Sponsored Links
Hausa NovelsSoldiers Family

Soldiers Family 11-12

Sponsored Links

Page 11&12

__”suna Isa jirginsu yatashi zuwa Dubai..Koda suka sauka sunsamu mota samada 10 najiran saukarsu domin lateep yasarda dazuwansu wa yaransu dakenan sojojine cinjim a wurin suna jira karasowar iyayen gidan nasu…cikin takonsu na izza da tak’ama suka sauko daga jirgin zuwa cikin motocinsu Amma kamun suk’arasa duk inda sukawuce se an busu da kallon birgewa musamman Mata jikake kawai ana fad’ar wow abun gwanin Sha,awa….mota d’aya suka shiga su duka ukku inda sauran zugar mitocin suka take musu baya tareda halbawa akan kwalta.

Acan gida kuwa perlon ammy cike yake da matasan gidan musamman yaranta dake kewaye da ita suna kuka domin yau sunwayi garida wani abun mmki atareda ita Wanda yak’ara daga hankalinsu…zaune take kawai ba ko motsi numfashinta kawai zakaji ka tabbar tana Raye Dan murmushin datakeyi yanzu Babu idanuwanta sun kafe wuri d’aya…wannan abun baƙaramin daga hankalin ahalin gidan yayiba….tinda suka doso gidan gabanshi kek’ara tsananta fad’uwa zuciyarshi se tsinkewa takeyi Amma bazaka iya gane hakanba sabida bebari abun ya bayyana a face d’inshi ba….da mugun gudu motocin suka yanko babban titin stet d’in suna rabka uwar jiniya wadda kebada shedar zaratan samarin gidan sukawo ziyara.

Cikin tashin hankali daya bayyana a fuskar kowa dake wurin habibbty takalli suhaif tareda fad’ar kid’auketa amarda ita bedroom d’inta Kuma kuyi k’ok’arin Dede face d’insu karsu fahimci wani abun kamun musan abunyi Dan Allah kundai San waye alyasat basena gaya mukuba…Aiko cikin sauri alhassan yad’auketa kamar yad’auki baby yawuce da ita yayinda sadam yayi saurin Kuna tv kana kowanne yayi k’ok’arin dedeta natsuwarshi…. najeeb yace mukirkirin wani abun Wanda baze Bari yagano akwai wata matsalar ba… gaskiya kam domin dasun gammu hakan sesunyi tinanin wani abun cewar Fahad… suhaif yashare k’wallar idonshi kana yace kawai Idan suntambaya ma,iya cewa Muna meeting ne akan auren su yaya sadeeq…”eh to hakan ma yayi cewar sulaiman Wanda ko Baki berufeba suka shigo perlon.

Mik’ewa duk sukayi suna tin k’arar Yan uwannasu tareda shiga rungumarsu suna musu sannu dazuwa…Amma alyasat kamun wani yasamu zarafin ganinshi yawuce bedroom d’in ammy acikin sauri batareda yagaisada kowaba Kuma ba Wanda ya lura da hakan se Yusuf da Kuma habibbty sekuma Al, Hussain dayaje rungumarshi yakauce…Amma dai bawanda yace komi acikinsu.

Zama sukayi dukkansu anan perlon kamun lateep yace lpy kuwa naganku duka part d’in ammy? Mike faruwa ne? Murmushi ya shareef yayi Yana fad’ar bakomai fa kawai muna ɗan tattaunawa ne…da Ido yakafeshi kamun yace Anya kunada gaskiya kuwa? “Eh munada gaskiya Mana Yaya lateep suka had’a baki wurin fad’ar hakan…kallan juna akayi tsakanin yusif da lateep kana suka girgiza kansu irin akwai wata ak’asa d’innan kamun yusif yace akanme kuke tattaunawar?

Akan bikinsu Yaya shareef Mana suka koma fad’a atare kamar masu jiran tambayar? “Humm yy kyau suka fad’a atare suma domin Basu yadda ba…..alyasat kuwa yanashiga yaganta kwance alrufeta da blanket yaje yashafa fuskarta tareda Kura Mata Ido nawani Dan lokaci kana yamanna mata kiss agoshi yafito dudda jikinshi nabashi wannan bacci bana lpy bane Amma koba komai yad’an samu sauk’i aranshi tinda yaganta..

Da kallo duk suka bishi daya fitodaga bedroom d’in shiko ko kallan inda suke beyiba yakama hanyar bedroom d’inshi..”haba mijin bazakazo nagankaba konaji sanyi hakan akeyine cewar habibbty tana dubanshi…tsayawa yayi kamar karya jiyo sekuma yadawo wurinda take zaune a perlon yaduk’a tareda rungomota jikinshi Yana sauke numfashi cikin cool voice d’in yace I miss you my sweet granny… Miss you too mijin kunzo lpy? Tafad’a tana goge k’wallar da taciko Mata Ido na tausayin yaran…Kuma tayi hakan akan idon Yusuf…sun jima ahakan kamun yasaketa Yana mik’ewa tsaye hakan yabawa dukkanin Yan uwannashi gaisawa dashi hakan suka rinka rungumarshi d’aya bayan d’aya har suka gama shiko idonshi na Al, Hussain domin tinda yarungumeshi yaji yadda zuciyarshi kebugawa hanka linshi be kwantada hakanba sedai kawai yashare domin yayi duk iyayinshi na su had’a Ido yaki yadda hakan yak’ara tabbatar da zarginshi na akwai abunda ke faruwa…ahakan kowa yawatse domin suna yayun nasu wuri sunyi wanka suhuta kamun aci abinci sai su gayawa yayan nasu abunda kefaruwa domin suhaif yace, “bazaiyu su biye masaba… dukkansu ukku anan part d’in ammy sukeda dakuna jere na Yusuf ne afarko na Alyasat a tsakiya yayinda na lateep karshe acan sama Kuma suke tareda abbe d’insu hakan yasa dukan iyayensu Mata basu gansuba sedai sunsanda zuwansu tinda jiniyarsu tayi shelar shigo warsu stet d’in..!

 

Mama

Tinda wannan matar tatafi da ita Bata ajiyeta ako inaba se a k’asar Ghana acikin wani jeji me girman gaske bayan gimbiya halila ta,jiye mama taje masarautar su tasamo wasu amitattun kuyanginta su 4 tazodasu gunda ta,jiye mama bayan tamayarda wurin kamar war k’aramar rugar fulani sabida kada mamar taji tsoron zana anan…kallansu tayi kamun tace kuzauna da wannan yarinyar anan domin kuyi tsaronta Kuma kud’ebe Mata kewa kamun maheer da maheerah sudawo sune ke kalada ita Kuma kunsan ayanzu basanan bazeyu tazauna a masarautarmuba tinda ba jinsinmu d’aya ba Kuma banaso wani abun nata yacanja daga bil adama wannan ne yasa nakawotanan kokama Yara kanana kamarta kuyi k’ok’arin sama Mata abunci da abunsha irin nasu karkuyi wanj abunda zataji tsoronku Kuma bazaku samu matsala da itaba da ta sabada twins sabida hakan kukiyaye Idan kunga wani abun da be muku ba kuyi gaggawar sanardani…”angama ya shugabarmu yadda kikace hakan za,ayi insha Allah…”to ngd sosai ku kula domin wannan yarinyar bakamar saura Yara bace amanace awurunmu…insha Allah zamu kiyaye… Allah yasa gimbiya halila tace tareda duk’awa ta shafa kan mama aiko tabud’e idonta tana kallonsu…. murmushi gimbiya halila tayi kamun tace ZARAAH kinga inda zamu zauna yayi Miki? Kai mama tad’aga tana murmushin kamun tamik’e zaune tana kallan yammatan dake kewayeda ita kyawawa dadu kamarta… murmushi suka Mata itama tamaida musu kamun hankalinta yakoma gun maganarda gimbiya halila kemata…kinajinako zaraah Kinga way’annan kawayenki ne kamun su bibibo d’inki sudawo zasu naunadake kinji ko duk abunda kikeso kigaya musu zasu Miki Kuma idan kinasan ganina kigaya musu zasu kirani kinji….Kai mama tad’aga tana murmushin itama gimbiya martani tamaida Mata kana tamik’e tabar wurin ko minti biyu batayida tafitaba tadawoda abunci tabawa mama bayan taci ta koshi suka shiga fira tsakaninsu gimbiya halila batabar wurinba seda ta tabbatar hankalin mama yakwanta dawurin hartayi bacci kana tayiwa kuyanginta sallama tatafi…haka mama taci gabada rayuwa wacikin wannan jejin tareda aljanu Wanda takeyiwa kallon mutane domin sundebe Mata dukwata kewa dazata dameta sune abokanin wasarta sune malamanta sune iyayenta sune komai nata Kuma gimbiya halila nazuwa lokaci zuwa lokaci tana ganinta rayuwa tayiwa mama dad’i sosai domin batada sauran damuwa takan fita yawo itada kawayenta suzaga cikin jeji da jikin gari sukan siya Mata duk abunda tagani tace tanaso ba,abunda ke wahalarda ita se kewar eggo d’inta Idan tatunata tazauna tayita kuka dakuga hakan matsala ne arayuwata sekawai suka gayawa gimbiya halila atakeko tashafe Mata tinanin kowa nata arayuwarta Bata tinawada eggo da mahaifinta setazo sallah shima sabida tamusu addu,ane take dawo Mata da tinaninsu awannan lokacin….watanni sunja azaman mama acikin k’asar Ghana cikin wannan bak’uwar rayuwar…yau jimu,a tinsafe tatashi tana Sha,awar Shan fura..mero ce tashigo cikin bukkarsu taganta zaune tace mama miyafaru ne kinayi shiru? Allah fura nakeso mero…”ahh to shine zakiyi shiru banajena kawo miki…””nidai zanbiki yau kwana hud’u fa bamu fitaba… murmushi mero tayi kana tace to shikenan zomuje inasu Biba ne? Mama ta tambaya…duka suna waje muje duk semutafi tareko? “Eh to muje..fita sukayi suka Sami su Biba din duk suka dunguma cikin gari inda mama ke kallon tafiyace bame nisaba Amma abunda Bata saniba tafiya wunice da kwana in ak’afa zakayita itace su mero ke gajarta Mata take ganinta hakan…bayan sunje sun siyo furar sundawo sunyi nisa atafiyar cikin jijejin domin sunbaro cikin gari tafe suke suna firarsu kamar wasu sa,anan juna…juyama mama tayi nata yiwa dija gwalo domin sundan yimata nisa Aiko idonta asauka akan wani mutin Yana tafiya Yana tangad’i kamar Dan maye kamun ya yanke jiki yafad’i awurin…Ido tazaro tana cewa dija duba bayanki wani yafad’i duk atare suka juya domin atinaninsu wani jinsinsune sekuma sukaga mutinne Shi to Amma waye wannan mutumin miya shigoyi a jeji kodaiba mutumin azzikibane kamun suyi wani yunk’urin tuni mama taruga da gudu wurinshi tana tallabo kanshi kyakkyawan mutinne fari kal sedai kallo d’aya zaka masa kasan ba bahaushe bane koma wahala da tagayarar rayuwa nataredashi bud’e idonshi yake k’ok’arin yi yakasa se bud’ar Baki yakeyi alamar yunwace takassarashi cikin sauri takarb’i furarda hannun mero tabud’e robar tareda Dora masa abaki Aiko ba musu yabud’e bakin Yana kwankwad’a kamar ba,acikinshi take shigaba atake yashinye cikin sauri biba yak’ara Miki Mata wata domin tana karb’ar ta hannun mero biba Takoma takarb’o wata abunka aljanu masu saurin iska😂

Seda yashinye tass kana yashiga sauke ajiyar zuciya tareda k’ok’arin bud’e Ida nuwanshi akuma Dede wannan lokacin gimbiya halila ta,iso wurin saka Makin kiranda dija taje tayi ganin abunda mama keyi…kallon dattijon tayi tsab kamun race baba miyakawoka jije? Amma shiru beyi maganaba se Ido kawai daya bita dashi… d’agowa tayi tana kallon mama kamun tace zaraah wannan bawan Allah akwai sihiri me matuk’ar ahad’ari ajikinshi baze iya maganaba har se ankaryashi…kallanta mama keyi kamar zatayi kuka tace bayada hankaline mommah domin hakan take Kiran gimbiya halila… murmushi tayi kamun tace da hankalunshi zaraah sedai besan abunda yake daidai ba da Wanda ba dedeba Kuma besan wayeshiba….ayya mommah kitemakeshi mana😥 kanta gimbiya halila tashafa kamun race kinaso natemakamai ko? Eh tace cikin sauri… murmushi gimbiya halila tayi kamun tace to kuje dashi gida kedasu mero zasu tayaki ki kuladashi Amma maganar kariyar sihiri sedai Idan su bibibo d’inki sudawo domin seda sa hannunki za,a iya karyashi wannan Kuma seda Amin cewarsu kin yadda? Eh nayadda mommah…to shikenan tashi kuje gida zamuzo taredashi semungani nudaku waze Riga zuwa☺️ murmushi mama tayi kamun tarungumi gimbiya halila sabida harin ciki domin hakan kawai taji tanasan tsohon…itama gimbiya kiss tayi Mata agoshi kana su mero suka jata suka tafi itako gimbiya halila tashafi fuskar wannan tsohon atake baccin wahala yadaukeshi kana tad’aukeshi tare da kaishi inda mama kerayiwa dama bukka ukku ce awurin ta sakashi a d’aya kana ta zauna tana jiran isowarsu….

 

*SOLDIERS FAMILY* na kud’i ne nera 500 kacal 👌 ga duk me buk’atar complete kuma 700 ne Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub’ar wannan number 👉 07037092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan number 08107819124

 

 

Autar Alheri ✍️

🚀 *SOLDIERS FAMILY*🚀
(Romantic novel)

*By Dr Yasmeen Ahmed*

Autar Alheri ✍️

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button