Sponsored Links
Hausa NovelsSoldiers Family

Soldiers Family 19-20

Sponsored Links

Page 19&20

 

 

Free page yak’are daga wannan kiyi hanzari kinemi naki domin karki Bari abaki lbr

 

 

__”amsawa sukayi duk suna kallanshi kana yasamu wuri yazauna kusan mama yace””uwar gijiyata nayi bince akan sihirin sedai kamar yadda anty halila tace doline sedake zamu karyashi nisawa yayi kamun yasake cewa aikin Yana cikin ruwa acan akajefashi Kuma gudu yakeyi yadda wannan sihirin ke gudu hakan abbanki zeyita yawo aduniya batareda sanin takamammen inda zashiba ajiya nasaka antsayarda aikin inda zamu samu sauk’in kamashi sedaifa bawanda ze iya fiddashi acikin ruwannan se bil adama sabida hakan Idan kinshirya semuje…..kamun tayi magana jalaludeen yayi saurin cewa aa kabari Ni muje ai wannan tayi k’arama kartasaka kanta ahad’ari…murmushi gimbiya halila tayi kamun tace ba Wanda ze iya wannan se ita domin tana tattareda abunda bakadashi sabida hakan kabari suje kawai kaide kayi musu fatan nasara…nisawa yayi kamun yace shikenan Allah yabasu sa,a akan abunda zasuje nema… ameen y Allah duk suka amsa kana mama tamik’e tana cewa bibibo suje mik’ewa shima yayi kana maheerah ma tamik’e sukabar wurin seya rage daga gimbiya halila sesu mero datawagar sojojinsu jalaludeen..!

 

Dubai

 

Alyasat nafita yawuce part d’in yusif aperlo yasameshi zaune Yana aiki a computer d’inshi zama yayi kusadashi tareda jingina bayanshi jikin kujerar batareda yace komaiba tinanin yake aranshi wannan wanne irin Bala,I ne ace y’ay’a family d’aya Amma suna neman junansu Idan son muhibbat shareef keyi baze auretaba itako dake fad’ar tana sanshi Ashe duka karyace Aiko zeyi maganinsu….tinaninshi ne yakatse lokacinda yaji yusif nakiran sunanshi yad’ago shima Yana dubanshi…”Miyake faruwa ne bro Naga kayi shiru se tinani kakeyi? Dan yamutsa face d’inshi yayi kamun yace no bakomai kawai inasan komawa London ne kamun mudawo bikinnan daza,ayi kaga daganan semu dawo aikinan Baki d’aya ko?

 

Shiru yusif yayi nadan wani lokacin kana yace hakan zeyu kuwa? “Eh mana kodama bazeyuba nibazan cigabada zama acanba domin gidannan namu akwai matsaloli sosai gaskiya doline murik’a saka Ido gudun faruwar wani mummunan abun…nisawa yusif yayi yace hakane bro to kodai kaga abunda kefaruwa ne acikin stet d’innan?

 

Da mmki alyasat ke dubanshi kamun yace wani abunne yafaru?

 

“Humm zokaga yusif yafad’a Yana nuna masa abunda ke cikin computer d’inshi…Ido alyasat yad’an bud’e kamun yadafe kanshi domin abunda yagani yabashi mmki sosai dudda yaga wani shima Amma beyi tinanin abun yake hakanba…ganin yayi shiru bece komaiba ne yasa yusif fad’ar yanzu minene abunyi?

 

 

“Humm zamuyi maganinsu soon bro daga hakan bek’ara cewa komaiba..ganin hakan yasa yusif fad’ar tashi muje mud’auko wani mlm danayi magana dashi akan rashin lpyr ammy tind’azu yace mun suntaso nasan izuwa yanzu jirginsu yakusa sauka daga saudia zezo…dobanshi kawai alyasat yatsayayi Yana tinani aranshi inama ace dukan soldiers family kamar yusif suke sedai Kash kowada kalar nashi ha layyar….seda yusif yarik’o hannunshi kana yamik’e suka Kira lateep sukabar gidan..!

 

 

Ghana

 

 

Suna fita suka d’auke mama tareda shiga keta jejuka da ita basuzarce ko inaba se wani k’aton teku Wanda mutin be Isa yace ga tsawon ruwan ko fad’insu ba balle ayi zancen ganin karshensu seda sukakai Dede wani katon dutse da ruwa kifita cikinshi suna gangarawa kana bibibo ya ajiye mama tareda fad’awa cikin ruwan itako maheerah tana tsaye tareda ita duk wani aljani Idan yazo wucewa yahangi mama seya kawo Mata Hari sedai daga zarar sun k’araso duba d’aya suke Mata sukoma bashiri (komiyasa hakan🤔)

 

Yad’auki tsawon lokaci acikin ruwan kamun ya k’walawa maheerah Kira Yana fad’ar yasamu ganin sihirin tashigo da Mama Aiko ko bakinshi be rufeba tarik’e mama suka nutsa aciki can kasan ruwan wani katon ledane aka nannad’e kamar ball ko tarewarda maheer yayiwa abun yakasa tsayi wuri d’aya cikin k’araji yacewa Mahira tanunawa mama tad’auka domin masu tsaronshi gab sukeda k’arasowa wurin…tana nunawa mama tasaka hannu biyu tareda bismillah tad’auko Amma me tana rikonshi aka fara janta kamar igiyar ruwar zata tafida ita ganin hakan yasa sukayi saurin fitowada ita ta gab’ar ruwan suna fitowa maheer yace tadoka abun ak’asa Idan tayi hakan baze k’ara komawa cikin ruwaba Kuma kowa ze iya k’arasa aikin

 

Hakako tayi domin dagewa tayida iya k’arfinta tadokashi k’asa aitana dokashi itama ana wullata cikin ruwan hakan sukaga anjefata kamar walk’iya kamun maheer yayi wani yunk’urin tuni maheerah tabi bayanta Amma se tamaula ruwan keyida ita sunaneman hallakata dak’arfi gaske Mahira tasamu nasarar cabkota kana tafitoda ita Amma tuni tasuma…seda suka B’ata lokaci sosai wurin ganin sun ceci rayuwarta seda ta farfad’o dudda batadawo normal ba kana suka shiga kiciciniyar walwale wannan sihiri wani irin mird’ewane akamasa wani abun cikin wani hakan sukayita banye abubuwa daga karshe suna Kai karshen kullin sekawai sukaga guntun takalmine dawani Kashi se dunkulin jini da babyn roba mekamada wancan dattijon sak…suna gama bud’ewa maheerah tak’ona kayan.

 

 

Aiko zunbur abban mama dake kwance tin bayan tafiyarsu yamik’e tsaye kamar Wanda aka tsikara duk seda suka bishi da kallo arazane Amma Banda gimbiya halila daketa famar murmushi…shiko rik’e kanshi yayi dake juya Mashi sosai kana yayi baya luuuuu ze Fad’i cikin sauri jalaludeen yataroshi yafad’a jikinshi… d’agowa yayi Yana kallon gimbiya halila kamar zeyi kuka se kawai ta girgizamai Kai alamar karyayi…shiru yayi Yana duban abbe nasu yakai kusan minti 5 ahakan kamun gimbiya halila tacewa mero takawo ruwa ba musu kuwa mero takawo mikawa jalaludeen tayi tana fad’ar kayi addu,a tukunnah kashafa masa a fuska…hakanko akayi bayan yakarb’a yayi addu,ar kamar yadda tace kana yashafa masa a fuska atake yasauke ajiyar zuciya me k’arfi kana yafara bud’e idonshi da salati d’auke abakinshi yabud’e su tarr akan fuskar jalaludeen…yunkurawa yayi zetashi jalaludeen yatemaka masa yatashi kana shiga k’arewa wurin kallo cikin sauri jalaludeen yace abbe.

 

“”Na,am jalal inamuke anan mimukeyi anan? Ina alyasat?

 

“Alhmdllh alhmdllh alhmdllh shine kawai abunda kefitowa daga bakin jalaludeen yabud’e baki zeyi magana kenan su bibibo suka bayyana awurin yanad’auka mama…cikin sauri gimbiya halila tamik’e Wanda sukayi atare itada jalaludeen miyasa meta maheer? Cewar gimbiya halila…karkidamu tajigatane sabida matsalar da kasamu Amma komai lpy insha Allah..to alhmdllh tafad’a tareda bashi wuri ya kwantarda ita… maheerah ce tashiga Basu lbrn abunda yafaru acan dakuma yadda sukayida abunda suka d’auko…shidai jalaludeen inbanda tasbihi ga ubangiji ba,abunda yakeyi…yayinda gimbiya halila tayi musu Adda,a sosai dakuma fatan alkhairi taname jinjinawa kannen nata dasuka kasance bayan sallah nagani☺️

 

 

“”Nisawa tayi tana fad’ar aiki yayi kyau sosai maheer domin abban zaraah yasamu lpy.. dukkansu murmushi sukayi hadda jalaludeen shiko abbe biye kawai yakedasu Yana kallo domin Sam besan inda kalamansu suka nufaba Kuma bayajin hausa garama jalal yad’an ji sabida zamanshi Nigeria

 

Ganin irin kallonda yake musune yasa gimbiya halila fad’ar sannu bawan Allah nasandai dukkanmu Nan baka sannumuba bancin wannan

 

 

Tanuna jalaludeen dake zaune kusanshi d’aga Mata Kai yayi domin da larabci take magana shiyasa yafahimceta… cigaba tayida fad’ar to abunda yafaru gaskiya wannan yarinyar itace silar had’uwarmu dakai tanuna mama dake kwance kana tabashi lbrn tin lokacin da mama ta tahad’u dashi har izuwa kawo yanzu da sihirin yabar jikinshi shera 4 kenan..seda takai karshe kana tace kaji yadda akayi muka sameka har zuwan wannan bawan Allah yace Kai abbanshine..

 

Shiru kawai abbe yayi Yana sauraronta idonshi suncika Tabb da k’walla Yama kasace komai se aikin kallon mama yake

 

 

Jalaludeen kuwa se murmushi yakeyi seda gimbiya halila tace kagaya masa yadda kuka rasashi domin hankalinshi yak’ara kwanciya Nan ko jalaludeen yabashi lbr iya abunda yasani na b’atanshi dakuma tashin hankalin da ahalinsu suka shiga Amma ya boye masa cinwon ammy…awannan Karon kuka sosai abbe keyi bawanda yahanashi domin dukkansu sunsan abunda ciwo sosai arabakada ahalinka natsawon shekaru…ana cikin wannan halinne mama tafarka tana turo baki gaba tana Kiran bibibo

 

 

*SOLDIERS FAMILY* complete ne ga duk me buk’atar complete akwai ak’asa 💃

 

 

 

Murmushi sukayi atare kana bibibo tarik’ata tatashi zaune kamun yace uwar gijiyata abbanki fa yasamu lpy…wani irin k’walalo Ido mama tayi kamun tasaka ihun murna tamik’e aguje taje gun abbe dake zaune Yana kallonta sekawai Tafad’a jikinshi tana abbana kawarkeko? Bazaka Kara ciwoba insha Allah yanzu mikakeso abbana naje nasaka Biba takawoma? Jin yayi shiru Kuma biyi Mata yadda yasaba ba seta d’ago tana dubanshi taga shid’in ma ita yake kallo kunya taji takamata atake Kuma jikinta yayi sanyi data tuna yafa samu lpy kardai ace yamantata janye jikinta tayi daga nashi zata Mike sekawai taji yamaidata Yana shafa bayanta hawaye nazuba a idonshi  godiya yakesan yimata Amma yakasa furta komai se aikin shafa bayanta yakeyi Yana hawaye Koda ba,a bashi lbrn ta ba iya yadda tayi yanzu da,akace yasamu lpy ya,Isa yanuna masa tsananin sonda take masa shiko mizeyiwa wannan yarinya yabiyata aduniya…sunjima ahakan sosai kamun yad’agata Yana fad’ar ngd ngd ngd sosai y’ata Allah yayimiki albarka Allah yabaki ingattacciyar rayuwa Allah yabaki Ni,imar duniya data lahira Allah yabaki miji nagari Wanda zekulada rayuwarki cikin amunci… dukkansu da ameen suka amsa kana wurin ya keceda fira kowana bada lbrn abunda yasani kamun haduwarshi da wani..!

 

 

Dubai

 

Suna kan hanyar zuwa d’aukar mlm Abba yakirasu yace suzo yadawo ance suna nemanshi…to kawai sukace tareda K’arasawa suka d’auko mlm pert d’in ammy sukakaishi inda sukace suhaif da alhusain sukaishi inda ammy zasuje suga Abba…hakanko akayi bayan sunje gun Abba sunjima awurinshi suna tattaunawa bayan sungama kana suka fito kowannen ji yakeyi kamar ancire masa k’aya ajiki ahakan suka Isa pert d’in ammy suka samu mlm nazaune shida su Al Hassan domin yaduba ammy har an mayarda ita d’aki wuri suka samu suka zauna..

 

Kana mlm yashiga yimusu bayi “”agaskiya ciwon mahaifiyarku ba komai bane face babbak’un aljanu sune aka izo Mata Kuma akowacce Rana ta duniya tsafi sukeyi ajikinta domin ba,abuk’atar tawarke Kuma Basu tashi kashetaba ba,ba,abunda zance muku anan illa kudage da addu,a Kuma akwai wasu addu,oi dazan Baku zaku Rika yimatasu da maganin dazan,arika yimata wanka ana shafe mata jikinta sedaifa kusani abune me matuk’ar wahala rabatada way’annan hatsabiban alajanun shiyasa nace kudageda addu,a….nisawa suhaif yayi kana yace shikenan mlm mungode sosai Kuma insha Allah zamuyi yadda kace.

 

To allah yabata lpy…duk suka amsa da ameen shidai alyasat Yama kasa magana domin inba lugudeba Babu abunda zuciyarshi keyi tinani yakeyi wayayiwa mahaifiyashi wannan mummunan abun? Mita aikata agaresu da har za,acutarda ita? Atake yaji komai na stet d’in yafara tsanarshi domin inba nanba to wazemata wannan mugun aikin lallai shakka Babu duk Allah yatoni asirin Wanda yayi Mata wannan abun to sedai uwarsa ta haifi wani wlh…wannan tinanin dayakeyi shine yusif keyi hakama su Al,Hassan lateep dabaya boyone kawai yafitarda nashi Ali bayan sunyiwa mlm rakiya sundawo kallonshi duka sukayi Jin yafad’i abunda ke zukatansu kamun sumeke zuwa Shirin masalachi domin yau jimu,a.

 

 

Dukkansu sunshirya cikin manyan Kaya na larabawa jallabiya ce ajikinsu da hirami sunyi kyau matuk’a kamar kasacesu kagudu…shidai gogan natse yagame fuska kamar besan minene dariyaba lateep ne yakalleshi kamun yace kaikam matarka nada aiki bro wannan cin magani hakan humm lallai zatasha fama…dariya suka saka atareda yusif yace Kai bro wato bama shine zesha famaba ita? Eh mana lateep yafad’a Yana k’ara kallon alyasat d’aya Kara yaderai kamar besan dashi sukeba…maganar lateep ce tamakale jin ana sanarwar an d’aura auren shareef da muhibbat se najeeb da yusra sadeeq da Maryam se Kuma sulaiman da ashnah dukkansu akan sadaki dubu d’ari Allah yabasu zama lpy..

 

Se a lokacin wani k’ayataccen murmushi ya bayyana akan kyakkyawar fuskarshi Yana shafa kwantaccen sajenda yayiwa fuskarshi kawanya..shiko lateep da yusif dariya sukayi lokaci d’aya ganin yadda fuskar dake mutuk’e yanzu tawayeda anuri ahakan suka nufi gidan zuciyarsu fyass..!

 

 

Ghana

 

 

Shiru wurin yad’auka suna saurarar gimbiya halila inda take cewa abbe””””bawan Allah bawai baka zaraah ne bamasanyiba aa zaraah amanace awurunmu bamasan abunda zesakata kuka arayuwarta domin muma wani gefene ita na rayuwarmu zamu iya isko zaraah aduk inda take afad’in duniya sedai abunda ka,iya zuwa yadawo ne bamaso tinda har aka,iya yima wannan aika aikar acikin jinsinku tofa ko zaraah wata Rana zasu iya cewa sucutarda ita….

 

“”Idan ko hakan taru Sena k’ararda ahalin duk Wanda yayi gangancin yin hakan cewar bibibo dake cika Yana batsewa..

 

“”Nafahimceku Kuma insha Allah baza,asamu matsala ba inaso na inganta rayuwarta acikin mutane Yan uwanta tinda rayuwa ajinsinku bazeyuba Kuma nabaku dama na Kuma amunce ga duk Wanda yayi yunk’urin cutarda ita m

Kuhukuntashi… shikenan zance yazo karshe cewar maheerah dukkansu murmushi sukayi Banda jalaludeen daya Lula duniyar tinani Wai sune kezauneda aljanu suna magana Baki da Baki kamar mutane Yan uwansu lallai inbaka mutuba kallo bek’are makaba aduniya.

 

Kallo mama bibibo yayi yace uwar gijiyata aizakibi abbanki ko? “Eh tafad’a ahnkali kamun tace to kufa? Dariya yayi kamun yayi magana maheerah tace duk inda kike a fad’in duniya Muna taredake k’awata iyarai da mutuwa..Aiko tawashe Baki tana dariya ahakan suka shiga jirginsu se garin Abuja inda jalaludeen yabar wasu daga cikin tawagarsu subi gimbiya halila takaisu gun way’anda sukazo nema ajeji captain Usman ne yajagoranci tafiyar..

 

Bayan saukarsu Abuja akashiga yiwasu abbe shirshiryen tafiya shida mama domin basuda passport da visa…cikin kwana ukku aka gama komai inda jirginsu yad’aga zuwa *Dubai* k’arfe 4pm jirginsu yasauka Al Hassan ne kawai yasanda zuwan nasu domin Shi kad’ai jalaludeen yagayawa Aiko yayi kuka yayi farin ciki marar misal tuwa Shi kad’ai yaje dokosu tin a filin jirgin dayaga abbensu ya rungumarshi Yana kukan farin ciki dakyar abbe ya,iya Raba jikinshi danashi kana yarungumi jalaludeen daganan suka shiga mota zuwa gida mama da abbe ne abaya jalaludeen kuwa na gefen Al,Hassan ahakan suka shigo cikin stet d’in Wanda tin daga babban Gert d’in shigowa stet d’in mama taware idonta tana kallon abunda idanuwanta kegani wasu irin miyagun halittune masu ban tsoro da firgici kowanne Yana sintiri asama da makamai ahannunsu kamar masu Shirin yak’i wani mugun launi da kallar stet d’in kebadawa kamar hadari ya had’u irin me Baki da jaa d’innan Kuma be saukoda ruwaba…cikin mmkin wannan tashin hankalin datake gani suke tafe har suka K’arasa bakin pert d’in habibbty duk suka fito nan ma kallon abunda ke faruwa tsakanin pert d’innan biyu takeyi wannan dasuka tsaya dakuma wani dakecan gaba Wanda ba pert d’in kowa bane Sena ammy wasu kalar launuka kefita daka kowanne part acikinsu gakuma wasu halittun nanma abun tsoro ahakan abbe yarik’e hannunta ganin tayi tsaye suka shiga cikin perlon habibbty..!

 

 

Tofa 🤔 wannan wanne irin abune ke faruwa acikin wannan stet?

 

Shin minene alak’ar dake tsakanin mama dasu gimbiya halila?

 

Ina dangin mahaifin mama suke?

 

Shin suwaye kena hannun acikin wannan mummunan abun da,akejifar ahalin habeeb shuraim dashi wato abbe?

 

 

Wanne irin zama mama zatayi acikin wannan stet d’in me tattareda abubuwan mmki da Al ajabi bugu da Kari kartawan sojojin gidan taza Kaya atsakaninsu?

 

Duk kubiyoni acikin *SOLDIERS FAMILY* Pat 2 danjin yadda zata Kaya

 

 

Free page yak’are *SOLDIERS FAMILY* na kud’i ne nera 500 kacal 👌 ga duk me buk’atar complete 700 Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub’ar wannan nomber 👉 07037092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan nomber 👉 08107819124

 

 

 

 

 

 

Autar alheri ✍️

 

*S  F*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button