
“Hilyaan yazanyi da wannan rayuwar ne? Nakasa jin tausayin inna a raina,nakasa jin soyayyarta a raina,nasan ina son ta amma banajin hakan,idan kuma na tursasa saina ji kaman akwai wani abu a bayan kaina dayake jana na daina.
Idan naƙi saurararsa kuma saina……..sai kaina yafara matsanancin ciwo,shigowar inna yanzu haka cikin gidannan,ji nake tamkar nikuma an jefani cikin ruwan zafi”
Tana maganar ne tana ciccijewa,babu wanda zai kalleta batareda yasan tana cikin mugun yanayi ba.
“shin daga ni har innata in zamuje da wanann tarin alhakin,naji kunya na muzanta kasancewata ƴa ga mushirika,bazan iyah sake buɗe baki na furta miki kiyi haƙuri ba Addah Bombee,saboda nasan ban cancanta kiyin min afuwa ba.
Ni yanzu zan tafi tunda na huta,dama na faɗawa inna idan nakawo ta zan tafi,tahakane kawai idan natafi zan samu sauƙi daga zunuban dana ɗauka”
Tana kuka take bayanin,kana ganinta zakasan nadama ce ƙarara a ranta.
Tashi zata tafi,har takai bakin ƙofah tajiyo muryar Bombee.
“A tunaninki dan kin shiga duniya shikenan sai hankalina ya kwanta na yafemiki,kinsan wanne irin nema nasaka ayimuku danaji labarin kuna garinnan,sannan kowacce rana saina saka an je andubo ya kuke?,kar shashancinki yasa ƙi ƙaramin abinda yafi wanda nake ciki,na daɗe da sanin kema kina cikin abin wasansu,koba ku taho ba dama inada niyyar turawa a kawoku,saidai bata yadda kuka taho zan sa a kawoku ba.
Inkin gama tsayuwar ki shiga ɗaki inna tayi bacci,na ajiyemiki kaya a kan gado,kiyi wanka kisaka na jikinki a shara.
Kafin nan da zuwa yamma zansan abinyi”
Sunkuyar dakai tayi jin maganar yayar tata,kenan har yanzu ta damu da ita kaman da,kawai halin da innarta tasakata ne yasata zama mai kaushin zuciya.
Hanyar inda taga Bombee ta nufah ɗazu tayi domin yin yadda tace ɗin.
“Anty Maryam lfy naga kina riƙe kai,zuwa kusada inna ne yajawo miki hakan?”
“Uhm shine,yanzu ykk ganin za’ayi,kuma banason na kaisu wani wajen daban,saboda gabaɗaya yanzu garinnan ban yarda dashi ba sam”
“Inaga mu ƙira khamees a san abinyi,to mai zai hana mu kama wani gidan inda zasu zauna,nima kinga saina zauna dasu,tunda Kince zan koma barrak na gano mai yake wakana”
“Ahah karki damu ,babu inda kowa zaije anan zaku zauna dukka”
“Hakan ba abune mai yiyuwa ba,ki kulada yanayin dakike ciki mana,idan kika cigaba da tursasawa kanki bakya ganin zasu iya cutar da haidar ko kuma Inna?”
“Sannan ki tsayah kiyi magana da Innayi kiji mai nene dalilinta ma na gudowar,inhar wani abu ake shirin yimusu,bakya ganin na jikinki zasu faɗamusu inda suke?”
“Eh hakan mai yasa banyi tunani nnan ba,shikenan zan faɗawa khamees yasamomin gida a wanda zaku zauna,zaki dunga shiga wajen aiki kina dawowa,innayi zata kulada inna nasan,to amma kuma inason ƙara wani plan ɗin.
Ina buƙatar wanda zai dunga ganemin abinda yake faruwa a gidan Gen abdu manga,har yanzu jikina ya daina bani shi kaɗai yakeyin komai,sannan duk neman danayi banga wani a waje wanda yake taimaka masa ba.
Ɗaurin gindin dayake dashi a shari’ah yasa na fara zargin akwai hannun matarsa akan komai,dan haka in buƙatar mai kawomin bayanan cikin gidansa.”
Ɗariya Hilyaan tayi tareda cewa
“Karki damu da wannan anty maryam,wacce ta dace da wannan aikin ta dawo,yau basai gobe ba zan shaida mata”
“Really ta dawo,ya ta samo wani bayanai gameda ahalinku kuwa?”
“Ahah tace wai wajen gidanmu ma a ƙone yake,da alama bayan munyi gudun ceton rai sun kashe iyayemu sun ƙone gidanmu”
“Am sorry Hilyaan”
“Babu komai anty maryam,nagode Allah dana haɗu dake,ba a iya shugabata nake kallon ki ba,harda yaya kuma ƴar uwa,Hakan kaman matakine na hawa wata rayuwar,na yarda da hakan”
“Shikenan ba komai,amma fah kinaga zata iyah,karfa mu sakata cikin hatsari”
“INAYAH(identical twin sister ta Hilyaan,su kaɗai suka tsira daga harin da aka kaimusu suda iyayensu a Chadi,a garin gudu har suka samu kansu a nigeria Lokacin suna ƴan shekara Sha uku
Inayah tana son wana mutum,sanja kama daga kuka zuwa dariyah,mutumiyar kirki zuwa ta banza.
Yayinda Hilyaan kuma take son zama jami’ar tsaro.
Da tafiya tayi nisa har aka kama inayah a wani Baɗɗa kama da tayi a gidan wani minister,Bombee ce ta taimakawa Hilyaan suka fitar da itah,dagananne ta fara shiryuwa har take abu irinna sauran mutane.
Banda wannan halayya tasu komai nasu iri ɗayane itada ƴar uwarta.),dama a hatsari take,yanzune ta ɗan fita,thanks to you ta shiryu da tadawo hanya”
Tam shikenan bari khamees yazo da yamma zamu tsara komai dashi.
“Nikuma anty maryam wanne aiki zanyimiki”
Maleekah tafaɗa tana ɗaga hannun daga bakin ƙofah,gaba ɗaya basu san tana wajen ba sai yanzu.
Ta tare suka kalli juna,wato taji abinda suke faɗa kenan.

Page 🖤31••32🖤

“Shigo Maleekah ki zauna,tunda kinji abinda muka faɗa banida zabi illah na sakaki cikin plan ɗinmu.
Saidai idan kika kuskura nasamu wani naƙasu a ciki,please don’t imagine mai zai biyo baya”
“Karki damu anty maryam,matuƙar abinda zakiyi bazai cutar da ahalina ba zan baki haɗin kai”
“Bazai cutar da ahalinki ba saima taimakonsu,domin yayanki na daf da faɗawa siradin plan ɗin wasu.
Badan ceton yayanki nake wannan aikinba,saidai kuma yin aikina zai taimaki yayanki”
“Dan Allah menene aikin,suwaye suke ƙoƙarin cutar dashi,dan allah Anty maryam kada ki barsu su cutar dashi,a shirye nake dana taimaka sosai”
“Ohk tunda kin yarda zaki taimaka abu ɗaya nake so kiyimin,idan ina buƙatar taimakonsa inason shiga rayuwarsa sosai,inaso kiyi iya ƙoƙarinki kada Mahaifiyar ku ta gano mai yake faruwa,inada dama ma ki dunga bata fake information akai.
Inkinyi hakan shikenan aikinki”
“Iya wannan kawai,dan Allah to shin zan iya sanin mai yake wakana”
“Abunda zan iya sanar dake a ciki shine,Mahaifin Matar yayanki wato Lubnah,yana ƙoƙarin lallai sai ya ƙarbi kujerar CEO na company JAAN daga ahalinku,ba iya shikaɗai ba harda ƙanin mahaifinku da matarsa Lylah,koƙarin jefah ɗan uwanki Prison suke akan wani Gurbataccen file,rannan nayi nasarar karba file din na wargazashi.
Suna aikine da Gen abdu manga,a tunanin su yana taimaka musune su karbi kujera,saidai basu san yana amfani dasu bane shi ya karbi share dake wajen Alhaji Abdullahi,wannan share ita kaɗaice damarsa ta ƙarshe dazata bashi lasisin ƙarbar Companyn”
Lokacin da Maleekah taji wannan bayanin jikinta rawa yafarayi kar kar.
Faɗawa jikin Bombee tayi ta kankameta.
“Innalillahi ,nake rokon ki taimaki yayana ashe kin daɗe dafara taimakonsa,tabbas ke Alkhairi ce a rayuwarsa,maƙiya sunyi masa hawa,a kowanne lokaci ƙaruwa sukeyi,sai gashi lokaci guda allah ya kawoki Anty maryam nagode nagode miki,abba zayyi farinciki idan yasan abinda kikayi,mafarkinsa ne Yah Jabeer ya zauna akan wannan kujera,bansan yazaiji ba idan yagane cin amanar da Baban Hanif yayi masa”
“Baisaniba amma inkin faɗamasa a surutunki zai sani,kuma saunawa zan faɗamiki cewar ba dan yayanki na taimakeshi ba saidan kaina”
Ƙarisa maganar tayi tareda ture Maleekah a jikinta tana haɗe rai.
“Nidai kodan wa kikayi bai dameni ba,amma nasan idan kika matsa kusada rayuwar ya Jabeer zakiga abubuwa dayawa wanda mu bamu ganiba a gameda shi,shi mutumne abin a tausayawa masa”
“Uhm to naji zan duba nagani,yanzu dai ki tafi aikinki shine ki saka mana ido akan Hajiya zeenah da kuma Lylah da ƙanin babanki”
“Amma mai yakawo mommah a cikin lamarin kuma?”
“Saboda itama bata tsiraba,Hajiya rabi mahaifiyar Jawaheer so take tayi amfani da ita irinna ahalin Lubnah,zatayi shuru taji ƴarta ta haihu,idan wata a cikin matansa tarigata haihuwa,ko kuma bata haihuba to ki sani zata bi wata hanyarne da karbar companyn tabawa babban ɗanta itama,musamman da companyn su na shirin komawa ƙarƙashin JAAN bayan aurensu da Jawaheer”
“Tabb badaƙala,ashe abubuwane ke faruwa boye da mungun yawa kenan,karki damu anty Maryam,zanyi koƙarin kawomiki rahoto yanda ya kamata,sannan inda hali zanyi ƙoƙarin kawomiki Takardun share na Abban hanif,inaga in muka samesu zamu iyah tsada gudun plan ɗinsu”
“Deal kinshiga Cikin member,akwai meeting da zanyi a guest palour na,4:00 pm naganku a wajen”
Dariyah Maleekah tayi tareda rungume Hilyaan
“Ƙawas finally zanyi wani abun dazai taimaki Yah Jabeer,da banida power yin hakan,amma yanzu na samu”

A tsaye take a gaban dining tana goge kan table ɗin bayan ta ajiye abincin.
Taji ƙarar buɗewar ƙofar,amma bata dagoba,duk da cewar tayi mamakin dawowarsa da wurin.
Idonsa kam ya haɗe da nata lokacin daya shigo,jiya bata kawo masa abinci ba amma yau ta kawomasa,da alama kenan ta yarda da neman taimakon daya nema a wajenta?,na idan ya nemi taimako a wajenta ta taimaka masa,shikuma ya amince bazai bincike ba ballantana yasan wacece itah.
Rigace fara a cikinta armless,saidai ta alama ta adoce ba simple gown ba,kawai adonta ne yazo a haka.
Dauke kanta tayi daga kansa taci gaba da abinda takeyi,tana jinsa har ya ƙaraso kusada itah,zazzafan numfashinsa maicikeda abubuwa dayawa,gajiyah,kaɗaici,buƙata ds yana sauƙa kan wuyanta.
“Nagode”
Shine abinda yafaɗamata a hankali,inda bata kusada shi bazataji ma ya faɗa ba.
“Dana mefah?”
“Dana shigo sashen atleast naga wani mutum aciki,kuma ya haɗamin abinci.
Godiya ta biyu kuma da kika ƙarbi roƙona gareki,it mean alot to me.
Zanahiga nacire kayan,please zan iya fitowa naganki a falon baki tafi ba”
“Um”
Murmushi yayi,duk da batayi magana ba,amma kuma hakan ya tabbatar masa ta yarda kenan.
Sai bayan ya shiga ɗakinsa ta buga kanta tareda cize yatsa.
“Kutt Bombee yaushe kika zama haka,dagaske wai um kika ce masa,you need to see a doctor”
Tunda ta yarda batada zabi,dan haka ta zauna a kujera tana jiransa.
Bai dade ba yafito saboda yana tsoron kada ta sanja ra’ayi ta tafi,ba har cikin ransa ba yasan yake jinta,duk da yayi ƙarya yace baya jinta.
Inaga rashin Jaleelah ne a kusada shi yasakashi son kasancewa da maryam.
A zaune take tasaka aljazeerah Ana labarai na harin yaƙin da aka kai wata ƙasa.
Gabaɗaya hankalin ta yatafi ga akwatin talebijin ɗin,ko motsin fitowarsa bata jiba.
“Maryam!!!”
Karon farko a rayuwarta yaƙira sunanta,wani lokacin har mantawa dake da sunanta kenan,tsikar jikinta ce ta zuba lokacin dataji Haruffan sun fito daga bakinsa.
Saurin juyowa tayi tasauƙe idanuwanta akan sa.
“Na’am”
“Am nace shin zaki taimakeni da saka abinci?”
“Ohk toh”
Gani tayi batareda musu ba taje ta zuba masa abincin,duk motsin datake yana zaune yana kallonta,har taje fridge ta ɗakko masa lemo,a cikin wanda taga yafison irinsa,dan dama ranar farko sunyi kala kala ne dansu ga wanne yafiso.
“Gashinan na gama nizan tafi.”
Juyawa tayi zata bar wajen taji ya riƙo hannunta na dama.
Jimm tayi kaman saƙago tana jira taji ta inda jinin sai cigaba da bugawa a zuciyarta,bayan ɗaukewar dayayi na wucin gadi.
“Stay with me please,ina buƙatar wani numfashin mutum a kusadani a yanzu”
A zuciye ta fisge hannunta tareda cewa.
“Wai ancemaka ni mutum ce ne,ko yaushe zai zance kake kana addressing ɗina da mutum”
Kallonta yake da mamakin sanjawarta,wanda hakan yabashi dariyah amma ya cije.
“Uhm..uhm ke mecece to idan ba mutum ba”
“Mutanen dukka jinsi iri ɗaya akayisu,miye banbancina dakai”
“Ohhh to ina buƙatar jin mace a kusada ni”
“Halinku ɗaya ai”
Tafaɗa a hankali yanda bazaiji ba
“Kikace me?”
“Babu abinda nace,ka gama cin abincin na hutama da dawowa na ɗauki kwanuka”
A zuciye ta zauna akan kujerar gefensa tana kallon wani waje daban.
Yayinda shikuma yafara cin abincin idonsa yana kanta har ya gama.

A bakin ƙofah ta tsaya tana kallonsu,domin taga sun cika koda saura,khamees,Maleekah,Inayah,Hilyaan saikuma ita tabiyar kenan.
“Barkanku da zuwa”
“Yawwa barka”
Suka faɗa a tare.
Bayan ta zauna maida kallonta tayi kan Inayah,wacce ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kakkaɗawa,wani kallo Bombee ta watsa mata,da sauri ta maida ƙafarta tareda cewa
“Sorry ogah”
“Da alama zuwanki chadi yasa kin manta hanyar dana sakaki koh,wannan karon ki maida hankalin ki banason rawar kai,dafatan ƴar uwarki da faɗamiki mai zakiyi koh?”
“Eh tafaɗamin Anty maryam,kuma bazan baki kunya ba nayi alƙwari,koda yake kin fi kowa sanin hakan ai my ogah”
Tafaɗa tana sanja magana tareda kanne ido ɗayah,Hilyaan ce ta zungureta yayinda Bombee kuma ta jijjiga kai.
Mai hali baya fasawa,tafaɗa a ranta.
Jin Maleekah tayi shuru itada khamees yasa ta kalli inda suke.
Gabadaya basusan mai ake ba,sun bige da aikawa junasu satar kallo.
Gyaran murya tayi mai ƙarfi wanda ya jawo hankalin su.
“Mr romeo business ɗinku yajira a waje,yanzu muna buƙatar hankalin ku a nan”
Murmushi mai dauke da ma’anoni khamees yayi,yayinda ita kuma Maleekah tayi ƙasa dakai tana ƙikkifta ido.
“Mai nayi miss haka?”
“Hilyaan!!!!”
“Ahh sorry zan tambaya an jima”
Bayan sun gama abinda zasuyi kowa yasan aikinsa,ita Maleekah a lokacin aikinta zai fara,yayinda ita kuma Hilyaan zata jira sai anyi approve na komawarta aiki,itakuma Inayah sai Brr Na’imah ta dauketa tukunna.
A taiƙace dai sun shirya komai yanda sati komai zai fara aiki.

Bayan wani lokaci…….

Tafara yanke farce kenan taji kukan haidar,dan yanzu yayi wata shida,ta daina bashi mama,madara kawai yake sha,kuma yaron yayi wayo sosai,gashi fulele irin yaran madarar,sai fitina sosai.
A wannan wata biyun da Bombee tayi ita kadai a gida,ji take kaman tayi ƙaramar hauka,ga haidar ya dameta ga kuma Jabeer,tunda yasamu lagonta nayi masa hidima shikenan ya maidata baiwa a ganinta.
Dan yanzu ko bata kai masa abinci ba zuwa yake ya ɗauka a sashenta.
Ga plan ɗinsu yanzu yafara zafi,dan ma Maleekah tadamu damar ɗakkomusu takardun Share na Alhaji Abdullahi,suna jinsa yana nema kaman zayyi hauka amma suka yi miƙis.
Maleekah ta dauke musu hankalin Hajiya zeenah,wanda suke da tabbacin harda na hajiya rabi,kodayake ita dama ta auren ƴar take wacce za’a ɗaura nan da sati biyu.
A cikin wata biyun inayah tasamu yardar brr Na’imah,yayinda ita kuma Hilyaan tasamu shiga Division ɗin gen abdu manga,tana yiwa Gen Sameerah aiki,saidai bata ganeta ba saboda Badda kama da tayi.
Duk bayan sati guda sukeyin meeting a gidan da innayi suke itada inna Danejo,wacce take samun kulawa sosai a wajen su Hilyaan da innayin.
Kowa a lokacinne yake bada record ɗin daya samu mai muhimmanci.
Yatsa uku ta samu damar yankewa ta tsaya da abinda take,saboda wayar ta datake ƙara da kuma kukan Haidar.
Mr annoying taga yafito akan fuskar wayar,aikuwa nan da nan ta cune baki sama.
“Kai kai…..ƙaramin fitinnanne yana kuka,can kuma ga babban yana ƙira,waya taba tunanin kamar captain Bombee zata kare a gida tsawon wata biyu tana yiwa wasu hidima”
Jefar da nail cutter tayi ta dau wayar.
“Am Boss nace ba……”
“Faɗi kanka tsaye kawai,mai kake buƙata kuma?”
Dariyah yayi saboda jin mai tace.
“Uhm idan kinzo zaki gani ai,dan allah hurry up minti biyar”
Tun kafin yasake cewa wani abin ta suri haidar tayi part ɗinnasa”
Ko ƙwanƙwasa ƙofar dakin batayiba ta shiga,yana kwance akan gado yafito da kayansa dayawa akan gadon yana danne danne a waya.
Tsayawa tayi batace komai ba har saida ya dago ya kalleta,kanne mata ido yayi tayi saurin dauke kanta tana zazzare ido.
“Uhm nayi zaton za’a bar wannan bawan Allah yana ta jira,dama kaya zaki zabamin nayin Sati ɗayah a tafiya irinna wancan watan please,tunda nake bantaba saka kayan dazasu dace da tafiyah ba irin wanda kikayi min,naji dadinsu sosai”
“Wancan ma ai bakai ka sakani ba nina ga damar haɗawa koh………ohh nayiwa kaina,wannan bai san ayimasa gwaninta sau ɗayaba”
Taƙarisa maganar can ƙasa kasa.
“”Mekikace banjiba””
“Basai kajiba mr CEO kawai cewa nace sannu.
Naji zan haɗamaka amma hungo riƙemin ɗana,kuma idan ka bari yayi kuka daga Lokacin ba haɗa kaya…..clear”
Tana gama faɗin haka ta ɗora masa haidar akan cinyarsa,tareda zaddada masa da idonta.
Wajen kayansa tace tana nazarta su ɗaya bayan ɗaya.
“Ohhhh wai meyasa inna nemi kiyimin abu saiki bani riƙon,ina ƴar aikinki ta tafine wacce nake gani da”
“Ba ƴar aiki bace ta koma bakin aikinta,nikadai nake kulada shi,idan har kasakani yimaka wani abu wazai rikeminshi.
To shikenan bani ɗana ka haɗa kayanka da kanka mallam”
“Ahah barshi zan riƙeshi,inda sabo ai yakamata na saba,hadamin kayan barinaje falor kanki gama,kona zauna,yafada yana ƙwaƙume yaron saboda karta fasa,shima yaron a ɗan lokacin har ya sanshi sosai.
“Kayimin me,yawwa wacce ƙasa ne zakaje?”
“Ukarain ne,za’a yi meeting ne na wanda suke da share companyn mu a can”
“Mutun nawa ne masu share a can”
Bombee tafaɗa da sauri.
“Uhm mutum biyar ne,saikuma sauran masu share duk zamuyi meeting dai kawai,meyasa kika tambaya amma”
“Ahhh……uhm bakomai kawai na tambaya ne. Gen abdu yana cikin wanda zaku haalrci meeting ɗin?”
“Eh yana ciki,kin sanshi ne”
“Ahah ba har can ba,mahaifin Lubnah ne tana faɗar yanada share na companyn shiyasa na sani”
Shuru Jabeer yayi da zancen,amma daga yanda yaga fusakarta yasan ba iya hakane yasaka shiga yanayin ba..
Tana hadamasa kayan tana nazari har ta gama.
Tunkafin tafito falon taji kaman muryar mace,
“Hmmm yanzu abinda kake kana kyautawa kenan honey,kwana shida kenan baka ƙwana a sashena ba ,kana zuwa ko awa guda bakayi kake fita,yanzu nina biyo naga ya kake kawai na ganka kana zaune hankalin ka kwance,riƙeda ɗan shagen matarka”
“Oh Lubnah yanzu duk zamana dake da abinda kikayi min duk yana a bana kyautamiki,kada ki manta fah rabonda ki sauƙemin nauyina dayake kanki anyi wata uku kusan,amma duk da haka ban kyauta ba koh.
Da kike faɗan bana kwana a sashenki idan na kwana zakiyi min maganin abinda yake damuna ne,tun ina tunanin bakida lafiya yanzu na gano da gangan kikayi hakan.
Amma ki zuba ido idan har nasake kawo mata biyu gidannan zanga yanda zaki yim rowar kanki.
Da kike faɗar na riƙe yaro kuma,ina abinda yafi yarone ma zan riƙe,saboda tafiye min ke itada shagen ɗannata da kike faɗa”
Kuttt akan ta kakemin Wannan tujarar JJ?.
Barina haɗu da ita munfukar Allah sai nayi maganinta”
“Gatanan basai kinsha wahalar nemanta kinyi maganinta ba”
Ɗaga ido tayi ta kalli Bombee wacce tayi maganar,Lokaci guda ta maida fuskar rashin wasa.
Takowa tayi har gaban Lubnah ido cikin ido.
“Meyasa kika kasa maganina Lubnah,wai a hakan har kika samu damar zuwa kiyi burga a gaban miji,nifah ko a namiji bana ganinki ballanta na kuma mace”
“Hehehe dadinta ma kema ba mace bace a gabansa face Robot mai yimasa aiki,saboda nasan har yanzu bai sanki a mace ba.
Koda yake wazai saka jikinsa a inda wani gardin ya huda babu aure,harda sakamakon ɗa na shege,shine aka zo ana mannawa mijina ɗan domin ya samu shiga.
Rashin haihuwar ai ba hauka yasakashi ba dazai ƙarbi ɗan shage a matsayin nasa”
“Ahahah mai kikeci nabaka na zuba Hajiya Lubnah,niban cusa masa ɗana domin yasamu shiga ba,hasalima aikin raino kawai na sakashi,tunda naga ita matarsa tsawon rayuwarta kashi kawai ta iya haifa,bata taba bashi dan da zayyi raino ba. Bashi nake ya koya kafin wanda ake ƙira mata suzo su haifamasa nasa,tunda wannan kazar ita batada gurbin ƙwai saina kashi Juyace”
Idon Lubnah ne yayi ja saboda bacin rai,hannun ta ɗaga zata kifawa Bombee mari.
Cikin zafin nama kuwa ta riƙe hannun tamm a nata tareda natseshi saida ta sau ƙarar wahala.
“Kull nasake ganin hannunki kusada fuskata ,idan kika kuskura kika aikata hakan kuwa,…..to a ranar hannunki ba hannunki bane ba,domin ko ubanki gen abu manga bilahillazi bai isa hanani cireshi daga jikinki ba a garinnan.
Shidama baki inyasan mai zai faɗa bai san mai za’a maida masa ba.
Kibi a sannu baki gama sanin ni wacece ba,zaifi miki ki dunga taka tsantsan dashiga layin dana shata.
Kullum ina faɗamiki,kuma shizan faɗawa masu zuwa ma.
Bombee babu ruwanta da shirginku harkar gabanta take,amma duk wanda yashiga jan layin data shata……..hmmm don’t imagine the consequences”
Saki hannun tayi yayi jawur abinka da fatar data sha mayuka babu ƙarfi,Lubnah ji tayi kaman ta saki fitsari a wando.
“Kaima bani ɗana nabar wajennan,damuwarka zata sakani ciwon kan da ban sababa”
Sakoko yake kallonta,itafah ta gama rigimar amma kuma wai shine ma zai sakamata ciwon kai,haidar daya fara bacci firgit ya tashi saboda hayaniyar su,amma ji abinda tace.
“See this woman”
Yafaɗa a kasanlance.

Can cikin dare kaman a mafarki taji wayarta tana ƙara.
Ɗagowa tayi taga ƙarfe shabiyu,kuma Jabeer ne.
Mamaki abin yabata,shin mai zaice mata kuma,dan rabonta dashi tun da yamma lokacin da suka rabo ta karbi ɗanta.
Ɗaukar wayar tayi cikin muryar bacci tafara magana.
“Hello lafiyah na…..”
Bata ƙarisaba taji maganar sa daƙyar cikin nishi.
“Am sorry but please zaki iya gareni yanzu,ina buƙatar taimakonki ne”
“Taimakona kuma mai yafaru haka”
“Zafi jikina zafi sosai,kuma…..”
Wayarne tafaɗi daga hannunsa tafaɗa ƙasa.
Da sauri Bombee tayaye bargon dayake jikinta da saka slipper tafita da sauri.
A kudundune tasameshi a bargo yana rawar ɗari kaman an jona masa shocking.
Yayewa bargon tayi tareda taba kumatunsa,kaman ta taba garwashi.
Hasbunallah garin ya haka yaushe zazzabi yayi maka wannan kamun.
“Uhmm dama inaji tun jiya haka,amma baiyyi yawaba sai ɗazu,ki miƙomin magani a cikin drawer can”
Drawer daya nuna mata ta zata buɗe.
“Ahh karki buɗe am…..”
Kafin ya gama magana har Bombee ta buɗe drawer.
Jada baya tayi tareda zaro ido tana kallon abinda yake cikin drawer a kiɗime.
“Menene wannan Jabeer nake gani haka uhm?.
Koyaushe drawer nan na kulle,dama abinda yake cikinta kenan”
Kallon ta yake da idanuwansa wanda sukayi narai narai saboda zafin zazzabi,yama gagara furta mata komai.

*sadi-sakhna ce*

Page 🖤33••34🖤

Kallonsa take tareda jin sanda zai bata amsar me waɗannan tarin magungunan suke a cikin drawersa,kaman companyn magani.
“Bakace komai ba,da alama waɗannan magungunan duk nasaka baccine,kanaso kacemin su kake sha?
Meyasa to bakada lafiyane na tsawon lokaci ka boye?”
“Uhm duk wannan tambayoyin fah,kin damu dani har hakane?”
Yaƙarisa maganar yana dariyar ƙarfin hali.
“Bafa abune na wasa ba Serious me wannan magungunan suke a wajennan?”
“Sha nakeyi amma bakoyaushe nake buƙatarsu ba sai ina cikin matsanancin yanayi,ba wani abune na serious ba yanda kike tunani ,yanxu dai miƙomin maganin zazzabin nasha,ƙarfina ya zuqe a maganar danayi ɗinnan”
Ajiyar zuciya ta sauƙe,bata sake cewa komai ba ta miƙomasa maganin yasha kaman yanda ya buƙata.
Saida taga yasha kana ta tashi zata bar ɗakin..kamo hannunta yayi ya riƙe gam,ja tayi amma ya riƙe sosai da guntun ƙarfin dayake jikinsa.
“Dan Allah kada ki tafi ki zauna”
“Uhm saboda kana buƙata ta koh,sai nan da sati biyu bazan sake ganinka ba ballanta wani abun ya haɗamu”
“Uhm nan da sati biyu kikace ai ,kafinnan ki taimakamin wajen zama a tareda ni”
“Ina matarka meyasa baka ƙirata ba saini”
“Meyasa kike son maimaita maganar da kin riga kinsanta uhm?”
“To yanzu dai bazan zauna dakai ba,saboda nabar ɗana a ɗaki shika ɗai”
“Idan bazaki zaunaba zan biki to mu tafi sashenki,i hope hidima bazai miki yawa idan mu biyune koh”
Jimm tayi batace ahah ba bata kuma ce eh ba,tarasama mai zatace da taji maganar da yayi.
Hannunta yasake yana ƙoƙarin tashi,batada zabi ta taimaka masa suka nufi sashennata badan tasoba.
A gado ɗayah suka kwanta bayab sun saka Haidar a tsakiyarsu.
Abinda bata tabayi ba tunani ba kenan daga wajen mijinnata na wata shida.
Bayan sallahr asuba tunda koma bacci bashi ya tashi ba saida kukan haidar ya jiyarci kunnesa,buɗe ido yayi suka haɗa ido da Bombee,wacce take ta kiciniyar sakawa yaron diafer,da alama kuma yunwa yake ji ba son saka kayan ba.
Kallonsu yake cikeda sha’awar su,abinda yake mafarkin samu kenan,amma kuma bai samu ba a rayuwarsa,shine ganin matarsa suna zaune lafiya da kuma ɗansa.
Yaron kwata kwata baya kama da itah,illah abu ɗaya dasuka hada dashi shine idonsa kawai.
Kallon fuskar yaron yake ko zai sake ganin wani abu da suka haɗa da Bombee,saidai sabanin ganin hakan saima wani abu daya gani a fuskar yaron wanda yasaka ƙirjinsa bugawa.
Saurin kawar da kai yayi yana jijjiga kai. Inaa rashin samun yaro nasa na kansa,baikamata yafara ganin dan da baisan asalinsa ba a matsayin nasa.
Yana tsoron kar zama da yaron waje daya yasa soyayyar yaron tayi tasiri a ransa.
Yasan ko tsafi yake da baƙar zaba Hajiya zeenah bazata bari yahaɗa alaƙa da yaron ba.
“Tunda ka tashi na haɗa maka ruwanka,ka gama ina jiranka a dining”
“Bazaki tambayeni ya jiki ba”
“Jikinka na ganshi ba buƙatar tambayarsa,Fatan Shine Allah ya sawwaƙe kawai”
Daga haka ta suri yaronta sukayi waje,saida zata fitane ma yakula da kayan dayake jikinta,daga ita sai bom short da t-shirt.
“Ohh Allah ya bani ikon tafiyar da wannan bauɗaɗɗiyar baiwa taka,ba sonta nake ba,amma kuma zama tareda ita yana sakani cikin nutsuwar zuciya,na ganta tana ta hidimarta da yaronta yana sakani jin inama suɗin iyalina ne danake da iko akan su.
Narasa wanne irin yanayine haka nake shiga gameda su”
Bayan ya fito daga wanka ya kalli kayansa nazaman gida,da alama tashigo dakin kenan yana wanka.
Madara take bawa haidar a feeder sa Lokacin daya fito.
“Wannan yaron ya kai cin abincine,bazaki bashi mama ba”
“Na yayeshi wancan satin,madarar formular nake bashi,dama dan jikinsa yaƙi karbar madarane yasa na bashi nono”
Zaro ido yayi jin tsaurinta gameda yaronnata.
“Haba ke kuwa,shiyasa yake kuka kenan,bai kamata ya wannan yaron ki cireshi daga abincinsa ba,abune da kowanne yaro yakeson samu a wajen mahaifiyar sa……….”
“Nasani Mr CEO sannan koda da lokaci kadan bantaba yin abu danna cutar dashi ba,ina sonsa kaman yanda uwa take son danta,bukatar hakan ce ta taso.
Kuma a yanzu jikinsa ya karbi madarar fiyeda da”
“Uhm”
Shine kawai abinda Jabeer ya faɗa,dan bashida tacewa a ciki,tunda ɗan ta ne kuma ikonta ne.
“Oh barina zo nabawa angon nan da lokaci kaɗan abinci,kar azo biki a ganka a rame”
Gogewa haidar bakinsa tayi tareda bashi abin wasa ta taho inda abincin yake.
Sai da ta gama zubawa kafin ya samu waje ya zauna yafara zubawa cikinsa.
Maganin yasake sha bayan abincin,kafin ya miƙe akan doguwar kujera..
“Naga ka samu sauƙi fiyeda jiyah,ka ci abinci kasha magani,toh bazaka tafi sashenka ba koka fita”
“Uhmm ni bazan tafi ba saina gama warkewa,saidai in korata kike toh”
“Menene amfanin ka taremin a sashe to bayan da naka,nina rasa mai yasa nake ta ɗawainiya dakai ba matar ka ba”
“Kema ai matata ce ina,ko kin sauke auren daga kanki?”
“Hhhhh habadai koda ni matarka ce amma ta wata hanyane daban,ka daina sakani cikin wannan matsayin”
Duk korafin da tayi Jabeer bai bar sashannata ba,dan inda sabo yafara sabawa da halayyarta. Sai wajen yamma kafin ya tafi,bayan ya yi wanka yaci abincin rana,wai suna yana jinya,amma ƙara ƙiba ma yayi fiyeda yanda tazo ta sameshi.
Yana fita itama tafara shiryawa saboda zuwan meeting din da zasuyi itada su Hilyaan,jiya yakamata suyi amma ta ɗaga saboda Jabeer.
“Zancen Dear gaskiya ne data faɗa maka,na fasa ɗora mahafinku akan wanann aikin,domin bazayyi min yanda nake so ba.
Dan haka ka gaggauta dawowa ƙasarnan kafin ba sanja shawara,kana jina koh”
“Ehh zan dawo,waye zaiqi zama ceo na company babba haka,gaskiya you are the best mommy”
“Wanann koɗaɗdiyar matar taka inzata zauna dakai a ƙasarka ta biyoka,in kuma bazata zauna dakai ba ka raba tsakaninku ka dawo gida”
“Kai mommy she have preganant,and you know i love her so much”
“Kai kuma ka sani”
Ta kashe wayar tana tsuka.
“Banda taurin kai irinna yaran yanzu,mai zayyi da wata baturiya oho,hakan ma ba musulma ba,Soon zanyi maka aure da wacce nake so,bazaiyiyu yayanta su gaji abinda nakeson ɗoraka akai ba kam”
“Hajiya akawomiki ruwane ki sha”
“Eh kawomin,da saikin tambaya,zamanki gidannan wata biyu yaci kinsan mai nakeso da wadda banaso ai”x
“Kiyi haƙuri Hajiya kai nne sai a hankali na tsufah,yanzu zaki faɗi magana an jima na manta.
Uhm dama inaso na tambayeki zanje ganin jikokina a wajen mamarsu da yamma Hajiya inba damuwa”
“Rose”
“Yeah Hajiya anything else?”
“Ki bawa Yalwa dubu biyar kudin mota zataje dubo jikokinta,
Ke kuma kidawo da wuri,karkiyi irin wancan zuwan ,mtsww wai nima narasa wanda zan dau aikin gogegoge sai tsohuwa,koda yake ba laifi kin iya aiki”
Taba gama faɗin hakan tashige ɗaki tabar Secatariyarta da Baba yalwan.
Naira dubu uku tabawa yalwan maimakon yanda Hajiya tace,sauran ta soke a nata aljihun.
Karba tayi kaman bata gane mai brr Na’imah tace bataba,godiya tayiwa Rose har ƙasa,inda itakuma take mata kallon raini .
Ɗakin masu aikin tashiga ta shirya kafin ta fito,tafiya take zugub zugub har ta iso wata kwana.
Wata dariyar yan duniya tayi tana kiƙƙifta ido wanda basuyi kamada na tsofi ba,dukkuwa da yanda tayi iya ƙoƙarinta wajen yin kwalliyar dazata tauye mata fuska,ka iya duniyanci mutum bai isa ganota ba.
Ta gefen ido take kallon wanda aka saka yafi bayanta,saida ta kula mota tatareshi tayi wuff ta faɗa wani butique.
Banɗaki ta shiga ta wanke fuskarta tareda saka kayanta wanda suke cikin buhun.
Powder da shafa da kuma jan baki,sai bakin glass tada saka.
Fitowa tayi tana taku irin na ƙwararru,a hanya suka bugi juna da wanda aka saka yabi bayanta,sai waige waige take yana neman tsohuwar dayake bibiya.
“Uhm guys baka ganine kana buge lady?”
“Am sorry madam bangani bane”
“Ohk ya wuce”
Dariyah ta sheqe da ita bayan ta tari taxi ta hau.

A bakin ƙofar gidan tayi parking motarta,ta daɗe kafin ta fito ta nufi gidan.
Innayi ce ta amsa mata sallamarta wacce take ta karatu,saboda makarantar jami’ar dazata shiga,wacce Bombee tace zata sakata.
“Innayi ykk ya karatu,ya kuma inna?”
“Lafiya kalau addah Bombee,su Hilyaan da inayah suna ciki,amma Maleekah bata zo ba”
“Meyasa bata zo ba,mun fa haɗu da ita a gida zata taho”
“Uhm naji Hilyaan tana cewa wai zasu tahone da khamees kaman”
“Ohh this girl,tanada rigima sosai,bana hanata biyema Khamees bane,su barni naji da wanda yake kaina ma na hidima”
Dariya innayi tayi,daga nan batace komai ba.
Ɗakin inna tashiga ta gaisheta,tana zaune a kan darduma tana jan carbi.
“Inna barka da yamma ykk,nayi magana da malamin dana ce zan kaiki wajensa,watakila sai a dace a wajensa”
Kama hannun Bombee tayi tareda nuna alamar suje su biyu.
“Ahah inna ke zaki fara zuwa,naki zai iya yin sauki yanzu,amma nawa dole sai nayi bincike gameda wacce tayi aikin,sannan kuma naki yafi wahalarwa fiyeda nawa,barina na tafi inna”
“Kitaaaafi anan wajen,bamason kizo wajennan Ta haramta mana kaiki wajen mahaifiyar ki kifitaaaaa”
Toshe kunnuwanta tayi tana cize baki,saboda yanda kan kemata kamar ana doka mata guduma.
Sakin hannunta tayi ta wuri tabar ɗakin,bayan tasake waigawa ta kalleta,tana son kasancewa da mahaifiyar tata,itama kuma tasan tana son ta ganta a kusada ita.
Sai bayan sun zauna sun kusa minti goma kafin Maleekah suka shigo itada khamees,dukkansu idonsu a ƙasa yake,Lokacin dasuka ga yanda Bombee ke aikamusu kallon tuhuma.
“Mal…….”
Da sauri tazo inda Bombee take ta durƙusa.
“Haba antynah karkice haka mana,wlh ina sonshi kuma kinsan bashida wani mungun hali,ko kowa yaki ke mai auramin shine ai”
“Saboda a matsayina nawa”
“Na matar babban yaya mana,allah nasan kinacewa yah Jabeer yabarni tareda shi ta zauna,shikuwa inya faɗawa abba magana ta kare”
“A ganinki ba,Maleekah har yanzu banida matsayin dazan shiga sha’anin danginku,ko kin manta matsayina ne a gidan uhm?
Har raina soyayyarku da khamees ban ƙita ba,amma babu abinda na tsana irin jawo magana,shiyasa nake taka muku birki kafin abin ya fi ƙarfina.
Yanzu dai ba wannan ba,jiya da daddare kin ƙirani kan cewar Hajiyah zeenah bata yarda da abinda kike faɗa ba mai yasa?”
“Uhm mijinkine sila ba laifina ba,kina bashi kulawa da yawa har ya sanja yaƙara kwarjini da fara’ah,shiyasa Mommah tafara zargin akwai abinda yake faruwa,musamman dayace wai a gidansa yanzu yake cin abinci.tasan kuma Lubnah bata girki,shikuma bayason cin na ƴan aiki,shiyasa tafara zargin akwai abinda yake faruwa.
Naji kuma waya da maman Jawaheer kan cewa an samu ƴar aikin dazatayi aiki a sashen,ta yanda zata dunga kawo musu abinda yake faruwa”
Aikinki yayi kyau,Hilyaan fah mai yake gudana a barrak.
“Nothing important,naji dai Gen nacewa shirin daya daɗe yana jiran zuwansa ya rushe,da alama Jabeer bazai halarci meeting ɗin ba,dan haka sun ɗaga shi sai next month”
Dariyah Bombee tayi tareda cewa.
“Uhm kawai ƴar ƙaramar rashin lafiya na haɗa yayi da daddare,shine kawai”
Zaro ido sukayi suna kallonta,musamman ma Maleekah.
“Oh kawai na saka masa grape(inibi)a cikin jus,kuma dama yanada allergy dashi,sai yasakashi night fever da kuma small rash.
Amma naji da komai he is normal now”
“Amma anty Maryam meyasa,muma munsan bayason grape sosai”
“Amma nibai faɗamin bayaso ba,da alama bayaso nasani,shiyasa nayi amfani da hakan na ceceshi.
Mai kike tunanin zai faru inya halarci meeting ɗin,zai rasa kunerarsa a ranar ne,shine abin gen abdu manga ya shirya,tunda basusan muna da takardun Alhaji Abdullahi ba ballantana su dakata.
Inaya fah mai ya faru?”
Tun ɗazu take zaune bata ce komai ba,saida aka zo kanta kafin tayi gyaran murya dan lumshe ido.
“Eh to maganar gaskiya ba gen abdu manga ne zai hau kujerar ba yanda kuke tunani,dan haka aikin Hilyaan ya ƙare na bibiyar Sa a barrack..”
“Mai kike nufi da hakan Inayah?”
“Barr Na’imah itake kalmasa koma daga gida,ganin mijinta bazai mata yanda take so ba,yasa ta yanke shawarar ɗora babban ɗanta waro Ammar.
Wanda ya tare a ƙasar England da matarsa juliet,yanzu haka tana ciki,kuma suna shirin dawowa nigeria saboda yazo yazama CEO yanda ta tsara”
Abinda Inayah tafaɗa gabaɗaya yabasu mamaki,inda basu saka Inayah tajiyo ba da bazasu san barr Na’imah ce ke komai ba.
“Okay Hakane abin,dama nazargi haka,amma ban taba tunanin tsanar da tayiwa ɗannata kaɗan bace sai yau,wato yanzu ta nemeshi tunda zai mat amfani.
Zanga kuwa ta yanda zai zama CEO ɗin inanan.
Mungama meeting daga nan,sabuwar haɗuwa kuma sai nan da bayan zuwan Amarenmu.
Saboda nasan dukkansu zasuyi ƙasa da makamansu saboda zuwan bikin,muma mu huta haka.”

“Wayyo jikina,wayyo bayana ku taimaka min yana ƙaiƙayi,wayyo zan mutu zan mutu nace”
Duk ihun da Inna laari take babu wanda ya jita,tana ɗakinta a ɗaure da sarƙoƙi.
Gaba ɗaya halittun jikinta sun sanja kamanni,babu wanda zai ganta ya ganeta a yanda take.
Wasu irin ƙuraje sun yayyame jikinta,da fuskarta ta jirkice.
Kurajen sunyi jawur saboda yanda take durja jikinta a duk inda ta samu.
“Nace kuzo ku taimakeni,Zilliyah ta cuceni bayan nayi ta bauta mata shine ta gudu ta barni.
Itace fah nabawa ɗan Danejo jaririnnan taba wa aljanunta suka cinye,nasa ta sakawa Bombee shaɗanu,wanda suke zukata da yi rashin mutunci ta daina tausayin iyayenta da daina sonsu,sannan kuma ta daina tsoron kowa a duniyah.
Nice nan laari nayi komai da komai.
Nina makanta Danejo na kumantata,nasa likita yace ciwone yayi mata haka duk fah nice nayi komai da komai.
Tunda na faɗamuku ku dawomin da ƴata Innayi nah innayi nah.
Nasan idan na kaiwa zilliyah ita ta aurawa ɗan ta,to zata warkar dani nakoma yanda nake,har kashemin Danejo zatayi itada zuri’arta,sanadin ta duk na shiga wannan halin nasan”
Mlm Ahmadu wanda yake bakin windownta yana jin abinda ta faɗa,share hawayen idonsa yayi tareda wurga mata Sinƙin biredin dayake hannunsa.
Tana ganinsa kuwa takaimasa wawura kaman dabba,haka da ledar ta dunga ci saida ta cinyeshi tasss .
Barin wajen yayi dan bazai iya jure ganinta haka ba sam.
Inhar abinda ta faɗa gaskiya ne,to kuwa bashida idon dazai kalli iyalannasa ba wanda suka shiga duniya.

Ke duniya…….!!!!

Page 🖤35••36🖤

Bayan meeting ɗin da sukayi ba ita ta dawo gida ba sai wajen magriba.

Tana zuwa kayan jikinta tarage,nan da nan ta hau haɗa abinci.

‘Wani Lokacin tana mamakin kanta yanda ta damu da rayuwar Jabeer,abinda bata taba yiwa wani ba kenan,ko kai saboda aljanun kanta basa kulawa da tsakaninta da shine kai,shiyasa take jin bond din tsakaninsu yana ƙara tasiri a jikinta.

Tana cikin zurfin tunanin taji ƙarar rufe ƙofah.

“Uhmm ɗazu nazo bakya nan,meyasa in zaki fina bakya sanar dani inda zaki uhm?

Ko so kike kema ki zama iri ɗaya Lubnah akan haka”

“Ba maraba akan hakn,amma kuma akwai banbanci,inda da buƙatar tambayar ma to Hajiya zeenah zan tambaya bakai ba”

“Meyasa ita take aurenki?”

“Wani abu mai kama da hakan dai”

Ganin yanda take amsa masa maganar yasa ya rabu da ita ya watso ruwa ya tafi masallaci.

Lokacin daya dawo ta kammala abinci ta saka a dining,zama yayi ta zuba masa yaci ya ƙoshi kafin ya sake ficewa.

Koda babu biyayya irin yanda yake son macen dazayyi rayuwa da ita ta kasance,amma kuma badai kulawa da cikinsa ba kam,da kuma kayansa da ɗakinsa.

Dan har ya zauna yaci abincin tana ta danne danne a system bata cemasa ƙala ba,yakula akwai abinda yake ranta,dan haka ya fita yabata waje..

Ƙarfe goma ya dawo gidan ya shiga ɗakinta.

Tana kwance daga ita sai wata riga iya gwiwa,wacce ta ɗage saboda kwanciyah,haidar kuma yana cikin gadonsa na yara a gaban gadonnata.

Tunda ya ɗora idanunwansa akan cinyoyinta ya gagara ɗaukewa,abinda ya taru masa tsawon lokaci ne yafara koƙarin taso masa.

A hankali yafara takawa har zuwa inda take kwancen,a bakin gadon ya zauna tareda kaiwa hannunsa kan cinyarta..

Duk da yanda ƙwaƙwalwarsa keson hanashi,amma kuma zuciyarsa tana muradin hakan,kuma tafi da hannayensa.

Cikin sanyi yake shafa duk inda rigar ta bayyana,vai ankaraba yaji caraf Bombee ta tashi tareda riƙe hannunsa,hakan da tayi ne yasa ya faɗa jikinta suka koma kan gadon..

Kallon idonsa take shima yana kallon nata,gashi duk ya bada ƙarfinsa akan ta.

Tana ƙoƙarin tureshi daga kanta shikuma yasamu damar haɗe harshensu waje guda.

Yadaɗe yana sarrafa harshennata batayi yinƙurin hanashi ba,saida taji yana shirin wuce gona da irine ta hanyar son rabata da rigarta yasata ta zame jikinta.

Numfashi yake sauƙarwa mai ƙarfin gaske yana ƙoƙarin saita kansa.

“Please…..mmmmaryam help me please”

Jijjiga kai tafarayi tareda yin magana cikin karyayyiyar murya,wacce take nuna tsantsar tausayinsa.

“Kayi hakuri Jabeer amma bazan iya ba sam,hakan zai karyamin plan dayawa idan nayi”

“Saboda kin tsaneni shiyasa bazaki bani kanki ba,ina buƙatar taimakonki a yanzu maryam a matsayina na mijinki,bakya ganin lokacin da muka ɗauka bai…….”

“Badan na tsaneka bane Jabeer ko kuma dan bana tausayinka,inda inada ikon baka wannan taimakon zan baka kaman yanda na yi maka sauran abubuwa.

Bazan iya baka kaina ba alhali bansan matsayar aurena ba a gareka”

“Kamanya,kina nufin zan sakeki idan na kwanta dake,ko kuma na juyamiki baya,bahaka nake ba maryam”

“Nasan ba haka kake ba,hasalima ba wannan dalilinne suka sakani hanaka kaina ba.

Jabeer aurena dakai yarjejeniya ne na tsawon wata shida wanda mukayi da mahaifiyar ka,banda na maidashi na shekara guda da yanzu saurana wata guda na bar gidannan,yanzu haka ma tana kan bakarta dana gama mata aikinta kowanne lokaci zan bar gidannan..

Dan haka banason ka saka ranka akan macen da koyaushe zata iya tafiya,tunda matarka ta ƙaurace maka,kayi haƙurin sati biyu mata biyu russ za’a baka.

Amma ni tamkar mafarki ce,duk yanda zaka tsaya a ciki dole zaka buƙaci farkawa,dan haka ina taimakonka ne ka farka kafin lokaci ya kure maka”

“Hmmm duk naji bayaninki,nasan bazai wuce saboda kina da zafin zuciya zakiiya korar Lubnah,shiyasa ta auroki,wannan dalilinne kenan kullum take gargaɗina dana nisanceki badan zaki cutar dani ba saidan itake buƙatar hakan.

Nikuma zan nuna miki cewar dasannu zaki zama mallakina Maryam,duk da bansan mai nakeji a kanki ba,amma kuma zuciyata tana bani bazan jure rashinki a cikin gidana ba”

“Wannan duk maganar zuciyarka ce,amma a yau idan Hajiya zeenah taga dama zata iya raba aure mu,abu ɗayane zai hanata yi shine tasan bazan yadda ba,saboda contarct ɗin mu bai ƙareba”

“Shikenan zanyi ƙoƙarin yin nesa dake har saina jaddada matsayin aurena dake Maryam,abu ɗaya nake so koyimin,shine ki yi ƙoƙarin kar mommah ta soke contract ɗin dake tsakaninku”

Ɗaga masa kai Bombee tayi alamar ta yarda,daga nan yadafa yafita daga ɗakin.

Da kallon tausayi Bombee tabishi kafin ta gyara kwanciyarta badan don bacci zaizo ba.

“Kabani lokaci Jabeer kafin nayi tunanin zama dakai ko akasin haka,amma ita kanta mahaifiyar ka saidai kayi haƙuri,amma in shirina yazo kanta bazan ragamata ba sam”

“Mommy kina ganin zan haska a bikinnan kuwa yanda ya kamata?”

Jawaheer tafada tana dudduba uban lallen da ake zana mata,duk wanda yaganta daƙyar zai ganeta,yanda tasha uban gyara da kuma kwalliyah..

Yaune za’ayi bridal shower,duk da cewar uban gayyar yace babu wani event da zayyi,su dama gidan su Jaleelah mahaifinta bayason wasu bidi’o’i a biki.

“Ƙwarai ma kuwa dear,kinyi kyau fiyeda yanda kike tunani,ina mai tabbatar miki idan ya ganki sai ya rasa tunanin sa”

Murmushin jin daɗi tayi jin abinda mahaifiyar tata ta faɗa,gobene ɗaurin aure,bayan an ɗaura zasu je gidan su na kwana biyu,daga nan su wuce honeymoon na Wata guda,kowaccensu zata samu sati biyu,zayyi sati biyu da Jaleelah sannan yayi sati biyu ma da Jawaheer a ƙasashe daban daban.

A bangaren Jaleelah ma ado na musamman danginnata sukeyimata,na gargajiya mai ratsa jiki,duk wanda ya ganta saiya sake,yanda fatarta tayi sharr da ita tamkar tuffah.

“Wlh fadeelah banason magungunan da Inna take sakani sha,ina tsoron fah kada a samu matsala kafin a gama bikinnan”

“Wacce irin matsala,babu abinda zai faru,keda zaki ɗaga dubai kisha amarcinki”

“Uhm ina son zuwa Kam amma fah kinsan bata yanda raina yakeso zanje ba”

“Kibar maganar nan haka kada tayi nisa,kar wani yashigo,muje na rakaki ki wanke lallen kada ya dame.

Ya kiraki ne Mutumin akan zancen sallamar ƙawaye?”

“Uhm munyi waya dashi dasafe,karkiji yanda yake tayimin zumuɗin ya ƙosa na zamo mallakinsa,yanaji dani sosai fa.

Batun sallama kuma kada ki damu kinsan zai baku sosai.

Kikace da yamma makarantarmu zasuyimin walima koh?”

“Uhm zasu haɗa walima,aikin cancanta suyimiki abinda yafi walima ma Hafiza Jaleelah”

Dariya sukayi a tare jin abinda Fareeda ta faɗa.

“Wai ka warke amma har yanzu naga baka shirin tafiyah sashenka,yau anyi sati biyu kusan.

Koda yake manene na damun kaina,ana kawo maka amarenka ai bazan ganka ba daga nan”

“Haka kike tunani,saidai in baki nemeni ba zaki ganni,bana manta Alkhairi ballanta irin wanda kikayimin.

Ohh tsayah wai kina nufin bazakiyi kewata ba inna tafi”

Ƙarisa saka sarƙar tayi tareda zaran gyalenta zata fita waje.

“Uhm kanka ake ji nina siyayya”

“Amaren zaki yiwa?”

“Saboda kaika bani kuɗin uhm?”

Dariyah Jabeer tareda sake komawa ya kwanta akan gadon nata,aikuwa fass haidar ya mari fusakrsa wanda yake zaune akan gadon.

“Maryam da alama ɗannnan naki shima ke ya iyo,kiga marin dayayimin”

“Ahah ba yanda za’ayi ya iyo ni,inaga ubansa ya ɗauko wataƙila”

Jimm yayi jin abinda Bombee tafaɗa.

“Akwai abubuwa da dama a rayuwarki wanda suke binne a ranki,shin a matsayina na mijin dakike aure bazaki faɗamin yanda kika samu yaronnan ba,duk da cewar alama dayawa suna son nuna asalin yaron bashida kyau,amma kuma zuciyata ta kasa yarda da hakan,kaman yanda takasa yarda da cewar cutarwa kikeson yi a gareni.

Sannan tawani bangaren inajin kaman kusanci tsakanina da yaronki”

“Kayi hakuri amma kozan faɗa maka menene asalin yaronnan badai yanzu ba,sannan inaga zaman dakayi dashine a kusa yasa kaji hakan,amma inkana ganin bakason ɗana bance kasoshi ba,babu wanda na tilastawa ya kalli dana a fuskar so ,tunda ina son abuna ya wadatar.

Batun aure kuma zuwa yanzu kasan matsayin aurenka a wajena,dan haka babu zancen boye boye a ciki,ni ma tafiyace,kowanne lokaci zan iya barin gidannan nan da wasu watanni shida masu zuwa”

“Abinda kike faɗa bazai dameni ba maryam,Saki a hannuna yake ina?”

“Kuma za’a iya saka ka kayishi koyaushe ba?”

Shuru yayi bashida tacewa har ta dauki ɗanta da jakarta tafita.

Har takusa shiga mota saikuma ta hango matar da aka kawo leƙen asiri tana leƙa windowanta.

Komawa tayi inda take tsaye tace.

“Ke mekike anan wajen,abinda aka turoki kiyi kenan?”

“Uhm Hajiya Maryam barka da fitowa,naga na gama aikin aka banine,shine nakeson na tambaya koda aikin dazan yi miki”

“Miye sunan ki?”

“Uhm Sunana Zaleeha hajiya”

“Toh Zaleeha (kallon mamaki tayiwa Bombee ganin takira sunanta kai tsaye batareda sakayawa dukkuwa da ta haifeta)

……miye kike yimin wannan kallon zatonki zance Inna ko kuma baba,uwata ce ke komai,kicire wannan a ranki,bana wannan shishshigin,ki nutsu kiji abinda zan faɗamiki.

Karki sake koda wasa ki tsallake layin dana shata tsakanina dake,kiyi aikin da ita uwar mai wajen tabaki,inkinga dama ko numfashi nayi kije ki sanarmata bai dameni ba,saboda kaff gidannan ba wanda nake tsoro.

Amma kika kuskura na kamaki kina shiga lamarina saina sanjamiki kamanni,ba ruwana da tsufanki”

Tunda Bombee tafara balbalamata masifah kanta yake sunkuye bata ɗaga ba,har saida tagama dan kanta ta tafi.

Sai bayan tashiga mota tatafi kafin Zaleeha tabi motar da kallo tareda yin wani shu’umin murmushi.

“Hmm yarinya kenan,kina tunanin zanyi wani abun dazan bar kusada abin farautana yake,da sannu zaku zo hannu na dakake har su innayin,kuɗin mallakina ne,jininku fansa ne gareni nida aljanuna,anriga an bani,kijira yanda zan wargaza rayuwar daga no kina ginawa mai ɗauke da haske a cikinta”

Tun Bombee bata shagon dataje siyyaya ba taji wayarta na ƙara a jakarta.

Fitowa da ita tayi ta kalli sunan Hajiya zeenah a jiki,ɗagawa tayi domin jin mai zatace mata.

“Hello Hajiya zeenatu ya akayi?”

“Uhm tunda kika samu part kike zuba fantamawarki banganki ba,zan turo miki address kizo zamuyi tattaunawa gameda aikinda kikemin”

Tana sauƙar da wayar taga address ɗin gidan Hajiya rabi,dariya tayi tareda nufar gidan dasu innayi suke..

Sharp sharp ta sanja kayanta zuwa wasu masu mungun kyau a cikin waɗanda ta siya,A wajen Hilyaan tabar haidar ta nufi gidan,domin zai bata mata budget idan ta tafi dashi.

Riga da wando ne kayan na sai farin kimono data ɗora akai,bakin farin glass tasaka tsanrparent mutun ba ganin blue iris ɗinta,bakin takalmi tasaka hight heel mai matuƙar tsini,sai jaka ƙarama mai adon fari da baƙi.

Gidan a cike yake da mutane kasancewar gobe ɗaurin aure,duk inda ta keta kallo ake binta dashi harta shiga falon Hajiya rabin,daga gani private falor don ba kowa a ciki sai su biyu..

Fararen kujerune a ciki kawai da TV da Fridge ƙarami.

Ko sallama.

Kafin tashigo ɗin da Jawaheer ta haɗu,wacce har yellow take saboda Gyaran data sha.

“Bride to be zan iya sanin inda iyayenki suke?”

“Ke kuma mai kike a gidannan yanzu,ko baƙin ciki kike zan zama matarsa ke kuma aikinki ya ƙare zakiyi waje?.

Samun gu naga har kuɗinsa kike ɗauka kina facaka dashi koh?”

“Ba wannan na tambayeki ba,tambaya nayi ina uwarki take,ta buƙaci ganina idan kuma har na zuwa to ba wanda ya isa yasani dawowa”

“Kut harke wacece dazaki dunga yin magana da mommy haka”

“Ishashshiya ce,wacce ta isa ita uwar taki wacece daba za’ayi magana da ita haka ba iyee ko uwatace kai”

Mari Jawaheer takaiwa Bombee,a tunanin ta ai gidansu ne babu abinda zata iya,tun kafin takai hannunta Bombee takifeta da nata marin saida ta hantsila.

Cikin ƙanƙanin Lokaci har shatun hannunta ya fito a fuskarta.

Duk abinda suke akan idon Hajiya rabi wacce fitowarta kenan jin hayaniyar Bombee da Jawaheer.

“Innalillahi yauni naga fitsararriyar yarinya,yanzu ƴar tawa kika sheƙawa wannan marin har cikin gidana?”

“Ko zaki rama mata ne kai,ina ruwana da ƴar taji toh,ki koya mata tarbiyya idan bakyaso ta sha wuya intazo sashena. Hadda tadaina shiga abinda bai shafeta ba zaki nuna mata”

“Shigo muna son magana dake,yau za’ayita ta ƙare ma”

Babu ko ɗar kuwa Bombee tabi bayan Hajiya rabi hankalin ta kwance,bayan ta watsawa Jawaheer kallo wacce take dafe da kuncinta masu aikinta sun tafi da ita.

Kujera ta nufa a falon ta zauna tareda ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.

Inda harara tana kisa da Bombee ta mutu sau ba adadi a wajen su Hajiya zeenah.

Tissue paper ta ɗauka a gefen kujerar ta goge hannunta tareda cewa.

“Mtsww waccar ƴar taki ta ahafamin wannan yellown abun a hannuna,daga ji ma ƙarni yake,wai a hakan kuma za’a kaita wajen miji,ohhh Jabeer kaga taikanka kaikam”

“To nunamin Kinibibi irin naku na ƴan bariki,kinaso kice ba’a kyautamasa ba komai,kinada wannan huruminne a matsayinki na bare”

“Banida shida mai ɗa,dadinta dai nima inada ɗan ba juya bace,sai kiyiwa matar ɗanki wannan maganar baniba.

Back to business meyasa kuka kirani wajenanan,inda abinyi na kasheshi in bakuda tacewa zanyi gaba”

“Batun contract ɗin da nayi dake sauran wata ɗaya da satuka ya ƙare,inaso ki gaggauta fitarda Lubnah daga cikin gidan ɗana kafin Jawaheer ta dawo daga honeymoon,daga nan kuma kema na sallameki ki tafi kamar yanda mukayi”

“Idan naƙi yin hakan kuma fah”

“Zaki dawomin da ƙudaɗena a yanzunnan ki tafi nafasa aikin”

“Hhhhhh Hajiya zeenah kenan,kin manta na maida contract ɗinmu shekara guda,kuma kin yadda da hakan,sannan kuma a shirin mu babu zancen janyewa daga gareki.

Mai kika maidani bansan mai nake ba?”

“Kinyi kusan wata biyar a gidana,amma har yanzu babu wani yunƙuri dakikayi akan Lubnah,kina nufin kicemin bazaki tafiba ne komai,wai tukunna ma mai kike shiryawa wanda ban saniba.”

“Dama to menene abuna da kik sani bayan labarin da Umaruje ya faɗamiki,kuma nina sakashi faɗamuku labarin,ba ra’ayin kansa bane,da ban sakashi ba babu abinda zaku sani gameda ni.

Hajiya ta wani gun bake kaɗai kika nemeni ba,nima na nemeki dana gane mai kikeso namiki,dan haka maganar tafiyata bata hannunki tana hannuna.”

“Baki isa ba toh,yau innaga dama zansa ya sakeki”

“Nikuma na saceshi na sace amaren ma,ke harkema na daukeki na kaiki dajin dakika ratsa kika shiga inda nake,inna ɗaureki ko ihu bazaki iya sakewa ba harki mutu.

Saiki zaba,nina tafi saina jiki sweet in law ta”

Maida glass ɗinta tayi tana murmushi tabarsu a zaune Sukuti kaman gumakai.

Page 🖤37••38🖤

Washagarin ranar Asabar aka ɗaura auren Aliyu Abdullahi da kuma Jawaheer Adulmumin & JALEELAH UMAR.
kan sadaki ko waccensu dubu hamsin hamsin.
Gabaɗaya gidaje biyun babu masakar tsinke na mutane.
Lokacin da iyayen Jaleelah sukaji cewar mata biyu za’a auramasa Lokaci guda ƙin amincewa sukayi,bayan sun san yanada wasu biyun dama.
Saidai abune da anriga an yi nisa,an ɗaura aure alƙalamin ya bushe,saidai muyi musu fatan zama lafiya kawai.
Duk da cewar Jabeer ya yage kan cewar bazayyi evrnt ba,amma Hajiya zeenah ta haɗa masa walima na uwa a harabar gidansu,wanda dukkka matansa zasu halatta idan ankawo su da yamma.

Maleekah ce tashigo sashen Bombee taci kwalliyah,ƙannen ango ba zama,ƙaramin akwatine a hannunta,tundaga bakin falon take zuba sallama,Bombee najinta bata kulataba,sai Hilyaan ce ta amsa mata wacce take zaune a kujera.
“Uwargida sarautar mata,munzo dannar ƙirji fah,dafatan dai bakya suma ana zuba miki ruwa,kishiyoyi biyu lokaci guda”
“Mai ya kawoki keda kike tsaka da hidima?”
“Uhm kayan dazaki saka a walima na kawo miki,na bawa Lubnah nata ma,amma fah da alama mommah bataso baki kayanba,dan kamar karta bayar tayi,anty maryam wata ƴar tsamar kukayi ne”
“Wannan tsakanina ne da ita bai shafeki ba kinji,yanzu dai mayar mata kayanta,dan ba wani biki dazanje”
“Habaaaa anty maryam,ni wlh duk cikinsu ke ma nakeso na gani a wajen,dan allah kizo kowa na tambayan ina matar yah Jabeer ta biyu,kubiyu tunda aka fara biki baku fita daga sashenku ba,kowa na cewa baƙin ciki kuke,tunda har anty Lubnah tace zataje dan Allah kema kizo”
“Hmmm to naji uwar surutu naga kina shirin fita ina zuwa,ko matan yayannaki zaki ɗakko daga ɗaurin aure uhm?”
“Ahh habadai,zamuje ɗakko yah Abdulkareem ne a Airport,shi yah Abdulmaleek jiya ya dawo da daddare.
Lahh ashe ma anty maryam baki san Brothers ɗina ba,karki damu ai sun dawo kenan,Abbah ne yace lallai su dawo ƙasarsu suyi aiki,zan kawo miki su ku gaisa sosai.”
“Bayan surutu wasu zaki gayyato min sashena kuma,to karma ki fara,maza shige kije zanzo taron”
Juyawa tayi wajen Hilyaan wacce takeyin game a waya,Inayah kuwa bacci take akan kujera..
Yau yini suka zo mata dukkansu,innayi tana bacci itada inna Danejo a ɗaki.

Haba big bros daga ɗaurin aure zai tafiya wajen amarya,ba zaka tsaya Dr.AK (Abdulkareem)ya dawo ku gaisa ba,rabonsa da gida fahi think 7 to 8 month,tun mutuwar sis hafsa koh?”
“Kake zancen rabonsa da gida ya dade,kaima ka dade ai vaka nan,daga Cewa Ka tafi yin wata 3 kaine kusan wata 6,ai abba yayimin daidai daya dawo daku dukka gida,bama ya wancan likitan bansan ya zayyi ba da zaman ƙasarnan yanzu”
“Hmmm ka barsu kawai Khaleel,duk yanda zasuyi ma zasuyine,daɗi sukeji ai su tafi sai sanda sukaga dama su dawo,sun girma har yanzu babu mai zancen aure a cikinsu.
Nikuwa ganinan kawai na buɗi ido na ganni da mata huɗu,kaman ana zamanin Era”
Dariyah Khaleel yakece da ita shida A.M(Abdulmaleek),wanda hakan yasake ƙular da Jabeer har wuyah.
“Haba big bro ka kamanta ratar dake tsakaninmu dakai da yawane,ga wanda zakayiwa nan abokinka ai,shine babban tujuru,ni barina fita Little sis na jirana zamu ɗakko wancan likitan a filin jirgi.
Favorite ɗin Mommah kenan,tun ɗazu take maganar ya iso kuwa?”
“Tunda kuka shigo duniyar nikam dama na zama bango ai mai daɗin jingina”
Jabeer ya faɗa yana sake gyara zaman hularsa.
“Kuma fah JJ Gaskiya A.M yafaɗa,kai kayi huɗu ni banida ko ɗaya,watan gaba zan turo ayi maganar mu da Madeenah dai inaga”
“Hmmm zo mu fara bi takan waccar kafin mu shige wajen Jaleelah”

Harabar da aka gyara domin walimar ba ƙaramin ƙawatuwa yayi ba sosai.
Da ko ina haske wajen yake dukkuwa da cewar yamma ce da rana a sama.
Wajen zaman amare da ango kujeru biyar ne,ta ango daban sai biyu a kowanne bangarensa. An ƙwatasu matuƙa,kuɗi kam in yana magana daya koka..
Gaba ɗaya wajen shigar kala biyu akayi,maza Blue shaddah,mata kuma yadi ne mai tsadar gaske pink.
Da mutane suka fara taruwa sai combination ɗin yadace da decoration na wajen.
Amaryah Jawaheer aka fara Rakowa itada tawagarta ta tsayah a bakin wajen,sannan sai Jaleelah wacce itama ta tsayah a ɗaya bnagaren.
Jabeer ne a tsakiyar su a filin.
Shadda ce a jikinsa kaman ta sauran mazan,saidai kunsan Shigar ango dole zata fita daban da saura..
Suma ga amaren haka take,yadine a jikinsu pink iri ɗaya,saidai anyi masa ado da blue a jiki. Sai mayafin dayake kansu shima blue mai adon roses pink.
Dukkansu sun haɗu babu da yasarwa.
Mc ne yafara magana ganin bayyanar wanda aka kafa taron dominsu.
“To mashaallah amare da ango su bayyana a wannan fili,yanzu zamu buƙaci suje ga wajen zama,saidai zamu buƙaci ango ya riƙe hannun matayennasa yayi musu jagora”
Idonsa yakai kan Jaleelah wacce take kallonsa da cute fuakarta ta cikin mayafinta mai shara shara wacce tasha kwalliyah,murmushi tayi tareda zura hannayenta a cikin nasa,karon farko kenan dayaji tattausan hannunta a cikin nata,nan da nan kuwa yayi ji wata ni’imah tana jiyartar jikinsa.
A ɗaya bangarenma wani hannun yaji yaciga cikin hannun nasa,lallausa kuma mai dauke da hutu.
Juyawa yayi bnagaren itama Jawaheer,wacce ta saka nata idanuwan dara dara a cikin nasa.
A lokaci guda ya runtse hannyen dukka,tareda fara tafiyah suna binsa a hankali har sukayi masauƙi a wajen.
Su Hajiya zeenah wanda suka kallon show ɗin sai murmushi suke,duk da taciki na ciki,dan iyah Jawaheer suka so gani dashi bada Jaleelah ba.

Basu daɗe da zama ba itama Lubnah tashigo filin da nata kayan irinna su Jawaheer,saidai babu mayafin fuskar irinna amaren.
Bayan zaman an shafe kusan minti goma ana jiran zuwan Bombee,mutane har sun fara magana ƙasa ƙasa,don dama kowa labarinta yakeji bai santa ba. Wai amaryar data kawo kanta gidan miji da safe,koya take oho ba wanda yasani.
Takun takalminta suka jiyo ta shigo wajen,daga yanda suka jiyo takalmin mutum zai san kayane a jikinsa haɗaɗɗe mai ɗaukar rai.
Saidai sabanin haka sai ta bawa mutanen wajen mamaki,Hijabi ne a jikinta pink har ƙasa,sai nikaf ɗin data saka blue,hakama mata biyun da suke binta baya,suma iri ɗayane kayannsu da nata,saidai su nasu nikaf ɗin babu ado a jiki irinnata.
Cike da izzah take bada sautin takalmin dake ƙafarta,bayan tasha baƙar safa ta hannu data ƙafa.
Saida suka rakata ta zauna kafin suma suka zauna a wasu kujeru dake wajen zaman sauran mutane.
Tun daga shigowarsu har zuwa zamansu wajen tsitt yayi baka jin bakin kowa,saboda shigar tasu tabawa kowa mamaki sosai.
Banda Jabeer wanda suka haɗa ido ta Bombee ya Jijjiga kai yayi dariyah,dan a iyah saninta yayi na zamansa yasan zatayi yafi hakan ma.
Kuma da alama badan jan hankalin mutane tayi ba,saidan batayi niyyar nuna fuskarta bane ga mutane saboda wani dalili nata.
Abdulmaleek ne yakalli Khaleel tareda cewa.
“Wannan wacce ta shigo yanzu da wasu mata da hijabi itace matar big bro ta biyun?”
“Uhm da alama itace,danni ma bansanta ba”
“Baka santa ba kamar yah,kana garin baka santa ba kuma,taya haka zayyi wu?”
“Haba Abdulmaleek tunda yace maka bai santa ba da alama batason nuna fuskarta ga mutanene,tunda shi ya santa ai shikenan”
“Kai habadai Abdulkareem,duk da rashin son jan maganarka wannan abin jane,zan samu little sis muyi maganar,inason nasan wacece”
“Sai kace dole?”
“Eh dolene kuma kabar wannan zancen,kaima dole dakai zamuje ka ganta taganka”
Ganin Abdulmaleek yasamu maganar sai ja yake,yasa Abdulkareem yin shuru,yayinda a bangare ɗaya kuma Khaleel yake tayimusu dariyah.
Haka aka gama taron kowa ya watse,bakin mutane ɗauke da maganar matar Jabeer da biyu da irin shigar da tayi.

Ba wuce da amaren sashensu ba,wajen Hajiya zeenah aka kaisu,anan zasu zauna kafin gobe su wuce honeymoon.
Itakuwa Bombee da Maleekah suka taho,sai mita take akan meyasa suka saka nikaf.
Kallonta Bombee tayi bayan ta yage nikaf ɗin ta jefar,dan dama duk ya isheta abinka da rashin sabo.
“Wai nikam Maleekah yaushe zaki dunga ɗago abinda yake da ma’anane,kina ganin aikinmu zai tafi daidai idan na bayyana fuskata..
Kaff cikin garin abuja nemana ake ruwa a jallo,ga kuma plan ɗin danake na ceton wannan companyn naku,sannan kuma kinga Hajiya zeenah ma zataji daɗi ganin ban nuna fuskata ba,duk da nasan abube mawuyaci tacigaba dayin moving ɗinta akaina yanzu.
Kinga ni bikinku fah bai dameni ba yanzu ma jinake kaman akan ƙaya nake sabida zafin kayan jikina,bariga na yage su na huta”.
“Um nace ba anty maryam kafin ki shiga ɗaki,kinga ƙannennaki kuwa su ya Abdul?”
“Eh nagansu mana,ina masu kama dake su biyu,mai zanmusu to daga ganinnansu”
“Ahh babu anty maryam,allah ya barmana ke”
Daga haka maleekah ta zauna suka cigaba da surutu dasu Hilyan.

Tunda suka dawo daga wajen dinner bayan sunje masallaci suka nufi sashen mahaifiyar tasu,abdulkareem ne ya zauna a one seater,yayinda shikuma Abdulmaleek ke zaune a kujerar da madeena take,danne danne take a waya hankalinta kwance,saidai da alama da saurayinta take,dan yanda take jefa murmushi akan fuskarta jefi jefi.
“Ke wato hira kike da chatting koh,wanene”
“Kai yah abdul,yah khaleel ne fah kawai,shima kuma yana tambaya ta abune”
“Ba waninan naga kina murmushi ai,ku yaran yanzu kun baci da hira”
“Kai A.M,menene bacin aciki,yanzu duk wannan ace bazatayi hira ba,to mai zatayi kenan uhm”
“Eh to naji,ke maganace dama a kan matar big bro,meyasa ta rufe fuskarta ne a wajen taron can,kyaune da ita da bata son a ganta sosai,ko kuma big bro ne yake kiahinta da yawa kai”
“Wlh yah Abdul bansani ba,dam nni ma ganina da ita uku ne inaga,saidai ka tambayi mutuniyarka itace mai yini a sashenta”
“Yess yawwa bari my girl tashigo nasan zanji komai daga wajenta ai,dama ku biyunnan ba’a samun abin arziƙi daga wajenku ai”
“Hmm kaika fiye surutu kai……”
Yana cikin magaanr ne Hajiyah Zeenah ta shigo sashennata.
“Ahh ku kuma anan kuke zaune,duk rashin son mutanene ko mai,amma shikuma wannan fah dannsan ba rashin son mutanene ya zaunarshi a falona ba kam”
Taƙarisa magana tana kallon Abdulmaleek ɗauke da murmushi akan fuakarta.
“Hmmm mommah wai nan ɗin jira yakeyi fah yaji labarin matar bro da tarufe fuska”
Lokaci ɗaya Hajiyah Zeenah ta tamke fuska da taji mai abdulkareem yace.
“Mai zayyi mata idan yaga wacece,nifah banason shiga sharri ba shanu tam.
Kuyi harkar gabanku,karma ku damu da saninta tamm”
Daga jin yanda ta kausasa murya akan ta mutum zai gane basonta take ba,dan gashinan a cikin muryar a fili.
Duk falon shuru sukayi da zancen bombee suka kama wani sabo.
Da daddare misalin ƙarfe tara,bombee na zaune tana shan tea taga ƙiran Jabeer a wayarta.
da kaman bazata ɗaga ba saikuma ta ɗauka,batayi magana ba dan haka shine yayi daga ɗaya bangaren.
“Kisameni a falona akwai abinda zan faɗa muku”
Daga haka ya kashe wayar,cigaba da kurbar shayinta tayi a hankali saida ta gama kafin ta miƙe ta shiga ɗaki,nan ma ta daɗe kafin ta fito,wandone 3-quater a jikinta sai t-shirt,dukka kayan baƙaƙe,bata saka ɗan kwali akan ta ba iya ribbon ne kawai,ƙafarta kuma ɗauke da slippers.
Tun lokacin daya ƙira bombee ya ƙira sauran,har suka shirya suka fito ita bata taho,in anjima lubnah da Jawaheer su ja tsaki,itakam Jaleelah dama bata santa ba.
Ƙarar buɗe sashenta sukaji,a tare suka kalli inda zata shigo harda uban gayyar wanda yake zaune a Three seater,lubnah na gefensa sai Jawaheer Jaleelah a ɗaya bangaren,dan sune suka fara shigowa,itama Jawaheer saida tayi nata sarautar kafin tazo.
Tun ɗazu take hararar su Jaleelah da suke gefen Jabeer a zaune.
Ƙarar slippers ɗinta ne yacika falon,hannunta a cikin wandon ta.
A gaban Jabeer ta tsayah tareda ware masa hannu.
Shuru yayi yana kallonta dan baisan mai take nufi ba.
“Common beb give me a hug”
Tashi yayi tareda bin umarninta ya rungumeta kaman yanda ta buƙata,bakin sa yakai kusan kunnenta tareda cewa.
“Meyasa bakyayimin abu sai kinga idon wasu uhm”
“Ko bakasone to sakeni”
“Ahah ina zanƙi wannan jikin mai cikeda taushi da kuma ɗumi,inzan dawwama a haka bazan gaji ba,saidai tsiyar inna fita hankalina babu daman a taimakeni saidai a tafi a barni,a kawomin dalilin dazaisa na haƙura,amma bakomai zai kawo ƙarshen wannan dalilin”
“Sakeni haka ya isheka”
Tafaɗa tana zame jikinta daga nasa,komawa yayi ya zauna yana yi mata dariyar gefen baki,yayinda ta bishi da harara abinda ya faɗa.
Kallon Jaleelah tayi wacce take gefensa a zaune tace.
“Gimbiya tashi ki koma waccar mai ɗaya ki zauna koh?”
“Kallon mai kike cewa tayiwa bombee tareda mai da idonta ga Jabeer domin taji mai zaice”
Shuru yayi yarasa mai zaice,shin Jaleelah dake gefensa zai tasa bombee ta zauna ko kuma bombee zaice takoma kujerar gefe,wanda yasan da tayi hakan ya tabbatar saidai ta bar falon.
“Ohh kallonsa kike saboda kinsan yana sonki bazaice ki tashi ba ƴan mata?,to barikiji wani abu,idan abu mallakina ne ko kuma matsayina,ko bana sonsa a raina babu wanda ya isa yazo yamin shigar kai tsaye ya mallaka,idan takama komai zan iya miƙawa domin mallakarsa,dan haka tashi ki koma inda ɗaya amaryar take ki bani wajena tun kafin raina ya baci”
Jabeer ne ya buɗi baki tareda cewa.
“Jaleelah tashi ki koma wajen Jawaheer ki zauna kinji,nan ba wajenki bane wajen tane a ƙa’ida”
“Ni banga abin tashin hankali a wajen zama ba,umarninka shine abin bina,tunda ka buƙaci na bata wajen babu matsala”
Cikin sanyin jiki ta tashi a wajen takoma kusada Jawaheer.
Murmushin jin daɗin yanda ta karbi maganarsa yayi,dan dama hakan yakeso.
Jawabi ya fara ma su na zaman lafiya,inda ya zartar zai dunga yin kwana ɗaya a ɗakin kowacce daga ya dawo a tafiyar dazasuyi.
Sannan ya sanar dasu wata ɗaya zayyi ya dawo.
Bayan yagama jawabin babu wanda ta yi magana,hakan na nuna sun yarda da hakan kenan.
Daga nan kowa yakama hanyar sashensa sai goben.kowa fuska a murtuƙe,musamman ma lubnah da Jawaheer.
Washagari da safe aka shirya tafiyar su Jaleelah honeymoon tareda Jawaheer Duk da saida akayi dambarwa da Jawaheer akan tafiyarsu da wata matarsa.
Tunda safe ƴan aikinta suka fara ƙoƙarin shiryata,wanda wannan ne kwananta ɗaya a sashennata.
Yasha ado kam na alatun duniya na gani na faɗa,duk side din babu sashen dayakai nata kyau saboda bajintar da hajiya rabi ta nuna a barin dukiya a bikin ƴar tata.
Ruwan wanka masu aiki suka haɗa mata,su uku ne hajiya rabi ta haɗata dasu.
Kafinta fito sun shirya mata breakfast da kuma kayan sakawa,ta haɗe rai tashirya ta fito zuwa sashen Hajiyah Zeenah inda zasuyi mata sallama su tafi.
Tashiga falon kenan hajiya Zeenah tafito daga ɗakinta,Jaleelah kuma na zaune a kujera tana jiran Hajiya.
Tana fitowa kallo ɗaya ta wurgawa Jaleelah daga nan kuma tanufi Jawaheer tana ware mata hannu,rungumeta tayi tamkar ba surukarta ba,
“Yakk Daughter kintashi lfy”
“Yeah kalau natashi,yah Jabeer ɗin ya fito kuwa”
“Ahah baizo ba inaga yana sashen sa tukunna”
Madeenah ce tashigo falon ,bata kalli Jawaheer ba wacce suke magana da Hajiyah Zeenah,wajen Jaleelah ta nufa wacce ke zaune tamkar gunki.
“Anty Jaleelah ya kwanan baƙunta,ko zakizo muje ciki kai kafin yah Jabeer ɗin yazo?”
“Lfy kalau Madeenah,uhm to shikenan babu matsala hakan”
“Ke Madeenah baki ganin Jawaheer ne wacce a yanzu take matsayin matar yayanki,bazaki gaisheta ba”
“Uhm mommah wannan ma ai matar yayannawa ce,inaga ai babu banbanci duk wacce na kulama a ciki ɗayane”
Taƙarisa maganar tana bankawa Jawaheer harara,dan dama basa ga maciji da ita,haka lubnah ma,bombee kuwa basu taba haɗuwa ba face to face,shiyasa ta zabi Jaleelah a matsayin favorite ɗinta,yayinda iyakuma maleekah duk cikin amaren babu wacce tayi mata,tana jin ana zancen tafiyar ma bata fito ba,sai anjima tayi sashen Bombee acan zata yini.

Hannunsa ya saƙala ta bayanta zuwa cikinta,tana tsaye a jikin table na dining tana gogewa.
“Nizan tafi yawon cin amarci ta amarena”
“Na riƙeka dama,nace kada katafi?”
Sake kwantar da kansa yasakeyi a gadon bayanta tareda yin magana,wanda hakan yakasata ajiye duster taja gwauron numfashi.
“Mr.groom wannan salon kuma namenene,ko so kake na fola maka na hanaka tafiya,shiyasa kakeyin haka”
“Bahaka bane zanyi missing ɗinki ne”
“Hhhhhh missing shin kana tunanin yakamata kayi amfani da wannan kalmar,dan Allah kaje tafiyarka suna jiranka,inna gama aikin gidannan inada abinyi sosai”
“Wai kina nufin bazakiyi kewata ba,bazakiji babu daɗi ba idan natafi?”
“Saboda kai iska ce ko ruwa,da babu su babu rayuwa,babu ɗaya ƙanwar biyu,barina je ana ƙirana a waya,Allah ya bada sa’ar shaƙatawa”
Daga haka tacire jikinta daga nasa tayi ɗakinta,ta barshi a wajen yana kallon hanyar data bi,haka kawai ya tsinci kansa da jin rashin daɗin tafiyar da zayyi ya barta,jiyake inama tace zataje su tafi,yasan hakan bazai taba yiyuwa ba.

Kasancewar private jet ne yasa kawai tafiya ce babu wani tsaiko a ciki.
Dubai suka nufah,inada Jaleelah ta zaba,taganan zasu nufi singapore inda itakuma Jawaheer takeso.
Jaleelah ce ta kalli Jawaheer a cikin jirgin tareda yimata magana,ganin Jabeer ya shiga banɗaki.
“Uhm nikuwa kaman kece Cat lady bah?”
Zaro ido Jawaheer tayi tareda ƙwaruwa a abinda ta zuqa,waiwayawa tayi ganin babu kowa ya kusa kafin tace.
“How on earth kika sani?”
“Lahh ba wani abin damuwa bane,naga baki daɗe da buɗe acct ɗin bama”
“Shine nace taya kika san nice cat lady a ciki,bayan bamu taba haɗuwa dake ba bare muyi wannan maganar,saidai idan kema…….”
“Ehh haka ne nima,Kinsanni a wajen saboda baki san nice bane,zan faɗamiki user ɗina saboda wani dalili.
Nice black slender a wajen,hannunta ta buɗe ta nunawa Jawaheer wani tatoo a hannunta na hagun.
Zaro idon da Jawaheer tayi a yanzu har yafi na ɗazu ma.
“Kina nufin kice dama kece wannan babbar…….”
Bata gama maganar ba Jabeer yadawo,dan haka suka sanja topic ta hanyar magana akan wani abun taban.

Page 🖤 39••40🖤

“Banjinki sosai Inayah Ki ɗaga murya kaɗan”
“Ai babu dama ne anty maryam,wani abu muhimmi nakeson faɗamiki yanzu,wanda na tabbatar yakamata ki sani”
“Menene ina jinki”
“Uhm ɗazu naji brr na’ima tana wani surkulle a ɗaki,magana suke da wata mata,bayan kuma batayi baƙuwa na,sannan maganar batayi kama da ta waya ba sam.
“””Karki damu yake Komai bai bar hannuna yana ƙarƙashin ikona,tun kafin ta kasance a cikin komar ki ni tashiga tawa tun bata faɗo duniya ba,ita ɗin kyauta ce a gareni,kuma gidan aljanuna,dolene na maidata sai abinda na sakata,kokuma na ɗaiɗaita rayuwarta.
Inta kusada ita,kusa mafi kusanci saidai batada masaniyar hakan,su kansu sauran na san inda suke ta sanadiyyarta,ina jiran lokacine wanda zan aiwatar da ƙudirina akansu.
Ƴar kima kada ki damu,duk da bazata san nice ba,amma zan kulada ita fiyeda yanda kike sani,kedai kicigaba da abinda na muka umarceki dashi””””
“To haka matar naji tace”
“Iya haka kikaji,okay ba matsala kinyi koƙari,amma kisake kulawa fah kada su gane,yawwa kin taba shiga ɗakinta?”
“Ehh ina shiga sosai kaimata shayi”
“Madubi nawa ne a ɗakin nata?”
“Eh biyune,ɗaya yanada dreesing mirror da kayan shafe shafe,ɗaya kuma a tsaye yake an rufeshi da wani baƙin ƙyalle”
“Ohk na fahimta,naji abinda nakeson ji,sai an anjima”
Tana ajiye wayar rest room tashiga inda allon plan ɗinta yake,zana inna lari tayi da Brr na’imah sai tayi link ɗinsu da Zilliyyah.
‘Okay inna fahimta daidai zancen da take na nice da kuma ahalina,wato bayan barinsu gyembu sun bata mata shirinta,hakanne yasa ta biyosu nan.
Tace tana kusa dani,amma duk shu’umancinta bazata iya bacewa ba ai,kuma tace tana kusa ba wai tasaka a ganni ba.
Duk yadda akayi tana cikin gidanann kenan kuma tayi badda kama’
Har tazo ajiye marker dake hannunta sai ta tsayah,tsohuwar dake musu aiki a sashen ta tuna,lokacin data tunkareta taji nauyin dayake kanta yana komawa ƙeyarta,data juya kuma taji yana komawa goshinta,maganar datakeji a kanta kuma a lokacin ta tsaya ɗiff.
Kenan aljanun dasuke kanta tsoron tsohuwar suka,kuma dama bata yarda da ita ba sam.
Ayar tambaya tasaka a sunan tareda yin murmushin samun nasara.
“Idan kuwa kece to lallai kinkawo kanki ramin kura……hahahaha”

*** ***

Tun lokacin da Jawaheer tagane wacece Jaleela,shikenan suka ɗinke,babu zancen faɗa kuma,koyaushe tareda suke komai,sai dare yayi kowa ta tafi ɗakinta,wacce Jabeer ke wajenta ya shiga.
Tun zuwansu a ranar ya aiwatar da ibadar aure shida Jaleelah,duk da cewa yanda yake tunanin zaiji bahaka yaji ba,amma kuma yasan babu wata matsala,dama kowacce mace da kalar ta.
A bangaren Jawaheer kam washagari a buɗe yasameta,duk sai bayyi wani mamaki sosai ba,dan biri yayi kamada mutum.
Da safe kyauta yayi musu mai tsoka,yaso yabawa Jaleelah wanda yafi yawa,saidai kuma yana tsoro kada yayi ba daidai ba.
Dan haka yabasu iri ɗaya,saidai a wajen mu’amala kam yafi nunawa Jaleelah kulawa fiyeda Jawaheer,ga mamakinsa in suna tareda yake yiwa Jaleelah maganar soyayya bata damuwa sosai,yawanci idonta baya kansa yana kan Jaleelah,domin taga wane reaction zata bayar gameda maganar tasa,tana mayar masa martani kuwa zata ɗebi fushi tayi gaba fuuu.
In hakan yafaru haƙuri Jaleelah take bashi,kana daga bisani tabi bayan Jawaheer ɗin,akan zata bata hakuri,ko kuma wani lokacin suje tare.
Shi har yawon ma ya isheshi,ga bombee ko sau ɗari zai ƙira numberta bata ɗagawa,yayi ƙiran watan har ya gaji ya haƙura,ji yake kaman yayi tsuntsuwa ya tafi ya barsu,wani bangare na zuciyarsa kuma yana son zama da Jaleelah a nan ɗin,maybe Jawaheer ce ta bata masa budget. Domin Allah yaga haƙuri yake na nuna mata kulawa,ba kaman yanda zuciyarsa take so.
Watansu guda a dubai suka nufo Singapore,a nan kam barsu yayi ya tafi wani uzurinsa,akan sai bayan sati biyu zai dawo,su suka cigaba da yawon buɗe idonsu tare.

*** ***
“Haba Mommy har yanzu baki ƙarisa bani ɗaya mahaɗin maganin ba,wani satin fah Jabeer zai dawo,nagama shirin yanda zanyi yakwana a wajena idan baki bani abin yanzu ba taya zan gama shirin to”
“Kaii Dear kinada ɗaga min hankali,baki ganin kullum busy nakene,ga Shari’ah sun sha min kai,ga shi wancan shashashan ɗan unnawaki,tunda suka dawo ƙasar jiya ya shiga sashensa banganshi ba..
Shi a dole matarsa tanada ciki,motsi kaɗan ya dubata motsi kaɗan ya dubata,ni ina tunanin anya ma kuwa ɗan cikinta nasane?”
“Meyasa kikace haka mommy,ko shima yanada irin matsalata bai sani ba kai?”
“Uhm da alama,amma bar wannan zancen ba yanzu ba zanyi maganinsu ne idan naga dama,baridai aikina ya kammala.
Yanzu mai kikayi shirin bayarwa kafin aikin yaci”
“Ohh sai an bada wani abu?”
“Ehh ƙwarai ma kuwa,mai zaki bayar a faɗama ta,kuma kada ki manta banda kuɗi fah,abinda kuɗi baya saya take karba”
“Uhm zan bada mahaifata tunda batada amfani”
“Bakiji nace miki mai amfani take karba ba?”
“Uhmm to nabada lafiya ta”
“Kutt bakida hankali ne wai,taya zakiyi ikon babu lafiyah?”
“Ahah ba iya haka ba,amma da sharaɗin idan bazasu karba ba har sai nayi wata ban haɗu da wanka nake mulka ba,in mutuwa kuma yayi babu zancen ɗaukar lafiyar,kinaga yayi?”
“Hmmm ina jiyewa dabbancinki,tunda kince haka shikenan,saiki kafa masa sharaɗi akan kada ya kuskura yayi wata guda baki ganshi ba”
“Ehh hakan yayi indai zan samu biyan buƙata”

*** ***

Tun safe take kulada shige da ficen Zaleeha a gidan.
Hasashenta kuwa ya fara tabbata,tabbas akwai abinda tsohuwar take kissimawa,ba Hajiyah Zeenah take yiwa aiki ba,aikin kanta takeyi kawai,tunda yanzu ai Jabeer baya nan,bai kamata tacigaba da saka ido ba.
Kokai itama Hajiyah Zeenah da hannunta aciki.
Ita kaɗai dai take saƙarta tana kuncewa,har lokacin dataga tafita daga side ɗinnasu ta tafi.
Kamar jira take kuwa da sauri tafito daga sashenta ta nufi ɗakin Zaleehan,dan dama shekaranjiya ta Copy key ɗinta data tafi banɗaki.
Buɗewa tayi tashiga ɗakin,tanajin cikin kanta ana bata umarni ta fita,amma tayi biris dasu tacigaba da bincikenta.
Su ƙoran maganine,kayin su macizai,hadda na jinjiri da gani,magunguna kam ba’a maganarsu su.
Idonta ne yakai kam madubin dake ɗakin,sak iri ɗaya dana ɗakin inna laari wanda tasani,saidai shi wannan maimakon adon yellow,da jini aka shafe gefe da gefensa,wato na ogah kenan.
Saida taƙare share tantamarta kafin ta fito daga ɗakin.

A filin harabar gidan ta zauna sunata waya da innayi,tanayi mata ƙorafin karatu da wuyah sosai.
“Kinga ni ba ƙorafin karatu na ƙira kiyimin ba,bayan ni da kuma hilyan akwai wacce ta taba zuwa gidannan?”
“Ehh…to banda almajirai dai,sai wata mata da ta taba zuwa wai a taimaka mata da ruwa,daga nan banga kowa yaxo ba,saidai bansani ba ko ina makaranta”
“To koma menene ki faɗawa sauran dukka su tabbatar baku sake barin wata baƙuwar fuska tashiga gidannan ba,kina jina koh?”
“Ehh naji addha maryam,uhm ki cewa maleekah lafiyah jiya naga ta dawo gida da wuri,bayan kuma tace sai yamma?”
“Cikinta ne ke ciwo,nan tazo ta kwantamin ai har yamman.
Kinji abinda na faɗamiki ku kula,idan nayi solving wani abuma dukka zaku dawo nan gabana,wajennan jikina bai bani akwai safe ba,kowanne lokaci komai na iya faruwa”
“Hakane kam amma addah ki dunga zaton alkhairi a kullum”
“Iyee wai kurace zatace da kare maye,don ruwa ya doki babban zakara koh? Duk ba uwarkice ta faro komai ba,yanzu gashi duk da ta haukace ban huta da warware abinda ta ƙulla ba”
“Kiyi haƙuri addah bombee dan Allah ”
“In banyi haƙuri na kashe kaina zanyi na barku da ita ta ɗaiɗata ku?,
Sai anjima ki kulada kanki da kuma inna,sannan ki maida hankali kiyi karatu kinji?”
“Uhm naji”
“Tamm”
Tana nan zaune har zaleeha ta shigo gidan ta ƙullin leda a hannunta.
Ƙwallamata ƙira tayi da ƙarfi,da sauri kuwa ta amsa tataho.
“Gani Hajiyah”
Wata yatsina bombee tayi,aranta tana cewa ƴar wasan kwaikwayo. Tasan dole tayi taka tsantsan,komai tayishi a iya cikin ranta kawai.
“Uhm nace ba jeki sharemin Wajen training ɗina ta baya,kiyi sauri kuma kafin magriba tayi”
“Hajiyah naji kince bazan yi aiki a sashenki ba”
“Dama ina ni nace,to yanzu kuma na sanja magana,na gaji dayin ayyukan gidan,hutu nakesonyi,dan haka kice ki sharemin yanzu,ko kuma kibar aiki a sashennan”
Ga hasashenta kuwa da sauri ta nufi wajen sharar kafin ta koreta,da alama komai zatayi indai baza’a koreta ba.
Kaman yanda bombee ta faɗamata kuwa sai wajen magriba ta gama sharar,lokacin ta tashi a wajen tashiga ciki,bakin ƙofar shiga falonta taje ta ƙwanƙwasa mata.
Buɗewa tayi tareda cewa.
“Har kin gama sharar?”
“Eh nagama hajiya”
“Ohk to jirani ina zuwa yanzunnan”
Bata daɗe da shigaba tafito da kwanon abinci a hannunta.
“Gashinan idan zaki ci,nayi yamin yawa”
Taƙarisa maganar tana miƙawa Zaleeha kwanon,tantamar karba tayi da farko,saidai daga ganin yanayin yanda bombee take mata tasan batasan ita wacece ba,dan haka ta tsugunna har ƙasa ta karbi kwanon ta tafi.
Sai bayan tabar wajen bombee tayi murmushi tareda cewa,
“Hmmm zakici bantan ubanki dani kike zancen,inkin fini da rarrafe aradu nikuwa saina fiki da tafiya”
Wayarta ta ɗakko da sauri ta bugawa wani ƙira.
“Hello khamees maza kazo yanzunnan,domin da daddare nakeson ayi komai a gama zuwa safiya,na tabbatar zata ci abincin”
Tunda zaleeha taci abincinta da bombee ta bata,bayan ta gama dubashi babu wani magani a ciki,dan in akwai dole zata gani ne.
Tunda taci abincin ta kwanta a wajen sai bacci,bata tashi sanin mai yake damunta ba saida ta bude ido ta ganta a asibiti.
Bombee ce a tsaye a window tana ta zuba tsuka da mita.
“Haba tsiyarka da tsoho kenan,daga sun kwanta kuma ba kanta”
Tarin da zaleeha tayine yasa ta juyo ta kalleta.
“Hajiya mai ya faru”
“Ohh shine tambayarki,jiya naje yimiki magana akan jagwalgwalon sharar dakikayi min na ganki a kwance numfashinki yana sama da ƙasa.
Likita yace kinsamu heart failure,wataƙila kinsaka abu a ranki ne.
Yanzu dai gashinan ya cire miki jinin daya taru a gefen ƙirjinki,ki duba zaki gani,ni zan tafi idan kin gama warkewa ki faɗawa likitan zan turo mota a ɗaukeki”
Tana gama maganar ta zari jakarta tayi waje,sai bayan ta fita ta tuncire da dariyah.
“Zilliyyah kinshigo hannuna finally,you are my ride to successed”
Ita kuwa zaleeha jugum tayi tana tunanin maganar da bombee ta faɗamata.
‘anya kuwa ba wani abu ta saka mata a abinci ba,to kuma ya akayi bataji komai ba,kuma in abu tasaka mata ta tabbatar na mutuwa zata saka mata,wanda kuma aljanunta bazasu bari taci ba,inaga to ciwonne da ita,gaskiya batasan ita wacece ba kam tunda har tayi mata magani’
Tana cikin wasiwasinne likitan ya shigo da magani a hannunsa da kuma plate na abinci.
“Iyah sannu ya jiki,ki dunga kulada lafiyarki sosai,banda takawoki da wuri da tuni abin yayi tsanani,yanzu dai zamu riƙeki nanda sati guda kafin ki tafi”
“Sati guda kuma likita,ahah bazan iya zama ba,jikina bayason wajennan,kabani maganin na tafi,zanyi amfani dashi yanda ya kamata”
Da farko yaƙi amincewa,amma ganin yanda ta damu yasa ya bata maganin tareda kafa mata sharaɗu na musamman.

Bombee kuwa a hanya tazo shiga motarta suka ci karo da wata likita,ɗagowa tayi zata fara magana,saikuma ta zare ido tareda cewa.
“Kuttt Rahama…..serious kece,yana ganki da farin kaya bayan na khaki?”
“Uhmm labari da yawa Captain maryam,tun bayan da aka miki wannan shunen komai ya rikice,Gen Muhammad yau da lafiya gobe babu,ƙarshe ma ya ajiye aikin,nima ganin haka yasa na tafi karatun likitar mata,yanzu haka nice babbar likita mai duba mata a asibitinnan,amma muje office mana ki sha ruwa Captain nasan akwai labarai da yawa koh”
“Da akwai kam amma ba lokacin bayar dasu,yanzu haka wai ina aure ne ma fah,amma dai ba standard ba”
“Aure captain ko a mafarki bantaba zato ba,nima ɗa guda ɗayane nake da shi,wa kike aure dan ina samun lokaci zanzo miki Shugaba shugaba”
“Hmmm da basai kinzo ba amma nasanki da naci,Jabeer Jaan nake aure,CEO na JAAN Company”
“Wow kin kama babban kifi captain,amma…..naji ance ya ƙara aure ai mata biyu koh?”
Kinga bari nayi gaba Rahama,da alama bayan Likitar harda jarida kika karanta”
Dariya ta sheqe da ita tareda cewa.
“Bazaki sanjaba Captain,to sai nazo zaki ganni”
Yau gidan da hidima aka tashi kowanne sashen,inka ɗauke na bombee,itace kawai babu abinda take na taryar angonnata.
Hajiyah Zeenah tanayi,Madeenah da kuma iyah sayyada sunayi a nasu sashen,domin sune mutanen Jaleelah,itakuma hajiya ta Jawaheer ce.
Sai shugaba lubnah wacce take shirin taryar mai gidannata da manufofi masu dama.
Maleekah ce a rest room tasaka head phone a kunne,duk ƙiran da Abdulmaleek yake yi mata bata jishi ba,saida ya jijjigata tukunna.
“Ke Dujal ɗin gidannan uwar san waƙoƙi,tashi muje ki rakani ɗakko big bro mana a airport.
Ke ana can ana shirin tarbarsu kina nan hankali kwance”
“Ahh to mai zanyi,wacce nake side ɗinta kona ce ta taryeshi ma bazata tareshi ba,amma kuma kada kasha mamaki duk welcom ɗinta sai yafi burgeka,shima nasan duk itace a ransa yanzu haka,burin sa ya haɗu da ita”
“Taya kika sani?”
“Bari kaga,idan mun dawo ka kulada ina zai fara zuwa,zaka ganewa idonka”
“Wai nikam har haka take kikeda confidence a kanta”
“Har yafima,kobaku yarda da maganata yanzu ba zaku yarda,am sure a rayuwa irinta yah Jabeer,anty maryam kaɗai yake buƙata tatsaya a gefensa”
“Hmm ke muje ni”
Su biyu suka tafi ɗakkosu daga filin jirgin,shikam Abdulkareem tunda ya dawo hutun sati guda yayi asibiti suka buƙaceshi ruwa a jallo,ba zama kenan.

Basu daɗe da isa ba jirginsu yayi landing,a tare suka fito su ukun kowacce tana gefensa guda,sukam sunyi fresh da kyau,amma uban gayyar kam ba hakan a tattare dashi sam.
Su ukune masu taryar tasu,kowacce ma anzo daga gidansu,babu ya Hajiyah rabi,kaman zata mutse dan murna,ganin yadda ƴar tata tayi fresh gwanim ban sha’awa.
Dukka Jaan estate aka nufah,gida ya cika kaman ana ƙaramin biki.
A cikin wanann taron Jabeer yasamu yazame ya nufi side ɗinsa,duk akan idon su maleekah wanda suka bishi a baya.
Bai shiga nasa sashensa ba sai ya buɗe na bombee.
Binsa sukayi a hankali suma,Abdulmaleek da ƙin shiga yayi,amma maleekah tajashi ƙarfi da yaji.
A zaune take akan kujera da waya a hannunta kamar kullum.
Taji buɗewar ƙofar,amma bata ɗago taga waye ba,duk da turarensa ma yabata amsa.
A yanda take zaunen ta yi magana.
“Ƴan yawan amarci kun dawo ne?”
A tsaye yake bai ƙarisa wajen ta ba.
“Can you drop your phone,sannan kuma ki tashi ki tsaya?”
Ɗago da idanuwanta tayi ta waresu akan sa,wanda sukayi tayi masa kizo a cikin watan dayayi batareda yagansu ba.
Tashi tayi kaman yanda yace,batareda tace komai ba.
Ƙarisawa yayi inda take tareda ƙanƙameta a jikinsa kaman zai maidata cikinsa.
“Uhmm i miss you koda ke baki yi tawa kewar ba,kin kyauta kuma da ƙin ɗaga wayata,ni zan shiga wanka,please ki samomin abinda zanci marar nauyi”
Yana gama faɗin hakan ya saketa tareda yi mata peck a goshi.
Haidar ya ɗaga sama wanda yake ta yawo a cikin falon akan keken tafiyarsa.
“Boy kai kayi missing ɗina koh,koda mommoynka batayi ba”
Ɗaki yashige da yaron a hannunsa yana yimasa magana kaman zai amsa masa.
Sai bayan ya shiga ciki kafin su maleekah suka bar sashen.
“To mai nace maka yah abdul uhm?”
“Ehh zancenki gaskiyane,duk cikinsu da alama ita yake yiwa son gaskiya batareda yasani ba,to amma wanann yaron kuma fah,shima naga ƙwayar idonnasa irin nata ne,inda itama idonta blue bane da saina ce anya kuwa ɗan ta ne?”
“Meyasa kace haka,ɗan tane mana dashi tazo fah,saidai ta harmata yimata tambaya akansa”

Bayan ya fito daga wankane ya kula ba haidar akan gado inda ya ajiyeshi,sai kayansa na shan iska kawai.
Murmushi yayi na jin daɗi,har saida haƙoransa suka fito.
Sakawa yayi tareda fita falon,batagama abincin ba da alama,dan yaji motsinta a kirchen.
Zama yayi akan kujera ya kunna tv yana kallo.
Tunda Lubnah taji shigowar Jabeer take zuba idon shigowarsa amma shuru har wajen yamma.
In ranta yayi dubu to ya baci,abincin data haɗa ta zuba a cikin dust bin,ga matsin datayi da magani tun safe sai damunta yake,kayan kwalliyar data saka ta yage ta zubar,tun tana kuka mai sauti har ta daina bacci ya ɗauketa a wajen.
Sai can duhun dare yafara taji alamun motsin mutum yana tashinta.
Ware idonta tayi akan Jabeer wanda yake tsugunne a gaban kujerar da take.
Kuka tasaka masa irinna kirsa tareda kaiwa hannunta kan fuskarsa.
“Kowa yarabani da mijina,sun rabani dakai gabaɗaya,tun safe na kasa zama saboda ɗokin dawowarka,amma ka kalli sanda na ganka saida daddare,yanzu na cancanci haka honey uhm?”
Sake fashewa tayi da wani kukan,wanda yaƙara saka jikinsa yin sanyi. Jawota yayi jikinsa yana rarrashinta.
Ta kuwa ƙara lafewa dan hakan takeso dama.
A sannu a hankali take jansa da kissa har kan gadonta,da farko yaƙi amincewa,sai kuma ya tuna da tsawon lokacin dayayi baya ɗakinta,duk da kuwa laifinta ne,amma yasan wani lokacin da nasa.
Salo take ta aika masa na buƙata,yayinda shikuma yake ta ƙoƙarin biye mata,duk da baya buƙatar hakan.
Buɗe baki yayi zayyi addu’ar ibadar aure,kafin ya furta wata kalmar tayi saurin haɗe bakinsa da nata waje ɗayah.
A haka naja musu ƙofa nima na datse alƙalamina akan wanann shafin.
Saikuma Allah ya kaimu na gaba……

Page 🖤 41••42🖤

Sanyin harshe taji yana bin fatar jikinta,tana farkawa taga Jabeer ne yake lasar ƙafarta tamkar kare.
Zabura tayi da zauna,da sauri ya matso inda take,jikinsa har rawa yake.
“Lubnah lafiya naga kin tashi a razane,mai yasameki ki faɗamin koma menene.
Na haɗa miki ruwan wanka da kuma abinci,kayan ki ma na zabomiki wanda zai yimiki daɗin sakawa yanzu,bayan haka kuma mai kikeso uhm”
Wani murmushin jin daɗi tayi tareda jawoshi jikinta.
“Finally ka dawo gareni bayan tsawon lokaci,wannan karon kazo kenan bazan taba bari ka koma garesu ba”
“Dama ba inda naje nina nakine ke kaɗai,yanzu ma idan kinaso saina sallamesu dukka”
“Ahah kabarsu su ɗanayimin bauta na ɗan lokaci,koya kace toh?”
“Duk yadda kikace haka za’ayi”
Cike da taƙama da farinciki lubnah tasaka Jabeer ya ɗauketa zuwa banɗaki,bayan sun fito yasaka mata kaya,yasake ɗaukarta zuwa dining.
Bayan sun gama cin abinci ma a falo suna zauna yana yimata tausa ta hakimce akan kujera.
Waya ta ɗauka taƙira Mahaifiyarta,tun kafin tace wani abu lubnah tafara magana.
“Mommyyyyy!!!! Aiki yaci fiyeda yanda kike zato,yanzu komai yana hannuna sai yanda nayi dashi mommy,wooww dama haka kikeji da kike mulkar abbah,gaskiya da daɗi.
“Eh da daɗi amma saikiyi taka tsantsan,kin tuna sharaɗin da kukayi da Matsafiya Zilliyyah kafin ta yarda da turomiki masuyin aikin koh.
Jinin kuliyar da kika basu shikaɗai bai isa ba,lafiyar ki na hannunsu,ƙaramin kuskure zakiyi shikenan komai zai lalace.”
“Nasani mommy i will take care,yanzu dai ya batun kuma shirin mu nagaba”
“Ahhh daga farawa,ki murji wanann lokacin da wannan damar tukunna,komai zaizo daga baya”
Ajiye wayar tayi ta kwanta Jabeer yacigaba dayimata tausa.

Kwana guda kwana biyu babu wanda yaga Jabeer ya fito daga ɗakin lubnah,tun abin baya damunsu har yazo kowa abin ya dameshi.
Babu ya hajiya Zeenah da kuma su Jaleelah.
Inda babu motarsa sai a yi zaton ya yi tafiyane,amma motarsa tana nan babu abinda yasameta.
Maleekah ce tashigo sashen bombee cikeda da damuwa.
“Anty maryam kema bakiga yah Jabeer ɗin ba”
“Naganshi mana,amma nima jiya na ganshi naje sashensa”
“Amma lafiyarsa kalau kuwa,mai yake a sashen anty lubnah to har yanzu,ga nan Mommah ta gagara haƙuri ta nufi sashennasa,yanzu ma tace na faɗamiki ku sameta a can ɗin,dan tun ɗazu take buga ƙofar ba’a buɗe ba”
“Ahh menene na abin damuwa kuma,mallakeshi akayi sannan aka hanashi fitowa,domin jiyan ma haɗuwa nayi dashi ya ɗauki takardun Companyn sa zaikai mata”
“Whattt……kuma hankalinki yake kwance anty maryam”
“Ohh tashi zayyi nawa hankalin,yaje ina?
Mallakarsa da tayi baya cikin plan ɗina,koyana ciki?”
Takaici ne ma ya ishi maleekah tarasa mai zatace.
“To yanzu anty maryam kina ganin menene mafita,dan Allah ki saka hannunki”
“Ehh akwai mafita idan naga dama,amma kafinni ku nema a wajen Allah,domin babu abinda yagagareshi”
Fita tayi daga falonta da nufi sashen lubnah,badan kiran da akayi mata ba sai dan tanason taga mai zai faru.

Kukan Hajiyah Zeenah suke jiyowa a falon tun kafin su ƙarisa.
Jaleelah da Jawaheer suna tsaye kaman gumakai,ita kuma sarauniyar tana zaune akan kujera ta ɗaro ƙafa ɗaya kan daya,Jabeer na tsugunne a gefenta,daga shi sai gajeran wando da kuma vest,kwana biyu yayi baƙi ya rame kaman bashi ba.
“Honey kace ma wannan tsohuwar ta bani waje na sha iska mana”
Tafaɗa tana nuna Hajiyah Zeenah,wacce take ta rubzar kuka.
“Uhm Mommah dan allah ki tashi ki tafi sashenki,na faɗamiki idan har na gama abinda nake zanzo na ganki in anjima,yanzu zafi takeji tana buƙatar iska”
“Wayyo Allah na ni Zeenatu,inda ranka zaka ga komai a wannan duniyar,mai zan gani,ɗana na cikina aka mayarmin shi kaman dabba?”
Bombee ce taja hannun maleekah wacce itama take kukan.
“Ke yanzu ba lokacin kuka bane,kija mahaifiyar ku ki fita da ita daga nan wajen ,in baso kike ku kwana yau a asibiti akan ta ba”
Ɗaga kai maleekah tayi tareda kama kafaɗar Hajiyah Zeenah, suka fita daga wajen.
“Yawwa ita waccar tsohuwar ta karbi nata lesson ɗin,shima ya karbi nasa nayimin bauta saboda auroku,sauran kuma kuma naku horon na shigomin gida da kukayi..
Bazan saka yasakeku ba,zanso ku baza ido ku kalli yanda zan zuba mulkina a gidannan,ku naku aikin shine bauta,ku tashi ku bani waje.
Idan anjima zan koma sashen honey da zama,ɗaya zata dunga yimin wanke wanke,ɗaya abinci,ɗaya kuma wanki.
Duk wacce taga bazatayi ba toga hanya nan zatayi waje a lokacin.
Ku bace ku bani waje.
Dukkansu su Jaleelah da Jawaheer barin falon sukayi,suna ganin yanda akayi da wanda suke zaune danshi,inaga kuma su karan kaɗa miyah.
Saidai kowaccensu da abinda yake ranta.
Bayan sun bar wajen saura bombee a tsaye kawai tana kallon Jabeer,wanda yagagara haɗa ido da ita,
Hannu tasaka a aljihun bujen wandonta,tareda jero feɗuwa mai ƙara.
“Weldone tun zuwana gidannan naga wani abu very interesting.
Karki damu kanki Lubnah da son taming ɗina da magani kokuma burga nayi miki abinda kikeso.
Ita kanta shugabar taku wato Zilliyyah,tun bansan kaina ba ta sakamin igiya a wuyah,saidai tana girma wuyannawa sai yayi kauri har ya ɗashe igiyar.
Kaman yanda nake faɗamiki har yanzu bakisan koni wacece ba,sannan mallakar shi wannan da kika baya cikin Plan ɗina.
Kicigaba da mulkinki a tsakanin matansa,ko babu magani a jikinsa ma bazai sameni ba bare yanada shi.
Inna gama aikin soon ma zan iya barin garin,dan haka kiyi harkar gabanki,batun abinci kuma da kike kallona na girka wai na girka miki,bazanyi ba,amma bansaniba komai magani kikeso na girka miki irin wanda ake yiwa beraye?”
Cigaba da feɗuwarta tayi zata fice,har tazo hanyar waje tasake dawowa.
“Amm lubbyyyy ki zama cikin shiri,wannan karon kinyi babban moving,wani karon Salon nawa ne,ƙwallota ce zata zura a raga,ki sha sha’aninki zan miki talala”

*** ***

Maleekah tana kuka tashiga sashen sayyada-tateen bayan ta raka Hajiyah Zeenah ɗakinta ta kwantar mata da hankali.
“Iyahh wlh wannan matar yah Jabeer ɗin bazata taba ganin rahama ba inshaallah”
“Wacce ina wannan mai ɗan shegen,dama menene da arziƙi a wajenta,matar da cimmana mutunci,nidama na fita harkarsu ne naga iya ina zasu tsaya”
“Kai iya ba wannan ba ni,waccar lubnah mana mai zubin kafirai,tun shakaranjiya ake neman Yah Jabeer ashe yana can sashenta ta maidashi kamar kare,banda aiki dare da rana babu abinda yake”
Saurin ajiye kofin kunun tsamiyar da take sha tayi,tareda zaro ido.
“Ke mekikace ƴar nan,mallaka tayi masa”
“Ai ƙazama ma iya sayyada”
“Muje ki kaini naga shi jabeerun,ko tofi ai sai ayimasa”
“Hmmm tofi koh,kina zuwa zata sakashi yayi waje dake,haka zai kalli tsabar idonki yace fitah!!!!”
Maleekah taƙarisa da ƙarfi cikin bacin rai,aikuwa sayyada-tateen tana jin haka idonta yayi ƙififi.
“Haka abin yazama,maxa ɗakkomin to mayafina ki rakani gidan malam Audu wali,nasan bazai rasa taimakon dazai bamu ba.
Yi sauri maza maza”
Jiki na rawa maleekah ta ɗakko mata mayafin suka shiga mota driver yajasu,har sannan bata daina jan majina ba.

*** ***
“Abban haneef wlh da gaske nake,yanzu nakeji a wajen mai aikina wai Lubnah ta mallake Jabeer,sai yanda tace yakeyi,hatta ƙofar gida bai isa fitowa ba saida izininta.
Koda wannen malami tayi aiki mai ƙarfin wannan oho?”
“Ohh kema kiji waye kiyimin koh?”
Alhj Abdullahi ya faɗa jikinsa a ɗan kware.
“Haba nayi maka irin wanann asirin,baka yarda dani ba haka?”
“Uhm da yarda nayi dake,kema ai sai a hankali”
“Yaushe kikaji wanann zancen ma tukunna”
“Yanzunnan aka faɗamin,wai Hajiyah Zeenah ma data je sashennnasa da kuka ta dawo.
Baka ganin yanzune lokacin dazamu sake ɗana wani plan ɗin?”
“Eh to hakane,amma dan yana ƙarƙashin ikonta bashi ke saka shikenan bazai ƙara zuwa aiki ba,dan aiki dole zaije aiki,saida abinda duk za’ayi a Company kuma sai abinda tace.
Keda kike cewa mu ɗana plan,kin manta hannun da muka haɗa da gen abdu manga,ni inaga shima akwai abinda yakeso,gashi ƙarin takaicin bansan inda takarduna suke ba,idan har aka gano basa hannuna,ko meeting fah bazanje ba kinsan”
“Karka damu za’a nemosu da kadan kaɗan a hankali.”
Bayan bombee ta koma ɗakinta runtse ido tayi tareda zama jagwab akan kujera.
Ita kadai tasan yarda zuciyarta take ganin halin da Jabeer yake ciki,waye zai hanata ɗaiɗaita iyalan gen abdu manga ne,sun gama cutarta da kowacce hanya,lokaci take jira dazasu girbi abinda suka shuka.
Tashi tayi kaman an jabureta tayi hanyar waje,ɗakin zaleeha ta nufah wacce ta dawo a daren jiyah,saida taje gidanta tayi magani kafin ta dawo..
Saida bombee ta kwanƙwasa bakin ƙofar kafin tazo ta buɗe mata,hadda fitowa da sauri kada taga mai yake ciki,murmushi bombee tayi batareda Zaleeha ta gani ba.
“Inkingama abinda kike,kizo yanzunnan ina jiranki a sashena”
“Hajiyah aiki ne?”
“Eh aikine babba ma kuwa,dan haka kiyi sauri”
“Yawwa Hajiyah nagode fah da asibitin dakika kaini”
“Karki fara min godiya tun yanzu,kizo ina jiranki a falo”
Komawa tayi tasake zama akan kujerar falon tana jiranta,dolene yau taji mai yake going gameda abinda sukayiwa Jabeer,da tace bazata shigaba amma kuma zuciyarta takasa barin abin ya wuce haka nan..
Idonta a rufe tashigo falon har ta samu waje ta tsugunna.
“Gani Hajiyah”
“Naganki,amma da farko zaifi kyau ki daina ƙirana da wannan Hajiyan,kinsanni wacece kuma nima nasan ke wacece,dan haka babu boye boye a ciki.
Tambaya naƙiraki nayi miki akan wani abu daban,dan haka kada ki batamin lokaci ki gaya min gaskiya.
Wanne irin asiri kika bawa lubnah tayiwa Jabeer?”
Zaro ido zaleeha tayi tana muzurai,saidai a matsayinta na ƴar duniyarce, lokaci guda tayi fuskar rashin sanin abinda bombee take faɗa.
“Hajiyah bangane……”
“Matsafiyah Zilliyyah tambaya kawai nayi miki fah,bana cikin mood ɗin jan magana,saidai idan hakan kike so”
Zumbur zaleeha ta tashi tsaye tareda murtuƙe fuska,girgiza tayi kayan jikinta suka sanja zuwa ainihin nata wanda take bayyana a mafarki da madubi.
“Hmmm dan kingane ni wacece shine me,kina tunanin harkinkai girman dazan faɗamiki duk abinda kika tambayeni ne,kema kanki a tafin hannuna kike dama sauran guda biyun,wato uwarki da ƙanwarki”
Saidai bombee tabari ta gama surutun kafin ta ɗan zaune daga kishingiɗen da take,idonta da suke lumshe ta buɗe tareda yin murmushi.
Hannunta ta ɗaga na dama tayi ƙass dashi..
Take kuwa Zilliyyah ta faɗi ƙasa tana birgima tareda riƙe ƙirjinta,saida ta galabaita kafin bombee tace.
“Turning off my robot”
Nan da nan Zilliyyah taji kaman an zare mata ƙaya a kahon zuci.
Yage rigarta tayi tana kallon inda zafin yafito,saitin zuciyarta tane wajen insa likita yace anciremata tarin jini.
“Taya haka ta faru”
“Me kike tunani Zilliyyah,banda ke daƙiƙiyace dan kawai kinsan maganin gargajiyah dana aljanu,kuma kina kashe mutane da mummunan aikin ki wasu kuma ki ɗaiɗaita rayuwarsu,sai aka cemiki baza’a iya ɗaiɗaita rayuwarki da fasahar zamani ba.
Na’urah nasa aka dasamin akan zuciyarki,wanda baza’a taba iyah cireta ba batareda kin mutu ba,sannan zan iya juyata yanda nakeso kaman yanda kike juya aljanu.
Idan na bada sauti na ƙass to zata hura zafi a jikin zuciyarki,idan kuma na tafah hannu to zata matse zuciyarki har sai ta maidata tamkar Fatar tsohuwa.
Karki kuma kice wai iya nan ne,duk maganar dakike inaji da ita,sannan duk inda kikaje ina gani a wayata da computer ta.
Sannan ba iya nikaɗai nakeda madannan ba harda likitan daya dasamiki dakuma wasu mutane guda biyar suma.
Idan nawa yasamu matsala to duk zasu danna a tare ne,”
Cikin haki da razana Zilliyyah tafara magana daƙyar,har sannan numfashinta sama sama yake fita.
“To koda kin kashe ni kina tunanin zan barki hakane,saina ɗaiɗai rayuwarki ne,indan asirin dana yiwa mahaifiyar kine da kuma ke toki sani bazan taba cirewa ba,koda kuwa zaki kasheni ne”
“Ahah dakata tsohuwa,menene na yanke hukunci da wuri haka.
Ai bake zan kashe ba,kinga wanda zan kashe.
Bombee tafaɗa tana nuna mata hoton ɗanta wanda taboye a kogo a cikin daji.
Abinci yake ci hankalin sa kwance bai sam mai ake ba,gefen fuskarsa a rufe sa farin ƙyalle.
Hannunta ta ɗaga ƙass,bayan da danna wani jan abu dayake hannunta,wanda zayyi connect ɗinta dana jikinsa.
Take kuwa yazefar da kwanon abincin yana fizge fizge kaman mai shirin fitar rai.
Hannun Zilliyyah ta haɗa biyu tana roƙon bombee akan ta dagata,saida taga dama kafin takashe abin.
Shuru yayi a ƙasa hana nishi dayaji abinda yake cinsa a zuciya ya daina.
Ajiye computer bombee tayi tareda maida kallonta ga Zilliyyah,wacce taga tashin hankali da sabon tantiranci muraran a wajen bombee.
“To Zilliyyah kinga dai yanda ɗanki yake burburwa koh,idan bakyason nacigaba da gana masa wannan azabar,to dole sai kinyi abinda nakeso.
Maganar farko itace ki tabbatar daga nan zuwa gobe kin warware abinda kikayiwa innata,inada wajen daza’a kaita ayi mata magani,zuwane bazanyi ba saboda bazan asarar ƙwandala ta ba,yanzu kike ɗaura haka zaki kwance shi.
Bayan wannan kuma yanzu kiyimin bayanin komai gameda shirin da lubnah suke itada uwarta”
“Batun shirinsu zan faɗamiki dukka,indai zaki rabu da ɗana,saidai asirin dayake kan Innarki idan aka warwareshi to Laari bazata taba warkewa ba daga cutar ƙurajen da takeyi,sanann kuma makantar da kurmantar dukka zasu koma kanta ne”
“To ina ruwana,idan tanaso ta mutu ma mana nina kasheta,ke nifah mutuwar wani bata dameni ba inshi yajawa kansa,nikaina nakashe ba adadi bare kuma dan wani ya kashe.
Ina saurarenki wanne irin Asiri kika danƙarawa bawan Allah can,kokuma yanzu aradu na baje zuciyar wancan mushen ɗannaki,kema na baje taki.
Abinda kike tsoro na rashin samun magaji ta tabbata yanzu nnan”
Tun kafin ta rufe baki Zilliyyah tafara bayani tiryan tiryan abinda yake faruwa.
“Karfa tayimasa,wacce bata taba karyewa har sai wanda kayiwa ya mutu ko kuma kai ka mutu,karyewarta ɗaya sai idan kaika karya dokarta da kanka.
Wata uku da ɗauka tana bawa aljanu jinin baƙar kuliyah duk wata,kafin suka yarda sukayi mata aikin,shima kuma saida tasake bada wani abun wanda yakeda muhimmanci a rayuwarta”
“Me tabayar?”
“Lafiyarta tabayar,amma da sharaɗin bazamu karba ba harsai tayi wata bata kalli wanda tayiwa ba tukunna,burin mallakar mijinta ne a ranta,shiyasa bata kulada abinda ta ɗorawa kanta ba.
Ita kuma mahaifiyarta hallitun haihuwar dukka ƴaƴanta ta bamu,ta ƙwammaci ta datse zuri’arta akan ta rayu da kiahiya a gidanta,wannan dalilinne yasa dukka ƴaƴan ta basa haihuwa”
“No wonder biri yayi kama da mutum,to amma ina ɗanta kuma matarsa tana da ciki”
“Ba dansa bane na wani ne daban,Mahaifiyar sa tayi shurune saboda kada ace batada magaji a cikin zuri’arta”
“Kutt tasanma batada magajin kuma shine take son mallakar Company?
Yanzu dai idan na raba ta dashi har na tsawon wata guda shikenan asiri ya karye”
“Ehh hakane,amma idan kika rabasu yanzu ba lallai yayi aiki ba,saboda bata daɗe dayin aikin ba,yanayin daɗewarsa yanayin jinyar dazata gamu dashi”
“Wata biyu zayyi ina daga nan zuwa kafin na rabasu kenan koh?”
“Ehh hakane”
“To tashi kitafi na sallameki,inkina so ki dau mataki akaina kinji,ni wandon robace,da yamma ki sharemin bayan gidana,sannan inzakiyi magana ta madubinki shegantakarnan taki,saikin faɗamin tukunna nagaya miki abinda zaki cewa brr na’imah,idan kuwa ba haka ba saikinyi wata guda a sume a gadon asiviti.”
Tana gama maganar ta dannna yellown madannin dake hannunta,haka Zilliyyah ta riƙe kirji tana tafe a hankali harta isa ɗakinta ta kwanta,baccin wahala ne ya ɗauketa,dan ma wahalar ba kaman ta ɗazu ba.
A garin tazo tarwatsa rayuwarta ita kuma tata rayuwar na shirin tarwatsewa a hannun bombee.

Page 🖤 43••44🖤

Anyi kimanin wata biyu kenan lubna na yanda taso a cikin gidan.
Jabeer ya rame yayi vaƙiƙƙirin,ba iya gashi ba harda ma Hajiyah Zeenah,wacce a neman magani babu abinda batayi ba amma abu yaci tura,kullum abu cigaba yake kaman jinyar ajali.
A tsawon lokacin duk hanyar da bombee zatabi su haɗu da Jabeer ta daina yin wajen,dan haka kawai zuciyarta bata jure ganinsa a hakan,yayinda kullum tsanar lubnah da danginta ke cin ranta.
Gashi har yanzu Duk azabar datake ganawa Zilliyyah ta gagara cire abinda ta ƙullawa innarta,a duk lokacin data yi ƙoƙarin kaita wajen magani kuma saitaji gaba ɗaya bazata iya ba,tasan baya rasa nasaba da yanda itama ba ƙalau take ba.
Abinda yafi dauremata kai ma shine ita kaɗaice a cikin damuwar,su waɗancan matannasa shirye shiryen barin ƙasar suke yi,kullum basuda aiki sai facaka da dukiya,musamman ma Jaleelah,ita da take ƴar talakawa to a ina tasamu kuɗi,ko kai a dukiyar Jabeer suke ɗiba,sannan duk wani bincike tayi akan ta,har yanzu bata gano wani abu da ta tabayi mai kawo kuɗi haka ba..
Ta sanja kayan ɗakinta ta sai mota,kaya kuwa inta saka bata sake sakashi,masu aiki ma biyar ta ɗauka nata personal,a yanda aka faɗamata dai ustaziyah ce bata damu da duniya ba,tabbas akwai wata a ƙasa,musamman yanda suke yawan fita kusan duk dare itada Jawaheer.
Inka gansu bazaka ce ma wai abinda lubnah take yashafesu ba sam,ko kallon inda Jabeer yake idan suka haɗa hanya basayi,shima dayake abi yana kansa ya haushi ko magana bayayimusu idan zasu fita.
A zaune take ta ɗora kanta a jikin majinginar kujerar,tana jiyo gwarancin haidar wanda yake koyon tafiyah kaɗan kaɗan,ƙarar wani abu tajiyo ya zube,amma bata buɗe idanunta ba,ta tafi cikin kogin tunani.
Muryar maleekah tajiyo a tana yimasa magana a corridor,
“Anty maryam allah mai sunan babannan nawa bayaji,kiduba kiga abinda yayi a kitchen”
“Uhm to ya zanyi dashi maleekah,ya jarrabawar dai?”
“Hmmm ba’a cewa komai ai,so nake muyi muyi mugama kafin bikin anty Madeenah da yah khaleel. Naso bikinnan yazo da raji amma nasan bazayyiyu ba,tunda ga can babban abokinsa baya hayyacinsa sam”
“Ba nan da wata biyune bikin ba?”
“Uhm nan da wata biyune”
“Kafin sannan ai zai warke inshaallah,zakusha raji kam sosai”
“Zamu sha bazaki je ba ai anty,taya kika san zai warke,dan allah faɗamin kin samo mafita,nasan bazaki gagara samu ba dan Allah ki taimakeshi anty maryam kinji”
“Kinga ki kyaleni yanzu tukunna,in akwai mafitar ma zaki gani ai,bari lokaci ya nuna”
“Yawwa kiji wani zance wai Jawaheer da Jaleelah zasuje Egypt a jirgin Yaj Jabeer,Hajiyah Zeenah suka tambaya tacewa yah Jabeer yabasu izini.
Sai yace wai lubnah bazata amince ba,bakiga ba kaman zasuyi kuka haka sukayi booking kawai na jirgi normal”
“Yaushe akayi zancen?”
“Uhm jiyane naji Jawaheer tana faɗawa Hajiyah Zeenah wai ita tagaji da wannan abin”
“Duk acting ne,babu wacce ta damu a cikinsu inkinga barin kuɗin da suke zakisha mamaki,duk kallonsu nake kafin nazo takansu,kowa barshi nake ya mori lokacin sa,ina so ki jiyomin yaushe zasu dawo idan suka tafin?”
“Tam bakida matsala,nasan bazasu gagara faɗawa mommah ba,ni barina je waje iyah sayyada,abinci nabiyo ci kuma naga baki gama ba,kuma fah saida Innayi tace na shiga naci hilyan ta dafa amma naƙi”
“Kinyiwa kanki,ni yau ba lallai ma nayi abinci ba,ki zama cikin shiri akwai gagarumin aiki a kwanannan”
“Wow really wanne iri”
“Kin fiye tambaya fah,zaki gani”

Tana shiga bacci bai daɗe da ɗauke ta ba taji muryar mutum a falo,batayi kama data su hilyan ba ko maleekah.
Tsuka taka tareda tashi tafito,da Dr Rahama sukayi ido biyu wacce take yimata dariyah.
“Ahh dakyau mrs JJ,baccine haka da rana,kina hutunki kice”
“Rahama kece,daga ina haka?”
“Uhm daga asibiti nake,Nagama aikin yau shiyasa na shigo miki,iya gaisawa zamuyi na wuce”
Zama tayi bombee ta kawo mata ruwa da abin motsa baki,kaman yanda kuwa tace bata daɗe ba ta tashi akan zata tafi.
“To nikam zan tafi Captain i hope kema zaki zomin koh”
“Zanzo idan har baki sake ƙirana da wanann sunan ba,banason abinda zaisa na dunga tunawa da rayuwar baya rahama,shiyasa na zabi mantawa da komai,saidai hakan bazai yiyu ba indai har bangama aikin dayaƙi ƙarasuwa ba”
“Hakane kam Maryam,nidai duk sanda kike buƙatar taimakona ƙofa a buɗe take”
Sun fito har inda motar rahama take,tana magana sai bombee taji tayi shuru tana kallon Jawaheer da Jaleelah waɗanda suka fito da trolly a hannunsu zasu fita,da alama jirgin rana zasu bi kenan zuwa egypt ɗin.
Basu kulada su bombee ba sunata surutu har suka bar gidan.
Kallon Dr Rahama bombee tayi wacce take kallon hanyar da su Jawaheer suka bi,idonta cikeda mamakin ganinnasu.
“Yadai kinsansu ne naga kina wannan kallon”
“Umm to kusan hakan,su ɗin suwaye a gidannan,sannan ya dama ƙawayene?”
“Ƙawaye kuma,sune fah matan da Jabeer ya aura wata uku da suka wuce”
“Aure…..aure kuma,waɗannan ya aura,dama sune Jawaheer da Jaleelah danakejin sunan matan daya aura,duk tsawon haɗuwata dasu bantaba sanin sunansu ba shiyasaka.
Indai kuwa hakane to da akwai babbn matsala,ina tausayawa Jabeer da Allah ya haɗashi ba iya da guda ɗaya ba harda biyu”
“Meyafaru ne a ina kika sansu?”
“Zancen bana nan bane muje ciki kiji,dama ina cewa duk taimakon dakikeso da gareni to zanyi miki in baifi ƙarfina ba,to ga wani anan muje ciki kiji shi kuwa”
Jan hannun bombee tayi a fusace suka koma falonnata,da falon bayyi musu ba suka cike can ɗaki,da alama koma menene yana buƙatar babban sirri.

Bayan dr rahama tagama fesawa bombee labari kafin ta tafi,Dariya take tana tafi a falo ita kaɗai kaman mahaukaciya.
“Ohhh dama hakane……kai ni bombee mai sa’a ce,mai yasa idan mutum ya binne abinsa saina samu hanyar dana bankaɗoshine??,A da nayi tunanin kuba matsala bace,ashe kuma manyan tantiraine,zakuwa kuzo hannun boss ɗinku ni nan bombee”
Message taga maleekah ta taturo mata,akan Sati guda zaauyi su dawo.
“Good satin bazayyi kaɗan ba na gama shirina,amma kafin su sai an gama da waccar ishashiyar tukunna”

*Conrad Hotel Cairo__Egypt*

Banɗakine amma yafi wani falon ma girma,gurare daban daban,na wanka,na rage pressure da kuma ƙaramin swimming pool duk a ciki.
Jawaheer ce a cikin ruwan tana linƙaya,yayinta ita kuma Jaleelah take zaune a bakin wajen daga ita sai bikini tana sipping lemo.
Fitowa tayi daga cikin ruwan tana taku zuwa inda Jaleelah take zaune.
“Uhm no wonder kin amsa sunan cat lady ɗin”
“Kaman yanda kema kika dace da black slender ba,wai ya akayi kina da waɗannan kuɗaɗen kika iya boyesu haka?”
“Uhm saboda na iyah kafce shiyasa,dama wanann lokacin nake jira,na auri mai kuɗi nayi facaka da dukiyata,a gida aga kamar da tasa nakeyi. Ya kike ce toh”
“Abin yayi kam,nikam ban fiye yin harka domin kuɗi ba,sai dan inaso”
“Tun mukazo kwanannan mu uku amma bamu fita ba,yau kam yakamata mu shaƙata sannan mu haɗu a wajen meeting ɗin gobe”
“Ohk shikenan,nifah ƙungiyar nan tafara isa ta yanzu,anya kuwa bazan fita ba”
“Uhm zaki iya fita kekam,amma nikam ba yanzu ba,musamman da yansu nake haskawa a cikinta,dan da duk cikin takura nake komai,ko meeting ma sai ayi biyar bansamu zuwa ba,koyaushe sai waccar islamiyyar”
“Uhm to amma ita fareedan yana ga yanzu bata fiye zuwa meeting ba”
“Nima yanda kikaga tanayi,ba’a tashi take tafiya haka nakeyi,nima irin taki ce na ƙara class yanzu,da burina ƙarbar kuɗin kawai amma yanzu babu wanann maganar”.

*** ***

Motsin mutum take gani yana wulagawa ta window.
Can kuma sai taji an buɗe cikin falon an shigo a hankali.
Tashi tayi ta tsayah tareda yin hanyar inda makunnar wutar take,dan data shigo falon bata kunna ba,saboda ganin iya ruwa kawai zatasha ta koma.
Yau daya tabar Jabeer yayi tafiyar kwana ɗaya,shima saida ta kafa masa sharaɗin ya tabbatar ya dawo dawuri washagari.
“Waye anan,Jabeer kaine ka dawo,idan kaine kadaina wannan wasan yanzunna bana so”
Tafaɗa cikin sigar umarni, tafiya takeji ta bayanta,saita juya taga babu kowa,gashi duk sanda tayi hanyar wajen socket sai a jawota tabaya.
“Wai wanene mai kuma kakeso?”
Tafaɗa cikin sigar karaya.
“Ohh kin karaya yanzu babu sigar umarnin ne,a zaton wancan ne dakika shanye shi koh,tun shakaranjiya nake auna ki sai yau nasamu bayanan,lokacin dana baki ki shaqata yaƙare lubnah”
“Maryam mai namikine kike shiga rayuwata,kefa kikace kowa yayi harkarsa ba zama kikazo da mijina ba”
“Eh haka ne ba zama dashine maƙasudin zuwa na ba,dalilin zuwana gidannan shine fatattaka rayuwarki,domin haka Hajiyah Zeenah tayi yarjejeniya dani”
Shuru ne yaratsa wajen kafin taji bombee tana cigaba tacewa.
“Ohh wai sanɗa kike zaki ɗakko wuƙa ko kuma zaki gudu,hhhhh kidaina wannan wautar,don ke bakya ganina sai akace ni bana ganinki kenan,Mai kika ɗauki kalar idona na banza kenan?.
In baki yadda ba saina faɗamiki duk abinda kika yi yanzu,ina ganinki kaman yanda kike gani idan gari ya waye rana ta kusa fitowa”
“Ki rabu dani ki fita harkarta,dama nasan ke ba mutum bace ke mayyace”
“Faɗi ki ƙara bake kaɗai bace kika faɗa,yanzu haka ma barina yimiki aikin mayun ”
Tana gama faɗin hakan lubnah taji an shaƙa mata abu a cikin towel,daga nan ba iya ganinta ne ya ɗauke ba,harda jinta da kuma hankalin ta.

Wajen dokar dajine babu mutum gaba babu shi a baya,sai iya wani kangon gida wanda babu mai zaton akwai wata halitta a ciki.
Bombee a cikin gidan a zaune kan kujerar katako tana lilata,gefenta kuma hilyan ce a tsaye da kuma khmees,baƙaƙen kayane dukkansu a jikinsu. Har sannan gari bai gama waye ba,amma kana ganin komai tarau.
“Ke hilyan ɗauki ruwan sanyin can ki sheƙa mata,lokaci yayi dazata farka daga mafarkin datake ciki ta fuskanci zahiri”
Aikuwa kaman jira take ta ɗauki ruwan mai uban sanyi ta sheqawa lubnah shi ta sama,wacce take ɗaure tamau kaman za’a yanka dabba.
Wani razanannen numfashi tasake tana zazzare ido,da bombee tayi arba a gabanta tana zabga mata murmushi.
“Yadai Hajiyah lubnah kingama baccin kenan,yanzu kuma keda baccin daɗi kingamashi kenan,dan a kabari ma nasan keman baza’aga dadai ba”
“Wayyo Maryam Mai nayi miki kika kawoni nan wajen,dan allah konawa kikeso ki faɗa zan baki,amma ki sinceni na koma gida”
“Kinga dakata ni babu abinda zanyi miki,kawai ɗaureki zanyi anan wajen na wata guda saina sakeki,ko ƙwandalarki bazan karba ba”
Zaro ido lubnah tayi jin jawabin da bombee tayi mata,wata guda?? In hakan tafaru shikenan tata taƙare kenan?.
“Meyasa dole sai na kai wata,ko nawa kikeso ki faɗa zan baki ki sakeni,in so kike ma zan bar Jabeer ya dunga zuwa wajenki,amma naroƙeƙi ki kwanceni na koma”
“To wai menene na tada hankalin ne,nace fah ba abinda zan miki,kinayin wata guda zaki tafi.
Ko kai akwai abinda kike boyewa?”
“Ni ba abinda nake boyewa kawai…..”
“To shikenan zakiyi zamanki anan wajen har wata guda tacika,ni barina tafi kar a gane nina ɗaukeki koh,ke hilyan ku dunga bata abincinta hankali kwance tanaci,iya kawai wata zatayi takoma wajen mijinta”
Ihu lubnah tasaka tareda jijjiga sarƙar da bombee ta ɗaureta dashi.
“Wayyo na roƙeki ko dukana ne kiyi,ke ko hannuna kikeso kicire,amma kada ki ɗaureni anan wajen harna tsawon wata guda,na yarda ki gana min azaba inyaso ki sakeni nan da sati uku”
“Wata guda nake so nagama magana”
Har bombee taje bakin ƙofah zata fita tajiyo wata magana.
“Idan har baki sinceni ba nakoma to Jabeer zai mutu a cikin wata gudannan,dan haka inkinaso yarayu to ki sinceni na tafi,saboda banason ya mutu nake roƙonki daki sinceni na koma”
“Hhhhhhhh kutt yau bayan tsawon lokaci an samu wacce ta ɗaukeni shashasha,ni zaki raina wa wayo lubby,kowa yaga mai kike ai yasan dan kanki kike wanann magiyar.
Kuma ki kwantar da hankalin ki ma,wlh inkinga kinbar wajennan to wata guda yacika ciff,saidai in allah ne yayi ikonsa akanki,wanda nasan hakan ma bazata faruba,saboda baya bayan mutane irinki,shiyasa ma yabani ƙarfin gwiwa da lasisin ɗaiɗaita rayuwarki.
Ki zauna nan da sati zanzo na ganki kinji,barinaje naga yanda za’ayi ta yawon nemanki a can”
Tunda lubnah taji abinda bombee ta faɗa batasake cewa komai ba,banda ruwan hawaye babu abinda yake bin kuncinta,a iya mintunan da basu fi uku ba gaba ɗaya saitin ƙwaƙwalwarta ya karkace,dan bata hango hanyar fita daga hannun wannan mai zubin sheɗanun ba .

Lokacin data isa gida babu wanda ma ya tashi,abinka da zubin rayuwar ƴan gayu,itama gado ta hau tayi kwanciyarta hankali kwance,tsawon lokaci sai yau taji rayuwarta tayi sanyi.

Muryar maleekah tajiyo tana ƙiranta,wayarta ta duba shabiyu da rabi,lallai ta kwashi bacci.
Dan dama Haidar tun jiya takaishi wajen innayi.
Fitowa tayi tasamu maleekah a zaune a falo,tun kafin su gaisa tashiga koro mata bayani.
“Anty kinji wani labari,wai Jiya masu garkuwa da mutane sun shigo gidannan sun ɗauke anty lubnah,harda gwalagwalai da kuma takardun gidajenta data siyah duk aka ɗauke.
Dafe ƙirji bombee tayi tareda cewa.
“Yaushe haka tafaru,nikam ti basu shigomin nan ba,sauran sashen fah sun shiga”
Ahah wai iya nata suka shiga,sukam basanan ai,amma mommah tayi musu waya kan su dawo suma,zuwa yamma zasu iso a duba ko anshiga sashensu”
“To ina Jabeer kuma fah yadawone”
“Hmmm ya dawo ɗazu,babu abinda yake sai ƙiran sunan lubnah yana kuka,gaba ɗaya ya tadawa kowa hankali”
“A wanne waje yake yanzu haka?”
“Uhm yana sashen momma,itama kukan take ganin yanda yake yi,anty maryam abinfah ba kaɗan bane ba.
Itama brr na’imah yanzu da tafi daga nan,sojoji da masu bincike sai fama suke tun safen”
“Amma har yanzu babu wani clue na inda take?”
“Eh babu fah anty maryam,gashi har yanzu basuyi maganar nawa suke so ba,inaga dan anga brr na’imah na neman minister ne shiyasa aka saceta saboda kuɗi”
“Ba mamaki kam To Allah ya kare”
“Ameen ni ba zafin batanta nakeji ba,abinda Jabeer yake duk shiyafi damuna,barina je wajen mommah Anty maryam”
“Ohk to nima barina shirya nashigo yanzunnan”
Maleekah tana fita Bombee tayi murmushi tareda cewa.
“Hmmm saikun jure wahala kafin ku samu sauƙi,brr na’imah yanzu ma kika gani,keda ganin ƴarki sai kamanninta sun juye tukunna”

Ɗaki ta koma tasaka goduwar riga da mayafinta,kafi ta fito ta nufi sashen Hajiyah zeenan dan ganin mai yake wakana.

*** ***

Waya take gabaɗaya banda gumi babu abinda yake zuba a jikinta.
“Wai kan nufin har yanzu ba’a ganta ba,duk ƙarfinka a bangaren tsaro ka kasa gano inda ƴarka take,kai wanne irin ubane,to kada ka dawo gidannan har sai ka samomin ƴata a duk inda take”
Tana cikin wayar Inayah a cikin shigarta ta tsofi tasake miƙomata wata wayar,nan ma detectives ne masu bincike suke ƙiranta.
Karba tayi ta danna suma tacigaba dayin waya dasu,tanajin babu labari lubnah ta buga wayar a ƙasa.
Kallon Inayah tayi tareda cewa.
“Kema wata tsohuwar marar amfanin,ina ammar ya shigo gidannan?”
“Eh yashigo hajiya amma yayi sashensa,dannaga yasaka akaimasa abinci ma irin wanda madam juliet take ci”
Tana jin haka taja tsuka tareda yin sashennasa.
Lokacin data shiga daidai zai sakawa juliet abinci a baki,wacce take ta narkewa tana shafa cikinta.
Ƙafa tasaka tayi ƙwallo da plate ɗin abincin a falon,sai huci take kaman kububuwa.
“Ammar kaikuwa mutum ne,anya kuwa baka samu tabin kai ba,ƴar uwarka tana can a hannun bata gari bamu san inda take ba,kaikuma kana nan da wannan fatalwar matar koh”
“Haba to mommy yakk so nayi,tun safe fah ake ta neman ta ba’a sameta ba,ƙinƙi kici abinci,kin hana abba yaci nima kin hanani,to sokike shima babyna bazai ci ba kenan.
Dan ƴarki ta bata shikenan nima sainawa ɗan yashiga matsala”
“Ɗan ka a gidan ubanwa ɗin,waye tacemaka ɗanka ne a cikinta,kodan kaga nayi shuru na zuba muku ido kai”
“Whatt…..mommy mai kike nufi wai,ba ɗana bane nawaye toh”
“Bansaniba ka tambayeta mana ta baka amsa”.

Page 🖤 45••46🖤

Tsit taji falon lokacin da shiga babu kowa,saidai ta kasa kunne kafin tajiyo muryar maleekah inaga da Madeenah a ɗakin su.
Hanyar wajen ta nufa harta fara jiyo muryar su.
“Waini kam maleekah meyasa kike min haka ne,sanin kankine rigar nan tunda na siyeta ban taba sakawa ba,shine kika ɗaukemin”
“Kai wai ke babu dama a ɗau kayanki ne saikin……”
Da bombee ta haɗa ido wacce take tsaye a bakin ƙofah.
“Uhm sannunku,yanaji gidan shuru,ko an sameta ne?”
“Ahah ba’a sameta ba anty maryam,suna sashen Iyah sayyada,barin rakaki can”
“Ahah ina shi Jabeer ɗin yake?”
“Uhm yana ɗakinsa na sashennan,muje na nuna miki”
Jefawa Madeenah rigarta tayi tareda yin gaba bombee tabita.
A bakin ƙofar ta tsaya tareda cewa.
“Gashinan maybe in yaganki ya yarda yaci abinci,amma babu abinda yaƙe ƙira sai sunan lubnah yana riƙe kai,ni wlh har na ƙosa a ganta saboda halin dayake ciki”
Bombee bata ce mata komai ba,sai murɗa hannun ƙofar datayi ta shiga,a zaune yake a ƙasa yasaka kansa akan gadon.
A hankali take tafiya har ita isa inda yake ta zauna,hannu tasaka tana dafa bayansa.
“An sameta,ta dawo gida lubnah n?”
“Ahah bata dawo ba,saidai kasani tana cikin ƙoshin lafiya,nasan inda take ma,idan har ka kwantar da hankalin ka zan kaika inda take”
Saurin ɗagowa kansa yayi yana kallon bombee,wacce ta kawar da idonta,don bazata iya kallon yanda yakoma ba a yanzu,ya sanja kamanni yayi wani iri,ga tunanin sa ma yazama tamkar na yara.
Dan ma yanayin aikin yana ƙara kwanaki batareda yaganta ba abin kuma yana rabuwa dashi,dolene ya jure ya zauna a haka idan yanaso abin ya rabu dashi.
Cikin lallama da bi a sannu ta samu yaci abinci kaɗan yayi bacci,saida ta tabbatar babu matsala tukunna tafito daga ɗakin zata tafi.
Karo suka ci da Hajiyah Zeenah zata nufi sashen alhj Aliyu,kallo ɗaya tayi mata ta ɗauke kanta.
“Uhm yanzu nafara share tantama ta,kenan kin kamu da soyayyarsa,tunda kika gagara haƙuri saida kikazo kika ganshi”
“Hmmm Hajiyah Zeenah kina bani mamaki,yanzu ki duba halin da ɗanki yake ciki,amma duk a haka kike?.
Inkin san mai kike banice abokiyar hamayyarki ba yanzu.
Batun barinsa kuma basai kin faɗamin ba zan barshi,ai na bar nonon uwata ma kuma na rayu,kaman yanda na faɗa a farko to kuwa zan cika wannan alƙwarin,sai hankalin ki ya kwanta”
Tana gama faɗin hakan cikeda bacin rai tabar cikin falon.
Madeenah da maleekah wanda suke tsaye akan idonsu hakan ta faru,harda su Abdulmaleek da abdulkareem da shigowarsu kenan sashen.
Kallo ɗaɗɗaya bombee tayi musu kana ta rabe musu ta wuce.
Da kallo suma suka bita,ganin yanda tasamu ƙarfin halin gayawa uwar tasu magana kuma tayi tafiyarta cikin izzah.
Jan numfashi Hajiyah Zeenah tayi tareda barin wajen itama bayan bombee ta tafi.
“Wayyo shikenan mommah takai anty maryam bango tace zata tafi,nikam banaso ta tafi tabar ya Jabeer”
“Ke dallah rufemana baki,kaf gidannan kowa yasan rashin mutuncinta bandake,kullum kina mamuƙe da ita,bakya ganin akan idonki yadda ta gayawa Mahaifiyarki magana ido da ido,ke wacce irin ƴa cd ne”
“Ehh nagani amma kaff cikinmu akwai wanda ya iya kwantarwa yah Jabeer hankali tunda abinnan yafaru,amma daga zuwanta gashi nan har yayi wanka yaci abinci yayi bacci.
Kafin aurensa da waɗancan matan da gwanda babu su,itake kulada wankinsa,dukiyarsa,cinsa,shansa akan lokaci,sannan in an kawo masa hari kafin yasani ma tasan da abin.
Bazaki ganeba saboda bakisan mai yake faruwa ba,nima bansani ba sai ta sanadiyyar ta,amma yah Jabeer yana kewaye da mugayen mutane bila adadin,zamanta kusada shi wani taimakone da allah yayi masa.
Kodan kwai mutum yanada zafin hali kuma yana bayyana gaskiyar mai yake ransa sai ya zama azzulumi da tantiri,ina jiyemiki ranar dazaki gane mutanen dakika ɗauka mutane ashe dabbobine masu fatar mutum”
Maleekah tana gama faɗawa Madeenah haka tabar falon cikin bacin rai.
Sukuwa su Abdulmaleek da basu san kan lamarin ba sai aka barsu da wasiwasi,dan ita kanta bombeen ganinsu na farko kenan da ita.

Hilyan ce riƙeda kwanon abinci,saida ta sincewa lubnah hannu kafin ta tura mata abincin,kallon kwanon tayi kaman mai nazari kafin ta miƙa hannu ta ɗiba takai baki.
Yau kimanin sati biyu kenan,duk wata magiya babu wacce batayiwa bombee ba,amma taƙi sinceta,har yazamana yanzu ta daina magana ma sai bin hilyan da ido kawai idan zata bata abinci..
Kuɗaɗe kuwa sun ƙarbi akallah yakusa miliyan hamsin ko sama a wajen brr na’imah,amma har yanzu shuru tana jiran dawowar ƴar ta.
“Uhm yafimiki kam takika daina magana,dan tunda ta yanke miki saikinyi wata gudannan to babu fashi”
“Dan allah to idan bazata sakeni ba kice mata ta kawomin Jabeer na ganshi inyaso”
“Hhhhhh wannan kuma ki bari sai tazo inyaso saikiyi mata bayani.
Ni nayi zaton kin zama kurmiya,ashe kina magana sarai kenan”
Cigaba ta cusa abincin tayi tana hawaye da majina,a ranta tana fatan bombee ta yarda ta kawo mata shi.
Kaman yanda tafaɗamata babu duka babu zagi,wanda tasa su kulada ita suna bata abinci mai kyau da lafiya,saidai fargabar abinda zai sameta yasa ta ƙanjame ta rame,babu wannan ƙibar ta da duk ta tafi.
A bangaren Jabeer kuwa yanzu yafara dawowa daidai,saidai har yanzu bayayiwa kowa magana,yana dawowa daga aiki zai shiga sashen lubnah ya zauna. A cewarsa umarnin data bashi kenan,kuma yasan zata dawo da sameshi.
Kaff gidan hankalin su yayi mungun tashi da wannan ɗabi’ar tasa,hakanne yasa ake tunanin ƙarbar kujerar CEO daga hannunsa,wanda kuma duk Alhj Abdullahi ne mai ƙarfafa maganar.
Itakuwa bombee duk abinda suke tana jinsu,kallonsu take kawai a baibai na gameda shirin dasuke,tsakanin Lailah da Alhj Abdullahi.

*** ***
Tun safe bombee suke kan inna Danejo,sai sanƙamewa take,sai anyi mata tofi da ruwan Addu’a Kafin take dawowa daidai kaɗan.
Innayi ce takalleta cikin muryar kuka tace.
“Dan allah addha bombee yanzu kam mu kaita wajen mai magani,wlh abinnan nata ƙara tsauri yake,gashi kullum jikinta ƙara laushi yake saboda ciwon,ko bazaki iya ba nida su hilyan zamu kaita idan yaso,dukkanmu munsan uzurinki,kuma munga ƙoƙarinki akan abubuwa da dama namu,wannan karon dakika gaza ki barmu muyi Addah bombee”
Hannun inna Danejo ta riƙe gam tanajin abinda innayi take faɗa,duk dauriyarta da kuma jajircewarta tagagara kaiwa Mahaifiyarta magani,wannan wacce irin ƙaddara ce.
Tashi innayi tayi ta ɗauko hijabinta tasaka,inna Danejo ma ta sakamata nata.
Hilyan ce ta inaya suka kinkime ta zuwa cikin motar bombee,har suka kaita tana nan zaune a inda suka barta bata motsaba.
Hilyan ce tashigo ɗakin ta dafa ta.
“Karki takurawa kanki dayawa harki samu matsala anty maryam,idan bazaki iyaba ki kawo makullin nakaisu,ai nasan gidan malamin,kuma dama kin biyashi kuɗin aikin tun wancan karon,wannan karbo maganin bazai yiyuba dole sai ya ganta tukunna”
“Uhm uhm hilyan zan iya zuwa,bazan zama mai tsoro ba,haka suke so bazan basu dama ba”
Tashi tayi ta ɗauki key ɗim motar,yayinda itakuma hilyan ta riƙo Haidar a hannunta suka fito daga gidan.Basuyi tafiya mai nisa ba cikin ikon Allah suka isa gidan,dan ma bombee tana tafiyah a hankali kaman bataso,kowane gudu kaɗan ji take kaman ana zare mata laka,amma taƙudura a ranta dolene taje yau a yita ta ƙare.
Wani yaronsa ne yayi musu iso zuwa cikin falonsa inda yake ganin marasa lafiyah,har sannan inna Danejo batasan inda kanta yake ba,ta sanƙare kaman gawa.
Cikin gaggawa yafara da yimata Addu’a da kuma yayyafen ruwan magani wanda zai taimaka.
Yadaɗe tana yi kafin aka samu naman jikinta yasaki daga ƙanƙamewar dayayi.
Duk abinda yake bombee tana gefe guda tariƙe kai bata sanma mai suke ba,kowacce kalma idan ya furta ji take kaman kanta zai fice daga gangar jikinta,ita kaɗai tasan mai takeji a lokacin.
Yanayima inna Danejo karatu,amma ta gefe ɗaya kuma yana kulada da yanayin da bombee take shiga,duk da tana iya ƙoƙarinta wajen bata nuna mai yake damunta a fili ba.
Wasu mata guda biyu ya ƙira suke shigo wajen,tashin Danejo sukayi tsaye Wacce jikinta yayi sanyi kaman babu laka..
“Kukaita ɗakin turare,ku tabbatar kusaka a kowacce ƙusurwa”
“To mallam”
Daga nan suka bar wajen sai iya bombee dasu innayi,gyaran murya yayi tareda gyara zama yana kallonsu.
“To Alhamdulillah an samu nasarar shawo kan matsalar,saidai fah gaskiya jikinta yadaɗe tana jure abin,a kowanne lokaci komai zai iya faruwa wanda ba,a fata,dan haka tana buƙatar magani gaggawa.”
“Uhm malm kaman ya kenan?”
“Maganin dazamuyi mata zai ɗauki lokaci,sannan ita,kuma jikinta yana buƙatar maganin akan lokaci ne,to maslaha ɗayace saidai itakuma ba lallai a yita ba”
“Waccece faɗamin ita naji”
Shuru naɗan lokaci batareda yace komai ba,yayinda dukkan wajen kuma suke jiran dakon abinda zai faɗa.
“Uhm mafitar itace a kashe bokan dayayi wannan aikin,idan an sanshi kenan. Ta hakane aikin daya kulla a rayuwarsa zasu bar kan wanda yayiwa sukoma kan wanda yasaka a yimasa,zance anan kenan ba iya bokane zai mutuba harda wanda yayi aikin shikuma abinda wancan yake fama dashi to kansa zai koma”
“Indai ta wannan ne angama,da banyi niyyar kasheta yanzu ba,amma tunda ya taba kan innata to banida zabi,dolene kuma mataki yabiyo baya,yanzu inaso ka faɗamin tsawon wanne lokaci zata iya kaiwa a wannan halin da take ciki?”
“Tsawon kwana ukune,saidai kina abin zaikai harga kisa kuwa?”
“Kisan wanda yayi kashkashe ladane,saidai kafin akai gayin hakan akwai abinda nakeson aiwatarwa,dan Allah ka kulamin da ita kafin lokacin,ni barina tafi”
Tana gama faɗin hakan tabar falon da sauri,su Inayah sai tsinkayota sukayi a mota,dan ji take kaman akan ƙaya take.
Bayan sun fara tafiya a mota kallon innayi tayi ta glass,wacce ta rungume Haidar da cinyarta tana kallon window,saidai kana gani kasan hankalin ta yana wani waje daban.
“Innayi kinji abinda mlm yace,sannan kuma idan na aikata hakan dole,zai shafi inna laari!! Am sorry i have no choice but to do it”
“Karki ce haka addah bombee,duk da cewa uwa uwace kam zanji babu daɗi,amma a yanxun ma ba daɗin rayuwar takejiba ai,tana girbar abinda ta shuka,a yanzu ni kaina nafison samun lafiyar inna Danejo,saboda ita nake gani a matsayin inna ta ba inna laari.
Duk abinda tayimin na yafemata a matsayinta na wacce ta haifeni,saidai babu wanda zan tursasa a waɗanda ta zalunta su yafemata,dolene ta tone abinda ta shuka”
Daga haka kaff cikin motar har suka isa gida babu wanda yace wani abu.
Waya bombee ta ɗauka taƙira khmees,wanda yau shikadaine a wajen lubnah,inshine kuwa dama bata magana,ta koma tamkar karya saboda ɗaurin dayake jikinta.
“Hello khmees ya wanann matar take?”
“Gata nan taci abinci yanzu”
“Okay a yau akwai gagarumin aiki da kuma gobe,inaso ka ƙira brr Na’imah kace mata na shiryah haɗuwa da ita a yau da yamma a bayan gari,kaje kai da yaranka ku satomin ammar ma ɗanta,domin inaso kada tayi min gardamar abinda zan tambaya. Ka tura mata hotunansu dukka kace ta fanshesu da share companyn jaan data mallaka da mummunar hanya,idan kuma ba haka ba to kace tayi bankwana dasu”
“Angama shikenan,yanzu ma kuwa zamu danƙoshi,GPS ɗinsa yana nuna hotel ne,da alama yana can yana kashe arna da ranar nan,scamp message zamu turamasa kada ki damu”
“Shikenan duk yadda kukayi,ganan hilyan ma zata zo,idan kuka gama tsarawa ku yimin text da yamma”
Tana kashe wayar ta karbi ɗanga tanufi gida,dukka tareda su inaya,wacce zata sauƙeta anguwar su brr na’imah wajen aikinta na spy.
Tana isa gida abinci ta ɗora marar wahala,ta zubawa innayi taci,saboda kowa yaganta yasan tana buƙatar a zauna tareda ita,saida ta tabbatar taci abincin tashiga wanka,kafin ta nufi ɗakinta na study.
Wajen wasu computer taje guda biyu da akayi musu connecting da CCTV camera,a ƙalla kusan guda shida,dukka kuma na bangaren Jawaheer ne da Jaleelah.
Dariya tayi mai ɗauke da takaici bayan tagama ganin abinda yayi record a ranar,kaman yanda tayi tsammani harma yafi haka,yanzu tariga tagama sanin mai yake wakana a gidan.
Sending vedion tayi ta email ɗinta,kafin ta rufe ɗakin ta fito.

********

“Me kake faɗa kaikuma yanzu haka inspecter,yanzu an tafi kusan sati uku kenan da batan ƴa ta,har yau kuma ba’a sameta ba,kuma yanzu kasake ƙirana kace wai ɗa na ma an ɗaukeshi,kunsamu motarsa baya ciki?”
Maganar take kaman zatayi kuka,tama rasa yazatayi da gashin hankalin dayake zagaye da ita.
Katse ƙidan insectern tayi jin message yashigo wayarta,hotunan ammar ne shida lubnah,dukka an ɗaɗɗauresu tamau kaman awaki.
Zare glass ɗin idonta tayi tana sake kallonsu,yaraf takoma dabaya ta jube akan kujera jikinta sai rawa yake.
Gen abdu manga ne yashigo gidan da waya a hannunsa da sauri,da alama shima yaga abinda tagani,samun waje yayi ya zauna a kusada ita.
“Dear ki kwantar da hankalin ki,ki daina saka damuwar nan,inshaallah za’a gansu dukka batareda wata matsala ba.
Bama sai ankai da basu takardun dasuka buƙata ba,ƴan bincike zasu nemo su”
“Ƴan binciken mai suka tsinana har iyanzu,kai kanka baka fini rashin son bada abinda suka buƙata ba,saidai ka bari kawai,tunda har suka tambayi takardun share na JAAN,to na tabbata a cikin gidannane wani yasan mai muke aikatawa,musamman ma Lailah da mijinta,idan na karbo ƴaƴana saina ɗaiɗai ta rayuwarsu.
Kaje ka kawomin takardun nan yanzunnan”
“Waikina nufin basu zamuyi,bakya fa son rabuwa da takardunnan?”
“Dallah kaje ka kawomin su,idan banason rabuwa dasuma yazanyi,a tunanin ka shikenan na nahaƙura daman,ammar dazai hau kujerar yana hannun su,itakuma lubnah banason takai wata guda a wajensu itama,domin akwai gagarumar matsala idan hakan ta faru”
“Wacce irin matsala kuma?”
“Bai shafeka ba,ka ɗau takardun kakai musu inda suka buƙata bayan kayi sign,kace musu basai na haɗu dasu ba,domin basuda wannan matsayin a wajena.Sunce sai gobe zasu sakesu,kada ka basu takardun harsai ka tabbatar sun sakesu ɗin tukunna,haɗuwata da ita kuma kace basai na haɗu da ita ba,saboda nasan bazata wuce Lailah ba”
Maida glass ɗinta tayi tabar falon,saidai kana ganin jan idonta kasan tashin hankali ne kwance a cikinsu.
Kaman yanda tafaɗa,gen abdu manga ƙiran khmees yayi domin ya faɗamasa inda zai ajiye takardun,da kuma inda zai ɗau yayansa.

**** ****

Kasancewar da daddare zasuyi musanyen,tunda farkon dare tawagar gen abdu manga sukayi likimo a wajen ƙarbar su lubnah.
Sai can wajen shabiyun dare kafin suka ji ƙarar waya,tun kafin khmees yayi magana gen abdu manga yace.
“Yah ka kawosu,gani nan a wajen daka kwatanta ɗauke da takardun”
Saida khmees yasheqe da dariya kafin yace.
“Hhhhhh akwai wata motar katako zatazo wucewa yanzunnan,ka jefa a cikin motar,ina kallonku daga nan,idan har wani yayi yunƙurin bin motar kafin ta bace,to zan harbe kan namijin a take.
Kuna jefawa in motar tatafi,to zakaji address ɗin inda ƴaƴan ka suke a wayarka ya shigo.”
Hakan kuwa akayi,tun kafin khmees ya rufe baki motar tazo wucewa,kasancewar a hankali take tafiya,har yasamu damar jefa takardun a bodin.
Tana bacewa ganinsa kuwa yaga message ɗin yashigo.
Signa yayiwa wasu mutanensa kansu bimotar,yayinda shikuma yanufi inda su lubnah suke.
Kaman yanda yafaɗa kuwa suna ɗaure damau a wajen,jikinsu duk yayi ja saboda ɗauri.
Yana farinciki yasamesu,saidai kuma ƙira yasameshi kan cewar sun samu motar,amma kuma babu takardun a ciki,shikuma drivern da alama bai ma san mai yake faruwa ba,kawai plan suka haɗa dashi a ciki.

Mashallah sai ku tara damu a give kuma domin jin mai zai faru a dokar daji tsakanin bombee da kuma Zilliyyah……..
Shin asirin zai karye ko ahah.
Taku sadi-sakhna…..

Page 🖤 47••48🖤

Zilliyyah wacce take kwance a cikin kogonnasu sai ganin bombee tayi a kanta tsakar dare.
Tashi tayi ta zauna tana kallonta,dan tasan ba abin daɗi ne yakawota wajenta ba,tana mamakin duk shu’umancinta wai ƙaramar yarinya tasamu ganin damarta.
“Me……me kuma kikazo nema wajena,ba kince inna faɗamiki abinda na’imah tayi zaki rabu damu ba?”
“Ahah ki sanja zancen,bazan rabuda ke badai,zan rabu da ɗanki nace,amma kekam ko a mafarki aka ce zan barki ki tafi hannu rabban ai yakamata kiyi maza ki farka.
Yau mai kankat ƙareki nazoyi daga duniyar nan,aje can a tarar da sabuwar rayuwa kafin muma mu ƙariso.
Ke hilyan tanƙwasomin ita ki fitomin da ita waje ina jiranki”
Bombee ta faɗa tanayin hanyar waje,domin amsa wayar da khmees yayi mata.
“Hello ina jinka,ka karbi takardun ka tabbatar sune……..okay to shikenan,barina gama da wannan ,amma kafin sannan ka taho yanzu muna jiranka,saboda bansan mai zai faru ba”
Tana ajiye wayar hilyan ta jeho Zilliyyah a gaban bombee,wacce ta bushe tayi baƙiƙƙirin tana riƙeda ƙirjinta inda bombee ke gana mata azaba,wanda zai hanata yin katabus balle ta ɗau mataki.
Nishin take sauƙewa ɗaya bayan ɗaya kaman wata mutuniyar arziƙi,wani banzan kallo bombee ta aika mata daga ita har ɗan nata,wanda fuskarsa take sunkuye,ta takwaikwaye kaman dodo.
“Wai don tsabar mugunta da son kai,wannan ƙazamin dodon ɗannaki zaki aurawa innayi,inda bangano ki ba Allah ne kaɗai yasan inda zaki tsaya kenan….hmmmm”
Duk abinda bombee take faɗa Zilliyyah tana jinta ko tari batayi ba,sai rawar ɗari take kikir kikir.. Suna cikin hakanne khmees ya iso wajen da motar bombee,takardun hannunsa ya miƙamata da gama dubasu,kafin ta bashi ya saka a mota.
“Hilyan madannin na hannunki bani nan na gama da ita mubar wajen”
Ɗan Zilliyyah ne ya rarrafo yana son roƙon bombee,da wata murya mai kamada gwaranci.
“Ohhh abin yayi yawa,bayan sauya kamanni ko magana ma bakayi,to shikenan kada ka damu bazan kasheta ba,abu ɗaya kawai zanyi shine maida komai data tabayi kanta,ta hanyar fasa madubinta…….hilyan hakan yayi koh”
Cikeda mugunta hilyan ta ɗaga kai tana dariyah,da sauri kuwa tashiga cikin gidan ta ɗauko madubin,wanda yasha fenti da jini.
Zilliyyah wacce ta rufe ido tana jiran ta inda zuciyarta zata tarwatse,da sauri ta buɗe idon jin abinda bombee ke shirin yi,wanda yafi mutuwar dazata bata tashin hankali,domin tariga ta basu ruhinta kafin su dunga yimata aiki,idan aka fasa madubinnan shikenan tata taƙare,rayuwa zatayi ita ba,a mafarki ba ita ba a zahiri ba,sannan kuma cikin azaba da ƙazanta.
“Ahah ahah bombee kada kiyi haka naroƙeƙi,aradu gwara kasheni daki fasa madubinnan kafin na mutu,gwanda ki kashemu nidashi gabaɗaya,inkika fasa madubinnan……”
Hannun ta haɗa taba roƙon bombee,jikinta har rawa yakeyi,wanda kuma hakan yasaka zuciyar bombee yin fari tass kaman farin goro.
Madubin ta ƙarba a hannun hilyan ta ɗagashi sama,saida tasakewa Zilliyyah murmushi,wacce take jijjiga kai kafin tasakeshi ta bashi waje a ƙasa,jin yabar hannunta kuwa gravity na ƙasa yaji izuwa fashewar sa fassss a ƙasa.
“Tsawon rayuwarki kina cutar da al’ummah,yau lokacin naki hukuncinne,kinsan kin shiga gonar bombee a yau,in baki mutu ba yazamemiki gargaɗi”
Wani ihu tasake mai cike da kama zuciyah,iska ce tafito daga cikin madubin tana ƙugi tana jan ƙafafun Zilliyyah,wacce take neman taimakon abinda zata kama,babu abinda yake kusada ita sai hannun ɗan ta,wanda kuwa tariƙeshi gam suna shirin shigewa tare.
Hilyan ce takalli bombee tareda cewa.
“Anty maryam shiɗin mu ceceshi,tunda babu abinda yayi?”
“Ahah koda kin ceceshi yazakiyi dashi,shikansa naga alamun ba cikekken mutum bane,sannan bakya ganin shine yakeson binta,barsu suje kawai gayyar tsiyah”
Bata gama rufe baki ba Zilliyyah taƙarisa shigewa cikin madubi itada ɗanta,wani haskene yafito mai ƙarfi wanda ya tarwatsa madubin kashi kashi..
Hakan a tare ya wakana da zubewar bombee ƙasa sumammiyah.
*** ***
Yauma kamar kullum yana tashi daga aikinsa yanufi gida,sashen lubnah ya nufa yacire kayansa yayi wanka.
Sallar la’asar ya haɗa da kuma magriba,ko Addu’a bayyi ba ya tashi ya naɗe sallayar,saboda lubnah tace masa kada yasake yayi Addu’a idan yayi sallah,ita kanta sallahr sa’a yaci bata hanashi ba.
Abincin daya shigo dashi a waje ya buɗe yaci,daga nan yasamu waje ya zauna.
Aikin da bayyi ba ya ɗauko yafarayi har lokacin isha,yana sallah yacigaba har cikin dare yana zaune.
Can kaman a sama yaji ana ƙiran sunansa da ƙarfi,bai amsa ba sai waiwayawa dayakeyi domin ganin mai ƙiran,bayan ƙirna yayi shuru sai yaji an kwaɗa masa wani abu a tsakiyar kansa,mai makon yaji zafi sai yaji tamkar ana warware masa wata igiya.
Riƙe kan yayi da hannyensa biyu,daga nan ya bingire a wajen sumamme.
*** ***
Tun safe har dare ya shiga brr na’imah bata zauna ba,yanzu ma zirga zirga take a cikin talatainin dare,saiga Gen abdu manga yashigo shida su lubnah,da sauri ta taresu tana duddubasu ko anyi musu wani abun,ganin komai sumul yasa ta maida ajiyar zuciya.
“Sannu maza muje ki wanke jikinki ki ci abinci ki huta,hmmm ai Lailah ta ɗebo ruwan dafa kanta,dani take zancenne”
“Mommy Lailah kuma,wacce lailan?”
“Wacce ta ɗaukeki mana?”
“Ba Lailah ce ta ɗaureni ba,maryam ce fah matar Jabeer,wacce nake faɗamiki muna sa insa da ita,tantiriyace ta bugawa a taro,domin bata tsoro ko kaɗan”
“Maryam kuma,to itakuma menene nata na kamaki”
“Uhm da alama tasan nayi wanannan aikin,dan cewa tayi bazata sakeni ba sai nayi wata guda,saikuma gashi wai ta sakeni a sati uku.
Ƙaƙƙarfa ce naji wasu yaranta hilyan da khmees sunace mata captain dai,yawwa akwai wani sunanta ma Bombee”
Zaro ido su brr na’imah sukayi a tare,wayarsa ya ciro ya danna wani hoto ya miƙawa lubnah.
Hoton bombee ne da kayan sojoji ta sara,kanta da jar hula irinta captain.
“Lahh itace ai,ya akayi na ganta da kayan sojoji,no wonder nake tunanin kaman na taba ganinta a barrack mana”
Wani duka brr na’imah ta kaiwa lubnah,dukkuwa da halin da take ciki.
“Nikam mai yasamu rayuwata na haɗu da dolayen ƴaƴane?
Tsohuwar maƙiyarki kina zaune da ita amma baki sani ba,har saida tagama dake kaff,Tazo da daɗi ma da bata barki kinyi watan ba,saikije ki wanke wannan dauɗar kana kici abinci.”
Cikeda takaici ta wuce ɗakinta,ko ammar bata kalla ba wanda yake zaune akan kujera ya mimmiƙe ƙafafu.
Tana tunanin tasan kan matsalar ashe duk ba haka bane,koda yake itama bombee bazata gagareta ba,abinda yafi bata mamaki shine ya akayi taje gidan ƴar ta a matsayin kishiyarta batareda tasani ba,yarinyar da shari’a take nemanta itace take cikin garin hankali kwance,kuma harda sace mata ƴaƴa,duk yadda akayi fansa takeson dauka ta hanyar katse mata burinta na mallakar JAAN Company’.
Ihun da lubnah ta kwarara da safene yasakata firgit tatashi ta nufi dakin nata da sauri,bata ganta a dakin ba dan haka ta shiga banɗaki inda take jiyo kukannata.
A tsaye take a bakin sink tana kallon wani ruwa mai kauri da wari kalar ruwan ɗorawa,wanda yake fita daga ƙasanta.
Itama brr na’imah wacce take bayanta saurin toshe hancinta tayi tareda girgiza kai.
“Ba haka bane,hakan bazata sabu ba,ai baki cika wata gudan ba,bahaka mukayi da Zilliyyah ba,mai yasa haka zata faru”
Komawa dabaya take tana maimaita duk abinda yazo bakinta,har bata saniba tayi tuntube ta drawer gaffo.
Miƙewa tayi batareda duba gurdiyar datayi ba tayi hanyar ɗakinta.
Gen abdu manga ta tarar a zaune a tsakiyar gado yayi haɗa kai da gwiwa yana kuka tamkar ƙaramin yaro.
Magana brr na’imah tayimasa amma ko kulata bayyi ba,abinda ya faɗane taji tamkar notin kanta ya kunce.
“Na’imah kincuceni duniya da lahira,Allah ne kaɗai zaimin hisabi dake ranar gobe ƙiyama,kin zalunceni,kin rabani da aminina Bello,kinsaka naci amanarsa na zalunceshi na kashe masa ɗan sa,yarinyar da bataji bata ganiba kinsaka na ɗora mata laifin da bata aikata ba,aminina yariƙe ta amana,amma saida kika saka ya koreta daga gareshi a matsayin wacce ta kashe masa dansa.
Hakan bai isheki ba saida kika sakani farmakar dukiyar surukina Na’imah,nikuwa mai nene bakimin ba,Allah saiki innata saida tace kada na aureki tun farko,amma nayi kunnen uwar shegu da ita,ni a dole inasonki,yanzu mai gari ya waya damai na amfana a zamana dake.
Wannan iya abinda nasani kenan,wanda bansani ba bila adadinne nasan”
Komawa tayi da sanɗa da bar ɗakin batareda tayi magana ba,dan batada amsar waɗannan maganganunnasa,tabbas akwai gagarumar matsala indai aikin kansa ne ya kwance.
Ɗakin data ajiye madubinta ta nufah,tana yaye ƙyallen dayake jiki da kalli hotonta a tsaye a ciki kamar kowanne sauran madubai.
Sab’anin da dazata ga duhu baƙiƙƙirin,inata saka hayaƙi sai Zilliyyah ta bayyana.
Bata daddara ba hayaƙin da dauka ta banga,saida suka kare tass batareda madubin yayi komai ba.
Wani duka takai masa da ƙafa saida ya tawarwatse gabaɗaya.
Kaman lubnah itama zaman durshan tayi a wajen tana nata kukan,zagi kuwa sa tsinuwa babu wanda batayiwa Zilliyyah ba,gashi banda ƙaiƙayi babu abinda jikinta yakeyi,saidai ba kamar wanda zai zautata ba.
“Mommy ni……nikam zan koma gida wajen Jabeer….inaga idan naganshi komai zai dawo daidai”
Tana kukanne take maganar.
Ɗan tsayawa brr na’imah tayi da kukan tareda cewa.
“Yakikayi da ruwan dayake zubowan ya daina?”
“Ahah bai dainaba ƙunzugu nayi,idan naje gida saina wanke nasake saka wani,in yaciba a haka nashiga uku mommy nikam duk yadda za’ayi ma kiyi wannan masifar ta daina fitomin”
Bata maida mata martanin maganar ba,dan intace tanada abincewa ma tayi ƙarya,maida gabanta tasakeyi inda madubin yafashe yanzu,tanajin lubnah ta tada mota tabar gidan.
Cikin sanɗa ta fita daga motarta tashige sashenta,lokacin data shiga ɗakin Jabeer yana kwance a falo yana bacci,mamaki abin yabawa lubnah,saidai bata ce komai ba zage tashiga banɗaki,domin cire ƙunzugun dayake jikinta.
Wasu kayan ta sanja tasake fitowa falon,har sannan yana nan kwance a inda tabarshi,matsawa inda yake tayi tareda bubbuga bayansa.
“Honey lafiya kake bacci anan,duk saboda kana jirana na dawo koh,gani na dawo tashi ka ganni”
Tashi Jabeer yayi yana mutstsika ido tareda ƙarewa inda yake kallo.
“Anan nayi bacci?”
“Uhm yanzu nadawo naganka a wajen a kwance,common i miss you”
Lubnah ta ƙarisa maganar tana ƙoƙarin rungume Jabeer”
Saurin tureta yayi daga jikinsa yana mata kallon bakida hankali.
“Ya isa haka lubnah,duk abinda kikayi bai isheki ba har yanzu,kijira dawowata ki karbi sakamakonki,abin yatsaya kuma iya haka”
Miƙewa yayi tsaye ko kallonta bai sakeyi ba yashiga part ɗinsa ta falonnata.
Banɗaki ya shiga ya dauro alwala,yana share hawaye ya tada sallahr asubar da bayyi ba,bayan yagama yadaɗe yana kuka akan sallayar kafin ya tashi.
Babu abinda ya faɗo masa a rai sai Jaleelah,gwanda ma Jawaheer ita gidan ba baƙonta bane,amma ita fah babu wanda tasani a gidan saishi,amma haka ya ɗauke kansa tamkar bai santa ba sanadiyyar lubnah,koya takeji oho?
Yasan a yanzu tana matuƙar jin haushinsa ba kaɗan ba.
Naɗe sallayar yayi da sauri ya nufi sashenta,ko kulawa da neman abinda zai saka a cikinsa bayyi ba,gashi rana tayi sosai sha biyu takusa.
Murɗa ƙofar sashenta yayi ya shiga,rabonsa da taka wajen tun wata uku dasuka wuce.
Zaro ido yayi yana sake mutstsikawa,ko har yanzu bai farka daga mafarki bane kai?
Domin shidai yasan bahaka yasan falonnata ba,wanda a yanzu yake dauke da wasu danƙara danƙaran funitures da ba iya a nigeria bama anaji dasu.
Ma’aikata kusan ukune suke kai kawo a falon,kaman sansanin ƴar sarki,wata nasaka turaren ƙamshi,wata na gyara labulayen falon,wata kuma sai mopping ɗin falon take da wata na’ura mai matuƙar tsada.
Basu taba tsammanin wani zai shigo daga ƙofar dayake tsaye ba,dan haka ko kulada shi basuyi ba saida yayi gyaran murya tukunna.
Dukkansu zubewa sukai suna gaisheshi,duk da kana ganin mamaki ƙarara akan fuskarsu na ganinsa a sashen.
“Jaleelah fah tana ina,kota sanja sashene?
“Ahah Hajiya Jaleelah tana sashen Jawaheer yau”
“Sashen Jawaheer kuma?,mai tajeyi can kuma?”
“Uhm idan suka yi kwana ɗaya anan washagari kuma can suke zuwa ranka ya daɗe”
Abin yasha masa kai,saidai bai sake tambayarsu ba ya nufi sashen Jawaheer ɗin.
Yanda na Jaleelah yake itama hakan nata yake sakk iri ɗaya,kala ne kawai ta bambamtasu,saidai nan tsitt kakeji babu alamar sawun masu aiki.
Ɗakinta ya nufah,batareda yayi magana ba ya buɗe,dan duk a zatonsa hade kai sukayi suna mutunci,tunda ya ɗauke musu ƙafah,duk sai yaji yanajin haushin kansa gameda abinda ya faru…….
Tunanin dayakeyi yatsayar dashi cakk sakamakon abinda yayi arba dashi a ɗakin.
Ɗakin har yafi falon ƙwatuwa da kuma kaya masu tsada,wannan shine abin burgewar ɗakin,abin takaicin kuma wanda ya riski Jabeer dabai taba tunanin sa a mafarki ba shine ganin amarennasa a gado ɗaya tsirara haihuwa uwarsu suna masha’a.
Sun wani kanannaɗe tamkar macijai a waje ɗaya,deep kiss suke aikawa junansu,sai bayan sun raba bakinsu kafin Jawaheer ta shafi fuskar Jaleelah.
“My reddish slender i love you,ina sanki fiyeda komai nawa,ni nafi ganinki a ja maimakon baƙa……..bantaba tunani ba ko a mafarki wai zan haɗu dake ido da ido kuma a waje ɗaya”
Hannun Jawaheer da kama tasaka a bakinta tana tsotsa,saida tacire kafin ta ɗora da cewar.
“Uhmmm nima haɗuwa ta dake is my blessing,saboda a lokacinne na koyi yanda zanfito da maƙudan kuɗaɗena nayi facaka dasu,abinda yafi bani dariya dake,shine yanda kike nuna kishina a dubai idan Jabeer yajani ɗaki.
Wow i love this side of you my lady,shifa yayi zaton sonsa nake koh???”
Dariya suka saka a tare,kana suka sake haɗewa waje daya.
Gabaɗaya basu kulada Jabeer ba wanda yake tsaye akansu jikinsa yana rawa.
Jijjiga kai yake saboda wani duhu dayake gani,lokacin daya samu kallonsa ya dawo daidai ɗakinsa ya koma da gudu.
Drawer dayake zuba magunguna ya buɗe,amma babu koɗaya a ciki,da alama bombee ce ta ɗebesu..
Gwauron numfashi yaja mai zafi yana murza kai,ganin abin bazai kaishi ba ya dauki makullan motarsa yanufi waje dasauri.
Ko gama bawa motar wuta bayyi ba yafigeta ya fice a gidan.

*** ***
Da farin silin ta haɗa ido lokacin data farfaɗo akan gadon asibitin.
Tashi tayi ta zauna tareda fige ruwan dayake shiga cikin jikinta.
Hilyan ce ta taso da sauri daga kan kujerar tanufo inda take.
“Anty mar….”
“”Karfe nawa ne yanzu?”
“Uhm 12:30 ne”
“Ina inna tatashi kuwa?”
“Ahah bata tashi ba har yanzu,amma itama daidai lokacin dakika faɗi sanann ta suma”
“Maza tayarmin da motata yanzunnan barina gyara nafito mu tafi gida,nasan tana wajen da za’a kulada ita,Jabeer yana gida maybe zuwa yanzu nasan shima yatashi”
Daga kai kawai hilyan tayi tareda fita waje,abinka da jinin sojoji koda ya daskare,tun kafin tagama fitoda motar a wajen parking harta shiga wajen drivern ta karba a hannun hilyan.
Figar motar tayi da gudu zuwa gida,daidai zuwa shigar motar taga mota ta fita a gidan a guje kaman mai shirin tashi sama,bata kulada da waye ba tasaka kan tata motar zuwa ciki.
A bakin sashen su tayi parking,bata shiga part ɗintaba don tasan koda yajema to zaiga bata nan,lubnah kuwa tayi zaton tana gidansu,dan tasan zuwa yanzu taga sakamako.
Sashen Jaleelah ta nufah da sauri ko yaje can.
Masu aiki ta tarar suna ta goge,gaisheta sukayi,bata amsa ba saima jefa musu tambaya da tayi.
“Jabeer yashigo nan kuwa yanzu?”
“Eh yashigo ranki ya daɗe,saidai da mukace masa Hajiyah Jaleelah tana sashen Jawaheer to ya tafi can”
‘Tabb Allah yasa bayyi mugun gamo ba ameen’
Tafada a ranta,cikin sanyin jiki ta nufi sashen Jawaheer ɗin,abinda take gudu shiya faru,domin tun a daga falon ta hango ƙofar ɗakinta a buɗe yanda ya barta,ga nan center table ya goce inda yayi hanya yabar falon.
Waya da ɗauka ta ƙira Security office na bakin get.
“Hello motar danayi clear da ita a bakin get wanene a ciki?”
“Ranki ya daɗe ogah Jabeer ne a ciki,kuma da alama baya cikin yanayi mai dadai,domin a zuciye ya bamu umarnin bude get ɗin”
“Kuma da kukaga haka babu wanda kuka ƙira koh?”
“Kiyi……”
Ƙitt ta kashe ƙiran tareda jan zuciya.
A zuciye ta karisa ɗakin da su Jawaheer tareda jingina a jikin ƙofar tana kallonsu.
Ganin basu san ma tana tsaye ba yasata yin tafi guda uku da hannunta.
“Hii less ladies the plessure has stopped,everything you did is on the camera”
(Barka yan mata,daɗi ya ƙare,komai kukayi yana cikin camera!!!)

Page 🖤 49••50🖤

Rawa jikinsu ya fara suna neman abinda zasu tare jikinsu dashi.
Duk abinda suke bombee tana kallonsu daga inda ta jijgina
“Miye kuke wani karkarwa,ohh da bakusan ba daidai kuke aikatawa ba sai yanzu,ai bakuji komai bama tukunna sai kunji wanene yaganku a haka yanzu.
Mijinku yazo yana murna da farincikin faɗawa masoyiyarsa ya warke,gashi ya dawo gareta,amma mai zai tarar,a kwance yaganta da fitsara da kishiyarta,wato ɗaya matar tasa,shin idan kune wanne hali zaku shiga in kuka ga haka….?”
Shuru sukayi suna saurarenta,zuwa yanzu kowa ta samu towel ta ɗaura a jikinta,wayarta ta danna,can saiga hilyan tashigo ɗakin.
“Kinzo da bulalar?”
“Eh nazo ta ita,gata ma a hannuna,mai suka sata haka? Rabonki dayin amfani da ita kin daɗe sai yau”
“Ba surutu na tsayayi ba anan wajen,na turawa security da khmees kan su bi bayansa nizan tafi naga mai yake faruwa.
Ki tabbatar kinwa ko waccensu bulala ɗari ɗari,bayan sun gama su gyara kaff ilahirin part ɗinnan gabaɗaya,idan suka gama su wankemin kayana gabaɗaya,daga nan kuma zan faɗi abinda zasuyi gaba.”
Har zata fita ta dawo ta kallesu,wanda idonsu ya raina fata.
“Jawaheer ce ta samu ƙarfin halin cewar”
“Mai kike nufi?”
“Bayi bayi kuka zama,da mai kuke tunani sai kawai naje nace ga abinda kukayi,ahah ahah wannan bazai faruba,ni dama na daɗe da sanin abinda kuke,hatta kadarorinku da su asusun bnakinku na sirri duk nasani,sannan kaff sashenku a cike yake dam da camerori wanda sukeyimin record na abinda kuke aikawa.
To ko iya haka na barku kunsan kuna hannuna,laifinku na cin amanar mijinku da sakashi cikin wani yanayi zaku girba.
Hilyan ki cika aikinki,sannan kibasu takardun dukka dukiyoyin da suka tara harda na banki suyimin sign kafin na dawo,duk kuma wacce ta kuskura ta saka ƙafa tabar gidannan batareda izinina ba,hmmmm ta kaɗe har ganye,sannan kuma yana gareku ku bari danginku su ɗau matakin abinda zanyi muku,a ranar zan shaida musu mai kuke.
Hilyan a cigaba da gashi”
Ƙirane ya shigo wayarta,dan haka da sauri ta fita tana magana.
“Me kun bishi baku ganshi ba har yanzu?”
“Ehhh har yanzu fah madam bamu ganshi ba,saidai cctv cameran da muka bi ya nuna cewar hanyar barin gari yabi”
Kashe wayar tayi tareda dannawa khmees ƙira,shima dai har yanzu dai babu wata kafa.
Duba lokaci tayi har an kusa yin la’asar,daga inda take tsaye a falonta tana jiyo ihun su Jawaheer waɗanda suke cin kakarsu a hannun matashiyar sojan.
Ɗakinta ta nufah ta ɗauko wasu takardu ta nufi sashen Hajiyah Zeenah.
Tundaga bakin falon take jiyo maganarsu da kuma ƙarar cokala.
A zaune suke a dinning tunda ga kan alhj aliyu har dasu Abdulmaleek,kasancewar yau juma’a dama tare suke cin abinci idan an saƙƙo a masallaci.
Ƙare musu kallo tayi na takaici kafin ta nufi wajen dinning ɗin ko sallama babu.
Gaban Hajiyah Zeenah taje tayi dire mata takardun dasuke hannunta..
“Sign”
Ta wulla mata biro tana kallonta,itama Hajiyah Zeenah kallon bombee take cikeda mamaki.
“Baki gane takardun bane ko kuma nayi miki bayani tukunna”
“Amma…….”
“Nagama miki aikinki,in baki yarda ba kije sashenta ki ganta da idonki,nice nan nayi kidnapping ɗinta dama bakowa ba,dan haka gatacan na dawo da ita sashenta.
Ɗaiɗaita rayuwarta kikasakani nayi tayanda zata buƙaci saki daga wajen ɗanki da kanta,yanzu ba iya wannan nayi ba,harda karya asirin datayimsa nayi.
Dan haka nina gama aikina a wannan gidan da a waje yakeda kyau amma cikinsa kurkune..
Kin haɗa familynki kuna cin abinci cikin kwanciyar hankali,batareda kinsan inda babban ɗannaki yake ba tun safe,ni kuwa anya ma kece uwarsa? Da alama bakya neman inda yake sai zakiyimasa aure ko kuma zai kulamiki da dukiyar gidan.
Nizan tafi daga nan,mun gama aiki dake tunda na cika aiki,jan jira idan kika samo ɗanki daya fita daga gida dun sassafe a zauce sai ki tambayeshi ya sakeni,inkuma takaicin duniya ya kasheshi matan dakika auramasa kuma sai nayi takaba..
Ga waɗannan takardun(ta faɗa tana sake wulla mata wasu takardun)
“Share ne na Companyn ku dayake hannun brr na’imah,wacce ta daɗe tana shiri na karbar sa daga hannunku,nasakata ta fanshesu da ƴaƴan ta.
Ba iya ita kaɗaiba a kwai sauran mutane irinta masu son Companyn,ni yanzu zan tafi ga nawa iyalan sun jirana,ruwanku ku ɗau matakin da kuma nemo halinda ɗanku yake ciki”
Wani kallo tabi dukkan table ɗin dashi kafin tafita daga cikin falon a zuciye.
Yanda kasan ruwa yazo ya cinye falon haka sukayi.
Dan jin maganganun bombee sukayi kaman a mafarki,lokaci ɗaya kuma suka fara ƙoƙarin yadda zasuyi.
Hajiyah Zeenah kuwa wacce takula da hankalin su yabar kanta,ɗakinta ta wuce da sauri tana yarfe gumin dayake zubo mata,shikenan bombee ta gama da ita a cikin iyalanta,yanzu kowa yasan abinda ta aikata,dama kuwa saida alhj Aliyu ya faɗamata cewar zatayi nadamar kawo bombee cikin gidanta.

A bangaren uwar gayyar kuwa direct gidan malamin ta nufa inda mahaifiyar ta take.
A zaune taka akan gado wata mata tana bata shayi a baki,gefenta kuma Inayah ce da innayi suna riƙe da hannayenta ta kowanne bangare.
Tsaida kallonta tayi akan ƙofar inda bombee take tsaye,kana ganin kallon kasan ta dade batayi ba,saidai ta alama tagane ƴar tata sosai.
Hawayene yake zubowa akan kumatun bombee,sai yau tasamu hawayen ta suka zubo,bayan wasu shekaru dasuka shuɗe an hanata sakinsu daga jikinta..
Zubewa tayi a gaban innar tata cikin karayar zuciya,kanta ta ɗora a cinyarta,take kuwa tafara rabzar kuka kaman anyi mata saqon mutuwa,saidai kanajin kukan kasan irin wanda mutum ya daɗe yana tarawa ne.
Ganin hakanne yasa su Inayah da matar da take bata abincin barin ɗakin da sauri,domin su bawa ƴar da uwar waje.
Saida inna Danejo ta barta tasha kukanta kafin ta ɗora hannunta akan bayanta tana bubbugawa.
“Bbb…….bommbeee”
Tafaɗa a hankali cikin ƙaramar murya,kamar mai son koyon magana.
“Inna inna ta kin ƙira sunana innata”
Ɗagowa tayi da fuskar shabe shabe da hawaye tanayiwa inna Danejo dariyah..
Hannu tasaka tana share mata hawayen tareda girgiza kai,alamar ta daina kukan..
“Idan bakyaso na daina bazan sake ba,ya jikinnaki bakyajin wani ciwo koh?”
“Babu abinda nakeji bombee……..kawai kawai bansaba ne ba dayin amfani da wasu wuraren”
“Zaki saba a sannu inna,komai zai wuce kamar bai faruba,duk wanda yace zai sake tabaki bazan barshi ba kowaye inna”
“Uhm naji,to kinci abinci yanzun,an sameshi mijinnaki?”
Jimm bombee tayi jin tambayar da ta aikamata,a ranta tana ƙiran sunan Inayah,tasan ita tafaɗamata mai yake faruwa.
“Ahah ba’a ganshi ba,karki damu inna zasu ganshi na gama abinda yasani zama dashi,yanzu babu komai tsanina dashi”
“Amm…..”
“Inna yakamata ki huta,yanzu kika tashi bai kamata ki dunga damun kanki ba har haka ”
Zama tayi a wajen tana kallonta,har saida ta koma baccin kafin tabar ɗakin..
Falo takoma inda su Inayah suke zaune.
“Yah innan take?”
Innayi ta tambaya cikeda zumuɗi.
“Ta yi bacci kafin na fito”
“Yah Jabeer ɗin kuwa an sameshi,yansu maleekah ma taƙirmu wai gatanan zuwa,da alama bata sani ba sai yanzu”
“Uhm dukka basu sani ba gidan,saida zan fito na faɗamusu,ki daina yimin zancensa haka,yanzu dai kawomin abinci naci nayi wanka kafin na faɗa..
Inna gama shiryawa zamu yiwa malam godiya mu tafi gida”
A cewarta ta rabu da sha’aninsu,amma lokaci zuwa lokaci sai duba waya take,domin ganin ko an ƙirata.
Duk abinda take a cikin motar kowa na kulada ita har suka isa gida.
Har suka isa gida dare yafari amma babu labarin Jabeer ba ɗuriyarsa,ƙiran waya daga wajenta tayi recieving sunfi sau a ƙirga.
A gidansu Jabeer kuwa duk sun taru a falon sayyada-tateen,kowa yayi jugum da abinda yake tunani.
Takaicin ɗaya ma yanda iyab sayyada ta cika musu kunne da surutu.
“Ohh ni sayyada ina jabeeru yashi ga a garinnan haka,anyi nema har angode Allah?”
“Hmmm nifa nafi zargin Wannan matar tasace ta ɗaukeshi,ba tace ita taɗauke lubnah bama,kuga fah irin azabar data ganawa sauran matan ma,duk yanda akayi dasu su fito daga ƙofar akaisu asibiti sunƙi wai ta hanasu fita?
Saida kuma ya bata lokaci guda ta ɗauke ƙafarta tabar gidan”
Lailah ce tayi maganar wanda suke zaune kujera ɗaya da Madeenah a falon.
Duk falon shuru akayi ana jin maganar Lailah,da alama kuma wasu dayawa a falon sun fara gasgata maganar tata,musamman duba da yanda ta zuba musu tujara ɗazu.
“Haba anty Lailah,wlh anty maryam bazata sace yah Jabeer ba,wannan wanne irin zancene?”
“Ke dallah rufemin baki,yanzu haka wani abun take baki a sashenta ta shanyeki kema,gashinan ta sakaki kina kaimata rohoton duk abinda yake faruwa a gidannan.
Ni wlh nafara yarda da zancen anty Lailah”
Madeenah ce tayi maganar tana hararar maleekah,yayinda ita kuma take kallon Lailah,jitake kamar ta tona mata asirin abinda take,amma tasan inta faɗa a yanzu batada hujja.
Tashi tayi daga falon ta nufi sashensu,dan tasan duk tarom da akayi a wajen babu abinda yake tsinanawa Jabeer ɗin,ƙarshema Lailah wata dama tasamu a wajen na yaɗa manufarta.
Ƙiran bombee tayi tashaida mata abinda ake a gidan,daga baya kuma tayi ta roƙonta akan ta dawo,saidai har sannan babu wata tsayayyar makafa.
“Dan allah anty maryam kidawo,nasan idan sunga dawowarki zasu daina yimiki wannan zargin,amma idan har kika tafi a yanzu za’a ce da hannunki a batansa”
“Ohh saboda ba’aga fitarsa ba kome,to duk mai cewa na dawoɗin kada ya fasa”
“Kiyi haƙuri amma gobe zanzo gidan,kema nasan kinaso ki dawo anty Maryam”

Tana cikin cin abinci taji falon yayi tsitt,kowa ita yake kallo,ganin yanda take zuba abincin kaman magani. Duk da cewar taki yarda amma duk wanda yakalleta yasan tana cikin damuwa,wanda duk bazai rasa nasaba da bacewar mijinnata ba yau kwana guda.
Jiyama da daddaren hanya ta sanɗa tafita da mota,amma haka ta dawo batareda sanin inda yake ba.
Tunda tatashi har yanzu babu wanda tayiwa magana bayan gaisawar da sukayi da inna Danejo.
Maleekah ma data fito tana kallonta amma batayimata magana ba,kaman bata santa ba.
“Maryam inkin gama cin abincin inason yin magana dake….kafin sannan ke innayi haɗo mata kayanta ta tafi yau zata koma gidanta”
“Amma inna bakiji mai maleekah ta faɗa bane,duk abinda nayimasa wai zargina suke da saceshi”
“Uhm suda suke zarginki shiya zargeki,koda shiya zargeki ai badan shi zakiyiba saidan wanda ya baki umarnin yi. Balanta mijinki a yanzu yana buƙatar komawar ki gidanki,dan haka kishirya ki tafi gidanki,dama tunda dan banida ikon cewa komaine lokacin dakikace wai auren wucin gadi kikayi,da kinsani bazan barki ba sam.
Aure ba abin wasa bane dazaki sakashi lokacin dakika ga dama kuma daga baya ki cireshi.
Sannan banda kin maida mutane shakatafi zatonki waye baisan abinda kike ba,kowa yaganki yaga damuwa ƙarara a fuskarki dason sa a idonki,kawai taurin kai ne yahanaki rungumar hakan.
Indan tani kika ƙi komawa ma to ki manta,dan nan da sati guda wajen nawa mijin zankoma tunda na warke,niba kebace mai juyawa miji baya”
Zumburo baki bombee tayi tareda sunkuyar dakai tana kallon kwanon abincin,ai shikenan kuma yanzu babu freedom.
“Ehh inna wai kina nufin gembu zaki koma?,ai basai kin je ba,nanda jibi ma baba suna tahowa shida muruje,na turamusu kuɗin motama tun a jiyan”
“Ya taho kuma? addah laari fah?”
“Har yanzu baki daina maganar ta,ita kam ai ta daɗe a ƙyauyensu tuntuni,a can take wai ƴan uwanta suna mata magani”
Takarisa maganar irin bata dame taba.
Hannu inna Danejo ta miƙawa bombee tareda cewa.
“Kinci gidanku nan,wai yaushe zakiyi hankali ne kina babba,nakula babu abinda kika koya a wannan shekarun sai yanda zaki kama wancan ki yiwa wancan barazana koh?”
“Ohh inna to shikenan naji ki daina wannan faɗan kada ki samu matsala mana,Naji zan koma amma dole sai an sameshi tukunna inna,idan ba’a ganshi ba babu amfanin komawa ta.
Yanzu dai ke ishashshiya kinyi nasara,saiki tashi mutafi ko na ɗauko kayan haidar a gida na dawo”
Taƙarisa maganar tana hararar maleekah,wacce take ta dariyar komawar bombee.
“Wow you are the best inna,ke kaɗai ce mai tanƙwasa mana ogah,idan ta kafe akan ra’ayinta bata sanjashi da wuri”

Har suka isa gidan bombee batacewa Maleekah komai ba,tana yin parking ta shige sashenta.
Itadai banda dariya babu abinda take yiwa matar yayannata.
Kayan haidar ta haɗa a ƙaramin trolly ɗinsa,har tazo fita saikuma ta juya wajen drawer da take ajiye abubuwa muhimmai aciki,harda su takardun Jabeer masu amfani da kuma nata..
Magungunan data ɗebo a ɗakinsa rannan tagani a ciki,tana cewa zata tsaya tayi bincike akan namenene har yanzu bata samu dama ba,saidai haka kawai jikinta yake bata bana lafiya bane.
Ɗaukar su tayi tana duddubawa,wata takarda ce ta faɗo a ciki kaman ta gida.
Ɗauka tayi tana nazarinta,lokaci ɗaya wani abu ya faɗo mata,da alama wannan gidan nasane tunda ga sunansa a jiki,sannan a cctv camera tanuna hanyar barin gari yabi,wannan address ɗin shima ba’a gari yake ba..
Saurin maida takardun tayi ta rufe tareda zarar key ɗin motarta,indai ba ɗaukeshi akayi ba kokuma yayi hatsari,to lallai yana can.
A ƙanƙanin lokaci ta isa gidan saboda gudun datakeyi.
Wata ajiyar zuciya tasaki lokacin da taga motarsa a wajen parking na gidan.
Ƙofar falon ta tura a hankali ta shiga,tsitt kakeji kaman babu mutum a cikin gidan.
Wucewa falon tayi ta nufi ɗakin dataganshi a buɗe.
Tun a baƙin ƙofar tafara cin karo da fankunan magani,hadda ƙwayoyin maganin irin wanda ta boye a gida.
Duk anyi zubar dasu birjik a cikin ɗakin.
Zaro ido tayi tareda rufe baki,ganin Jabeer a sheme a ƙasa bakinsa yayi shuɗi(blue)kumfar datayi fita daga bakinsa ta bushe,da alama ba sannan tafara fitowa ba.
Zaman durshen tayi tareda ɗagoshi jikinta tana jijjigashi,ta ƙira sunansa yafi sau a ƙirga amma shuru kaman maye yaci shirwa.
Ƙarar wayarsa tagani da alama ƙira yana shigowa,kuma wayar ba wacce yake amfani da ita bace,sunan data gani a jikine yasakata saurin ɗagawa har tana shirin sakinta a ƙasa.
(My doctor)
“H….ello”
“Hello hello ina Jabeer ɗin yake lafiya ƙalau kuwa yake,jiya naga ƙiransa da daddare,kuma naji numfashinsa yana ƙasa da sama,kuna ina yanzu haka”
“Muna…..amm wani gidansa ne nima sai yanzu na ganshi tun jiyan,yanxu haka baya motsi,bakinsa sai kumfa yakeyi”
“Innalillahi yanzu maza ki kawoshi General hospital,neorological ward yanzu yanzunnnan akwai problem babba”
Yana gama faɗamata hakan yakashe wayar.
Tashin hankali ba’a saka masa rana,bayan ta ajiye wayar rasa ma mai zatayi tayi,hatta fatar bakinta ma rawa takeyi.
Kinkimarsa tayi a jikin kafaɗarta ta fito dashi daga gidan,buɗe bayan motar tayo tana nishi tana komai tasakashi a ciki.
Babu bata lokaci tayi asibitin nan ma da wani gudun
Tun kafin su isa dama doctorn nasa ya shiryah tarbarsu,dan haka direct emergency akayi dashi babu bata lokaci.
Sai bayan an shiga dashi kafin ta tuna da wani abu waishi ƙiran wayar familynsa.

Page 🖤 51••52🖤

Maleekah ta ƙira ta shaida mata tafaɗawa ilahirin gidannasu halinda ake ciki.
Tana kashewa wayar khmees ta ƙira shima tafaɗamasa halinda ake ciki.
Daga nan tacigaba da safa da marwa tana jiran fitowar doctorn domin jin mai yake faruwa.

*** ***

“Mommy mommy”
Tun kafin ta ƙariso sashen take sabga musu ƙira da waya a hannunta.
“Menene kike zabgamin ƙira kaman wata sabuwar makahuwa,kibarni naji da abinda yake damuna ma”
“Mommy anty maryam tasamo yah Jabeer,saidai lokacin data ganshi a sume yake,yanzu haka wai suna general hospital anshiga dashi emergency”
“What hospital kuma,maza-maza shiga ki ɗauko min mayafina,barina ƙira su abdul na faɗamusu,shikamma abdulkareem ai yana asibitin,barina fara faɗamasa”
Cikin sauri jikinta har rawa yake tafara danne dannen wayar,yayinda itakuma maleekah tashiga ɗauko mata mayafin.

Suna gama wayar ya nufo emergency ɗin daga ward ɗinsu,tun a bakin room ɗin yahango bombee wacce take ta safa da marwa tana cizan yatsa,ajima ta zauna saikuma tasake tashi. Kana ganinta kasan tarasa mai zatayi ne.
A hankali yake tafiya har ya isa inda take,sallama yayi mata amma sam batajishi ba,gabaɗaya hankalin ta baya cikin kanta.
Maimaita sallamar yasakeyi wannan karon da ɗan ƙarfi.
“Am likita ya ake ciki ya tashi, mai ya sameshi babu matsal…..”
Shuru tayi ta zancen tareda dafe kanta lokacin da taga ashe Abdulkareem ne ba doctorn datake jiraba.
“Ohh ashe kaine am sorry”
“Ahh no babu komai,amma dai ki kwantar da hankalin ki inshaallah zai samu lafiya,inkika cigaba dayin haka to kema zaki iya samun matsala,kowa yaganki yasan…..”
“Ba kayi haƙuri amma ba wannan bayanin nakenson ji ba,shin zaka iya dubomin mai yake faruwa,ta hakane kawai zan iya samun kwanciyar hankali”
“Okay to shikenan bari su abdul su iso kafin na tafi,kada na barki ke kaɗai a wajen,kicigaba da Addu’a Allah zai bada mafita inshaallah”
Shuru tayi daga haka batasake magana ba,har Abdulmaleek ne ya iso wajen shida maleekah da saurinsu.
“Yanaganku ku biyu ina mommah take?”
“Uhm ta tsaya jiran Sayyada-tateen wai dole saita jirata,nikuwa danaga haka nafaɗawa yah abdul.M mutaho tare.
Anty maryam yadai ya ake ciki,a ina kika sameshi ne uhm”
“A wajen da banyi tsammani ba kuma nayi tsammani”
Kallonta sukayi su ukun da mamakin maganar ta.
“Ba yanzu ne lokacin daya kamata ayi magana akan wannan ba,Abdulkareem kaine likita,akwai abinda Jabeer ya daɗe yana boyewa kowa,wanda kuma abune mai matuƙar muhimmanci,kasamu likitan dayake gani kuyi maganar dashi,na tabbatar abinda yake damunsa yanada nasaba da halinda yake ciki yanzu.
Ni kaɗai naga yanayin dayake ciki ku baku gani ba…….it’s so heartbroken”
Hawayen da maleekah take rikewa ne yazubo akan kuncinta,zama tayi a gefen bombee tareda rungumeta,wacce itama take ƙoƙarin wajen ganin zuciyartata bata karaya ba.

Kafin likitocin dasuka rufu akan Jabeer su fito,tuni bakin wajen ya cika da ɗumbin mutane,harda Hajiyah rabi da kuma gidansu Jaleelah wanda suma suka samu labarin kwanciyar tasa,banda ƴan wajen aiki dasuke ta zuwa.
Lokacin da likitocin suka fito daga ɗakin aikin su kansu saida sukayi mamakin yawan mutanen dasukayi dafifi a bakin wajen.
Cikeda damuwa babban likitan ya kallesu kafin yayi magana.
“Uhm dan allah wasu dayawa si ɗan yi gefe,bamason hayaniya a kuda nan wajen,sannan ina buƙatar wasu daga cikin familynsa na kusa zamuyi magana dasu”
Wannan ya kalli wannan,daga ƙarshe dai ƴan biyun ƙannennasa suka tashi domin bin bayan likitan,Hajiyah Zeenah ce ta tashi zata bi bayansu itama,dan dama tun ɗazu datazo batace komai ba tana takure a gefe,su kansu ƴaƴan tunda sukaji abinda tayi jiya babu wanda yayi mata magana.
“Am mommah dakin zauna basai kinzo ba,saboda zai iya yiyuwa abune da bai kamata kijiba a yanayin dakike,Anty maryam ke taso muje domin yakamata aje da matarsa”
Zabin Abdul.K yayi bayyiwa mutane da dama daɗi ba inka ɗauke maleekah saikuma su danginta wato su hilyan da innq Danejo.
Tashi tayi batareda tace komai ba tabi bayansu. A zaune suka samu likitan yana ɗan bubbuga biro akan benci,alamar yashiga tunani.
Sallam Dr.Abdulkareem yayi masa kafin suka ɗanyi magana ta likitoci.
Maganar serious Doctorn Jabeer ɗin yafara,dan haka dole sukayi shuru suna sauraransa
“Ehh wato da dafarko banyi niyyar faɗa muku abinda yake damunsa ba,amma tunda abin yazama haka dole ne na karyah rule na patient akan jinyarsa.
Jabeer yana ɗaukene da Matsala ta INSOMNIA,wato cutar da bata barin mutum yasamu bacci da dare batareda magani ba,ko kuma inya samu baccin ma to saiya tashi yajishi a gajiye tamkar bayyi ba.
Shekara uku dasuka wuce yazo shi gwaji nan wajena saboda matsalar cutar,wato lokacin da matarsa tabiyu ta mutu,a lokacin bata yi serious na sosai,amma saboda yawan tension dayake ciki da kuma fargaba a koda yaushe yasa dole muka ɗaurshi akan treatment.
Maimaikon dayana karbar kulawa tayi sauƙi sai abu daya cigaba da hawa,musamman ma a mutuwar matar sa ta uku,wanann lokacin saida muka sakashi bacci na tsawon sati guda kafin yake gane mutane sosai.
A nanne ma damu akan yasanar da familynsa abinda yake damunsa,amma duk da haka yaƙi amincewa,a cewarsa koda sunjin babu abinda zai sanja,musamman mahaifiyar sa haka taso ta ganshi kullum cikin aiki dakuma bin umarninta,koda kuwa hakan zai saka watarana ya faɗi ya gaza.
Magani nasanja masa zuwa wanda yafi nada ƙarfi kaɗan,saboda yadunga samun bacci ya wuce wannan stage ɗin na damuwar,saidai ba’a daɗe ba kuma wani tension ɗin shima yashigomasa wanda magance cutar yayi wuyah a lokacin.
Dan ma akwai lokacin dayazo yasameni yana farincikin yake faɗamin wai akwai matarsa da idan yana kwance a waje tareda ita ko kuma yashiga sashenta yana samun nutsuwa sosai,har yayi bacci batareda shan magani ba.
A lokacin ni kaina nayi murna da farinciki danaji haka,domin mun saba dashi sosai tamkar ɗan da na haifa.
Saidai me…..jiya da daddare nasamu ƙiran wayarsa yana magana numfashinsa yana fita sama sama,tun a lokacin naketa ƙiran wayarsa har Allah yasa ita matarsa maryam da ɗauka,to itace ta kawoshi asibiti ɗazu”
Tun kafin suce wani abun sukaji sautin kukan Hajiyah Zeenah a bakin ƙofah,da alama duk taji abinda likitan yafaɗa akan matsalar ɗannata,anya kuwa zata ƙira kanta da uwa kuwa,wannan abinda ta aikata har yaushe.
“To menene dalilin shiga wannan condition ɗin dayayi a yanzu,sannan me ya haifar masa hakan”
“Bansan dalilin daya sakashi shiga cikin wannan halin ba,amma koma mai menene babban abune sosai,sannan abinda ya haifar shine wanda zan faɗamuku dana ƙiraku……..
Matsalarsa tayi girma har ta taba masa ƙwaƙwalwa jini yashiga da wani position,sannan kuma yasha magani fiyeda overdose ma,aikin da muke akan sa tun ɗazu na cire toxin ɗin maganinne daga cikin jininsa.
Munyi nasarar yin hakan,saidai akwai aiki a gaba shine zamuyi masa tiyata akai mu zuqe jinin,hakan zai iya zuwa da abubuwa da yawa.
Idan munyi nasara zai tashi batareda ya manta komai ba,kuma inshaallah har matsalarsa ta rashin bacci zata kau.
Idan kuma aka samu akasin haka zai iya tashi,amma kuma zai rasa tunanin sa,inayayi yawa harda rasa hankali ake samu.
Sannan a kowanne bangare idan aka yi zai iya shiga coma wanda bamusan iyah Tsawon lokacin da zayyi ba yana kwance.
Kowanne possibility a ciki 50-50 ne”
“Idan kuma ba’ayi tiyatar ba kuma mai zai faru?”
Sai yanzu bombee tayi magana tun ɗazun datake wajen.
“Uhm idan ba’a yiba zamu sakashi ne a na’urar dazata dunga saka ƙwaƙwalwarsa bacci duk bayan wasu awanni,wanda hakan is no a solution”
“To kawai ayi tiyatar,na tabbatar inshaallah zai tashi lafiya,batun shiga coma kuma muna masa fatan kada ya shiga doguwa,zamuyi ta masa Addu’a har Allah yasa yasamu lafiya,akwai wanda suke jiran tashinsa,dan haka inshaallah zai tashi batareda matsala ba.
Ina kyautata zaton hakan,idan akwai wajen sign na matarsa ga bani nayi,inason barin wajennan”
Dukkansu basuce komai ba har likitan ya miƙa mata takardar.
Karba tayi cikeda dauriya,duk da kowa yana kulada yanda hannunta yake rawa..
Sign ɗin tayi cikin sanyin rai ta miƙa masa takardar ta fita a wajen,hannu tasaka da ɗauke ƙwallar hawayen da take shirin zubomata.
A bakin ƙofah ta samu Hajiyah Zeenah a zaune tana rabzar kuka,kaman bata ganta ba haka tawuce tabarta a wajen,haushi iya haushi take ji gameda ita,domin duk abinda yafaru da rayuwarsa tana da kaso mafi tsoka akai,shine dan munafurci tazo ta takure tana kuka..
Shirye shiryen tiyatar aka farayi bayan an biya maƙudan kuɗi,sai zuwa washagari zasuyi masa tiyatar,kafinnan jikinsa yayi relax ba kaman yanzu ba.
Sau ɗaya aka bawa su bombee damar su ganshi,shima kuma ta glass ɗin ƙofah ne,daga nan kowa aka bashi damar tafiya gida,domin basa buƙatar kowa ya shiga wajensa.
A gidan baya take a motar,dan yanzu batada ƙarfin tuƙa wani abu waishi mota.
Gidanta direct hilyan ta wuce da ita hadda su sukkansu,domin a halinda take cikin tana buƙatar zama a cikin mutane.
Wanka hilyan tasakata tayi tarama sallolin da ake binta kafin takawo mata abinci.
Nan ma daƙyar taci abincin sama sama,daganan ta kwanta bacci ya ɗauketa.
Tsakar dare bombee ta tashi ta ɗauro alwala tafara salloli,tun tanayi har jinkinta ya gaji da zauna,anan ma Addu’a tacigaba da zubawa kala kala,duk akan neman lafiya ne ga mijinnata,wanda yake gadon asibiti rai a hannun Allah..
Tun duru duru ba’a daɗe dayin sallahr asuba ba suka nufi asibitin,kasancewar da wuri za’a shiga tiyatar.
Duk da cewa ba magana zaimusu ba ko yasan suna wajen,amma ganinsa kafin ya turashi ɗakin ma abune da basaso ya wuce su.
Ƙarfe 7:00 am daidai aka gama shirya tiyatar,suna nan tsaye a corridor ɗin aka turoshi,duk jikinsa an sassaka igiyoyi.
Ƙuri sukayi masa da ido kaman idan suka ƙirfa zai bace,da haka suna kallo har aka shiga dashi ɗakin ƙofah taja tarufe.
Hajiyah Zeenah da sayyada-tateen a tare suka saki kuka suna zubewa a wajen.
Kowa a wajen bashida bakin faɗa musu suyi shuru,alhj Abdullahi ne ma wanda abin bai shigeshi sosai ba yake ƙoƙarin basu haƙuri,itakam Lailah batazo bama tun zuwan ta na jiya,a cewarta ɗanta itama bashida lafiya,intazo ma ba abinda zata ƙara ko kuma ta rage.

Ƙarfe shabiyu daidai aka gama tiyatar,kuma Alhamdulillah anyi nasara,yanzu kuma sai ya farfaɗo aga mai sakamako zai bayar,wanda dama shine tashin hankalin.
A tsawon wannan lokacin banda roƙon Allah da fatan nasara babu abinda dangin Jabeer sukeyi,duk abinda ake a asibitin har sannan su Jawaheer suna sashensu itada Jaleelah,kaman yanda bombee tace kada su kuskura su fito suna ciki,zama daƙyar tashi daƙyar,saboda izayar da hilyan take shuka musu,abinda da jiki irinna masu hutu,duk sun goje sun sanja kama,komai su sukeyi a sashen dan bombee takori duk wata mai aiki daga sashen.
Lubnah kuwa tunda taji ance Jabeer ya bata,kuma ta tabbatar lallai aikinda tayi masa ya karye,saita ɗauki abinda takeso na amfani ta nufi gidansu.
Nan ma gidannasu ba daɗi gareshi ba,shi ammar ya tattara yabar ƙasar ma gabaɗaya,daya gane cewar ashe uwarsa ta saida haihuwarsa akan buƙatarta,itakuma matarsa daya narke akan sonta ashe cikin wani take shirin laƙana masa.
Shikuwa gen abdu manga yarasa ma mai zaice da brr na’imah,kokuma mai zai mata a duniyar nan yahuce ko kuma yagyara abinda tasakashi aikatawa na tsawon lokaci.
Dan haka tsinuwa yayi mata ta uwa ta uba,dagannan ya ɗau kayansa yabar gidan bayan yayi mata saki uku.
Ita sakin dayayi mata bai dameta ba,halinda ƴaƴan ta suke ciki yafi komai tada mata hankali,gakuma wasu munanan halittu da suke hanata sakat a duk lokacin data rufe ido.
Ganin yadda gidan ya cakuɗe yasa lubnah yin hanyar nata ɗakin,kuka tayishi har gaji ta sallama.
Ko nan da nan bata zuwa,koyaushe tana kusada banɗaki,saboda abinda yake ciyayowa daga ƙasanta,duk batajin zafi yanzu yazamo da ƙyar take zama kuma take tashi.
Yanke shawara tayi kan zata sayarda gwalagwalanta ta tafi asibiti neman magani,wataƙil sai ta dace,duk da tasan cewar hakan abune mai matuƙar wahala.

Wasa wasa anyi kusan sati guda da yiwa Jabeer tiyata,amma har yanxu bai farfaɗo,tun suna saka rai da tashinsa har sun fara karaya.
Bombee ce da Hajiyah Zeenah a wajensa suna kulada shi,kaman juyawa ta kuma goge jiki.
“Yakamata ki koma gida kawai zan kuladashi,tunda ba idonsa biyu ba,babu wani aiki sosai.
A gida kuma Baba yana buƙatarki,tunda shima bayida cikekkiyar lafiyah”
“Bombee ce tayi maganar wacce take zaune a kujera tana duba wani abu a labtop ɗinta”
“Eh hakane kam mommah kizo mutafi tareda Abdulmaleek,kuma kinga abdulkareem ma yana nan zai dunga leƙosu,Abba yana gida daga shi sai Madeenah kawai”
Maleekah ce tayi maganar itama,dan tun jiya suke fama da ita ta tafi taƙi fafur..
Ga mamakinsu kuwa saita tashi ta ɗauki jakarta,bakin gadon Jabeer ɗin taje inda yake kwance kaman gawa.
“Kayi haƙuri nasan banida ikon daina zargin kaina amma……”
Bata karisa maganar ba maleekah taja hannunta suka fita waje,wacce itama hawayenne a fuskarta.
“Anty maryam mu zamu tafi,gobe ta sassafe zan dawo”
“Okay ba matsala maleekah”
Daga haka bata sake cewa komai ba har suka tafi,jin wajen yayi tsit daga ita sai numfashin ta,yasa ta ajiye system tareda nufar inda Jabeer yake kwance.
Rigar da take jikinsa ta cire tareda ɗakko lotion ɗin da ake goge masa jiki dashi.
Tana zubawa tana gogewa da tissue har saida tagama tass kafin tasanja masa wata rigar.
Kayan baccinta tasaka kana ta hau gadon gefensa ta kwanta..
Kallon gashin idonsa take wanda sukayi zarara,gani take kaman bacci yake zata ƙirashi ya amsa.
“Kada ka cire tsammani da dawowa garemu Jabeer,dan Allah katashi daga wannan baccin daka keyi,akwai mutane masu muhimmanci a rayuwarka da suke jiran wannan farkawar,inka tashi nayi alƙawarin faɗamaka duk wani abu dakake buƙatar sani daga gareni”
A haka tana sambatun a jikinsa har itama bacci ya ɗauketa.

*** ***
A zaune yake a zuba tagumi a gidannasa dake cikin barrack,abin duniya ya taru yayi masa yawa yarasa shin ta ina zai fara.
Sati guda kenan da barinsa gida,amma yanda yaga dare haka yake ganin rana batareda ya samu maslaha ba.
Ƙwanƙwasa ƙofar akayi daga waje,saida yaɗau wasu lokuta kafin yabawa mai ƙwanƙwasawar damar shigowa.
Gen sameerah ce tashigo Falon kanta a tsaye fuskar nan a murtuƙe.
“Sir”
“Samu waje ki zauna”
Takulada sauyawar shugabannata,saidai batace komai ba ta zauna domin taji mai zaice.
“Kimsamomin bayanan gameda Gen Muhammad Bello?”
“Eh nasamo sir,baya ƙasar nan yana India akan matsalar ciwon zuciyar dayake dashi,saidai iya ganin likita zayyi ya dawo.
Iyalansa kuma suna nan a garinnan cikin ƙoshin lafiya”
“Kin tabbatar baya ga haka babu abinda yake faruwa na matsala gameda su?”
“Ehh babu yallabai,amma mai yasa ka damu dashi dakuma halin da ake ciki”
“Saboda kinsani nima nasani mune sanadiyyar mutuwar ɗansa da kuma silar rashin lafiyarsa”
“Amma yallabai wannan abune daya faru da daɗewa,meyasa kake shirin dawo dashi baya?”.
“Saboda na gyara kuskuren dana aikata a bayan,zuwa gobe zan miƙa kaina dana iyalina a kotu har dake. Kan miyagun makaman da muke shigowa dasu,kisan Haidar ɗan gen muhammad,barazanar mu na karbar Companyn JAAN,samun babban matsayi ta gurbatacciyar hanya.
Ita kuma matata zan maka ta kotu kan laifinta na rufe mugayen laifuka da kuma yiwa gurbatattun ayyuka shaidar bogi,sannan kuma sun haɗa da kisan kishiyoyin ƴar ta har guda biyu da suka haɗa da ƴata suka aikata..
Kekuma naki laifin shine An haɗa hannu dake wajen yin wadannan ayyukan dukka.”
Tashi tayi ta tsaya tsaye tana kallon gen abdu,gabaɗaya takasa gasgata abinda kunnenta suka jiyo.
“Amma yallabai?”
“Karki ce komai,sannan kuma kada kiyi ƙoƙarin yin komai,gobe nida ke zamu ajiye uniform ɗinmmu na khaki,wani satin kuma zamu nufi kotu domin girbar abinda muka shuka,bayan barrack sun zartar mana da namu hukuncin.
Kike gidanki dayake nan ki zauna,domin na bada oder daga kin shigo kar kowa yabarki ki fita”
Jikinta rawa yake tana jijjiga kai,ko a mafarki bata taba tunanin haka rayuwarta zata ƙare lokaci guda ba. Kuma wai a kurkuku,duk bayan wannan abubuwan da tayi? Kai inaaa hakan bazai tana yiyuwa ba.
Tana nan ƙame kaman dutsi har yatashi yafita daga falon.

Page 🖤 53••54🖤

Tun kafin asuba bombee ta tashi,saida ta tabbatar ta gyara Jabeer kafin tashiga banɗaki ta ɗauro alwala.
Nafilfili tayi kafin lokacin da alfijir zai keto,yanzu tana iya yin ibadunta yanda takeso batareda ciwon kai ba,saidai fah halin rashin haƙuri da ƙin ɗaukar raini takula su sun zama a jininta suke.
Tana nan zaune akan sallayah har haske yafara shigowa ta windown ɗakin,tashi tayi ta nufi bakin gadon ta zauna,kaman ko yaushe haka yake a yanda take barshi kullum batareda ya motsaba.
Tsira masa ido tayi ƙyam ko ƙyaftawa batayi,ita kaɗai tasan tunanin datakeyi a cikin zuciyarta,burin a yanzu shine samun lafiyar mijinnata,komai ma idan zaizo daga bayane.
Zamewa tayi ta ɗora kanta akan ƙirjinsa,a haka bacci yasake ɗauketa tana saurare bugun zuciyarsa wanda sai lura take jiyowa a hankali,shikaɗai ne kullum hope ɗinta datake dashi na cewar zai tashi wata rana..
Hayaniyar dataji a ɗakinne yasaka ta farkawa,Hajiyah Zeenah ce da kuma su maleekah,wanda ganin inda ta kwanta yasaka su sosa ƙeya.
Ko a jikinta ta tashi ta nufi banɗaki,sai bayan ta kintsa kana tafito.
Ƙasa ƙasa ta gaisheda Hajiyah Zeenah yayinda itama a takaice ta amsa tareda tambayarta ya mai jikin.
Suna nan zaune suma su inna Danejo suka shigo,saidai wannan karon akwai sabin fuska guda biyu,wato ummaruje da kuma Malam Ahmadu.
Duk da bombee tasan da zuwannasa amma ganinnasa bayan tsawon lokaci saida yabata mamaki..
“Baba”
“Na’am bombee ta ykk ya jikin mijinnaki,naji duk labarin abinda ya faru a wajen innarki da daddare,sannu kinji”
Bombee bata bari ya ƙarisa ba ta faɗa jikinsa,so take tayi kuka amma kuma yanzu ba lokacin kuka bane,dan haka kawai tayi shuru luf a jikinsa,innayi ce itama tazo ta baya ta rungumesu,ita kam tayi ɗan kukanta.
Ƙaramin hannu bombee taji ta bayanta ya rungumeta,dariya tayi tareda juyawa ta ɗagoshi jikinta,ɗan ta farincikinta nata na kanta,wato haidar.
Daga shi tayi sama yana ƙyalƙyala dariyah,banda mamma ba abinda yake faɗa.
“Um boy hadda kai aka zo asibiti?”
Ajiye shi tayi ƙasa tana ƙoƙarin boye farincinkinta na ganin ahalinnata saboda halin da ake ciki.
Abdulmaleek ne wanda ya tsugunna tareda kamo hannun haidar wanda bombee ta ajiyeshi a lokacin.
Kallon hannayensa yake da alama akwai abinda yagani daya tuna masa abu,saidai kuma shigowar Hilyan sai ya katse masa hankali daga kan yaron.
Kallonta yake yana kallon abdulkareem ma wanda shima ita yake kallo kafin ya kalli hilyan ɗin.
A tsawon wannan watannin gabaɗaya da dagula musu lissafi,a rana ɗaya saisu haɗu da ita lokaci guda, a wurare daban da kaya daban,amma kuma idan su suna tare guda ɗaya suke gani,kuma duk saita kallesu tayi musu murmushi.
Sun kasa gane wanne siddabaru takeyi a tsakaninsu.

Kiftawa abdulkareem ido Abdulmaleek yayi kafin yayiwa hilyan alama da ido kan tazo.
Ba musu tabi bayansa zuwa corridorn dayake ɗan nesa da inda ɗakin Jabeer yake.
Suna nan tsaye baicemata komai ba,itama batayi magana ba har abdulkareem ya iso wajen.
“Uhm shin kinsan wannan”
Ƴar dariya hilyan tayi tana kallon Abdulmaleek ɗin,mai yasameshi kuma yake tambayarta wanene ɗan uwansa.
“Aisha magana nake miki kin sanshi?”
“Na sanshi Dr. Abdulkareem ne ɗan uwanka mana”
“Okay to bayanni kina haɗuwa dashi?”
“What akan me zan haɗu dashi,kaima har yanzu ban amince da abinda yake tsakaninmu ba tukunna,saboda bakasan komai akaina ba, nikuma bazan iya faɗamaka ba”
“To amma duk sanda nake tareda ke muna magana sai yacemin shima yana tareda ke”
“Nikuma ohh…..minti ɗaya ina zuwa yanzunnan”
Barin wajen tayi da sauri,can anjima saigata ta janyo hannun Inayah sun taho,tundaga nesa da Inayah tagane mai yake faruwa tafara sunne kai,dan da alama ita take haɗa komai kenan.
“Kayi mistake inaga bani kake nufiba Dr abdulkareem,da alama ƴar uwata kake gani.
Kayi haƙuri ba sunana aisha ba Abdulmaleek.
Sunana Hilyan ita kuma wannan Inayah,mu yan biyune kuma marayu gaba da baya,bamusan kowa anan ba sai anty maryam wacce take tamkar jigonmu,iya wannan zan iya faɗamuku gamedamu mu zamu tafi”
Hannun tahaɗa tana roƙon su afuwa,amma Inayah ko a jikinta,saidai kana gani kasan akwai abinda take boyewa.
“Kince masa sunanki aisha,to amma nima cewa tacemin sunan ta aisha,kuma itace take tareda Ɗan uwana,inna ƙirashi kuma sai yace daga inda yake yana kallonki a wajen matar babban yaya,wani lokacin har hotonki yake turomin daya ɗauka a lokacin. Mu munyi tunanin mace ɗayace takeyin siddabaru”
Juyawa hilyan tayi cikin bacin rai ta kalli Inayah wacce take buya a bayanta.
“Inayah mai kika aikata faɗamin”
“Ohh ni babu abinda na aikata,kawai ranar ne naje shopping anty maryam ta aikeni sai ya ganni,najuya zan tafi sai yace min……..’Am kaman aisha koh wacce take zaune a gidanmu’
Nikuma dana gano ke yake nufi da alama kince sunanki Aisha,sai nace eh itace.
Wannan ne fah kawai”
“To meyasa bazakice bake bace toh?”
“To miye dannace nice ɗin,kema naga ba sunaki Aisha ba ko?”
Murmushi su Abdulmaleek suka tsaya sunayiwa adorable twin ɗin dake sa’insa a gabansu,sun shagala da kallonsu har basaso su daina faɗan.
Abdulkareem ne yayi gyaran murya tareda cewa.
“Yanzudai ke hilyan bakece mai ɗaukar zafi ba nine koh,to na yafe abinda tayimin,dan da alama naga abinda tayin ya sakata nishaɗi sosai,saidai fah bazan yafe dukka ba har sai kin bani dama munyi magana tukunna”
Cuno baki Inayah tayi tareda ɗaga kai.
“Uhm nima anyimin ƙaryar sunan Aisha,dan haka abani damar yin maganar kafin nayafe”
Abdulmaleek shima yafaɗa yana kallon hilyan ta gefen ido,wacce duk kunya takamata sai matse hannun Inayah take dayake cikinnata.
“Ke dallah sakemin hannun zaki karyani,duk salon soyayyar ne haka”
Ta faɗamata daidai kunnenta,amma Abdulmaleek yaji ta duk da tafaɗa a hankali.
“Looovvee is in the air”
Dukka tareda suka juya suna kallon maleekah wacce takeyimusu tafi.
“Sannan kuma ga wani labari dana ji yanzu a gida danaje ɗakko abincin da aka manta.
Baban haneef shida anty Lailah suna nan sun saka iyah a gaba wai saita amince da Abban haneef ya karbi kujerar yah Jabeer,tunda bazai tashi ba”
Dukkansu a tareda suka zaro ido gameda labarin da sukajin.
“Hmmm nima danaji abinda ake faɗa ɗin nayi matuƙar mamaki,kumada alama iyah ta yarda da abinda suke faɗa,a kowanne lokaci zakuji an ƙira family meeting.

Bayan sati biyu dayin aikin Jabeer aka ƙira family meeting domin tattaunawa akan waye zai riƙe Companyn na ɗan wani lokaci.
Duk da cewar babu wanda zaiso Alhj Abdullahi ya karbi Companyn,amma kuma kowa yasan shine yakamata ya hau.
Alhj aliyune ya fara magana tareda cewar.
“To Komai da ake ganin ya faru muƙaddarine daga allah wanda ba’a saka masa rana,Jabeer har yanzu yana kwance a gadon asibiti,sannan kuma likitoci sun tabbatar dacewa koda ya tashi toba lallai ne ya koma yanda yake ba a da.
Dan haka na yanke shawarar zan miƙa kujerar Companyn a hannun…….”
“A dakata haka Abba”
Muryar bombee ce wacce shigowarta kenan ɗakin meeting ɗin.
“A ƙai’dar tsari na riƙon Company,wanda yakeda mafi kason share shine zai karbi shugabancin sa,duk da cewar shine na biyu a kaso na biyu a yawa…..
Alhj Abdullahi bashida lasisin hawa kujerar wannan Company,saboda bincike ya nuna ya daɗe da siyarda da share sa a hannun wasu dasuke son karbar kujerar nan,duk tsawon lokacin da takardun jabu yake aiki”
Kowa kallon bombee yake da mamaki wacce take nuna takardun Alhj Abdullahi a hannunta.
Cigaba tayi da cewar.
“Shugaban Company yana kwance halin jinya,mataimakin sa kuma bashida share ko ɗaya a hannunsa,shin za’a miƙa kujerane ga na waje.
Zuwa yanzu wannan yafara kallon wannan,ciki kuwa harda manyan mutane biyar da aka gayyato wanda sukeda kaso mai yawa suma a cikin Companyn.
Magana suka farayi ƙasa kasa akan kowa nason karbar ragamar Companyn,wasu a cikinsu har sun fara murna da labarin da bombee ta kawo,domin hakan shine babbar damarsu.
Wata harara Lailah taje makawa bombee,yayinda mutanen gidan suke ganin sakarci na abinda bombee tayi.
Faɗa yafara kaurewa a tsakanin mutanen,kowa yana iƙirarin shiya cancanta da wannan kujera,har yazamo hayaniya tafara yawa.
Buga table ɗin bombee tayi,saida kowa yayi shuru kafin tayi gyaran murya.
“Wannan kujerar da kuke magana akan ta ta mijina ce,ƙannensa dukka suna da aikin yinsu,ƙanin mahaifinsa kuma bashida takardun riƙe Company a yanzu. Sannan shi wanda ake ƙoƙarin karbar kujerar sa ai bai mutu ba da ransa.
Dan haka ni matarsa Maryam Ahmad,nayi alƙawarin zan riƙe wannan kujera na tafiyar da ita yanda ya kamata,batareda na bari ta fada hannun wanda bai dace,har zuwa lokacin da mijina zai samu lafiya ya karbi abinsa.
Uhm na manta ma ban faɗamuku ba,barona asibiti a yanzu ya farfaɗo daga doguwar sumar daya shiga.
Saidai likitoci sun tabbatar da cewar komawar sa normal sai a hankali.
Dan haka na ɗaura ɗamarar karemasa matsayinsa da kuma kuladashi,har zuwa lokacin dazai iya aikinsa dakansa.
Abba idan ka amince dabani kujerarsa na kulada ita kasaka hannu akan wannan takardar,nizan koma Wajensa a yanzu”
Tana gama maganar ta tsugunna a wajen da Alhj Aliyu yake zaune ta miƙa masa takardar.
Hannu yasaka ya karbi takardar yana murmushi.
Tashi tayi zata tafi taji yayi magana.
“Keda kike buƙatar saka hannuna meyasa kuma zaki tafi?”
“Abba ba dole sai yanzu zaka saka hannun ba,miƙa ragamar aikin ɗanka a hannuna kana buƙatar yin dogon tunani,zan jira har sai sanda ka amince kafin kasaka hannun”
Jijjiga kai yayi tareda faɗaɗa murmushin sa kana yayi sign a wajen da ake buƙata,mika mata takardar yayi tareda cewar.
“Na yarda dake ɗari bisa ɗari da dukiyarsa da kuma kulada shi,maleekah tana bani labarin duk abinda kike masa,babu abinda zancemiki sai Allah yayi miki albarka kuma yabawa mijinki lafiya kinji”
Kallon dattijon take cikeda shauƙin jin girmansa a idonta.
“Nagode Abba,ina mai tabbatar maka bazakayi nadamar miƙamin amanar dukiyar ɗanka ba”
“Ina fatan hakan”
Tashi tayi ta tsaya,lokaci guda ta sauya yanayin fuskar tata.
“Defuty CEO and directors,ina buƙatar kasancewarku a office 7:00 am na safe,akwai abinda za’a tattauna”
Tana gama faɗin hakan tayi waje da sauri,bata daɗe da fita ba sukaji tashin motarta.

A bakin ɗakin taci karo da doctorn zai shiga.
“Mr Jabeer kin dawo,ɗazu nashiga bakya nan sai nurse kawai na gani”
“Uhm wani urgent abune ya taso,ɗazu kacemin ya tashi amma ni banga wani cigaba ba sosai”
“Bazaki gani a haka ba dama,amma yanzu baya numfashi da inji da kansa yakeyi”
Nurse ɗin da bombee ta buƙata a bata ta suna zaune a gefe guda.
“Sister Haleema shin akwai wani abu da kuka gani gameda shi?”
“Ahah babu komai doctor,saidai kaman yatsansa ya motsa,naga ya motsa daga yanda yake”
Ƙarisawa wajen bombee tayi da sauri tana nazarin abinda suka faɗa.
Kafin wani lokaci ƙanƙani kowa labarin farfaɗowar Jabeer yabaza yan uwa,saidai har yanzu baya motsi sosai,abinma sai yafi bada damuwa fiyeda da.
Da daddare bombee kwana tayi tana nazari gameda aikin da Jabeer yake,in bata gane abuba ta ƙira khaleel ta faɗamasa,dan da farko shi ta cewa ya karbi Companyn amma firr yaƙi ya manna mata.
To yanzunma dai kusan komai shizayyi,tunda ita ga kulada Jabeer.
Kaman koyaushe datayi asuba bata koma ba,zama tayi a bakin gadon tana ƙare masa kallo,alamar motsawa taga idonsa yanayi.
Fitila da ɗakko da sauri ta haska,tabbas hakane ba idonta bane yake mata gizo,fatar idonsa ne suke motsi.

“Mashallah nasan dama zaka tashi bazaka cigaba da barmu muna jira ba koh,ka tashi ka nuna musu,wanda burinsu shine faɗuwarka”
Maganganu tacigaba dayi amma ba amsa.
”Anty Maryam yah khaleel wai yana ƙiran wayarki,shin dagaskene 7:00 za’ayi meeting ɗin?”
Madeenah ce ta tambayeta cikin muryar bacci,ita da maleekah yau a nan suka kwana,tunda ita bombee tana bukatar zuwa aiki.
“Ohh wayar tawa inaga tana silent,kice masa eh yasanardasu nima yanzu zam shirya”
Tana gama faɗin hakan ta shiga banɗaki.
Bayan ta shirya kafin ta tafi saida su maleekah suka sha kashedi,kan ko motsi ɗaya suka gani suƙirata su faɗamata.
Abin harsai da yabasu dariya,itakuwa babu ruwanta.

Bakwai daidai tayi parking a ƙofar Companyn,ga wani baƙin glass data tare fuskarta dashi,wata tafiya take ta kasaita,duk da safiya ce amma kowa ya fito,don kowa yaci abinda aka faɗa na zuwan sabuwar CEO Mr Jabeer,wato Bombee.
Secretary yace tazo da sauri ta karbi jakarta zuwa cikin office ɗin.
A hawa na sha shida yake final floor yake,dan haka saida ta elevator,office ɗin ta nuna mata.
Saida ta ƙarewa ƙofar kallo kafin tashiga.
Mashallah wajene a tsare yasha kayan Alfarma irin na zamani.
Office ɗin Secretary ta wuce ta nufi na shigaban wato na CEO.
Akan table ɗin Ta ajiye mata jakar tareda komawa gefe ta tsayah.
Ƙaremata kallo bombee tayi bayan ta zauna a kujerar tans juyawa.
“Miye sunanki”
“Sunana Fadeela ranki ya daɗe”
“Tun yaushe kike aiki anan”
“Shakera uku kenan,amma nakusa dainawa zanyi aure nan da 6 month inshaallah,amma ƙanina ya cika gurbin aikin zai cigaba da aiki da ogah”
“Good Allah ya taimaka,menene schedule ɗina na yau?”
“Ranki ya daɗe basuda wani yawa,iya gabatar dakene ga directors dakuma Share holders,saikuma sign dazakiyi a takardun sabbin ma’aikatan da aka ɗauka”
“Ohk muje ki kaini meeting room ɗin,takardun dasuke buƙatar sign kuma in zan iya yinsu a gida to ki saka min su a mota kawai,dan ba zama zanyi ba”
“Ba matsala ranki ya daɗe”
Lokacin data shiga ga iya share holder ta gabatar dakan,sukam sauran dama sun ganta.
Daga nan tabar sauran aikin a hannun khaleel ta koma asibiti.
Tun a wajen fitowarta daga mota maleekah ta tareta tana dariya.
“Anty maryam albishirinki”
“Ahah ba goroba barina je nagani da idona,bazan iya bari naji mai zakice ba”
Dana dariya tabi bayanta da gudu har tuntube take.
Turus tayi a bakin ɗakin ganin likitoci a ƙalla uku zaunar dashi sukayi idonsa yana kallon ƙofah,saidai kana kallon idon kasan babu abinda yake gani dashi.
Wasu ƙarafa aka saka suka tareshi,saidai yana motsa hannunsa da kuma ƙafafunsa.
“Doctor yatashi kenan”
Bombee tafaɗa cikin zumuɗi
“Eh ya farka amma kuma har yanzu majority na jikinsa baya respond,hakan yana buƙatar ɗan lokaci,za’a dunga ɗagashi anan kwantarshi,idan hakan ya cigaba zamu baku wheelchair a dunga sakashi a kai”

Bayan kwana uku da farfaɗowarsa an samu cigaba sosai,dan wunin ranar yau bombee yi tayi tana kewayawa dashi cikin asibitin a wheelchair,dan yanzu har buɗe baki yake yana ƙarbar abinsha marar nauyi idan aka kai kusan bakinsa.
Sannan in aka kai haske kusan idonsa yakan ƙoƙarin saida kwayar idonsa akai.
Ganin hakan da akayi ne yasa Alhj Aliyu da kansa yanemi a dawo dashi gida,suma likotocin basu wani damuba,saboda zaman sa cikin mutane zai ƙara saurin samun sauƙinsa sosai.
Tsawon kusan wata guda Jabeer yayi a asibiti kafin aka dawo dashi gida,har sannan Jawaheer da Jaleelah basu fita daga sashensu ba,lubnah kuwa run a ranar daya fita itama tabar gidan.
Gabaɗaya babu wanda yakulada halinda suke ciki,saboda hankalin kowa yana kan jinyar Jabeer ɗin.
Su suke tafa abincinsu suci,kana kuma su gyara gidan tsaff,Hajiyah rabi tun tana zuwa akan Jawaheer tazo su tafi harta daina,yanzu sun fara tunanin ko rashin lafiyar mijinnasune ta taba su.

Sanda aka dawo da Jabeer gida,Hajiyah Zeenah taso akaishi shashenta,amma alhj Aliyu ya nuna mata ƙin amincewarsa,tareda yi mata magana akan tabar matarsa ta kulada shi,dan yanzu kowa yasan abinda Hajiyah Zeenah tayi wajen auro bombee ,shiyasa hatta ƴaƴan ta idan tace ga yanda za’ayi sai kowa yayi shuru kawai.

“Yanzu shikenan duk shirin yatashi a banza kuma haka zamu zuba ido?
Ka duba wannan Jabeer ɗin munyi zaton bazai tashi ba,saigashi kullum lafiya yake samu,kaman duk bakin duniya aka haɗu ana masa fatan tashi”
“Hmm kedai bari ni narasa ma mai zanyi,babu abinda yafi ɗagamin hankali kaman rashin takarduna,da yannzu fah na zama nine shugaba,koda zai dashi daga baya kenan,amma yanzu kiga yanda rishe ya juye da mujiya.
Waccar yarinyar yaishe ma to tasan banida takardu,ko itama wani aikin takeyi a boye?”
“Da alama,ko itace ma tasace takardunnaka ba. Takamar data fito tanayi duk dan Jabeer yana rayene ai,da ya mutu ai kowa yasan kaine mai gadon takardunsa ko kana da naka koda kuma bakada shi,tunda bashida magaji har yanxu.
Kuma dama haka akayi da alhj Aliyu ɗin,inba Jabeer kaine mai karba kujera idan Jabeer bashida magaji.”
“Uhm kuma kinsa nafara wani tunani”
“Irin wanda nakeyi koh?”
“Wanne kikeyi ke”
“Na kawar da Jabeer daga doron ƙasa,ai haka mukayiwa Aliyu ma ka manta,saida yarasa ƙafarsa kafin ka samu matsayin dakake kai a yanzu”
“Eh hakane amma yakike ganin zamuyi da Hajiya rabi wacce mukeson haɗa hannu da ita.
Kimsan dai bazata bari a kashe surukinta ba,musamman datake son ƴar ta haifi ɗa gidannan”
“Abu mai sauƙi saimu sanar da ita cewar Jabeer bazai haihu ba,kuma inka zama shugaban Companyn zaka bawa ɗan ta mataimakinka”
“Eh wannan shawara tayi,an gaisheki mamar haneef,nasarar mu takusa zuwa”

Page 🖤 55••56🖤

Su ukune yanzu kacal a falon,daga Jabeer wanda yake kan wheelchair sai haidar dayake ta wasa da motocinsa,bombee kuma tana kitchen,lokaci lokaci takan zo ta wucesu a falon.
Idonsa akan tv yake inda ake labarai,sai haidar yayi ƙarane ya juya ya kalleshi,ko kuma in bombee zata wuce yabita da kallo.
Duk sanda zata wuce idan suka haɗa ido murmushi take sakar masa,dan har cikin ranta tanajin daɗi yanda yake samun lafiya akan lokaci..
Yanzu har yana iya laluransa a banɗaki ya fito batareda taimakonta ba,duk da cewar har yanxu babi wani yanayi dayake nuna wa a fuskarsa bayan kallo.
Mutane gidan kusan kaff a sashenta suke yini idan ka ɗauke Hajiyah Zeenah da su Lailah sai kuma iya sayyada,sai yamma tayi kowa ya kama gabansa.
Gidan data siya inda su innayi suka zauna yanzu ta tamƙawa baban ta shi. Sjn samu kuma ya karba ya zauna bayan an kai ruwa rana.
Yana cewa da yarasa yaransa yanzu gashi allah yayi masa kyauta da guda huɗu russ mata,wato hadda su hilyan.
Ya riƙesu kuma gam tamkar mahaifinsu lokacin dayaji labarin rayuwarsu,inna Danejo ta warke yanzu kaman ba itaba.

Yau ma kamar kullum ɗin dare yayi kowa ya tafi saisu kaɗai a gidan.
Su Jawaheer ma tun lokacin daya dawo daga asibiti ta koresu,dan karma ya gansu hankalin sa ya tashi.
Abincin ta kawo ta ajiye akan dinning,haidar yana gani ya jefar da abin wasan ya taho da tafiyarsa irinta yara.
Dariya bombee tayi tareda cewa.
“Tun ɗazu nake magana kaƙi kulani saida kaga abuna koh?”
Zaunarshi tayi akan cinyarta tareda jawowa kujerar Jabeer ma ya matso kusada itah.
Ɗebowa tayi a cokali ta miƙawa Jabeer a baki,haidar yana gani yafara darun yara yana kuka,ala dole shine farko,dan hakan har yazamar mata tamkar jiki a iya sati biyu datayi tanayi.
Kaiwa bakinsa tayi tasakamasa dan dama nasanne.
Tana cikin hakanne tatsaya cakk da abinda take ganin bakin Jabeer ya na motsawa,da alama murmushi yakeson yiwa yaron.
Ita tana kallonsa shikuma yana kallon yaron dayake kan cinyarta.
Batace komai ba haka ta gama basu abincin kafin ta hau aikinta na Company,wanda ɗazu khaleel ya kawo mata da zai wuce,dan yau batasamu zuwa wajen aikinba.

Can wajen misalin sha ɗaya na dare ta rufe system tana shirin kwanciya sai taji kaman alamar dirowar mutum ta bayan windownsu.
Kallon Jabeer tayi wanda yake kwnace da haidar a gabansa,sai kuma fili a gabansu wajen dazata kwanta.
Bakin windown ta nufah da sanɗa tareda leƙawa..
Duk da cewar akwai duhun dare,amma hakan bai hanata ganin wulgawar mutum ba da baƙin kaya.
Saurin dawowa tayi ta baya bayan ta rufe windown..wind
Zuwa da dawowa take a ɗakin na wasu daƙiƙu,don tarasa ma mai zatayi.
Kasancewar bata kashe hasken ɗakin ba tana kallon Jabeer wanda shima yake kallonnata,da alama yaji motsi kenan.
Wajen wardrop ɗin ta ta nufah ta ɗauko dogon wando ta saka,doguwar rigar baccin dake jikinta tayi saurin cirewa tasaka ƙaramar riga..
Ribbon ta ɗauka ta ɗaure gashinta ta baya tareda komawa bakin gadon ta zauna.
Saitawa tayi a bakin ƙofar ɗakin tana jiran shigowar wani,dan zuwa yanzu tana jiyo muryarsu a kusada ɗakinsu..
Shidai Jabeer yana nan kwance yana kallonta.

Bankaɗo ƙofar sukayi da ƙarfi,maza ne guda uku ƙarti dasu sun sha baƙaƙen kaya,hannun kowannensu ɗauke da pistol ƙarama.
Kallon ƙananan shegu bombee tayi musu amma kuma bata nuna a fuskarta ba,saima tashi tsaye da tayi jikinta yana rawa,alamar batayi zaton shigowarsu ba.
Babban ne ya kalli na kusada gefensa tareda cewa..
“Wow Kalli wata jar cika hadaɗɗiya,ai da hajiya saitace bayan ganimar kuɗi akwai kuma na mata.
Kai mai kake kallo riƙemin ita nan,shin na fara ta kanta ko kuma na fara da kashe wancan gutun gawar kai?”
“Ogah duk wanda ka zaba zakayi,amma inaga ka fara da ita,kaga inka bari muma saimu lasa kafin kacika aikin koh?”
“Ahah ogah inaga ka gama dashi tukunna,sanin kanka ne sati guda mukayi muna tsara yanda zamu kawo farmakinnan mu gama dashi,bai kamata mu tsaya bi takan mace ba”
“Kai dallah ana za’a kwashi romo kai kuma kana wani zancen aiki,dare fah bai kusa ƙarewa ba akwai ishashshen lokaci”
“Ya isheku haka wannan surutun,kai riƙemin ita ka ciremin kayanta,kai kuma wancan ɗakkomin shi daga kan gadon can,Hajiyah tace dama babu abinda yake sai yanda akayi dashi”
Wanda bashi umarnin riƙe bombee ne ya nufi wajenta,ja da baya take tareda kallon wanda ya nufi inda Jabeer yake.
“Wai ku suwaye waye kuma ya aikoku,kada ku kuskura ki tabashi mai yayi muku”
“Sai yayi mana wani abu ƴan mata? Matar ƙanin babansa ce ta aikomu da kuma uwar matarsa,sunce suna sonsa a mace yakike so muyi banda mu aikata abinda suke so,tunda muma zasu bamu abinda muke so”
“Ahh ogah ya kake faɗamata wanda ya bamu aiki”
“Saboda babu yadda zatayi,a gabanta zan kashe shi kuma na tafi da ita,itada ta ƙara taka ƙasar gidannan har abada,tazama tawa”
Yana gama faɗin hakan ya nufi inda Jabeer yake kwance yana kallon su da wuƙa.
“Tun har kayi yunƙurin taba iyalina to you leave me no choise,dolene kaga wacece ni”
A kausashe tayi maganar,tana gamawa ta bawa wanda yake riƙeda hannyennata ƙafa a fuska,kafin suyi wani yunƙuri ta kashe wutar ɗakin.
Gab gab kake ji na lokaci ƙalilan kafin wutar ta dawo..
Bombee ce zaune a bakin gadon tana haki,ƙasanta kuma ogan nasune ta ɗora ƙafarta a wuyansa,goshinsa kuma ta saita shi da bindigar datake kunkuminta.
Sauran kowa yana angle guda na ɗakin,wani yana riƙeda ciki wani kuma yana riƙeda kai.
“Shugaba dama kece?”
“Miye to idan nice,dana faɗamaka nice wato babu abinda zakayi,idan kuma wata ce da yanzu ka kashe mata muji kuma kayi mata fyaɗe ko,daka cemin ka shiryu ashe ƙarya kake koh.
Uban me ma yakawoka garinnan tunda ga gembu?”
“Na……nazo neman kuɗine,tunda kika tafi mun daina karbar kuɗin ƙungiya shikenan muka rasa sana’a”
“Da cewa aka faɗamaka a rayuwata ƙarewa zanyi ina zama maka hanyar sana’a,ubana ne kai iyeee,faɗamin ku nawane kuka zo kuke wannan ɗanyen aikin?”
“Wlh babu ni kaɗai ne,waɗannan ma a gidan yari na haɗu dasu an sakomu tare,shine muke aiki,kuma dama mun yi aiki tareda su da a wajen Hajiyah lailan,mune wanda tasa muka kwancewa ubansa ma tayar mota,shekara goma da suka wuce,bayan munyi wannan aikinne tasa muka bar garin,ni saina na nufi can hanyar taraba,to shine bayan lokaci da muka dawo tasake bamu aikin kashe ɗansa,saboda idan yana raye koba ya motsi to kece zaki cigaba da kulada Companyn injita,amma idan ya mutu kuma tunda bayada magaji to dole alhj Abdullahi ne zai riƙe Companyn”
“Wonderful naji wannan,to itakuma Hajiyah rabi mai ya tsomota cikin aikinku”
“Iyee ita kuma zata taimaka musu da nata ikon,idan sukayi nasara to ɗanta ne zai zama babban director na Companyn,tunda hajiya Lailah sun tabbatar mata da Jabeer bazai haihuba”
Dan tsabar takaici wani duka bombee ta kai masa a hanci saida ya rasa hankalin sa.
Suma wanda suke ɗakin dukansu da dungayi da bakim bindiga saida taga basa motsi..
Kuka tasaka mai cin rai dan tarasa ma mai zatayi.
“Yan…,yanzu da ni watace da shikenan ta kashe shi kohh?”
“Mar…..rrryaam”
Saurin goge hawayen tayi tana kallon inda sautin dushashshiyar muryar ta taho.
Jabeer ne a yake ta ƙoƙarin tashi ya zauna da kansa,hannayensa dukka rawa suke amma kuma bai daina ƙoƙartawa ba.
Tashi tayi da sauri ta nufi inda yaken,hannayenta tasaka a ƙasan nasa ta zakagayeshi ta baya tareda ƙanƙameshi a jikinta.
“Ka ƙira sunana,kafara magana……..yanzu da tuni ta kasheka kenan,ta daɗe tanayin abu ina ƙyaletane saboda matsayinta,amma tasaka ƙafah ta take shi ta tsallaka matsayinnata.
She will pay for touching my family,dole ne saita gane kuranta na taba iyalin bombee,wannann alƙawarine danayi.
Sun daɗe a haka bombee tanata sambatu,shidai kawai jinta yakeyi,dan bashida ikon maida mata doguwar magana,shikansa sunan nata Allah kaɗai yasan iya ƙoƙarin dayayi wajen jawo hankalin ta gareshi,a tsawon zamansa da ita koyaushe takan kasancewa dashi a duk lokacin daya buƙaceta,hakanne yasa shima yayi ƙoƙarin zama a gefenta a wannan yanayin,duk shima shikaɗai yasan mai yakeji gameda abinda suka faru a rayuwartasa,saidai buɗar ido dayake yana kallonta a gefensa yasa yafara daina damuwa da abinda suka faru dashi a baya..
Kamasu tayi ta ɗauresu tamm tasakasu a cikin store kafin safiya..
Da safe ta tashi kaman babu abinda ya faru jiyah,saida tayi wanka ta tayiwa haidar ma,shima Jabeer ta haɗamasa nasa kafin ta nufi ɗaura musu abinda zasuci..
Bayan tagama aikace aikacenta misalin 9:00 maleekah tashigo gidan.
“Morning anty maryam ya jikin bro”
“Jiki da sauƙi yama fara magana jiya”
“Really wow”
“Yawwa kinga riƙemin abincinnan barina je na tayashi wanka”
“To shikenan”
A bangaren bombee kuwa data shiga banɗakin taimaka masa tayi ya hau kujerar suka fito,saida yagama saka kaya tass kafin ta tsugunna a gabansa.
“Am ka ɗan yi haƙuri zanyi wani acting show a waje yanzu”
Ɗaga mata kai yayi kawai,duk da bai san mai zatayi ba..
Hannu tasaka tashafi gefen fuskarsa cikin kulawa kafin tabar ɗakin.
“Maleekah maza ki ƙira kowa da kowa yanzunnan kiyi sauri kowa fah”
“Anty maryam mai ya faru ki faɗamin……?”
“Kedai ki ƙira kowa nace yanzunnan,hatta abba shima da matan Jabeer dukka suzo yanzunnan”
Ganin yadda bombee ta kiɗime yasa maleekah ƙiran kowa da kowa ba bata lokaci,duk da batasan mai ya faruba amma har kowa yafara shirin tahowa,dan dama ta ƙware a hakan.
Cikin lokaci ƙanƙani kowa da kowa ya hallara,daga kan matan gidan da iyalansu harma da dana gidan suma da ƴan uwansu..falon bombee saida ya cika danƙam da mutane.
Kowa idan yashigo maleekah yake tambaya mai yafaru,wanda itama saidai ta kalli bombee,dam batasan mai yake faruwa ba.
Saida bombee ta tabbatar kowa yabar abinda yake ya taho kafin tayi gyaran murya.
Kallon Lailah take wacce tayi ɗan murmushi,dan lokacin da taji ance kowa yazo da saurinta ta taho itada nata familyn,dan tasan Jabeer ne ya mutu.
Itama Hajiyah rabi tare suka taho itada Jawaheer,Jaleelah ma tasan mai yake faruwa a wajen Jawaheer dan haka batayi gaddamar zuwa ba,dan tasan idan Jabeer ne ya mutu ti bawanda kuma zai kulada abinda sukayi kenan.
“Kin ƙiramu maleekah mai ya farune?”
“Uhm nima bansaniba,anty maryam ce tace na ƙira kowa akwai abinda yake faruwa”
“Ina….”?
Tun kafin Hajiyah Zeenah ta rufe baki sukaga tafito daga ɗakinta tana riƙeda ƙafadar Jabeer wanda yake takawa a hankali.
Kujera suka matsa masa ta zaunar dashi ya jingina,kowa babu wanda bayyi mamaki ba daganinsa,wasuna farinciki wasu na razana wasu kuma suna baƙin ciki.
“Ba dalilin Jabeer na tara kowa a wajennan ba,dalilin tara kowa shine jin jawabi daga bakin waɗannan.
Zaku iya fitowa yanzu”
Tafaɗa cikin ɗaga murya.
Ɗaya bayan ɗaya suka fito daga cikin store ɗin kai a sunkuye,da bindigoginsu a hannunsu,sakk kana ganinsu kaga ƴan fashi.

“Na tara dukkan mutanen nan wajen domin kuyi musu bayanin abinda kuka faɗamin”
“Daamus,mai kuma kake anan?”
Khmees da hilyan suka faɗa a tare suna kallonsa da mamaki.
“Mai kukeci na baka na zuba,duk yanzu zayyi bayani ai”
Kaman kuwa jira yake tiryan tiryan yafara bayanin abinda su Lailah suka sakashi ya aikata,tundaga na shekara goma baya harna daren jiya.
Furgaga laila tafara tana wani fige fige.
“Ƙaryane wannan zancen ƙarya kike,ni ban sanshi ba sam,komai daya faɗa ke kika sakashi faɗansa,tunda gashi nan yaranki yana fitowa suka ganeshi”
“Lailah abin basai yakaimu ga haka ba, tunda na shigo gidannan babu wanda yasan wacece ni,duk da cewar Ba hajiya zeenah bace ta tunkareni ita kaɗai,nima na tunkareta domin cimma wani kuɗirina a gidannan da kuma garinnan.
Maida kallonta tayi kan Jabeer wanda ya kafeta da ido.
“Tunda nazo gidannan kakeson sanin koni wacece,saidai naƙi faɗamaka saboda wani dalilina.
Babu abinda kasani gamedani daga garinsa saikuma sunana,a yau zakaji komai”
Labarin rayuwarta tafara bawa ɗaukacin falon,tundaga labarin gidansu haihuwarta da tashinsu da ƙanwarta,harda halinda ta tsinci kanta na rayuwa, da barinta gida harma da kuma riƙonta da gen muhammad Bello Yayi,dakuma irin sharrin da akayi mata.
Kowa a wajen dayaji labarin saida ya jinjina abin,musamman yanda tayi tsara abubuwa a gidan na maganin lubnah da danginta,harma dakuma wanda Lailah tayi itada mijinta da kuma Hajiyah rabi.
“Ba iya ga haka abin ya tsayaba,nasan dukkanku babu wanda yasan dalilina na yiwa su Jaleelah hukuncin tsare su a gida dasakasu aiki,wanda kuma har yanzu basu faɗawa kowa suma abinda ya faru ba.
Da farko naso barinsa shi mijinsu dakansa yafaɗi abinda sukayi masa wanda yayi sanadiyyar shiga halinda yake ciki a yanzu,saidai kuma a yanzu yabani izini na nasanar dakowa abinda suka aikata.
Jaleelah da Jawaheer kun sani nima nasani inada videon abubuwan da kuke aikatawa a wajena,saboda saboda kunci albarkacin ina daraja ni mata bakaman yanda kuka watsa taku kimarba,bazan saka aikin dakukayi kowa anan wajen ya kalla ba,dan haka yanzu ku fito ku sanar dakowa abinda kuke aikatawa,ko iyayenku zasu daina tsinemin suna ganin laifina da cewar na rabaku da mijinku”
Jiki na rawa ido ya raina fata suka fito zuwa tsakiyar a falon..
A tare suka zube ƙasa suna kuka kaman ransu zai fita,kana gani kasan rana ce tazo musu ta ƙin dillanci.
“Kuyi haƙuri sharrin shaiɗanne,Baba da inna dan Allah kuyi haƙuri,haƙiƙa kunyi iya ƙokarinku wajen ganin kun bani tarbiyya dakuma karemin mutuncina,amma saboda ƙyamatar talaucin da muke ciki,da kuma son kuɗi irinnawa da daula yasa na fara ƙazamin abu a boye da dalilin ƙawaye,wato neman ƴar uwata mace”
Itama Jawaheer ɗin nata labarin ta bayar babu yadda zatayi.
Dukka wajen kowa salati yafara da sallallami,babu ma ya mahaifin Jaleelah wanda saida matarsa innarta ta riƙeshi ta zaunar dashi,wacce itama take ta kuka.. Ko kallon inda take basuyi ba suka nufi ƙofah suka bar gidan.
Ko uffan basu ce mata,dan a halinda suke ciki basuda abinda zasuce mata.
“To ku mungama da babinku saura kuma Hajiyah rabi da Lailah da kuma alhj Abdullahi,wanda zasu karbi nasu hukuncin a gaban kotu a gobe tareda su brr na’imah,wanda suma lokacin za’a yanke musu abinda suka shuka suyi ta ci”
“Hee aikin banza,bar ganin kin tona aikin kowa kuma kin samu nasara kiyi tunanin ke kuma zaki zauna a gidan kiji daɗi.
Kaman yadda sauran basu haihu da Jabeer ba kema bazaki haihunba,haka zaki zauna kiyi ta kashi,dan an riga an rabashi da samun nasa ɗan,gadon dukiyar gidannan badai daga jininsa ba saidai ƙannensa”
Murmushin takaici bombee tayi tareda cewa
“Lailah kenan,a tunanin ki wai maganin dakikayi ƙoƙarin bashi yasha yayi aiki?wanda kika bawa tayi aikin zatonki ta aikata? Andai cemata tace ta aikata dai..
Dan kinga cikin matansa babu wacce takeda ciki sai akace miki aikinki yayi?.
Jaleelah da Jawaheer dama sun bada mahaifarsu ga ƙungiyarsu,lubnah kuma uwartace ta bada tata domin samun abin duniya,nikuma babu abinda yahaɗani dashi. Kinji inda lissafinki yake?.
Kuma koda bazan haihu da Jabeer ba ni naji na amince,amma ki daina sakawa a ranki cewar Jabeer bashida ɗa a raye,Jabeer yanada ɗa a raye,kuma a yanzu duk duniya ko a addini ko a shari’a nice nakeda matsayin uwa a wajensa.
Dan inajin son haidar a raina tamkar ɗan da na haifa a cikina,domin a kaf abinda uwa takeyiwa ɗanta abu ɗayane banyiwa haidar ba,shine haihuwarsa.
Shine babban dalilin dayasakani shigowa gidannan,domin haɗashi da mahaifinsa da kuma danginsa.
Na boye matsayinsa ne kuma badan komai ba sai dan irinku Lailah wanda kuke jagaye a duhu,dama wannan lokacin nake jira,idan nagama shafeku sannan zan bayyana matsayinku,ta hakkanne ɗana zai zauna lafiya a gidan ubansa batareda fargabar taba lafiyarsa ba.
Wannan kaɗai abinda zan iya masa a matsayina na mahaifiyar sa mai ƙaunarsa da kuma muradin kareshi……
Toh fah mu haɗu a chapter gaba ƴan uwa……
Labari yakusa zuwa ƙarshe inshaallah…..😂😂😂

Page 🖤 57••58🖤

“Hilyan lokaci yayi dazamu fita daga wannan kogon mu tafi,yakamata ki rarrashi Maryam ki faɗamata”
“Taya kake ganin zata saurara,har yanzu fah taƙi amincewa dacewar haidar ya mutu”
Matsawa kusada bombee sukayi wacce take durƙushe a cikin kogon dutsen,ta runtsa hannunta da ƙasa.
“Anty maryam yakamata mu bar garinnan idan har kinazo mu ɗau fansar dakike muradi”
“Da bancemuku bazan tafiba hilyan,saidai shin bazan samu lokacin da zan lissafawa zuciyata yawan abinda zata rike ba,har zuwa lokacin da damarta zatazo ta ɗaukar fansa.?”
Shuru sukayi a gefe suna jiranta har ta tashi dan kanta ta nufi fita daga wajen.
Tafiya suke tsakar dare cikin dokar daji batareda ɗar ba ko wani tsoron wajen,dan hakan dama yazamemusu jiki aikinsu ne nayi,kasancewar bombee tafisu damar gani idan duhu yayi yasa tayi gaba suna binta a baya.
Kwanan su biyu a jejin suna tafiya,in sun gaji su huta su cigaba,abinci kuwa wanda Allah ya horemusu su saka a cikinsu.
A zaune suke a bakin wutar dasuke haɗa da itatuwa.
Tunda suka bar kogon har yanzu bombee batace komai ba,suma ganin haka yasa basuyi mata magana sosai.
Dan in sukayi ma ba kulasu zatayi ba,a kuda bakin hanya suke,dan suna jiyo wucewar motoci da kuma haskensu.
Wata ƙarace ta doshi cikin kunnensu can lokacin da dare ya fara.
Hilyan ce ta kalli khmees da sauri a razane tace.
“Inaga fah hatsari akayi,kuma babu wasu motoci dasuke wucewa,baka ganin muje mu duba?”
Tashi sukayi zuwa wajen,basu daɗe da tafiya ba bombee tajiyo suna ƙiran sunanta,da baxata jeba saikuma ta tashi ta kaɗe wandonta ta nufi wajennasu.
Motace ta kifah sai jini ne yake zubowa daga cikinta.
Kallon su hilyan tayi wanda suke tsaye sun rasa mai zasuyi,ga kuma kukan jinjiri da suke jiyowa a ciki.
Ƙarisawa wajen motar bombee tayi fasa glass ɗin,hannu tasaka tazaro yaron daga hannun wata mata a cikin motar wacce take kusada window,sai callara ƙara yake saboda matsuwar dayayi da kuma ƙara,duk da kana jin kukan kasan yaron bashida cikykykyiyar lafiya.
“Innalillahi anty maryam da ransa kuwa,ko zamu kaishi cikin gari kai gidan marayu?”
Hannun matar taga yana motsi a hankali tana nuna musu hanyar gaba,wato kada sukoma garin.
Daga nan ta daina motsi.
Miƙawa hilyan yaron tayi tareda yin magana a taƙaice.
“Kisan yadda zakiyi dashi,tunda ku kuka ga haɗarin,ko kuma ki ajiyeshi a wajen ƴan sanda suzo,mukuma mu tafi kafin su taddamu”
Karbar yaron hilyan tayi cikin sanyin rai tareda cewa.
“Amma anty maryam kefah kika Ceto rayuwarsa a cikin motar,sannan idan muka barshi bakya ganin sanyin wajen zayyi masa illah?”
“To me kikeso nayi masa,ki lullubeshi da bargo ki ajiyemusu shi inda zasu ganshi”
Har bombee tafara tafiya tatsaya cak saboda abinda taji hilyan ta faɗa.
“Bakya ganin da hatsari mu barshi anan,wannan ba halin ki bane ba haka kike ba anty maryam”
Tahowa tayi ta ƙarbi yaron a hannun hilyan zata aijiyeshi a gefen motar,sai kuma ta tsayah tana kallon fuskar yaron,wanda yanzu yayi shuru kaman bashiba,duk da har sannan yana ɗan jan zuciya a hankali.
“Hilyan idonsa………”
“Meya faru baya ganine?”
“Irinnawa ne sakk idonsa,blue ne nasama cak nawa,bazan iya ajiyeshi ba zan tafi dashi”
“Meyasa ba…….”
Katseta tayi tareda cewa.
“Saboda inna barshi gidan marayu zasu kaishi,kuma am sure zayyi rayuwa irintawa kenan,wacce ko a madarki banason tunawa,zan tsayamasa naga waye zai masa irin abinda akayi min”
Ƙarisa maganar tayi tana cije baki tareda nannaɗeshi suka bar wajen.
Kallon kalllo khmees sukayi shida hilyan,inda bata da aljanu dama sai suce sun shigeta yanzu,tashi ɗaya saita sanja yanayi.
Komawa cikin jejin da sukayi yaro yace sam bazai zauna ba,dan haka basu da zabi dole suka koma cikin gari a dare.
Musamman yanda suka kulada yankan Dayake ƙaramar cinyarsa jini yana zuba.
Tun kafin su isa bombee taƙira wani abokinta wanda yake aiki a asibiti,tare suka tafi rasha dashi da kuma rahama.
Saidai su sun rigashi dawowa,tunda dama Military doctor ya karanta.
“Hello dr na’im ina kan hanyar dawowa cikin garinnan ta sirri,ganinan nakusa shigowa ka tabbatar ka sameni a bayan gari please”
“What maryam meyasa zaki dawo bayan kinsan haɗarin hakan”
“Uhm wani soul ne yake buƙatar kulawa yanzunnan shiyasa”
Kashe wayar tayi ta cigaba da jijjiga jinjirin wanda yake ta kuka.
Fuskarsu a rufe suna sauƙa a motar har safiya tafara.
Dr na’im suka gani a motarsa,nan da nan ya ɗaukesu zuwa cikin asibitinsa. Ƙaramine amma kuma yana tsari da abubuwan aiki sosai.
Tun a hanya bombee ta shaida masa mai yake faruwa,dan haka gwaji yayiwa jikin yaron domin ganin wanne kalar abincine zai shiga jikinsa.
Safa da marwa take a cikin ɗakin,sudai su hilyan suna zaune suna kallonta,yayinda yake ta ƙoƙarin yiwa yaron gwaji,an jima tace an gama shuru.
Cirewa abinda yake kunnensa yayi tareda fitowa daga cikin labulen inda yaron yake.
“Captain maryam gaskiya yaronnan jikinsa is very weak,duk wata nau’in formular ta madarar jarirai bazata ƙarbi jikinsa ba,sannan bugu da ƙari yayi loosing jini a ciwon daya ji.
Inaga abinda yafi kawai ku kaishi gidan marayu a samu wacce zatayi feeding ɗinsa”
“What na kaishi ina,da kenan amma ba yanzu ba,babu wata mafitar saita kaishi can”
“Akwai mafita amma nasan baxakiyi ba”
“Mecece inajinka”
“A halin da kike ciki bazaki so wata a kusada ke ba,sannan da alama bakyason rabuwa dashi,to mafitar shine saidai ki roƙi abokiyar aikinki kozata amince ta shaya dashi”
“Wai hilyan kake nufi,budurwace fa batayi aure ba,taya zata shayar da jinjiri”
“Wacce bata taba haihuwa ba ma zata iya shayar da yaro,saidai za’abi wasu prosess na injecting wani chemical dazayyi activating ɗin hormones ɗinta na haihuwa da kuma wanda yake kulada sarrafa ruwan mama”
“Ahah naji zayyiyu amma bazanyi wanann son kan ba na lalata mata rayuwa saboda muradina duk da kuwa nasan bazata ƙi amincewa ba.
Karka manta nima macece har yanzu,dan ina maida lamurana kaman maza hakan bai taba halittata da kuma matsayina na mace ba.
Idan har zayyiyu ni zan shayar dashi kayimin aikin akaina,
Amma abin zai ɗauki lokaci kuwa,yaron sai kuka yake?”
“Oh god kina nufin wai zaki shayar dashi,duk da ko aure bakiyi ba”
“Ehh zan shayar dashi,a yanzu shi nake da,zancen aure kam kuma kama barshi”
“Shikenan to zaki saka hannu akan takarda,batun ɗaukar lokaci kuma idan mun yi miki allurar zaki kwanta na wani lokaci,shikuma kafin sannan zamu saka masa ruwa wanda zai zame masa tamkar abinci”
“Okay deal”

Buɗe idonta take a hankali wanda yayi mata nauyi sosai,ƙoƙarin tashi take amma sai taji jikinta yayi mata nauyi,musamman ma ƙirjinsa wanda taji kaman an ɗora musu dutsi.
Tashi tayi ta zauna tareda jingina da jikin gadon,hilyan ce a zaune a gefenta ta taso da sauri kusada ita.
“Wai anty maryam mai ya kaiki wannan gangancin,baki duba da halin da kike ciki ne a yanzu zaki sake sakawa kanki wani,da nasan har haka zaki bi wajen ceton yaronnan da tun farko na ajiyeshi a gefen hanyar”
Taaƙarisa maganar tana share hawaye kaman zata rushe da kuka.
“In kin gama mitar miƙomin ruwa nasha,jinake kaman maƙwogarona zai daskare dan ƙoshirwa. Wai tukunna ma tsawon wanne lokaci nayi a kwance?”
“Awa shida fah da wani abun”
Tayi maganar tana miƙamata ruwan.
Ƙarba tayi takafa shi a bakinta saida tayi masa kaff kafin ta ajiye.
Gumine yake to mata,duk da ac dayake ɗakin.
Suna cikin hakane dr na’im yashigo riƙeda yaron a hannunsa,wanda yayi luff a farin ƙyalle.
Miƙawa bombee shi yayi tareda cewa.
“To bismillah saiki gwada ki gani shin ko ruwan nonon yazo”
Babu wata nadama kuwa bombee tasaka hannu ta karbi yaron a hannunsa,fita yayi shida hilyan aka barta ita kaɗai.
Kallon fuskar yaron takeyi,ƙyakykywane sosai,amma babu komai a fuskartasa sai hanci zuwatt,saboda ƙanƙantarsa,ga ƴar carnula da aka saka masa hannu.
Yaron yayi matuƙar shiga zuciyarta da kuma tausayinsa daya kama ta.
Ɗaga t-shirt ɗin dake jinkinta,tana kallon yanda ƙirjinnata ya sauya a lokaci guda.
Matsawa tayi ga mamakinta kuwa ruwan madara fari tass yafito daga ciki.
A bakin yaron tasaka masa,duk da ba wani sanin takamaimai yanda akeyi tayi sosai ba,amma dai tunda yashiga bakinsa kuma yana nema yana sha shikenan.
Ɗan jingina kanta tayi a jikin gadon tanajin yanda yaron yakejan ruwan zuwa bakinsa,kowacce ja ɗaya idan yayi har cikin ranta take jinta,tamkar ƙara dasa mata kusanci ake da yaron.
Muryar hilyan taji tana yimata magana.
“Uhm dr. Na’im yace wai dole zamu yi koda sati biyune saboda ki gama sanin mai yake faruwa,sannan zaki dunga shan magunguna da kuma allurar na kwana uku kafin ruwan nonon yazam standard”
“Ba matsala,amma kice masa sati guda kawai zanyi anan,kafin sannan kicewa khmees yaciro kuɗi a acct ɗina kusiyo min duk abinda nakeso,sannan kice ya saci hanya da ɗakko min motata a bayan ga barrack inda na ajiyeta”
“Tamm zan faɗamasa,to baki saka masa sunaba ma,yawwa ga nan kayan da aka cire a jikinsa da towel ɗin”
Miƙowa bombee kayan hilyan tayi kafin ta fita faɗawa khmees saƙon.
Bacci yaron yayi a jikin nonon,dan haka ta cireshi tareda kwantar dashi a gefe.
Kayan tafara duddubawa,purse da samu a cikin towel ɗin,da alama ta mahaifiyar yaronne.
Buɗewa tayi da ID card ɗinta a ciki na Nurse da kuma wasu takardu.
Buɗewa tayi taga takardar yarjejeniya ce tsakaninta da wani,harda sign a gefe.
Da alama wani ne yabata yaron akan ta riƙe,kuma ta mince ta karba.
Da alama kenan ba ɗanta bane matar.
Sunan wanda ya bata yaron ta gani.
Abdulmaleek Aliyu Jaan,(biological uncle).
Itakuma nurse ce wacce ta ƙarba ɗin..
Kenan basason ɗan ya rayu a gidanne,abu biyune ya faɗo mata a rai shine.
Ko dai Mugun nufi ne yasakasu nesanta yaron da gidansu,ko kuma saboda kareshi ne daga wani a gidan,koba komai binciken hakan bazai mata wuya ba,tunda tasan JAAN Company,amma kuma issue na gidanne bata sani ba sam.
Kafin lokacin dolelene ta boye identityn yaron kafin tagama gane kan komai.

*** ***

“Daga lokacinne bayan nakoma gembu gabaɗaya bincikena yatafi a familyn Gen abdu manga da kuma na gidannan,dama nariga nasaka a raina cewar idan na ɗau fansar Haidar,to zan bayyana matsayin ƙaramin haidar a wajenku,koda kuwa a bana zaune a gidan.
Saikuma gashi tun kafin hakan yafaru Hajiyah Zeenah ta nemeni da kanta,bawai kuɗinda zata banine yasaka ni amincewa da ƙudurinta ba,saidan ganin yanda damammakina suka zomin a lokaci guda.
Ganin hakanne yasa na faɗawa su hilyan cewar kada koda wasa suyi maganar da wani kan cewar bani na haifi haidar ba,har sai wannan lokacin yaxo”
Wannan ne labarin haɗuwata da Haidar da kuma rainonsa wanda nayishi a cikin gidannan tsawon wata takwas kenan zuwa yanzu.
Sauran kuma dalilin bada shi da Abdulmaleek yayi duk zakuji daga bakinsa,duk da nasan ina kyautata zaton ɗan Hafsa ne,tunda ranar daya bata shi a ranar ne kuma hafsa ta rasu itada ɗan cikinta”
Kowa shuru yai,yayi jugum da labarin da Bombee ta bayar,babu wanda yataba kawo haka a cikinsu,ciki kuwa harda Abdulmaleek ɗin.
Tunda kafin wani yasake magana sukaji iyah sayyada ta rushe da kuka,durƙusawa tayi tareda kamo hannun yaron,wanda shima ya runtuma kukan bai santa ba.
“Yaka nan ɗan arziƙi,dama ashe jinin hafsafuna yayi saura kuma zan ganshi a duniyar,kuma ma wai yana cikin gidannan tsawon lokaci ban sani ba,ohh Allah ni ƴa su,sannu ƴar nan aradu kinyi ƙoƙari,ashe muna tareda tarin maƙiya munan bamu sani ba,hmmm bama ya wannan shegiyar mai ido kaman na ƙwarƙwata,ashe zambo take mana cikin aminci bamu sani ba”
Ɗauke kai Lailah tayi cikin nadama,firgici da kuma razani na labarin data ji a yanzun.
Abdulkareem ne ya kalli ɗan uwannasa wanda ya tsurawa yaron ido ko ƙiftawa bayayi,dama tun kallonsa dashi na farko yaga kaman yagane idon yaron,saidai abinka da maza taya zai tuna,kuma ganin idon bombee shima haka yake waye zayyi tunanin ba ɗan ta bane.
“Bro kaikuma menene dalilin ka nacewar haidar ya mutu bayan ba haka bane”
“Saboda ina son cetar rayuwarsa mana,baka ganin lokacin halin da ake cikine,kowa fah yasan lubnah ce take cutar da matan yah Jabeer,to amma wazai yi magana kowa yayi shuru.
Ganin hakanne dana shiga ɗakin naga gawar Hafsah a kwance,ga kuma jinjirin yana motsi kaɗan kaɗan, tausayinsa da kuma muradin tseratar dashi suka shiga raina.
Itama Sister suwaiba wacce take tsaye a gefena tausayin yaron nagani a idonta sosai.
Hakanne yasa mukayi yarjejeniya da ita akan takarda,kan cewar zata raineshi har zuwa yagirma yayi koyi kare kansa batareda matsala ba kafin ta dawo dashi.
Kafin sannan kuma zamu kai gawar jaririn daya rasu mu ajiye mata mu boye rayuwar ɗan.
Hakan kuwa akayi na fito nace sun rasu dukkansu itada yaron,har doctorn ma a lokacin bashida masaniyar mai ya faru.
Bayan angama zaman makoki an ƙare na nemi number sister suwaiba na rasa,dan dama tacemin zata tafi garinsu adamawa,inyaso saita dawo tace ɗan kanwarta ta dakko a can.
Ganin ban sameta ba yasa na je asibitin,ananne aka shaida min cewar tayi hatsari a hanyarta tafiya,kuma dukka mutanen cikin motar suka rasu babu wanda ya tsira.
Anan na tabbatar shima ya rasu kenan,tunda babu wanda yacemin jinjiri a rayu a motar.
Wannan ne nima abinda nasani gameda lamarin,naso faɗawa Jabeer abinda ya faru,saidai kuma a ganin yanayinsa a lokacin labarin babu abinda zai haifar koda yaji”

Bayan jin labarin Abdulmaleek nan kowa ya tabbatar da cewar haidar ɗan Jabeer ne na jini gaba da baya.
A lokacinne kuma ƴan sanda suka shigo fita da Hajiyah rabi da kuma Lailah da mijinta.
Kowa a falon bayyi magana ba ballantana yaji tausayinsu har aka fice dasu.
Lailah da Hajiyah rabi sai zage zage suke kan cewar bazasu yarda sam,dole su ɗauki mataki,amma wannan duk ihu bayan harine.
Tunda aka fara bada labarin Hajiyah Zeenah take kukan nadama,wanda daman kowa yake faɗamata zaizo watarana,wanda tabawa yardarta take ganin sune masu sonta ashe burinsu ɗaya ne a rayuwa shine ganin bayanta itada a halinta.
Wacce kuma ta tsana take ganin ta a matsayin tantiriya ashe tsawon lokaci ta ɗauka tana taremusu harin abokan gaba batareda saninsu ba.
Wai kuma ƙarshen bayani ma har jinkanta ta riƙe tamkar ɗan cikinta ta shayar dashi ta kulada shi,sannan ta toshe kunnuwanta ta aibatashi da akeyi,duk ta kuwa tasan asalinsa da matsayinsa,badan komai ba saidan Kada ta bayyana koshi a waye a cutar dashi.
Yau itakuwa mai zatace da wannan matar ɗanta,wacce a yanzu kunyar haɗa ido take da itah.

A hankali kowa yake watsewa yabar sashen bombee ɗin,daga ita sausu inna Danejo kawai danginta,wanda rabin zamannasu duk nasiha Malm Ahmadu Yake musu itada su hilyan,haƙiƙa shi kansa yaji tausayin ƴar tasa sosai dayaji abinda tashiga a rayuwa.

Kanta a sunkuye tashiga cikin falon,kana ganinta kasan dama taji labarine daya birkita mata tunani.
Da alhj Aliyu taci karo a falo shida Maleeka..
Ƙarisawa tayi wajen sa ta zauna a gaban kujerar tasa.
“Shin yanzu kin yarda da abinda na dunga faɗamiki a baya,na cewar ki daina fifita watacan bare kina ɗaukar maganarta fiyeda ahalinki,sannan bakomai ne dan bakyaso zaki ce sai ya zamo yanda kike so ba,wani lokacin akwai yiyuwar mutum yayi haƙuri da abinda yagani kokuma yake faruwa,yarinyar nan babu abinda bakice gameda ita ba,kin sheganta ɗanta fiyeda kima ashe yaronnan jikanki ne kuma jininki”
Rushewa tayi ta kuka kaman ranta zai fita,dan dama neman hanya take.
“Wlh nagani,naga ayah fiyeda yanda kowa yake zato,a yanzu banajin zan iya fuskantar ta ma,dan allah ka yafemin mijina”
“Nidama ban taba riƙarki da komai ba,saboda nasan akwai ranar dazata zo ki gane abinda kike kuskurene,yanzu tubanki a waje ɗaya zamu ganshi shine aikinki da kuma yanda zaki zauna da mutane”
“Inshaallah zan gyara daga yanzu”

Yana kwance akan gadon yana kallonta har tagama shafa mai tasaka kayan bacci.
Bakin gadon ta matso ta zauna,daina abinda takeyi tayi tana kallon Jabeer wanda ya kafeta da ido.
“Ina yake?”
Murmushi tayi takaitacce kafin tace.
“Uhm nemansa kake,ai yanzu kam ganinsa zayyi maka wahala,yana wajen iyah wai,maleekah ce tazo ta ɗaukeshi da magriba,wai a can zasu kwana wajenta”
“Amma ai zayyi kuka tunda ɗazu ma kuka yayi data ɗaukeshi”
“Uhm amma bazayyi ba idan da maleekah ne tunda yasanta,sannan ba fitsari yake ba inya kwanta saida safe,ɗazu yatafi har kayi kewarsa?”
“Uhm nayi kewarsa,amma idan ke kika tafi ba kewa zanyi ba,zuwa zanyi na sameki”
A hankali yake maganar kamar mai koyo,kana gani kasan tursasa kansa yake yin maganar da itah.
“Yakamata ka kwanta jikinka yasamu hutu,don yau baka samu baccin rana ba”
Taƙarisa maganar tana jawowa system ɗinta.
Tun kafin ta buɗe yaɗora hannunsa akai,tsayawa tayi da buɗewar tana kallonsa,shima kuma itan yake kallo.
“Naji zanyi bacci amma kema yakamata ki bar wannan aikin ki kwanta ki huta,kada ki damu da taruwarsu,idan nasamu sauƙi dukka zan gama su a lokaci kaɗan”
“Amma……”
“I need to hug you and sleep with together,zan iya samun damar hakan,yafaɗa yana buɗemata hannyensa”
Sauƙe a jiyar zuciya tayi tareda ajiye system ɗin.
Fuskantarsa tayi tashige jinkinsa ,a hakan suka kwanta maƙaleda juna…..

Gud night,muhaɗu a last chapter inshaallah……..

Page 🖤 59••60🖤

Fitowa tayi daga motar ta zagaya ɗaya bangaren ma ta buɗewa Jabeer.
A hankali yafito daga motar,kana ganin jikinsa kasan sauƙi yasamu,amma duk da haka bai ware sosai ba.
Kallon harabar kotun yake wacce take cikeda mutane,saboda shari’ar daza’a gabatar.
Hannun bombee yakama wanda ta miƙomasa tana murmushi,riƙewa yayi ya ɗam bada ƙarfinsa a jikinta suna tafiyah.
“Sai yanzu dana fito waje na san cewa lallai nadaɗe a zaune a gida,amma yakike ganin shari’ar zata ƙare”
“Yanda ake tsammani,kowa abinda ya shuka zai girba a yanzun,zai fi kyau ka daina surutunnan haka muƙarisa ka zauna”
“Hmm ke kike ganin haka,naji ƙarfin jikina fah sosai,tuƙin motar ma dan kinƙi banine”
“Hhhh nasan dalilin dayasa kake son tuƙin ai,dan ka nunamin ne saboda yau karn hanaka abinda kake tasonyi…….”
“Karma kifara dan kince sai angama komai kowa ya karbi hukuncinsa dama zaki bani damar shiga rayuwarki,dan haka babu fashi yaune”
Dariyah bombee tacigaba dayiwa Jabeer suna tafiya,har suka iso bakin ƙofar shiga kotun,dan dama tuni an fara shari’ar,bayan sati guda dasu Lailah sukayi a hannun ƴan sanda sai yau za’a zartar musu da hukuncinsu.
Kotun tacika sosai da mutane,Lailah,Hajiyah rabi,lubnah,brr na’imah dakuma sameera.
Dukkan su suna wajen tsayuwa guda,duk wanda yaga fuskarsu da kuma halinda suke ciki,dolene zai tausaya musu.
Musamman ma lubnah wadda ta moje ta yamushe,abinda duniya ya isheta,ita kamma tasan nata lokacin ne yakusa,tunda an tabbatar mata a asibiti cewar cancer mahaifane da ita saboda abinda ta cuccusa.
A ɗaya bangaren kuma alhj Abdu manga ne da kuma su daamus.
Kasancewar akwai cikakkun shaidu,kowa kuma ya amsa lainfin sa,yasa basu bawa mutane wahala ba..
Dukkansu a laifinsu akwai kisa ko kuma yunƙirin aikata hakan,hakanne yasakasu zaman gidan yari tsawon rayuwarsu.
Hajiya Lailah kuma da mijinta zasu biya alhj Aliyu tarar kuɗi mai yawa na farmakin dasuka amsa sun kaimasa,sai brr na’imah da kuma lubnah zasu biya diyyar kashe kishiyoyin lubnah,yayinda zasu haɗa su biya diyyar haidar kuma harda sameerah.
Shikuma Gen abdu manga bincike yanuna cewar baya cikin hankalin sa lokacin da abubuwan suka faru,dan haka kotu ta yanke masa yin wata shida a gidan yari daga nna yakuma inya fito za’a wankeshi daga zargi.
Hayaniya ce ta kaure kotun,kowa yana faɗin albarkacin bakinsa.
Ganin yanda wajen ya hargitsene yasaka Jabeer ƙanƙame hannun bombee kaman an liƙa su da gum,da haka suka fito daga cikin harbar kotun,zuciyar su fari tass,musamman bombee sai yau taji nauyin daya hau kanta ya sauƙa na ɗaukawa Hidar fansar abinda yayi mata.
Magana taji anayi mata bayan sun fito daga cikin kotun.
Waigawa tayi ta kalli nu’aimah itada Hajiyah Zulaiha,Gabaɗaya nauyin ganinnasu ne yakamata sosai,rabonta dayin tozali dasu tun Ranar dasuka rabu akan ita ta kashe haidar.
Hannunta take ƙoƙarin zarewa na haidar domin nufarsu.
“Mr. CEO kabar Mrs.CEO taje ga mutane ana ƙiranta”
“Uhm kinsanfah bazan iya jure tsayawa na dogon lokaci koh?”
“Nikuwa nake da tabbacin haka,yanzu zan dawo ka jirani a mota yanzunnan”
Sakin hannunnata yayi yana haɗe fuska,ita in yana wani abun kwanannan har dariya yake bata,babu dama ya waiga bai ganta ba saidai taji ƙiran wayarsa ko kuma aike.
Su maleekah har dariyah suke masa amma bai dameshi ba,shikansa baisan yanada wannan halin ba sai yanzu daya gamu da soyayyar gaskiya..
Indai suna zaune a falo to kuwa kansa yana cinyarta ko kuma ya jingina da ita,babu kunyah haka zasuyi da faɗa da haidar idan ya sauƙeshi akan cinyar shiya kwanta.

Ƙarisawa inda su Hajiyah Zulaiha tayi cikin sanyin jiki,tunkafin tayi magana ta jawota ta rungumeta a jikinta,kuka tasake tana magana a hakan.
“Kiyafemin ɗiyata kiyafemin,koda kowa yagaza fahimtarki nibai dace nayi hakan ba,ban tashi sanin gurbinki cikin Ahalinmu ba saida kika tafi haidar ma ya tafi,a nanne nafara tunanin tabbas ba lallai kece kika aikata abinda aka zargeki ba.
Yanzu da komai yafito fili har kunyar kaina nakeyi da abinda nayi miki bombee.”
Ƙanƙame Hajiyah Zulaiha tayi wadda itama takejinta a matsayin Mahaifiyarta har cikin ranta.
“Karkice haka mommy,kidaina zargin kanki dayawa,kowacce uwa a lokacin iya abinda zatayi kenan,dan haka ki bar komai ya wuce kaman bai faruba,tunda a yanzu kowa yasan mai yafaru sannan wanda suka aikata kuma sun karbi hukuncinsu daidai laifinsu”
Sakin juna sukayi bombee tana share mata hawaye,a lokacinne Gen Muhammad bello ya iso wajen shiga ƙanin haidar.
Har ƙasa bombee ta tsugunna ta gaisheshi,shima haƙurin yafara bawa bombee saida ta katseshi tukunna yayi shuru.
“Uhm mommy barina tafi Yana jirana a mota,har yanzu bai warkeba bayada cikykykyiyar lafiya”
“Oh haka fah ai munji duk labarin abinda yafaru,Ƙaramin haidar ma na ganshi a wajen hilyan dakuma ƙanwar mijinnaki,sukamma basu fito ba har yanzu,kinsan abin zai fi tabasu fiyeda kowki saisun taho daga baya.
Karki damu momy zanzomuku inshaallah idan komai ya lafah”
“To shikenan Bombee,nima zanzo naga ɗakinki,nagode dakika bar komai ya wuce,idan nazo zanji girkinki shin ya ƙaru kokuma yana nan tun wanda nakoya miki”
Dariyah bombee tayiwa Hajiyah Zulaiha,saboda tunowa rayuwar ta a gabannata.
Kafaɗar nu’aimah ya tafah tareda cewa.
“To kema saikinzo min ina jiranki,duk da nadaɗe ina duba yanayin shigarki makaranta da kuma tafiyar gida,saboda kar har sannan basu daina kulla abinsu akanku ba.
Uhm naga saurayinnaki nan,shima nayi bincike akan sa,kicemasa antynki tace yayi mata”
“Wow really anty Bombee kinsan mai nake?”
Tafaɗa a kunyace tana sunkuyar dakai bayan sun haɗa ido da Hajiyah Zulaiha.
“Ohh mai kike nufi,yanzu nice kaɗai antynki dan haka ki kula sosai hmm?”
“Ehh zan kula amma irin wannan zancen ki barshi sai mu biyu tukunna”
Dariya sukayi a tare Hajiyah Zulaiha tana kallon su cikeda sha’awar sake ganin hirar tasu bayan tsawon lokaci.

Lokacin da bombee tashiga mota Jabeer ɗauke kansa yayi.
“Hubby bazaka min magana ba wai,ban daɗe ba fah nadawo baka ganine”
“Hakanne baki daɗe ba,tun ɗazu fah nake jiranki nikaɗai,gashi can naga su maleekah sun fitoma,yanzu nasan da sun haɗu dake bazaki dawo ba yanzu.”
“Nifah nayi mamaki wai bazakayiwa lubnah bankwana bane,ku wuce gidan amarennaka suma kayi musu”
“Hmmm bazawarai dai,tun yaushe na sakesu,maima yakawo maganar su yanzune,inaga in wanine yake maganar su zaki ce yabari kafin naji”
“Hhhhh to in ita baka mata bankwana ba,Babannaka fah shida matarsa,ga surukarka ma duk a wajen”
“Kai dan Allah Ummu haidar kibar zancennan haka,ni yanzu mu tafi gida ke nafi buƙatar gani a sirrance basu ba,banda kindamu ma nida bazan zo ba,dan ba daura ɗamarar zubar da rayuwar baya na fuskanci ta gaba yafimin”
Hannun ta yakama ya acikinnasa yafara tuƙa motar.
“What mai kake nufi,wai kai zaka tuƙa motar?”
“Menene to a ciki,nida zan tuƙaki in anjima mota ai ba komai bace”
“Naji naji kabar zancen toh”
Dariyah yayi ganin yadda lokaci ɗaya kumatunta yayi ja.
Ƙutt taja bakinta tayi shuru tana kallon ɗaya windown,danta kula surutunnasa marar burki yazo shi.

Shiga cikin gidan sukayi,maimakon yakama hanyar sashensu sai kuma taga yanufi wani wajen daban.
Batace komai ba har suka isa wani sabon sashe da akeyi a cikin estate ɗin.
Gininsa akeyi a lokacin,saidai kana gani kasan aiki yayi nisa sosai.
Ƙoƙarin fita Jabeer yake daga motar,hakanne yasa bombee kasa tsuke bakinta har zuwa sannan hakan yasakata tayi magana.
“Abban Haidar inane nan kuma muka zo kafin gida,naji kacemin ka gaji sosai”
“Uhm nagaji amma ba har can ba,zo muje na nuna miki wani abu”
Fitowa tayi daga ɗaya bangaren ta riƙe hannunsa suka nufi wajen ginin.
Sashe biyune a cikin wajen,amma suna nesa da juna sosai.
Kowanne ciki da falone da kitchen da kuma ɗakuna biyu a ciki.
Kallon Jabeer bombee takeyi domin yayi mata bayanin ginin wanene,tunda taga yanda ya damu da nuna mata ya yake.
“Nagode da zuwanki rayuwata,wanda ƙaddara ta daɗe da shigowa dake tun kafin nasani.
Kinga abubuwa dayawa a cikin ta amma hakan bai saka kin juya baya ba,saima jajircewa dakikayi kika tsaya gefena.
Masu iya magana suna cewa a kowacce nasara da namiji zai samu,takan kasancewa ne idan ta jajirtacciyar mace a gefensa,niba iya jajirtacciya kawai nasamu,nasamu jaruma tsayayyiya a gefena,shin wanne abu kuma zan sake nema Allah yabani indai a wajen abokiyar zamane.

Wannan gidan part ɗin dayake farko na Umar ne wanda zai auri khadija,munyi maganar dama baba kece baki sani ba,zan sama masa aiki a Company tunda yayi karatu.
Ɗaya side ɗin kuma nasu inna ne zasu dawo nan da zama. San…….”
Tun kafin yagama magana bombee ta rungumeshi tama manta da cewar jikinsa har sannan babu ƙarfi.
“Duk da cewar zan ce maiyasa kayi haka,nasiya musu gida tunda daɗewa,amma kuma hakan bashine zai daƙushe farincikina na abinda kayi min mahaɗin rayuwata,nima ka zamemin tsagi na gangar jikin rayuwata,wadda rashinka cikinta bansan taya zanyi tunanin cigaba da rayuwar ba ma?”
“Kiyi Addu’a da fatan Allah yabarmu tare kawai,danni kinyimin abinda komai nayimiki ma anan gaba Basai kinyimin godiya ba,domin kin daɗe da biyana.
Badan nagaji ba da mun je kinga yanda aka raba sashena ba na da,wato nasu Abdulmaleek tunda shi wancan likitan yace shima bazai koma indian ba anan zai zauna”
“Ohh hmm ya zancen maganar su da waɗancan ƴan biyunne,nidai naji suna cemin jiya wai sunyi wa baba magana(malam Ahmadu) kan cewar suna son su hilyan,shine yace su bari zayyi magana da Abbah”
“Uhm sunyi maganar jiyan da daddare,zakusha bikifah wajen shida inaga,tunda akwai nasu Maleekah da Madeenah ma,naji sunce wai duk tare za’a haɗa tunda na gidane”
“Uhm Aidama tunda naga yakoma bakin aikinsa nasan shiri yakeyi,wayaga maleekah matar gen Khmees,gakuma amaryar Khaleel ma.
Hmmm gaskiya kam za’a sha biki,gashi duk nice mai shirya komai ba”
Da sauran lokaci ai tunda ko tsaida rana ma ba’ayiba.
Komawa cikin motar sukayi suna ƴar hirarsu har suka ƙarisa sashensu.
Tun daga bakin ƙofar shiga sashennasu ta kula yanda yake aika mata wani kallo mai cikeda ma’anoni.
Bata so biyeshi ba lokacinma,saidai yanayin yanda yake ciki tasan yayi ƙoƙari sosai,dan haka bata hanashi miƙa saƙonsa zuwa gareta ba,saima taimaka masa tadayi wajen ƙarfafa saƙon yatafi yanda ake so.
Dan ita kanta idan tace bata buƙatar mijinnata da kuma jin tsagwaron kasancewa dashi to tayi ƙarya.
Wannan dalilin ne yasa ta bada kai bore ya hau,suka taka mataki na gaba ba zama abu guda a zamannasu,cikeda soyayya da kuma annashuwa.
A ranar farinciki a wajen Jabeer baya misaltuwa,dan yaune ya amsa sunansa na angon Amaryar tasa bombee,wacce akayi auren da daɗewa amma cikin gwargwamaya sai yau akai ga cimma buri na zaman taren.

**** ****

*Bayan wata bakwai*

“Ahh serious fah dagaske cikin juyawa yake Abban haidar tunda na tashi dasafe”
A zaune take akan doguwar kujera ta mimmiƙe ƙafafu wanda Jabeer yake mammatsa mata saboda kumburin dasukayi.
“Wai dagaske kike dama,hmmm saida nacemiki ki rabu dasu da wani bikinsu ki huta saboda yanayin dakike ciki,yanzu gashinan kimgama bawa kanki wahala su kowa ya ɗauke amaryarsa sun lula basama ƙasar.
Suna shirin sakaki haihuwa tun lokaci bayyi ba,ai idan har wata matsala tafaru dukkansu saisun dawo ƙasar nan a yau”
Masifah Jabeer yake har cikin ransa,yana matsa mata ƙafar cikeda kulawa.
Dariyah bombee tayi tana kama gefen ciki.
“Easy mana my man,bana tunanin haihuwa…….”
“Ohh inaga fah itace ɗakko ɗakko min zani na saka akan kujerar nan,naji abu yana zubowa ba tsayawa”
Cikin azama jikinsa har rawa yake ya ɗakko mata zanin,zuwa lokacin tana ƙoƙarin miƙewa,amma abu yagagara saboda riƙewar da mararta tayi sosai.
Zanin yasaka mata ta bayanta,tun kafim tayi magana ya kinkimeta zuwa cikin mota,a hanya yaƙira Hajiyah Zeenah ya faɗamata itada Su inna.
Direct asibitin su ƙawarta ya nufah wato dr. Rahama,dan haka tun kafin su isa ma har an shirya komai.
Suna zuwa babu bata lokaci aka shiga da ita labour,har ta galabaita sosai,banda jijjiga kai babu abinta take.
Saida suka shiga ɗakin kafin Jabeer ya dawo wajen dazai zauna ya jirasu,yana nan tsaye yana safa da marwa su inna suka iso itada Hajiyah Zeenah.
“Jabeer yaya jikinnata dai”
“Hmm wlh mommah bikinnan da akayi nasu Abdulmaleek gabaɗaya bata samu da zauna ta huta ba har aka gama,tun jiya dama take cewa jikinta yayi nauyi sosai,sannan abin cikinta baya motsi sosai,nayi tunanin gajiyace nasaka ta yin wanka da ruwan zafi ta kwanta.
To dasafe kuma sai tatashi da ciwon mara,kafin wani lokaci haihuwa tazo”
“Tabb yo ina aka san wanann lamari,kaga fah ranar yininnan sau kusan uku ina ƙiranta ta zauna ta huta a sashena,amma abu kaɗan saikaga sun turo a ƙirata,nayi faɗan har gaji,ƙarshema saina daina ganinsu.
Yanzu gashi sun jawo mata haihuwa a wata bakwai su kuma suna shan shagali koh.
Maza ka ƙirasu kace su dawo to”
“Ahah haba Hajiyah ayi haka,kibarsu suci lokacinsu,ita kuma muyi mata fatan allah yaraba lafiya kawai”
Haka Hajiyah Zeenah tacigaba da sababi innna Danejo tana dannarta,ba ita tayi shuru ba saida Dr. Rahma tafito tana murmushi tukunna.
“To Alhamdulillah ta haihu hajiya,tasamu ƴaƴa biyu mata,amma daga ita har su suna hutu,kasancewar dama jikinta a gajiye yake,sukuma yaron ƴan bakwaine basuda ƙarfi sosai,sai an basu kulawa ta musamman”
Sauran bayananta iyah Jabeer ne kawai ya nutsu yajishi,sukam tunda aka ce babu matsala murna ce kawai tabiyo baya.

*Paris*

A hotel guda suka zauna,saidai kowa da nasa ɗakin.
Dukkansu shiryawa suka yi dasafen zuwa jaga gari.
A zaune suke a irin grass field ɗinnan suna karyawa,kowa matarsa tana gefensa,sunyi sharr dasu cikeda nishaɗi.
Wayar Abdulmaleek ce tayi ƙara hilyan ta miƙamasa.
“Honey big bro yana ƙiranka”
“Da sanyin safiyar nan,yanzu kam tunda mun basu waje suma ai saisuyi cin amarci na biyu”
Dariya suka saka kafin ya ɗora wayar a kunne.
“Sannun ku newly wed,ya kuke ya kowa da kowa”
“Ahh sannu big bro kowa ƙalau yake,muna tarene muna karyawa ma”
“Uhm to inkun gama karyawar saiku juyo ku dawo,kun gajiyarmin da mata gashinan Ta haihu lokaci bayyi ba”
Saurin tashi tsaye Abdulmaleek yayi tareda zare jikinsa daga na hilyan.
Suma sauran wanda kowa ke bawa tasa matar abinci a baki kallon sa sukayi.
“Hasbunnallah garin yaya haka?”
“Kai kaga is nothing worse ta haihu lafiya ta samu ƴan biyu mata,dukkansu suna cikin ƙoshin lafiyah,amma dai dr. Rahama zata riƙesu su huta na kwana ɗaya,saboda yaran basuda ƙarfi sosai”
Wata ajiyar zuciya Abdulmaleek yayi tareda komawa ya zauna.
“Ahh thank god,da daɗi tunda ba’a samu matsala,ai abu kam hardamu yasashafa kam,wanne honeymoon zamu cigaba nephews na jiran a gida,muna nan dawowa”
Sauƙe wayar yayi yana kallon idanuwa suna jiran yayi musu bayani..
“Congratulation!!!! Anty maryam ta haihu twin yanzunnan,komawa gida kenan ya kamamu dan uban gayya yana cewa mune muka saka matarsa naƙuda da wuri,dan haka yanzu saimu koma mu kuma muyi shirin yimata bikin suna”
“Ahh Lallai bro ,indai wanann ne ai ba matsala bace,nihar na matsuma mukoma na gansu,i think yanzu can zaifi interesting akan nan,koya kuka ce”
Maleekah tafaɗa cikeda murnar jin labarin.

A kwance take akan gadon asibitin,an saka mata bargo rabin cikinta.
Bacci take kana gani kasan na hutune.
A hankali ya zauna a bakin gadonnata tareda saka hannunsa a nata.
Idonsa ya cire daga kanta ya mayar wajen jinjiran,wanda aka lullubesu da kaya masu laushi,ɗan motsin su kawai kake gani.
“Har sun ɗauke maka hankali dakaina koh?”
Tafaɗa a hankali tana tsuke baki,itama wajen da yaran suke take kallo.
“Wanene ni na isa idona ya ɗauke daga kan gimbiyata,ya jikinnaki toh?”
“Jiki Alhamdulillah kawai karfin jikinne har yanzu da saura,ya yaran lafiyarsu kalau?”
“Mommah na da inna tah lafiyarsu ƙalau,maman su suke jira da gama samun sauƙi mu tafi gida”
“Haka kasaka musu?”
“Uhm haka nasaka musu inafatan yayi miki koh?”
“Sosai Allah ya albarkacesu ya rayasu,ina fatan dai baka faɗawa su Maleekah ba koh”
“Tun ɗazu ma na faɗamusu ai dole su dawo suma suji”
“Ohh dear dabaka faɗamusu ba atleast sai ana jibi suna”
“Ahah gwanda su dawo suyi komai abinda za’ayi ranar sunan,dan daga nan har ranar hutawa zakiyi tayi”
Murmushi tayi tareda ɗaga masa kai,dan ita wani lokacin har mamakin soyayyar da mijinnata yake mata take,wanda tayi imani daga Allah ne hakan yafaru.

Babu abinda zatace sai Allah yabarta da ahalinnata,kuma yabata ikon tsayawa akan su dabada dukkan taimakonta wajen ganin sun dawwama cikin farinciki.
“Nagode”
Ɗagowa yayi daga kallon yaran ya kalleta tareda sake matse hannunsa a nata.
“Shin mai nayi miki dana cancanci wannan godiyar?,nine mai godiya gareki da kika bani Ahali maryam,a lokacin dana yanke tsammanin samunsu,ke haskece da Allah ya turomin bayan tsawon lokacin danayi a duhu.Nagode miki har fiyeda da yanda baki ba zai iya furtawa ba,fatana faranta miki da kuma kyauta muku keda Ahalina gabaki ɗaya”
Yunƙurawa bombee tayi ta tashi tareda sako hannunta a kafaɗarsa..
Sunkuyowa yayi kaɗan ta kanƙameshi a jikinta,hakan ba ƙaramin bashi dariya yayi ba.
“Karka ce komai,bansan taya zan maida maka martanin maganarka ba sai iya ta haka.
Koda ban mayar maka ba amma dolene nace

“ALHAMDULILLAH”
Da kyautar dayayimin.

Nima anan na datse alƙalamina tareda cewa Alhamdulillah.

*AFUWAN*
Kuyimin afuwa masu karatu na takure labari a kusan ƙarshe,buƙatar hakan ce ta taso saboda banida ishashshen lokaci,inaga dana tsaya ban ƙarisa ba,gwanda na taƙaiƙata labarin ya tsaya iya haka.
Nagode da nuna ƙaunarku ga littafina.
Zanyi muku sallama saikuma in Allah da ikonsa yasake haɗamu a wani littafin inshaallah.

Wassalamu Alaikum

Ga number wayata inda mai ƙarin bayani,godiya ko kuma ƙorafi duk ƙofata a buɗe take.
09035784150

_*SADI-SAKHNA CE*_

“Iyani iyani iyani na barshi ya wuce?…. Ke ganau ce ba jiyau ba akan abinda wannan tsinanniyar yarinyar tayimin,nifa na haifi yaron amma ta maidashi gabaɗaya ƙarƙashin ikonta,har faɗamin take tafi ƙarfin babu abinda na isa nayi..

“Oh haka fah ai munji duk labarin abinda yafaru,Ƙaramin haidar ma na ganshi a wajen hilyan dakuma ƙanwar mijinnaki,sukamma basu fito ba har yanzu,kinsan abin zai fi tabasu fiyeda kowa”
“Hakane kam shiyasa ma zamu tafi saisun taho daga baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button