Sponsored Links
Hausa NovelsSoldiers Family

Soldiers Family 55-56

Sponsored Links

Page  55&56

 

__”a Perkin space yacimmasa Yana k’ok’arin bud’e mota yashiga,,rik’o hannunshi abu yayi hakan yasa yajiyo da azabar k’arfi tareda d’aga hannu zekai duka kawai seyaga Abu ne hakan yasa yamayarda hannunshi Yana zubamasa rinannun idanuwanshi dasukayi kamar wuta…shidai Abu hannunshi kawai yarik’o tareda juyawa dashi zuwa part d’in ammy yakaishi har bedroom d’inshi kana yad’auko ruwan sanyi yabashi amma yak’i Sha seda Abu yayi da gaske kana yad’ansha ruwan Kuma cikin ikon Allah zuciyar tad’an fad’a,,,ganin Yana sauke numfashi ahankali tareda lumshe kyakkyawan idanuwanshi yasa Abu rik’o hannunshi yace “alyasat,,d’agowa yayi ya kalli Abu batareda yace komaiba hakan yasa Abu cigabada magana.

 

“Inaso kazamo me d’aukar k’addara me kyau ko akasinta alyasat abunda yafaru yarigada yafaru bawanda ya,Isa yacanja wannan k’addarar Kuma dakafita Ina zakaje awannan halin? Nasan baze wuce asibitiba gun najeeb Kuma kaga halinda yake ciki shin K’arasashi zakayine? Komi mazaka Masa aibazemasaniba bazamu hanaka hukuntashiba dudda cewa yakarb’i hukuncin daya dace Amma kabari yasamu lpy tukunnah Kuma kasani wannan abun dayafaru kama kanada hannu aciki domin dakanatareda matarka ba yadda za,ayi wani namujin yayi k’ok’arin aikata hakan agareta Kuma ka godewa Allah ba abunda yafaru tsakaninsu domin duk Wanda yabijirewa umurnin iyeye tofa seyaga abubuwa marasa dad’i arayuwarsa dudda baka fito fili kace bazakabi umurnin habeeb ba Amma yadda kayi yanuna bazaki biyayya akan umurninsaba sabida hakan kurik’a kiyaye duk wani abunda iyaye zasu umurceku Koda kuwa bakwaso domin samun kwanciyar hankali arayuwa,,,Dan shiru Abu yayi kamun yace yanzu inaso kameda hankali wurin addu,ar Allah yamaida maka matarka lpy tareda abuncikinta batareda wata matsalaba kajiko?

 

Girgiza kansa kawai yayi alamar yaji d’in domin yadda yakejin zuciyarsa bayajin ze iya magana Kuma tabbas jikinsa yayi sanyi yasan duk abunda Abu yafad’a gaskiya ne seyanzu yake danasanin beyewa zuciyarsa dayayi harya aikata hakan,,,tashi yayi yashiga bathroom tareda d’auro alwala yafito yashinfid’a sallaya ganin hakan yasa Abu mik’ewa yafita shiko yashiga jero nafilfili tareda nemawa kansa da Marta sassaucin abunda kedamunsu dakuma fatan Allah yasa su hak’ura sumaida masa matarsa.

 

 

Part d’in habibbty kuwa alyasat nafita abbe yacewa dady kaga abunda yasa nahana agayawa alyasat wannan zancen yanzu gashi ai kafad’a..sudai duka matan sunshiga sabon tashin hankali da mmkin wannan Al amarin dayakutsokai acikin ahalinsu daga wannan se wancan,,,,appey kuwa fad’a sosai yayiwa dady akan fad’ar wannan abun dayayi agaban alyasat daga Nan Kuma ya,umurci kowa da abar zancennan Kuma sudage da addu,a acikin wannan abun ko Allah zekawo sauk’in Shi daga hakan suka d’unguma zuwa asbiti gun najeeb Amma Banda dady.

 

Bibibo

 

Yana fitada mama bedireta ko inaba se masarautarsu turakar gimbiya halila yayi Mata bayanin komai dake faruwa,,Aiko fad’a sosai gimbiya halila tayi masa akan d’auko ta dayayi koba komai hankalin abbe zetashi sosai tanuna Masa b’acin ranta sosai inda tace doline yamaidata gidan mujinta tana gama fad’ar hakan takira maheerah tazo tabata temakon gaggawa tunda asome take,,,bayan maheerah tazo tayiwa mama duk wani abunda yadace Kuma ta tabbatar da cikinta besamu wata matsalar ba yanzuma yashigo 6 month (kenan dai tin had’uwar su tafarko wannan cikin yasamu kenan🤔)

 

Umurni tabashi cewar maza yamaidata Amma yakaita part d’in ammy,, mik’ewa yayi ze d’auketa kenan wani bafad’e yace suzo dukkansu me martaba nasan ganinsu domin lbr yakaimasa cewa maheer yashigoda wata bil,adama acikin masarauta.

 

Hakan yasa yad’auketa duk suka nufi turakar memartaba d’in inda suka samu har mahaifiyarsu nacan,,,bayan sungaisaida iyayen nasu maheer yakwantarda mama dake bacci agefe.

 

Kallonsu duka memartaba yayi Yana nazarinsu gabaki d’aya dukkansu sunshige gashi kamar Muna fukai,,cikin dattako me martaba yafara tambayar maheer miye had’inshida mama yace kodai “abunda nake hanakune kuka fara maheer cutadda nak’asa daku? Shin banhanaku shiga jikin bil,adama ba balle har kuzama silar wata cutarwa agaresu?

 

D’agowa maheer yayi dasauri Jin abunda mahaifin nasu yafad’a cikin girmamawa yace “wlh memartaba bahaka bane Babu abunda ke tsakanina da wannan yarinyar se alkhairi Kuma bamani kad’ai ba hadda Y’an uwana da cutarda ita zanyi bazan Bari ahalina susanda itaba hasalima temakonta mukeyi kumafa tanada aure,

 

“Aure? Kuma kad’aukota? Cewar memartaba ahasale kana yace wannan wanne irin temakone Wanda bazayimatashi aduniyarsuba? Wannan karon gimbiya halila ce tayi magana cikin girmamawa tafarabawa mahaifin nasu lbrn komai dayashafi mama tinda had’uwarsu da mahaifiyarta alokacinda zata haifeta hai izuwa yanzu abunda yafaru maheer yad’aukota seda takai karshe kana tace Muna neman afuwarku mahaifanmu abisa b’oye muku wannan Al,amari damukayi.

 

Gabaki d’aya wurin yayi tsit bame cewa komai harna tsawon lokaci kamun memartaba yanisa Yana fad’ar tabbas kuntemaki way’annan bayin Allah Kuma tinda daniyar temako kukayi sabida Allah bazan hanakuba sedaima na k’arfafa muku Amma fa kasani maheer kayi kuskure nad’aukar matar wani koba jinsinku d’aya ba kaide namujine itako mace sabida hakan kadena tab’ata kasani cewa haramunne amusulunci duk abunda yafaru karik’a saka Y’an uwanta Mata kajiko?

 

“Insha Allah memartaba baza,ak’araba,,,yawwa Allah yayi maku albarka yanzu halila kimaidata gidan mujinta kinjiko…”aa ranka yadad’e baza,ayi hakanba Koda wancandaya nemi keta Mata haddi yayi kuskure shima mijin nata akwai nashi kuskuren sabida hakan gaskiya baza,amaidata yanzuba seyaji ajikinshi sedai abunda zance anan shine raunida maheer yayiwa wancan yaron tabbas Idan likitocin duniya zasu taru baze warkeba kokamanta yadda hannun maheer yakene? Shiru memartaba yayi Yana tinanin wannan gaskiya ne abunda tafad’a d’aga Kai yayi yace”ban mantaba tabbas indai jinsinsune baze warkeba Amma aike Zaki iya yimasa maganin daze warke acikin mako d’aya,,shiru mamarsu maheer tayi tana kauda kanta agefe,,ganin hakan yasa memartaba yayi murmushi domin yagano bazatayi bane cikin rarrashi yace haba uwar gidana Kuma amaryata maman gimbiyarmu da twins ketemaka kodan kitaya yaranki aikin ladanda suka d’auko Kuma kigyara b’arnarda yaronki yayi Dan Allah… murmushi tayi Jin yadda yake Mata magiya kana tace shikenan zanyi insha Allah,,yawwa kokefa cewar memartaba kana yace gimbiya halila takai mama turakar mamarsu domin karta farka taga wani abun da ze tsoratata,,kana yace Kuma duk wani abunda kan iya tasowa karsu tunkareshi su kad’ai susanar dashi zeyi abunda yace,,dahaka ya sallamesu kowannensu yatashi cikin farin ciki hakan gimbiya halila takai mama d’akin mamarsu Kuma tazauna tareda ita.

 

Bayan kwana biyu da faruwar hakan kowa acikin wannan family Yana cikin damuwa musamman alyasat daya koma kamar wani marar lpy bayaci baya Sha sedan abunda ba,arasaba gabaki d’aya yazama wani kala kallo d’aya zakayi Masa kasan cewa Yana cikin tashin hankali duk yafita hayyacinshi..mom ma tadamu sosai itada ammy dusu umma anty Billy ma tadamu tunda D’an tane yayi wannan aikin Kuma Bata goyi bayanshiba hasalima kuka tayi sosai Akan wannan abun daya aikata,

 

Anacikin wannan halinne su suhaif da twins suka dawo yadda zukasami ahalinnasu yayi Bala,in d’aga musu hankali Kuma tambayar duniya sunyi Ank’i gaya musu Mike faruwa kawai ance musu zaraah ta b’ata…jalaludeen ma yazo dayaji abunda kefaruwa domin shikam abbe yagaya masa komai acewarshi shine yayan zaraah doline yasan komai gameda ita,,,hankalin jalaludeen bakaramin tashi yayiba hakan yasa yad’auko hutu yadawo gida..yusif da lateep ma sunji suma suheil ne yagamusu Amma bancin way’annan bawanda yasanda wannan abun dukan s,tate d’in.

 

 

Gimbiya halila

 

Kulawa ta musamman take bawa mama itada mahaifiyarsu da maheerah,,hankali kwance mama kerayuwa acikinsu kamar acikin jinsinta domin dukkansu kallon mutane take masu,,agefe d’aya kuwa takullaci alyasat sosai domin aganinta shine yajamata wannan tozarcin agun k’annenshi shiyasa kozancenshi batasonji yanzu kusan 3 week kenan tana zamanta abunta,,,yaune mamarsu tashirya zataje asibiti gun najeeb inda gimbiya halila zatayi Mata jagora maheerah kuwa tazaunada mama,,a hakan suka shigo asibiti tareda zugar hadimanta..!

 

 

 

 

*SOLDIERS FAMILY* na kud’i ne nera 500 kacal 👌 ga duk me buk’atar complete kuma 700 ne Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub’ar wannan nomber 👉 07037092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan nomber 👉 08107819124

 

 

 

 

 

Autar alheri ✍️

 

*S F*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button