Sponsored Links
Duk Karfin Izzata Book 1Hausa Novels

Duk karfin Izzata Book 1 Page 15

Sponsored Links

Episode 15*

Bayan sungama shiryawa kamsu abubuwar dasuke buƙata na buɗa baki nan take masu aikima suka fara shigo da kulolin abinchi suna jerawa a kan table ɗin komawa ɗaki sukayi ɗaya bayan ɗaya sukayi wanka suka ɗauro alwalla hiyana diyana Zahra dogayen riguna na material sukasa maroon colour ” lamrat da amrat kuwa riga da sket na atamfa suka sa kai tsaye palon mai martaba suka nufa danyin buɗa baki da sallam suka shiga suka wuche kai tsaye kan table zama sukayi suna jiran time yachika a kira sallah ” shiru suka zauna kowa da tunanin dayake ” diyana che ta katse musu shirun dachewa Aunty Zahra sai narinƙa jin gidan ba ɗaɗi wlh saboda ba kowa ki kalla kan table ɗin nanfa da chika muke muna chin abinchi amma yanzu saura mukaɗai kai gaskiya na kosa su Abba sudawo ” Zahra zatayi magana saitaji an daƙa musu tsawa daga bakin kofar shigowa ” da sauri suka ɗago kai suna bin bakin kofar da kallo ” Auntyn Maryam suka gani tsaye fuskar nan babu annuri ko kaɗan nan take jikin Zahra yafara ɓari dan tasan halin Aunty Maryam sarai ” diyana kam kawar da idon ta tayi tachigaba da abun datake kamar bata san da wata Aunty maryam awajen ba “a nitse chikin sanyin murya hiyana tafara magana ina wuni Aunty Maryam ” wani mugun kallo Aunty Maryam ta wurgawa hiyana batare da ta amsa gaisuwarba chikin tsawa tafara magama uban waya baku izin kurinƙa zuwa nan kuchi abinchi inachewa Aisha itace yar uwar ku a gidan nan ” shiru sukayi basu che ko kalaba ” Aunty Maryam tachigaba dachewa to tunda wajen Aisha kukazo ku tsaya a iya ɓangarenta idan nasake ganinku a wani ɓangare na gidan nan, ba bangaren Aisha ba wlh sai na babballa yarinya kuzo kuficemin daga nan ko nashiga na muku mugun duka ” tunkan takai karshen maganarta suka mike gefenta sukabi zasu wuche ” hannu tasa ta damkoh wuyar rigar diyana tana faɗin ke ki buɗe kunnenki ki saurare ni da kyau daga yau bawanda zai sake share bangaren Aunty amarya keche zaki rinƙa yi har nabar gidan nan, ke bama shara kawaiba wankin kanana kayana wankin toilet mopping da yimini tausa kinajina bakinche ke bakida kunyaba to wlh zan gyara miki zama ” diyana binta kawai take da ido batace komaiba tayi shiru ” su Zahra kuwa wuchewa bangaren Ammi sukayi jiki ba kwari ” hannu Aunty Maryam tasa ta tsolewa diyana ido tana faɗin shegen ido kamar na mayu ai kedaga ganinkuma dangin mayune shiyasa aka faɗamin kun lashe zuchiyar kowa na gidan nan to nikam nafi karfinku ” hannu diyana tasa tana goge idonta tana hawaye zafi idon yake mata sosai ” sakin rigar nata Aunty Maryam tayi san nan tace yanzun nan kije ki wanke toilet’s dasuke bangaren Aunty amarya dukka san nan ki shiryamin abinchin buɗa baki ” ba musu diyana tanufi bangaren Aunty amarya tana hawaye Aunty Maryam kuwa ta wuche chikin ɗakin mai martaba

Abangaren su Zahra kuwa palon Ammi suka koma suka zauna a kan sofa nan take Zahra tafara hawaye ” hiyana tamike ta dawo kusa da ita tana faɗin lfy Aunty Zahra kike hawayen ” chikin kuka Zahra tace diyana nakewa kuka wlh dan nasan tun da Aunty Maryam ta tsai da ita wani muguntar zata shirya mata ” kiyishiru Aunty Zahra ninasan duk abunda Aunty Maryam zatawa diyana bazai kai kaso ɗaya chikin goma na wadda inna tamana ba dan haka ki daina damuwa ba irin muguntar da’bamuganiba chewar hiyana ” mikewa Zahra tayi tana faɗin kuzo muje muyi buɗa baki gashi chan ana kiran sallah ba musu suka nufi kichin na Ammi ” ruwa ko wannensu yafara sha san nan sukachi dabino ” zahra tace ku zauna a palo kujirani bari naje palon mai martaba ba ɗaukoh mana abinchinmu ” inkinje Aunty Maryam bazata bugekiba chewar hiyana ” eh bazata bugeniba ai duk dokar datake kafawa ku take kafawa baniba nikam ai bata isa tahanani yawo a gidan babana ba tana gama faɗin haka yanufi hanyar fita .

KASAR SAUDIA ✈️

Gaba ɗayansu suna chikin masallahchin a nan sukayi buɗa baki bayan sungama sunyi sallane suka zauna hira ” Ammi ta dubi Ummi tace Maryam fa tazo ” yaushe tazo chewar Ummi ” yau tazo Mai martaba yabasu amsa ” ya akayi wan nan karon tazo dawuri chewar Ummi ” tsaki Aunty amarya taka san nan tace oh bakisan tazo daman koh to tazo kuma bayadda zakuyi da ita ” mikewa DON yayi zai bar wajen ” Aryan yace jirani muje tare, tare ya faɗin hakan yana mikewa tare suka jera suka nufi hotel ɗinsu ” mai martaba yama Ammi magana da fillanchi Mikewa tayi tana faɗin Ummi muje Koh, mikewa Ummi’n tayi dan tasan mai Martaba ne ya umarchi Ammi dasu tafi ɗaki dan baisan hayani kuma baisan subiyewa Aunty amarya ” Khalid Aiman Ahmad suma suka mike a tare sukabi bayan DON da Aryan ” dawo da kallansa mai martaba yayi kan haidar da umar dake zaune basu tashiba, to me kuke jira, ai tun bai karasa magana’ba suka mike suka bar wajen ”
dawo da kallansa kan Aunty amarya daketa chika tana batsewa yayi a nitse yafara magana wai meyasa Hajara bakyasan zaman lfy’ne eh meyasa kullun ke kike tada husuma a chikinkune tunfa kina amarya kike irin wan nan hali wadda kikazo kusamuma baki kyaletaba haka wadda tazo tasamekima ” zatayi magana ya ɗaga mata hannu banasan inji komai daga gareki kawai abun danakeso karnasake jin wata fitina tatashi ,” ke ko kunyar ƴa’ƴanku ba kyaji kitashi muje mu kwanta yaƙarisa maganar yana kokarin mekewa hanyar ɗakinsu yanufa itama tamike tabi bayan’sa tanata chika tana batsewa

NIGERIA ✈️

Har wajen karfe 9 na dare diyana ta dawo ɓangarensu da kyar take tafiya saboda yinwa ko buɗa baki batayiba ko sallama babu ta shiga ɗakinsu ” tasamu su Zahra har sunyi wanka sunyi shirin barchi “Zahra na ganinta ta mike tana faɗin sannu diyana san nan tayi waje da sauri ” zama bakin gado tayi ta ɗago blue eyes nata dasuka sauya izuwa ja saboda yinwa da gajiya, tana kallan hiyana dake tsaye tana mata kallan karin bayani takeso ” diyana zatafara magana saiga Zahra ta dawo hannunta ɗauke da plate ɗin abinchi da cup mai ɗauke da tea mikawa diyana tai nantake ta karɓa tafara chi ” zama sukayi kusa da ita shiru itakuwa sai ɗura abinchi take hannu baka hannu kwarya

Wayar Zahra tasoma ringing da sauri amrat dake rike da wayar tamiƙa mata my lovely bro ne yabayyana a kan screen ɗin wayar da sauri Zahra tayi picking call ɗin tare dasa wayar a H-free tana faɗin hello yaya khalid ” wani dogon numfashi Khalid yaja tare da sauke ajiyar zuchiya kana yace my lovely sister ykk ya makaranta ” muna lfy makaranta alhamdulillah Zahra zata sake magana taji ” diyana takwache wayar tana faɗin yaya Khalid ina yaya Aryan dan Allah inasan inyi magana dashine ” baki buɗe’su Zahra ke kallanta ” Khalid kuwa chewa yayi ai daman dan ke nakira shima magana yakesanyi dake ” yauwa to bashi,”miƙawa Aryan dake zaune kusa dashi wayar Khalid yayi ” ansa Aryan yayi yasa a kunnensa yana faɗin hello ” yauwa yaya Aryan ina wuni ” lfy lau y school ”
khalid kuwa miƙewa yayi yana faɗin inazuwa hannunsa Aryan yakama yamai’dashi ya zauna yana harararsa ” yaya Aryan wlh yau wan nan Aunty Maryam ɗin takusan kasheni chewar diyana ” a zafafe Aryan yace what ? bana rabakuba mekuma yasake kai ki wajenta ” turo baki tayi kamar tana gabansa tafara bashi lbr abun daya faru daga farko harkarshe ” shiru yaɗanyi yana tunani daman yasan za’ayi hakan tunda yaji Aunty Maryam tazo ba lokachin zuwansuba yasan da dalili yayi nisa chikin tunani ” muryan ta ta katse masa tunanin dacewa ” yaya Aryan dan Allah kudawo kaga idan kun dawo Abba bazai bari tarinƙa buguna ba ” karki damu saura kwana 10 mu dawo kuma I next week Aunty farida zatazo domin tarbarmu idan Aunty farida tana nan bazata bari a muku komaiba, amma duk dahaka zanmata magana ” to shike nan sai dasafe ” murmushi kaɗan yaɗanyi kafin yace bakyasan hira danine kikechemin sai da safe ” khalid dake zaune kusa dashi ya ɗago a sukwane yana kallansa fisge hannunsa yayi daga rikon da Aryan yamasa yamike yana faɗin idan kagama hirar, kasameni a ɗaki kaga tafiyata ” harara Aryan ya wurga’masa ” khalid bai bita kansaba yayi waje
Diyana kuwa dariya tai san nan tace to ai abinchi nake chi nifa yanzu nake buɗabaki ” shiru yayi zuchiyarsa tana masa zafi sosai yafara tunanin matakin daya kamata ya ɗauka wan nan wani irin zalunchi’ne yarinya tayi azumin san nan kijib’ga mata wan nan uban aiki kuma ki hanata buɗa baki yanzu kusan karfe 10 nadare wai batayi buɗa bakiba, dole na ɗau mataki ” jin yayi shirune yasa diyana cewa yaya Aryan kodai kayi barchine ” aa banyiba kawai ina ɗan tunanine ” to shike nan sai anjima bari nagama chin abin china ” ok kichi a hankali dai kuma banda chin fruits dayawa dan inchikin’ki yafara chiwo kinga bamunan bare namiki allura ” dariya tayi san nan tace to bazan chiba ” ok kawai yace san nan ya katse kiran ya ajiye wayar a gefe ya dafe kansa yana tunani ” dayaga dai tunanin ba wata mafita, sai yaike ya nufi kan katafaren gadansa ya konta yajawo wayarsa yafara latsawa

Bayan diyana tagama chin abinchinta tamike tanufi toilet wanka tayi tafito daure da towel kayan barchi tasa doguwar riga mai siririn hannu yar shafal mara nauyi kwanche ta iske su Zahra sunata yar hirarsu, dayake yanzu su amrat ma sun dawo ɗakinsu, saboda suna tsoro tunda ba kowa a gidan sai suka haɗu suka chure waje guda
Hayewa samar gadon nasu tayi itama tana faɗin Aunty Zahra kunna mana kallo ” to kawai Zahra tace tare da dauko wayarta dake gefenta ta shiga gallery tana kokarin neman film sai taga kira yashigo ” da sauri tayi picking call ɗin tana faɗin yaya Khalid bakayi barchiba ” eh banyi barchiba ya’za’ayi nayi barchi bamuyi wayaba ” Zahra zatayi magana sukaji an banko kofar ɗakin nasu da karfi gaske ” zubur suka mike gaba ɗayansu har sai da wayar Zahra tafaɗi kasa dan tsorata dasukayi ” a zafafe Aunty Maryam ta shigo chikin ɗaki kai tsaye wajen diyana tanufa damkoh wuyarta tayi tafara bugunta ta ko ina ” diyana tafara ihu ” nizaki haɗa faɗa da ɗan uwana koh to wlh yau sai na kasheki, tun danake dashi baitaba kirana a wayaba amma yau saboda’ke sau biyu yana kirana bugunta Aunty Maryam keyi tana surutai ” diyana kuwa sai ihu take ” hiyana naganin Aunty Maryam na kokarin kashe diyana da gaske ta kwasa a guje tayi wajensu tana kokarin kwache diyana a hannunta ” hankaɗe ta Aunty Maryam tayi da karfi ta tafi ta bugu da bango nantake kanta yafashe ” ihu mai karfi Zahra tabuga tayi kan hiyana tana kiran su nanta ” lamrat da amrat kuwa sai kuka suke ” duk da raunin da hiyana taji bai hanata sake mikewa a zafafe tayi kan Aunty Maryam tana faɗin karki kashemin ƴar uwa dan allah ” wani bugu Aunty Maryam tasake kaiwa hiyana a baki ” kukan kura hiyana tayi a fusace ta damki wuyar Aunty Maryam ta baya ” bashiri tasaki wuyar diyana ta juyo ta damki hiyana tashiga bugu ” da gudu Zahra tazo ta duƙa takama kafar Aunty Maryam tana rokonta ” dan allah Aunty Maryam kiyi hakuri ki kyalesu wlh marayune basu da uwa basu.. Zahra bata karisa ba taji saukar mari a faskar ta a zafafe Aunty Maryam tace. Kifita a ɗakin nan zahra’u kokuma na haɗa dake ” mikewa Zahra tayi tana kuka takama hannun amrat da lamrat tace muje ” kwache hannunta lamrat tayi tayi gun Aunty Maryam da gudu tana faɗin dan allah ki kyalemin yan uwana haka ” kafa Aunty Maryam tasa ta amɓare lamrat tafaɗi kasa tana kuka ” da kyar diyana tamike tana ɗingisa kafa ta karisa wajen ta duka gaban Aunty Maryam tace ninamiki laifi basuba kiyiwa Allah kisakemin yar uwata ni ki kasheni inkinaso ” juyowa tayi ta damki wuyar diyana ta damkoh hiyana ta haɗe kansu ta buga da karfin gaske wani kara suka sake a tare ” Zahra da amrat dake tsaye a bakin kofa da gudu suka dawo chikin ɗakin ” Aunty Maryam kuwa duk da hakan bata kyalesuba sake damkar gashin kan diyana tai tana janta a kasa har zuwa wajen mirrow tasa hannu kan mirrow ta dauki wani kwalbar turaren humra zata buga mata ke nan taji anche STOP chikin tsawa da sauri ta ɗago kai idanunta suka sauka akan…✍️✍️✍️

 

More comments an share pls 🙏

 

*

 

 

💫STAR LADY💫*27*

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

 

*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button